Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da damuwa yayiwa yawa ba,har wani shining da sparkling ke fita a fuskarsa mai d'aukar idanu,cikin sauri² ya sake tattara phones,car keys d'insa da envelope da Daddy ya bashi a daren jiya yayi waje,bai zame ko ina ba bayan fitowarsa sai wudil dan yadda yake jin zuciyarsa na azalzalarsa a lokacin idan har baiyi abunda take sak'a masa ba tabbas za'a iya samun gagarumar matsala.
Lokacin daya shigo cikin k'auyen ko daya isa cikin gidan,a nan ne kuma sak'on tafiyar da su baffa suka yi ya riske shi,inda aka sanar da shi sunje d'aurin aure can a wani k'auye da ake kira *INDABO* sannan ba lallai ne su dawo da wuri ba,gaba d'aya guiwoyinsa ne suka sanyaya lokacin da labarin ya iso shi,yayin da damuwa ta sake lullub'e shi bcos a lokacin gani yake daga wannan lokacin ba lallai ne ya sake samun wani chance ba,haka nan zuciyarsa sai shaida masa take shi kenan idan bai samu damar ganin baffa ba a wannan lokacin ba yayi loosing duk wani hope,,wannan shi ake kira samu da rashi,,ya taho da tunanin da zaran yazo ga baffa komai zai zai zo masa da sauk'i sai gashi ya iske baffan baya garin,shin har tsawon wane lokaci ne zasu d'auka kafin su dawo..?? Ya tambayi kansa,yana ganin shi da a yau jirginsu zai bar k'asar,gashi ko kayanma bai had'a ba ya fito daga gidan,saboda kasa samun nutsuwar zuciya da yayi sai kuma ya riski wannan abu,sake kallon agogon dake d'aure a tsintsiyar hannunsa yayi a karo na sau babu adadi,a yinin ranar gaba d'aya gani yake lokacin kamar wanda ake zuk'ewa da wani abu dan yadda yake fella gudu,dai² yana sauke hannunsa a k'asa ta shigo d'akin da sallama kanta a k'asa,tunda ya d'ago ya sauke idanunsa akanta ya kasa janyesu har sai data ajiye tray d'in dake hannunta,d'an nesa kad'an ta zauna har lokacin bata d'ago ba ta gaishe shi,sai daya saki ajiyar zuciya kafin ya iya amsa mata yana ci gaba da kallonta,dan yadda yake ji a zuciyarsa game da ita ji yake a lokacin tamkar ya had'iyeta ko zai samu sassaucin abunda yake ji d'in game da ita,,,duka sunyi shiru tun zamansu,yayin da kowanne da tunanin da yake a k'asan ransa,hiran ma da suka saba duka a yau sun gagara yinta sai kallon kallo da suke,ga Hammad kuwa a wannan lokacin rashin samun nutsuwa yasa shi kasa magana gashi har lokacin baiga baffa ba bare ya warware masa damuwarsa,shi yasa duk wasu kalmomin da yake tunanin yana da su suka tsere,ita kuwa Sabina ba komai ya hana mata yin magana ba sai tsabar kunyarsa da take ji,musamman daya kasance idanunsa suna kanta.

5:00pm agogon hannunsa ya nuna masa,zuwa wannan lokacin tuni ya gama fidda rai da samun damar ganin Baffa,dan haka kawai sai ya yankewa kansa hukuncin komawa inda ya fito yayin da yake jin babu dad'i a k'asan zuciyarsa,kallonta yayi ba tare daya samu damar fad'an komai ba ya mik'e,sai daya dai²ta tsaiwarsa sannan da kyar yayi k'ok'arin tattara kalmomin da suka masa saura a bakinsa ya furta
"My Lady..! Zan koma,,amma ina so idan baffa ya dawo,ki sanar da shi na zo muyi sallama ban same shi ba..Tafiyar gaggawa ta tasomin yau da dare zamu tafi idan Allah ya kaimu.."
Muguwar fad'uwa gabanta yayi lokacin da taji abunda yake fad'a,cikin sauri ta d'ago kanta ta zuba masa manyan idanunta,so take tayi magana amma ta kasa furta komai sai girgiza kai kawai data samu damar yi
"My Lady..!"
Ya kirata cikin wani sanyayyar murya,kasa amsawa tayi saboda wasu masifaffun hawaye da suka kunno mata kai,bai damu da rashin amsawar da tayi ba ya ci gaba da magana while yana tunkaro inda take tsayen
"My Lady.. Ina neman alfarma a gurinki..Ina fatan zan samu hakan daga gare ki..!"
Girgiza masa kai tayi sai dai tak'i yarda ta kalleshi haka tak'i yarda tayi magana dan tasan tana bud'e baki kuka ne zai fara fitowa,,murmushin k'arfin hali ya saki dai² lokacin daya tsaya nearer to her
"Da gaske kina so na..?? Kuma zaki iya aurena..??"
Maganar ta fito daga bakinsa,kai tayi saurin sake girgizawa tana murmusawa duk da tana jin damuwa,d'an murmushi jin dad'i shima ya saki sannan ya sake fad'in
"Zaki iya rik'e min amanar kanki..??"
Nanma ta kuma girgiza masa kai
"Shin zaki iya jiran dawowa na ko da zan kai tsayin shekaru ban dawo ba..??"
Wannan karon sai data d'ago ta kalleshi wanda yin hakan ya taimakawa hawayen da take b'oyewa damar sakkowa saman fuskarta sai dai tayi saurin k'unshe bakinta gudun kada sautin kukanta ya bayyana,tasan da zaran an jiyota jama'ar gidan suyi zaton ko wani abu yayi mata,sai ta sake girgiza masa kai,kai shima ya shiga girgiza mata alamun kada tayi kuka amma ina tuni hawaye sun gama wanke mata fuska
"Don't cry my lady..Kina son ki karya min zuciya ne.? Kukanki a irin wannan lokacin dai² yake da yasa ni fasa tafiya,duk da umarni ne na mahaifina,,Kiyi hak'uri ki daina min asarar hawayen ki, in sha Allah kamar yanzun zanje na dawo gare ki,,I promised..!"

Tana sheshshek'ar kuka take fad'in
"Har tsayin wane lokaci ne zaka tafi ka barni..??"

"Bana tunanin zan wuce shekara guda..!"
Shiru tayi bata sake cewa komai ba sai hawaye da take sharcewa a zuciyarta kuwa fad'i take
"Shekara guda..Kenan zai d'auke mu tsayin lokaci ba tare da mun had'u da juna ba..?? Waya sanima ko shi kenan ba zamu sake had'uwa ba..!"

"Am really sorry my Lady,,haka k'addarar mu yake,dole ne ko muna so ko bama so sai hakan ya kasance,buh idan muka yi addu'ah komai zai zo har wata rana ya wuce..Amma dan Allah ina so kada ki manta da cewar wata rana zan dawo gare ki kamar yanzun..!"
Zuwa yanzun kam tuni kuka yaci k'arfinta,durk'usawa tayi a k'asa taci gaba da kuka sai dai babu sauti a cikinsa sai zallar hawayen da yake zirara daga idanunta,saboda toshe bakinta da tayi,shi kansa Hammad kasa jurewa tsayawa yayi nan ya durk'usa a gabanta yana girgiza mata kai nd yana jin kamar ya rik'o ta zuwa jikinsa ya rarrasheta
"Please my lady..ya kamata kiyi shiru haka nan,kada ki sawa kanki damuwa,,ko kina son wani ciwon ya shige ki..?"
Saurin girgiza masa kai tayi
"Ok..! To ya isa haka,idan ba so kike ki karyamin zuciya nima nayi kuka ba..Shin kina son ganin hawaye na..??"
Sai ta girgiza masa a hankali cike da sakarci
"Ok..ya isa to kinji..ki bar kuka."
Hannu tasa ta fara sharce hawayen tana sakin ajiyar zuciya,zuwa lokacin idanunta har sun fara rikid'ewa,Hammad kuwa ganin yadda take sauke ajiyar zuciya akai² da yadda damuwa ya lullub'e fuskarta sai yasa shi kasa cewa zai tafi duk da lokaci ya tafi sosai,a haka yayi ta fad'a mata kalmomin da yasan zasu taimaka mata wajen samun nutsuwa,,sai daya tabbatar ta samu nutsuwa kafin da kyar suka hak'ura suka sake yin sallama,ba dan taso ba sai dan ya nuna baya son ganin kukanta yasa wannan karon tayi ta had'iye kukan,tafiya suke kamar marasa laka a jika har suka fito zauren gidan,suna daf da fitowa kwatsam sai ga su baffa sun sawo kai cikin zauren,lokaci guda wani gagarumin farin ciki ya ziyarce shi har bai san lokacin daya furta
"Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat..!"
A fili yana mai sakin k'ayataccen murmushi,ita kanta Sabina ganin murmushin dake fuskarsa sai daya bata nutsuwa,,cikin tsananin farin ciki da dawowarsu tun bai kai ga tafiya ba ya shiga yiwa musu barka da dawowa,da fara'a a fuskar dattijan uku suka amsa masa ma'ana baffa,baban SABINA sai kuma baban LADO,bayan sun gaisa da su baffa yake fad'in
"Mai babban suna..! Yau kuma sai kazo ka iske bama nan ko..!?"
Murmushin k'arfin hali yayi sannan ya amsa
"Wollahi kuwa baffa,ai har na fidda rai zamu had'u,sai kuma kuka dawo.."

"Allah sarki..Wollahi fa da yake munje INDABO d'aurin auren y'ar aminina ne,to kasan harkar jama'a shi yasa bamu samu tahowa da wuri ba sai yanzun.."

Sun sake gaisawa,sannan sun d'an tab'a hira a hakan,kafin su baffan suka bishi da fatan alkhairi tunda sunga ya fito yana shirin tafiya,sun san dai zai yi wahala ace ya tsaya,,amsawa yayi kansa a k'asa,zuwa can kuma har su baffa suna niyyar wucewa cikin gida Hammad yayi ta maza da cewa
"Baffa..Dama na zo ne muyi magana,sannan nayi muku sallama,sai kuma na iske bakwa garin..."
Dakatawa baffa yayi da tafiya sannan ya kalle shi yana fad'in
"Eyyaahh..! To ko zamu bari zuwa wani lokaci,tunda yanzun lokaci ya k'ure ko..??"
A hankali ya sosa k'eya dan yasan baffan bai fahimci abunda yake nufi ba sannan yace
"Baffa idan babu damuwa yanzun muyi maganar,saboda idan na tafi babu lallai na sake dawowa kwana kusa..Dan ina akwai tafiya a gabana yau da dare.."

Murmushi baffan yayi sannan ya bashi izinin su shiga daga ciki idan magannar tana da tsayi daga nan suka wuce yayin da shi da Sabina suma suka bi bayansu,suna shiga ta wuce tayi ciki ta barshi nan ya k'arasa d'akin da baffan ya shiga,sun sake gaisawa bayan nan shiru ya biyo baya har na wani lokaci kafin baffa ya magantu
"Mai babban suna.. Shin wane magana ne kake son sanar dani ne..??"
Sai daya gyara zama sannan ya d'ago kansa dake sunkuye a k'asa yayi d'an murmushi nan ya fara zayyanawa baffa duk abunda ke faruwa da tafiyar da zaiyi a yau d'in,tabbas ba don kasancewar baffa mutum mai ilimi ba gami da kaifin basira da har ya iya gano damuwar dake kwance saman fuskar Hammad sannan ya gano adadin k'aunar dake tsakaninsa da Sabina tabbas da sai yace dama can k'arya yake yi,nd yazo ne kawai da niyyar yaudararsu,sai da yayi jimm na tsayin lokaci yana tunani kafin ya jinjina kai ya fara magana
"Tabbas wannan magana taka,wani AL'AMARI ne wanda Allah (S.W.T) ya hukunta faruwarsa,wanda dabararmu ko k'arfinmu bai isa ya hana afkuwarsa ba,hak'ik'a Ubangiji shi kad'ai ya barwa kansa sanin dalilin da yasa wad'annan al'amura suke faruwa,dan haka bamu da bakin yin wata magana ko yanke hukunci har sai mun jira ganin ikonsa akanmu,dan gaka sai muci gaba da addu'ah Allah yasa hakan ya zame mana alkhairi mu da ku baki d'aya,,,batun tafiya kuma da zaka yi,in sha Allah zamu yi ta maka addu'ah har Allah ya dawo da kai lafiya,ALK'AWARI ne mun riga mun d'auka dan haka kada kayi tunanin faruwar wannan lamari zai sa mu karya ALK'AWARIN mu gare ka..Muna yi maka fatan alkhairi da fatan Ubangiji ya bada sa'a kan abunda akaje nema.."
Duk da yaji matuk'ar dad'i da furucin baffa,sai dai a gare shi a kuma nasa hasashen sam ba haka yake muradin yaji ba,a nasa ra'ayin da kuma son ransa yaso ne kawai ace baffa yace idan har da gaske yake sonta to kawai zai d'aura musu aure,idan yaso bayan dawowarsu sai su san yadda za suyi da lamarin Daddy,amma sai yaji ya tsaya iya kan maganar har yanzun suna nan akan batun zasu jira dawowarsa,duk da bawai ya raina hakan bane yaso ace kawai baffa ya yanke hukuncin aura masa ita daga nan sai ya tafi da abarsa zuwa sanda zasu dawo,yasan Daddy'nsa zai sauka ya kuma karb'i batun tunda yana sa rai zuwa lokacin ma tuni har da rabo zasu dawo masa.
D'agowa yayi saurin yi ya kalli baffa,zuciyarsa da taraddadin abunda zaice idan har yaji maganar da zai fad'a yanzun,daurewa yayi a hakan bayan ya sake sunkuyar da kansa k'asa sannan ya furta
"Amma baffa..! Shin babu yadda za'ayi ku aura min ita.!?"
Shiru baffa yayi yana kallon Hammad har ya dasa aya kafin ya murmusa da fad'in
"Haba mai babban suna.. Ta ina ka tab'a ji anyi irin wannan auren babu sa albarkar iyaye,,sannan kasan matakan aure da abubuwan da suke hallata shi,dole ne idan za'ayi aure sai da waliyyai,sadaki sannan shaidu,to mu da babu ko d'aya daga ciki a tare damu sai muce zamu yanke hukunci..?? Ina ganin ya kamata ace muyi hak'urin har zuwa lokacin da Allah zai dawo da kai,in sha Allah zuwa lokacin komai ya daidaita.."
Sam ba haka Hammad yake son ji daga bakin baffa ba,dan shifa har ga Allah idan har da ace a yanzun zai ce ya amince masa to a shirya yake ya nemo komai da baffan ya ambata,dan haka kai tsaye sai ya sake fad'in
"Baffa ina ganin wannan duka ba abun damuwa bane ba,zamu iya samunsu a duk lokacin da muka buk'ata,fatana shi ne amincewarka,nayi maka ALK'AWARIN ni da kaina zan nemo sauran a duk inda ya dace.."
Murmushi baffa ya sake yi masa kafin ya ce......



*Kyal Kyal.. Lallai Hammad ka deb'o da zafi aradu.. Aaa! Abu yayi soyayya ta k'arfafa,,irin wannan yanke hukunci haka da gaggawa...To dai fan's kunji hukuncin da Mutumin ya yankewa kansa,,amma kuna ganin baffa zai amince ya aura masa ita kamar yadda yake muradi..?? Shin yaya matsayin hakan zai kasance ga Daddy'n Hammad idan har hakan ta faru,anya kuna ganin zai amince ya karb'i auren nasu a nan gaba..??*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*21.*
_#The explicit romance_

"Haba mai babban suna.. Ta ina ne ka tab'a ji haka ya faru..?? Ka tuna fa babu yadda za'ayi ayi aure ba tare da amincewar mahaifanka ba,tunda bai baka goyon baya ba,me yasa kake son yin amfani da damuwarka wajen kaucewa matsalar ka..?? Shin baka tunanin hakan zai sake janyowa mahaifinka ya aikata wani abu daban a gaba..??"
Shiru Hammad yayi bayan sauraren baffa babu abunda yake yi,yayin da zuciyarsa ke hasaso maganganun Daddy'nsa,tabbas yafi kowa sanin mahaifinsa mutum ne mai tsatstsauran ra'ayi wanda idan har ya fad'i magana tamkar yankan wuk'a,baya tab'a soke magana idan har ya riga ya furta haka nan ba'a tab'a canja masa ra'ayi,shi d'in tsayyaye ne wanda baya tab'a d'aukan ra'ayin kowa,kamar yadda yayi masa wannan sanin tuni ya san da kamar wuya ace tunda ya yanke masa hukuncin tafiya ya janye,to amma duk da bai fito ya nuna k'in amincewarsa k'arara akan lamarin ba,ai ya kamata ace yayi na'am da buk'atarsa,tunda shima bai musa hukuncinsa a kansa ba,lallai ne yana buk'atar ya fahimci wani abu,,,shin ra'ayin Daddy akan karatunsa yake ko kuwa yarinyar da yake so ne bata yima Daddy'n ba..?? Ko kuwa dai da gaske ne bai isa aure ba..?? Wannan shi ne tunanin da yayi ta fama da shi,sai dai ya kasa fahimtar komai
"Ina tunanin yin haka ba shi ne zai haifar mana da d'a mai ido ba,,hakur'in dai shi yafi cancanta muyi mu duka,in sha Allah da sannu komai zai zo mana k'arshe..Amma batun d'aura muku aure duk ba shi ne mafita ba,neman amincewar mahaifa da sanyawar albarkarsu abune da yake da matuk'ar muhimmanci a rayuwa,,idan ka samu iko kayi k'ok'arin fahimtar da mahaifinka muhimmancin yin hakan,saboda wasu lokuta al'amura sukan canja kansu,,sai dai ina horonka daka kasance mai yiwa mahaifanka biyayya akan duk abunda za su umarce ka matuk'ar bai sab'awa fad'in Allah (S.W.T) ba ko koyarwar Annabi (S.A.W),yin hakan zai sa ka had'u da alkhairin da baka tab'a tunani ba a rayuwa..Amma ina so ka k'ara hak'uri.."
Fuskarsa sam babu wani alamu da yake nuna zai iya yin hak'uri kamar yadda baffa yake so,a hankali ya kifa kansa a k'asa yana tunanin maganganun baffa tun daga farko har k'arshe,cikin tsantsar damuwa ya kai hannu ya d'auke hular dake kansa ya ajiye a k'asa zuciyarsa banda ingiza shi babu abunda take tunaninma duka ya rasa wanda ya kamata yayi,ya d'auki lokaci cikin wannan yanayin da baya iya bambance a inda yake kafin ya d'ago jajayen idanunsa da damuwa ta sauyawa launi ya sauke su akan baffa,shi kansa baffa ko daya kalli yanayin da yake ciki sai da yaso bashi tsoro bcos tunda yake bai tab'a ganin wani ya shiga makamancin yanayin da Hammad d'in yake a ciki ba
"Subhanallah..! Muhammadu me yake faruwa da kai haka..?? Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un..!"
Wani murmushi ya saki mai ciwo,cikin muryansa daya jima da sanyaya ya furta
"Babu komai baffa..Am fine..!"
Girgiza kai baffa ya shiga yi yana fad'in
"A'a Muhammadu ka fad'a min abunda ke damunka..Shin kaga yadda ka koma kuwa..? Me yasa baza ka sanar da ni gaskiya ba..?? Nima fa kamar mahaifi nake a gareka..Kayi k'ok'ari ka fad'a min idan damuwar ka..!"
Kansa ya shiga moving asides nd yana gripping lips cike da tsantsar damuwa
"Nothing baffa..Am fine..!"
Shi dai baffa ba jin turanci yake ba saboda haka ko da Hammad yayi magana bai fahimci me yake fad'a ba,ci gaba da tambayarsa
"A'a Muhammadu baka sani ba,ka daina cewa ka sani..Ka daure dai ka fad'a idan ina da damar taimakamaka sai nayi..Amma zama a cikin damuwa ba shi da amfani.."
Saurin kallon baffa yayi yana sakin murmushi,cike da yarda da kai ya furta
"Baffa da gaske zaka taimaka min..?? Idan kaji abunda nake muradi zaka yi min..?? Baza ka k'i ba,ko da ba haka kake so ba..??"

"In sha Allah zanyi k'ok'arin yi maka idan har ina da ikon yin hakan.."
Wani irin murmushi ya saki mai kama da mutum ya samu matsalar kwakwalwa kafin ya ce
"Baffa ka auramin ita..Na san Daddyna zai karb'i aurenmu nan gaba,baffa batun ace har sai lokacin daya amince ne zaka auramin ita da nisa sosai,ya kamata ace baffa ka fahimci halin da zuciyoyin mu zasu shiga..Please baffa i implores u.."
Kallonsa kawai baffa yake yi dan yadda yake abu kamar zararre lamarin fa ya fara d'aure masa kai,tunaninsa me yake faruwa da Hammad d'in haka lokaci guda ya sukurkuce masa,tabbas idan har ace dan soyayyar da yake yiwa y'arsu ne ya kamata yayi wani abu da gaggawa idan kuwa ba haka ba tofa yasa rai da ganin abunda yafi wannan muni da tashin hankali,cike da yin na'am da shawarar da zuciyarsa ta kiyasta yayi saurin d'agowa ba tare da tunanin komai ba ya furta
"Shi kenan Muhammadu na amince..Amma akwai sharud'a.."

"I will agree baffa..Duk abunda zaka fad'a bazan musa ba,matuk'ar zaka auramin ita.."
Kallonsa kawai baffa yaci gaba da yi har yayi shiru dan kansa
"Tabbas..Mai babban suna na amince zan aura maka ita,,amma ba a irin wannan lokacin ba.."
Murnar sace ta fara k'ok'arin komawa ciki,nan da nan y'ar fara'ar dake saman fuskarsa ta fara disashewa
"Baffa sai yaushe ne zaka aminta da batuna..I swear zan rik'e ta amana ka yarda dani baffa.."
Zafafan hawayen da suka biyo bayan maganarsa su suka tilasta masa yin shiru,izuwa yanzu kam ko da baffa yaga yanayin da yake ciki ga hawaye a fuskarsa tuni tausayin Hammad ya gama ratsa masa zuciya,sai dai kawai yana jin ba lallai ne ya iya yi masa abunda yake so ba
"Kayi hak'uri Muhammadu nima ba'a son raina hakan zai faru ba,idan da ace ina da ikon aura maka ita a yanzun zanyi,sai dai nasan babu yadda za'ayi ko da na aura maka ita ku tafi tare sannan ba lallai ne mahaifanka su amince ba.."
Saurin katse shi Hammad yayi ta hanyar fad'in
"Amma baffa idan ka d'aura mana aure na tabbatar kaima zaka fi samun nutsuwa daga irin maganganun dake yawo cikin garin nan,sannan ko babu komai su kansu jama'ar dake surutun zasu saurara daga lokacin da suka tabbatar da kasancewar mu ma'aurata.. Ka aminta dani baffa,,ni kaina ko da na tafi zan kasance ne a kullum ina tunawa da cewar akwai *ALK'AWARI* akaina,sannan ba zan manta da cewa akwai mutanen dake jira na ba,hakan zai bani damar yin abunda ya kaini na kuma dawo gare ku..Idan dan batun ko baka sanni ba ko asalina mahaifina ba b'oyayye bane,na san ko da ace kuna zaune a nan baza ku kasa sanin chief judge Aliyu Sani ba.."

"Haka ne Muhammadu kayi gaskiya,sai dai babufa ta yadda za'ayi ni da kaina na aikata abunda kake so,saboda idan har na yarda na d'aura muku aure za kayi tafiya ne mai nisa,yayin da mu da ita za ka barmu muna zaman jira,sai dai zan iya yi maka abu guda shi ne,zan iya karb'ar sadaki na ajiye har zuwa lokacin da zaka dawo.."
Sam Hammad bai so haka ba,dan haka suka ci gaba da tirzawa da baffa,shiru baffa yayi zuwa wani lokaci sannan yaci gaba da cewa
"Bazan iya amincewa da wannan buk'ata taka ba Muhammadu,bayan na sani da yawa daga cikin ma'abota ilimi sunyi maganganu dangane da irin wannan matsalar,dan haka ina so ka saurari abunda zan fad'a maka game da abunda kake son na aikata,,,kamar yadda yazo wasu daga cikin magabata sun iyakance adadin watanni shida (6) a matsayin wanda mutum zai yi a halin tafiya sannan yadawo wajen iyalinsa,ba don komai ba sai dan saboda sun dogara ne da abunda aka ruwaito daga sayyadina Umar ibn khattab (R.A),malamai su kace asali kuma a shari'ance ba'a samu wani nassi daga Manzon Allah (S.A.W) ba wanda ya kayyade adadin kwanakin da miji zaiyi baya gari a yayin da yayi tafiya,to amma an samu wani *(ASAR)* daga sayyadina Umar ibn khattab (RA) cewa ya k'ayyade watanni shida (6) ga sojojin da suke a wajen yak'i,wannan kuma yana daga cikin *IJTIHADI* ne wanda Sayyadina Umar (R.A) yayi lokacin da ya tambayi y'arsa nanna Hafsat (R.A) akan hakan,sai dai babban abunda ya kamata a lura da shi a nan,shine yanayin canjawar zamani da kuma wurin da ake zaune,ko shakka babu zamanin sahabbai (Radhiyallahu anhum ajma'iyn) yafi wannan zamanin da muke ciki inganci da kuma adalci,sannan b'arna bata yi yawa ba kamar ta wannan zamanin da muke ciki.Dan haka kaga kenan abu mafi kyau shine ya kamata ace miji da mata suyi tsarin da zaifi dacewa da zaman takewarsu domin su sukafi kowa sanin yanayin halinsu,sai suyi tsari gwargwadon k'arfin sha'awarsu,su iyakancewa kansu adadin kwanakin da suke ganin zasu iya jurewa ba tare da sunyi jima'i da juna ba,saboda akan samu bambamci tsakanin wata matar da wata haka shima mijin,sannan kaga wata matar yarinyace matashiya tana da buk'atar ace miji baiyi nisa da ita ba,wata matar kuma girma ya kamata

Please Login or Register in order to submit comment