Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


"Uhhuumm..!" Shi ne abunda Badra ta iya fad'a ba tare da tayi magana ba tabi bayanta da sauri,,a k'ofar gida ta isketa ko inda yake bata k'arasa ba ta coge a guri guda,,shi kuma gogan yana zaune cikin mota yana kallonta tun data fito yake kallonta amma yak'i fitowa,yadda ta tsaya rai b'ace yasa jin babu dad'i,duk da dama yasan za'a rina,,a hankali ya sauke glasses d'in dake gefensa ya yafito Badra da hannu,wuceta tayi ta isa inda yake bata ko kalli inda take ba,shima d'in tana k'arasowa ba tare daya kalleta ba yace
"Mene ne ya faru.??"
Tana kallonsa tace
"Babu komai.."

"Kin san bazan yarda ba ko..? Fad'a min gaskiya me aka yi mata.!"
Sunkuyar da kai tayi k'asa tace
"Inna ce tayi mata fad'a.."

"Akan mene ne..??"
Sake sunkuyar da kai tayi sannan tace
"Cewa tayi baza ta zo ba."

"Shi ne sai aka yi mata fad'a akan wannan y'ar maganar..??"

"Ehh.! Haka ne.."

"Me yasa baki zo kin fad'a min ba to kika bari aka b'ata mata rai..?? Kina son ganin b'acin raina akan ki ko..?"
Saurin d'agowa tayi tana kallonsa da fuskar damuwa
"Yah Hammad..! Bafa haka bane.."

"Uhhuumm.! Fad'a min yaya ne to..?"

"Nifa bani na fad'awa Inna ba,,kawai taji maganar ne,kuma lokacin zan fito na fad'a maka sak'on shi ne Innar tayi mata magana.."
Sai lokacin ya kalleta shima a kaikaice ya tab'e baki sannan yaci gaba da magana
"Kin tabbatar bake kika fad'a aka mata fad'a ba..??"
Dai² mak'ogoronta tayi saurin rik'owa tana sake marairaice masa kamar za tayi kuka tace
"Na rantse Yah ni bance komai ba.. Ka yarda dani,wollahi ko su Jannat ma ka tambaya kaji zasu fad'a maka..!"
Yadda idanunta suka fara tara ruwan hawaye ya sashi jinjina kai ba tare da damuwar hawayenta da yanayin da tayi maganar ba yace
"Uhhuumm..! To da kyau.!"
Daga haka kuma yayi shiru bai sake magana ba kuma bai kalli inda ita kanta Sabinar take tsaye ba,,tsaiwa Badra taci gaba da yi while shi kuma yana kallon tsuntsuwar tasa data mak'ale a guri guda ta wutsiyar idonsa,sai daya d'auki ak'alla mintuna biyar yana kallonta kafin ya juyo yana murmusawa ya kalli Badra data kasa tafiya
"Tsaiwar me kike yi ne kuma..?"
Fuskarta da damuwa ta kalle shi tace
"Yah..! Naji ne kayi shiru baka ce na tafi ba ai.."
Wani irin kallo yayi mata na ban gane me kike fad'a ba kafin ya ce
"Sai kici gaba da tsaiwa ai,idan nace sai ki tafin..!"
Yadda yayi maganar kamar da gatse yasa ta fahimci yanayin da yayi mata maganar,a hankali sai taja k'afafunta ta bar wajen,tana zuwa dai² inda Sabina ke tsaye ta kalleta sosai k'asa² tace
"A nan zaki tsaya ne madam..?? Ko kuma dai saina shiga na fad'awa Inna har yanzun baki ji maganar ta bane..??"
Saurin kallonta tayi ba tare da Badran ta tsaya jin abunda zata fad'a ba tayi cikin gidan da sauri gudun kada ta janyowa kanta fad'an Yayan nata da cikin k'ank'anin lokaci duk ya rikid'e ya koma wani masifaffe,,haushin yadda ake neman takurata tayi abunda bata so shi ne ya sake kamata,a hankali kuma maganar da Badran tayi kafin ta shige yayi mata reverse cikin kwakwalwa,gauron numfashi ta sauke bayan tayi tunanin idan har Inna taji labari zata sab'a mata,tayi saurin kawar da tunanin k'in zuwa inda yake a ranta,jiki babu k'wari ta d'ago ta sake kallon motar nasa sannan taja k'afafunta zuwa inda yake.
Tunda ta fara tahowa yake kallonta,sai dai ba lallai ne ayi saurin fahimtar hakan ba bcos ba directly yake kallon nata ba,shi yasa babu yadda za'ayi mutum yayi saurin fahimtar hakan,sai dai ko shi da yasan siririn yin hakan a gurinsa,murmushi ya saki wanda yake sake bayyanar da asalin cikar kamalarsa a dai² lokacin data k'araso,sannan ya d'age glasses d'in zuwa sama bcos baya so ya bata fuskar da zata nemi ta jashi a k'asa,duk da yasan tana yi masa kallon mai laifi,,yadda yayi lokacin data k'araso sosai yasa ta d'agowa ta kalli motar,gaba d'aya glasses d'in jikinta tint ne,saboda haka ba lallai ne a iya gano wanda ke ciki ba bare kuma a iya gano abunda yake yi,,a gefe ta sake tsaiwa a tunanin ta ko zai fito,amma sai taga ya bud'e mata d'ayan side d'in na mai zaman banza,sai data gama jan class d'inta kafin ta zagaya ta shiga ta zauna,shi ya rufe k'ofar had'e da locking motar gaba d'aya ta yadda babu yanda za'ayi ta iya fita ko wani shigo har sai idan shi ya bada damar yin hakan,ba tare data kalleshi ba tace
"Mene ne nufinka na zuwa gidan mu ne..?"
Kallonta ya d'anyi bai ce komai ba yayi shiru,sake maimaitawa tayi still yak'i yin magana,haushin shirun da yayi mata yasa a fusace ta d'ago ta kalle shi,cikin azababben fad'a mai tafe da kishi tace
"Wai me kake nufi da ni ne..??"
Sai lokacin da tayi maganar sannan ya juyo ya kalleta fuskarsa d'auke da murmushin dake narka mata zuciya ya zuba mata idanunsa daya shanye
"Me aka yi miki ne My Lady..?"
Sosai tambayarsa ta bata haushi,sai dai ta daure bata tanka masa ba
"Nayi tunanin ko da kika zo ya kamata ne ace kin nema min amincin Allah,amma kin shigo min babu sallama,nd kina tuhumata abunda nake nufi dake,without kin yimin kara kin gaishe ni.!"
Ya k'are maganar dajifanta da hararar wasa,kunya ta d'an ji da yayi maganar,sai kawai ta juya masa k'eya da fad'in
"Assalamu alaika.!"
Sai da yayi murmushi mai sauti kafin ya amsa mata da
"Wa'alaikis salaam warahmatullah wabarkatuh.!"
Har lokacin bata juyo ba tana kallon waje tace
"Ina yini.. Ya mutanen gida..??"
Shiru yayi mata bai bata amsa ba shima akan lokaci sai daga baya yace mata
"Komai lafiya."
Itama daga hakan sai tayi shirun bata sake ce masa komai ba,a haka har suka d'auki tsayin mintunan da su kansu basu san adadin su ba,gajiya yayi da zaman shirun yana kallonta yace
"Wai ke haka ake yi ne,mutum yazo wajenki amma sai kiyi masa shiru.?? Me kike nufi ne Yallab'iya..?"
Bata kalle shi ba k'asa² tace
"Abunda duk kake nufi da ni nima shi nake nufi.."
Kallonta yayi sosai jin yadda ta bashi amsa kai tsaye duk da bawai tayi don yaji ba
"Wai mene ne matsalar ki ne Lady..?"

"Kafi kowa sanin matsalata ai.. Mene ne na saurin tambaya..?"
Murmushi ya sake yi,cikin sanyin magana yace
"I dunno Lady,,kinga ya kamata ki fad'a min sai na sani ko ba haka ba..??"
Juyowa tayi ta kafe shi da kallon mamakin abunda yake fad'a,wai bai san abunda ke damunta ba yake cewa,bayan yafi kowa sanin abunda aka yi,ita zai rainawa hankali ya fad'a mata wannan maganar banda ma ya rainata,,maganar Sultan ce ta dawo mata kamar yanzun yake yi
_"Ur Lady fa.!? Dama itace amaryar kake wani nok'ewa,sai cewa kake baka so,,ashe duk munafirci ne abun.."_
Yanayin kallon da Hammad yayiwa Sultan lokacin da yayi maganar shi ne abunda yafi komai d'aga mata hankali da tsaya mata a rai,dalilin da yasa tayi saurin fahimtar akwai wani abu a bayan maganar da yayi,dan haka da sauri ta fahimci komai duk da bai k'arasa ba
"My Lady.. Kin daina magana ne..?"
Tsabar haushinsa da take ji a lokacin bai hanata tambayar saba
"Me ka gani..??"

"Naji kinyi shiru ne,,kiyi min hira mana.."

"Da baka nan waye yake maka ne..??"
Murmushi yayi mata mai kwantar da hankali yana bata amsa a lokaci guda
"Lokacin da bana nan,,aiki baya barina zama da kowa,,amma yanzun tunda gani ga ki kinga zaki d'ebe min kewa ko.??"

"A'a'a.. Ni ban iya ba ai.."

"Wane ne ya iya kenan..?"
Ya tambaya yana kallonta
"Amaryarka mana..!"
Sosai maganar ta zo masa a bazata,gyara zamansa yayi yana fuskantar ta while ya kwantar da kansa jikin seat sai dai bai ce mata komai ba akan maganar da tayi,yayi k'ok'arin canja musu hiran da fad'in
"Babah yana gida ne ko ya fita..?"
Bata kalle shi ba tace
"Mene ne zaka yi masa..??"

"Ina ruwanki da abunda zanyi masa..?? Ko ke dana kira ki kika ce ace min baza ki zo ba wani ya tambayeki abunda ya had'a mu kika fad'i hakan.?"
Tab'e baki tayi alamun bata ji haushin maganar ba sannan kuma bata bashi amsar tambayar da yayi mata ba,haka tabarshi yayi ta magana duk da ba ma'abocin yinta bane,da ya gaji shi da kansa ya kyaleta,yana sake maimaita mata tambayar da yayi mata da fari game da Baba,still ta sake masa shiru bata kalle shi ba dan tana jin bata yi niyyar magana ba,d'agowa yayi daga jikin seat daya kwanta ya matso daf da ita
"Wai mene ne yake faruwa dake ne..? Na kasa fahimtar inda kika nufa fa..??"

"Ai kuwa bana tunanin zaka gane in dai haka ne."

"Me yasa haka to.!?"
Kallonsa tayi a fakaice sannan tace
"Babu amfanin nayi maka bayani bcos bana jin zaka fahimta.."
Murmushi yayi mai sauti,kafin ya kyalkyale mata da dariya,irin wacce daga ji zaka fahimci shak'iyanci da rainin wayi yasa shi yin ta,a cikin dariyar yake mata magana
"Ke yarinya ce ai har yanzun.."
Saurin kallonsa tayi tana nuna kanta da fad'in
"Ni ce yarinyar..!?*

"To idan ba keba da waye nake..?"
Baki ta murgud'a masa tace
"Wollahi ni ba yarinya bace,,sai dai idan wannan mai bak'ar fuskar kake fad'awa haka.."
Sake kyalkyalewa yayi da dariya ita kuma ta had'e rai a dole taji haushinsa,ganin ba shi da niyyar daina dariyar ya sake tunzurota,a fusace ta nemi bud'e motar ta fita,saboda haushi har ta manta ya rufe motar tun shigowarta,sai da tayi iya yinta ta bud'e ta kasa ta juyo tana kallonsa
"Bud'e min ni na fita.."
Dakatawa yayi da dariyar da yake mata yana tambaya
"Ina ne zaki je..?"

"Inda na fito.. Bud'e min ni dai na wuce.."
Yana kallonta yace
"Wai wace cema mai bak'ar fuskar ne.?"
Harara ta wurga masa tace
"Matar ka mana da zaka aura.."
Murmushi yayi mai sanyi yana dafe saitin zuciyarsa,a hankali ya lumshe idanunsa yana fad'in
"Bak'ar fuska ne dama dake..??"

"Ban gane ba..??"

"Dama baza ki gane ba ai."

"Saboda mene ne bazan gane ba to..?"

"Ban fad'a domin ki gane ba.. Idan ni na fahimta ya wadatar.."

"Uhhuumm.!" Tace ta sake jan baki tayi gum daga haka bata sake magana ba.

*Some hour's leave...*
Sai wajen Maghreb sannan Baba ya dawo gida,tun daga k'ofar gida da suka gaisa,Baba cikin tsananin mamakin ganinsa yasa ko tsayawa bai iya yiba,ya wuce cikin gida,a lokacin kuwa tuni su Badra har driver ya zo ya maida su gida,,shigarsa bai ko zauna ba ya kabartawa Ina wanda Allah ya nuna masa,murmushi tayi cikin zuciyarta tana mai yiwa Allah godiya had'e da yi masa tsarkaka kuma mafiya dad'in kirari, daga nan suka tsunduma hiran abunda suke ganin zai fishshesu.

Gaba d'aya hirar tasu fiye da rabinta shiririta ne a cikinta,in banda tsokana da neman fitinannen babu abunda yayi ta mata,tun tana jin haushinsa ita da kanta ta sauke,,duk da a gefenta da farko idan ya fad'i magana ko ya tambayeta sai dai ta bashi amsa a tsaye,,a hankali cikin hikima yayi ta tsokanar ta yana watso mata tambayoyi cikin hikima,,duka basu wani jima sosai ba tuni ya gama fahimtar damuwarta,yinin ranar gaba d'ayan a unguwar yayi shi tare da ita.
Dama zaman yayi shi ne ba don komai ba sai domin ya jira dawowar Babanta,coz yana maganar da yake son su tattauna sa shi tunda Allah ya dawo da shi,,a wannan ranar tunda Hammad yazo bai yarda ya tafi ba sai da tarihi ya maimaita kansa a gurin iyayenra,bayan an tuna baya ya basu labarin yadda rayuwa tayi masa bayan barinsu da yayi,da duk abubuwan da suka gabata a raguwarsu gaba d'aya,ciki kuwa harda Baffa zuwaa mutuwarsa,wacce tayi matuk'ar girgiza Hammad,,dattijon arzik'i mutum mai kamala da sanin ya kamata,ga daraja mutane ko da bai sansu ba,,bayan da k'ura ta lafa duk dama dai ba wani tashin-tashina suka yi ba,kasancewar suna sane da bayanin da baffan Inna yayi tun a wancan lokacin,shi yasa ko da yayi musu bayanin abunda ya faru basu ga laifinsa ba,suka dangantaka faruwar hakan a matsayin K'addarawa ta ubagiji.
Bayan duk sun gama magabar suka ci gaba da hira irin wacce aka jima ba'ayi irin ta ba,,sai da dare ya riske shi sosai sannan yayi niyyar tafiya,bayan yayi musu sallama da alk'awarin dawowa gobe idan Allah ya kaimu,fatan alkhairi suka yi masa duka,sannan yayi hanyar fita yana sake yin sallama da su,,Inna ce ta kirata dan ita tuni ta k'ule a d'aki ta basu guri,lokacin da taji Inna na kiran nata hijab ta sake sakawa ta fito da fad'in
"Inna gani..!"

"Sai kije ai kuyi sallama,tunda ya fita ko.?"
A sad'ad'e ta amsa mata jiki babu k'wari sannan ta wuce tabi shi,,a zaune ta tarar da shi a cikin mota ya zuro k'afarsa d'aya waje,d'ayar kuma da sauran gangar jikinsa a ciki,jikin motar ta samu ta jingina bayan tayi masa sallama,ya amsa yana d'an kallonta k'asa² har na tsayin mintuna biyu sannan yace
"My Lady.. Zan tafi,,sai munyi waya kenan.!?"
Bata kalle shi ba tace
"A ina ka samo number da zaka kira ni..?"

"A gurinki zan samu.."

"Ni bazan baka ba..!"

"Da gaske..?"

"Ehh! Bana bayar wa.."

"Dole ne ki bani,ko da kin hana kowa.!"

"Idan nak'i fa.? Zaka k'wata ne ta k'arfi..??"
Sai da ya sakar mata wani murmushi sannan yace
"Sosai ma..! Ko zaki gwada hanawa ne na nuna miki yadda zanyi dake.?"
Shiru tayi bata amsa ba,shima sai ya kawar da batun ta hanyar mik'a mata wayar daya janyo a gefensa,k'in karb'a tayi akan lokaci har sai data janyo ya kusa fizgota,Allah ya dai rufa mata asiri duk da line babu kowa tayi saurin kaucewa amma da tuni ta fad'o jikinsa
"Karb'i ni kina b'ata min lokaci,,kin san kuma na fad'a miki bana son kina min wannan jan ajin.."
Kafad'a ta mak'ale masa alamun A'a,idanu yasa mata na tsayin wani lokaci kafin ya kalleta bayan ya maida wayarsa ya ajiye yace
"Zaki iya tafiya.. Sai da safen ko kuma dai sai kinji muryana zaki iya yin bacci.!?"

"Allah ya tashe mu lafiya,,ka gaida min Mammah.!"
Murmushi yayi ganin bata kula wancan maganar ba da fad'in
"Zata ji in sha Allah.. Sai munyi waya..!?"

"Umm!" Tace masa sannan yace mata ta shiga gida,kamar baza ta tafi ba haka tayi ta jan jiki daga baya kuma ta shige,kai ya girgiza a hankali saboda tunawa da shiriritar da tayi ta masa a fili ya tsinci kansa da fad'in
"Daddy.! Gani nan tafe,zuwa gare ka. "
Yana fad'a yayi saurin juya kan motar ya bar unguwar da mugun gudu.

A can gidansu ma,lokacin ko da Mamma ta cewa Dad
_"Ehh! Sai kasa ido ai,,wani abune dan baka jeba..?? Ni zanje kuma zan nemawa Hammad aurenta tunda har ita yake so,,in Allah ya yarda zaka sha mamaki..!"_
Takaicin maganar ne yasa Dad yin fushi,ba tare daya sake yi mata magana ba,a fusace ya fice ya bar mata d'akin,d'age kafad'a tayi itama alamun bata damu ba,sannan ta fita ta bar d'akin cikin zuciyarta tana tunanin mafita data rage nata duk duniya,nata d'akin tayi saurin nufa,kai tsaye ko da zuwa ta d'auki wayarta ta bazama cikin contact d'inta tana laluben numbersa,,dai² kan sunan daya bayyana *MALAM BABBA* ta tsaya a fili ta fara jera sakin ajiyar zuciya,bayan tayi y'an tunanin da take ganin zasu taimaka mata ta tura kiran ya tafi.
Lokacin da wanda ta kira ya d'auka da sallama ta fara yin magana muryarta a sanyaye cike da girmamawa,har suka gaisa ya tambaye ta iyali da mai gidan nata,still jikinta yana a sanyaye ta amsa masa,daga nan kuma ta zayyana masa jawaban duk abubuwan da suke faruwa a gidan,saurarenta Malam d'in yake yi amma daga dukkan alamu cike da damuwa yake shima lokacin,daga bisani kuma ya k'are da bata hak'uri sannan ya ce ta bari zaizo gidan gobe da yardar Allah saboda maganar sam bata danganci wacce za'ayi a waya ba,,godiya tayi masa sosai kafin suka yi sallama,lokacin data gama wayar sanyayyar ajiyar zuciya tayi tana murmusawa saboda ko babu komai a yanzun kad'ai ta samu nutsuwar zuciya,while a gefe guda kuma tunanin zata tabbatarwa da Daddy yayi wasa d'an zaki ya girma yasa ta sake sakin k'ayataccen murmushi,a fili kuma bayan ta ajiye wayar haka nan ta rik'e waist tana kallon wall clock da fad'in
"Uhhuumm..! Yallab'ai kenan,,kayi zaton kai kad'ai ne kake da iko da Hammad..? Hammad Yaro na ne da nake matuk'ar k'auna fiye da rayuwata,kuma kai kanka ka tabbatar da wannan k'aunar,saboda haka na d'aura d'amarar k'watar masa y'ancinsa a hannunka tunda kai da kake matsayin mahaifinsa ka kasa yi masa abunda ya kamata,,bazan tab'a bari ka wulak'anta min rayuwarsa ba,ta hanyar hana shi farin cikinsa,wannan yak'in na shirya yisa ne ba don kowa ba haka nan ba don komai ba,sai dan saboda farin cikin Yarona.. Idan kayi jayayya da mu na tabbata bazaka tab'a iya yin jayayya da Malam ba,shi yasa nayi tunanin saka shi a ciki,,idan kuma har ka iya yin jayayya da shi to na tabbata bazaka tab'a ja lamarin ubangiji ba,,amma kuma tunda ka tirje ni da hannuna zan zarge maka wuya da igiya na janyeka daga gefen hanya,tun kafin rabo ya kaika k'iyama..!"
Numfasawa tayi a fili bayan kamar minti guda ta sake cewa
"Yanzun wasan namu zai fara,,saboda haka ka shirya ga Malam nan tafe zuwa gare ka.!"

Yana shigowa cikin parlor da Daddy ya fara arba zaune yana kallon news,inda yake ya k'araso da sallama,bayan ya gaisheshi bai zauna ba yayi hanyar staircase zaiyi sama,tun shigowarsa Dad baiyi magana ba kuma dama shi ya zauna jira a zaman da yayin,dan idan batun TV ne,ko wane d'aki akwaita sai dai da yake sunfi son zama a parlor'n idan suna nan,yasa na d'akunan suka zame musu kamar pictures sai lokaci² ake kunna su,har ya fara tsallakawa Daddy ya kirashi
"Hammad..! Zo nan.!"
Dawowa yayi kamar yadda Daddy'n ya buk'ata yana zuwa gabansa ya zauna saman rug da fad'in
"Gani Dad.."
Tambayar farko da Dad yayi masa ita ce
"Yaya muka yi da kai d'azun..??"
Sunkuyar da kansa yayi yana fad'in
"Daddy.! Naje fa,yanzunma daga can nake.."
Kallon rashin yarda yayi masa ba tare da yayi saurin k'aryatawa ba yace
"Are u sure..!?"

"Ehh.! Dad am very much sure.!"

"Good.. Allah yayi maka albarka."
Amsawa yayi da fad'in "ameen" a fili kafin ya kalli Dad d'in daya mayar da hankali kan News yana fad'in
"Daddy.! Shi kenan,zan iya tafiya..!?"
Bai d'ago ba yace masa
"U can go.. Ni ai na gama magana,tunda kaje aiken da nayi maka ai duk mai sauk'i ne,,jeka Alla ya tashe mu lafiya..?"
Da sauri ya tashi ya bar wajen,dan ma kada Daddyn ya sake masa maganar yasa shi had'awa da tsallake matakalar benen da sauri² kafin kace me tuni ya b'ace a gurin,,sai daya tabbatar ya shige bedroom d'insa murmushin mugunta ya sub'uce masa a fili ya shiga magana da kansa
"Dad.! Kenan,,me yasa tun farko zaka k'i amince min ne akan abunda zuciyata ke so..? Shin baka san hakan yana cutar da ruhi na ba..? Ko kuwa baka san a duk lokacin dana tuna kai kayi min silar rashinta a lokacin daya gabata ina ganin laifinka ba.??,,shi kenan ma dai duka wannan ya wuce,abar tuna baya,,kamar yadda kace nan da 1 month idan har nayi yadda kace zaka amince ka aura min burin zuciya ta,shin yanzun da na nemo inda ajiyata take,,zaka amince ka karb'i batun auren nawa ko kuwa..?" 🤔



*Kuyi sorry fan's naje unguwa yau,ban kuma dawo da wuri ba,,shi yasa zaku ga rubutun kamar bai kai inda nayi niyyar ajiye shi ba..Ayi min afuwa..🙏🏻*


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_




Please Login or Register in order to submit comment