Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

neman ku.."

"Inna neman mufa kika ce..?? Waye yake neman namu..??"
Lokacin har Inna ta juya zata fita ta dawo inda ta barta tsaye,hannunta ta rik'o sosai suka zauna a gefen k'atuwar katifarta da Baba ya siya mata tun bayan fara aikinsa a wani textile company
"Rannan ba kince min kinje kai takardu ba..?? Kuma har muka yi magana dake..?"

"Ehh! Inna.. Amma ai..!"

"Ba sai kince komai ba Mamana,,kamar yadda na fad'a ne yanzun kiyi maza ki shirya sai kije kiji kiran da ake muku ko..??

"Kiyi hak'uri Inna,,ba sai na koma ba,ni dai tuni na hak'ura,,gashi Baba bai sani ba har yanzun,shi yasa duk jikina yayi sanyi da al'amarin.. Ina tunanin kawai na fasa zuwan..!"

"Kul..! Na sake ji kinyi irin wannan maganar,tafiya idan har Allah ya nufa babu fashi zaki je da yardarsa,,toma banda abunki tunda har mu da muke matsayin mahaifanki kike fargabar zamu k'i amincewa ya zama mun amince,mene ne dalilin da zaisa kiji kin fasa..!?"
Saurin kallon Inna tayi baki bud'e da mugun mamaki
"Da gaske Inna.. Yanzun kina nufin Baba ma ya amince min.!?"

"K'warai kuwa,,ya amince.."

Tsantsar mamakin yadda akayi Baba yayi saurin amincewa ne yasa ta rik'e Inna ta k'ank'ame,fuskarta cike da fara'ar da bata san ta yadda zata misalta ba ta fara jerowa Inna surutu
"Wollahi Inna duka fargabata da damuwa akan amincewar Baba ne,,nasan ba lallai ya yarda naje wata k'asar ba,,shi yasa tun farko na kasa sanar masa.."

"To ai kinji yanzun na fad'a miki ya amince,,saboda haka sai kiyi maza ki tashi kafin ki makara kuma ki makarar damu,,daga yau in sha Allah babu sauran fargaba.. Ayi maza a shirya a tafi.."
Murmushi tayi ma Inna cikin sauri ta mik'e tabi ta a baya
"Ai Inna yanzunma kuwa zanyi sauri na tafi kada na b'ata lokaci.."

In less than 1 hour ta gama shiryawa,file d'in takardunta da duk abunda tasan zata tafi dashi Inna ta tattara mata guri guda,tana kammalawa ta d'auka sannan ta yima Inna sallama,banda addu'ah babu abunda Inna take yi mata.
Tunda ta fita daga gida har ta isa cikin *AUDU BAK'O SECRETARIAT* bata fasa kiran sunan Allah ba da addu'o'i,,da tambaya da komai ta samu ta iso wanjen da aka ce su je d'in,lokacin data iso ta iske jama'a sosai,amma yawansu sam bai bata tsoro ba,duka addu'ar ta har lokacin bai wuce ace tayi nasara ba,sai da suka wuce awa guda tsaitsaye suna jira kafin motocin gidan gwamnati suka fara isowa,bayan anyi musu bayani da abunda ake buk'ata suyi,sannan aka fara raba musu forms da zasu cike,,then kuma aka sake karb'ar takardunsu da passport guda biyu,tana gama cikewa ta mayarwa da secretary d'in gidan gwamnati,bayan kowa ya mayar da form d'in da aka bashi aka sake musu bayanin daga yanzun zuwa k'arshen sati zasu iya jin kira,saboda haka sai kowa ya kasance ya fara shiri,,godiya suka yi duka after an tab'a siyasa aka sallame su,tunda ta fito take jin zuciyarta cike taf da farin ciki tana tafe tana ci gaba da addu'ah har ta fito titi,napep ta samu da zai mai da ita gida,tana dawowa ta shiga bawa Inna labarin abunda aka shaida musu,daga wannan lokavin bata sake zama ba ta zage taci gaba da addu'ah,babu dare babu rana addu'ah take all the day akan Allah ya basu sa'a,,Inna ma a gefe guda ba'a barta baya ba ta dage sai addu'o'i take musu.
Batun Baba kuwa tunda ya bada izinin taje taji kiran yayi shiru bai sake magana ba,da dare bayan ya dawo ya kirata,tambayoyi yayi mata cikin nutsuwarta tayi masa bayani yadda ya kamata,shima ,addu'ar dai yayi dan tun a daren da Inna ta sanar masa batun ya fara istikara,haka nan kuma tunda ya fara addu'ar neman zab'in Allah sai yaji al'amarin ya shiga zuciyarsa.

*NEW YORK STATE..*
Zuwa yanzun kam Hammad yana aiki ne kawai amma badon ra'ayin kansa ba,,buh still duk da irin nasarorin da yake samu ta fannin aikin ko kad'an baya jin dad'in zamansa a k'asar haka duka baya kallonsu a matsayin abun alfahari,kawai dai yana rayuwa ne saboda yadda Daddy yake son zaman nasa a can amma ruhinsa tuni ya jima da barinsa a 9ja,,a wasu lokutan kuwa idan tsumin soyayya ya tayar masa sai dai ya tafi park yayi zamansa,ranar yini zaiyi baya gida,sai yaga dare yayi ko ya d'an ji dama sannan zai kamo hanya ya dawo.
Shirye²n zuwansa 9ja kuwa a kullum sake k'aruwa yake,sai dai aiki da a kullum yake sake toshe masa k'ofofin damar da yake samu yake,wannan dalilin yasa babu halin ya motsa,bcos yasan yanzun za'a fara nemansa,a wasu lokutan kuwa saboda haushin da yake ji idan aka kirashi cikin takaici zai amsa kiran bcos har yanzun aikin bawai ya gama shiga ransa ba ne.

Sultan da Sadeeq kuwa cikin wannan d'an tsukin idan har ba ranar aiki bane,zaka same su tare,amintar dake tsakaninsu kamar dama can tare suka fara zuwa k'asar,,cikin rayuwarsu a kullum canji ta ko ina a y'an wattani sai sake samuwa yake,yayin da suke ta yin sama a kullum ta fannin aiki.

*NIGERIA..*
Tana kwance kanta a saman cinyar Inna suna fira,while Inna nayi mata tsifar kai,,a hankali y'ar Nokia Inna dake gefen kanta tayi k'ara alamun shigowar sak'o,kamar baza ta kula ba sai Inna ta d'auka ta mik'a mata
"Mamana! Duba min nan ki gani,sak'on mene ne aka turo..?"

"Toh.!" Tace then kuma ta ansa,sai data fara cire key sannan ta fara dubawa,cikin ihun murna ta fara kwararo addu'ah
"Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus salihaat..!"
Tana kaiwa k'arshe ta janyo Head tie d'inta ta yafa a jikinta,sannan tayi sujuda hawayen farin ciki na sakkowa saman fuskarta
"Mamana..! Mene ne..??"
Inna ta tambaya tana jiran taji k'arin bayani,ta jima tana addu'ah kafin ta d'ago tana maimaita
"Alhamdulillah ya Allah..! Alhamdulillah.!³"

"Wai Mamana ki fad'a min abunda yake faruwa kink'i..?"
Sai data gama addu'o'in sannan ta kalli Inna fuskarta har lokacin cike da hawaye
"Inna..! Tabbas Allah maji rok'on bayinsa ne.."

"Haka ne Mamana.. Amma me ya faru ne..?? Sanar dani.."

"Inna batun tafiya karatu ne ya taso,sunce zuwa ranar alhamis mu kasance cikin shiri.."

"Alhamdulillah alaa kulli halin..! Lokaci yayi kenan..?"

"Ehh! Inna.."

"Toh..! Mamana,Ubangiji ya bada sa'a ya kare ki sharrin mutum da aljan.. Ya rufe idanun mak'iya akanki.."
Nasiha sosai Inna tayi mata mai ratsa zuciya a lokacin kamar yaune zata bar k'asar,, a ranar kuwa saboda tsananin farin ciki kasa bacci duka gidan suka yi,washe gari da yake ranar talata ne 2 days before tafiyarsu Inna tasa ta shiryawa taje gurin baffanta,da yamma sai tabi motar da zai kaita garin had'ejia (GINSAU BIRNIN DOKI),,duka kwananta d'aya a garin ta juyo cike da alkhairin baffa gare ta.

Babanta ma yayi mata y'an siye² dai² k'arfinsa ba tare daya zafafa ba dan har waya ya siya mata da zasu dunga jin yadda take,,ta b'angaren Inna ma ta d'an yi mata siyayya dai² aljihunta,,tun da batun tafiyar ya taso,gaba d'aya suka fara alhini,bacci kuwa sai dai da yake ana cewa b'arawo ne,amma sam basa wani samun isasshen bacci,,a daren data dawo daga had'ejia alhinin tafiyarta yaci gaba da k'aruwa,ita tana jin babu dad'i saboda rabuwar da zata yi da iyayenta a dai² lokacin da bata zata ba,suma suna alhinin tafiyar nata,a haka dai da taimakon Inna da Baba ta samu ta harhad'a y'an kayan tafiyarta.
Washe gari da safe misalin karfe 7:00am suka d'unguma gaba d'aya da niyyan yi mata rakiya zuwa airport,kasancewar tun dare suka gama sallama,amma ko da suka fito daga gida suna tafe a hanya cikin napep sai da Baba ya sake mata nasiha sosai,,Inna kuwa tunda suka taho da tayi shiru bata k'ara magana ba har suka iso airport,,,a gabansu akayi mata komai,har zuwa lokacin da aka fara kiransu,,cikin rashin kuzari ta mik'e tana musu kallon bankwana,sabbin luggage's d'inta da Baba ya siya mata akan tafiyar ta bi da kallo sannan ta sunkuyar da kanta hawaye yana bin kumatunta,juyawa tayi ta fara tafiya bayan sunyi sallama,jikinta duka a sanyaye taci gaba da jan akwatinta hawaye yana ci gaba da sakko mata,har ta d'anyi nisa dasu sai ta juyo a hankali tana kallonsu,su kansu jikinsu duka a lokacin ya sake yin mugun sanyi bare kuma itan da take jin kamar ta fasa,sakin jakunkunan tayi a k'asa ta dawo inda suke da gudun ta,tana zuwa ta rungume su tana sakin kuka mai sauti.
Daga ita har Inna zuciyoyinsu sun gama karyewa,banda kuka babu abunda suke,tun baba yana lallashinsu har sai da suka sa ya fara fusata,da kyar da kuma fad'a² nasiha² yayi k'arfin halin rarrashinsu,shima d'in sai daya bud'e musu ido sosai,bcos da fari hak'uri yayi ta basu suka k'i sauraronsa sai da suka ga yayi fushi ne sannan suka hak'uran,,sallama ta sake yi musu sannan ta juya a hankali tana tafiya daga nan bata sake dawowa ba kuma bata sake waiwaye ba kai tsaye ta wuce abunta tana goge hawayen dake sakko mata.....



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Really sorry fan's,last page i was mistaken,maimakon *NEW YORK* na sa *FLORIDA*,amin afuwa sabo ne yasa ni aikata hakan,,hope za kuyi min uzuri,nd kunga kenan page d'in da nayi alk'awari wa duk wanda ya gano KUSKUREN nawa ne ba.?😉_

🎉
_May u celebrate this day till u blow hundreds of candles nd still hop,skip nd jump all the time dear..Happy Birthday Cweet *MAI DADDAWA'S.*_
🎊

*32.*
_#Relocation_

Sai data b'acewa ganinsu sannan suka ja k'afafunsu da sanyayyen jiki,cike da niyyar komawa gida,yayin da zuciyoyinsu suka cika da damuwar rabuwa da ita,,suna fitowa daga airport cab suka d'auka da zai maida su gida,tunda suka kamo hamya duka suka yi shiru ba tare da wani yayi magana ba har suka k'araso gida,haka nan tunda suka dawo suke sake ci gaba da binta da addu'o'in fatan sauka lafiya.

Dai² lokacin data juya tafiya kawai take amma duk wani k'warin guiwarta yana tare da mahaifanta,tabbas yadda take ganin damuwa shimfid'e saman fuskokinsu,yana k'ara tafiyar mata da sauran kuzarinta,sosai hakan yasa ta fara ji aranta ba don tafiyar da zata yi saboda ci gabansu bane gaba d'aya lallai ne da babu wani dalilin da zaisa ta tafi ta barsu da kewarta,,wannan dalilin yasa tunda ta juya taji bazata iya sake juyawa ta kallesu ba,bcos tana tana ji a ranta yin hakan a gareta yana dai² ne da rugujewar muradinta.
Har ta shiga cikin jirgi bata daina hawaye ba haka nan bata fasa addu'ah ba,a hakan ta fara kokarin duba seat d'inta,lokacin da taga seat d'inta daga gefen window hamdala tayi sannan ta wuce ta zauna,a hankali kuma sai ta lumshe idanunta,karo na farko kenan data tsinci kanta a jirgi,sai duk take jin wani iri buh ba lallaine mutanen dake cikin gurin suyi saurin fahimta ba,bcos kowa aikin gabansa yake,kallon mutane ta d'anyi sama² taga yadda suke ta gaishe² da juna abunsu kowa yana ta murna,wasu kuma data kallesu sai taga kamar sun san juna,,tana zaune tayi shiru bcos har lokacin akwai wad'anda basu gama shigowa ba nd babu wanda ta gani data sani,kowa a gurina bak'on fuska ne,yasa ta d'auko y'ar wayarta kirar techno camon ta shiga ciki da d'an dubawa saboda ba komai ta sani ba,kasancewar wannan shi ne karo na farko data fara rik'e waya,camera ta shiga kamar yadda taga mutane suna ta d'aukan photo,da nufin d'aukan kanta saboda ta ajiye tarihi,buh bata san yadda za tayi ta d'auka d'in ba,jigum tayi tana kallon mutane,zuwa wani lokacin kuma ta sake d'ago wayar tana kallo,so take ta gano inda damuwar yake amma abu ya gagari saninta
"Lemme help u..!"
Sanyayyar muryar ta ambata,a hankali ta d'ago kyawawan idanunta ta sauke su akan kyawawan y'an matan biyu dake tsaye suna mata murmushi,murmushin itama tayi musu sannan ta d'aga hannunta biyu 🙏
"Assalam alaikum warahmatullah.!"
Fahimtar abunda take nufi yasa su yin murmushi sannan suka yi mata sallama had'e da bata hak'uri,tana amsawa tana musu murmushin ta mai kyau,a mutunce suka gaisa da su sannan d'ayar data fara magana ta karb'i phone d'in nata ta fara yi mata pictures masu kyau,tana ganawa ta mik'a mata wayar da fad'in
"Gashi ko..? Amma fa gaskiya sunyi kyau sosai.."
D'ayar da suka zo tare itama tayi murmushi
"Haba dear kema banda ke,ai itan mai kyau ce,so kinga kuwa pic d'inma dole su yi kyau.. Bcos kyau ya had'u da kyau.. So.! What will it be kenan..??"

"Most beautiful..!"
Dariya suka yi dukansu biyu,sannan Sabina ta karb'i phone d'inta da take mik'a mata tana ganin pictures d'inta,,sanye take cikin Arabian gown black colour mai adon red a jiki,yadda tayi rolling vail d'in ba k'aramin kyau yayi mata ba,kayan sunyi matuk'ar dacewa da jikinta tamkar dama can daga united Arab ta fito,musamman kuma daya kasance ta k'awata y'ar fuskarta da light make-up,powder kawai da tasa sai lip gloss da d'an kajol data zizarawa idanunta,amma shi ne suke ta zuzuta kyaunta haka,ita har mamaki suka so bata dan yadda suke ta kod'ata,sai dai bata ce komai ba,tana gama kallon pictures d'in ta d'ago tana murmushi tace
"Thanks Sis.."

"Never mind princesse.. Buh can we be friends..!?"

"Why not..?"
A kusa da ita suka zauna suna fad'in
"Thanks once again.."

"U are welcome.."
Still ta farkon ta sake cewa
"Am BILKISU ALIYU (BADRA).. Ke fa.??"
Sai da tayi murmushi ta amsa da
"Hafsat Al'amin Usman..buh u can call me *SABINA.."*

"Wahh.! What a nice name.."
Murmushi ta sake yi tana fad'in
"Thank u,,buh friend d'inki fa..??"
Itama Sabinar ta tambaya,murmushi d'ayar tayi mata tana fad'in
"Ismiy.! JANNAT MUKHTAR BABANGIDA.."
Dariya suka yi jin ta fad'a da larabci,Sabina cikin tsokana tace
"Gashi kuma ni anyi rashin sa'a.."
Da sauri Jannat ta tari numfashinta
"Ohh.! Friend na mene ne fa..??"

"Bana jin Arab.."

"Ahh haba.. Yanzun waye zai kalle ki ya yarda bakya ji..??"

"Serious ban san mene kika fad'a ba,,ki fassara min..."

"Uhmm! I think dai ba ni kike fad'awa ba..?"
Dariya suka yi daga haka suka ci gaba da hira kamar sun jima tare,,suna ta fira Badra ta kalli Sabina
"Princess.! Na tambaye ki wani abu mana.."

"Allah yasa na sani.."
Za tayi magana kenan staff d'in jirgi suka fara yiwa wad'anda ke d'auke²n photo magana da su kashe wayoyi,,wayarta ta d'auko tayi switching nata off,sannan ta mayar cikin handbag d'inta,,taimakonta d'aya a lokacin duk da bata tab'a shiga jirgi ba ta kula da yadda y'an matan suka d'aura seatbelt,nan itama tayi k'ok'arin d'aurawa,a hankali jirgi ya fara k'ok'arin tashi,idanunta ta mayar ta rufe bakinta d'auke da addu'ah har suka lula cikin sararin samaniya.
_(Safe trip our princess).._

*NEW YORK CITY..*
A gaggauce ya shirya kasancewar daren jiya bai samu isashen bacci ba,saboda damuwar daya sawa ransa,yana gama shirin ko tsayawa baiyi ba ya fito da sassarfa bcos yana daf da makara a aiki,,har ya fito zai shiga mota ya tuna wayoyinsa daya bari,siririn tsaki yaja before ya sake komawa,yana shiga ya tarar da wayan da alamun kira ya katse,bai tsaya duba waye ya kira shi ba ya d'auka yayi waje,,har yayi nisa sosai a hanya kiran Sultan ya sake shigowa,hands free ya maida ita cikin isa da mulki yana fad'in
"Dude.. Ya aikin..!?"

"Normal man.. Buh ka tayani murna,,yau na shiga aka bani takardar canjin gurin aiki.. Yanzun hakama ina kan shiryawa zan baro Las Vegas,,dama duk bana jin dad'i da nayi nisa da ku,ni kad'ai kamar bani da relatives.."

"Ina suka maida ka kenan..?"

"Nan kusa daku ne.."

"Uhhuumm..! Kaji dad'in ka,dama yanda kake dawowa ka tare a nan gara da suka maka canjin kaga zirga² ya ragu,,kaima ka samu ka maida hankali sosai akan aikin.."

"Nufinka dai kace bana bawa aikina muhimmanci ko..??"

"Nop.! Buh kusan hakan nake nufi.."

"Ok.. Good,,idan na iso zan nemeka.."

"Ok.. Sai naji kan."
Suna gama wayan ya sake bawa motan wuta dan yana son ya k'arasa before 8 tayi masa,,har lokacin daya isa gurin aikinsa sannan ya sassauta gudun sa.

*PENNSYLVANIA CITY (U.S.A).*
Cikin katafaren filin tashi da saukar jirage na *Philadelphia International Airport* jirginsu SABINA yayi dirar mikiya,a kuma cikin garin na Pennsylvania,,zuwa lokacin tuni jikin kowa dake a cikin jirgin ya gama yin tilis dan gajiyar zama,saboda tafiya da suka kwaso mai d'an karen nisa from 9ja to U.S hours d'in akwai nisa,,jiki duk yayi tsami masu bacci sunyi sun gaji,haka masu hira ma sunyi sun bari,yayin da kowa ka duba fuskarsa ya gama k'osawa jira kawai yake a iso.
Lokacin da aka fara sanarwar mintunan da suka rage a sauka kada kuso ganin k'auyenci a gurin mutanenmu,tun ana sama kafin jirgi ya gama sauka,mazauna gefen windows suke lek'en k'asa,hatta da na tsakiya suma ba'a barsu a baya ba,,k'asar kam akwai ci gaba sosai tun a haka da muke hangota,a raina nace wani abun kam sai ma mun sauka,,har jirgi ya sauka suka fara fitowa basu fasa nuna hali ba,kowa sai bud'e baki yake anata kalle² munga tsari ba kamar mu nan ba,duk dai nasan 9ja ma ba baya ba akan wasu k'asashen duk da yadda na raina ci gabanmu da naga U.S nasan muma a aljannar wasu muke hakan sai yasa ni godewa Allah bisa ni'imar da yayi a gare mu,,a nan suka iske wakilan gidan gwamnati da zasu jagoranci ragamar nemawa d'aliban admission a mabambanta schoolsa cikin k'asar da zasu yi karatu,bayan kowa ya shiga mota aka sake d'aukan hanyar da zai kai su *VILLANOVA UNIVERSITY* dan su Sabina kam can aka nema musu.
Kowa inda yake so nan aka ajiye shi,Sabina kam da yake dama ita b'angaren *LAW* take so,saboda shi ne muradin ranta,,sai aka yi sa'a a nan d'inma suka sake had'uwa da k'awayenta na cikin jirgi (Badra da Jannat),cos dukansu a k'ark'ashin school d'aya ne zasu yi karatu,ma'ana dai *villanova school of law* lamarin sosai yayi musu dad'i daya kasance suna cikin faculty d'aya nd kuma dama tun kafin su baro 9ja zumunci ya fara k'ulluwa a tsakaninsu.
An raba kowa zuwa school d'insa,yayin da ya kasance musu zasu zauna a hostel,,wajen rabon d'akunan kwana sai ya zama an kusa samun sab'ani,inda aka so rabasu da juna,,Jannat na zaune kan seat Badra ta sameta sai had'e rai take
"Heeyy lady..! What's up..?? Naga kina had'e rai,,mene aka miki ne..??"
D'agowa tayi ta kalleta fuska babu walwala
"Ba d'aki d'aya zan zauna daku ba.."
Teasingly Badra ta ci gaba da kallonta
"So..! Sai kuma aka yi yaya..??"

"I don't wanna leave ur side..!*
Dariya ta kyalkyale da shi tana fad'in
"Kaii..Lady kina da ban dariya.. Me yasa bakiyi musu complaining ba to..??"

"Haba mana ki gane abunda yake faruwa,ni ban san mene ne zance ayi saurin canjani zuwa room naku ba.."

"Good.. Kinga kenan zaki zauna a duk inda aka kaiki tunda baki sani ba.."

"Ohh! Dear.. Kizo muje nasan zaki yimin k'ok'ari ai,Allah bana son wancan room d'in duka fa ba y'an nahiyarmu bane.."

"So what..? Ba sai ki zauna tare da su ba,tunda ke baki da baki.."

"Please dear.. Muje to tare kinji..?"
Kallonta tayi from head to toe ta tab'e baki,Sabina dake zaune gefensu tana kallon damar su yanayin yadda Badra tayi sai ya fara k'ok'arin tuna mata wani fuska,buh saboda ta d'an rud'e kad'an a time d'in sai yasa bata yi saurin ganowa ba
"Kinga idanma zaki jene ki dawo to,if not kuma mu zamu yi tafiyarmu.."

"Haba friend ke kuwa ai ya kamata ki rakata,, babu dad'i ace kunzo tare wajen kwananku ya bambanta.. Ko kema baza ki so hakan ba.."
Sabina da tun da suke magana bata ce dasu komai ba ta fad'a tana kallon Badra
"Ni kam babu inda zani,ko ina sai dai ni na zama bakinta,idan bata iyawa ta zauna da sababbin fuska.."

"Ok.. Shi kenan,muje friend na raka ki kinji.."
Sabina ta fad'a tana mik'ewa tsaye,fuskar Jannat da fara'a ta rungume Sabina tana cewa
"Thank u.! thank u³.!! Princess."
Murmushi tayi suka kama hanya su biyun,,basu jima sosai ba suka dawo suna tafe suna hira sama² har suka k'araso inda suka barta,kallonsu tayi ta ce
"An canja d'in..!?"
Harararta Jannat tayi tana cewa
"Ba'a sani ba..!"
Not minded ta ce
"Ok.. Let's go ko..?"
Luggage's d'insu duka suka ja daga nan suka kama hanyan hostel.

*NIGERIA..*
Tunda Badra suka tashi akan idon Mamma,bayan ta dawo gida take ta k'ok'arin kiran line d'insa dan ta sanar da shi ya dunga sa ido akansu,buh bata samunsa,,a gefe guda kuma batun da Daddy yazo mata da shi wanda sam zuciyarta bata aminta da batun nasa ba,shi yasa take ta nemansa

Please Login or Register in order to submit comment