Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yasa shi sauka downstairs,nd can d'inma bata nan,har kitchen duka sai daya duba ko da yaga bata nan wannan tasa shi komawa parlor kawai yayi zamansa,dan yasan duk inda ta shiga idan har ta fito zai ga shigowarta.
Kun san akan ce tsakanin mata da miji sai Allah,,kamar haka ne ya kasance ga Mamma da Daddy a wannan safiyar,,a kwanaki kusan uku da suka gabata sam idan ka gansu ba zaka tab'a zaton zasu d'inke a cikin k'ananun kwanaki kamar haka ba,amma a wannan safiyar dukda cewa da dare kafin wayeyar garin sun d'an samu sab'ani,amma a yanzun idan har ka kallesu lokacin da suka fito parlor kai baka ce sune suka samu sab'ani akan maganar Hammad ba,,ya samu ak'alla mintuna ashirin zaune kafin ya jiyo fitowarsu,suna tafe suna hira cike da shauk'i har suka k'araso cikin parlor'n,shi kansa Hammad lokacin da yaga fitowarsu sai da gabansa ya fad'i,amma kuma ko daya tuna alak'ar dake tsakaninsu da juna,sai kawai yaci gaba da addu'ah akan Allah ya taimake shi,duk da yasan abune mai wuyar gaske ace yayi winning over his Dad,a hankali ya janye idanunsa akansu sannan ya furta
"Barka da fitowa.."
Ko kad'an baiyi tunanin samun amsawar Daddy ba,amma sai ya ji shine ma ya fara amsa masa,mamaki fal zuciyarsa yake tambayar kansa
"Shin me hakan yake nufi..??"



*Nima dai tambayar da bayi kenan,shin hakan yana nufin Daddy ya hak'ura ne ko kuwa ya kuke gani fan's..?*


*Afuwaan fan's jiya munyi rashin wuta saboda sun sanar zasu yi gyara,nd sisterna tayi ta fama da nak'uda 2 days shi yasa jiya kuka jini shiru..Buh cikin hukuncin ubangiji Allah ya sauketa,sai dai tana asibiti still saboda matsalan data samu,ku samin ita a addu'o'inku please.Allah ya bawa dukkan marasa lafiyar mu lafiya mai d'orewa,ya jik'an magabatanmu..👏🏻*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*Am back again my pepz...🏃*

_Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat..👏 Y'an uwa,k'awaye,abokan arzik'i,masoya Smasher da rubutunta,na b'oye dana sarari,ina matuk'ar mik'a d'umbin godiya ta a gareku,karamcin da kuke nuna min ban san da wane irin lafuza ya kamata nayi muku godiya ba,na gode³ k'warai da gaske,yadda kuka nunamin k'auna ubangiji (S.W.T) ya dubi al'amuranku,dukkan wani mai buk'ata a cikinku ta alkhairi ubangiji ya cika masa burinsa..Ameen.💝_

*18.*
_#Life alteration_

Tun kafin ya gama kokwanton da yake akan al'amarin tuni muryan Daddy ta dawo dashi daga mafarkin ido biyu daya tafi
"Son.. Ka tashi lafiya.."
Sake kallon Daddy yayi cike da tsananin mamaki,hakan sai yasa shi kasa amsawa saboda yadda yake ganin kamar ba Daddy'n ne da gaske yake masa magana ba,Mamma data farga da halin da yake ciki ne ta d'anyi magana da k'arfi ta hanyar kiran sunansa yadda tasan zai jita sosai,,a hankali ya waiwaya sashen da take ya kalleta,ido ta lumshe masa tayi masa alamun ya kwantar da hankalinsa,a hankali shima d'in sai yayi murmushin basarwa yana sosa k'eya
"Dad..! Barka da safiya.."
Da kulawa a maganar Daddy ya amsa masa da
"Ka tashi lafiya..? Ya sauk'in jiki..?"

"Alhamdulillah Dad..!"

"Masha Allah,,haka muke fata a koda yaushe,ku kasance cikin k'oshin lafiya.."
Shi dai kam yana cikin rud'anin abunda Daddy yayi,sai dai ba tare daya sake magana ba daga gaisuwa yaja bakinsa ya tsuke,kallonsa Mamma ta sake yi da tambayar
"Ina wad'annan yaran suke..?? Kada dai ace duk magasannan nayi baisa sun fito ba."

"Anya Mamma..? Bana tunanin sun sakko.."
Jinjina kai tayi cike da takaici sannan ta bashi umarnin ya kira su suyi break,cikin biyayya da nuna girmamawa ga maganarta ya mik'e ya nufi sama,bedroom d'in Bassam ya fara dubawa kasancewar shi ne daga farko,ko kafin ya shiga sai da yayi knocking sannan ya tura k'ofar ya shiga da sallama a bakinsa,kwance ya iske shi a saman bed yayi d'ai² yana ta zuba bacci abunsa cikin kwanciyar hankali,alamun da suka tabbatar masa da baima san ya shigo ba kenan,jinjina kai kawai yayi sannan ya nufe shi,duvet daya rufa ya janye sannan ya koma gefen windows ya yaye curtains d'in da suka sa d'akin yayi duhu,hasken rana daya hasko masa fuska sai yasa shi fara motsawa,kafin a hankali ya soma bud'e idanunsa da suka masa nauyi saboda azabar baccin dake kansa coz daren jiya bai samu ya kwanta da wuri ba yana ta aikin research,da Hammad ya fara arba yana tsaye a kusa da shi daga gefe fuskar nan kamar ba tasa ba,ya kafe shi da idanu nd hannayensa nad'e a chest d'insa
"Broahh..!"
Bassam ya fad'a cikin muryan bacci while yana mik'ewa ya zauna,hararansa Hammad yayi sannan ya juya ya kama hanyar fita a room d'in while yana fad'in
"Idan kaga dama ka sakko yanzun,if not kuma kaci gaba kasan ba dawowa zanyi na sake tashin ka ba..Tunda ita mamma ka rainata shi yasa za tayi ta zaryan zuwa tashinka.. "
K'ok'arin tashi ya fara dan yasan halin Hammad idan har ya fita bazai dawo d'in ba kamar yadda ya fad'a,haka nan yasan kansa zai cuta idan har bai sauka ba akan lokaci,,yana fita bedroom d'in BADRA ya sake lek'awa,lokacin ita kam tuni ta jima da tashi dan har tayi wanka ta shirya tana shirin fitowa shi kuma yana shigowa
"Hi Yah Hammad.."
Ta fad'a cikin y'ar siririyar muryanta tana masa waving,d'an murmushi yayi kafin ya amsa da
"Hello..! Daddy's kiddo.."
Ganin da yayi ta gama abunda take yi ba tare da yayi mata magana ba ya juya zai fita,murmushi ta sake yi kafin ta gaida shi,yana tafiya yana amsa mata har ya fice,nan ta biyo shi suka sakko tare yana gaba tana biye da shi a baya har dining space,zaune suka tarar da Daddy da mamma tuni har sun fara break abunsu dan da dukkan alamuma Daddy yana niyyan fita ne da zaran ya kamalla abunda yake,sai da suka yi sallama kafin suka nemi guri suka zauna kowannensu ya shiga k'ok'arin bud'e plate dake rufe a gabansa sannan suka fara ci,babu wanda yake magana a gurin har zuwa sanda Bassam ya zo gurin a gaggauce,hararansa mamma tayi sai dai bata ce da shi komai ba taci gaba da cin abincinta har zuwa sanda ta kammala,ture plate d'in tayi gefe kad'an da fad'in
"Alhamdulillahillaziiy ad'a'amaniy haaza warazak'anihi min ghairi haulin minniy walak'uwwatiy.."
Daga haka sai bata sake yin magana ba har suka kammala sannan suka nufi cikin parlor dukansu,while daddy shi kuma yayi hanyar upstairs cikin sauri,mintuna biyar ya d'auka kafin ya sakko yana gyara zaman babbar rigarsa,sanda ya shigo tsakiyar parlor sannan ya kalli Hammad da fad'in
"Ehemm! Son yaushe ne zaka koma school..!?"
Kallon Mamma yayi sannan ya juya ga Daddy yana cewa
"Dad gobe ne zamu tafi.."
Jinjina kai Daddyn yayi kafin yaci gaba da tafiya yana fad'in
"Allah ya kaimu.."
K'asa² Mamma da Hammad suka amsa da "ameen"
"Toh.! Ni na tafi d'aurin aure,sai Allah ya dawo dani.."

"Allah ya tsare hanya Daddy.."
Cikin had'in baki dukansu suka fad'a,yayin da Mamma tabi bayansa suka fita tare dan yi masa rakiya,,a hankali Hammad ya maida idanunsa ya lumshe yana sakin ajiyar zuciya,deeply yake zancen zuci
"I know Dad zaka amincemin matuk'ar Mamma tasa baki,wannan dalilin yasa tun a farko na amincewa zuciyata na sanar da ita damuwata,,Thank u Mah..! Ba don keba da ban san adadin damuwan da zan shiga ba..Rabb ya biyaki da mafificin sakamako.."
Murmushin samun nutsuwa ya d'an saki sannan ya mik'e ya bar wajen..

*Monday TUSHEN aiki,ko bature na tsoronki.. Taken da bahaushe yayi kenan wa wannan rana.*

Tun asubah bayan da aka idar da sallah a masallaci bai tsaya ba ya nufo gida dan ya samu daman shirya sauran abubuwan da yasan zai buk'ata,around 7:00am ya gama packing kayansa a side,sannan ya shige bathroom,within 30 minutes cikin sauri har ya gama komai sai tafiya daya rage masa,lokacin daya tabbatar babu sauran wani abu daya rage masa ne ya d'auki phone da niyyar kiran Sultan,sai dai har yayi masa kira kusan uku duka bai d'auka ba,sai a kira na hud'u sannan Sultan d'in ya d'aga cikin muryan bacci
"Yane broah..!"
Ya fad'a yana murza idanunsa,shiru Hammad yayi bai tanka ba saboda takaicin jin sai yanzun nema ya tashi,kenan hakan yana nufin ko shiryawa Sultan d'inma baiyi ba kenan..??

"Hello..! Man..!?"
Ya sake fad'a yana mik'ewa tsaye,cikin matuk'ar jin haushi Hammad fara magana
"Amma dai kai wollahi anyi d'an iska,,banda ka rainawa kanka hankali sai yanzun ne zaka tashi a bacci..?"

"Sorry broah maa d'an kwanta ne bayan na dawo a masjeed sai bacci ya d'an d'auke ni..Buh lemme pack my luggage's.."
Bai k'arasa ba Hammad ya tari numfashin sa da fad'in
"What..!? Ur luggage's..? Kana nufin bakama had'a suba sai yanzun..? Wollahi to ba dani zaka tafi ba,,zanyi gaba idan ka gama shiryawa ka same ni a school..!"

"No! Broah..Ka bari mana yanzun zan kammala mu wuce,,ka san bamu saba tafiya mutum d'aya ba,ka bani minti ashirin ma,it's ok for me na gama..!"
Tsaki yaja ba tare daya k'arasa jin zancen ba ya katse kiran,fuskarsa babu alamun wasa a samanta ya shiga jan luggage d'insa yayi waje ba tare daya bi ko takan ma'aikatan gidan ba bare yasa a fitar masa da su,,sai daya fitar da duka kayansa haraban gidan sannan ya koma ciki da sauri dan yiwa Mamma sallama,a kitchen ya isketa suna aikin shirya breakfast,bayan ya gaidata suka gaisa da housemaid's d'insu cikin mutunci ya amsa musu babu wulak'anci kamar na wasu y'ay'an masu kud'in,daga haka suka fita tare da Mamma zuwa parlor,as usual idan har zaiyi irin wannan tafiyan na barin gida takan yi masa nasihohinta masu shiga jiki,yauma d'in sai data tabbatar ta sake yi masa nasihar ya kula da kansa sannan ya kasance mai takatsantsan da rayuwa a duk halin daya tsinci kansa,daga haka tayi maaa rakiya har bakin mota,ba ita ta koma ciki ba sai data ga ya kama hanyar fita a gidan sannan ta saki numfashi tana masa waving had'e da binsa da addu'o'i har zuwa lokacin daya fice a gidan.
Ko daya fito daga gida bai tsaya tunanin duba Sultan ba bare ya tuntub'e shi yaji ya gama d'in coz shi a tsarin rayuwarsa baya ta'ammali da mutumin da bai san muhimmancin lokaci ba,haka nan ya tsani jira,shi yasa da zaran yayi ALK'AWARI baya sab'awa k'a'idarsa,kai tsayen ko daya fito direct ya d'auki hanyarsa ta komawa garin na Wudil.

In less than an hour ya iso garin wudil,ko da yayi parking bayan ya zare seatbelt dake jikinsa yana k'ok'arin fita a motan kiran waya ya shigo masa,d'aukan wayan yayi ba tare daya tsaya dubawa ba,can daga d'ayan gefen muryan Sultan ya d'aki kunnensa
"Man..Wai ina ka mak'ale ne..? Tun d'azun fa na gama amma na jika shiru.."

"Da yake ai ka ajiye ni ne shi yasa zanyi zaman jiranka ba..??"

"Haba mana man,,duka fa ba wannan maganar bane,kana ina yanzun ni sai nazo na same ka..!?"
Jinjina kai yayi irin na ka rainawa kanka hankali kafin ya ce
"Ina school,,idan kayi sauri zaka iya tarar da ni acan."
K'it ya sake katse kiran sannan ya shiga tattara sauran y'an kayansa ya nufi hanyan hostel..

*One week later..*
Cikin sauri ya fito ya nufi inda ya parker motansa,a lokacin Sultan ya biyo shi a baya cikin saurin yana tambayarsa inda zashi,bai kula shi ba ya shige cikin motan had'e da take ta,dai² isowar Sultan shi kuma ya d'aga a gurin,tsayawa kawai Sultan yayi rik'e da waist d'insa yabi shi da kaallo zuciyarsa cike fal da mamakin inda za shi cikin sauri haka,,ta mirror yake hango Sultan har ya b'acewa ganinsa,murmushi ya saki mai burgewa sannan a fili ya furta
"Ba zan tab'a bari ka san inda zani ba.."
(Tofa fan's kunji wata sabuwa,ko mene ne dalilin Hammad na fad'in haka..?? Allah shi ne mafi sani,,amma bari muci gaba da binsa a baya,da sannu zamu gano dalilin)
Tun daya d'auki hanya yake shek'a gudu a bunsa,yayin da zuciyarsa take cike da wani irin shauk'i,cikin mafi k'ancin mintuna sai gashi ya iso dai² mararrabar daya saba tsayawa,bayan ya bar motan a gurin mutumin da yake bawa ajiya,sannan ya d'auka hanyan da zai kaishi cikin k'auyen nasu,yayi tafiya mai d'an tsayi kafin ya iso k'ofar gidan,tun a bakin zaure ya tsaya yayi sallama sannan ya koma gefe daga jikin bishiyar dake gurin ya jingina,bai wani jima sosai da tsaiwa a gurin ba Baban Sabina ya fito yana duba wanda yayi sallamar,ganin wanda ke tsaye a gurin sai ya sashi sakin fuska yana nufar gurinsa yake fad'in
"Maraba da takwara.. Yau a gari..??"
Murmushin shimaya mayar masa kafin ya durk'usa har k'asa ya gaida shi,cikin mutunci Baban ya amsa masa,sannan yayi masa jagaba suka isa cikin gidan,sun gaisa da jama'ar gidan kafin suka nufi turakar baffa da a lokacin yake k'ok'arin fitowa nan suka had'u a bakin k'ofa,ko da ganin Hammad tare da d'an uwansa take baffa ya saki fuska yana fad'in
"Maraba da mutanen Kano.. Kune tafe da wannan ranar..?? In ce dai ko har ka dawo makarantar..??"
Fuskarsa a sake ya amsawa baffa
"Na dawo baffa,,yau sati guda kenan,sai dai rashin lokaci da yasa ban zo ba.."

"Kayyahh.! Dama samun lokaci a gurin y'an makaranta ai da wahala,,musamman ku da kuke jami'a.. Fatan dai har kullum baya wuce ubangiji yasa ku kasance masu samun nasara.."

"K'warai kuwa Yaya,, ai sunama k'ok'ari a karatun,,mu kam da yake ba muyi ba bamu san dad'in saba,sai dai y'ay'a da jikoki da muke fatan ace su samu suyi.."
Daga haka duka sai suka d'unguma zuwa cikin d'akin dan su samu dama su tattauna musamman Hammad da yake tafe da magana a bakinsa zuwa ga baffa,lokacin da suka zauna,bayan sun sake gaisawa sannan ne Baban Sabina ya fita ya barsu su biyu a cikin d'akin,,bayan fitarsa a d'akin babu jimawa sai baffa ya juya ya kalli Hammad da kulawa yana fad'in
"Mai babban suna ya ka baro magabatan naka..?? Fatan duka suna lafiya..??"
Sai daya gyara zama sannan ya amsawa baffa da
"Suna nan lafiya k'alau baffa,sunce ayi muku godiya sosai,sunga abun sak'o,Allah ya saka da alkhairi.."
Murmushi baffa yayi sannan yayi shiru,, shima Hammad sai yayi shirun cikin zuciyarsa banda tunanin hanyar daya dace ya sanar da baffa abunda ke faruwa babu abunda yake yi,,yanayin yadda yayi shiru fuskarsa ta bayyanar da alamun damuwa yasa baffa kallonsa da kulawa kafin yayi magana
"Mai babban suna,,ince dai kana lafiya..Kuma babu wani abu da yake damunka..??"
D'ago kansa yayi dake sunkuye yana sakin ajiyar zuciya,kafin ya girgiza kai,cikin sanyin jiki da rashin hope ya fara magana
"A gaskiya baffa ba lafiya ba.."
Saurin gyara zama baffa yayi yana fad'in
"Subhanallahi..! Wani abu ya faru da kai,ko kuwa da wani naka..??"
Shima d'in gyara zaman ya sake yi kafin ya fara zayyanawa baffa duk abunda ya faru tun daga kan maganar da suka yi kwanakin da suka gabata akan Sabina,lokacin daya shaida masa zai sanar da magabatansa har zuwa duk yadda suka yi da Daddy'nsa,sai dai ya b'oye masa batun ra'ayin Daddy akansu,,fuskar baffa duk da yaji batun na Hammad kuma baiji dad'in hakan daya faru ba,amma kuma bai hana masa yin murmushi ba
"Mai baban suna,ina ganin wannan ba matsala bane da har zaisa ka shiga damuwa,tun da farko ko da kazo min da wannan batun nina amince maka ka nemi soyayyar yarinyar nan,saboda haka dan mahaifinka ya nuna cewa sai ka kammala karatu ai ba wani abu bane,kayi hak'uri da duk abunda yace akan maganar,sannan ka zama maiyi masa biyayya in sha Allah komai zaizo da sauk'i,, mu idan har ta b'angaren mune baka da matsala damu,da yardar Allah babu wani abu da zaisa mu canja ALK'AWARIN da muka yi maka,,sannan matuk'ar akan SHALELE ne ni da kaina na amince maka ka ci gaba da nemanta daga yanzun har zuwa lokacin da mahaifinka zai sakko ya tuntub'eka da batun..Amma kayi hak'uri da duk hukuncin da zasu zartar,in sha Allahu alkhairi yana nan zuwa.."
Maganar baffa sosai tasa Hammad jin tsananin farin ciki coz baiyi tunanin samun wata dama daga garesu ba akan batun,sai gashi a garab'asa ya samu amincewar baffa,har kuma yana bashi tabbacin yaci gaba da kafa gwamnatinsa,godiya sosai yayi masa had'e da addu'o'i na fatan samun tsawon rai,sun d'an tab'a hira kafin baffa ya fita ya barshi zaune shi d'aya da niyyar turo masa ita idan ya fita,ko daya fita a d'akin baffan da kansa yaje wajensu Sabina ya kira ta,bayan daya tabbatar ta tafi gurin Hammad d'in sannan ya fita daga gidan..

Lokaci ya ci gaba da tafiya yayin da shak'uwa,yarda da juna had'e da soyayya mai tsuma rai ta sake shiga tsakanin Hammad da Sabina,a duk lokacin da aka ce yau weekend ne cikin kwanakin bazaka tab'a samunsa a cikin skul ba,tun safe idan ya tafi k'auyen nasu tofa ba shi zai dawo ba sai yamma sosai,a haka rayuwa taci gaba da gangarawa,yayin da ta b'angaren karatunsa ya sake nutsuwa coz yana son cika burin mahaifinsa akansa,duk da soyayya daya tsinci kansa a ciki ko kad'an hakan bai hana masa mayar da akalar hankalinsa kan karantun ba,musamman daya kasance yanzun suna tsakiyar last semester nasu....



*Kuyi hak'uri fan's da abunda ya faru,kun san rayuwa kana naka tsarin,ubangiji yana nashi,wanda mu duka ni da ku mun sani tsarin Ubangiji akanmu shi ne dai²..Buh in sha Allah yanzun zamu ci gaba da tafiya tare da yardar Allah.Na gode sosai da addu'o'inku,fatan rabb ya k'ara mana zumunci.*




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*Am really sorry friends,wollah kwanakin nan ni kaina nasan dauriya ne kawai nake yi amma bawai dan ina jin dad'in jikina ba,besides ma yanzun duka bama samun wuta akai² sai dare,da rana aiki ya kan had'armin,dare kuma kun san mahuta ne a gurin ko wane bawa,,sai dai muyi ta fatan su daidaita al'amuran wutar NEPA kamar da can,buh in Allah ya yarda ko da ace babu yawa idan har na samu aiki yayi min sauk'i za kuna jina..Ku k'ara hak'uri da ni,ina tare da ku a koda yaushe..💝*

*19.*
_#Tension_

Cikin wannan lokacin a hankali semester d'insu yaci gaba da yin nisa,yayin da bisa dole yasa Hammad jingine duk wasu al'amura nasa a gefe yaci gaba da fuskantar exam dake hararo shi,batun zuwansa k'auye kuwa a yanzun kasancewar baya samun wadataccen lokaci sosai na zirga² tsakanin k'auyensu da skul shima sai ya ajiye shi gefe,ya tattara hankalinsa kacokam a guri d'aya,ma'ana dai ya maida shi kan karatunsa,wanda a kullum addu'arsa,fatansa da kuma jajircewarsa baya wuce ace ya fita da sakamakon da Daddy'nsa zaiyi alfahari da shi,har ma da fatan ace Daddy ya yarje masa kan batun soyayyar sa duk da yasan abune mai wahalar gaske..

*Some month leave...*
Lokaci ya tafi sosai,yayin da ta kowane b'angare ake samun ci gaba,,a gefen Hammad kam a wannan lokacin yana ta sake had'uwa da ci gaba a rayuwarsa,wanda a yanzun haka abunda ya rave masa ya kammala service nasa bai wuce y'an kwanaki ba,,wanda tun a wancan lokacin da yake shirin tafiya,kasancewar Daddy'nsa da yake sananne a k'asar nd ya shiga ya fita kan batunsa da yace baya son yin nisa da gida,yasa sai aka barshi a nan Kano,dan haka ko da aka tashi posting nasa shi da kansa ya zab'ama kanshi inda yake muradi watog garin WUDIL,coz a gurinsa yana ganin hakan shi ne hanya mafi sauk'i da zata sake bashi damar kusanta kansa zuwa ga soyayyar ta.

A b'angaren iyayen Sabima kuwa,tun lokacin da baffa suka yi magana da Hammad akan batun soyayyarsu,ko kad'an baffa bai sake tayar masa da batun zuwan mahaifansa ba,ko ya tambaye shi har tsawon wane lokaci ne zasu zo a tsayar da maganar auren su,duka tsakanin baffa da baban SABINA babu wanda ya tab'a tuntub'arsa da maganar har zuwa yanzun da shak'uwarsu ta sake yin k'arfi sosai,,duk da irin tsaigumin da yake yawo a cikin garin,akan al'amuran familyn a yanzun,wanda cikin wannan lokacin duk inda mutim zai zauna hiran da zaiji yana yawo kenan,haka nan babu wani majalisa da zata taru ta watse ba tare da an sako zancen family'n ba,nd haka nan ba zaka tab'a jin wani maganar kirki akansu ba sai dai akasin hakan duk da kasancewar sune asalin kafuwar garin,haka nan kowa da irin abunda zaka ji yana fitowa daga bakinsa,yayin da wasu ke fad'in alkhairi,wasu kuwa sharri ne zaka ji ya biyo bayan maganganun su,a lokacin da wasu ke cewa kwad'ayin abun duniya yasa su baffa bawa SABINA goyon bayan kula d'an binni,yayin ne kuma zaka ji wasu sunce su baffan suna son yin amfani ne da wannan damar ta hanyar tallata ahalinsu a gurin manyan masu kud'i,muaamman ma ita SABINA data kasance SHALELE a gurinsu duka,shi yasa suka k'i barin wani cikin samarin garin ya nemi aurenta,kamar yadda suka k'i had'a ta da LADO,ko wane lokaci suke cewa sun bada aurenta ga wani bare can a waje,,haka dai maganganu marasa dad'i suka ci gaba yawo,wanda basu tsaya iya kan su baffa kad'ai ba hatta da sauran yaran gidan dukansu suma basu tsiraba daga zage²n da ake yi d'in,buh duk da haka baffa sai ya sake toshe kunnensa bai kankama kowa ba,haka nan duka ahalinsu ya gargad'e su akan kada yaji ko ya gani,wani ciki ya tanka maganar duk da zaiji an fad'a.Cikin wannan yanayin rayuwa mai cike da nutsuwa gami da kwanciyar hankali taci gaba da gudana a tsakanin wad'annan ahali..

Cikin nutsuwa take tafiya kan hanyarta ta dawowa daga makaranta,duk da tare suke da su Hamudan amma ba lallai ne ayi saurin gano hakan ba,kasancewar tsakaninsu da ita akwai y'ar tazara sunyi d'an nisa da juna,da yake sunyi gaba da ita saboda guje²n da suke suna tafe suna tsokanar juna,a haka har suka k'araso k'ofar gida,,shigowarta a zauren gidan yayi dai² da lokacin da LADO ya sawo kai zai fito,ko da ganin ya riga ya shigo tsakiyar hanya babu kuma yadda za'ayi ta kaucewa had'uwa da shi sai yasa ta matsawa gefe ta bashi hanya tana jiran ya wuce,coz tasan idan tace zata wuce ba zai tab'a bata hanya ba,nd yana iya hankad'eta gefe ya kuma bi ta kanta,duk a dalilin k'in amincewar da tayi da

Please Login or Register in order to submit comment