Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sannan ta jinjina masa kai_
_"Lafiya muke baffa amma ba k'alau ba.._

_"Subhanallah..! Me ya faru haka kike fad'in irin wannan maganar,,shin wani abu ya samu *HAFSATU* ne ko kuwa Babanta..?"_

_"A'a! Baffa,al'amura dai ne suke faruwa,sai dai ina jin tsoron wani al'amari ne kawai."_

_Tambayarta baffa ya fara yi,cikin yanayin damuwa ta fara warware masa kaf abunda ya farun,dama wanda yake kan faruwa,ba tare data yi kwauron baki ba ta sanar da shi tun daga kan asalin had'uwar Hammad da Sabina,,murmushi baffa yayi sannan a hankali ya kalleta yana cewa_
_"Kada ki sawa ranki damuwar komai,,alkhairi ne ya had'a su kuma in sha Allah shi zaici gaba da wanzuwa a tsakani,,,amma yanzun abunda nake so shi ne,ki bani nan da gobe in Allah ya yarda zanyi istikara,da yardar Allah zaki ji bayanin komai zuwa goben..Tunda kince jibi zaki koma ko...!?"_

_"In sha Allah baffa,,jibi nake son juyawa tunda na bar yarinya ita kad'ai gashi kuma tana jarabawa..."_

_"Allahu ya kaimu da rai da lafiya kuma muna masu imani..!"_
_Bayan Inna ta amsa da ameen,suka ci gaba da hira irin ta yaushe gamo.. Washe gari da rana bayan ta gama kintsa y'an kayayyakinta tana zaune suna hira da k'annenta y'ay'an wajen baffan,sak'on kiran baffan ya riskota,da sauri ta mik'e ta nufi d'akinsa,tun kafin ta shiga tayi sallama,daga ciki baffa ya amsa mata sannan ya bata izinin shiga,a hankali ta d'aga curtains d'in d'akin ta shiga kanta a k'asa,saboda girmamawar da take masa a matsayin baffa na shak'ik'in mahaifinta,bayan ta zauna baffa ya kallota_
_"MAIRAMU..! Wane ne zaiyi tafiya a cikinku,,Mijinki ko y'arki ko kuma ke.??"_
_Fuskarta da alamun damuwa ta d'ago ta kalli baffa_
_"Tafiya kuma baffa..?? Ai kam ina tunanin babu wanda zai yi wani tafiya,,to ban k'i ba dai da yake gani nayo tafiya yanzun.."_

_"Ba wannan tafiyar nake magana akai ba,akwai tafiya da d'aya cikinku zaiyi,tabbas na gani.."_
_Shiru Inna tayi tana nazari,amma iya tunaninta da hasashenta ta kasa gano ma'anar abunda baffan yake son sani_
_"Shi kenan mu bar wannan batun ko,tunda Allah bai nufa muna da rabon gano wannan ba,amma tabbas akwai alkhairi a cikin tafiyar da za'ayi,, sannan batun istikara nayi,cikin hukuncin ubangiji kuma akwai haske cikin lamarin,in sha Allahu kamar yadda ya fad'a muku zai dawo d'in zaku ganshi ya dawo ba da b'ata lokaci ba,,in ba don an samu sab'ani ba,da tuni kun had'u,to Allah bai yanke ba,shi yasa har yanzun suka gagara gamuwa da juna,,amma shi kansa yaron yana cikin damuwa a halin yanzu,sai dai za muci gaba da addu'ah Allah ya sauk'ak'a mana baki d'aya.."_

_"Allah ya sauk'ak'a mana kam.."_

_"Ameen..sai abu na gaba da nake son sanar miki,ina so ki sani ko da zuwa nan gaba kinga an d'auki shekaru ba tare da yaron nan ya saeo ba,ko baku had'u da shi ba,,ina horonku da kada kuyi k'ok'arin raba su bisa b'acin rai ko fushi,,duk abunda kuka ga ya faru *MUK'ADDARI* ne daga rabbal izzati,saboda haka mu bamu isa zartar da hukunci ba,sai wanda Allah ya zana,ita k'addara a koda yaushe d'an adam baya tab'a kauce mata,,muyi hak'uri da duk abunda muka ga ya faru,in sha Allah lokacin farin ciki yana nan zuwa.."_

"Innata..! Ina ta miki magana naji kinyi shiru,tunanin mene ne kike yi.!? Har ya janyo duk baki ji magannar da nake yi ba..!?"
A d'an firgice Inna ta dawo duniyarta tana kallon Sabina data tsare ta da ido,murmushin k'arfin hali tayi mata sannan ta furta
"Babu komai y'ar Inna.."

"To amma Inna kina ji ina tayi miki hira amma kika yi shiru.."
Kanta Inna ta shafo tana fad'in
"Kada ki damu kinji autata,ina d'an wani nazari ne shi yasa kika ji nayi shiru ban amsa miki ba."
Zumb'ura baki tayi gaba while tana buga k'afa a k'asa,da sauri Inna ta rik'o ta tana dariya da fad'in
"A'a'a..! Haba autata kada kisa mak'ota su shigo kallonmu mana,kuka ai ba naki bane,,maza d'auko min jakar can na baki tsabar ki da baffa ya aiko miki da shi.."
Murmusawa tayi sannan ta mik'e
"Allah yasa kifi baffa ya aiko min da shi.."

"Kaji kwad'ayin ba,,har addu'ah ma kike yi..?? To ba shi bane goruba yace na kawo miki ki tattauna wai ko hak'oranki za suyi k'wari kamar nasa."
Cak ta tsayawa a gaban sack d'in da Inna tazo da shi tana kallon Innar
"Da gaske Inna..!?"

"A'aahh! Yo zanyi miki wasa ne..!?"
Sosai ta had'e girar sama dana k'asa nd ta dawo ta zauna kusa da Inna
"Barshi kawai Inna,,na yafe.."

"Auuu! Ba kya so kenan.. Kin raina hakan..??"

"Haba dan Allah,, yanzun Inna fisabilillahi kawai shi baffan nan sai ya rasa me zai bayar a kawo min sai ya wani aiko min da goruba.!? Goruba fa..? Allah ni dai A'a bana so.."
Dariyar zolaya Inna ta shiga yi mata
"Dama sai daya fad'a min,idan na baki kai tsaye ba lallai kiyi murna ba,shi yasa yace na fad'a miki haka.."
Saurin kallon Inna tayi da rashin fahimtar inda maganarta ta nufa,kafin tayi magana cikin hanzari Inna ta tari numfashinta
"Ni d'auko min kaya na fitar da abunda zan fitar.."
Saurin tashi tayi ta d'auko har lokacin fuskar ta tana yadda take,k'amshin kifi data fara jiyowa yasa ta matsowa gaban Inna tana baza idanu kamar zata ci babu,kallonta Inna tayi tana girgiza kai kafin ta janyo k'unshin kifi kashi² ta tura mata guda da fad'in
"Gashi nan sak'on baffana.. Shi kenan dai ko.?"
Washe baki ta fara tana fad'in
"Haba baffa yanzun ka biya ni,ai da wollahi idan naje sai ya siyo min kifi na ya bani..Kuma a baki ma zan sashi ya dunga bani.."

"K'aniyar ki,,baffan nawa sa'anki ne..??"

"To Inna ba kakana bane,ai kinga ni dai jika ce kuma matarsa,idan yana son auren sai ya fanshi kansa.."
Girgiza kai Inna tayi tana ci gaba da fitar da kayayyakin da tazo dasu,yayin da Sabina kuma take gefe tana ci gaba da turawa cikinta kifi babu wasa.

*FLORIDA STATE..*
Aiki kam a y'an kwanakin nan tuni ya kankama,tsakanin su uku da suke tare duka babu wanda yake sanya,kowa ya kama aikinsa bisa gaskiya duk da a yanzun suna kan matakin karb'ar horo na musamman da ake gudanarwa,kasancewar ba iya mutum goma na skul d'insu bane kawai,ko cikin makarantun da suka yi selecting ma bayan skul d'in Jacksonville sai daya had'a har da makarantu irin su Florida state university,nova southeastern university,embry-riddle aeronautical university,valencia college,stetson university,miami dade college,st petersburg college,ave maria university da sauran wasu fitattun universities dake cikin k'asar American,amma duka a ciki anfi d'aukan universities d'in FLORIDA state nd ko a yawa ma mutanen su sun ninka sauran a ciki,though ma dai tun a interview suka fara tantancen wad'anda suke ganin za sufi jajircewa akan aikin.
Cikin watanni biyu kuwa akayi komai daya shafi basu horo aka gama,bayan nan kuma aka fad'a shirye²n k'addamar dasu a matsayin sabbin ma'aikata a k'ungiyar *FBI*,cikin gagaruman taruka da k'ungiyar ta tanada ya had'a har da taron bada lambar girmamawa ga mutanen da suka fi kowa k'wazo cikin d'aruruwan mutanen da aka horar,secretly baa tare da sanin ko mutum guda ba hukumar tayi selecting mutane goma kacal wanda take ganin sune suka fi kowa jajircewa.

Had'ad'd'u kuma tsadaddun manyan motoci na alfarna dake fakawa a harabar *McCormick's Place* a cikin birnin Chicago tun a wayewar garin,yasa jama'ar da basu san da taron ba duk iya sanarwar da akayi tayi kafin lokacin ya sake janyo hankulan al'ummah,,yayin da mutane iri² daga sassan duniya,kama daga farar fata zuwa bak'ak'e da suka riga suka ji batun,wasu kuma ta sanadiyyar y'an uwansa da suke cikin hukuma yasa gurin sake d'inkewa,jama'a suka ci gaba da hada-hadar ganin sun shiga d'akin taron,ni kaina da kyar na samu hanya na shige,duk da gayyata ta aka yi amma y'an gayyar sod'i har sun rigani wucewa ciki,lokacin dana shiga ciki kuwa sakin baki nayi saboda tsatuwar da gurin yayi gami da girmansa,a iya da shige²n da nayi ina tunanin ko a tarihi bana tunanin na tab'a ganin convention center da yakai kwatankwacin girman wannan,a labari ma ni ban tab'a jin wani ya fad'a ba,,sai dai kamar yadda najiyo wani yana fad'a a gurin cewa yayi,"wannan d'akin taron yana d'aya daga cikin manyan d'akunan taro mafiya girma a k'asar amuruka,sannan ak'alla yana iya d'aukar mutane sama da 4,249,idan kuma har batu ake na fad'insa gurin daya ci,tabbas zai kai girman k'afa 2.6 million sq.ft",,sake k'arewa gurin kallo nake ina k'arawa gami kuma da maimaita abunda naji baturen yana fad'a,kafin na samu damar samun matsuguni na hakimce abuna ina jiran naji an fara gudanar da abunda ya tara mu dominsa
(kunsan dai ni ba gayyar sod'i naje ba,,amma tun daga nan fa inda nake na hango su o'o anzo d'aukar rahoto)
Wasa² sai da aka d'auki tsayin mintuna talatin ana ta hayaniya k'asa²,wanda ahalinsu suka zo musu sai murnar ganin y'an uwansu da danginsu da suka zo domin taya su farin ciki suke,,isowar shugaban k'asa da wasu daga cikin governors zuwa masu manyan matsayi a cikin k'asar yasa dole guri ya d'auki shiru tamkar babu wani mai rai a gurin,bayan wucewar wasu tak'aitattun mintuna aka fara gudanar da taron,,banda zallar yaren nasara da baturen yake kwararo dogon jawabai babu abunda yake tunda ya cafki kan electromechanical transducer, ba saurara ba sai daya d'auki dogon lokaci cikin bayanin nasa da suka had'a da jawabin maraba ga shuwagabanni zuwa sauran relatives da suka samu damar halartar taron,,tun daya fara bayani guri ya d'auki harami kowa ya saurara yana jin bayani cikin tsaftataccen turancinsa da babu algus,har ziwa sanda ya kai matsaya,bayan nan kuma sai aka kira shugaban k'ungiyar FBI shima domin jin ta bakinsa dangane da irin nasarorin da k'ungiyar ta samu a lokutan baya,shima dai tunda ya fara zuba magana sai da ya d'auki tsawon ak'alla mintuna arba'in sannan ya saurara,duka guri nan ya kacame da sound na tafi saboda bayanin da yayi ya shiga jikin jama'a sosai,,bayan duk an gama jawabai,sai aka sake kiran shugaban k'asa dan ya mik'a lambar girmamawa ga wad'anda Allah ya nufa suna da nasara.
A nan fa ake yinta,kada kuso ganin d'umbin ma'aikatan da k'ungiyar ta d'auka a wannan karon,Muslim da Christian kowa addu'ah yake tunda yaji batun bada shaida ga mafiya k'wazo, kowa rok'on Allah yake akan yasa ya kasance cikin mutum goman nan,,shugaban k'ungiyar FBI shi yake mik'a lambar girmamawa ga shugaban k'asa shi kuma ya mak'ala musu a jikin rigunan suit d'insu,mutum taran farko da aka kira duka Christian ne,kuma babu wani d'an Nigeria,sai dai idan an fad'i sunan k'arshe kaji ance daga k'asa kaza,haka ko su a cikin k'asar bisa wani hukuncin na ubangiji ba'a samu ko da mutum d'aya da ya kasance d'an k'asar amuruka ba,duka sun fito ne daga wasu k'asashen daban²,a kan mutum na farko kuma na k'arshe wanda yafi kowa jajircewa shugaban k'ungiyar ya tsaya,sai daya sake janyo dogon bayani akan wannan hazik'in,d'aya tamkar da dubu,yabo da zuzutawa yayi masa mai girma sannan ya sake yin kira ga sauran ma'aikatan k'ungiyar da su kasance sunyi koyi da shi wajen bada gudunmawar su akan ayyukansu,,guri duka yayi shiru kowa jira yaji wane mai sa'ar ne,juyawa yayi gefen da suke zaune yana murmushi da kallonsu,yayin da idanun jama'a da dama suke rufe suna addu'ah da kiran allolinsu (Ina nufin Christians)

Hammad na hango zaune can daga line baya,kansa a k'asa yana latsa waya,sam hankalinsa a lokacin zan iya cewa baya gurin haka nan jawabin duk da ake yi baya tare da su bare ya iya fahimtar abunda ake fad'a,,tab'a shi Sultan yayi yana fad'in
"Dude! Get ready..!"
Bai d'ago ba nd hankalinsa still yana akan phone d'insa da yake ta k'ok'arin kiran Mammansa ya furta
"Akan me fa..!?"

"Kai dai kawai ka shirya,,zaka ji ko akan mene..!"
D'agowa yayi da niyyar magana,shima Sultan d'in yana shirin ya sake masa magana shugaban k'ungiyar FBI ya ambaton sunan
"MUHAMMAD ALIYU MUHAMMAD... From Nigeria..!"
Kallon-kallo suka yi tsakaninsa da Sultan,fuskar Sultan d'auke da wani irin murmushi ya d'age masa eyebrow d'insa
"Na fad'a maka ai..Za ka nemi rainamin wayo.."
Girgiza kai Hammad yayi kafin yayi magana aka sake maimaita kiransa,babu yadda zai yi a lokacin,dan haka dole tasa shi mik'ewa daga gurin da yake ya nufi saman deck,tun daya taso daga mazauninsa kada kuso ganin idanun da suka yi masa caa akai,a lokacin da dangi suke murnan nasu ya samu,hatra wad'anda basu had'a alak'a da shi ba,ta y'an uwantaka suma suna farin ciki sakamakon k'asa d'aya da suka fito,hakan sai yasa suke jin kamar sunfi kowa sa'a sanadiyyar nasarar daya cimma,,y'an jaridu kuwa zuwa y'an mata masu ji da kansu da suke gurin ganin handsome kamarsa yasa su rububin haska shi da ruwan flashes,,bayan ya tsaya gaban a gutin suka yi hannu da Mr president sannan ya mak'ala masa d'an tag mai d'auke da rubutun da na kasa ganowa saboda nisan da muka yi da juna,sannan ya sake mik'a masa wani had'ad'd'en envelope a samansa kuma an d'ora k'aramar pistol mai masifar kyau,,bayan duk an kammala k'addamar da su a matsayin sababbin ma'aikata taro ya fara k'ok'arin watsewa,,ana tashi a gurin duka suka fito da niyyan ganawa da y'an uwa da abokan arzik'i wad'anda suka samu damar halartar taron,tun daga fitowarsu kafin su kaiga niyyarsu tuni y'an jaridu suka rufe su suna son d'aukan jawabi daga bakunansu,cikin dabara su Sadeeq da suka ga surutun ba mai k'arewa bane suka zare jiki suka gudu ba tare da Hammad ya fargaba ba. Bayan tafiyarsu shima d'in ya samu ya sha da kyar,yana tserewa jama'a a tunaninsa ya baro su Sulran a gurin ya kamo hanyar masaukinsu.

Bayan taro da y'an kwanaki aiki ya kankama,duk inda zaka ga Hammad to tabbata yana tare da Sadeeq kasancewar su d'in an ajiye su a New York,,yayin da Sultan shi kuma da aka tashi d'auke shi daga nasu headquarter d'in sai aka yi posting d'insa zuwa Las Vegas,rayuwa kam a yanzun tayi kyau a b'angaren su,ko wannensu yana zaune a muhalli mai kyau da ma'aikatar ta basu,cikin kwanciyar hankali da nutsuwar rai,,sai abunda ba'a rasa ba.


*SOME MONTHS LEAVE...*

*NIGERIA..*
A matuk'ar gajiye ta shigo cikin gidan ta fara ajiye hijab d'inta da file d'in da takardunta ke ciki tana fad'in
"Wash..! Gaskiya na gaji sosai.."
Inna da shigowarta cikin d'akin kenan ta kallota tana fad'in
"Sannu da dawowa mamana.."
Saurin juyowa tayi ta kalli Inna da murmushi a fuskarta
"Inna..! Wollahi nazo miki da albishir mai d'an karen dad'i.. Amma barin fito daga bayi.."
Tana fad'a ta fice a gurguje ta d'auki buta tayi hanyar bayan gida
"To Allah ya fito dake,,yasa kuma muji alkhairi.."
Bata d'auki dogon lokaci ba ta fito,nan a bakin rijiya ta zauna tana nad'e hannun rigarta da niyyar yin alwala
"Inna.. Kinga mun jima ko.."

"Ehh! Mamana nima nan har na fara tunanin anya bazan bi sahunki ba,sai naji shigowarki.."
Murmushi tayi sannan ta ci gaba da magana
"Ai Inna in baki labari ko,, har mun fito daga makaranta bayan mun karb'o takardun da nace zanje na anso,,sai naji labarin wai gwamnati tana neman masu credit 9 a jarabawarsu,,to shi ne dai nima da naga duka na samu,sai banyi jinkiri ba na bada nawa takardun a inda akace akai.. Kuma kin san me ya faru Inna da muka kai..??"
Inna daga cikin kitchen ta amsa da
"A'a.. Ina ni kuwa zan sani al'halin banji wani yazo min da irin maganar ba.."

"Uhhuumm.. Inna cewa akayi gwamnati za tayi sponsoring d'inmu zuwa k'asar waje karatu.."

"Ke mamana bana son wasa fa.."

"Allah Inna da gaske babu wasa."
Shiru Inna tayi tana nazari zuwa wani lokaci ta furta
"To mamana Allah yasa haka d'in ne.."

"Ameen" ta amsa ma Inna,kafin ta sake magana
"Umm! Inna. Nace ba.. Shin zaku amince kuwa na tafi wani gari karatu..!?"
Har Inna za tayi magana nan take sai maganar baffa ya fata dawo mata
_"MAIRAMU..! Wane ne zaiyi tafiya a cikinku,,Mijinki ko y'arki ko kuma ke.??"_
Shiru tayi tana tunani a ranta
"Shin wannan itace tafiyar da baffanta yake nufi ko kuwa...?"





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*31.*
_#Her first trip_

Can k'asan ranta ta yiwa kanta tambayar,buh babu wani a kusa da ita da yake jinta bare ya fidda ita daga duhun data shiga,,jin yadda Inna tayi shiru take ya haddasawa Sabina mummunar fad'uwar gaba mai tsanani,still duk da hakan ta mak'alawa ranta dauriya gami da k'arfin hali,yadda Inna tayi zugum tana kallonta ba tare data ce mata komai ba yasa jikinta sake yin sanyi,a hankali ta sake d'ago kanta ta kalli Innar muryarta cike da fargaba
"Inna..! Dan Allah kiyi hak'uri,, wollahi ban san ranki zai b'aci akan maganar nan ba,tun farko ma da ban fara bada takarduna ba,,dama ni ban riga na sawa raina zanje ba,kawai dai dalilin da yasa na kai takardun ina da sa rai ne akan ko da ban samu an tura ni wata k'asar ba,ace na samu dama gwamnati ta d'auki nauyin karatuna a cikin k'asata,kinga kenan zanci gaba da zama tare da ku ba tare da fargabar wani abu zai faru da ni ba,,nd kuma hankalinku zaifi kwanciya akan ace nayi nisa.!"

"Waye yace miki baza mu amince ba..? Mamana karatu a duk inda kake sunan shi karatu,imma a cikin k'asa ko a wajenta duka d'aya ne,,a duk inda kake Allah shi yake karewa kuma yake tsarewa,dabarar mutum ko k'arfinsa bai isa ya hana Allah ikonsa ba,tsakaninmu da ke addu'ah ce da fatan Allah ya baki ikon kiyaye dokokinsa akanki.. Sabnan tarbiyyar da muka yi shekaru muna gina rayuwarki akai,muna fatan babu wani kyale²n duniya da zai rud'e ki har ya lalata mana ita,,in dan Allah ya tsara tafiyarki mu bamu isa mu hana hakan kasancewa ba,,kada kiyi tunanin baza mu iya yarje miki tafiya ba tare damu ba,a duk inda kike addu'ar mu zata ci gaba da riskarki,mun yarda dake kamar yadda muka tabbatarwa kawunanmu baza ki tab'a bamu kunya ba..Idan wannan damar ta samu muma masu yin alfahari ne da duk abunda zaki zama a nan gaba,,kiyi tafiyarki kinji ko,,kada ki ce saboda wani dalili zaki fasa,da yardar Allah zaki kasance cikin masu nasara..!"
Kuka ne ya fara taho mata da sauri ta sakko daga gefen rijiya tayi zaman dirshen a k'asa
"Na gode Innata,,Ubangiji ya dubi bayanku,,in sha Allah kamar yadda kuka d'auki yarda kuka bani,da yardar Allah ba zan tab'a baku kunya ba.. Zan kasance mai kulawa,tare da takatsantsan da duk inda na samu kaina.."

"Allahu ya baki iko.. Ya kuma karemin ke a duk inda kike.."

"Ameen Innata.. Ina rok'on ubangiji yayi muku tsayin rai,,domin kuyi alfari da samuna matsayin y'a.."

"To Ubangiji ya amince.."
Da "ameen" ta amsa sannan ta mik'e daga inda take zaune ta koma saman gefen rijiya tana sharce hawayenta,sauri² tayi ta d'aura alwala,sannan ta nufi hanyar d'aki.

Duka da yin maganar kwanaki biyu,gwamnati ta fara neman duk wad'anda suka kai takardunsu domin tantancewa,kasancewar Sabina bata saba sauraron radio ba yasa ko da aka sabar sai bata samu labarin ba,,yadda tak'i jinin sauraren radio yasa a mafi yawan lokaci ko Baba ya kunna matuk'ar tana zaune barin wajen take,shi yasa sai bata sani ba,Inna kuma ko da taji lokacin da Baba ya kunna radio dare ya riga ya fara nisa,nd lokacin tana da yak'inin a Sabina ta jima da yin bacci,shi yasa ma ko tunanin sanar da ita tun a daren bata yi ba,ta bari akan zuwa da safe suyi maganar,,lokacin bayan sun gama sauraren labarai,Baba yana shirin kwanciya Inna ta kalle shi,duk da tana fargabar fad'a masa,amma wani sashi daga zuciyarta yana fad'a mata ta sanar masa,ba tare data yi jinkiri ba tayi amfani da damar data samu tayi masa bayanin duk abunda yake faruwa,,da fari an so kai ruwa rana dan Babah,dan ya gwada k'in amincewarsa da tafiyar Sabina wata k'asa da sunan karatu,,amma ko da Inna ta fayyace masa yadda suka yi da Baffanta,sai yayi shiru bai sake yin magana ba har tsayin wani lokaci,,Inna kuwa ko da taga haka gaba d'aya cikin zuciyarta sai taci gaba da addu'ah akan Allah yasa kada ya kafe akan maganar da yayi na farko,,tana cikin tunanin maganganun baffa,ta jiyo maganarsa yana amsawa akan ta fara zuwa goben taji kiran da ake musun,zuwa dare idan ya dawo zai zauna dasu duka bayan yayi shawara akan tafiyar ko akasin haka,,sosai Inna ta fara murna bcos ta san tunda yayi wannan maganar baza'a sha wahala ba sosai gurin amincewarsa,wannan dalilin yasa ta k'udurce jajircewa wajen ci gaba da addu'ah har Allah yasa ya amince.
Ga Baba kuwa deeply tunda ta sanar dashi yake sak'a abubuwa da dama akan maganar,buh abunda yafi kwanta masa a rai gane da naganar shi ne furucin baffa,kan haka shima ya k'udurce a ransa zai jajirce yayi istikara domin nema musu mafi alkhairin zab'i agurin ubangiji,wannan yasa shi jinkirtawa bai riga ya yanke hukunci kai tsaye ba.

Washe gari da safe tana kwance tana bacci Inna ta lek'o d'akin da niyyar sanar da ita abunda ke faruwa,tana shigowa ta tarar da ita kamar yadda tayi zato,tashinta ta fara yi cikin farin ciki ta bata umarnin tayi maza ta shirya,kallon Inna ta tsaya yi,tunani daban² suna kawo mata farmaki a rai
"Mamana lafiya kike min irin wannan kallon..?"
A hankali ta janye idanunta tana kallon gefe
"Inna ina zanje da wannan safiya kike cewa na shirya..??"
Murmushi Inna tayi mata mai kyau
"Ya Allah..! Ashe fa baki san da batun ba ko..? To maza dai kiyi sauri kada lokaci ya tafi,ana can ana

Please Login or Register in order to submit comment