Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

amsawa..Shi kenan Hammad,kaje ga abincin can idan ka gama yana jiranka.."
Sake juyawa tayi da niyyar tafiya ya sake rik'e hannunta gam a nasa,wannan karon a fusace ta juyo dan iya b'aci ranta ya b'aci da abunda yayi d'in
"Sake min hannu Hammad..Ka san ban fiya son wasa ba a wasu lokutan ko..!?"
Kasa sakin ta yayi kamar yadda ta buk'ata,zuwa lokacin ba idanunsa kad'ai suka birkice ba hatta da jijiyon kansa tuni duka sun gama bayyana afili,tsawar data yi masa ne ya sashi saurin sakin hannun nata yana binta da kallon mamaki,da b'ari a cikin muryansa yake fad'in
"Mah please..Ki saurare ni,wollahi i will explain..!"

"Kamin shiru Hammad,da kasan zaka min bayanin kana ji ina kiranka ka kasa amsawa..!?"

"Mah please,,kiyi hak'uri Zan miki bayanin komai..I promised u zan fad'a miki..!"
Yadda yake a birkice zuwa lokacin yasa ta yin jimm tana k'are masa kallo kafin ta ce
"Uhhuumm.! Ina sauraren ka,buh don't try to lie on me..Ka san zan gane."

"Mah..! I know u will understand,,buh ki d'an zauna tukun sai na miki bayanin.."
Da farko kamar baza ta zauna ba,kome kuma ta tuna sai ta nemi guri a saman resting chair tana basarwa,a kusa da ita ya zauna sannan ya sake rik'o hannunta,cikin nutsuwar dole ya fara mata bayanin abunda yake faruwa,kaf babu abunda bai sanar da ita ba,,yanayin kallon da take masa tun daya fara bata labarin ne yasa jikinsa yin sanyi,a hanaki kuma sai ya sunkuyar da kansa k'asa lokacin daya gama bata labarin,ci gaba tayi da kallonsa har na tsayin lokaci kafin tasa hannu ta d'ago chin d'insa ta zubawa fuskarsan nan mai cike damuwa idanunta
"Hammad..! Kalle ni nan..!"
Ta fad'a cikin wani irin muryan da bai tab'a jin tayi masa magana da shi na,kasa d'agowa yayi kamar yadda tace d'in,ajiyar zuciya ta sauke kafin taci magana,muryanta cikin rauni zuwa lokacin
"Hammad.! Na ce ka d'ago ka kalle ni..!"
A hankali ya d'aga idanunsa ya sauke su a fuskarta sai dai cike yake da tsoron abunda zai fito daga bakinta dan yadda yaga yanayin da take ciki,marairaicewa yayi kamar zai mata kuka yana girgiza kai ba tare data kula da abunda yake yi d'in ba ta furta
"Da gaske kake..Kana son ta..!?"
A bazata maganar ta tazo masa,buh duk da yana cikin tsaka mai wuya sai daya saki siririn murmushi,sake rik'o fuskarsa tayi a hannayenta biyu tana fad'in
"Kayi magana kai nake sauraro..Na ce da gaske kake..!?"
Kai ya girgiza kafin ya ce
"Ehh! Mamma buh..!"
Saurin sakin fuskarsa tayi kafin taja baya kad'an
"Shin ka san abunda kake shirin aikatawa Hammad..?? Kasan mene ne zai faru kuwa idan har ka bari Daddy'nku yaji wannan maganar..!?"
Girgiza mata kai yayi alamun ya sani
"Ka san irin halin da zan shiga a sakamakon wannan maganar da kazo da ita idan har ya sani.!?"
A hankali ya sake girgiza kai
"Me yasa Hammad..? Bayan ka sani amma kake k'ok'arin saka mu cikin damuwa..!?"
Da kyar ya iya raba lab'b'ansa kafin ya furta
"Mah..duka ba komai ya sani yin haka ba face soyayyar ta.. Ki taimaka kiyi ma Daddy bayani,,i know he'll understand.."
Jinjina kai tayi tana had'iye yahu sannan ta mik'e tsaye
"Shi kenan Hammad,tunda haka ka zab'a mana daga ni har kai,,zanyi iya k'ok'arin da zan iya na fahimtar da shi..Amma ka zauna cikin shiri,kasan hukuncinsa akan magana irin wannan bana wasa bane,daga yanzun zuwa ko wane irin lokaci dole ne dukanmu na san zamu fuskanci hukunci..!"
Tana gama fad'in haka gudun kada ya sake cewa zai fad'a mata wani maganar tayi saurin ficewa a d'akin,ajiyar zuciya shi kansa ya shiga jerawa lokacin daya tabbatar ta bar d'akin kafin ya zame ya kwanta saboda sarawan da kansa yayi a dai² lokacin,ya jima a kwance cikin wannan halin kafin ya tashi a daddafe ya nufi bathroom da niyyar sawa jikinsa ruwa ko zai ji dama².

Mamma kuwa lokacin ko data fita a d'akin nasa cikin tsantsar tashin hankali ta isa nata bedroom d'in,tana shiga ta maida k'ofar ta kulle kanta,duka tunanin ta a lokacin da damuwarta shi ne ta yaya ne zata fuskanci Daddy da wannan maganar bayan ta san burinsa da sharad'insa akan duka yaransa..?? Shin yanzun ta ina ne zata nemo mafita,sannan da wane irin k'warin guiwa ne zata tunkari shi ta sanar da shi buk'atar Hammad d'in a gare shi na zuwa nema masa auren yarinyar da yace d'in..?? Tambayoyi ba iyaka suka dunga zuwa mata a zuciya da kwakwalwarta buh ta kasa tantance wanda ya kamatama tayi adopting.
Wannan ranar ko nace dare dukansa yazo mata ne a wani irin hargitse,nd ta dage kan lallai sai tayi finding hanyan daya kamata tabi wajen shaidawa Daddy irin matsalar da za'a iya samu idan har yak'i amincewa,,a wannan lokacin kuwa taimakon da Allah yayi mata a wannan ranar duka daddyn baya garin,da bata san inda zata sa kanta ba dan tsananin tashin hankali,,har gabannin ketowar alfijr bata iya runtsawa ba,sai dai kuma a lokacin ne wani irin bacci ya fara kawo mata farmaki,buh still tana sake enduring kanta akan ba zata kwanta ba har sai ta samo abunda take nema d'in,sai da taga alamun zata iya fad'uwa sannan ta hak'ura shima d'in a dalilin bacci ne da yake neman cin k'arfinta yasa sai ta yankewa kanta shawaran d'auro alwala,bayan data d'auro alwala ta shimfid'a pray mat sannan ta daidaita a tsayen ta kabbara sallah duk da yadda take jin jiri na d'iban ta kad'an²,nafila tayi sassauk'a mai gajerun surori kafin ta shiga jera addu'o'i akan ubangiji ya bata nasara,nd ya saka mata juriya akan duk abunda zai biyo baya,,ta d'auki tsayin lokaci tana addu'o'i kafin ta d'an jingina bayanta da jikin bed still tana ci gaba da lazimi a hakan.

A b'angaren Hammad shi kansa a wannan daren bai iya runtsawa ba saboda fargabar abunda zai biyo baya idan har Daddy ya san da zaman wannan maganar,haka nan sai bayan lokacin daya sanarma da Mamma abunda ke faruwan ya fara dana sanin rashin dakatar da ita daga fad'awa Daddy,haka nan sai a lokacin ya fahimci irin matsalar da yake k'ok'arin jefa ta,tabbas ya san kafin daddy ya same shi dole ne sai yayi mata fad'an ita ne ta bashi goyon bayan da har zai zo masa da irin wannan batun,dan haka shi kansa a daren kasa runtsawa yayi,,duk da yadda kansa ya addabe shi da ciwo amma ko kad'an bai samu daman runtsawa ba,wannan yasa ciwon sai ya sake had'e masa,yana kwancen banda juyi babu abunda yayi ta fama da shi a daren,,har aka fara kiraye²n sallah bai samu daman runtsawa ba.A hakan da yake lokavin da yaji kiran sallah ya lallab'a ya shiga bathroom ya d'auro alwala,sai dai ko daya fito d'in nan yaji bazai iya fita ba,nan a d'aki yayi sallah sannan ya koma ya sake kwanciya,zuwa lokacin kuwa ko idanunsa da kyar yake bud'e su,kafin safiya tuni har zazzafan zazzab'i ya saukar masa.

Lokacin da gari ya gama wayewa,har around 12:15pm yana kwance cikin mantle ba tare daya iya ta shi ba bare ya iya sanar ma da wani a gidan,,Fitowar Mamma a karo na sau babu adadi yasa ta kula da har lokacin bai fito ba,dan haka sai ta yanke shawaran duba shi ta gani ko lafiya yake,while deeply tana jin zuciyarta tana tsinkewa,a bakin k'ofar bedroom d'insa ta tsaya tayi shiru zuwa wani lokaci kafin ta fara knocking,shirun da taji ba'a amsa ba ba kuma ayi mata alamar da zata gane cewa da mutum a ciki ba yasa ta jin hankalinta yana k'ok'arin sake tashi,cikin sauri sai ta tura k'ofar nd tana sake kiran sunansa,d'akin gaba d'ayansa banda duhu babu komai a cikinsa,duk da gari ya gama wayewa a lokacin har azhr tana neman kawo jiki,amma idan har kana ciki babu yadda za'ayi ka gane hakan,fluorescence d'in d'akin ta shiga k'ok'arin activating nd tana sake ambaton sunansa,idanunta ne suka sauka kansa a kwance cikin mantle duk ya duk'unk'une daga gani ba sai ta tambaya ba tasan akwai damuwa,cikin sauri ta isa kusa da gadon tana maimaita fad'in kalmar
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..!"
Sai data zauna daga bakin gadon sannan takai hannunta ta d'an janye mantle d'in tana tab'a jikinsa
"Hammad..! What's wrong with u..!?"
Ko idanunsa baya iya bud'ewa zuwa lokacin amma a hakan so yake ya bud'e su dan yayi mata magana,yayin da wasu irin hawayen azaba suke biyowa ta gefe,da sauri ya maida su ya runtse yana sakin numfashi da kyar
"Mah..!"
Abunda kad'ai ya iya fad'a kenan,yana sake runtse idanunsa,saurin d'ora hannunta tayi a saman kansa cike da tausayin halin da yake ciki take fad'in
"Lemme call ur Dad..!"
Tana k'ok'arin tashi shima d'in duk da halin da yake ciki sai k'ok'arin mik'ewar yake,da sauri ta dakatar da shi cikin rud'ewa tana fad'in
"A'a Hammad.. Koma ka kwanta ina zuwa yanzun."
Cikin sauri bayan ta maida shi ta kwantar sannan ta fice,bedroom d'inta ta koma da niyyar d'auko wayarta sannan ta sake dawowa d'akin nasa,ba tare data iya zama ba ta shiga neman line Daddy'nsu,sai data masa kira ya kai uku kafin ta samu ya d'auka,bai ko tsaya jin me zata ce masa ba ya hau fad'in
"Haba Asiya,,mene ne yasa baza ki iya hakur'in jira kiga na kira ki back ba,,u know ina meeting,nd still kina sake kira na..Duk da nake shugaba kin san saina girmama doka kafin na k'asa dani su bi ko..!?"
Ajiyar zuciya ta saki ba tare data kula da fad'an da yayi mata ba,da kamar ta b'oye masa halin da ake ciki d'in sai taji yin hakan ma wani laifin ne zata k'arawa kanta a burinsa idan har ta bari sai daga baya zai sani
"Am really sorry Yallab'ai..! Buh idan ban yi haka ba,yaya kake so nayi..!? Ka tafi ka barmu yau kwana nawa kenan ko kiranmu kaji halin da muke cikima baka yi ba,,,forget ma,shin dan na kira na shaida maka cewa yaronmu ba shi da lafiya sai ya zama laifi..??"
Saurin katse ta yayi cikin d'aga murya da fad'in
"Yaronmu kika ce..?? Wanne a ciki..? Hammad ne ko Bassam..?"
Yadda yake a d'an rud'e yasa ta saisaita muryanta sannan ta furta
"A'a Hammad ne..!"

"Ya Allah..! Amma shi ne ba zaki sanar dani tun da wuri ba..?? Wannan wane irin sakaci ne haka kike yi Asiya..??"
Shiru tayi masa tana jin yadda yake naganar a d'an hasale,sai data bari ya gama fad'an sannan ta shiga bashi hak'uri nd ta shaida masa duka ciwon nasa ba'a d'auki lokaci ba,itanma shigowarta kenan ta iske shi bashi da lafiyan,ajiyar zuciya Daddy yayi sannan yace mata a yau d'in zai baro duk abunda yake yi ya taho duk dare,nd yanzun zai kira doctor'nsu ya sanar da shi halin da ake ciki,daga haka ko sallama bai jira sunyi ba ya katse wayen sannan ya kira likitan ya sanar da shi,,ko daya gama wayan hankalinsa kasa kwanciya yayi nan take yasa ayi canceling zaman nasu,,,kafin wani lokaci tuni har yasa masu tsaronsa sun d'auki hanyar airport da shi.

Within 45 minutes da zuwan likitan da duba jikin na Hammad zuwa yi masa allurai ya tafi,har motocin Daddy shida escorts d'insa sun fara jeruwa a harabar gidan,securities d'insa ne suka fara fitowa ko kafin su bud'e masa k'ofar motan tuni har ya bud'e ya fito,babban mutum ne da ak'alla shekarunsa baza su wuce (65) ba,sai dai yanayin daular da yake ciki da zaisa ayi masa kallon kamar bazai kai hakan ba,,cikin shiga ta alfarma ya ratso ta tsakiyar securities d'insa yayi gaba,a baya suka shiga binsa,ba tare da yabi ta kansu ba ya nufi hanyar da zata sada shi da ainihin cikin gidan nasa.....



*Na riga da na sanar da ku tun farko,yanzun ba sosai muka cika samun wuta ba,kamar yadda nasan da yawa kun san da matsalar da ake fama da ita kenan a gari,nd chajin engine kunsan bai cika value ba,dan haka daga ni har ku sai mun k'ara hak'uri..*😢


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_My fan's aradu ina ji da ku,a duk inda kuke ina matuk'ar k'aunar ku,especially wad'anda ke sank'amo comments ina jin farin ciki da comments d'inku,mutane na dake duniyar whatsapp,Facebook nd wattpad dukan ku a koda yaushe ina tare da ku kuma ina jinjina muku,fatan rabb ya bar k'auna.💞_


*16.*
_#Rejection_

Shigowarsa cikin parlor'n ya iske shiru alamun babu kowa a ciki,dan haka kai tsaye ya ratse hanya ya nufi hanyan staircases d'in,cikin sauri yake tsallake su kamar zai tashi sama,daga nan bai tsaya ko ina ba sai a cikin bedroom d'in Hammad dan yadda yake jin hankalinsa har yanzun bai kwanta ba duk da Mamma ta fad'a masa ciwon na lokaci guda ne,da ita ya fara arba lokacin daya shiga cikin d'akin,sallama yayi wacce ita kanta a ciki² yayi ta sannan ya nufi gurin da Hammad ke kwance a saman gado,dai² kansa ya d'an tsaya kafin ya kaalli sashin da Mamma ke zaune jigum,a hankali ya sunkuya ya shafa suman kan Hammad dake wani irin wahalallen bacci sannan yayi pecking nasa a chicks,k'asa² ya furta
"Maybe u are down now,but with the love nd care that we are for u,u shall soon recover..Get well soon baby.."
(Ni dai sakin baki nayi a gurin dan yadda naji daddy ya kira saurayi kamar Hammad da baby,shin dan Allah ku fad'a min ni kuma me za'a kira ni da shi..?? face smile).
Dai² k'afafunsa ya koma ya zauna yana kallon yaron nasu zuciyansa da wani irin pain na ganin halin daya iske shi a cikin,har lokacin bai iya furta ko da kalma d'aya ba wa Mamma,ita kanta Mamma'n k'arfin hali ne kawai take izuwa lokacin dan tasan matuk'ar ace yasan dalilin ciwon na Hammad dole ne a kwashi drama a gidan,cikin dauriya tana kallon mijin nata ta furta
"Welcome home dear..!"
Kai ya jinjina mata ba tare daya amsa ba,zuwa can kuma yana kallon Hammad ya furta
"Me likita ya sanar dake game da ciwonsa..!?"
Sai da tayi jimm while itama tana kallon Hammad d'in ta furta
"He say's yayi stressing kansa ne da yawa,shi yasa ciwon ya masa mugun kamu lokaci guda.."
D'an yamutse fuska yayi sannan ya maida hankalinsa duka kanta
"Kina nufin kice min akwai wani abu dake damunsa da bai iya sanar miki ba..!?"
D'auke kai Mamma tayi zuwa gefe ba tare data bashi amsan tambayar da yayi mata ba
"Asiya..! Dake nake magana,ina son ki sanar dani dalilin da yasa kika yi wannan sakacin.."

"Ya sanar da ni komai,,buh..!"

"Buh what..!? Mene ne dalilin da yasa baza ki sanar da ni tun da wuri ba tunda kin san matsalar.!?"
D'an kallonsa tayi tana cije gefen lip kafin tace
"Haba Yallab'ai,, ta yaya ne har ka bani wannan damar,,kada fa ka manta tsayin kwanaki uku kenan baka kira mu kaji a halin da muke ciki ba,wannan fad'an naka ai na rashin gaskiya kake yi..!"
Kallonta yayi wani iri kafin yace
"Asiya..! Ban tambayeki wannan ba,ko nayi fad'a kan gaskiya ko nayi akan rashin ta,wannan duk ba damuwar ki bane,all i know shi ne na barki da yara nd kin san amanar su duka tana hannun ki,ni ban tambayeki komai ba yanzun daya wuce dalilin da yasa baki sanar dani ba.."
Yadda taga neck veins d'insa sun fara d'agawa alamun a ko wane irin lokaci zai iya d'aga murya yayi mata fad'a,tsam sai ta mik'e tayi waje ba tare data tanka ba,kallon ta yayi ya jinjina kai sannan ya mik'e a fusace yabi bayanta,tana shiga bedroom d'inta shima yana shigowa
"Asiya..!"
Ya kira sunanta da wani irin murya,a hankali ta waiwayo ta kalleshi kafin ta d'an juya a ranta tana fad'in
"Na san dama za'ayi haka.!"
Baya ta sake juya masa kafin ta amsa
"Me yake damunki ne.. Ina magana kina juya min baya..!?"

"Baka damu ka san damuwata ba,,to ni wace cema da za'a damu da damuwarta,aikina kawai na kula da kai,gidanka da yaranka..Ko ba shine aikin daka d'auko ni nayi ba.!?"
Tana maganar tana bud'e closet tamkar mai neman abu,rufe idanunsa yayi sannan ya k'araso inda take,ta bayanta ya tsaya a hankali ya rungume ta yana sakin ajiyar zuciya,,sanyin daya ratsata sakamakon yamayin rik'on da yayi mata yasa ta lumshe idanunta,cikin nutsuwa haka nan muryansa a sanyaye ya furta
"Haba masoyiya,, me yasa ne wasu lokutan kike son ki fad'a min irin wannan maganar,al'halin kin san nafi kowa jin b'acin rai da jinsu..!?"
Juyowa tayi k'ok'arin yi,tana kallon cikin idanunsa take fad'in
"Idan banyi haka ba,yaya kake so nayi,tunda ka nuna min fifiko akan yaranka..? I thought ko dai ace ba nice mahaifiyar data haifa maka suba,ya dace ace ko rik'on su nake kayi min irin hakan..?? Zuciyafa bata da k'ashi,yaya kake tsammani idan akace yaran nan ba nawa bane..? Kana ganin zasu samu irin wannan kulawar ne,ko kuwa ita matar taka zata juri ka dunga nuna mata fifiko akan yaranka..? Ba ni kad'ai ba koma wace mace ce idan har zaka nuna mata haka zata yi k'ok'arin zare hannunta ne akan yaranka matsawar ace yaran ba nata bane,,haka nan abunda kake min akansu gaskiya ya fara damuna,nima fa ina da nawa hak'k'in akan su,akan wane dalili ne zaka na gwadamin fin k'arfi akansu..? Ni fa na haife su.."
Yadda take fidda maganar dalla² fuskarta da alamun damuwa yasa dole Daddy ya sake sassauta murya,a hannakli ya kamata sannan suka nufi bakin bed d'inta,sai daya zaunar da ita sannan shima ya zauna,cikin sanyayyar murya ya fara mata magana
"Look Asiya..! Ya kamata ki fahimce ni,nd ki fahimci inda magana ta ya nufa,ko kad'an ba wai ina nuna miki na fiki iko da yaranmu bane,kiyiwa lamarin nan kyakykyawan fahimta,duk abunda kika ga ina yi ina yinsa ne ba don komai ba sai don ina son na gina rayuwarsu,,ta inda ko da ace bama raye ni dake zasu yi alfahari da cewar mun basu tarbiyyar daya dace mu basu a matsayin mu na wad'anda Allah ya dank'a amanar su a hannunmu,,idan naji kina irin wad'annan maganganun akan irin haka na kanji babu dad'i,sannan kina sawa na fara tuhumar kaina da ko na tauye hak'k'in ki da Allah ya d'ora shi bisa wuyana.."
Shiru tayi tana saurarensa har zuwa lokacin da yayi shiru,kafin ya ci gaba
"Shi kenan Asiya, amma ya kamata ki sanar dani matsalar da ake ciki,tunda Allah yasa na dawo yanzun.."

Numfasawa tayi kafin tayi magana
"Ehh toh.! Ni dai a iya sanina da kuma maganar da muka yi da shi a jiya,shi ne ya zomin da batun wata yarinya ne daya ganta kuma..!"

"What..!? Yarinya kika ce,,wannan wane irin maganar banza ne kike yi..!?"
Shiru tayi cikin ranta tana jin yadda maganarsa ya dake ta nd dama dole ne tasan za'a yi hakan
"Ya kamata ki sani har yanzun Hammad bai kai munzalin da zan masa aure ba,ni a gurina har yanzun yana matsayin k'aramin yaro ne,nd idan lokacinsa yayi da kaina ba sai wani ya sani ba ko shi ya fad'a min zan masa aure final..!"

"Haba Yallab'ai.. Wannan maganar taka ai ba mai yiwuwa bane,tunda har yanzun da kansa ya fito ya nuna auren yake so mai zai hana ayi masa,shin kasan matsalar da k'in amincewarka zai haifar..?? Kayi tunani kafin ka yanke hukunci.."

"Na ruga na yanke hukunci,,kin san magana d'aya nake bana maimautawa,to yanzun zai maimaita miki shi ne matuk'ar Hammad aure yake so a wannan lokacin bazan tab'a yi masa ba,sannan ina so ki jawa yaron ki kunne matuk'ar yace zai ja da magana ta akan wannan zancen,zan zare hannuna akansa,dan haka sai ya zab'a cikin biyu,,ni ko kuma maganar auren.."
Sosai rnta ya b'aci akan furucin da yayi buh ya zatayi idan har ta nuna zata bijere..?? Ita kanta ta san ba abune mai wahala ba ya zazzaga mata ruwan bala'i,to amma shin idan ta bar shi aka samu matsala fa..? A matsayinta na mahaifiya ita abun zai fiwa ciwo dan haka dole ta mik'e tsaye tayi yak'i da wannan ra'ayin nasa idan kuwa ba haka ba tofa lallai daga ita har Hammad suna cikin matsala,saurin dak'ile tunanin ta tayi sannan ta kalleshi
"Amma fa Yallab'ai kada ka manta wannan ra'ayi ne kawai irin naka,ba wai addini ne yace dole sai yaro ya had'a master's ko sama da haka ya isa aure ba,akwai bambanci mai nisa tsakanin rayuwar mu ta da,da kuma yanzun,ya kamata kaima ka fahimta.."

"Asiya..!! Ki yimin shiru da wannan maganar,hunkuci ni ya dace na yanke shi ko..? To na gama magana,ba rashin lafiya ba idan mutuwa zaiyi matsawar akan wannan maganar ne,wollahi na gwammace na rasa shi,dad'in abun ai ba shi kad'ai na haifa ba,idan ya mutu ina da wasu yaran,Bassam da *BADRA* sun isheni rayuwa.."
Jinjina kai tayi cike da takaici,ba tare data sake tofa wani abu cikin zancen ba ta mik'e tana shirin fita
"Ina zaki je da kika tashi..!?"
Chak ta tsaya a bakin k'ofar kafin ta bashi amsa cikin jin haushi
"Mene ne amfanin da zamana zai yi maka ni kuma..? Ina cewa maganar ta k'are..!?"
Girgiza kai yayi dan yasan a fusace take da shi akan maganar, buh ya zaiyi dole ne ya nuna mata k'in amincewarsa tunda shi dai har ga Allah, bai shirya yiwa yaransa aure a k'ananun shekaru kamar na Hammad ba (amma fa a ganin daddy),,shi kad'ai yasan iya adadin wahalar daya sha a rayuwa,dan haka dole ne ya tsaya ya gina rayuwar yaransa,nd itanma yasan yadda zai ji da lamarinta,dan haka zai zuba mata ido yasan da sannu zata yi fushin ta sakko,,bayan fitar Mamma shima ficewa yayi daga d'akin.

A b'angaren Hammad kuwa tun kafin shigowar Daddy bedroom d'in ya farka,kasancewar bai bud'e idanunsa ba yasa koda yaji muryan Daddy'n sai bai nuna alamar ya farka d'inba,haka nan tsoron abunda zai biyo baya idan har suka yi four eyes da Daddy yasa shi k'in bud'e idanun nasa,dan haka lokacin da Daddy yake masa addu'ar samun sauk'i duk ya jishi

Please Login or Register in order to submit comment