Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

biyo bayanta,yana takowa yana murmusawa,gaba d'ayan kamar wad'anda aka gina sai suka tsaya kallon-kallo mamaki duka bayyane a fuskokinsu,Bassam kam ko da yaga bazai iya yin shiru ba yace
"Daddy har da kaima.!?"
Murmushi Daddy ya sake yi fiye dana farko yace
"Ehh! Shi Daddy saboda ba mutum bane sai ake mamakin ganinsa..!?"
Dariya suka yi Sabina cikin jin dad'i take ta murmushi tana musu barka da zuwa,k'arasowa su Daddy suka yi ciki,amma Hammad still yana tsaye inda yake,juyawa Sabina tayi ta kalleshi tana masa alamun ya k'araso cikin,sai yayi mata alama da ido ta zo gare shi,mak'ale masa shoulder tayi alamun bata zuwa,sai ya sake mata magana da baki but k'asa² yace
"Zo mana,,i have something special ne da nake son nuna miki."
Sake mak'alewa tayi ganin dai bata da niyya yasa shi kallon k'ofar da fad'in
"Shi kenan,,kawai ku koma abunku tunda tace bata son ganin ku.."
Gaba d'aya suka sake sawa hanyar idanu suna jiran su ga waye kuma next,Zee ma still tana tsayen tana kallon dai² entrance d'in tana sakin wani irin kwantaccen murmushi,a sad'ad'e ko da taga haka sai ta fara tahowa kamar mai jin tsoron faruwar wani abu while idanunta na kallon k'asa,har ta iso inda yake bata iya d'agowa ba,sai data tsaya sosai a kusa dashi da yace
"D'ago kiga wani abu.."
Slowly ta fara d'aga wider rounded eyeballs d'inta ta fara kallo shi tun daga kan k'afafunsa dake sakaye cikin wani had'ad'd'en cover shoe na maza har ta k'araso fuskarsa,murmushi ya sake sakar mata irin wanda yake k'ara mata nutsuwa,a hankali sai ya janye jikinsa yayi gefe,mugun mamakin daya bayyana saman fuskarta shi yayi sanadin da tana bud'e baki za tayi magana sai hawaye suka riga maganar ta ta fitowa....





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*55.*
_#Vacation_

Kallonsu take duka da wani irin farin ciki k'unshe a saman fuskarta wanda ya hanata kyakykyawan motsi bare ta iya k'arasawa gare su,yadda take ganin sun nan a tsaye gaba gareta sai duk zuciyarta ta kasa yardar mata da gasken su d'in ne,ta d'auki lokaci tana kallonsu da jiran taga sun b'acewa ganinta kafin Inna da suke ta tsaye a bakin entrance ta kalleta tace
"Shin mu koma ne ba kiyi farin ciki da zuwanmu ba..!?"
K'urii ta sake yi musu da ido tana ci gaba da kallonsu a hankali kuma sai ta bud'e baki cikin karkarwar gab'b'ai data murya tace
"Innata..! Da gasken ku idanuna suke gane min.!?"
Abunda ya fara fitowa daga bakinta kenan,followed by kuka mai tsanani,slowly kamar k'asar da k'wai ya fashewa a ciki ta fara tafiya nd tana neman yin k'asa zata silale duka a lokaci guda,Hammad yayi maza ya rik'o ta jikinsa yana mata murmushinsa mai kyau da girgiza mata kai alamun kada tayi kukan,rufe bakinta tayi saurin yi da duka hannayenta tana k'ok'arin hana kukanta bayyana amma da yake ya riga ya taho sai ta sauke wani irin jan zuciya cikin son had'iye hawayenta tana murmushi mai had'e da kuka ta zare jikinta a nasan ta nufi inda Innarta take,lokacin sata k'arasa wani irin lafiyayyen runguma tayiwa mahaifiyarta kamar wacce suka debi tsayin shekaru basu ga juna ba tana sake fad'in
"Innata.! Da gaske kece..!?"
Sai ta d'ago tana tab'a fuskar Inna da take sakar mata wani irin kwantaccen murmushin ni'ima tana girgiza mata kai,gefen Babanta ta sake juyar da kanta tana kallonsa cike da so da k'auna,yadda suka yi wani irin gogewar ban mamaki a cikin tsakanin da bata gansu ba sai ta tsaya kallonsu tamkar ta samu motion pictures,a zuciyarta kuwa godiya kawai take yi ga Allah da yasa mahaifanta a yanzun basa tare da wani k'unci ko tsananin rayuwa,,cike da shak'iyanci bayan ta gama y'an hawayenta da murnan ganin sun still tana jikin Inna ta saki murmushi da kallon Baba tace
"Alhaji Babana..!"
Sai ta zare jikinta a na Inna ta nufe shi,jikinsa tayi saurin fad'awa tana sauke wasu wahalallun ajiyar zuciya,dattijon sai yayi mata murmushi yana shafa kanta while dai² yadda zata ji shi a kunnenta yace
"Ja'ira! Har yanzun kina nan da hali baki fasa ba..!?"
A hankali ta d'ago kanta tana kallonsa fuskarta da fara'a sosai tace
"Nayi kewarka ne Babana."
Cheeks d'inta ya rik'o kamar wata yarinya yana shirin yin magana su Badra duka suka nufo inda suke suna musu barka da zuwa,shi kuwa yallab'ai Hammad sanyayyan murmushi yayi daga tsayen da yake har a lokacin kafin ya wuce yana fad'in
"Shi mutum bai bari an zauna an huta ba,kuma bai iya bada gurin zaman bama,sai aikin nuna wani tiny murnar da yake.."
Sarai ta san da ita yake slowly sai ta d'aga kanta ta bishi da kallo tana murmushi kafin ta janye daga jikin Baba taja hannunsa zuwa cikin parlor'n,da zuwan sun duka basu d'auki wasu mintuna ba amma kafin kace me tuni su Badra har sun cika su da kayan ciye²,,yara kuwa suna hannunsu Daddy while d'aya tana hannun Baban Sabina suna ta shan addu'o'i,,su Badra kuwa sai hira suke musu sam sunk'i barinsu su sarara,iyayen sun kuwa duka sunji dad'i suna cikin farin ciki da suka tarar hankalin y'ay'an nasu yana kwance babu wanda yake tare da wata damuwa,,Inna dai tun da suka shigo suke ta bin gidan da y'ar tasu take rayuwa da kallo,mamakin daular da take ciki da d'aukakar data samu lokaci guda sai yasa suka kalli juna ita da Baba suka yi ajiyar zuciya,sun san dai wannan duk d'aukakar daga ubangiji take,dan shi kad'ai yake da ikon juya AL'AMURA.

A gefen Hammad kuwa lokacin daya barsu a parlor master bedroom d'insa ya wuce yana murmushi cos shi kam yana matuk'ar jin dad'i a duk lokacin da yaga tana cikin farin ciki,shi yasa ko yaya abu yake idan har yasan zai sata farin ciki yake k'ok'arin yi mata shi ba don komai ba sai dan shi kansa yasan ranar yana tsintar kansa cikin farin ciki mara misaltuwa,slightly kwantacen murmushi ya kub'uce masa,gently nd slowly sai ya zauna a gefen bed yana shafo beard d'insa yana d'an lumshe idanunsa,,bud'e k'ofar da tayi a lokacin shi yasa shi gyara zama,har ta shigo bai daina kallonta da wani irin malalacin kallo ba,lokacin data kusa isowa daf da shi itama kallon nasa take ci gaba da yi da idanunta masu d'auke da hawaye tana kuma yi masa murmushi,a hankali taci gaba da tahowa har ta k'araso gabansa,kamar wata kuliya (mage) haka ta d'age hannunsa sai ta shige jikinsa ta lafe,soundly ta saki kuka mai sosa zuciya,murmusawa yayi yana sake holding d'inta tight,bai hanata ba taci gaba da rera kukanta saboda yasan duk murna ce da ganin iyayenta yasa ta yin,sai da yaga bata da niyyar dainawa sannan ya d'ago fuskarta yana kallonta,still hawaye take yana kallonta ya d'an had'e rai
"Wai kukan bai isa ba har yanzun..!?"
Kai ta kad'a masa alamun "Ehhh.!" Saurin sake had'e fuska yayi yana mata hararar wasa da lakuce mata hanci yana fad'in
"Lalaci ne da shagwab'a suka sa ki kukan..!?"
Hanci taja tana saurarawa kad'an daga kukan da take tace
"A'aahh.! Kai ne."
Idanunsa ya fiddo waje yana nuna kansa yace
"Ni da kaina..!?"
Ta kad'a masa kai,sai daya sake matseta a jikinsa suna kallon juna yace
"Uhhuumm.! Fad'a min mene ne nayi miki wanda na saki kuka..!?"
Wasu slender tears ne suka sake zubo mata a hankali tana rausayar da kai tace
"Ai kasan abunda kayi kaima.."
Girgiza kai yayi yace "A'a! A'aahh.! Ni ban sani ba,but d'an fad'a min naji,mene ne nayi miki da zaisa ki zubar da hawaye.!?"
Sai data sauke ajiyar zuciya tana sake k'ank'ame shi,idanunta a cikin nasa tana masa murmushi tace
"Shukhraan'kthiir habibiiy,, ban tab'a tunani ko zaton a irin wannan lokacin zanga mahaifana ba,sai ga shi ka kusanta ni da su,na gode sosai da wannan kyautatawar..Ka sani farin ciki sosai.!"
Kallonta yake tunda ta fara magana yana bin bakinta da kallo har ta idar ba tare da yace komai ba,sai ta d'anyi fari da idanunta tana kallonsa da niyyar yin magana amma sai ta fahimci hankalinsa yayi wani gurin da ban,hannunta dake sak'ale da wuyansa ta gyarawa zama tana bin idanunsa da kallo,passionately ta sunkuya dai² lips d'insa slightly ta bashi gagarumin kiss daya dawo da shi hayyacinsa,sake rik'eta yayi tsam a jikinsa yana sauke ajiyar zuciya continuously yana kallon lips d'inta da suke fizgarsa,tana ci gaba da kallonsa itanma da wani yanayi na gane nufinsa sai ta fara k'ok'arin zare jikinta a nasa tana niyyar guduwa,holding d'inta tight ya sake yi yana murmushi yace
"Ina zaki je ne kike niyyar guduwa ki barni..!?"

"Uhmm.! Zan koma ne wajen su Mamma.."
Ta fad'a tana fuskewa,y'ar dariya yayi a ciki yace
"Mene ne za kiyi musu idan kinje..!?"
Wani malalacin kallo ta bishi da shi tace
"Gaisawa za muyi fa da su.."

"Banda wanda kuka yi..!?"
Tana kallon idonsa tace "To ai ban zauna mun gaisa ba.. Ni ka bari naje kada suga bana nan.."

"Uhmmm.! Amma ba yanzun ba ko..?"
Saurin had'e rai tayi tace "kamar yaya ba yanzun ba.!?"

"Ehh.! Ina son a bani tallafi ne yanzun,anjima sai muje tare,ko ba haka ba..?"
A hargitse tace "Meh.!? Wane irin tallafi kuma..!?"
Rungume ta yayi yana sauke mata numfashinsa a jikin wuyanta,k'asa² yace
"Irin wanda aka bani yanzun.."
Sai da tayi murmushi sannan taci gaba da kokawar kwacewa while tana fad'in
"Wasa kake ko..?"
Ta tambaya tana son ture shi
"A'aahh.! Ni ai bana neman abu da wasa."

"Dan Allah to ka bari ni dai ba yanzun ba.."

"Sai yaushe..!?" Ya tambaya

"Ummm! Ka bari to naje yanzun,,kuma ma ai kasan jego nake.."

"Umm! Na sani ai,,amma yanzun ba ke kika kawomin kanki ba..!? Dan na buk'aci abuna ai banyi laifi ba,tunda tallarsa aka kawo min,na buk'aci a sallama min kuma shi ne za'a fake da batun jego..!?"
Kamar zata fasa masa ihu ta d'ago kansa dake mak'ale da ita tace
"Ni dai dan Allah kayi hak'uri ka bari naje.. Allah kuwa kaga dai bana son abunda kake yi.."

"Ni kuma ina so.."
Ya rad'a mata a kunne yana ci gaba da shafota
"Wayyoo! Allah dan Allah ka bari."
Dariyar tsokana yayi mata yace "Me zan bari ne wai..? Naga ai ke kika kawo kanki,kuma sai kice na bari..?"

"Ehhh! Ni dai dan Allah,,ka gafa da Allah ma nake had'a ka amma kak'i bari.."
Saurin cikata yayi ya koma baya yana mata dariya,a hankali ya kalleta yace
"Matsoraciya..!"
Saurin gyara rigarta tayi ta juya cikin saurin kada ya biyota zata fita,sai da ta bari taje bakin entrance ta tsaya,tana juyowa ta harare shi tace
"Naji d'in.."
Sai ta murgud'a masa baki,da sauri kuma sai ta fice tun kafin yayo ta kanta tana jiyo lokacin da yace
"Zan kamaki ne yarinya."
Murmushi tayi kad'an ta ci gaba da tafiya abunta ba tare data waiwayo ba bare ta tanka masa,cos yana biye da ita a time d'in,tsoronta kuma ya kamota a corridor d'in ta san ita zata ji jiki a hannunsa,,hira sosai suka iske su Mamma suna yi suma sai suka nemi guri suka zauna aka ci gaba da hiran har su,but Sabina duk bata wani sake ba saboda zaman Daddy a gurin,,tun daga ranar da su Innarta suka sauka k'asar sai ya zama kullum a nan suke yini sai bacci ke maida su hotel d'in da suka sauka kasancewar babu nisa sosai da su,a hakan kullum su zo su koma masaukinsu har sai da aka cinye sati guda da yin haihuwar,ranar sati (Friday) daya zagayo manyan raguna Hammad yasa aka babbake a *TRUMP GRILL* a wannan yinin sai ya zama duk wanda yazo cin abinci gurin ya zama free ne a gurinsa,sai dai kawai mutum yayi order yaci ya tashi ba tare da kud'insa ba,,suma a nasu b'angaren a apartment guda suka tattare kwansu da k'wark'wata,suma ranar gaba d'aya sai suka yi order na abincin da zasu ci,da yake su Mamma ma suna nan sai ya zama ita take take kula da Sabina cos Inna dai ta gwada halin Fulani,,duk wasu kayan da Mamma tasan zasu yi mata amfani sai tayo gurzirinsu tun daga 9ja,a y'an kwanakin da suka kwashe da zuwansu kafin sunan ta gwada sata tayi amfani da su,kuma itama sai ta dage take amfani da duk abunda Mamma'n zata bata,kafin kwanaki goma su rufa da haihuwar ta sake yin kyau fatarta sai haske take,,zamanta a y'an shekarun da bazasu wuce biyu ba da y'an watanni a k'asar ta sake gogewa tayi fresh,hutu ya sake zama a jikinta,,kwanakin su Mamma goma duka a U.S wanda yayi dai² da sati biyu da yin haihuwar suka d'auki haramar tafiya ranar kada kuso ganin koke² a gurin mata,bayan sun musu rakiya har airport suka yi sallama da su cike da kewa,jirginsu Inna ya d'aga daga U.S zuwa Saudi Arabia,,duk da a gefen su Baba basu san da tafiyar ba sai a nan bayan zuwansu amma sosai suka yi farin ciki,,yara fa sun zo duniya da farin jini kowa sonsu yake,Daddy ma kansa wata irin soyayyar da yake nuna musu da dukan zuciyarsa sai abun yaso baku mamaki,nd tun da aka yi haihuwar suna shigowa k'asar yake hidima da su,kaya kad'ai da yayiwa yaran da mamansu akwatuna set guda yayi,haka su Jannat duk ya had'e su yayi musu nasu kayan,kyauta kuwa idan ya tashi na bajinta yake yi babu nuna k'aranta,Mamma ma dai ba'a barta a baya ba ta gwada nata bajintar,musamman ma da taji sunanta aka sawa Hussaina,,Baba ma dai lokacin da aka ce masa sunan Marigayiya ne matar Baffa aka sawa Hassana shi da Inna har da hawaye saboda sun san Inna Safiya mace ce mai hak'uri da kauda kai,lokaci guda ajali yazo ya d'auki rayuwarta bayan jinyar y'an kwanaki da tayi da ko sati guda bai kaiba,saboda halin dattakonta nema yasa tun data rasu suke kewarta kuma wannan shi ne dalilin da yasa baffa ya kasa yin wani auren,,su kansu su Inna basu yarda an barsu a baya ba sun yi hidima dai² k'arfin su.
Cikin haka rayuwar taci gaba da zuwa tana wucewa,yayin da a gefe guda Sabina ta ci gaba da bawa yaranta kulawa sosai duk da hidimar gidan yanzun ya k'aru a kanta musan haihuwar da tayi sai Hammad d'in ya nema mata mai taya ta rainon yaran,idan zasu tafi skul wani lokacin shi da kansa yake kaisu,wani lokaci kuma sai subi bus,,rayuwarsu a kullum gwanin sha'awa,yau da gobe haka har yaranta suka fara yin wayo sosai.
Lokacin da suka kai watanni biyar da haihuwa sun sake yin wayo sosai fiye da baya,sun kuma yi girma gwanin sha'awa,kamanninsu da juna yana sake bayyana,tun haihuwarsu har zuwa lokacin saboda tsananin kama da suke da juna yasa ba kowa yake iya gane su ba,idan aka cire ita da Hammad,amma even su Badra wani lokacin idan sun shigo ko a skul da yake basa barinsu gurin Nanny da take taimaka mata da ayyuka yanzun,sai sun tambayeta suna cewa
"Mufa kinsan ba gane yaran nan namu muke yi ba,saboda haka kawai ayiwa d'aya shaida,cos muna son gane Mamma'n mu.."
Sai tayi dariya tace
"Sai kuyi musu da kanku ai.. Amma ni baza ku janyo min fad'an da yafi k'arfina ba.."
Suna jin ta fad'i haka sai suyi dariya suma,da haka hiran nasu sai dai ya canja salo,wannan an rufe babinta kenan sai idan kuma wani lokacin ya sake zuwa da makamancin sa,,zuwa lokacin su kansu su Badran cikinsu duk ya tsufa,sai dai lokacin fitowarsa duniya ne da bai k'arasa yi ba,da yake kuma su a lokacin da suke faman sun samu hutu sai al'amarin yazo musu da sauk'i sosai,kullum idan mazajen su sun fita aiki sai su had'e a apartment guda suna hira abunsu,zumunci suke sosai,idan har ba wai mutum ya sansu ba kafin wannan lokacin tofa babu yadda za'ayi yayi tunanin basu da wata alak'a mai k'arfi (ta jini).

Bayan wasu kwanaki Badra ta haihu,a inda ta haifi y'arta mace da suka mayarwa da sunan Maman su Sultan wato *AMINA* amma suna mata inkiya da *MEENAL* y'an biyu anyi k'anwa duk da yake lokacin sun fara iya zama haka zasu yi ta mik'a hannu suna so rabasu ita,idan suka ga an hana su d'aukan haka zasu cika gidan da kuka,har sai anyi musu dabara kafin suyi hak'uri,,tazararsu da Zee duka a lokacin bai wuce kwanaki goma ba itama cikin hukuncin ubangiji ta sauka amma ita d'anta namiji ne *MUHAMMAD* but shi sunansa suke kiransa da shi,sai su Sabina da suke kiransa Little,ma'ana little Hammad,,bayan nata haihuwar sai ya zama tsakaninsu da Jannat babu nisa dan ita da itan duka tazarar kwanaki hud'u aka samu,itama ta haifi d'anta namiji,wannan dalilin ne yasa ko da suka tashi yin hidimar sunan sai suka had'e suka yi shi rana guda,yaro yaci suna *ALIYU* sunan Daddy sai suke kiranshi da *AABAN,* tun daga kan haihuwar Sabina saboda su Sultan sunga yadda Yallab'ai ya jajirce akan tafiyar SABINA 9ja suma haka duka suka kafe akan basa so,kuma sai duk aka yi sa'a a lokacin suna ta k'ok'arin komawa skul ne suma sai basu tada hankalinsu kan lallai sai sun tafi wankan gidan ba suka dasawa zuciyoyinsu hak'uri kamar yadda Sabina tayi a nata zamanin,,a haka duka suka ci gaba da bawa yaransu kulawa irin wacce ta dace,kwanaki suna ci gaba da tafiya,yara na sake yin wayo,duk da a lokacin y'an biyu su har sun fara koyon tafiya kuma suna iya cin wani abun bayan nono shi yasa yanzun sai tayi tafiyarta skul kuma har ta dawo d'in ba tare da sunyi kuka ba,tunda yake suna tare da Nanny a gida tana yi musu komai,yara suna k'ara wayo da sake rarrabe ahalin su.


*4 YEAR'S LATER...*
Sanye suke da wasu irin bodycon dress na wani bak'in yadi su duka hud'un,sai vail mai kalar egg yolk da suka yi rolling a kansu,fuskokinsu d'auke da simple make-up sai fara'a suke,yadda suke ta sauri da hada² ne zaisa mutum yayi saurin fahimtar akwai wani guri mai muhimmanci da suke shirin zuwa a lokacin,,har sun kusa da entrance na apartment d'in cos a yaune suke bikin fitowarsu daga school of law a matsayinsu na wad'anda ke shirin karb'ar shaidar zama cikakkun BARRISTER'S,fuskokin nan k'unshe da wani irin farin cikin da baya misaltuwa,har suka kusa da k'ofa,Sabina dake baya tsaye a parlor tana kokawar d'ora graduation gown saman nata dress d'in ta kalle su tana murmushi da fad'in
"Heeyy! Mamma's stop."
Dakatawa suka yi a taren suka juyo suna binta da kallon yaya akayi kuma.? Sai ta kallesu itama while tana fad'in
"Amma dai ba haka zaku fita ba ko..? Kuma kanku kunsan dai bamu isa mu fita a hakan nan ba,nd u all knows ko wane irin hukunci ne zai biyo baya ko.!?"
Dariya suka sa Jannat tace
"Matsoraciya,,da waye yace mki zamu fita a nan a haka..?? Ai kuwa da mun ci kaniya yau d'in nan,ana bikin farin ciki mu ma kare da b'acin rai.."

"Lallai.! Kuwa ni dana san hali ai shi yasa ban soma kama hanyar fita bama,,ni da aka gwadawa reality na gani ai dole bazan manta ba,,ranar nanfa wollahi kada kuso ganin yadda ya murd'e,mutum kamar mai iska yayi ta fad'a kamar zai dake ni,,shi yasa ni tun a lokacin nake kiyayewa nd nake sake rok'on Allah akan ya nisanta ni da sake ganin fushin sa kamar haka,ko da wasa wollahi bana fatan wani abu ya had'ani da shi,cos ni kad'ai nasan irin bak'ar wuyan da nake ci kafin na samu ya sauka.."
Zee ce ta jinjina kai alamun tana tuna wani abu daya wuce a bayan itama sai cewa tayi
"Uhhuumm.! Ku dai ku bari kawai,mazan nan fa duka ba sauk'i ne da su ba idan wannan gefen ne,kuna kallonsu nan a haka kamar babu zuwansu da abu wollahi bak'in kishi ne da su na wuce misalin,,ni kaina nawa ogan tun kafin muyi auren sai da ya gwada min nasa colour d'in shi yasa nayi saurin haddacewa tun wuri kafin muzo muna raba abun fad'a,,idan baku manta dinner da akayi na binkunku ba,a kan wannan gowns d'in da muka yi amfani da shi ranar,kada kuso kuji yadda muka kwashe da shi,kuma naga lokacin duka bamu jima da had'uwa ba,amma da dare bayan mun dawo ya kira ni yana fad'a,saboda nayi magana wollahi kusan sati guda muka yi ko miss call d'insa ban gani ba bare na samu full phone call,shi yasa tun daga lokacin da naga ya dawo layi na koyi iya takuna,,bare kuma yanzun da yake ganina a mallakinsa ai sai abunda na gani kuma.."
Ajiyar zuciya Badra tayi bata ce komai ba ita kam,sai dai tayi musu tuni tana cewa
"Kunga fa gara mu wuce,tun kafin a fara kiranmu,kun san suna jiranmu ne yanzun,wannan hiran namu kuma ba mai k'arewa bane,ya kamata muyi abunda ya kamata yanzun idan mun isa 9ja sai mu d'ora,ko kuwa yaya kuka gani.!?"
Amsawa suka yi da hakan yayi musu,sannan duka suka fara kokawar rufe dress din sun da black graduation hoods mai toluwa Asama

Please Login or Register in order to submit comment