Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ak'alla 2-3 minutes a tsayen,a time d'in su Sultan tuni har sun shige amma sai yaji shiru babu alamun zata zo,wani mugun fad'uwa gabansa daya sake yi tunawa da conditions d'inta take wani irin gumin wahala ya fara fito masa,sake danna bell d'in yayi a jere har wajen sau biyar,jin shiru still a zafafe ya ciro wayarsa daga aljihun trouser d'insa ya fara kiran line ta,,wayar ta shiga sai ring take amma shiru babu alamun za'a d'auka,nan d'inma sai daya jera mata miss calls yafi a lissafa yana yi yana sake maimaitawa had'e da zarya a gurin kamar ya yiwa sarki k'arya,,zuciyarsa zuwa lokacin tuni ta gama saduda,ya gama yankewa kansa hukuncin wani abu ya faru da ita,a hankali wasu irin azababbun hawayen fargaba suka fara taruwa cikin kwarmin idanunsa,sai ya jingina bayansa jikin door d'in ya d'age kai sama cikin tunanin yadda safiyarsu ta kasance kafin ya fitan,,yayi nisa cikin tunanin sai ji yayi daga d'ayan gefen an bud'e k'ofa,,a hankali ya d'ago kansa ya bi gurin da kallo cos tunaninsa ya bashi ko wani cikin y'an uwan nasa ne ya sake fitowa,murmushi ya hangota tana yi while tana kallon cikin apartment d'in data fito tana d'aga hannu da fad'in
"Sai an jiman dear..!"
Yadda take tafiya a hankali kamar wacce cikin ya gama tsufa,sai ya sake k'ureta da kallo yana sauke wahalallen ajiyar zuciya daya tabbatar lafiyarta k'alau,dai² ta juyo tana ci gaba da tahowa itama idanunta suka sauka akansa,sai da tayi wani slow cikin kallonsa da karantar yanayinsa kafin da d'an saurinta ta nufo shi,shima d'in tunda ya tabbatar itance nd lafiyarta k'alau babu abundabya faru da ita da sauri sai ya nufeta suka had'e a tsakiya,wani irin rungume juna suka yi,kowa yana sauke ajiyar zuciya kamar sun shekara basu ga juna ba,sai da suka d'auki ak'alla mintuna biyu a gurin sannan suka yi hanyar apartment d'insu still suna mak'ale da juna,sai dai ba'a samu mai yin magana ba har lokacin,suna shigewa ya sake rik'o ta sosai yana kallonta kafin yayi k'arfin halin d'age lip's d'insa da yake jin kamar an had'e masa su da glue
"Ina kika ajiye phone d'inki ne.!?"
A hankali ta juya idanunta tana kallon saman armchair data manta wayar a nan ta masa nuni zuwa gefen da yaken,slowly ya juyar da kansa inda take nuna masa duk da bisan me hakan da tayi yake nufi ba,wayar ya gani ajiye a gurin sai yasa hannu ya d'auka,pressing d'inta yayi a hankali then ya nuna mata jerin kiran da yayi mata,ido waje ta kalli tarin miss calls d'in,sai kuma ta kalli fuskarsa da har lokacin take cikin yanayin da ta kasa bambance wane iri ne,a hankalin sai ta marairaice fuska,za tayi magana ya riga ta
"Kada ki sake fita babu waya a tare da ke..!"
Tun kafinma ya k'arasa har ta bashi amsa da
"In sha Allah,i won't..buh pardon me Hayat.!"
Ta fad'a cikin salon janye hankalinsa,sai da yayi ajiyar zuciya yana kallon cikin idanunta kafin ya janyota jikinsa sosai ya sumbaci chicks d'inta then ya sake rungume ta tsam a jikinsa yadda yasan ba zata ji wahalar rik'on nasa ba,,har ya bud'e baki zai yi magana ko me ya tuna kuma sai yayi shiru,yayin da yake jin babu dad'i cikin maganar da zai yin ga muguwar fargaba data sako shi gaba tunda yaji batun aikin,haka nan sai yaji ya kasa daurewa ya sanar mata,,again bayan wasu lokacin sai ya sake attempt na ya fad'a mata amma sai ya sake yin shirun,ak'alla sai da ya gwada sanar mata yana fasawa tafi a lissafa,,daga k'arshe ne ko da yaga dole dai sai ya fad'a d'in tunda aikin ba fasa yinsa za suyi ba sai yayi sahadar k'uda,bayan ya d'an janye kansa gefe cikin wani salon lallashi yana kallon ta ta side ya ce
"Helpmate.!"
Yanayin da ya kira sunanta ita kanta sai da taji fargaba musamman da taga yak'i kallonta,buh sai ta nuna rashin damuwa sosai inwardly kuwa ita kad'ai tasan me take ji,duk da hakan tayi k'ok'arin dannewa ta amsa masa,sai da yayi d'an jimm kafin yace
"U know everything apart of my work,,right..!?"
A hankali sai ta kad'a masa kai tace
"Ehh! Na sani."
Inwardly sai yace "Thank God,,she knows everything about it.."
Sai ya sake kawar da kansa gefe slowly yace
"Toh.! Allah sa dai baza ki damu kanki ba idan kinji abunda zan fad'a."
Duka a cikin zuciyarsa yake maganar,a zahiri kuwa sai daya d'an saci kallonta yana gyad'a kan shima before ya iya furta
"Kin san an kira ni d'azun ko.? To bayan naje na tarar anyi selecting d'inmu har su Sultan,nd we are going to lead.." Sai ya d'anyi shiru yana tunanin me zai cene a gaba,,fuskantar da tayi masa tun shigowarsa yasa ta kamo fuskarsa ta tsayar da ita dai² suna kallon juna ido da ido,tasa hannunya tana shafo beard d'insa a hankali kamar mai yi masa susa sai tace
"Aikin har wane lokaci zai d'auka ne da naga duk ka damu kanka.!?"
Ajiyar zuciya yayi yana kallon cikin idonta yace
"Zai d'auke mu lokaci gaskiya,,nd ni kuma ban shiryawa yinsa ba yanzun.."
Yadda yayi da fuskarsa sai yasa tayi murmushin k'arfin hali,sake had'e rai yayi yana kallon yadda take murmushi kafin yace
"Abun dariya nema a gurinki ko..!?"
Kai tayi saurin girgiza masa,sai ya harare ta yace
"Ci gaba ma da abunki,ba dai ina fad'a miki kina d'auka wasa ba,sai kinga bana nan tukun,za kiyi bayani wa y'an garinku..!"
Y'ar dariya ta sake yi cike da zolaya tace
"Su Jannat kenan.!"
Shima sai yayi murmushin k'arfin halin,sai da suka tab'a wasa da dariya sannan ya saka fuskar serious yace
"I'm serious aikin nan zai d'auke mu lokaci mai tsayi,buh naga kina d'aukansa wasa.."

"A'a nifa ba haka bane,kawai dai naga ka kasa concentrating ne ka sanar min,besides kuma ba kace komai ba har yanzun akan tambayar da nayi.."
Kallonta ya sake yi a nutse yana shafo spine d'inta yace
"Umm! Zai iya d'aukar mu tsayin wata guda kafin mu gama."
Sanda ta tab'e baki har tasa ya tsaya kallonta kawai kafin tace
"Nama yi tunanin zai kai sama da haka ne,,mene ne na damuwar ma a cikin 1 month,,ai dai naga ba yau ka fara ba ko.!?"
Sake kallonta yayi sai dai ba irin na farko ba,a hankali sai yace
"Za ki iya yin watan ba tare da kin ganni ba.!?"
Sai ta gyad'a masa kai tace
"Ehh! Indai da waya ai nasan zai d'ebe min kewarka.! Fiye da haka ma zanyi.!"
Sake kallonta yayi yace
"Za ki iya yin watan kuma baki ji muryana ko a waya ba.!?"
A firgice tayi saurin kallon shi tace
"Wane irin aiki ne wannan kuma.!?"
Harararta yayi yace
"Shi ne wanda kika yi tunanin ina damun kaina akansa.!"
Duk da taji fargaba akan abunda yace d'in amma dan ta nuna masa itan jaruman ce sai tayi k'ok'arin aro jarumta ta lik'awa zuciyarta,murmushin k'arfin hali shimfid'e saman fuskarta tace
"To mene ne dan kayi wata kana aiki,sai nasa damuwa akaina,ko kuma nace ban yarda kayi ba..!? Duk matar k'warai zata so ne ace mijinta a kan neman halal d'insa yake kullum,,ni kam idan har dan ni kake damuwa ya kamata ma ka daina,kullum burina da fata na dama baya wuce ya zama a kan hanyar gaskiya kake,,dan batun wani aiki in sha Allah babu abunda zai faru har ka kammala,,don't bother ur self mana,ai nasan mijina jarumi ne zai iya yin komai ba tare da fargaba ba.."
Tunda ta fara magana yake kallon bakinta har takai aya,duk da har ransa ne yaji baya son yin aikin amma maganganunta sosai suka k'ara masa k'arfin guiwa,soyayyarta mai girma taci gaba da taso masa,sake rungume ta yayi cike da tsantsar k'aunarta,yana ci gaba da sauke ajiyar zuciya.Sun jima sosai suna magana duk akan aikin,tana sake kwantar masa da hankali da bashi shawarwarin da tasan zasu k'ara masa confidence,kafin ta taya shi shirya duk abunda yasan zai buk'ata,aikin shiryawan kawai take amma yadda zuciyarta take a raunane sai take jin kamar zata yi kuka,bayan sun gama yayi parking komai a side duk da ba ranar za su fara aikin ba amma gudun k'urewar lokaci yasa ta takura suka yi tun yanzun,,janyota yayi ta dawo closer da shi,hannayensa duka rik'e da waist d'inta while itan sai ta d'ora nata duka a wuyansa,d'an murmushi yayi mata mai sanyi a hankali muryarsa can k'asa yace
"Kuka za kiyi ne..!?"
Girgiza masa kai tayi tana ta k'ok'arin mayar da kukan,murmushi ya sake yi sannan yace
"Muje to ki bani abinci ko.? Duka na gaji nd ina jin yunwa.."
Sai ta sake gyad'a masa kai,hannunta ya rik'e a hankali sannan suka fita daga d'akin.

Two day's after waccan maganar tasu suna kwance da dare yake mata tuni akan batun aikin da zasu yin,a sanyaye ta d'an kalle shi kawai tunda tasan gobe war haka baya nan amma sau bata iya ta ce masa komai ba,inwardly dai ta bi shi da fatan samu nasara,shima d'in tunda yaga tayi shiru bata ce komai ba sai bai sake yi mata maganar ba,,washe gari daya kama ranar da zasu tattara a can headquarter din tun da safen around 7am yayi mata sallama,har bakin elevator sai data rakashi,bayan sun sake yin bankwana ya wuce cike da kewarta,tun kafin ma ace yayi nisa da tafiyar wasu irin hawayen da take ta b'oyewa kusan kwanaki uku suka shiga sakko mata,tana nan tsaye tana rera abunta har sai data tabbatar zuwa lokacin ya kai first floor sannan ta juya ta koma apartment d'insu jikinta duk a sanyaye,yinin ranar haka nan ta zauna shiru ita d'aya tunani da kewarsa fal zuciyarta,,wasa² tunda ya tafin sai daya d'auki kusan kwanaki uku bata ko ji muryarsa ba,tun tana zaton kamar maganar da yayi mata ba gaskiya bane zai dunga samun time suna yin waya har abun yafi k'arfin tunaninta,wani lokacin idan ta zauna tana tunani sai taji duk duniyar tayi mata babu dad'i,dama² ace sun fita makaranta da yake suna zuwa station d'in Pennsylvania da yake a nan 34th street sai suke tafiya can su hau bus da zai kaisu skul,sauk'in da take samu kenan,sai idan sun dawo gida ne lokacin bacci yayi sai tayi zugum tana tunani wani lokacin ma sai ta gama kukanta take yin baccin,,akan haka lokaci yaci gaba da gudu.
Yauma d'in dau kamar sauran kwanakin da suka wuce bayan sun gama fira da yake dare ya d'an fara yi shi yasa duka kowacce sai ta wuce apartment d'insu,,tana zaune bisan armchair tayi zurfi cikin tunaninsa tana ta hasashen ko sai yaushe zata ganshi,sai ga doorbell yayi k'ara wanda hakan yayi sanadiyyar data d'an firgita,sai ta dago kai ta kalli wall clock d'insun dake dining area,kamar baza ta tashi ba ganin dare ya fara yin nisa har 10pm ta haura sai kuma aka sake matsa doorbell d'in a lokacin,hakan yasa dole ta mik'e a hankali ta nufi entrance d'in tana tambayar waye,shiru aka yi ba'a amsa mata ba,hakan yasa ta d'an ji tsoro ta koma da baya kad'an kamar zata koma,again aka sake danna doorbell d'in,wani irin frightening saliva's ta had'iye da sauri sai ta rik'o k'aramin base dake saman center table ta nufo k'ofar,duk da a tsoracen take amma hakan bai hana ta d'ora hannunta ta cire key had'e da bud'e k'ofar a hankali ta d'an lek'a ba,ganin babu kowa a gurin ne yasa ta saki wani irin ajiyar zuciya sai kawai ta koma da nufin ta fara ajiye base d'in sannan ta kulle k'ofar,after ta ajiye d'in tana shirin juyowa da niyyar rufe k'ofar kamar walk'iya ta ganshi ya shigo ciki had'e da maida k'ofar ya rufe,wani irin ihun tsoro ta saki jikinta yana kyarma saboda bata ga fuskar ko waye ba ta fara ja baya tana fad'in
"Who are u..!? Nd what brought u there.??"
Sake sunkuyar da kai yayi da yake akwai p-cap akansa bak'i,looking nasa tayi all from head to toe,jikinta har time d'in yana kyarmar tsoro cos duka bak'in kaya ne ma a jikinsa,besides kuma ita kanta p-cap d'in an rufeta da wata rigan mai had'e da tire,duk da tana tsorace da ganin mutum ba tare data san waye ba amma cikin salon bada tsoro a zafafen sai tace
"I said who are u..!?"
D'agowa yayi da kansa dake sunkuye sai ya sauke tire d'in dake kan p-cap d'insa yana mata murmushin sa mai tsada,wani irin ihu ta saki har bata san ta ture base d'in data ajiye a hannunta ba,ta kwaso da gudu ta mak'ale shi,wani irin rik'on tsauri yayi mata da fad'in
"Easy madam.. Kin san bake d'aya bace kike min gudu,kina son nakashe min baby ne tun bai zo duniyar ba..!?"
Had'e rai tayi taja baya tana murgud'e masa baki da fad'in
"I knew ai dama,i don't have any use daya wuce nayi ciki na haifa maka.."
Wani irin kallon daya mata na mamakin maganarta shi ya hana shi cewa komai,da wani irin force a tattare da shi sai ya k'araso inda take yace
"What did u says..? U don't have any use,,to whom ne baki da amfanin.?"
Sai tayi shiru ta kasa magana,idanunsa a d'an birkice saboda rashin jin dad'in furucin da tayi masa,sai kawai ya girgiza kai ba tare daya iya cewa komai ba yace
"Shi kenan barin koma inda na fito,tunda duk d'aukin da nayi tayi zanzo na duba ki bashi da amfani,,Allah ya k'ara lafiya.."
Yana gama fad'ar haka ya juya zai fice
"HAYAT..! Please don't go..!"
Ko juyowa baiba yayi ficewarsa yana jin wani irin b'acin rai da yake kartar masa zuciya,,kuka ta fashe da shi lokacin data tabbatar ya fitan a hankali sai ta silale k'asa ta ci gaba da rera kuka mai ban tausayi,inwardly tana nadamar abunda tayi masa,kusan minti d'aya tsakani har ta yanke tsammani da dawowarsa sai aka sake bud'e k'ofar,da sauri ta mik'e a gurin tana ganin sa tsaye bakin entrance ta nufe shi da gudu cewa yake mata
"Don't run,,stop²..!"
Amma ko saurarensa ma bata iya yi ba bare ta fahimci abunda yake fad'a ta rufta kansa tana sake sakin mahaukacin kuka,sanyayyar ajiyar zuciya yayi yana shafa bayanta,a hankali sai yace
"Shhhh! Stop shading those tears.."
Tana jikin nasa take gyad'a masa kai kawai,cikin sauri kuma sai ta d'ago ta shiga whipping d'insu,ajiyar zuciya ya sake yi ya rik'ota suka k'arasa cikin parlor'n,sai daya fara zama saman armchair sannan ya zaunar da ita a saman jikinsa,ita kuwa har lokacin hawaye take k'asa² sai dai babu sound cikin kukan,yana mata wani irin kallon k'auna yace
"Please mana na fad'a miki nayi hatin kallon ana kuka a kusa dani,amma baki ji ba ko.!? Idan baza kiyi min shiru ba zan tashi na koma yanzun tunda baki yi maraba da zuwana ba.."
Da sauri ta k'arasa goge su tana sake yin luf a jikinsa had'e da jera wahalallen ajiyar zuciya,sai daya d'ago chin d'inta suna kallon juna a hankali yayi breaking shirun da suka yi da fad'in
"Have u missed me..!?"
Sai tayi saurin gyad'a masa kai,tab'e baki yayi kad'an yace
"Really.!?"
Ta sake gyad'a masa kan
"Ok..! Muje to ki nuna min yadda kika yi missing d'ina.."
Kallonsa ta tsaya yi har sai daya mik'ar da ita tsaye sannan tace
"What.!?"
B'ata fuskarsa yayi yana kallonta da maimaita abunda tace
"What..!? Muje mana, ko na tafi ne baki shirya ba.!?"

"A'a ni ka dena cewa za ka tafi.!"

"Uhhuumm!" Yace yana kama hannunta,suka wuce master bedroom d'insa,tun daga shigarsu kafin ma su k'arasa inda bed d'insun yake tuni ya fara detaching musu kayan jikinsu cikin mayen son kasancewa da ita,ya d'agota suka k'arasa saman bed d'in,,wani irin juyata yayi ta koma samansa a hakan sai suka shiga aikama junansu sak'onnin da suka tabbatar musu sunyi kewar junan,,a wannan daen sun raya shi ne ta hanyar nunawa junansu adadin kewar junansu da suka yi kafin suka sarara,,ko bayan sunyi wanka ma suna cikin nishad'i duka har suka kwanta manne da juna tana ta masa salonta na janye hankali,a hakan har bacci ya d'aukesu duka cike da tsantsar k'aunar junansu.

Sai around 6am sannan ta iya farkawa da wani irin nishad'i buh still hamma take saki cos baccin bawai ya isheta bane,dama fitsari ne ya tada ita lokacin,babu shiri kuwa ta nufi toilet,tun kafin ace ta k'arasa cikin toilet d'in a guje fitsarin ya taho,dole tasa ta sakin abunta a nan inda take,cikin jin haushi bayan ta gama ta hau zubawa jikinta ruwa,tana gamawa kuma gaba d'aya sai ta cire kayan tayi wanka,bayan ta d'aura alwala sai ta fito ta dawo cikin bedroom d'in still tana jin haushin fitsari da tayi jikin kayanta,arabian gown da take sallah da shi tayi wearing mai had'e da hijab then ta kabbara sallah,,lokacin data idar bayan tayi azkarus'sabah sai ta cire kayan duka ta mayar inda ta d'auko su,bayan ta adana sai data gyara dakin tsab ta kuma gyara jikinta,sannan ta d'auko ma kanta wani irin french consenza gown mai one shoulder fari k'al ta sa a jikinta,da wani irin k'aramin ribbon fari k'al kuma sai ta d'auko ta kame gashinta a gefe da shi,y'ar k'aramar d'an kunne mai wasu irin fararen stones ta d'auko mai siririn chain ta mak'ala,ta kawo colourless lip bam daya haska bakinta ta shafa,nan da nan sai ta d'auki kyalli saboda kyau da tayi a cikin shigar,ta feshe jikinta da turarukansa da take masifar so,,murmushi ta saki mai aji bayan ta gama kallon kanta sannan ta yi hanyar fita daga d'akin da tunanin zata same shi a parlor.
Tunda ta fito daga ciki take dubawa amma bata ko ji motsinsa ba,har ta gama zagaye kaf gidan,sake komawa tayi cikin bedroom d'in fuskarta da damuwa cos ta kasa ganewa a gasken ta ganshi ko kuma dai mafarki tayi ya zo.? Sai dai har ta gama caje kaf d'akin shima d'in ba tare data samu wani kwakwaran shaidar daya tabbatar mata ya zo ba,wayarta ta d'auka ta koma parlor,sai ta zauna a k'asa tana k'ok'arin kiransa,buh har tayi kiran ta gaji bata same shi ba duka wayoyinsa a kashe,,hak'ura tayi ta ajiye wayar cikin damuwa ta jingina kanta a jikin kujeran da take,,da tunanin anya yazo ko kuwa dai sharrin mafarkin data saba yi ne....??




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*52.*
_#Boldface_

Ranar duka haka ta yini tunani,gashi ko ta kira wayarsa bata tafiya sai ace mata wayar tana kashe,wasa² haka tayi ta fama har dare bata fasa gwadawar ba suma kuma basu gaji sun daina fad'a mata wayar tana kashe ba,,ko da daren ma tana zaune bayan su Badra sun shigo mata hira sun fita,da damuwa sosai a kwance saman fuskarta bayan ta kulle k'ofar sai ta shige master bedroom d'insa saboda wani gajiyayyen bacci da take ji,ko data shiga a matuk'ar kasalance ta daure ta yi wanka da ruwa mai mugun d'umi,after ta fito kuwa ba ta tsaya shafa komai ba sai ta bud'e cikin closet d'insa,wasu pyjamas d'insa ta d'auko mai makon ace ta d'auki nata,da yake kayan basu da wani girma kasancewar wandon irin breathable seamless boxers ne kuma silk sai rigan da yake arm lace kuma duka farare,kawai sai tasa duk da sun mata girma amma a hakan ita dai sun mata,turarukansa da duk dare suke d'ebe mata kewarsa ta d'auka ta shiga spraying d'insu a jikinta da kayan har sai data fara jin babu dad'i a zuciyarta sannan ta mayar ta ajiye tana sauke ajiyar zuciya a wahale,wayarta ta d'auka bayan ta kashe selfie masu matuk'ar kyau ta masa sending via chat,sai tayi ma kanta deactivation na fluorescence d'in ta nufi bed a mugun kasalance,dai² tana kwanciya a inda ya saba kwantawa sai ta shiga sauke gawurtaccen ajiyar zuciya had'e da matse pillow d'insa da yake ajiye kansa akai ta lumshe idanunta masu cike da bacci a hankali wani irin nauyayyen bacci ya sace ta.

A gefen Hammad kuwa lokacin ko da suka fito daga wanka,har suka kwanta hankalinsa na kan agogo yana hararar lokaci,da yake yasan babu wanda yasan da fitarsa a time d'in shi yasa sai ya jira yaga tayi bacci,after bacci ya kwasheta daya tabbatar baza ta tashi ba sai ya tashi ya sake kimtsawa,,gefen bed d'in da take kwance ya k'araso bayan ya gama yana yi mata wani irin kallon da yake sake narka masa zuciya,ak'alla ya b'ata lokaci sosai a kanta tsaye yana kallonta kafin ya farga,slowly sai ya d'ora mata peck a chicks d'inta sannan ya fice yana mata addu'ah kasancewa cikin farin ciki da nutsuwar rai ko da ta tashi bata same shi ba ya kasance bata ji damuwa ba sosai,,lokacin daya fito parlor akan k'aton wall clock idanunsa suka fara sauka inda lokaci ya nuna masa 12:36am,sauri² yayi ya fice dan almost 3 hours kenan da fitowarsa,a gaggaucen bayan ya fice dafa apartment d'in ya kulle mata k'ofar sai yayi gaggawar barin cikin ginin gaba d'aya.

Lokacin daya shigo cikin plaza bai iske kowa ba a hanyarsa ta shigowa har ya dawo office d'insa yana dubawa yaga still lokaci ya sake nuna masa 12:41am,within 5 kenan ya k'araso daga gidan zuwa Federal plaza d'in,ajiyar zuciya ya sauke sannan ya nufi inda kujerarsa take sai dai yana zama ko gama nutsuwa bai ba Sultan ya shigo da fad'in
"Dude.! Ina kaje ne haka nayi ta jiranka ban same kaba,yanzunma har na hak'ura na tafi kuma sai na hango kana dawowa.!"
D'agowa yayi ya kalli Sultan d'in fuskarsa d'auke da wani irin k'unsasshen murmushi ya shafi sumar kansa,ko da yake dai bai fito ya fad'i inda yaje d'inba amma tabbas kallo d'aya da Sultan yayi masa ya gama karance shi tsaf musamman ganin yadda yake murmusawa abun nayi masa dad'i sosai,sai kawai shima d'in yayi murmushi yana sake fad'in
"Hope.! Tana lafiya babu wani damuwa..!?"
D'agowa ya sake yi ya kalleshi sai kuma ya girgiza masa kai alamun babu damuwar yana lumshe idanunsa cikin wani irin shauk'i
"Haka muke fata,,Allah dai ya raba su lafiya.."

"Ameen" ya fad'a k'asa² yana sake

Please Login or Register in order to submit comment