Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

murmushi ba,a hankali kuma tasa hannunta ta goge fuskarta da hawayen farin ciki ya gangaro.

In less than 20 minutes motocinsu suka iso line gidansu Sabina dake cikin unguwar *KAWON MAI GARI* bayan duka sun samu guri sun yi parker a gefe,sannan Malama yasa Hammad ya kira Baban Sabina,,cikin k'ank'anin lokaci Baban Sabina shima ya hallara a k'ofar gidansa da yake yasan da batun zuwan nasu,kuma har yasa an tanade su,ko daya fito gaisuwa aka fara tsakaninsu mai cike da barkwanci,daga nan suka k'arasa zauren gidan suka zazzauna a kan k'atuwar tabarmar da yasa a shimfid'a musu,fita ya sake yi ya barsu da niyyar yiwa wasu cikin mak'otan su,da kuma wasu cikin irin mutanensu tun na can wudil magana,kasancewar shima duk ya sanar dasu,kuma shi d'in suke sauraron jin yayi magana,sai kuma k'anin sa wato baban LADO da shima sanar masa.
Lokacin da suka riske su,sai da aka sake y'an gaishe² sannan Malam ya shiga koro bayanan abunda yake tafe dasu,cikin mutuntawa da girmamawa Babah ya wakilta k'anin sa Baban LADO sai wani dattijo d'aya a cikin wad'anda suka tab'a karb'awa Hammad auren a wancan lokacin suka amshi batun,,cikin mutunci da girmamawa aka yi komai aka gama,Daddy da kansa yana batun bada sadaki,Baban LADO yayi hanzarin tarar su,ta hanyar sanar da su komai daya wakana a baya,wanda ya had'a har da batun bayar da sadaki da Hammad yayi,bayan nan kuma ya d'ora musu da fad'in
"Dama mu tuni abunda muke jira shi ne lokacin da za'a tsaida batun aure.."
Mamaki sosai ya bayyana saman fuskokinsu,wad'anda basu fahimci dalilin aikata hakan da suka yi ba suka nemi farawa daga gurin Malam, shi ya fayyace musu kaf abunda ya sani,daga nan suka bukaci sanin bayanin yadda aka yi hakan ta faru,,Baban LADO dai still shi ne ya sake shaida musu kaf yadda al'amarin ya kasance,bayan gama sauraren bayaninsa jikin Daddy ya sake yin sanyi,,yayin da a b'angaren Malam kuma yake binsa da kallo cikin wani irin fuskar da sai daya haddasa masa shan jinin jikinsa,,lokacin da ake batun yanke ranar aure Daddy da kansa ya sake rok'onsu Baba akan suyi hak'uri a had'a bikin ayi shi lokaci guda tunda duka ko an yinma dai bayan auren tattarawa za suyi duka su tafi U.S kasancewar gurin aikinsa nacan,ba don su Baba sun so ba haka suka amince aka tsayar da nan da kwana biyun da suka rage a matsayin ranakun biki,duk da dai ba haka su Babanta suka so ba,sai don dattijon da suke gani a tare da su Daddy da yasa baki.....


_#Finally dai SABINA ta kusa zama ta Hammad forever..👌🏻_

*Toh.! Ko yaya za'a k'arke da FALISHA idan taji maganar aurensu su biyu a lokaci guda ya tabbata.?? Ku biyo ni don jin yadda zata kasance...*


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*43.*
_#Rescheduling_

Kai tsaye su Daddy bayan sun baro gidan su Sabina sallama suka yi da Malam ya wuce gida,yayin da su biyun shi da Abba'n Sultan suka d'auki hanyar gidan su Amarya Falisha domin ganawar sirri da iyayenta akan gagarumin uzurin daya taso musu lokaci guda,tunda suma d'in da kansu basu yi tsammanin hakan zai faru ba,shi yasa ko yanzun da al'amarin ya taso musu a haka,suka ga dacewar sanar da su akan lokaci kafin azo ana k'ananun maganganu na ba'a san hakan zai faru ba,koma wasu suce an munafiurce su,,su kuma su Hammad Daddy sai ya basu izinin tsayawa suga ita Sabinar su samu damar shirya abunda suke ganin zai yi kafin sake k'urewar lokaci,a zaton Daddy yana ganin kamar Hammad d'in bai zo gidan ba kafin wannan lokacin.
Ko da su Daddy suka tafi a waya ya fara kiranta,sai dai har ya k'araci kiran bata amsa ba,dalilin da yasa yayi tunanin ko fushin da take yine yasa tak'i d'aukan kiran bayan yasan warhaka ma tana kallo,,duk dauriyarsa sai da lamarinta ya matuk'ar d'aure masa kai,buh all he knows kuma yayi believing wa zuciyarsa shi ne duk wannan abun da take da zaran an daura musu aure komai zai zame musu mai sauk'i,imma gobe ko jibi or whatever ma duka idan har Allah ya nufa sun kai lokacin komai zai zama tarihi a gurinsu,sanyayyar ajiyar zuciya yayi ba tare daya kalli side d'in Sultan ba ko taking any excuses apart from him yayi ficewarsa daga cikin motan yana dumfarar k'ofar gidansu,cikin sauri Sultan ya sauke glasses d'in motar da tambayarsa
"Dude.! Ina zaka je ne.!?"
Bai juyo ya kalleshi ba continuously yana tafiya har lokacin yace
"Kasa ido kayi kallo.!"
Yana fad'a ya wuce abunsa kai tsaye zuwa cikin gidan ya bar sultan da binsa da kallon tsantsar mamaki,a zauren gidan yayi sallama,Inna dake tsakar gida tana y'an hidimominta ta amsa masa da fad'in
"A'ah.! Muhammadu,shigo mana,kai da gidanku mene ne na tsaya a zaure.!?"
Da sallama ya shiga ciki his head where looking to the ground,Inna tayi masa masauki zuwa d'akin da Sabinar take kwana,wani sallamar ya sake yi yana shiga ciki,babu kowa a ciki sau shi kad'ai,a lokacin daya gana sauke tsammanin samunta a cikin sai ya zama bai tarar da itan ba,tun daya shigo a hankali ya fara kallon yanayin d'akin ta ko wane edge,,babu laifi gidansu dai² zaman mutum d'aya a talauce,nd cikin d'akintan ma gaba d'aya babu wani tarkace,gaba d'aya abunda ke cikinsa idan aka d'auke katifarta ta bacci sai d'an madaidaicin closet d'inta mai k'ofa biyu,lesser dake shimfid'e a cikin d'akin ta ko ina,sai ko wani d'an k'aramin table da aka yishi da katako,ajiyar zuciya ya saki a bayyane kafin a hankali ya nemawa kansa gurin zauna half a gefen katifar,yayi shiru yana tunanin ganin ta inda zata b'illo.
Sai yanzun daya zauna ne yake jin zuciyarsa tana tuhumarsa dalilin da yasa tun baya ya kasa kaima su Badra ziyara a skul d'insu,yanzun gashi har ana neman rufe shekara guda da batun zuwansu k'asar amma sam bai tab'a tunanin zuwa ba dai² da rana guda yace yau bari ya duba su,sai ko yanzun da yaji hakan yazo masa a zuciyarsa,,tunani ya sake sauyawa inda yake kallon kasa a matsayin mara sa'a,cos duk da ace ya je babu ta inda za'a ce ma baza su had'u ba,sai dai ko daya tuna hukuncin ubangiji wanda sai ya nufa ne al'amari yake kasancewa,sai yayi ajiyar zuciya a bayyane nd ya kai hannunsa kan wayarta dake ajiye gefensa yana jujjuya ta hannunsa,sai daya d'auki tsayin wani lokaci kafin ya ajiyeta yanda ya gani.
A tsakar gida bayan da Inna tayi masa iso d'akin ta duk babu wanda ya sani tsakanin ita ko Baba,buh abunda zasu iya d'orarwa kawai da batun sallamarsa shi ne Innar ta amsa daga nan kuma su da yake suna tare ne a d'akin Baban nata,yana mata bayanin komai da yadda ya kasance shi yasa basu ji lokacin daya shigo ba,bayan kamar minti uku Innar ta lek'o tana shaidawa Baba Muhammadu ne yake jiranta,izinin tafiya kawai ya bata da yake dama sun gama maganar a time d'in kawai yana tambayarta ne ko akwai abunda zata fad'a,tace masa A'a bata da shi,sallamar ta yayi daga nan itama ta kama hanyar fita.

*FALISHA's DOMICILE..*
K'ara ta fasa mai firgitarwa bayan da tayi jifa da wayar a fusace,had'e da sakin kuka mai tsanani tana cakumo gashinta,yadda take yi sai ya zama kamar irin wacce ta fara wucewa d'in nan ne (haukace),cikin muryar kuka take dukan tsakiyar bed d'in tana watsi da duk abunda idonta ya kai kai da fad'in
"Dama na sani.. Bazan tab'a daraja a gurinsa ba..! Me yasa..?? Me yasa³.!"
Ci gaba tayi da kuka,a cikin wannan yanayin Mamah ta shigo ta same ta,da sauri ta nufo inda take,sai data rik'o ta gam a jikinta sannan tayiwa fuskarta kyakykyawan rik'o tana mata kallon tsanaki mai tafe da tambaya
"Leesha.! Mene ne..? Me yake damunki..??"
Still sake kecewa tayi da kuka without ta furta even a single word da Mamah zata gano dalilin damuwar,jijjigata ta fara yi cikin sigar rarrashi,bayan ta kwantar da kanta a jikinta cikin muryar mai d'auke da tsantsar tausayi ta fara magana
"Yi shiru My Lee,kiyi hak'uri haka nan kinji.. Kefa amarya ce,kuma u know amare basa kuka.! Me zai sa tun yanzun zaki b'ata taron bikinki da hawaye.?"

"A'ah.. A'aahh! Mama,dole ne nayi kuka.. Ki tafi ki kyale ni kawai.."

"Me yasa ne Lee.!? Kiyi hak'uri ki bar kuka kinji,ko mene ne yake damunki ki sanar da ni kinji..!?"
Kai ta girgiza alamun toh,kafin ta fara whipping tears d'in da suka mata kaca² da fuska tana yi tana gyad'a kai kamar lizard,sake rik'o shoulders d'inta Mamah tayi tana tambaya
"Yanzu fad'amin mene ne yasa ki kuka..?? Aahh..!?"
Ido ta matse a hankali wasu sabbin hawayen suka sake gangarowa,sai da ta sake matsewa kafin tace
"Mamah..! Da gaske ne mu biyu zai aura..?"
A bazata tambayar tazo wa Mamah wanda yasa har sai data nemi rud'ewa amma ta dake bata nunawa Falisha komai ba a zahirance,da sauri ta matso kusa daita sosai tana k'ureta da kallo
"Me kika ce Leesha..!? Ku biyu kamar yaya..!? Ban gane ba."
Gyad'a kai ta sake yi cikin kuka² tace
"Is that true Mamah..!? Just answer me with yes or no."
Kafad'a Mamah ta d'age tana girgiza kai
"Bana tunanin haka..! Amma idan har hakan nema ai ya kamata ace mun sani tun da wuri,,to ma ke waye ya fad'a miki wannan maganar ne..!?"

"Shi ne ya sanar da ni yanzun da kansa.!"
Girgiza kai Mamah ta kuma yi a hankali ta sauke wahalallen numfashi tana cewa
"Bana tunanin wannan maganar gaskiya ne,tunda mu ba'a sanar damu da wuri ba,idan ma ace gaskiya ne,ina tunanin sai dai idan tun farko babu ita yanzun ne aka k'irk'iro ta..Amma.!"
Sai tayi shiru tana sake zurfafa tunaninta akan maganar,tabbas tunda har Falisha take kuka akan maganar da basu tabbatar ba zai yi wuya ace babu alamun k'amshin gaskiya a cikinta,toma wai idan ba gaskiyar bane me zaisa ne Hammad ya fad'i irin wannan maganar da wasa.?

"Mamah.!"
Cikin kuka tayi kiranta amma sai ta kasa furta komai,dole yasa tayi shiru tana sakin sheshshek'ar kuka mai cin rai,tarairayota Mamah ta sake yi cikin alamun da suke bayyanar da tana saurarenta tace
"Uhhuumm.! Fad'a min mene ne..!?"

"Bana son mu zauna mu biyu,,please ki fad'awa Abba,bana son zama da kishiya.."
Ran Mamah a jagule ta kalli y'ar tata tana shafa kanta cikin rarrashi
"Kada ki damu Leesha,hakan ba mai yiwuwa bane,,ki kwantar da hankalinki kinji..!?"
Kai ta gyad'a mata da sauri
"Mamah do u know something..!? Har cikin zuciyata jin ba zan iya sharing miji da wata ba,u know ina da tsananin kishi a kan abunda zuciya ta ke so,ta yaya ne zan yarda mu had'a miji da wata kucaka..!?"

"Bazai tab'a yiwu ba Leesha,, ki kwantar da hankalinki then ki nutsu sosai har mu tabbatar da ingancin maganar,ni nan da kaina zanyi magana da Abba'n ku,ya kamata ya tambaya mana iyayensa gaskiyar magana,idan har magana ta tabbata gaskiya sai dai su san yadda za suyi da waccen,saboda ba zai yiwu a had'a min y'a da kishiya ba,kina k'aramarki ace za ki zauna da kishiya,ta yaya ne za'a ce ni ban zauna da ita ba,ke ina ji ina gani,da raina da lafiyata zan yarda a kaiki gidan kishiya..!? Wannan ai abune da bazai tab'a yiwuwa ba a gurina.."
Wahalalliyar ajiyar zuciya ta saki tana sake rik'e mahaifiyar ta a jikinta sosai
"Thank u Mom,, am so proud of u.."
Rungume ta Mamah tayi back tana shafa kanta had'e da yi mata murmushi mai sanyawa zuciya nutsuwa,a hankali ta lumshe idanunta da fad'in
"Maza to ki kwanta ki huta kinji My Lee,, da safe idan Allah ya kaimu zan yiwa Abba'n ki maganar kinji ko..!? Bana son ki kuma tashin hankalinki akan irin wad'annan minor things d'in,kin fahimce ni ai.?"
Jinjina kai tayi slowly ta zame ta kwanta tana sakin wahalallun ajiyar zuciya,Mamah dake kusa da ita taja mata bedspread ta rufeta half da fad'in
"Sai da safe..!?"

"Ehhh Mamah..!"

"Ok.. Bye,,sleep tight."
Ta d'ora mata peck a chicks sannan ta fita bayan ta tabbatar Falisha'n ta kwanta.

Tun kafin su Daddy su k'araso gidan tuni har sunyi magana da Abba'n Falisha sun sanar masa suna kan hanyar gidansa,ba tare da sun d'auki lokaci mai tsayi ba sai gasu sun k'araso,,tsarin gidan kam babu laifi,flat ne amma ya tsaru tun daga wajensa har ciki,dai² gwargwado dai yayi kyau nd dai² arzik'in mamallakinsa,a mutunce cikin rufin ashirin Ubangiji,,lokacin da suka k'araso sun samu tarba mai kyau daga hadiman gidan cikin umarnin Abba'n Falisha,bayam yasa an musu masauki a guestroom d'insa,da yake shima d'in baya gidan sun dai yi waya lokacin yana daf da k'arasowa,a gurguje lokacin bayan ya k'araso garesu ko daya shiga inda suke suka gaisa Abba'n Sultan yayi masa bayanin dalilin zuwansu,a zahiri ya nuna yayi na'am da batun nasu harma ya nuna musu ai babu komai hakan da suka yi shi ne dai² kuma sun samar da masalaha kasancewar sunyi masa bayanin komai daya shafi alak'ar Hammad da Sabina tun kafin wannan lokacin kamar yadda suma aka sanar musu,bayan sun gama magana kuma suka yi sallama da shi ya musu rakiya har bakin mota drivern su dake jira a waje yaja suka bar gidan.

Kanta a sunkuye tana kallon k'asa tunda ta fito daga gurin Babah har ta shigo d'akin,tunani take amma wani irin kwantaccen murmushi ne a saman fuskarta,har ta shigo bata san me yake faruwa ba sai dai tayi magana k'as² cikin shauk'i har tana had'awa da lumshe idanunta
"Lokacin nasara ya soma.. Gaskiya na tabbata cikin mutane masu sa'a..!"
Tun kafin ma ta k'arasa ta hango shi zaune,da mugun mamaki ta sake kallonsa not believing shi take gani ta juya zata koma waje,sai a nan shima d'in ya d'ago kansa ya bita da kallo,har ta kai bakin k'ofa zata fita ya dakatar da ita ta hanyar tambaya
"Ina kike shirin zuwa kuma.!?"
Saurin juyo tayi tana kallonsa cos da bata yardarwa kanta shi ne da gaske ba,sai data tab'e baki sannan ta dawo da baya cikin wani sabon salon had'e fuska,inda wayarta take ta nufa ba tare da tayi masa magana ba,gently tasa hannu ta d'auki wayarta ta bud'e still kuma bata yi yunk'urin masa magana ba taci gaba da clicking,number Badra take k'ok'arin kira ganin bata da niyyar masa magana yasa shi fizge wayar a hannunta shima fuskarsa a had'e
"Me kike nufi ne.!? Baki yi kama da masu irin wad'annan behaviours d'in ba,sam banyi tunanin haka daga gare ki ba.. Wai ma mene ne matsalar ne..!? Mene ne matsalarki da ni..? Ina binki kina nuna min u don't care about me.? Me kike so nayi..??"

"Ni babu abunda nake so.."

"Ban yarda ba,,defiantly there must be something hidden.. Ki fito ki sanar min,bana son wannan halin da kike nunawa,,am frank idan zanyi abu kai tsaye nake yinsa,so bana son ki b'oye ki sanar min.."
Idanunta ta rausayar slowly sannan ta juya masa baya
"Ni na fad'a maka babu.. Tunda na fad'a ka yarda.."

"Ba zan tab'a yarda ba kuma kema kin sani."

"Okay..!"
Ko gama bari ta kai aya baiyi ba ya mik'e a fusace ya birkitota suka fuskanci juna,yadda ya taso mata da zafinsa ya haddasa mata tsoronsa,yadda yaga ta firgice sai ya sassauta murya k'asa² yana mata magana
"Fad'amin ina sauraron ki yanzun.."
Tsabar kishinsa dake sakatar mata zuciya da tsoron daya bata har bata san lokacin data fad'a jikinsa ba ta fashe da wani irin kuka,idanunsa ya runtse yana jin haushin kansa,all he knows kuma yayi believing ma zuciyarsa at that time shi ne ya janyo zubar hawayenta,nan kuwa bai san tsabar damuwa ne da kishinsa ne suka sa ta shiga yanayin ba,hannayensa ya mayar bayanta yayi holding d'inta tight a jikinsa,calmly yake caressing spine d'inta
"Please Lady idan baki yi shiru ba zaki sa na rasa control.. Kiyi shiru haka nan ki fad'amin damuwar.."
Sai ya d'ago chin d'inta yana goge mata hawaye,shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya,a hankali ya zubawa kyakykyawar fuskarta idanu
"Uhhuumm.! Zaki fad'a min yanzun..??"
Da kai ta amsa masa sai ya kama hannunta suka zauna duka a bakin katifarta,sai da d'akin ya d'auki shiru na wani lokaci,sannan ya sake yin magana
"Lady tell me mana,ina son na koma gida da sauri cos akwai shirye²n daya kamata ace nayi wanda da ban samu nayi ba.."

"To kaje kawai ni ba saina fad'a maka ba ma.."
Wani irin kallo ya bita da shi mai shiga jiki,dan yadda tayi magana a sakarce sai daya haddasa masa jin shauk'i har k'asan ransa
"Babu inda zani sai kin fad'a min.."
Bakinta ta turo gaba cikin gungunin shagwab'a kan takurata da yayi tace
"To ni me zan fad'a maka ne..!? Nimafa ban sani ba.."
Juya idanunsa yayi akanta ya had'iye wani irin yawu
"Kina ganin wannan hanyar shi ne zai b'ille miki..?? Tun yanzun kina bani amsa a haka..!? Me kike tunani zai faru gaba.!? Ban tab'a zaton haka daga gare kiba,tun kafin tafiya tayi nisa ya kamata ki gyara,idan ma akwai wanda yake baki shawara ne,to ya kamata kice masa bakya so ya rik'e abunsa,,sam bana jin dad'in hakan,nd banyi zaton samun wannan tarbar daga gare ki ba."
Sabbin hawaye ta sake saki cikin sheshshek'ar kuka tace
"To ni wai mene ne nayi maka da yasa kake ganin laifi na..!? Kai ba'a ce kayi laifi ba sai nice za'a ga laifina.."
Yana cikin mamakinta ya ce
"To wai mene ne nayi miki haka..? Na tambayeki tun kafin yanzun kin kasa bani cikakkiyar amsa,ta yaya ne zan san laifin da nayi.. Aahh..??"

"Dama ai baza ka sani ba,tunda ba damuwa kayi da ni ba..!"
Murmushin takaici ya saki lokaci guda ya sake kusantota har numfashinsu yana gwamuwa
"My Lady.. Ni kike fad'awa ban damu dake ba.? Ni ne wai ban damun ba.? Let me tell u to,idan baki sani ba zan sanar dake idan kuma kin sani zan tunatar da ke.."
Hannunsa yasa cikin aljihunsa yana fitowa da shi ya d'ora mata abunda ya ciro d'in a hannunta
"Kin tuna wannan..??" Kafin tayi magana ya riga ta
"Tun daga lokacin dana tafi da shi babu dare babu rana kullum ina tare da shi,gida ko office babu abunda yake rabani da shi,idan ban damu dake ba,me yasa zanyi haka..!? Soyayyar da nake miki idan har dan ban damu dake bane,me zai sa na dawo..? Tsayin lokaci na d'auka ina bulayin neman ki bau dare babu rana ko wane lokaci tunani na da lissafina inda zan ganki amma ban same kiba,nayi yawo tsakanin U.S da Nigeria duka saboda na ganki,me yasa ban manta dake ba sai yanzun.!? Haba Lady,bai kamata ki sawa ranki wai kamar ni da nake jin duk duniyata babu wata mace a zuciya ta data kai ki daraja da k'ima ki bud'e baki kice ban damu dake ba,idan har ban damu dake ba,me yasa ban shafe babinki a rayuwata ba..!? Me yasa³.!?"
Runtse idonsa yayi saboda takaicin maganar yana dafe forehead,daga haka gaba d'aya ya rasa abunda zai sake fad'a mata next ta yarda da shi
"To ai dai duk da hakan daka fad'a bai hana maka neman auren wata macen ba,har ma ka shirya ma kanka rayuwa da ita,,idan ka damu da ni me yasa zaka sawa ranka sonta..!?"
Saurin bud'e idanunsa yayi ya sauke su a kanta,murmushi ya saki mai sauti saboda ya gama gano inda ta nufa,slowly yasa hannu ya d'ago fuskarta had'e da zuba mata idanunsa
"My Lady.! Are u jealous.!?"
Saboda tana cikin damuwa har bata ma san lokacin data kad'a masa kai ba cikin sakin wasu hawayen ta k'ara da fad'in
"Ba dole naji kishi ba,mutumin da na gama killace rayuwata dominsa,rana a sama sai na tsinci labarin zai auri wata macen daban..!"
Kyakykyawan murmushi ya sake saki a hankali yana kallon motsawar bakinta,shi kam in dai yau ne to yana tunanin babu wani abu da za'a fad'a masa wanda zai sashi jin cewar shi na daban ne daya wuce samun wannan kyakykyawan labarin daga bakinta,gaba d'aya saurarenta kad'ai ya sashi zama wani speechless,sai daya d'auki tsayin lokaci yana kallonta without ya furta a single word,ita kanta a lokacin bata yi zaton daga haka zai sake cewa komai ba amma sai ta jiyo shi yana fad'in
"Thank u My Lady.. Ban san mene ne ya kamata nayi wanda zai faranta miki ba,nd ki daina ganin laifina akan waccan maganar,,buh all i knew shi ne kwata² ni ban san da maganar taba,cos nima tsintar ta nayi a sama kamar yadda kika ji,lokaci guda Daddyna yazo min da batun auren y'ar amininsa,nasan kin kin sani bai kamata ace iyayen da suka raineka ka nuna musu basu isa da kai ba.. Toh! Wannan dalilin yasa nima nayi hak'uri duk zuciyata bata so na amsa buk'atar Daddy,,gashi a lokacin ke kuma kin yi min nisa,ban san ina ne zanje na nemo kiba,ko kafin na amsa ma sai da nayi yawon nema

Please Login or Register in order to submit comment