Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gare ni,tabbas YAYANAH zuwan ka gare ni yasa ka zamo min wani jigo na d'orewar farin ciki a zuciyata.A kullum tun daga lokacin da muka fara had'uwa da juna fuskar ka ce kad'ai abunda nake kallo na samu farin ciki.Kada ka damu da rashin bayyana maka gaskiyar *AL'AMARI* na da banyi ba tun a baya,,amma a yau kuma a ranar da nake jin babu dad'i sakamakon rabuwar da zamuyi yasa ni jin bazan iya sake b'oye maka wannan sirrin ba,shi yasa kai tsaye nake sanar da kai abunda ke k'unshe cikin zuciyata,,duk da bawai ina cikin yanayin jin dad'i bane,ina son furta maka cewa INA SON KA! INA SON KA!! INA SON KA.!!!"

Wani irin murmushi yake saki mai tattare da shauk'in jin irin kalaman da take masa amansu,tunda yake tare da ita kusan sai yace yau ne rana ta farko da yaji kalamai makamantan wad'annan sun fito daga bakinta,,shin shi kuwa me ya kamata yayiwa Allah baya ga yayi ta godiya a gare shi bisa tarin ni'imomin da yayi masa.!? K'ura mata idanunsa yayi yana kallo kamar bazai daina ba,yana shirin sake yin magana sai ga Hamudan ya shigo cikin d'akin kamar wanda aka cillo da fad'in
"Yaya wai baffa yace lokaci yana k'urewa.. Kuma wai an fara kiran sallah.."
Saurin dawowa hayyacinsu suka yi,a hankali Sabina ta janye hannunta dake mak'ale a nasa ta matsa gefe kad'an tana k'urawa tafin hannun ido,sai daya kalleta sannan ya amsawa Hamudan
"Ok.. Kace da baffa yanzun zan fito..In sha Allah.."
"Toh" ya amsa sannan ya fice a guje dan isar da sak'o,mik'ewa tayi tsaye ta wuce gaba,tana niyyar fita ya dakatar da ita ta hanyar kiranta,cak ta tsaya sai dai bata yarda ta juyo ba,handkey dake aljihunsa ya zare a sannan ya zagayo ta gabanta,a hankali ya kamo hannunta ya shiga d'aure mata inda ta yanka,yana gamawa ya juya zai bar wajen ta rik'o masa hannu,a hankali ya juyo yana kallonta,d'an kwalin dake kanta yaga ta zame sannan ta d'ago hannun tana d'aure masa had'e da yi masa murmushi,shi kam kallonta kawai yake dan idan da ace labari ne ake bashi tsaf zai musanta,amma sai gashi ya gani a zahiri,,saida suka sake d'aukan mintuna ak'alla uku suna ma juna wani irin kallo mai kama dana *BANKWANA* irin na har abada,kafin suka fito kowanne sai b'oye hannu yake yana gudun aga abunda yake jiki,,a lokacin kusan zan iya cewa ya wuce a kira yanayin da yamma dan yadda Maghreb sosai ya kawo jiki,ko data raka shi iya karta zauren gidan ta tsaya suka sake yin sallama a karo na sau babu adadi ya barta akan sai yazo ziyartar su,,daga nan ya juya ya fita yana waiwayenta,,itanma kasa barin gurin tayi har sai data ga sun d'auki hanya,duk da haka bata hak'ura ba,sai data sake mak'alewa a zauren gidan tana lek'ensu,ba ita ta koma cikin gida ba har sai data daina hango su,a lokacin ne kuma wani irin kuka mai tattare da k'unci ya taho mata dan yadda take jin jikinta na bata kamar shi kenan daga wannan lokacin sun rabu kenan bazata sake ganinsa ba,da gudu ta koma cikin gida duk da yadda take k'ok'arin had'iye kukan,tun kafin ta kaiga k'arasawa tuni har kukan ya kwace mata.

A b'angaren su Hammad kuwa lokacin daya fita daga zauren,zazzaune ya tarar da su baffa suna jiran fitowarsa,lokacin ko kafin suyi sallama sai da yayiwa dattawan da suke tare alkhairi,sannan ya buk'aci ganin waliyyansa a keb'e,,yayi musu godiya akan alkhairin da suka gwada masa sannan suma yayi musu hasafi fiye dana sauran sannan suka yi sallama da shi,a lokacin kuma zak'in alkhairinsa yasa d'aukacin mazauna gurin suka shiga binsa da addu'o'in fatan alkhairi da sauka lafiya.Sannan suka d'auki hanyar raka shi,sun fara tafiya sai ya waiwayo ya kallo k'ofar gidan kamar wancan lokacin daya gabata cike da k'awa,,a lokacin tana tsaye tana hangensu,,shima ko daya kallo gurin zuciyarsa cike take taf da fatan ubangiji yasa idan ya tafi nan da wani d'an lokaci ya dawo zuwa ga abar k'aunarsa sannan ya juya suka ci gaba da tafiya,yayin da yake jin zuciyarsa cike da wani irin matsananciyar fad'uwar gaba,hannunsa ya d'ora dai² saitin zuciyansa ya dafe yana karanta duk addu'ar data zo bakinsa,a haka har suka fito titi inda yake barin motarsa,har bakin mota sai da suka rakashi,backseat na motan ya bud'e ya fito musu da kayan dake ciki,sannan ya dank'a sak'on *ABAR KAUNARSA* a hannun baffa,duk dama dai da fari kamar baza su karb'a ba,amma ganin irin magiyar da yake yi sai yasa suka karb'a,suka yiwa juna godiya sannan suka yi bankwana ya kama hanyar tafita suma suka kama hanyar komawa cikin k'auyensu..

Tun daya daidaita kan motarsa a bisan asphalt (kwalta) ya shiga shek'a gudu ba na wasa ba,kasancewar titin babu yalwar motoci bare cunkoso yasa kafin awa guda sai gashi ya iso cikin gari,lokacin daya shiga gida tun kafin yayi parking sai daya fara bin carports d'in da kallo,cike da farin cikin samun nasarar ganin babu motar Daddy yayi hamdala sannan ya gyara parking ya fito,,a gurguje ya haura sama ba tare daya tsaya bin d'akin Mammansa ba dan lokacin daya fito bai tsaya sallah a wudil ba ya taho,nd yanzun kuma tuni aka idar da sallah,bai iske kowa a parlor'n ba dan haka direct ya wuce bedroom d'insa,tun daga shigarsa d'akin ya tabbatar da lallai akwai wanda ya shigo,dan yadda ya fita ya bar shi ba haka d'akin yake ba a yanzun,saman resting chair daya jibge outfit,luggage's da duk wasu muhimman kayan da zai tafi dasu ya sake kalla,babu komai a gurin ko ina a tsaftace kamar ba'a shigo ba,hatta da handkey bai samu a yashe a gurin ba,gefe inda luggage's d'in suke ajiye ya sauke idanunsa a hankali ya saki ajiyar zuciya sannan ya tasamma hanyar toilet,a gaggauce yayi wanka bayan ya d'auro alwala ya fito,sai daya fara gabatar da sallah sannan ya fara shiri,within a few minutes tuni har ya kammala,landline dake cikin d'akin yayi kira dashi,bayan an d'auka ya sanar da mai maganar yazo ya fitar masa da kayansa,cikin girmamawa aka amsa masa sannan ya ajiye ya fita,bedroom d'in Mamma ya wuce,a lokacin itama bata jima da idar da sallah ba,tana zaune saman pray mat tana addu'ah ya shigo da sanyin jiki,daga gefenta ya samu guri ya zauna yana jiran ta idar suyi sallama,a gaggaucen itama ta k'arasa addu'o'in sannan ta waiwayo gefen da yake
"Son..Tafiyar ta tashi ne..!?"
A hankali ya jinjina kai sannan ya bud'e baki da kyar ya ce
"Ehh! Mah.."

"To..! Sai muce Allah ya tsare,ya bada nasara cikin abunda za'a je nema,,ubangiji ya k'ara kare min ku baki d'aya,,sai dai ina so a koda yaushe nasihata ta kasance itace abun tunawarka,a kullum ina maka nasiha akan ka kasance mutum na gari wanda ba iya mu da muka haifeka ba,al'ummah gaba d'aya za tayi alfahari da kai,,ka kasance mai kiyaye dokokin Allah a kanka,duk abunda kasan ya sab'a dokar mahaliccinmu ka zama mai guje masa,,sannan kada ka manta irin rayuwar da kayi a baya,wacce dukaninta kayi tane a cikin yarenka,k'asar ka kuma cikin jama'arka duk da akwai wad'anda addininmu ya bambanta da su amma ba kamar inda zaka je bane,yanzun a tafiyar da zaka yi zaka had'u ne da jama'ar da fiye da rabinsu addininku ya bambanta,,sab'on Allah a gurinsu basu d'auke shi a bakin komai ba,ina horonka daka kasance mutum mai tsare kansa daga dukkan abunda kasan ubangiji zai yi fushi da kai,,,a k'arshe ina sake yi maka nasiha daka kasance mai yawan jin tsoron Allah,sannan ka kiyaye lokacin ibada,in sha Allah nasara tana tare da kai..Allah ya dawo min da kai lafiya..!"
Jikinsa yayi mugun sanyi da nasihar Mamma,a hankali sai ya bud'e bakinsa
"Ameen Mah.. Na gode sosai da nasihar ki,,,in sha Allah kamar yadda kika sanni,zanci gaba da kasancewa haka har k'arshen rayuwa,ina fatan za kici gaba da sani cikin addu'o'inki,,kamar yadda nake yi miki fatan Ubangiji yayi miki tsayin rai mai amfani.."
Tafiya dai kamar Hammad bazai yi taba a wannan daren dan yadda aketa sallama,,lokacin ko da zai fito tare suka fita duka gidan,Mamma,Bassam da BADRA suka masa rakiya har airport Daddy ne dai da baya garin,,duk abuda za'ayi a kan idanunsu aka gama masa komai aka fara kiransu,jikinsu duka a mugun sanyaye ya rungume y'an k'annensa sannan ya juya ya tafi,a tak'aice dai suma kansu su Mamma'n basu suka koma gida ba sai da suka ga shigarsa cikin ad'd'a'irah (jirgi) sannan suka koma suna masu binsa da addu'o'in fatan samun nasara,haka nan jikinsu duk a sanyaye..

Lokacin daya tsinci kansa a gaban jirgin da zai nisanta shi da k'asarsa a karo na farko a rayuwarsa tun bayan fara soyayyar sai ya tsinci kansa cikin wani irin kasalan da bai tab'a tsintar kansa a cikinsa ba,duk da ba yau ne karon farko daya fara shiga jirgi ba,amma yau sai yake jinsa a damuwa,dan haka da kyar ya shiga d'aga k'afafunsa ya fara taka stairs d'in jirgin,yana tafe yana waiwayen bayansa ma'ana k'asarsa yayin da yake jin kewar tafiyar da zaiyi ya bar duk wani abu nasa mai muhimmanci,lokacin daya je k'arshen matakalar tsayawa yayi a bakin k'ofa ya kasa shiga,ak'alla sai daya d'auki tsayin minti guda yana kallon k'asa ba tare daya wuce ciki ba har sai da wanda yake bayansa yayi masa magana sannan ya d'auke idanunsa a hankali ya juya zuwa ciki,shigarsa a cikin jirgin babu jimawa ya fara duba seat number d'insa yana tafiya yana duddubawa har ya kaaiga inda idanunsa suka nuna masa 9c,hamdala yayi ga ubangiji sannan ya matsa,yana niyyan wucewa ya zauna sai yaji an tab'a shi ta baya,cikin nutsuwarsa ya waiwaya bayansa cike da son ganin waye ya tab'a shin,idanunsa suka yi arba da......




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*Ku k'ara hak'uri fan's,,kwana biyun nan ina fama da ciwon ido,shi yasa na rage yawan posting akai²..Buh in sha Allah idan naji dama sosai komai zai tafi dai² da yardar Allah.*

*23.*
_#Disasters_

Sultan ya gani tsaye a bayansa yana masa murmushi,kallonsa kawai ya tsaya yi kamar wanda bai gane shi ba,ko kuma irin sabon kamun nan a cutar makanta haka yayi ta kallonsa har na tsayin lokaci,kafin ya janye idanunsa akansa yana tab'e baki,tabbas zuwa yanzun kam ya fara tsinkewa da lamarin Daddy'nsa,sannan kuma sai yanzun nema ya fara k'ok'arin gano ma'anar had'a su tafiya da Sultan amma kuma aka b'oye masa,shin mene ne ma'anar k'in fad'a masa tare zasu tafi..!? Blazer dake rataye saman shoulder d'insa ya sauke sannan ya wuce ya zauna a seat d'insa ba tare daya cewa Sultan d'in ko da ci kanka ba,murmushi shima Sultan d'in ya saki bayan ya zauna kusa da shi yana fad'in
"Man..! Ko darajar magana ma bazan samu ba..!?"
Bai kalleshi ba ya fara k'ok'arin d'aura seat belt bcos a lokacin an fara sanarwa kowa ya zama ready jirgi yana niyyan tashi,sake tambayarsa Sultan yayi dai² lokacin yana jingina bayansa jikin seat,still ya sake yi masa banza saima rufe idanunsa daya sake yi saboda wani haushin Sultan d'in da yake ji,bakinsa d'auke da addu'ah ba tare daya tanka masa ba har jirginsu ya d'aga zuwa *U.S.A..*

A can k'auye kuwa lokacin ko da su baffa suka koma Sabina bata san dawowarsu ba,dan tunda ta shiga d'aki ta kife tana gama koke²n bacci ya d'auke ta,da yake kuma tana fashin sallah sai abun yazo mata a dai²,ba ita ta farka ba sai tsakiyar dare misalin k'arfe sha biyu,yadda garin yayi shiru baka jin hayaniyar komai yasa ko data farka sai ta fahimci dare ya soma yin nisa,a hankali ta tashi ta lallab'a zuwa bayan gida ta sake gyara jikinta sannan ta dawo ta kwanta,duk da a lokacin baccin ya sake ta haka ta kwanta shiru yayin da damuwa ta sake bijiro mata,addu'ah taci gaba da yi zuciyarta cike da fatan ya dawo gareta cikin k'oshin lafiya.
Da safe kuwa ko data tashi nanma basu samu had'uwa da baffa ba dan tuni suka fita gona,haka gaba d'aya yinin ranar da ciwon kai ta yishi kasancewar kwana da tayi tunani baya ga kukan da tayi,,ba ita taga baffa ba sai yamma sosai,shima ko da suka gaisama shaf baffa ya manta da sak'on da aka bashi ya bata,,cikin kwanakin gaba d'aya duk da baffa yana ganinta sam sai bai tuna ba har aka deb'i kusan kwanaki hud'u da tafiyarsa sannan ya tuna ya bata,lokacin data nunawa Innarta kayan daya aiko mata bata ce komai ba,kasancewar dama ba mai yawan magana bace musammanma akan wannan lamarin da idan ta cika magana za'a ga baikenta,duk da cewa ta samu labarin duk abunda ya faru a bakin Baban ita Sabinar amma shi d'inma sai bata tanka masa ba tayi dai fatan alkhairi a lokacin daga haka kuma taja baki ta b'ame,,sai addu'ah da taci gaba dayi akan Allah yasa a wanye lafiya,,a haka kwanaki suka ci gaba da tafiya.

*U.S.A FLORIDA STATE..*

A can k'asar amuruka kuwa tun bayan lokacin da suka sauka misalin k'arfe 8:00am a agogon 9ja,koda suka fito daga airport cab suka samu da zai kaisu cikin school,ba tare da b'ata lokaci ba suka d'auki hanya mafi sauk'i da zai kaisu *Jacksonville* wanda a nan ne skul d'in da aka nema musu take,har cikin skul d'in *University of North Florida* duk tsayin wannan uban tafiyar da suka kwaso tun daga 9ja zuwa U.S.A har a lokacin duk iya nacin da Sultan ya gwadama Hammad da son sai lallai ya kula shi,amma sai gogan ya d'auke masa wuta,kallonsa ma yak'i yi bare ya samu arzik'in akula shi,a hakan har suka shiga room d'insu kowa ya samu guri ya ajiye kayansa.
Gefen bed ya samu guri ya fara ajiye blazer d'insa dake mak'ale a hannunsa,bayan ya gyara zaman luggage's d'insa ya dawo ya zauna yana kallon blazer d'in dake gefensa,kamar wanda ya tuna da wani abunsa mai matuk'ar muhimmanci ya saki sanyayyar ajiyar zuciya sannan a hankali yasa hannu cikin aljihun rigan,head tie d'in data d'aure masa hannu ya zaro ya zubawa ido har na tsayin lokacin da shi kansa bazai iya tantancewa ba,kafin ya kaishi jikin fuskarsa yana lumshe ido,ya d'auki lokaci yana ta tunanuka iri daban² kafin ya maida shi cikin rigan ya mik'e yayi shirin wanka.
Bai wani d'auki dogon lokaci ba ya fito,har ya fara shirin kwanciya aka yi knocking door d'in room nasu,juyawa ya fara yi ya kallo k'ofar kafin ya kalli inda sultan yake zaune da waya a hannunsa yana ta latse²,sake kallon k'ofar yayi bayan ya ja dogon tsaki sannan ya nufi k'ofar bcos shi a tsarinsa bai cika son takura ba musamman idan yana tsaka da son ya kwanta,d'agowa sultan yayi ya raka shi da ido dan sarai yaji kuma ya ga duk abunda ya farun hatta da kallonsa da Hammad d'in yayi kafin ya tafi bud'e kofar,wanda a tunaninsa yayi tsammanin Sultan d'in zai mik'e da niyyar bud'e k'ofar,sai kuma yaga hankalinsa duka ya ta'allak'a kan waya,tab'e baki yayi sannan ya sake maida kansa akan phone d'insa ba tare da damuwar komai ba,,shima Hammad d'in ko daya je gurin bai tsaya tambayar waye ba kai tsaye ya bud'e k'ofar,,matashin saurayi ne tsaye a gurin rataye da rucksack a shoulder d'insa sai luggage's dake gaban k'ofar,,murmushi yayima Hammad daya bud'e k'ofa yana fad'in
"Hi dude..! How fa..?? Am Sadeeq.."
Ba tare daya tsaya jin k'arshen jawabinsa ba ya juya a hankali ya sake tab'e baki bayan ya gama k'are ma guy d'in kallo,bai iya amsa masa maganar da yake ba sai dai ya mik'a masa hannu kamar yadda Sadeeq d'in yayi nufin suyi musabaha sannan ya juya zuwa ciki abunsa,a baya Sadeeq d'in ya biyo shi while yana fad'a masa shi ne d'aya daga cikin abokan zamansa tunda a lokacin baiga Sultan ba,bai tanka masa ba dan yadda zuciyarsa ke cike da damuwa ji yake duk duniyar tayi masa d'umi,a haka har suka iso tsakiyar room d'in wanda sai anan ne Sadeeq d'in yaga Sultan,waving yayi masa yana sakin fuskarsa,cikin fara'a yayima Sultan magana da harshen nasara,da harshen hausa Sultan ya mayar masa bcos ya fahimci duk inda Sadeeq d'in ya fito baya rasa samun nasaba da *AFRICANS* suma d'in y'an 9ja,ko da jin yayi masa magana cikin yarensa nan da nan Sadeeq ya sake matsawa kusa da shi sosai cikin farin cikin samun d'an uwa da suka fito k'asa d'aya ya zauna a gefensa yana fad'in
"Broah..! Ashe kaima kana jin hausa,wollahi banyi tunanin zan samu y'an k'asar mu ba a nan.."
Murmushi sultan ya fara yi masa kafin ya bashi amsa
"Sai gashi kuma ka samu an had'a ka room gudama da jinsinka.."
Dariya yayi masa da fad'in
"Wollahi kuwa..Ai ba k'aramin murna nayi ba da Allah ya had'a ni da kai..Kaga na samu d'an uwa ba,,nasan dai in sha Allah babu abunda zai dameni ko ya shige min duhu..To amma nace ba..??"

"Uhhuumm..! Fad'i mana ina sauraronka.."

"Shi wancan amma ba d'an k'asar mu bane ko..??"
Murmushi sultan ya sake yi da fad'in
"Me ka gani ne yasa ka fad'in haka..!?"

"Ehh! To naga baiyi min kama da y'an nahiyarmu ba ne..Allah sa dai ba..!"
Duk maganar da suke yana jinsu, kasancewar ya juya musu baya a lokacin ko da yaji suna maganarsa baisa ya juyo ba bare ya kallesu,har ya gama abunda yake yi,sannan ne ya d'an waiwaya a hankali ya bisu da kallo,,har Sultan ya bud'e baki zaiyi magana ganin Hammad yana kallonsa sai ya fasa,yana dariya k'asa² ya maida kallonsa kan Sadeeq dake gefensa,saman kafad'arsa ya d'ora hannunsa yana sakin murmushi
"Uhhuumm..! Kasan matsalar su irin wad'annan mutanen masu jan kunne dama ba sosai suke sakin fuska ba,idan ka gansu yadda kasan shanu haka suke gurin had'e fuska..Ko da yake share kawai idan ya gama shan k'amshin zai neme mu ai.."
Murmushi Hammad yayi mai d'an sauti yana gyara tsaiwarsa sai dai bai ce komai ba,kallonsa Sadeeq yayi da mamakin ganin yana murmushi sannan ya sake kallon Sultan
"Broah..! Anya kuwa baya jin me muke fada,,naga yana dariya fa..Kada muje muyi shuka a idon makwarwa.."
Bubbuga kafad'arsa Sultan yayi cikin sigar kwantarwa da Sadeeq d'in hankali yana fad'in
"Manta kawai Man..Ka san wani lokacin suna d'an tsarguwa duk da baji suke ba,amma dan su nuna maka suna ji sai yasa su dinga maka acting as suna fahimtar ka,,,kuma fa duk bogi ne.."

"Allah ko aboki..!?"

"Aaa! Sosai ma kuwa.."

"Toh ai shi kenan,,ka k'ara min karatu yau.."
Mik'ewa yayi shirin yi domin ya gyara nasa kayan ya jiyo kamar muryan Hammad yana fad'in magana cikin yaren da baiyi tsammanin yana ji ba,da sauri sai ya d'ago ya kalli Sultan
"Friend..! Kace baya jinmu..!?"
Dariyar mugunta Sultan yasa yana kwanciya a saman bed d'insa
"To kai in banda abunka kawai dan na fad'a maka magana sai ka yarda..Bayan nima a nan na ganshi..!?"

"Ta yaya ne to ni bazan yarda ba.?? Tunda dai tare na zo na ganku.."

"Uhhuumm..! To ai sai ka hanzarta yin abunda yake gabanka ko kada ka b'atawa kanka lokaci.."
Yana magana yana dariya k'asa²,,girgiza kai kawai shima Sadeeq d'in yayi sannan ya d'auke rucksack d'insa daya ajiye ya bar kusa da Sultan,dan a yadda ya fara fahimtar sa yana da mugun son wasa nd yana ganin idan har yaci gaba da zama kusa da shi tofa yana daf da sashi ya aikata abunda zaiji kunya.Ga Hammad kuwa harya gama shirin kwanciya lokacin guda yaji baya ra'ayin yin hakan,nan da nan sai ya sake canja akalar shirinsa,har ya gama shiryawa babu wanda yayi masa magana sai daya zo fita,yana daf da k'ofar fita sannan Sultan ya kalle shi yana fad'in
"Broah..! Ina zaka je ne..!?"
Bai juyo ba bare ya kalle shi yaci gaba da tafiyar sa while yana fad'in
"Ka aike ni ne..!?"

"Ba saina aike kane zan tambaya ba,,,nd garama ka daidaita kanka da nutsuwarka,idan ba haka ba kuma..!"
A fusace Hammad ya waiwayo ya kalleshi dan dama a ciki yake da shi
"Idan ba haka bafa..!?"

"Zanyi waya na sanarma da Dad.."
Ajiyar zuciya ya sauke yana girgiza kai,cikin wani yanayin takaici mai tattare da rashin tsoro yace
"Kada ka fasa..Kai baka san tuni na jima da sanin duk abubuwan da kuke k'ullawa bane,,dan kayi masa waya kace na fita shi ne me..?? Duk abunda kuke yi ina sane,sannan na sani cewar Daddy ya jima da saka ka dunga bibiyana.. So yanzunma kana da dama ka kira ka fad'a masa na fita bayan nan kuma saika bini a baya kaga inda zani.."
Yana fad'in haka ya fice a fusace ya bar musu d'akin,,yana fita da sauri Sadeeq ya waiwayo ya kalli Sultan,gane abunda yake nufine yasa da sauri Sultan ya janye idanunsa nd yana had'e rai danma kada ya tambaye shi wani abu game da alak'ar su shi da Hammad.

A b'angaren Hammad kuwa lokacin ko daya fita a room d'in yana tafe yake neman wayan Mamma,bayan sun gaisa ya tambayeta su Bassam,,a nan nema har ta samu ta sake yi masa nasiha sosai sannan suka yi sallama,,daga nan kuma sai ya nausa cikin skul yana d'an zagawa da kallon tsarin gurin,duk da su a lokacin dare ya fara yi amma akwai yalwar mutane tamkar da ranakowa sai sabgoginsa yake babu ruwan wani da wani,sai daya ga gurare da dama sannan ya kama hanyar komawa d'akin su dan yayi alwala,kasancewar lokacin sallar Isha yayi,ko da ya gabatar da sallah nan ya haye saman gadonsa yayi kwanciyarsa zuciyarsa cike da tunanuka iri daban²,lokacin da su Sultan suka yi niyyar fita kuwa ko da suka masa magana yazo suje su samu abinci,k'in kulasu yayi har suka gaji suka tafi,suna tafiya ya sauko ya bud'e blazer d'insa da d'ankwalinta ke ciki,fuskarsa ya rufe da shi zuciyarsa da tunanin ko zai iya samun bacci idan yayi hakan..

*SOME MONTHS LEAVE..*
Yanayin zafi ya tafi,,yayin da damuna ta kawo jiki sosai,a wannan lokacin ne kuma duk wani mutumin da yasan yana da gona zaka ganshi yana ta kimtsawa,yayin da wasu kuma sukan bada hayar gonakin,,idan kuwa har aka ce mutumin k'auye ne tofa zaka tarar da shi yana hada²r yin noma da kansa.
A mafi yawancin ranaku tunda damuna ta fara kamawa kusan kullum ne sai ka iske anyi ruwa a y'an kuna da dama.Yau ma d'in tunda aka tashi garin yake ta had'uwa da wani irin black cloudy wanda har yamma yini sur garin

Please Login or Register in order to submit comment