Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya ce
"Tani..! Shin da kika zo nan na baki damar kiyi magana..!? Ko kuwa kinga na ware wani na tambayeshi..!?"

"A'aahh! Toh ai MALAM gani nayi yau kwana biyu amma har yanzun maganar tak'i wucewa a gurinku,, ko kuwa dan an tab'o y'ar lelenku ne,,shi yasa zancen ya gagara wucewa..!?"
Babu wanda baiyi mamakin kalamanta ba,buh da yake duk sun san hali kowa sai ya shiga tofa albarkacin bakinsa akan rashin dacewar abunda tayin
"Kin kyauta Tani.. Kuma wannan ya sake tabbatar mana cewa kece silar lalacewar rayuwar yaron nan,,wanda dalilin yasa sam baya ganin kowa da mutunci a cikin garin nan baki d'aya,,baga mutanen waje ba,hatta muma da muke gida d'aya duk ya raina mu,babu wanda ya isa yace masa yi wannan ko kuma bari wancan,duka babu wani babba a idanunsa,,to amma abunda nake so dake shi ne,tun da har kina ganin y'ar lelenmu kika ce an tab'a ko..? Tabbas baki yi k'arya ba,dan haka nake son ku kwana da shirin ku,daga rana mai kamar ta yau idan har ana son zaman lafiya damu a gidan nan,tunda gida dai namu ne ko..?? Kuma mune muke da iko da shi ko..?? Mutanen duk dake cikin gidan nan babba da yaro duka k'ark'ashin mu suke ba,,matsawar daga yau na sake ji an sake kawo mana k'arar d'anki,tofa ki kwana da sanin ni da kaina nayi alk'awarin zan d'auke shi na kaishi Maiduguri almajiranci..Idan yaso muma bakinmu ya huta da ban hak'uri,da kuma neman maganar da yake yi.."
Ba Tani ba hatta LADO ko da jin furucin baffa sai daya tsorota a dalilin yasan tunda baffan ya furta,tofa lallai ne yana iya aikatawa dan yadda yake kaifi d'aya,amma duk da haka saboda duniyanci irin na Tani bata fasa magana ba
"Ahayyeeh..! Cas..! Allah nawa! Yo Allah na tuba dan an fad'i haka shine me,,nifa wollahi na k'una bana tsoron k'auri,,zancen almajiranci kuma wollahi ba dai akan d'ana ba,,idan har za'a kai kowa a gidan nan wollahi banda nawa,,,haifarsa fa nayi bawai tsinto shi nayi a juji ba,dan haka sai dai asan wanda za'a kai amma ba LAD..!"
Marin da ya d'auke ta dashi ne ya datse k'arshen maganar tata,cikin tsananin mamaki mai had'e da takaicin tsinkata da akayi a gaban jama'ar gidan ta d'ago da niyyar ganin wane ne ya mareta haka,ido hud'u suka yi da Mijinta wato mahaifin LADO,ya sake d'aga hannu da niyyan sake wanketa da wani marin sai aka yi rashin sa'a baffa cikin hanzari yayi masa tsawa yana fad'in
"Ashsha..! Isiyaku bana sonka da saurin fushi,,me yasa zaka biye mata kaima ka aikata haka a gaban yara,,da ka bari anbi komai a sannu,saurin hannu bai kamaceka ba.."
Haushin Tani fal idanunsa ya sake watsa mata mugun kallo kana yana amsawa baffa
"Yaya ai daka kyaleni da ita,,wollahi wannan matar na rasa wace irin shaid'aniya ce ita,,duka gida tak'i zaman lafiya da kowa,sannan kai da muke kallo a matsayin babban wa kuma uba a gurinmu,ta tsaya a gabanmu tana fad'a maka magana son ranta,,wollahi Yaya dama tuni na gaji da zama da ita,hak'uri kawai nake yi tun tuni,bawai dan ina jin dad'in zama da ita ba,amma yau tunda ta fito da halinta kowa ya ganj shi kenan tayi kai,sai ta tafi gidansu dan ni dai banga dalilin da zaisa ni ci gaba da zama da matar da bata san darajarku ba..Yau d'innan aradun Allah zata tattara,sai ta barmin gida na.."

"A'a a'a..! Isiyaku baza ayi haka ba,,hakur'in dai shi za'a ci gaba da yi,,,nemi guri ka zauna tukuna muyi maganar a tsanake ko..!?"

Komawa yayi ya zauna yana zub'awa Tani mugayen kallo,ita kam har lokacin tana nan tsaye dafe kumatumta kamar mutum-mutumi,a lokacin ba komai yafi b'ata mata rai ba illa irin maganar sakin ta da yayi,wacce ko zafin marin da yayi mata a nata ganin bata ji shi ba,kamar yadda taji saukar kalamansa,a ranta tayi k'wafa mai ciwo kana ta nemi guri itama ta zauna sakamakon magana da baffa yayi mata akan idan bazata zauna ba tana iya barin gurin,,ci gaba aka yi da maganganu akan matsalar da aka samu d'in yayin da a b'angaren Tani tayi shiru tamkar bata gurin aketa maganar,a nan ne kuma baban LADO da baffa sai suka sake tsayar da magana akan duk abunda zai samu Sabina daga lokacin zuwa nan gaba dai² da k'wayar zarra aka ce musu yau ga wani abu ya sameta tofa kafin su tuhumi kowa zasu fara ne ta kan LADO tunda an faro da shi daga haka,gaba basu san me kuma zai sake yi mata ba,,after kuma aka musu tsakani,nd babansa yace ko kallon banza idan yayi KUSKUREN yi mata taji bata gamsu sa shi ba tazo ta sanar masa,shi da kansa zai d'auki matakin daya dace,,nd idan har ya sake ta kawo k'ara akan shi ko abokansa sunyi mata wani abu,tofa ya kuka da kansa,,,bayan duk an gama da waccan maganar sai baffa ya sake jaddada musu hukuncin sa na soke batun auren gida da yayi,inda yace daga yau kowannensu ya fita waje ya nemo matar da tayi dai² da ra'ayinsa,,ko da aka gama baban LADO sai hak'uri yake bawasu baffa dan shi kam ji yake duka ya muzanta a idanun y'an uwan nasa,sai da baban Sabina ya nuna masa jan ido sannan suka samu kansa yayi shiru amma kana kallonsa zaka tabbatar abun ya tab'a shi Sosai.Ko da baffa ya tabbatar babu wani mai k'orafi nan take duka ya sallame su ba tare daya nemi shawaran wani a cikin k'annen nasa ba,duk dama dai ya san halinsu akan duk hukuncinsa bazasu tab'a jaba sak dai suyi na'am,,a hankali duk yawan su suka shiga watsewa kowa ya nufi harkokin dake gabansa,kafin kace me tuni sai ga gurin ya dawo fayau babu kowa sai su baffan da suka yi saura su uku,suna sake tattaunawa akan matsalolin da suke fuskanta game da LADON..

A can campus kuwa tun bayan da Muhammad suka dawo hankalinsa kacokam sai ya maida shi kan karatunsa kasancewarsa mutum mai k'wazo,nd duk wasu al'amura da basu shafi harkar skul ba duka ya tattara su ya maida gefe,nd yaci gaba da tunkaran exam dake gabatowa kasancewar semester da suke tazo ending,,while a gefe guda kuma kullum zuciyarsa tana kan tunatar da shi *ALK'AWARIN* da yayi ma baffa na kai musu ziyara idan har ya samu sarari.

*Almost 2 weeks leave...*
A duk tsayin wad'annan kwanakin da suka gabata,kullum cikin sa rai yake akan zai samu chance na zuwa,buh maimakon ace lamura sunyi masa sauk'i sai ma sake cakud'e masa suke,,duk da kullum cikin son zuwan yake amma daya motsa can nan wani uzurin zai sake gifto masa da zai hana masa zuwan kamar yadda yayi niyya,deeply kuma a kullum da tunanin zuwan yake tashi yake kuma yini sai dai babu wani isashen lokaci a gare shi.

Yau ranar ya kasance Friday,,ganin ba wani jimawa za suyi a skul d'inba sosai sai yasa shi fitowa cikin shiri,a zuciyarsa yana saka ran zuwa ya gaida dattijan,,da misalin 10am suka fito a lectures wanda kuma daga shi d'in sai ya zama basu da wani sauran abu daya rage musu a skul d'in,banda su zauna tutorial (ma'ana su k'arawa juna sani akan abubuwan da suka shigewa wasu cikinsu duhu) lokacin kam ko da yaga prof ya tattara kayansa zai fice daga lecture hall d'in da sauri shima ya mik'e yabi bayansa kamar wanda yake shirin tambayarsa wani abu,buh suna fitowan sai kawai ya kama hanya abunsa ya bar gurin,kai tsaye motan da Sultan ya d'auko shi wancan ranar da suka fara had'uwa ya d'auka sannan ya fice a skul d'in,kasancewar shi kad'ai ne a cikin motar shi yasa sai ya shiga fella gudu abunsa a saman kwaltar ba tare da damuwar komai a ransa ba,,within 10 minutes ya iso dai² bakin hanyar da suka rako shi wancan had'uwar,can daga d'ayan side dai² inda ya tsaya ya kira sultan a waya yazo ya d'auke wancan ranar yayi parking kana yayi sallama wa mutumin daya gani zaune kana ya barma masa ajiyan motan a gurin mutumin,duk da ba wancan mutumin ya tatar ba,,sannan ya tsallaka titin yana nufar hanyan da zai shigar da shi cikin d'an k'auyen nasu Sabina,,yayi tafiya mai d'an tsayi kafin ya iso inda castle na rugar yake,kai tsaye k'ofar gidan ya yunk'ura kana ya samu guri ya tsaya yana tunanin yadda zaiyi ya samu wanda zai aika,ko da ya tsaya a k'ofar gidan kuwa bai yi mamakin yadda aka yi ya iya dawowa ba duk da uban jejin daya yake tsakaninsu da titi nd sai mutum ya wuce shi kafin ya riski inda gidajen nasu suke,ya kwashe ak'alla mintuna sama da biyar a tsaye a k'ofar gidan shi bai lek'a yayi sallama ba kuma shi bai tafi bazhaka nan ba tare daya samu d'an aike ba,,a haka mintuna biyu suka sake zuwa suka wuce kafin ya hango wasu yara can nesa da shi suna tahowa,sai daya jira har suka k'araso inda yake sannan ya musu magana akan suyi masa sallama da masu gidan.....


*Ga masu tambayan number na ga shi nan zan ajiye muku ita,buh dan Allah kada namijin daya min maganar na saka shi a group,duk groups d'ina bani da wani group dana bud'e saboda maza,,Pleasee nd please dan Allah kada namiji ya d'auka number na,,,ban iya wulak'anci ba,amma duk namijin daya d'auka zanyi blocking nasa,kada kuce ban fad'a muku ba,wannan shi ne doka na nd ina fatan za'a kiyaye 08165726609,,na gode da soyayyar ku gare ni,,lurv u more n more..*💝


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*8*
_#Hidden_

Shigar yaron zuwa cikin gidan da fitowarsa duka ko minti uku ba'a d'auka ba,sai ga baffa ya fito da mamakin wanda yake sallama da shi,,a tsaye ya iske Muhammad ya jingina a jikin k'atuwar bishiyar maina dake k'ofar gidan,fuskarsa cike da fara'a ya k'araso inda yake yana fad'in
"Lale marhaban..!"
Shima murmushin yayi yana nufar baffa dake tahowa,nan suka had'u a tsakiyar awning na k'ofar gidan,durk'usawa yayi har k'asa da niyyar gaida baffan yayin da shi kuma baffa yake mik'a masa hannu alamun su gaisa yana kuma fad'in
"A'a! Mai babban suna ba haka addini ya nuna mana ba,,mik'e tsaye mu gaisa a haka..Wannan ai al'ada ne."
Kunya ce ta kama shi dan shi a ganinsa idan har yace zai gaida baffan a tsaye ba k'aramar rashin kunya yayi ba,,amma kuma saboda baffan ne yace masa ya mik'e d'in,ganin babu yadda zaiyi sai ya mik'e tsayen yana mik'awa baffa hannu cike da matsananciyar kunyarsa,musabaha suka yi while still yana rage tsayinsa had'e da kallon k'asa,sun gaisa da baffa cikin mutunci da girmama juna kafin baffan ya sake kallonsa,kallo irin na tsanaki,duk da bawai baffa ya san tsadar kaya ba da sauran ababen more rayuwa ba,amma daga tsarin shigarsa zuwa yanayin fatar jikinsa kad'ai sun sake tabbatarwa da baffan cewa lallai ne daga gidan masu da shi ya fito,buh kasancewar ba abunda ke ran sa ba kenan sai ya ce
"Yanzu mai babban suna banda abunka ai kai ka zama d'an gida,mene ne abun tsayawa a waje ka nemi d'an aike..!?"
Murmushin dai still yake sake yi sannan ya amsawa maganar baffan
"Baffa gara dai nayi hakan,shiga gidan mutane kai tsaye ai ba addini bane,dole ne duk mutum mai hankali kuma wanda yasan ya kamata,sannan ya fahimci addini dole ne ya tsaya ya nemi izini gudun fad'awa halaka,kamar yadda Allah (S.W.T) ya bayyana mana a cikin littafinsa mai tsarki cikin suratun nur (verses 27-28) game da shiga gidan mutane
"Ya ku wad'anda suka yi imani.! Kada ku shiga gidaje wad'anda ba gidajen ku ba har sai kun sami izni,kuma kun yi sallama a kan ma'abotansu (ma'ana mammalaka daga gidan).Wannan ne mafi alkhairi gare ku,tsammaninku,za ku tuna.To,idan ba ku samu kowa a cikinsu ba,to kada ku shige su,har sai an yi muku izni.Kuma idan an ce muku,"Ku koma." Sai ku koma,wannan shi ne mafi tsarkaka a gare ku.Kuma Allah game da abin da kuke aikatawa,Masani ne.."
To kaga kuwa baffa wannan hujjar itace tasa ni tsayawa a nan,saboda kada na sab'a dokar da mahaliccinmu ya shimfid'a a gare mu.."
Tun daya fara janyo masa ayoyin baffa yake bin tafsirinsu har ya dasa aya a bayanin nasa,kallon tsanaki baffa ya sake binsa da shi fuskarsa cike da tsantsar farin ciki,cikin gamsuwa da abunda Muhammad ya fad'a d'in ya sake rik'o hannunsa sosai yana fad'in
"Lallai kayi gaskiya,kuma hak'ik'a nayi matuk'ar farin cikin had'uwa da mutum kamar ka,,a iya tsayin shekaruna a wannan k'auyen tunda nake ban tab'a ganin matashi daya had'a nagarta kamar ka ba,kai abun alfahari ne a cikin duk wani ahalin da suka same ka,ta ko wane fanni halayenka abun ayi koyi da sune,,ka godewa Allah da irin baiwar da yayi maka,sannan kaci gaba da kiyaye abunda ka riga ka sani..Allah yayi maka baiwa mai girma,ka kuma godewa mahaifanka domin sunyi matuk'ar k'ok'ari wajen gina rayuwarka da ilimi,,fatan Allah yayi musu tukuici da gidan aljannah,dan nasan jajircewarsu ce ta kaika ga zama abunda ka zama a yau.."
Da "ameen" ya amsawa baffa yana mai jin dad'in irin yabawa iyayensa da baffan yayi bisa jajircewarsu akan tarbiyyarsa,,,nan baffa yaja shi suka shiga ciki,suna tafiya baffa yana sake jadadda masa kan cewa,nan gaba ko da yazo kada ya sake tsayawa a k'ofar gidan wannan umarnin sa ne gare shi,kuma shi ya bashi damar shigowa kai tsayen,,godiya yayiwa masa dai² lokacin da suka shiga d'akin da baffa ya saukar bak'inshi,sun sake gaisawa a mutunce da tambayarsa karatu zuwa sauran harkokinsa,kafin baffa yayi niyyar fita yana fad'in
"Bari na nemo Aminu yazo ku gaisa ko..!?"
Godiya ya sake yiwa baffan,after kuma ya fita ya barshi shi kad'ai,sai ya d'auko phones d'insa dake cikin aljihunsa ya zube su a gabansa,d'aya daga ciki wacce ta kasance k'irar samsung galaxy s10 plus ya d'auka ya fara clicking cikin kwanciyar hankali,kira ne ya shigo masa dai² lokacin yayin da sunan *SULTAN* ya shiga lilo akan screen d'in,tuna dalilin da zaisa ya kira shi sai yasa shi ajiye wani slender breathe,daf da kiran zai katse ya d'auka had'e da sa wayan a hands free,,muryan sultan kamar zai Faso wayan yake fad'in
"Hello..Man ina ka shige ne..!? Duka class sai neman ka ake,,ka sanfa kai ake jira,shi ne zaka shanya bayin Allah,me hakan yake nufi..!?"
Sai daya bari sultan ya dasa aya kafin ya bashi amsa
"Ka aike nine da kake tambayata inda na je..!?"
Da mamaki a cikin muryan sultan yake fad'in
"Bala'i..! Ba dai ace ka fice a skul ba..!?"
Siririn tsaki yaja kana yace
"Ehenn.! Dafa.?"

"Tabbb' amma dai mutumin nan ka cika d'an rainin sense wollahi,banda tsabar wulak'anci kasan bayin Allah nan sun saba jiranka,kawai sai ka fice ka barsu a nan,without taking excuses..??"

"Hey! Man..Mene ne abun wulak'ancin a nan..? Shi kenan sai aka ce ni ba zanyi nawa uzurin ba,sai dai kullum naita aiki bani da lokacin hutu..!? An fad'a maka agogo ne ni da bazan huta ba..!?"

"A'a..! Ni kam ban ceba,,amma dai da kasan zaka fita,sai ka sanar dasu kaga ba sai sunyita jiranka ba..!"

"Ok..good.! Buh why don't u expiate me..kaga kenan zai zama basu yi jiran banza ko..!?"
Murmushi sultan yayi kafin ya ce
"No man..! Kafa san bana iya tsayawa gaban jama'a haka nayi magana kamar kai...Kawai dai ka san yadda za kayi da su,,suna nan suna jira..Nd zanma sanar dasu nan da 10 minutes zaka dawo..!"
Cikin sauri ya tari numfashin sultan d'in yana fad'in
"Tabbb' wollahi kada ma ka soma,dan ni nan da ka ganni bana kusa,nd yanzun ma banga lokacin dawowa ba..Idan ka sasu jira kai ka sani,ni bance kowa ya jira ni ba.."
Murmushi sultan yayi cikin tsokana kafin ya sake cewa
"To wai kai ina kaje ne haka da wannan safiyar ma.!?"

"Ina ruwanka da inda naje..ko kuwa dai salon sa idonka ya motsa..!?"

"Aaa! To Allah ya bada hak'uri,,, amma dai da alamun ko..!"

"Ko me..!?"
Ya sake tarar numfashinsa,,dariya sultan yayi yana fad'in
"No..! Babu komai,kawai dai sai ka dawo d'in.. Buh when ma zaka dawo ne..!?"

"Wai kai ina ruwanka ne da inda naje,ko sanin lokacin da zan dawo,,ka aiki ni ne..!?"

"Allah baka hak'uri.. Sai na ganka."
Daga haka sultan ya katse kiran yana murmusawa,while a fili kuma yana furta
"Idan tayi wari dai zamu ji..!"

A can gefen Muhammad kuwa koda yaji sultan ya katse kiran wayan,tab'e baki yayi kana yaci gaba da abunda yake yi a phone d'in nasa,yana kuma jiran ganin dawowarsu baffa.

Cikin nutsuwarta take takowa,sannu a hankali har ta zo bakin k'ofar d'akin,,dai² ta cire takalmanta tana niyyar yin magana his uniquely perfumes aroma suka kaiwa hancinta ziyara,a hankali ta maida kyawawan idanunta ta lumshe yayin da k'irjinta yake tsananta bugawa,while kyam ta mak'ale a gurin ta kasa koda motsa even bakinta bare ta iya yin sallama,,duk da bawai ta ganshi bane,ko kuma ace ta ga even a clue da zai bata tabbacin ya zo gidan,amma haka nan zuciyarta take shaida mata yana nan a kusa² da ita,,sai data shafe ak'alla mintuna uku cikin mugun yanayin zurfafa a tunani kafin taja dogon ajiyar zuciya,sai data gama saita nutsuwarta sannan ta motsa harshenta da kyar tana furta kalmar sallama,,yana zaune a cikin d'akin yayin da yayi flexing legs d'insa tamkar basarake muryanta ya doko shi,sai daya d'ago kansa daga kan wayan sannan ya amsa mata da wannan husky voice d'in nasa a lokacin Sabina tuni har ta shigo ciki hannunta d'auke da mug na robber mai kyau,,kallonta ya d'anyi a fakaice kafin ya janye idanunsa akanta yaci gaba da abunda yake yi akan wayansa,,itanma ko data shigo nd taji wani muryan daban ya amsa mata sab'anin na baffanta da take tsammanin yana cikin d'akin,duk da ta fahimci ko waye ya amsa d'in sai data waiwaya ta kalli inda yake,a nan tayi arba da shi a zaune kamar yadda baffa ya fita ya barshi,cikin shigar kayan mu na hausawa,shadda ne zubin feitex material getzner fara sol sanye a jikinsa wacce darajarta ya kai 58k+ ta sha d'inkin zamani,haka nan kansa sakaye cikin hular zanna wacce ta b'oye suman kansa,haka nan ta k'ara masa kwarjini da k'ima,banda haske da k'amshi babu abunda yake bazawa tamkar wanda ya juye tandun turare a jikinsa,,da kyar ta samu tajanye idanunta akansa kana ta matsa daf da shi ta ajiye mug d'in a gabansa,kallonta ya sake d'agowa yayi musamman ganin ta ajiye a kofin a gabansa,ba tare data sake kallonsa ba cikin zazzak'ar muryanta bayan ta nemi guri ta zauna ta furta
"Barka da safiya..!"
Kamar bazai amsa taba dan yadda yake sake binta da kallo,wanda itama kanta Sabina a lokacin tayi tsammanin ko bai jita bane,hakan sai yasa ta d'ago kad'an ta d'an kalle shi,nan take kuma sai taji ya amsa mata da
"Kin tashi lafiya..!?"
Kad'an ta sake sunkuyar da kanta k'asa zuciyarta na skipped buh cikin dakewa itama ta amsa masa
"Lafiya k'alau.. Ya ka koma gida..!?"
D'agowa ya sake yi ya kalleta,while yana d'age one eyebrow d'insa kamar mai son nemo amsa ya amsa mata a tak'aice
"Lafiya Alhamdullah..!"
Shiru tayi daga haka bata sake magana ba dan duka iya kalaman da taji zuciyarta zata iya furtawa kenan a lokacin,,shima gogan shiru yayi sannan ya d'auke kai,daga hakan still sai yayi kamar bai san tana gurin ba,yayin da zaman shiru ya ratsa tsakaninsu,sun shafe ak'alla mintuna goma a haka zuwa can ko daya gaji dan kansa sai ya ajiye wayan hannunsa,unexpectedly Sabina taji muryansa a cikin kunnuwanta yana fad'in
"Bakya zuwa skul ne..!?"
Kai ta d'am girgiza kad'an kafin tace
"A'a,, ai tun d'azun muka taso.."

"Ok..! Good..!"
Abunda kad'ai yace kenan daga haka kuma bai sake magana ba dan jin sallamar su baffa a k'ofar d'akin,saurin mik'ewa Sabina tayi zata fita nd tana amsa sallamar su baffan,shima d'in sallamar ya amsa kuma yana binta da ido ganin tana shirin fita,kamar zaiyi mata magana kuma sai ya fasa,a tare su baffa suka shigo da Babanta,bayan sun musu barka da dawowa Sabina ta fice ta nufi cikin gida,a lokacin baffa ya kalle shi yana murmusawa da cewa
"Mai babban suna ince dai baka gaji da jira ba ko,da kaji mu shiru.!?
Fad'in baffa da yake neman gurin zama
"A'a baffa babu komai.."
A mutunce suka gaisa da Baban Sabina,inda baffa yake yiwa Muhammad bayanin sai daya dangana da zuwa gona sannan ya samo Aminu d'in,murmushi ya sake yi daga haka suka ci gaba da d'an tab'a hira da su,,sai daya samu ak'alla awa guda a k'auyen yana tare da su suna ta hira sannan yayi musu sallama da niyyan komawa,,wannan karon ma har bakin titi suka rako shi buh wannan lokacin baffa da Babanta suka rako shi suna ta masa godiyan ziyara daya kawo musu,sai da suka ga ya tsallaka sannan suka kama hanyar komawa,shi kuma nan ya nufi inda ya bada ajiyar motansa yayiwa mutumin godiya,bayan yayi masa alkhairi kuma ya d'auki hanyan komawa skul..

Wasa² rayuwa ta fara yin nisa a tsakani,yayin da zuwa wannan lokacin tsakanin iyayen *SABINA* da *MUHAMMAD* zumunci mai k'arfin gaske ya sake k'ulluwa,,yayin da a b'angaren Muhammad kuwa a iya tsayin wannan lokacin ya kasance yana yawan kai musu ziyara lokaci zuwa lokaci idan ya samu dama,,,suma kansu dattijan biyu a tun bayan had'uwarsu da shi duk lokacin da zai zo d'in suna jin dad'in hakan sosai,haka shima a duk lokacin da yazo d'in har ya koma yakan tsinci kansa cikin tsantsar farin ciki da jin kamar yana tare da wani b'angare na ahalinsa,,a haka ne lokaci ya gangaro dan kuwa har sun yi exam sum gama sai dai tunda ya fara bai samu dama ya lek'a suba,ko da suka kammala exam d'in a lokacin da sun samu break irin na tsakanin semesters,sai yayi shirin komawa zuwa gida,sai dai ko kafin ya tafi d'in sai daya je k'auyen domin yayi musu sallama dan yasan zai kwana biyu acan,a nan ne yake shaida musu ya samu hutu zai tafi gida saboda ya jima bai jeba,kuma hutun zai d'auke shi tsayin lokaci kafin su sake had'uwa,,ko kafin suyi sallama da shi d'in tuni su baffa suka shiga hada-hadar had'a masa tsaraba,sosai suka cika shi da alkhairi had'e da tsaraba mai yawa,duk da a gurinsa bai so tafiya da komai ba dan gudun kada yaje gida a tuhume shi,buh yadda su baffa suka nuna rashin jin dad'i akan k'in amsar kyautar tasu sai yasa shi amsa kana yayi musu godiya,sannan suka sake yin sallama yana sake jaddada musu shi da dawowa sai ya k'are hutunsa.

Lokacin ko da suka fito daga d'akin da baffa yake saukar sa nan suka tsaya a tsakar gidan suna sake

Please Login or Register in order to submit comment