Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba,bcos kaika janyowa kanka faruwar hakan,shirun da yayi mata bai bata hak'uri akan ta daina ba yasa ta sake cewa
"Pleasee Yah Hammad,,idan so na ne baka yi me zai hana kawai ka fad'awa Daddy.. Kaga sai muyi hak'uri da juna,ba sai mun shiga rayuwar junaba matsaloli su fara tasowa.."

"Kinga da Allah da fari dai ki fara dakatar da kukan da kike yimin a kunne,,na biyu kuma ki kyale ni na huta,bcos a gajiye nake,so ina buk'atar hutu yanzun.. Matsalar ki ce wannan idan kina ganin fad'awa Daddy masalaha ne,ke me zai hana kice da baban ki bakya ra'ayina ne kawai.."

"Amma Yah Hammad ban san mene ne dalilin da yasa kake min haka ba,,ko kuwa dan saboda ni baka sona ne,shi yasa na kasa yin daraja a idanunka..??"

"A'ahh..! Saboda dai ke d'in kin kasance *ZAB'IN MAHAIFINA* ce.."
Ji tayi kamar an kwad'a mata guduma a tsakiyar kanta saboda yadda maganarsa tazo mata a bazata,dama tayi tsammanin jin haka daga gare shi,tun lokacin da suka fara maganar ta fahimci abunda yake son fad'a,kuma wannan shi ne dalilin da yasa ta takura masa akan lallai sai ya fad'a mata matsayinta a gare shi,sai dai ko data tambaye shi dalilin da yasa zai auresu su biyu da cewa yayi
"Saboda ita waccen ita yake muradin yin rayuwa da ita,,,amma ita kuma.!" Sai yayi shiru bai k'arasa ba,yanzun kuma ya kira ni da *ZAB'IN MAHAIFINSA* kenan ya tabbata zai aure ni a matsayin *MATAR CUSHE* wacce bata daraja..??"
Maganarsa ce ta dawo da ita cikin hayyacinta inda yake cewa
"Da Allah Malama idan baki da abun fad'a ki kashe waya,ni ina da nawa aikin da nake son yi.."
Kuka ta sake fashewa da shi saboda tsabar takaicin abunda yayi mata ko tsayawa sake saurarensa bata yiba bare ta tsaya bashi amsa,ita kanta wayar saboda bak'in ciki jifa tayi da ita,bayan tayi tsalle daga nan inda ta aiketa sai data daki jikin d'aya wall d'in dake opposite d'inta kafin ta dira a k'asa ko ina na daga sassan ta ya tarwatse ya kama nasa hanyar,yana jin sautin ya fahimci abunda ya faru,amma sai ya tab'e baki had'e da d'age shoulders sama alamun bai damu ba,,waya kuwa tuni tayi d'uu³ ta kashe kanta,kwanciya yayi abunsa bayan ya sata silent ya ajiyeta a gefe saman bedside drawer had'e da juya mata baya,,addu'o'in kwanciya bacci ya fara reciting yana gamawa yayi bismillah ya kwanta a gefen dama had'e da rufe idanunsa.

Tun da farar safiya yau a gidan da gagarumin bak'o suka wayi garin na jumu'ah,wanda ganinsa kad'ai sai da yasa kowa dake cikin gidan jikinsa ya sanyaya,,Daddy kansa ganin Malam sai da yaji wani abu ya tsirga masa a ransa,game da zuwan na Malam,saboda kaf girman gidan tun daga ma'aikata har masu mallakin gidan babu wanda bai san Malam baya tab'a zuwa haka nan ba sai idan da wani babban dalili ko wani abu ya faru sannan ne zaka ga zuwansa,shima kuma yana gama abunda ya kawo shi baya zama yake tafiya. Malam kuwa a nasa gefen babban dalilin da yasa shi doko sammako a wannan lokacin duka baya rasa samun nasaba da son ya tari Daddy a gida,shi yasa ma tun farar safiyar yasa aka kawo shi,saboda su samu suyi maganar daya dace akan lokaci kafin lokacin sallah yayi.
Isowar Malam tasa wasu cikin hadiman dake gidan suka shaidawa Mamma a kan lokaci,ita kuma tun kafin ta fito tuni har ta sa an yiwa Malam d'in masauki a parlor,kasancewar kowa dake gidan yasan matsayinsa shi yasa kafatanin duk wani wanda yake cikin gidan babba da yaro,bayan anyiwa Malam iso suka fara shigo d'aya bayan d'aya suka kwashi gaisuwa cike da girmamawa da kuma karramawa,sannan yasa ayi masa magana da Mamma saboda yana sauri,kasancewar kafin 11am yake son isa masallaci,kun san iyayen mu da kakanni a irin wad'annan b'angarorin na bautar Allah basa tab'a wasa,haka wannan kuma shi ne d'abi'ar Malam a irin wannan ranar,tun kafin yanzun sun kasance tare suke tafiya masallaci da mahaifin Daddy tun kafin Allah ya karb'i rayuwarsa.
Labarin zuwansa ko daya riski Mamma sai da tayi addu'o'i domin neman yardar Allah akan ya d'orata tayi nasara akan mijin nata,daga nan ta taso duka yaranta a gaba suka kamo hanyar sakkowa k'asan dan ayi wacce za'ayi,,lokacin da suka k'araso gaba d'aya a gabansa suka durk'usa saboda girman da yake da shi a gurinsu,ko da suka gaisa aka tab'a wasa da dariya tsakaninsu sannan Mamma ta nemi su basu guri,tashi suka yi gaba d'aya har Hammad amm sai Mamma tayi saurin dakatar da shi ta hanyar cewa ya dawo,,hankalin Malam gaba d'aya yana ga Mamma domin so yake yaji babban dalilin da yasa Daddy yace bai amince ba,kafin ya waiwayo inda yake da yake dama duk ya riga su zuwa,dogon jawabi Mamma ta janyowa Malam cikin abunda ta sani dangane da alak'ar dake tsakanin Hammad da Sabina tun daga tushiya bata yarda ta dire shi ba sai data kai har kan ganyensa sannan ta d'ora da fad'in
"Malam duk wani k'ok'arin da nake tunanin zan iya akan Daddy ya fahimci matsalar da zata iya faruwa nayi,ba don komai ba sai don ya fahimci abunda zai je ya dawo,amma ya nuna min baya ra'ayin na dunga fad'a masa,dana matsa kuma k'arshe cewa yayi tunda har akan batun auren yarinyar ne daga ni har Hammad muke neman yin jayayya da shi to ya haramtawa Hammad aurenta ko da da zinare aka k'irk'ireta.."
Murmushi Malam yayi mai sauti da fad'in
"To too! Kai yanzu Aliyu idan banda abunka kaf fad'in duniyar nan akwai wani d'an adam d'in daya isa haramta wani abu ga wani bawan,idan ba lillahi rabbal alamiiyn ba..? Shi kad'ai yake da ikon hanawa kuma yake da ikon sawa ayi dole ko ana so ko ba'a so kuma haka tilas za'ayi,ba don komai ba sai don me..? Saboda a kaucewa fad'awa cikin fushi da azabarsa.. Duk al'amarin da kaga kayi jayayya akansa amma bai fasu ba,ya kamata ka sake shi,don idan kaci gaba da ja tabbas ubangiji zai nuna maka ishara,,shi lamarin aure ba'a yi masa katsalandan domin idan ka gwada masa taurin kai k'arshe sai azo ayi kai kuma Ubangiji ya amshe rayuwarka,ka godewa Allah da har aka zo wannan lokacin babu wani abu daya same ka,sannan nima ban san da maganar ba sai yanzun,da duk hakan bai faru ba,kuma ni abunda nake so ka sani shi ne batun aure babu fashi tunda har yaro yace yana so,sai mu bishi da addu'ar fatan alkhairi.."
Shiru Daddy yayi tunda malam ya fara magana,sai dai tab'o batun hurumin Allah da yake k'ok'arin saka kansa yasa jikinsa ya sanyaya,to amma shi duk fa ba wannan bane matsalar sa,idan har aka ce an yarjewa Hammad yayi mata biyu lokaci guda ta yaya zai iya sauke nauyin kowacce a kansa,al'halin daga shi har su matan dukansu yara ne.? Ya tabbatar gidan zai zama ana samun sab'ani
"Ka godewa Allah Aliyu,a iya tsayin lokaci da nake ganin matsalolin gidajen aure zan iya cewa ban ga gida irin naka ba,biyayya dai duk irin wacce mutum yake nema da girmamawa daga iyalinsa ka samu,shin me zaisa baza ka saakawa iyalinka da tukuicin da za suyi alfahari da kai ba ko da bayan baka raye.? Wannan hanyar daka biyo ba mai kyau bace domin kuwa kana nuna musu butulci ne akan k'ok'arin kare hak'k'in ka akansu,kuma kasan me gobe zata haifar sakamakon yin watsi da nasu matsalolin..!? Saboda haka ni dai ina baka shawara idan boko tasa kake k'ok'arin danne hak'k'in iyalinka akanka kayi k'ok'arin canjawa tun kafin a samu matsala wata rana suyi maka bore."
Nasiha sosai dai Malam yayiwa Daddy mai shiga cikin jini da b'argonsa kafin ya tambaye shi dalilinsa na k'in amincewa da maganar da Hammad d'in yazo masa da ita,nan fa Daddy yayi shiru saboda shi da kansa ya fahimci duk wani dalilin da zai kawowa Malam ba mai k'arfi bane,bare ace za'a yarda da shi,wannan dalilin yasa sai yayi shiru bai ce komai ba bare ya kaishi ga jin kunya,,ga Malam kuwa tunda yaga yayi shirun nan,kawai sai ya rabu da shi,ba tare daya tilasta masa ba,bcos shima d'in ya fahimci amsar shirun na Daddy,wanda da ace zai tursasa shi tofa k'arshe kunya zai bashi a gaban iyalinsa,,juyowa yayi inda Hammad yake zaune a gabansa ya dafa kansa da fad'in
"Muhammadu.! Allah ya albarkaci rayuwarka,,yadda kake kamanta yin biyayya akan umarnin mahaifanka,ubangiji ya dube ka,ya baka y'ay'a na gari,shiryayyu wad'anda zasu ji k'anka,masu yi maka biyayya.."

"Ameen Malam" shi ne abunda gaba d'aya suke fad'a hatta Daddy dake zaune gefensu,,lokacin bayan sun gama duk tattaunawar da za suyi akan batun daya kawo shi,suka tab'a hira wacce ta sake d'aukan su tsayin wani lokaci kafin Malam yayi sallama dasu da shirin komawa,sai dai kuma ko kafin ace ya tafi,sai daya barwa Daddy sallahun lallai² kafin nan da bayan sakkowa a masallaci yasan yadda zaiyi ya nemo masa wad'anda zasu yi masa rakiya wajen nemawa Hammad auren,tunda shi yayi furucin babu hannunsa a ciki to shi ya saka nasa.
Da girmamawa Daddy ya amsa masa,daga nan suka masa rakiya har bakin mota,sai da suka ga tafiyarsa sannan duka suka juyo jikin kowa cikinsu a sanyaye,yayin da fuskokin Mamma da Hammad kana kallo zaka hango tsantsar farin cikin da suka tsinci kawunansu aciki.Daddy shi ya fara barin gurin ba tare da yayi musu magana ba,Hammad kuwa ganin babu Daddy a gurin yasa shi rungume Mamma idanunsa d'auke da hawayen farin ciki yana fad'in
"Thank u Mah.! Ana ahabbuk..!"

"Wa'ana ahabbak-thtiir habibiiy.."
Sake k'ank'ame ta yayi yana sakin sanyayyen murmushi mai bayyanar da samun nutsuwa da kwanciyar hankali kafin ya sake ta yana fad'in
"Mah.! Ki samin albarka,,zanje gurin surukarki yanzun na dawo..!"
Ido waje take kallonsa
"Baby..! Yanzun bai yi safiya ba..??"
Kai ya kad'a mata yana fad'in
"A'a Mah,, bai yi ba,nifa d'an gida ne ko kafin wannan lokacin naje babu wanda zai tambayeni dalili,tun kafin wannan lokacin sunyi sabo da ni,kawai dai ki samin albarka..!"
Dariya tayi masa while tana bashi amsa
"Kullum a cikin saka maka albarka nake Yarona,, kai dai kaci gaba da godiya ga Allah sannan ka nemi yardarsa,in sha Allah idan har ya yardar maka babu kai babu tab'ewa."

"In sha Allah Mah..! I will."

"Yawwa.! To maza jeka abunka Allah ya bada sa'a.. A gaida min y'ata.."
Murmushi yayi mata yana lumshe idanu had'e da rausayar da kai alamun zata ji,sannan ya juya da sauri ya nufi carport,yana tafe yana sakin murmushi mai burgewa,sai daya shiga cikin mota ya zauna dai² sannan ya ciro handkey daga aljihunsa ya goge hawayen da suka gangaro masa,,lallai ubangiji ya isa a bauta masa shi kad'ai ba tare da an had'a shi da kowa ba,,idan ba har ubangiji yana sonsa da rahama ba,da kuma k'addarawarsa cikin al'amuran ko wane bawa,ta yaya ne yake tunanin zai samu irin wannan damar a lokacin da babu zato haka..? Murmushi ya sake yi mai ban sha'awa yana kad'a kai sannan ya fice daga gidan,,cikin sak'e²n zuci har ya k'araso k'ofar gidan yayi parking bai daina jinjina al'amarin ubangiji ba,sai daya kalli k'ofar gidan sannan yayi k'ok'arin sauke seat d'insa yayi baya da shi kad'an bayan ya zare seatbelt daga jikinsa ya d'auki wayarsa ya kira line ta,sai daya kira ta har wajen three times kafin ta d'auka cikin kumburi tana fad'in
"Mene ne kuma..??"
Dariya yayi mata mai sauti had'e da fad'in
"Fito waje..!"
Yana fad'a ya datse kiran ba tare daya bata damar yin magana ba.

A cikin gida tsabar takaici ne ya sake kunnota dama haushinsa take ji tun dare shi ne zaiyi mata titsiye yanzun,tsabar ma ya raina mata aji shi ne bazai bari tayi magana ba ya kama ya kashe waya,ai kuwa zai gane KUSKUREN da yayi,dan ita bata shiryawa hakan ba,kuma ita a niyyarta ma tace masa bata garin kawai sai bai saurare ta ba,wayar tabi da kallo bayan ta cije gefen lip d'inta na k'asa a fili tace
"Barin je naji da wacce wannan halittar yazo min.."
Tana fad'a ta zaro hijab tayi tsakar gida,sai data lek'a d'akin Innarta ta fad'a mata sannan tayi waje,lokacin data fito a dai² side d'insa ta tsaya tayi knocking glass d'in gefensa,tunda ta taho yana kallonta har ta k'araso baiyi yunk'urin tashi ba,ganinta tsaye kusa da shi yasa shi sakin murmushi kafin ya gimtse ya sauke glasses d'in da fad'in
"Mene ne.!?"
Fuskarta a tamke ta kalle shi da fad'in
"Kamar yaa..??"
Kallonta yayi ya tab'e baki bayan ya d'auke kai gefe ya ce
"Shigo ni mu tafi,kafin ki b'ata min wasa..!"
Har lokacin tana tsaye wajen da take tace
"Ban gane ba..! Ina za muje..??"

"Ke dai ki shigo mana,ko an ce miki zan saida ke ne..!?"

"Waye ya sani.."
Murmushi yayi ba tare daya sake magana ba,ita ma saita zagayo ta d'ayan side d'in,da kansa ya bud'e mata motar bayan ta shigo ta zauna ya fara k'ok'arin tada mota kamar gaske,kallonsa tayi da sauri tana fad'in
"Wai ni ban gane ba,ina ne zaka kai ni..??"
Har lokacin bai kalli inda take ba yace
"Zance zaki raka ni..!"
Hankali a tashe ta ce
"Meh..!? Wollahi ba dani ba.."
Tayi maza zata bud'e motar ta fita ya danna lock,sank'amewa tayi a zaune kafin ta waiwayo ta kalle shi
"Dan Allah ka bari,,kaga dai bana so ko.!?"
Lumshe idanunsa yayi yace
"Uhmmm! Na sani,,amma me yasa baza ki raka ni ba..!?"

"Akan mene ne zan bika..??"

"Rakiya fa zaki yimin daga nan sai na gabatar dake a matsayin mata ta da zan aura a nan gaba.."
Girar sama data k'asa ta sake had'ewa,a fusace ta d'ago za tayi magana amma kuka ya riga maganar tahowa,dole tasa tayi shiru ba tare data ce komai ba ta juyar kanta d'ayan side d'in tana kallon waje,sai data matse son ranta sannan ta saki sanyayyar ajiyar zuciya da fad'in
"Bud'e min na fita..!"

"Zuwa ina..??"
Shiru tayi masa bata bashi amsa ba,shima yayi mata shiru while har lokacin idanunsa akanta yana jin zuciyarsa kamar ya kamota ya rarrasheta,sai da suka d'auki tsayin lokaci a haka kafin ya d'ago daga kishingid'ar da yayi yana kallonta
"My Lady.. Zaki iya aurena kuwa..??"

"A'aahh..!" Shi ne amsar data bashi kai tsaye ba tare da tunani ba
"Me yasa zaki ce haka..??"
Idanunta ta sake lumshewa hawaye suka sake gangaro mata,,still tana kallon waje tace
"Saboda bana sonka..!"
Murmushi yayi mai santi sannan yace
"Ban yarda ba..!"

"Ya kamata ka yarda." Tayi saurin sake bashi amsa
"Bazan tab'a yarda dake ba."

"Me yasa ba zaka yarda ba.."

"Saboda ba ni kika kalla kika fad'awa bakya so na ba."
Murmushi tayi mai ciwo kafin tace
"Idan na kalleka na fad'a shi ne zaisa ka yarda..!?"

"Ehh! Zan yarda mana.."
Juyowa tayi a fusace sai dai idanunta a k'asa tace
"Na fad'a bana son ka..!"
Murmushi ya sake yi da fad'in
"Ke yarinya ce har yanzun,idan na fad'a miki magana ki dunga yarda,,buh idan kina ganin kin isa ai d'aga idonki za kiyi ki kalleni ido da ido ki ce Hammad bana son ka,,sannan ne zan yarda kin daina sona.."
Lumshe idanunta tayi had'e da matse su gam,a hankali ta waresu tas akansa with much confidence na zata fad'a masa,,yadda kyallin hawayen suke kwance ciki suka k'awata su tamkar an tsoma cikin mai,a hankali ta shiga jujjuya su tana kallonsa,tunda ta d'ora su akansa da murmushi ke kwance a saman fuskarsa take yasa ta kasa furta ko kalma d'aya sai kallon-kallo da suke ma juna mai d'auke da manyan sak'onnin k'auna,sun d'auki tsayin mintuna a haka kafin yayi gyaran murya da fad'in
"Uhhuumm.! Ke nake saurare..!"
Kasa magana tayi sai kallon kawai da take binsa da shi,yayi magana wajen sau biyu amma bata amsa ba,wannan dalilin yasa shi kallonta a nutse,babban yatsansa ya had'a dana tsakiya ya murza har sai da suka bada sound a dai² fuskarta,saurin kyafta idanuwanta tayi,shi kuma hakan yasa shi tabbatar da batama san abunda ake yi ba,fuskarsa ya matso dai gefen kunnenta ya rad'a mata
"Haba yarinya ni dai nasan baza ki iya ba, taurin kai ne kawai irin naki yasa kike tunanin ke d'in wata jan wuya ce,,kallona kad'ai yasa ki manta inda kike ina kuma ga..."
Shiru yayi bai k'arasa ba yayi saurin komawa ya jingina yana sakin murmushi,tsuke baki tayi tana kallonsa
"Mene ne tunanin kane a kaina..??"

"Na aure ki..!?"
Ya bata amsa ba tare daya kalle taba
"Bazai yiwu ba..!"

"Ya yiwu an gama.."
Bata kalle shi ba itama tace
"Sai ayi na gani,,ba dai saina amince ne za'ayi ba..!?"

"Amincewar wa..!? Naki wai.?"

"Ehh! To da nawa.!?"
Murmushi ya saki mai sauti kafin yace
"Shi kenan,zamu gani,,buh yanzun dai kije gida,anjima idan na dawo daga masjeed zan zo sai muyi maganar.."
Yana fad'a ya bud'e mata lock d'in,ba tare data juyo ta kalleshi ba tace
"Kazo kayi min me..!?"
Tana fad'a tayi maza ta d'ora hannu kan murfin motar zata bud'e,had'e da masa gunguni,saurin fizgota yayi ta dawo,tana tahowa tayi masauki a jikinsa kamar wacce mayen k'arfe ya fizgo,rik'eta yayi sosai a jikinsa while yana kallon fuskarta,yadda duk ta firgice ta kasa d'aga ido yasa shi sakin siririn tsaki sannan ya sake ta
"Allah ya baki sa'a,ina magana kina bani amsa,wata rana idan kika yi sai dai kiji..!"
Saurin katse maganar yayi ba tare data k'arasa ba ya dai girgiza kansa kawai alamun zata ji jiki idan hakan ta sake faruwa,a tsorace ta fice daga motar ko waiwayowa bata yarda ta sake yi ba ta shige gida,yadda yaga ta fita ko waiwayensa bata yi ba yasa shi sakin ajiyar zuciya sannan shima ya tada motar ya bar unguwar.

*After salatul jumu'ah...*
Cikin sauri² Daddy ke sakkowa daga stairs yana tafe yana gyara zaman wristwatch dake d'aure a tsintsiyar hannunsa,Mamma ce ta biyo shi a baya cikin sauri tana fad'in
"Yallab'ai please..! Wait a minute..!"
Juyowa yayi saurin yi fuska a d'aure dan tun tafiyar Malam har lokacin bai yarda yayi dariya ba kuma wani magana bai had'a su ba,har ya fita masallaci ya dawo,kallonta yake har ta iso daf da shi,itama sai data kalleshi kamar yadda yayi kafin tace
"Malam fa kasan yana hanya.. Kuma..!"

"Na sani,,ba sai kin fad'a min abunda zanyi ba.."
Yana fad'ar haka ya juya abunsa ya fice,nan inda ya barta tsaye fuskarta cike da mamakinsa yasa ta sauke dogon numfashi kafin ta koma ciki da damuwa a afuskarta,,a harabar gidan bayan fitowar Daddy ya had'u da *ALHAJI MUKHTAR BABANGIDA* shima yana niyyar fitowa daga motarsa,da sauri Daddy ya k'arasa ya iske shi a gurin suka yi hannu cikin farin ciki da barkwanci irin na dad'ad'd'iyar abota data rikid'e zuwa y'an uwantaka,bayan sun gaisa suka koma can gefen garden saman wasu fararen kujeru domin su tattauna batun yadda zasu fuskanci *ALHAJI ISHAQ BUNAWA* da maganar auren Hammad,duka basu jima da zama a gurin ba motar Malam ta shigo cikin harabar gidan.Mamma dake tsaye ta balcony tana sauraren taga Daddy ya fita sai taga sun nemi guri sun zauna,still tana tsayen kuma dai ta hango shigowar motar Malam,godiya ta d'aga hannunta sama tayi ga rabbul alamiiyn kafin ta samu kwarin guiwar barin wajen.
A gefen su Daddy lokacin da motar Malam ta shigo kallon *ALHAJI MUKHTAR* yayi da fad'in
"Shi kenan,ina ganin wannan maganar kuma sai dai musan yadda zamu yi da ita,dan ga Malam nan ya samu damar k'arasowa.."

"Toh.! Alhamdulillah ai tunda ya k'araso sai mu tafi ko..!?"

"A'a tafiya kam babu ita har sai Hammad ya zo.. Ni banma san ina ne ya nufa ba tunda aka sakko daga masjeed.."
Murmushi Daddy'n Sultan yayi yana fad'in
"Sha'anin yara kenan,sai hak'uri.."
Mik'ewa suka yi duka suka nufi inda motar Malam take while Daddy yana ta k'ok'arin yaga ya kira line Hammad,,a nasa gefe kuwa Hamad cikin fad'uwar gaba ya d'auki kiran Daddy da sallama a bakinsa,bayan da Daddy ya amsa yake tambayarsa
"Hammad.! Kana ina yanzun..!?"
Amsa ya bawa Daddy akan yana tare da Sultan a gidansu,Daddy cikin sauri yace
"Maza² duk abunda kake yi ka bari kazo gida ka same ni..!"
Yana fad'a ya katse kiran,duka tsakani ko mintuna biyar ba'a d'auka ba suka k'araso tare da Sultan,cikin girmamawa bayan zuwansu zuwansu suka gaida iyayen da kakan nasu wato Malam,daga nan Daddy yayi musu umarnin su shiga mota dan su samu suje gaba d'aya,,jin abunda Daddy ya fad'a yasa waiwayowa ya kalli Daddy daya shiga mota yana murmushi kafin yace
"Aliyu..! Kai da babu sa hannunka ina ne kuma kake k'ok'arin zuwa yanzun..!?"
Fuskarsa da damuwa ya d'ago ya kalli Malam da fad'in
"Ayi min hak'uri Malam,,tuntub'en harshe ne yasa ni aikata hakan."
Jinjina kai Malam yayi ba tare da ya sake magana ba ya shiga mota suka kama hanya gaba d'ayansu.
Mamma dake tsaye har lokacin tana kallon duk abunda yake wakana bata san lokacin data saki wani kwantaccen

Please Login or Register in order to submit comment