Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

cikin kwanakin dan suyi maganar amma sam ta kasa samunsa.
Har dare ya fara rabawa hankalinta yana kan taga ta same shi amma abu ya faskara,,bisa dole ta hak'ura,ko data duba time taga zuwa lokacin zaiyi ace su Badra sun sauka,sai tayi k'ok'arin kiran nata don taji ko sun isa lafiya,cikin sa'a nata line d'in tana gwada kiran ya shiga.

Su kuwa a b'angaren bak'in k'asar turawan a dai² lokacin a nasu k'asar lokacin tsakar rana ne,tun da suka iso room kowa cikinsu sai hada²r shirya kayansa yake,kiran Mamma ne ya shigo wayarta a time d'in suna ta hayaniya ita da Jannat,special ring d'in dake tashi cikin wayar ya tabbatar mata da Mamma'nta ce take nemanta,tsalle tayi daga inda take ta rarumo wayarta,dai² lokacin da take d'aukan wayan da fad'in
"Amincin Allah ya tabbata ga mahaifiyar da tafi kowace irin uwa a duniyata..!"
Murmushin jin dad'i Mamma tayi sannan ta amsa da
"My little kiddo,,fatan kun sauka lafiya..?"

"Lafiya k'alau Mammana..!"
Sunyi hira sosai da Mamma,dukansu suna cikin farin ciki da kasancewar kowannensu cikin aminci sannan suka yi sallama,har Mamma zata ajiye wayan Badra cikin ihu ta ce
"Mamma..! Pleasee! Kada ki ajiye waya,,ga sabuwar k'awata da nayi ku gaisa.. Mah! U know what..?"

"Ohhh.! My Kiddo yanzun daga isarku har kin fara k'awaye..??"

"No.. Mah.! Wannan she's so special,, tun a jirgi muka had'u,kuma itama y'ar Kano ce.."

"Ok.. Toh dai ku kula,ba kowa nake so kuyi abota da shi ba,,kinji ko baby..?"

"Toh! Mah,,in sha Allah,zamu kiyaye.."

"Yawwa to bani itan mu gaisa.."
Tana fad'in haka,Badra ta juyo inda su Sabina suke kowa da kaya a gabansa
"Hey..! Princess.. Ga Mamma na zaku gaisa.."
D'agowa Jannat tayi saurin yi daga kan kayanta tana fad'in
"Kaji rinto wai Mammanki,, Mamman Yah Hammad dai.."
B'ata fuska Badra tayi
"Allah babu wani nan,ai kowa yasan Mamma tawa ce,kuma nima tata ce.."

"Noo.! Madam da dai kince ke ta Daddy ce,zan yarda amma idan kince ke ta Mamma ce,fashi kawai zaki yiwa Yah Hammad.."

"Ke kika sani.. Ni ban san wannan ba.."
Ta mik'awa Sabina waya ta juya daga kusa dasu,,tunda ta karb'i wayan haka nan jikinta yake wani irin karkarwa kamar wacce ta kama wuta,muryarta tana b'ari tasa wayar a kunnenta tayi sallama,,a ladabce ta gaida Mamma,itanma ta amsa mata cikin sakin fuska da mutuntawa,har suka yi sallama sannan Mamma tace ta bawa Jannat waya jikinta bai daina rawa ba,tunda ta mik'a mata haka nan muryar Mamma sai amsa kuwa yake mata cikin kunne,tunaninta,kwakwalwarta da zuciyarta gaba d'aya suka tafi yajin aikin son tuno mata da muryan waye magabar wannan matar suke yi mata yanayi.

Bayan Mamma ta gama waya dasu tana cikin farin ciki sosai,haka nan itama tunda ta tuno shirmen Badra sai taji muryar yarinyar da suka yi magana ya tsaya mata a zuciya,tunani daban² suka fara zuwa mata a rai sai dai ta kasa bambance mene ne hakan yake nufi.

*NEW YORK CITY..*
Tunda ya shigo gidan a matuk'ar gajiye yake,cikin kwanakin gaba d'aya nutsuwar sa bata jikinsa saboda wani mugun bincike da suke kanyi na wani aikin da suke ta bincikensa.
Yana shigowa ya kunna wutar gidan sannan ya ajiye suit d'insa saman armchair ya nufi hanyar bedroom d'insa,,gidan flat ne sai dai tsarinsa akwai masifar kyau dan ya matuk'ar had'uwa kasancewar ginin turai ne,komai yana nan a muhallinsa,,bai d'auki dogon lokaci ba ya fito sanye cikin wani black d'in 3quarter sai short-sleeved t-shirt dake jikinsa,a ta gaban rigar anyi rubutu da white nd red colour da manyan harufa, *JUST DO IT* shi ne rubutun dake gaban rigar ya nuna,sai tick daya ratsa tsakiyar rubutu ma'ana btwn just nd do it,sosai yayi kyau a cikin kayan musamman daya kasancewar fari tas,,k'afarsa sanye cikin benassi slide sandals na maza yake takowa,kai tsaye ya wuce hanyan kitchen zuciyansa cike da nufin nemawa kansa abunda zai d'umama uwar hanjinsa.

Coffee kad'ai yayi ma kansa preparing sannan ya fito hannunsa da cup yana tafe yana sipping,har ya dawo parlor inda ya bar laptop d'insa da wayoyinsa,saman mini table dake gurin ya d'ora cup d'in sannan yayi operating na computer yana sake zurfafa bincikensa kan evidence da yake tarawa,gefe guda kuma yana ci gaba da had'iyan coffee har ya shanye tas,sannan ya sake maida hankali sosai kan aikin da yake yi d'in.

A hankali door bell yayi k'ara,d'agowa yayi da sauri ya kalli k'ofar kafin ya mik'e ya nufi k'ofan da shirin bud'ewa,,Sultan ya gani tsaye da uban luggage's d'insa,a hankali ya kauce ya bashi hanya,murmushi Sultan yayi sannan ya wuce ciki yana yin sallama,k'asa² ya amsa sannan ya sake binsa while yana tambayarsa bcos yana mamakin abunda ya gani
"Dude.. Wai dama nan suka dawo da kai..??"
Yana murmushi yake fad'in
"Ko kuma na nemi a dawo dani ba..!"
Fuskarsa da mamaki fal samanta ya kalleshi
"Ohh! Kai kace adawo da kai dama..??"

"Ehh! Na gaji da zaman kad'aici ne,shi yasa na nemi transfer."

"Ok.. Amma ni d'azun ai ba haka ka sanar dani ba."

"Yanzun kuma na fad'a maka yadda akayi ai."
K'wafa Hammad yayi sannan ya nemi guri ya zauna ba tare daya sake yin magana ba yaci gaba da aikinsa,,kallon gurin Sultan yayi sannan ya sake kallon shi
"Dude.. Wai babu wani abun ci ne a nan..?"

"Gashi nan ka fad'a.."
Slowly Sultan yayi tsaki sannan ya mik'e yayi hanyar fita,d'agowa yayi ya kalleshi sai dai bai ce masa komai ba har ya fice,shi kuma ya sake maida hankalinsa kan aikinsa.

*PENNSYLVANIA CITY..*
Tana daga kwance saman gadonta wayarta a hannunta tana y'an tunanukanta,bacci ya fara kawo mata ziyara,dama a gajiye take sosai,hakan yasa sai ta yanke shawaran yin baccin ko yaya ne tasan zata ji dad'i,a gefenta Badra ta zauna
"Princess..! Tashi muyi hira.."

"Sorry friend,,am already falling a sleep.. Bazan iya wani hira ba yanzun,,idan nace zan takura kaiba kuma shirmen ne kawai zanta fad'a.."

"D'azun baki yi bacci ba ne..??"

"Yeah..! Ai bana iya bacci a abun hawa.."

"Ok..! Yi baccin ki,,idan kin tashi ina da bashi akanki.. Kin yarda zaki biya..??"

Murmushi tayi mata idanunta a lumshen tace
"Yeah..! Na amince.."

"Ok..! Shi kenan,a tashi lafiya.."
Still ta sake yin murmushi sai dai bata ce komai ba saboda baccin da take ji,gashi zuwa lokacin har ya fara neman sa mata headache.

Mintuna sha biyar tsakani tuni bacci ya d'auke ta,kallonta Badra tayi fuskarta da murmushi ta juya tana kallon Jannat
"Dear.. Ki duba min nan.."
Wayan dake hannunta ta k'awar gefe da fad'in
"Mene ne..??"

"Ohhh..! Ke matsalar ki bakya saurin gane magana dole sai an yi miki fashin baki.."
Murmushi tayi cikin dariyar zolaya tace
"Kamar ke ba.?"
Harararta tayi za tayi magana Jannat ta dire akan gado ta nufi hanyar toilet,k'wafa tayi cikin k'unk'uni tace
"Zaki san dani kike,,kuma saina fad'awa Yah Sultan.."
Ita kam Jannat dariyama maganar ta bata,tana daga tsaye a bakin k'ofar toilet take fad'in
"Ohoo! Dai nima zan fad'awa Yah Hammad ya rad'amin.."
Jifanta tayi da flat sandal d'in k'afarta,suna cikin shirmen jifan juna akayi knocking k'ofar room d'in,a tare suka juya suna kallon k'ofar kafin su bada izinin shigowa.....



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*Sai kun k'ara hak'uri fan's,wollah kwanakin nan ina jin jiki,amma Alhamdulillah..! Yanzun kam,am stepping toward recovery,,godiya ta musamman ga masoya,da duk wad'anda suke aikomin da sak'onnin fatan alkhairi,ubangiji ya bar zumunci..🙏*

*33.*
_#Surprisal 2_

Sai da aka fara bud'e k'ofar d'akin,ko kafin mai shigowar ta bayyana sai data d'auki y'an mintuna sannan ta shigo cikin takun isa,kallon-kallo aka fara tsakaninsu da ita,ta d'auki lokaci tana kallonsu suma suna kallon ta,sannan tayi magana cikin wani yanayin da na kasa ganewa
"Hello..!"
Shi ne abunda ta fad'a,maimakon sallama da aka san duk wani musulmin k'warai da ita,daga haka bata sake cewa komai ba ta wuce tana jaye da luggage's d'inta da backpack goye a both shoulders d'inta,wani irin kallon raini Badra ta jefeta da shi ta kama waist
"Heeyy! Malama da Allah fita kiyi ma mutane cikakkiyar sallama,,ko an fad'a miki nan duka christians ne..? Zaki shigowa mutane guri da wani hello,,hello d'inki na banza,da kinsan baki yi ba ai kin shigo kai tsaye..!"
Dakatawa tayi da tafiyar da take tana sakin luggage's d'in,a hankali kuma ta waiwayo tana kallon Jannat data tsareta da ido,tunaninta duka a lokacin ya gama bata ita tayi maganar,muryan fad'a tayi wearing kan nata itama cikin masifa ta hayayyak'o mata kamar yadda taji anyi magana tun farko
"Bazan yi ba d'in,, sallama ko..?? Haka naga daman yi idan zaku amsa ne ku amsa,if not kuma kuyi shiru,ba lallai ne sai kun amsa ba,,nd daga yanzun duk lokacin dana shigo zanyi abunda naga dama ne,sai inga ta tsiya,,tunda ba a kan mutum zan zauna ba,sai ku samin ido.."

"Haka kika ce..??"

Juyawa tayi saurin yi zuwa inda ta jiyo maganar sannaan ta furta
"K'warai fa.."

"Fita to.. Ba'a nan room d'in zaki zauna ba.."
Kallon shek'ek'e ta yiwa Badra cike da rainin wayo tace
"Allah ko..?? Kece zaki hana ni zaman,ko kuma kinga an kafe hakan a allon sanarwa ne..??"

"Malama idan fa ba zaki mana sallama ba,wollah yanzun zamu watsaki waje da kayanki.."

"Da gaske..??"

"Ya isa haka Dear,,kyaleta kawai,bai kamata ma ace kin biye mata ba,duk da yin sallama ba wajibi bane,amma mu nan tunda ta shigo kallo d'aya zai bata amsar daga ina ne muka fito.."
Jannat da tunda bak'uwar ta shigo bata ce komai ba ta tofa nata
"Haba Lady..wannan ai iskanci ne ace mutumin da yake muslim,kuma cikaakken bahaushe ya shigowa mutane guri da wani hello,,ke dan Allah baki ji kunyar tozarta addininki bama..??"

"Kamar yaya kenan..?? Kinga nifa bana son shishshigi,, daga zuwa na zaki fara kawon k'abli da ba'adi,rayuwa ne kowa da irin nasa,so kowa yayi abunda ke gabansa,ina ruwanki da rayuwata..??"
Gyad'a kai Badra tayi cikin jin zafin maganar ta tace
"Amma dai kinji kunya wollahi,indai haka wannan tsarin kika zab'ar ma rayuwarki,kina cikin wani hali,,a matsayinki na muslim,har ayi miki gyara,amma ki danne ki shigo da son rai..?? Idan baki sani ba zan sanar da ke,idan kuma mantawa kika yi ni zan tunantar dake,,Annabi (S.A.W) cewa yayi a hadis:"Baza ku shiga aljannah ba har sai kunyi imani,kuma baza kuyi imani ba har sai kun so juna..Shin bana nuna muku wani abu da idan kun yi shi zaku so juna ba.? Kin san mene ne yace..??"

"Ku yad'a sallama a tsakaninku.."
Duka suka kalli juna da mamakin amsawar da tayi,,jinjina kai Badra tayi sannan taci gaba
"Sannan Ammar (R.A) yace:'abubuwa guda uku (3),wanda duk ya had'a su ya had'a imani.."
Kafin ta sake yin magana ta karb'a mata
"1-Mutum yayi adalci ga kansa,2-yad'a sallama a cikin jama'a,3-yin kyauta a cikin rashin wadata.."

"Sannan an karb'o hadisi daga Abdullahi Ibn Umar (R.A) yace:'wani mutum ya tambayi manzon Allah (S.A.W) wane abu ne a cikin musulunci ya fi alheri..?"

"Sai manzon Allah (S.A.W) yace:"Ka ciyar da abinci,sannan kuma ka yad'a sallama ga wanda ka sani da wanda baka sani ba.."
Badra cikin tsananin mamakinta ta fara tafa hannayenta
"Da kyau..! Wato da duk kin sani amma kika take..?? Shin mene ne fa'idar ki na shigowa ba tare da sallama ba.?? Kuma a mazaunin kina cikakkiyar musulma..??"
Kallon Badra ta d'anyi sai kuma ta sauke dogon numfashi,da fari yadda taji Badran na fad'in zasu watsata waje da kayanta har ta fara hasala,sai dai jin ta fara kawo mata hadisai take yasa jikinta yayi wani irin mutuwa,kallonta ta sake yi muryar ta cike da sanyi ta furta
"Am really sorry Sis.. Gaskiya ni kaina na ji kunyan abunda na aikata,buh na gode sosai da tunatarwan da kika min,,in sha Allah hakan bazai k'ara faruwa b.."

"Better..!"
Daga haka Badran ta juya tana tab'e baki ta nufi gefen bed d'inta,tana shirin zama bak'uwar tasu ta koma da baya,can bakin k'ofa ta tsaya,bayan ta kallesu duka ta furta
"Assalam alaikum warahmatullah wabarkatuh..!"
Ba tare data kalli inda take ba ta amsa tana had'e rai kamar wacce aka aikowa da sak'on mutuwa,kusa da ita ta k'araso cikin sauri tana mik'a mata hannu
"Am ZAINAB HARIS,,buh zaku iya kirana Zeeharis kamar yadda sauran k'awayena na secondary suke kira na.."
Sanin wulak'anci babu dad'i da fad'an da Mamma take yawan yi musu yasa Badra ta d'ago bayan sunyi shaking hand ta furta
"U are welcome.."
Har lokacin bata saki fuska sosai ba,yanayin ta yasa Zeeharis ta d'an tsaya jimm kafin ta furta
"Sister..! Kiyi hak'uri fa da abunda ya faru,naga kamar har yanzun duk da na gane KUSKURE NA,kamar baki karb'i hakan a matsayin KUSKURE ba.."
D'agowa tayi da kanta ta kalleta tana yamutse fuska
"Noo! Kada ki damu,,ya riga ya wuce,shi d'an adam ai aajizi ne,so.. Sai mu kiyaye faruwar hakan a gaba.."

"Yeah.! Haka ne,,na gode sosai da nunamin KUSKUREN na da kika yi.."

"Babu komai..!"
Murmushi tayi mai kyau har ta juya zata bar wajen kuma ta d'an dakata
"Buh..! Sis zan iya tambayar ki wani abu,Please..??"

"Babu damuwa,,ina sauraronki.."

"Daga wane k'asa kuke please..?"

"9ja.."

"Ohh! Kuma daga Kano kuke ne.??"

"Ehh.."

"Alhamdulillah..! Na samu y'an uwa,,amma zan iya sake tambaya..?? Idan babu damuwa.?"

"Babu.."
Duka amsoshin nata a tak'aice take yinsu kamar ana mata dole,amma sam basu sa Zeeharis jin babu dad'i ba
"Please..! Nace k'ark'ashin wane school za kuyi karatu ne..??"

"Law school.."
Ihun murna tayi wanda a sanadin yinsa ya farkar da Sabina dake bacci
"Ohhh! Yah Allah.. Kinga kin tashi baiwar Allah tana tsaka da bacci.."
Badra dake harhad'e rai ta fad'a tana kallon Sabina data gyara zama tana kallonsu,saurin juyawa Zeeharis tayi ta kallo inda Badran ke kallo,ido hud'u suka yi da ita tana kallonsu,a hankali sai ta kama kunnenta tana fad'in
"Yi hak'uri y'ar uwa,,ban sani bane,buh mujhe maaf karte.."

"Tofa.. Har da bak'in indiyawa muke da kuma.??"
Jannat tayi maganar tana jinjina kai

"Ke kam dai Lady yau gulma kike ji wollah,tun d'azun kina nan tsaye ke baki yi abunda za kiyi ba,nd baki bawa mutane guri ba.."

"Bazan yiba d'in,, ina ruwanki da ni..??"
Har ta juya zata shige wayar ta dake gefen gadonta ta fara kuka,duka ring d'in yasa su dakatawa daga musayan maganar da suke,a hankali ta dawo ta tsaya kusa da wayar,sai data fara lek'a fuskar wayar kafin ta d'auko tana fad'in
"Hello.. Yah Sultan na.."
Ko gaisawa basu kai ga yi ba,Badra dake zaune taji an ambaci Sultan ta taso a sad'ad'e tana zuwa dai² gurinta bata tsaya jira ba ta wafce wayan daga hannun Jannat ta bar gurin da sauri
"Hello.. Yah Sultan nah..! Hope kana cikin k'oshin lafiya.. Ya aiki..??"

Daga gefen Sultan jin muryan Badra a waya ya sashi dakatawa da tafiyar da yake,lokacin duka fitowarsa kenan daga gidan Hammad yana son zuwa gurin Sadeeq
"My angel.. Kina kusa dama..?"

"Ehh! Ai tare muke da Lady.."

"Ok..! Ni ai ban san kuna hanya ba,sai yanzun da mukayi waya da Mamy take sanar dani kun riga kun taho,,amma a wane location kuke cikin U.S d'in..??"

"Muna nan cikin Pennsylvania ne.."

"Ok.. Kusa damu kenan.. Wane school ne..??"

"Yah Sultan.! Muna fa VILLANOVA UNIVERSITY ne.. When zaka zo mana ziyara..??"
Tayi maganar cike da shagwab'a
"Ohh! Angel,, zan lek'o muku ziyara,amma ku maida hankali kuyi karatu kinji my angel..??"

"Toh Yah..in sha Allah za muyi.."

"Yawwa daddy's kiddo.. Bani Jannat d'in mu gaisa ko..!?"
Sallama tayi masa tana murmusawa sannan ta mik'a mata wayar fuskarta da murmushin tsokana
"Ai da kinsan baki bani ba,,y'ar rainin wayo kawai."
Gwalo ta mata sannan tayi gaba abunta,girgiza kai Sabina tayi tana d'an murmushi sannan a hankali ta sauka daga saman bed tayi hanyar toilet.

*NEW YORK CITY..*
Cikin y'an kwanaki da dawowar Sultan New York da aiki,al'amura a gefen Hammad komaai ya tsaya masa cak,ba'a gurin aiki ba,haka nan ba'a gida ba,,duk da cikin y'an watannin k'ok'arin kawai yake saboda investigation da suke kan wani case,nd burinsa har kullum shi ne ya kai inda yake so amma ina zuciyarsa da kwakwalwarsa a cikin wannan tak'aitaccen lokacin ta gagara sarrafuwa,ji yake komai ya kafe masa a guri guda tamkar tsohon k'arfe,ba don ya so ba haka nan bisa dole yake tattara komai ya ajiye a duk lokacin daya tsinci kansa cikin damuwa,sai dai har yanzun babu mafita,,ko yanzun yana zaune akan computer yana aiki,zuciyarsa tayi wani irin harbawa,still bai ajiye aikin ba yaci gaba,a hankali rubutun dake saman screen d'in suka fara watsewa wasu kuma suka shiga juya kansu zuwa upsidedown,dakatawa yayi ya shafo sumar kansa har ya gangaro kan kyakykyawa kuma gyararren mustache d'insa,sake k'urawa screen d'in idanu yayi amma still sai yake ganin komai yana sake juyewa,duk wani rubutun dake kai ya koma masa baya gane komai sai *MY LADY*,tab'a computer yaci gaba dayi yana ta k'ok'arin saitawa,amma yayi iya yinsa rubutun sai sake nuna masa shirme suke,a hankali ya zame ya kwanta saman armchair tare da rufe idanunsa,cikin k'ank'anin lokaci labarin ya fara sauya salo,yayin da komai yake dawo masa farko,idanunsa yayi saurin bud'ewa ya zubawa rufin kayataccen parlor'n kallo,tunaninta gami da soyayyarta masu girma dake mak'ale cikin zuciyarsa tsayin shekaru suka sake taso masa
"My Lady..!"
Ya furta a fili yana jera sakin wahalallun ajiyar zuciya kamar wanda ya ganta a gabansa,saurin mik'ewa yayi tsaye,kamar walk'iya ya shige bedroom d'insa,duka da shigarsa da fitowarsa ko cikakken mintuna ashirin bai ba,ya fito sanye da wasu kayan,a gaggauce ya kwashe duk wasu tarkacen kayansa masu muhimmanci da wayoyinsa bayan ya kashe computer ya fice a gidan cikin sassarfa,fitowarsa a lokacin yayi dai² da dawowar motar su Sadeeq,yana niyyar shigewa nasa motan suka k'araso kusa da shi,basu ko gama gyara parking ba Sultan yayi hanzarin fitowa a d'an hanzarce yana fad'in
"Dude..! Sai ina kuma kai da muka bari kana aiki..??"

"Zanyi tafiya ne.."
Kallon juna suka yi cikin had'in baki kuma suka furta
"Zuwa ina kenan..??"
Ba tare daya kallesu ba ya ce
"9ja.."

"What..!? 9ja fa kace,,ana tsakiyar aikin zaka yi tafiya..?? Uhhuumm! Wasa kake yi guy.."

"Uhhuumm..!" Shi ne kad'ai abunda yace dan ya fahimci suna d'auka da wasa yake yi,daga haka bai k'ara magana ba yayi shigewarsa mota ya bar arean tamkar zai tashi sama,bcos a lokacin ji yake gaba d'aya zuciyarsa ta gama kiransa,nd yana jin matuk'ar bai kwana a 9ja ba a wannan lokacin komai zai iya faruwa da rayuwarsa,,tafiya kuwa tunda yayi niyya yana jin babu dalilin da zai hana shi fasawa tunda ya shirya yinta,shi yasa ko daya fito babu wanda ya kira bare ya fad'awa yana hanya,yafi so ne kawai su ganshi kai tsayen,ya san babu wanda zai ce masa saboda mene ne ya taho.

*PENNSYLVANIA CITY..*
Wasa² zamansu cikin d'aki guda su hud'un ya zama gwanin sha'awa,zuwansu k'asar da fara karatunsu duka ba'a d'auki lokaci ba amma har sunyi sabo sosai da juna,shak'uwa da mutunta juna kuwa har ba'a cewa komai,idan ka gansu matuk'ar bawai ace ka san su ba tun farko,sai kayi tunanin dama can taren suke,saboda k'ullaliyar alak'ar su mai k'arfi da ko a class basa zama daban²,a ko ina zaka same su tare da juna,cikin makaranta ko wajen ta,,wannan dalilin yasa tsananin aminci da shak'uwarsu jama'a da dama ba iya kad'ai wad'anda suka fito k'asa d'aya da su ba,hatta da farar fata suke sha'awar zama dasu.Ta b'angaren karatu kuwa a ko wane lokaci suna sahun gaba,haka ma idan aka dawo b'angaren barkwanci da tsokana suna nan,,mutum ko waye matuk'ar kun had'o hanya,yanzun kana yin abu ko da cikin kuskure ne,indak gabansu ne zasu sako ka gaba da tsokana,tun jama'a basu fahimce su ba,har salon nasu ya fasu kowa ya fahimci yanayinsu,,dai² gwargwado ta fuskar girmamawa shima suna k'ok'arin bawa duk wanda wani alak'ar mutunci ta had'a su da shi,shi yasa ko farar fatar suke jinjina musu ta wannan fannin,nd wannan dalilin yasa suma suke samun karramawa daga gurin abokan karatunsu har ta b'angaren malamai.

Tana kwance bayan dawowarsu a skul yayin da Zeeharis,Jannat da Badra suke ta hiran gida da y'an uwansu,,tayi shiru yayin sa hankalinta tuni yayi gaba,tayi nisa cikin duniyar tunanin rayuwarta
"Princess,, taso kiga wani abu dan Allah a nan..!"
Cikin ihu su Jannat suke mata magana,yadda tayi shiru bata ce komai ba yasa Badra tasowa ta dawo kusa da ita,a hankali ta dafa shoulder d'inta
"Me yake damunki ne..?? Kwanakin nan duka na kula da kefa kina yawan b'oye mana wani sirri.. Shin har yanzun ba muyi jimawar da zaki sanar damu damuwar ki ba ne..??"


Please Login or Register in order to submit comment