Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*14.*
_#Love fearing_

Da kallo ya bita har ta fice daga d'akin,haka nan sai yaji zuciyarsa tayi masa wani iri sakamakon yanayin da yaga ta fita a ciki,wanda kallo d'aya kawai da yayi mata tuni ya tabbatar masa ba k'alau take ba,jikinsa ne ya sake yin sanyi da lamarin,nan take yaji zuciyarsa ta fara tambayarsa
"Shin mene ne hakan ka aikata Hammad..?? Me kake nufi ne da yarinyar mutane..? Shin Wannan shi ne abunda dama kake buk'atar yi..?"
Shiru ya d'anyi na wani lokaci ba tare daya iya ko da tari ba sai maganar da zuciyarsa ke yi masa da yake sauraro,maganar baffa ce ta katse shi daga duniyar daya tafi
"Mai babban suna,, na tambaye ka amma naji kayi shiru..Nace shin wace yarinya ce,,kuma a ina take..!?"
Dogon numfashi ya sauke a hankali cikin rashin kuzari ya furta
"Baffa..Dama.!"
Sai ya sake yin shirin nd deeply yana jin kamar idan ya tona sirrin zuciyarsa ga baffan bazai tab'a amince masa akan maganar ba
"Uhhuumm! Ina sauraren ka..Ka fad'a min duk abunda kake da buk'ata,, in sha Allah ni kuma zanyi iya yina akai da yardar Allah,har saina tabbatar da cewa ka samu wannan abun.."
Jimm ya sake yi yana jin yadda zuciyarsa ke wani irin mugun bugu,a hankali ya maida idanunsa ya kulle kafin cikin sanyin jiki ya furta
"Baffa ba kowa nake magana akanta ba data wuce *SABINA,* ita nake so,ba kowa ba,kuma ita ce nake nufi..Duk maganar da nake yi akanta ne baffa,,tun daga ranar dana fara ganinta har yanzun na tsinci kaina a cikin wani irin hali,wanda ban tashi fahimtar abunda ke shirin faruwa da ni ba sai cikin kwanakin nan da nayi ban zo ba,,dan Allah baffa ina rok'on ka,ko da ace bayan kasan wannan sirrin bazaka k'i bani ita ba,,nayi maka *ALK'AWARI* baffa kuma na tabbatar maka da cewa zan kasance mai rik'e ta amana,,ba zan tab'a cutar da ita ba,hakama bazan bari a cutar da ita ba..Idan har kuma kana ganin baka amince dani ba baffa,kana da ikon hana ni ita,,amma wannan wani sirri ne daya kasance daga zuciyata..Sai kuma idan har ace ka riga kayi mata miji,na tabbata babu yadda zanyi dole ne nayi hak'uri sannan na janye maganata..!"
Shiru baffa yayi yana saurarensa nd idanunsa duka akan Hammad d'in har ya dasa aya ba tare daya iya cewa da shi komai,jin yadda yayi shiru yasa Hammad d'ago kansa dake sunkuye ya d'an kalli baffa da idanunsa da suka fara sauyawa,irin kallon da yaga baffan yana yi masa shi ne yasa shi sake sauke kai k'asa,sun d'auki ak'alla mintuna biyar shiru babu wanda yayi magana,kafin baffa ya nisa tare da fara magana
"Tabbas.! Mai babban suna wannan *WANI AL'AMARI* ne mai girma kazo min da shi,,sai dai ni ban isa na yanke hukunci ba,har sai mun jira munga abunda Allah zai yi,,amma wani hanzari ba gudu ba,kaga mu nan a da,bisa al'adar gidan nan da muka gina rayuwarmu akanta shi ne,mun kasance muna aure ne na zumunci,ta yadda mukan had'a y'ar wannan da d'an wannan,duka a cikin gida muke aurar da yaranmu ba don komai ba sai dan gudun fad'awa cikin matsala,sannan kuma mun sani cewa yin hakan zai sake taimaka mana wajen rik'e junanmu da mutunci kuma bisa amana,babu yadda za'ayi ace mu cutar da junanmu,sai dai kuma a kwanakin da suka gabata,idan har baka manta ba ni da kaina na soke irin wannan maganar auren na zumunci da muka kasance muna k'ullawa tun shekarun da suka gabata,saboda wani dalili da kuma matsalolin da suka fara shigo mana cikin danginmu,,duk da cewa ni da kake gani nine babba sannan duk hukuncin dana zartar da shi ake amfani a gidan nan,hakan ba wai yana nufin zan yanke hukunci akan maganarka da Sabina kai tsaye bane...A tsarin addini da kuma al'ada da muke tafe akansa tun iyaye da kakanni shi ne,matuk'ar yaro yaga y'ar mu,ko d'anmu yaga wata yarinyar ya nuna yana ra'ayinta da gaske bawai da wasa ba,to zai sanar da magabatansa ko kuma mu a sanar damu,daga nan sai mu da su mu zauna mu tsayar da magana ta gaskiya.."
Shiru baffa ya d'an yi yana jan numfashi,ko kafin yaci gaba Hammad yayi magana
"Shi kenan baffa,in sha Allah kamar yadda ka fad'a,nima zanyi k'ok'arin na zauna mahaifana akan maganar,kuma in sha Allah zaka same ni mai bin duk wani sharad'i da dokar da zaka sakamin akanta,matuk'ar dai ace bai sab'awa addini ba.."
Murmushi baffa yayi masa duk da kan Hammad d'in yana k'asa
"Hakan yana da kyau sosai MUHAMMADU,,halayenka da tarbiyyar ka suna k'ara bani sha'awa,,,to amma kai d'in kana ganin idan har akace dan ka nuna kana son yarinyar data fito daga zuri'ah irin tamu,ina nufin kasantuwarmu talakawa kaga mu daku ba d'aya bane,shin yaya matsayin wannan maganar zai kasance a gurin mahaifanka,,shin kana ganin zasu d'auki batun har su amince maka..!? Ya kamata fa kayi wannan tunanin.."

"In sha Allah baffa bazasu k'i ba,talaka da mai kud'i dukafa bayin Allah ne,haka kuma a lokaci guda idan yaso sai ya canja AL'AMARIN,,Talakawa ya koma mai wadata,shi kuma wanda yake ganin shi mawadaci ne a wayi gari ya koma talakawa,,ni ina ganin wannan ba abun damuwa bane baffa,Allah shi ne farkon abunda ya kamata ace bawa yasa a gabansa,dan haka ina ganin babu wata matsala da za'a samu ta wannan fuskar.."
Jinjina kai baffa yayi cike da gamsuwa kafin ya ce
"Toh..! Shi kenan ai,tunda har kana ganin baza'a samu matsala ba,zan baka dama daga nan har zuwa wasu kwanaki,ka samu kuyi magana da maganbatan naka,in yaso duk yadda kuka yi da su sai ka sanar dani ko..!?"

"In sha Allah,, baffa dana koma zanyi k'ok'arin sanar da su.."

"Masha Allahu..! Allah ya bamu sa'a,sannan yasa muji alkhairi.."
Da "ameen" ya amsa yana sake sunkuyar da kai,baffa kam murmushi yake ta saki dan yadda maganar ta faranta masa rai ji yake kamar duka duniya babu wanda ya kai shi shiga tsantsar farin ciki da batun,,shi kansa Hammad idan da ace za'a tona zuciyarsa a lokacin ta wani gefen fari k'al take dan yadda baffa ya nuna aminceaarsa akan maganar,sai dai kuma ta wani gefen yana jin zuciyar sa cike da tsoro,shin ta yaya ne zai tunkari Daddy'nsa da wannan batun,tun ba yanzun ba ya riga yasan halinsa nd waye shi d'in,idan har dan ace ta Mamma ne baya tunanin zai samu matsala da ita,to amma Daddy fa..? Ta wace hanya ne zai bi yayi masa bayani.? Da wace fuska ne ya kamata yabi ya sanar da shi..?
"Shin ko dai zan bi ta wajen Mamma ne kawai..?? Na san bazan samun matsala da ita ba.. Anya ba itan zan fad'awa ba kawai na huta,idan yaso sai mu bar maganar a tsakanin mu ba sai Daddy ya sani ba,daga nan har zuwa lokacin da komai zai daidaita sai muyi k'ok'arin sanar masa,i know zuwa lokacin babu abunda zai faru,nd duk wani matsalan danake tunanin za'a samu ma zuwa time d'in nayi solving nasa.!"
Shi kad'ai yake magana a zuciyarsa buh sai dai duk ya rasa yadda zaiyi,,maganar baffa ce ta sashi d'agowa cikin hankalin sa
"Amma! Mai babban suna ina tunanin wani abu kuma.."
Maganar baffa tazo masa a wani irin yanayi da tasa shi jin fargabar abunda baffan zai sake fad'a a gaba,cikin rikicewa ya bud'e baki yana fad'in
"Baffa..! Shin da akwai matsala ne..!?"

"Ko kad'an babu wata matsala,,kawai dai ina son sanar da kai wata magana ne."
Sake gyara zama yayi yana tankwashe k'afafu yayin da k'irjinsa ke tsananta harbawa
"To baffa..Allah yasa alkhairi ne..!"
D'an murmushi yayi masa sannan ya ce
"K'warai kuwa alkhairi ne da yardar Allah,,kamar yadda ka sani yanzun zamani ya sauya,,kamar yadda aka samu ci gaba da kuma sauye²,wad'anda sune suka sa mu ta dole muka watsar da al'adunmu na hausa/Fulani,,,a da za kaga anyi aure ba tare da ma'aurata sun san juna ba,wasu ma duka ko da sun tab'a had'uwa gabanin ayi auren zaka tarar had'uwarsu d'in bata kai ta azo agani ba,,to shi ne nake ganin kamar ya dace ace ka samu K'ANWAR nan taka ku fara fahimtar juna da ita,tunda naga yanzun haka ake yi ko..!? Idan yaso in Allah ya ara mana rai da lafiya kuma kun daidaita falillahil hamd,muma zamu so hakan,bawai ace kai tsaye mun yanke hukunci ba ko..!?"
Gawurtattun ajiyar zuciya ya jera saukewa,cikin tsananin jin dad'in maganganun na baffa ya saki murmushi mai k'ayatarwa
"Haka ne baffa,,in sha Allah za'ayi duk yadda kace,,na gode sosai Allah ya k'ara girma,yaja da nisan kwana..Ubangiji ya jik'an magabata.."

"Ameen ya rabb,,Allah yasa mu kuma mu dace..Idan namu lokacin ya zo mu cika da imani.."
Shima da "ameen" d'in ya amsa masa,,daga nan kuma hiran nasu sai ya koma jefi² nd duka ya ta'allak'a akan harkokin noma da kiwon da suka kasance suna yi,,har yamma Hammad yana cikin k'auyen,inda duka yinin ranar yayi shi a cikin gidan su Sabinar,ba shi ya tashi tafiya ba sai can bayan la'asar sosai.
Lokacin daya tashi tafiya baffa da kansa yasa a kira masa Sabinar suyi sallama,ko data k'araso baffa fita yayi ya basu guri,,tun data shigo kanta yake a k'asa sam tak'i yarda ta had'a ido dashi,yadda ta sunkuyar da kai sam babu wanda zaiyi tunanin tana magana,shima kansa Hammad d'in yadda yaga ta zauna tayi shiru sai ta sashi yin murmushi
"Me yake damunki ne my lady.!?"
Ya watso mata tambayar,a hankali ta d'an d'ago kanta dake sunkuye ta kalle shi,shima d'in itan yake kallo nd still fuskarsa da fara'a ba kamar wasu lokutan ba da har take jin shayin ta d'aga kai ta kalleshi,one eyebrow ya d'age mata alamun tambaya,cikin sanyi ta d'an kad'a masa kai kafin tace
"Babu komai..!"

"Sure..!?"
Ya sake tambayar ta,kai ta sake girgizawa sannan tace
"Ehh.!"
D'an murmushi yayi cikin salon sa na zolaya kafin yace
"Kan ya daina miki ciwon..!?"
Saurin sake d'agowa tayi ta kalleshi buh sai bata ce komai ba,illa wani irin salivary data had'iye,sake sakin murmushi yayi amma wannan karon mai sauti
"My lady..Kada fa ki nuna zaki min wayo..Dan ni nan da kike gani babu abunda zaki b'oye min a kaf halayenki..Zuwa wannan lokacin idan har akwai wani abu da ban fahimta ba a game da d'abi'unki,,Ina tunanin to sai dai..!"
Shiru ya sake yi yana murmusawa,sake sunkuyar da kai tayi,shi kuwa yana kallonta nd yana sake murmusawa
"Ohh.! Wato yanzun ma ni kad'ai zaki bari nayi ta magana..!? Am not a radio fa,,kin sani sai surutu nake,al'halin ban wani saba da yawan magana ba.."

"Uhhuumm..!"
Tace ba tare data sake cewa komai ba
"Speak ur mind my lady..!"
Ba tare data d'ago ba can k'asa tace
"Ni babu abunda zance dama.."

"Uhumm! Shi kenan,tunda baza kice ba,,saboda ni..Zan tafi,idan kina da wani sak'o ina sauraro ki sanar dani..!"
Shiru ta d'an yi ba tare data ce komai ba,haka nan yanayinta a hankali sai ya fara sauyawa,duka yana monitoring nata da duk wani motsinta,ba tare da tayi aune ba sai ganinsa tayi a daf da ita,cikin wani irin muryan da bata tab'a jin yayi magana da shi ba yace
"My lady..! A haka ne za muyi sallamar..?"
Tun daga idanunta har zuwa kan toes d'inta babu inda baya motsawa a jikinta,yanayinsa a yau da al'amuran sa ita kam gaba d'aya sun fara bata tsoro,gani take kamar ba shi ne wannan miskilin mutumin data sani ba wanda ko magana ma sai ya zama dole yake yinta,,d'an ja baya tayi kad'an ta bar kusa da shi kafin ta shiga sakin ajiyar zuciya akai²
"K..ka.gaida gida..Allah ya tsare hanya..!"
Iya abunda ta iya furtawa kenan shima cikin sark'ewar harshe,a hankali ya sake yin murmushi kafin ya matsa baya shima yana hard'e hannayensa a k'irjinsa ya zuba mata idanunsa
"Na gode my lady..Buh ban karb'i wannan sallamar taki ba.."
Idanunta ta d'an runtse a hankali cike da dauriya sannan tace
"Sai wanne ne zaka amsa..!?"
D'an jimm yayi yana kallonta yana murmusawa kafin ya ce
"Umm! Har sai kin..!"
Jin bai k'arasa fad'a ba yasa ta d'an d'agowa ta kalle shi kamar za tace wani abu kuma sai yaga ta sake sauke kanta k'asa ba tare da tayi maganar ba
"My lady..! Ba zaki tambayi me zan fad'a ba..!?"
Shiru tayi masa na wani lokaci har sai da yayi zatonma ba zata yi magana ba sannan yaji tace
"Mene ne zan tambaya..!?"

"Abunda zan fad'a na fasa.."
Murmushi ta d'anyi kana tana d'an tab'e baki
"Uhmm! Ai ka fasa fad'a ne shi yasa kayi shiru.."
Sake murmusawa yayi cikin sigar zolaya kuma ya furta
"Ummm! A'a! Kawai dai dan bakya ra'ayin jin abunda zan fad'a ne yasa kema baki damu ba ko da nayi shirun.."
Idonta ta d'an lumshe sannan ta sake bud'ewa,deeply kuwa fad'i take
"Dan dai baka san yadda nake son jin bane shi yasa kaima d'in kayi shirun,,da ace ina da k'arfin guiwan da zan iya tambaya,babu abunda zai sa na gaza tambayarka..! Ya Allah..!"

"Shi kenan my Lady,,ba dan yamma yamin ba,nd ina tunanin yadda hanya zai kasance min ni kad'ai,,da nayi ta zama a nan har sai kin min magana..Buh ban so ace zan tafi na barki ba.."

"Ya tafi ya barni..!? Me yasa ne yake min wad'annan maganganun masu kama da surkulle..!? Na kasa fahimtar inda kalamasa suke tafiya ni kam..!"
Can k'asan zuciyarta take ta maganar ita d'aya.Hammad kam ranar ba shi ya tafi ba sai daya gama zolayarta sannan suka yi sallama ya fito,wad'anda ya tarar a tsakar gidan yayiwa sallama sannan suka yi sallama da su baffa daya iske a k'ofar gida,kana suka d'auki hanyan rakashi kamar yadda suka saba a lokacin biyar har ta gota.

Sai around 6:30pm ya shigo gidan,yanayin da yake ciki na farin ciki a lokacin duk da wani b'angaren nasa yana jin fargaba duk wanda ya sanshi babu yadda za'ayi ya kasa gane farin cikin dake tare da shi. Yana tafe yana murza carkeys dake hannunsa,lokaci zuwa lokaci kuma ya saki murmushi idan ya tuno yadda suka yi da ita,shigowarsa cikin parlor'n tayi dai² da tsaiwar Mamma a bakin staircase d'in daga sama,kallonsa ta ci gaba dayi har ya gama shigowa yana niyyar zama a parlor'n ya tsinkayo muryanta a sama tana fad'in
"HAMMAD..! Daga ina kake da wannan lokacin.!?"
Ko kafin ya d'aga kansa sai da yayi murmushi sannan ya d'an d'ago yabi inda ya jiyo muryanta da kallo,yanayin fuskarta da yayi arba da shi nan ya sashi saurin mik'ewa daga zaman da yayi ya nufi hanyan staircase d'in,still tana a tsayen tana kallonsa har ya gama haurawa saman ya isketa,daf da ita ya tsaya kafin ya rik'o hannayenta duka a cikin nasa
"Mamma..! Na fita ne tun safe..Nd..!"
Hannun ta zare daga nasa kafin tayi saurin d'aga masa wanda shi ne sanadiyyar yin shirun nasa daga fad'ar abunda yayi niyya
"Amsan tambayar da nayi maka kawai nake buk'ata.. Daga ina kake..!?"
Kallon ta ya d'anyi kafin ya rausayar da kai yana fad'in
"Mamma naje skul ne..Nd uzurin gaggawa ya taso min ne,shi yasa na fita ban sanar miki ba.."

"Ban yarda ba Hammad.."
Saurin sake kallonta yayi,yadda ta had'e rai da gani kasan da gaske take bata yardan ba har zuciyarta,marairaicewa yayi cikin sigar son tabbatar da magannar sa sannan yace
"Mamma i swear, ban je ko ina bafa.."

"No! Hammad..Kasan bazan yarda ba..Saboda haka ka fad'a min gaskiyar inda kaje..Kada ka manta fa tun nice nan na haifeka,nd tun safe baka gidan nan,na san kasan da haka ko..!?"
Kai ya shiga gyad'awa
"Ehh! Mamma buh..!"

"Shhhh.! Ya isa haka,,muje na shirya maka abinci kaci..Na san tun safe zai yi wahala ace ka sama cikinka wani abu ko..!?"
Sake gyad'a mata kai yayi cije da sanyin jiki,nd a b'oye kuma yana sakin ajiyar zuciya,ita da kanta taja hannunsa suka bar wajen sai data tabbatar ta raka shi har bakin bedroom d'insa sannan ta tsaya tana kallonsa tana shafa fuskarsa
"Maza kaje kayi wanka ka shirya kaji..zan had'a maka abincin kafin ka fito.."
A hankali ya rausayar da kai yana had'iye yahu,sakin hannunsa tayi sannan ta juya tana murmushi,saurin rik'o hannunta yayi nan ta tsaya kafin ta juyo ta kalle shi,kamar bazai yi magana ba,kuma sai cewa yayi
"Mamma..! Idan na fito akwai maganar da nake so muyi..Please.!"
Ajiyar zuciya tayi sannan ta gyad'a masa kai itanma
"Ok..! Je ka fito d'in,, ina nan ina jiranka kaji Yarona.."
A hankali ya kad'a kai sannan ya juya ya shige ciki,sai data tabbatar ya wuce ta bar wajen,shi kansa Hammad sai lokacin daya shiga ciki sannan ya fara tunanin anya bai yima kansa gaggawa ba kuwa da har yake k'ok'arin sanar da Mamma tun yanzun...? Ko kuwa dai zai bari ne har zuwa gaba sannan ya shaida mata,to amma idan har bai fad'a mata ba lamarin ya kwab'e masa yaya zaiyi a nan gaba...?
Wad'annan tambayoyin sune suka fara zuwa kwakwalwarsa a lokaci guda.....

*Fan's ya kamata ku kawowa HAMMAD d'auki da shawaran ku,,anya kuna ganin sanar da Mamma abunda ke wakana shi ne mafitar da yake nema..??*





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_Way to go.!🏃 All the hard work paid off.Congratulations.! *HASSAN & HUSSAIN ATK'S* Allah ya sanya albarka da alkhairi._👏

*15.*
_#Love & Trauma_

Rasa yadda zaiyi da tunanin daya addabar shi yasa shi runtse idanunsa a hankali sannan ya d'ora hannunsa d'aya a saman goshinsa yana matsawa kad'an² while d'ayan ya hannun ya d'ora shi saman waist d'insa yayin da zuciyarsa take masa wani irin suka,k'asa² yake furta duk addu'ar daya zo masa a baki,ya d'auki tsayin lokaci kafin ya jinkirta,zuwa wani lokaci kuma a fili ya furta
"Ya rabb.! Help me..Mene ne zanyi na fita a matsala ne..?? Should i inform Mamma or..!?"
Sai kuma ya d'anyi shiru yana tunanin hanyar daya kamata ya bi wajen sanar da itan idan har hakan ya kama yayi,ya d'auki lokaci mai tsayi banda zarya da zagaye bedroom d'in babu abunda yake wanda shi kansa bai san iya adadin lokacin daya shafe a cikin wannan yanayin ba.

A b'angaren Mammansa kuwa tun bayan data bar wajensa kai tsaye kitchen ta nufa,ita da kanta ba tare data sa wani cikin housemaid d'insu aiki ba,ta shirya masa abinci mai sauk'i nd wanda tasan ba zai d'auki lokaci ba,ko data gama sannan ne ta sa housemaid d'in su shirya mata dining itan kuma ta koma danta kira shi tunda taga har lokacin shiru babu labarin fitowarsa,,har ta hau saman bata ga alamun ya fito ba,dan haka kai tsaye ta nufi bedroom d'in nasa,a hankali ta kai hannunta saman handle d'in k'ofan ta murd'a,yadfa taji k'ofar a kulle nd alamu sun nuna daga ciki ne aka kulle,sai ta d'anyi jimm a gurin,AL'AMARIN kuma daya sata fara tunanin anya lafiya yake..? Hankalinta a d'an tashe ta shiga knocking k'ofar had'e da fara kiran sunansa,,yana tsaye har lokacin a tsakiyar d'akin ba tare da yayi abunda ya kai shi ba,haka nan duka hankalinsa ma shi kam a lokacin duka baya tare da shi,knocking d'in da Mamma keyi tana kiransa shi ne yayi sanadiyyar dawowarsa cikin nutsuwarsa,da sauri sai ya juya ya nufi bathroom dan yasan ganinsa da ita idan har taga baiyi abunda tace masa ba,har ya kai bakin k'ofa yana niyyan shigewa kuma sai ya fasa had'e da dawowa baya,dai² bakin k'ofan ya tsaya jin yadda take kiransa daga ji kasan ba'a nutse ita kanta take ba
"Hammad..! Na ce ka bud'e min k'ofar nan..Hamma..!"
K'afin ta k'arasa fad'a ya bud'e k'ofan da sauri,kusan karo suka yi yayi saurin rik'o ta,d'agowa tayi cikin sauri ko da ganinsa a yadda ta barshi sai ta shiga k'ok'arin gyara tsaiwarta tana sake k'are masa kallo,kula yayi da irin kallon da take masa nan take yasha jinin jikinsa nd sai ya shiga sauke kai k'asa da yake yasan ba shi da gaskiya
"Hammad..! Me zan gani..!? Dama kana tsaye kana jina amma ka gagara amsamin..!? Ka kyauta kaji ko..Ya maka kyau.."

"Mah..Please..!"

"Ni ba saika bani hak'uri ba,amma abunda kayi ka sani ba ni kayiwa ba..Kanka kayiwa,,ace kana ji amma ka kasa amsamin,shi kenan ai,,,sai dai ni kam na rasa gane kanka duka a kwanakin nan..Me kake b'oyewa ne Hammad.!?"
A hankali ya d'ago da niyyar yin magana tayi saurin d'aga masa hannu nd tana jinjina kai cike da mamakinsa
"Yayi maka kyau Hammad,,ka kuma kyauta,,sai dai ka sani ko mene ne kake b'oyewa wata rana dole zan sani..Ko da ace baka so ba..Ka ci gaba da b'oyewa tunda babu wanda kake so ya sani..Allah ya taimaka.."
Tana gama fad'a dan yadda ranta yake a d'an b'ace nan ta juya zata fice,saurin rik'ota yayi yana girgiza mata kai alamun kada ta tafin,wani irin kallo ta bishi da shi kafin tayi magana
"Mene ne kuma..? Ina baka son kowa ya sani ne shi yasa ka gwammace zama cikin damuwa..!?"

"A'aahh! Mamma duka fa ba yadda kike tunani bane.."

"Idan ba haka bane,yaya ne Hammad..? Idan da ace kana so na sani,babu ta yadda za'ayi kana ji na bud'e murya nayi ta rafka maka kira,na san kana jina kuma kasan nice nake kiranka,amma me kayi..!?"
Sunkuyar da kai yayi k'asa yana runtse idanunsa
"Shiru..!? Kamar ni nayi kiranka Hammad,,amma kayi shiru ka kasa

Please Login or Register in order to submit comment