Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi ya biyo shi a baya
"Kamar yaya zan iya tafiya..!? Idan na tafi naje ina..!?"
Tsaki yaja ba tare daya kalle shi ba yaci gaba da tafiya,while yana kallon napep da suke yawo a arean ko zaiga mai number da yaga ya d'auke ta.
Tun misalin k'arfe 5:00pm har aka fara kiran sallar Maghreb suna cikin arean Kwanar maggi,ba tare da sun ga abunda suke nema ba har aka idar da sallah,lokacin bayan sunyi sallah a wani masallaci dake gefen hanya,Sultan ya koma mota ya zauna dan shi dai Allah ya gani ba zai iya wannan zagayen azabar ba,,wasa² har k'arfe 9pm tayi suna cikin unguwar,,kuma har a that time Hammad yak'i yarda ya shigo su tafi gida tunda dai haifa abunda yake nema ba,gajiya Sultan yayi da masa maganar su tafi kawai ya d'auki waya ya kira Mamma dan yana sa yak'inin duk duniya itace mutum ta farko da zata cewa Hammad yayi,haka nan idan tace bari ba saita k'arasa ba zai bari d'in,,bayan sun gaisa da Mamma kai tsaye ya fad'a mata abunda ke faruwa,,suna gama maganar tace ya bata Hammad d'in suyi magana,lek'owa yayi a motar ya kirashi amma gogan yak'i yarda ya amsa masa,har sai da yace masa gavMamma akan line tana son magana da shi sannan ya juyo da sauri ya karb'i wayar,a kunnensa yasa tun kafin yayi magana ta furta
"Hammad..! Duk inda kuke yanzun ina son ganin ku.."

"Buh Mah..!"

"Bance ka bani ko wane irin excuse ba,abunda kawai nace shi ne,i want see u now.!"

"Ok.! Mah..Gamu nan dawowa.."
Katse wayar tayi,cikin jin haushi shima ya cillawa Sultan wayarsa sannan ya bud'e motar ya shiga,tun daya zauna bai sake magana ba har Sultan yayi reverse suka d'auki hanyar komawa gida.

Tana zaune a tsakar gida da littafin physics a gabanta,a zahiri duk wanda ya kalleta tabbas zaiyi zaton karatu take,sai dai a wannan lokacin sam zuciyarta bata tare da abunda idanunta ke kallo,,daga d'ayan gefen kuma Babanta da Innarta ne bisa tabarma suna hira,yayin da radio take nata b'ab'atun a kusa da Baba,,zuciyarta tayi nisa da gangar jikinta,zuwa cikin tunanin abunda a kowane rana shi ne aikinta,sai dai tunanin a yau ya sha bamban da sauran ranaku,tayi zurfi a duniyar tunanin dalilin rashi dawowarsa gare ta,,yaro ya shigo gidan da sallama,Inna da Baba ne suka amsa masa,yaro ya durk'usa har k'asa yana fad'in
"Wani ne yace yana sallama a k'ofar gida..!"
Baba ya kalli Inna yayin da itama take kallonsa dukansu fuskokinsu da mamaki,hankalin Baba akan Inna ya amsawa yaron ya tambayo wa ake nema,juyawa yaro yayi ya fita bayan y'an mintuna ya dawo yace
"Wai yace HAFSAH yake nema.."
Sake kallonsa Inna tayi shima ya kalleta kafin ya juya ga Sabina data k'ure littafi da ido
"Uwata..!"
Ya kira sunanta,sai dai sam bata ji ba,har kusan sau biyu yana maimaita kiranta duka bata ji shi ba
"SHALELE..!!"
Ya sake kira,firgigit tayi tana amsawa sannan ta ajiye littafin ta taso da sauri,girgiza kai kawai Inna tayi dan ita kam da jimawa ta gama fahimtar inda hankalinta ya tafi
"Kije ki duba k'ofar gida ana sallama.."
Amsawa tayicikin girmama maganar Baba ba tare data tsaya tambayar da waye ake sallama ko wa ake nema ba,ta zira hijab d'inta ta fita cike da son cika umarninsa,,a k'ofar gida kuwa lokacin data fita tsaye ta iske mutum ya jingina jikin mota,sai da tayi addu'ah bayan ta gama k'are masa kallo ko zata iya gane waye daga inda take,rashin wadataccen haske a gurin shi ne babban abunda ya hana mata ganin fuskarsa tun daga nesa,kai tsaye bisa umarnin zuciyarta ta fara takawa ta nufi inda yake tsaye.....



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_I really appreciate ur gesture of sending me this lovely gift.Thank u so much friend of mine *RABI'ATU SBS.*💞_

_It is time to party 💃🏻 after all that hard work.Congratulations.! *CWEET JANAF💕* I wish and pray that u always succeed in whatever u do.✊_

_Ina mik'a sak'on ta'aziyyata gare ki *CWEET LEEMA* fatan ubangiji yayi mata rahama,gafara tare da afuwa,,idan tamu tazo Ubangiji yasa mu cika da imani.👏_

*28.*
_#Conflict_


Lokacin da suka shigo gida a parlor suka tarar da Mamma tana jiransu,suna shigowa bayan sun gaisa da Sultan,ya nemi guri ya zauna,yayin da shi kuma gogan ya nufi hanyar barin gurin bcos duka yana jin ransa yana yi masa babu dad'i,so yana tunanin ba zai iya zama ba
"Hammad..!"
Mamma ta kira sunan sa dai² lokacin da yake d'aga k'afarsa d'aya,a bakin staircase ya tsaya yana runtse idanunsa ba tare daya amsa ba,ya d'auki kusan mintuna biyu a tsayen kafin ya iya juyowa,yafito shi tayi da hannu alamun yazo,guiwoyinsa a sanyaye ya dawo sannan ya nemi guri ya zauna d'an nesa dasu kad'an buh not far
"Mene ne matsalar kane..!?"
Tayi maganar tana kallonsu duka duk da a zahiri tana magana ne da Hammad,gyara zama Sultan yayi bayan ya kalle shi da niyyar bata amsa
"Mamma..! Wollahi nima abunda yake damuna kenan,,tun kafin yanzun na so ya sanar dani abunda yake damunsa,sai dai har yau bai bani damar sanin damuwarsa ba..Buh ban sani ba ko zuwa gaba idan zuciyarsa ta aminta daya sanar min.."
Kallonsa Mamma tayi da fuskar serious
"Baby..! Me yake damunka ne..!? Kasan ba tun yanzun kake b'oyemin damuwarka ba ko..!?"
Shiru yayi ya kasa magana,itama bata wani damu da shirun da yayi ba taci gaba da magana
"Baby.. Zaka sanar dani damuwarka ko kuma zaka jira Daddy ya dawo,,kaga sai ka sanar masa ko.!?"
Saurin d'agowa yayi ya kalleta,jinjina masa kai tayi alamun abunda ta fad'a d'in haka take nufi,marairaicewa ya fara yi
"Mamma.. Daddy fa..!?"

"Ehh! Mana ba haka kake so ba..!?"

"No Mah.. Duka fa ba yadda kike zato bane..!"

"Ba sai ka ce min wani abuba,,bcos na jima da sanin abunda yake damunka..So kawai dai na sa maka ido ne ina jiran ganin ranar da zaka sanar da ni,,ko dan kaga ban takura maka ba wannan karon,shi yasa kake tunanin b'oye min..!?"

"Mah..!"

"Yaro² ne,,tunanin k'in fad'a min da kayi zai sa na kasa fahimtar damuwarka..?? Bari to ni na fad'a maka dalilin rashin lafiyar ka yasa ni rabuwa da kai,ba don komai ba sai don bana son na haifar muku da damuwa,shi yasa na saka maka idanu,amma yanzhn lokaci yayi daya kamata ace munyi maganar..! Shin da gasks ne a dalilin *SO* ne kayi rashin lafiya..!?"
Saurin kallon Sultan yayi da fuskar tuhumakafad'a ya d'age masa alamun bashi da sani akan abunda yake son tuhumarsa
"Tambayarka nayi ba'ayi haka ba..!?"

"Mammah amma fa..!"

"Just answers..! Anyi ko ba'ayi ba..!?"

"Anyi Mah."

"Good..! Me yasa to ka kasa fahimtar duk boy'ewar da zaka yi ni d'in zan sani..!? Ko baka yi wannan tunanin ba..!?"
Shiru yayi bai amsa mata ba
"Shi kenan tunda ka maida ni surukarka,,shi yasa ma ka fara wasan b'uya dani ko..!?"
Dafe k'eyarsa yayi yana kallon k'asa dan yadda kalaman Mamma'n yasa jikinsa fara yin sanyi
"Bari mubar wannan maganar tunda naga kamar baka shirya yinta da ni ba..Kun san dalilin kiran da nake muku..!?"
Sultan yayi k'arfin halin amsawa da "A'a",bayani komai dake faruwa tayi musu nd kamar yadda idanunta suka gane mata videon da Daddy ya aiko mata,,bayan ta gama kuma tayi musu fatan alkhairi da samun nasara,Sosai Sultan ya nuna jin dad'i a fili da kasancewarsu masu nasara a cikin dubbanin wad'anda suka yi karatu tare,tabbas yana jin alamun nasararsu ne ya fara baytana,,kafin su rufe babin wancan maganar na farko suka fad'a kan batun yadda tafiyar tasu zai kasance,tun da suka fara magana ko "ehemm" Hammad bai furta ba har suka yi suka gama sannan Sultan yayi musu sallama ya tafi gida,hankalin Mamma akansa bayan fitar Sultan ta juyo tana kallonsa
"Baby..! Yanzun yaushe ne kuka yanke za kuyi tafiyar..!?"
D'agowa yayi saurin yi ya kalleta
"Mah! Ina zamu..!?"
Mamaki sosai akan fuskarta take kallonsa
"Ban gane ina zaku jeba..!? Baka san maganar da nake yi bane..!?"

"Banji ba Mah..! Buh me yake faruwa ne..!?"
Jinjina kai ta shiga yi tana kallonsa da mugun mamaki shimfid'e a saman fuskarta
"Baka ji komai ba kace.!?"

"Mamma da gaske fa ban san mene ne kuka ce ba.."
Sake jinjina kai tayi tana k'arewa fuskarsa kallo,tabbas daga dukkan alamu iya gaskiyar sa yake fad'a mata,nd shi ne abunda ta hango a cikin idanunsa,to amma idan har ace duk maganganun da suka yi da Sultan bai ji komai ba,ina hankalinsa yake a lokacin..!?
"Mah..! Baki ce komai ba.."
Magannar da yayi ita ta dawo da ita hayyacinta
"No..! Ba saina sake maimaitawa ba,ka jira idan Daddy ya kiraka zaka ji komai a bakinsa,,ehmm! Dama yace min yana kiran wayoyinka a kashe..Shin akwai dalilin da yasa ka kashe waya..!?"

"Babu Mah,kawai dai.."
Sai yayi shiru kuma yana sunkuyar da kai k'asa
"Kawai dai me..!?"
D'agowa yayi ya d'an saci kallonta
"Nothing Mah.."

"Uhhuumm..!" Tace daga haka kuma sai bata sake magana ba,shima d'in shiru yayi a zatonsa zata sake yin maganar amma sai yaga gaba d'aya ma bata da niyyar cewa wani abu,hak'ura yayi da yaga bata da niyyar yin ko da kwakwkwaran motsi yayi mata sallama sannan ya wuce bedroom.

Har ta k'arasa kusa da inda yake bata gane ko fuskar waye a tsaye a gurin ba,sallama tayi a daf da shi cikin sanyin muryanta tana sake watsa idanunta a kansa
"Barka da fitowa ranki ya dad'e.."
Muryansa ya daki kunnenta,tunanin inda tasan muryan kwakwalwarta ta tafi yi,a lokacin da zuciyarta kuma take tambayarta
"Shin ia nasan mai irin wannan muryan..!?"
Tayi furucin cikin salon son ganowa,shirun da tayi bata tanka ba yasa shi juyowa sosai yana fuskantar ta
"Ranki ya dad'e fatan kina lafiya,,ya mutanen gida..!? Nd ya kika dawo gida..?"
Damm.! Taji k'irjinta ya buga a sakamon muryan da taji a karo na biyu,wanda shi ne ya bata damar tuno ko muryan waye
"Mutumin da muka had'u d'azun,,shi ne yanzu yazo gidan mu kuma..?? Ta yaya aka yi ya san gidan mu..!?"
Kamar yasan abunda take tunani yana murmushi yake fad'in
"Kiyi hak'uri fa,,da fari dai barin gabatar miki da kaina ko..!?"

"Ba buk'atar haka..!"
Tayi saurin katse shi ba tare data ko kalli inda yake ba,da mamaki shi kam yake kallonta cikin salon nuna damuwa ya furta
"Why not *My Lady..!?"*

K'irjinta ne ya sake bugawa sakamakon sunan da taji ya ambata,nan da nan taji kwakwalwarta tana sake tuno mata da ainihin wanda yake fad'ar sunan,dana tunaninsa take kan yi aka tura kiranta
"Kayi hak'uri.."
Ta fad'a tana kauda kai gefe saboda wani mugun haushinsa da tsayuwarta gaban wani ba shi ba ya haddasa mata
"Amm! Babu damuwa..Amma me yasa kike bani hak'uri..?"
Sai data ja dogon numfashi kafin ta iya furta
"Saboda a gidan mu an riga anyi min miji..!"
Wani wawan kallo ya mata cikin kid'imewa
"Ke d'in,, aka yiwa miji a gida..!?"
Kallonsa tayi itama tana sake tsuke fuska
"Ehh! Ko ban isa bane..!?"

"A'a..! Ni ina na isa na fad'i haka..!?"

"Ka isa mana,,tunda ai bakin kane,, kaga kenan kana da damar yarda ko ka k'aryata.."

"A'a..! Ranki ya dad'e mene ne abun rashin yarda,,tunda har kin fad'a kinga ai ban isa nace ba haka bane,,sai dai gaskiya bazan b'oye miki ba,Allah ya sani da gaske nake sonki shi yasa ko d'azun da muka had'u a abun hawa har munyi nisa naji bazan iya daurewa ba,kawai sai nabi umarnin zuciya ta akan na bi bayanki dan naga inda zaki je,,buh tun da Allah ya k'addara al'amarin yazo da haka,sannan Annabi (S.A.W) yayi mana hani akan nema cikin nema,,kinga kenan dole na hak'ura,saboda haka ina yi muku fatan alkhairi,,Allah yasa albarka,sannan idan lokaci yayi da fatan baza'a manta damu ba.."
Saurin kallonta tayi,not minded shima ya kalleta fuskarsa da murmushi
"Kada ki damu fa,,ni yanzun ina matsayin kamar yayan ki ne,ko ba haka ba..!? Kinga kenan idan babu soyayya ai ina ganin sai muyi zumunci ko..!?"
Murmushin k'arfin hali tayi masa a lokaci guda kuma tana girgiza masa kai duk da dai ba haka taso ba,sun d'an jima tsaye yana ta mata hira sai dai ita kam a gareta daga "Ehhh" sai "A'a" iya amsanta kenan idan yayi mata magana,har ya gaji dan kansa yayi mata sallama,bcos ya fahimci hankalinta duka baya kansa,sai da yaga shigarta gida sannan ya shige mota ya tafi.

Tun daga shigarta gida yanayin kallon da taga Inna da Baba suna binta da shi yasa kunya ta fara neman rufeta,sallamar tata ma a sad'ad'e tayi,bata jira kuma amsawarsu ba sum² ta wuce ciki,girgiza kai Inna tayi tana murmushi,kafin ta juyo ta kalli Baba da shirin yin magana yayi saurin taron numfashinta bcos ya fahimci akan abunda za tayi maganar
"Mairo..! Ba sai kince komai ba,in dai akan wannan maganar ne.."

"Amma Malam..! Me yasa za kace haka..!?"
Gyara zama Baban Sabina yayi daga kishingid'a zuwa zama sosai ya sake fuskantar ta
"Na san dai kisan da *ALK'AWARIN* dake kanmu..? Bayan nan kuma kin san ko waye ya k'ulla,,to dan haka idan har kin manta,ni ban manta ba saboda haka bari na sake tuna miki,,idan har baki manta ba Yaya Allah yayi masa rahama,kafin ya rasu shi ya bada auren Uwata ga Muhammadu,sannan wannan abu ba wai kai tsaye muka yi shi ba,saboda haka dan baya raye a yanzun,ba shi yake nuna zan gaza da cika masa *ALK'AWARIN* daya d'auka ba..Amma bari nayi miki y'ar tunatarwa game da muhimmancin rik'on amana da cika *ALKAWARI* la'alla ki sake fahimtar dalilin,a masulunce ko nace kamar yadda Allahu (S.W.T) yace acikin surutun-nisa'a (ayata 58):"Lallai ne Allah (S.W.T) yana umarninku da ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.Kuma idan zaku yi hukunci a tsakanin mutane,ku yi hukunci da adalci. Lallai ne,Allah madalla da abunda yake yi muku wa'azi da shi.Lallai ne Allah ya kasance mai ji ne,kuma mai gani".Dalilin saukan wannan aya kuwa shine,kafin ayi fathu makkah,ya kasance key (wato makullin) d'akin Ka'abah,yana wajen Uthman Ibn Talha.To a lokacin da akayi fathu Makkah kuma sai Manzon Allah ya cewa Uthman Ibn Talha ya bashi key d'in d'akin Allah mai alfarma(Ka'abah),sai ya bashi yana mai cewa 'AMANA' na baka,sai manzon Allah ya bud'e d'akin Ka'abah sannan ya fidda dukkan gumakan dake ciki.A dai² wannan lokacin kuma baffansa Abbas da Aliyyu (R.A) sai suka buk'aci makullin ya kasance a hannunsu,amma sai Annabi yak'i basu.Kamar yadda sayyadina Umar ya rawaito (R.A) yace Manzon Allah ya fito daga Ka'abah yana karanta wannan aya ta surutun-nisa'a kamar yadda fassaran ayan ya gabata,sannan sai ya mayarwa Uthman Ibn Talha makullin,wannan abun ya baiwa Uthman mamaki da sha'awa sosai,ya kuma sa masa k'aimi na ya karb'i addinin musulunci,tunda a matsayin manzon Allah (S.A.W) na wanda ya samu nasara akansu ya cika wannan amanan,ya nuna addinin na gaskiya ne,wannan dalilin yasa Uthman Ibn Talha yaji dad'in hakan sosai kuma anan take ya shiga musulunci,ma'ana ya karb'i kalmar shahada..Anas (R.A) ya rawaito cewa ba kasafai manzon Allah yake khud'ubah ba,face sai ya ambaci cika *ALK'AWARI* da rik'on *AMANA*.."
Kabbara Inna tayi cikin jin dad'in k'issar da Baba ya bata,ko kafin ta kaiga sake yin magana nan ya d'ora da fad'in
"Saboda haka nake son ki k'ara sani akan wanda kika yi,matsawar kika ga an fasa auren yaran nan ko bai yuwu ba kamar yadda Yaya yayi buri,to ki tabbatar cikin biyu aka samu d'aya,ko dai ace yaron nan da kansa yazo yace ya fasa,ko kuma ya zama bana raye..Tabbas wad'annan dalilan su kad'ai ne nake tunanin zasu sa kiji an fasa wannan auren.."
Jikin Inna a sanyaye ta kalle shi duk da k'issar daya bata ta tab'a mata zuciya,sannan kuma tana jin akwai maganganu sosai a bakinta,sai dai hujjar daya kafa mata tasa taji jijiyon jikinta duk sun sake d'aure ta,harma taji baza ta iya sake cewa komai ba.

Yana shiga bedroom kayan jikinsa yayi k'ok'arin cirewa,d'aure da towel daya tsaya masa iya waist ya zauna gefen bed,yana tunano yadda AL'AMARIN ya faru,tabbas badon sab'anin da aka samu ba,yasan babu yadda za'ayi ya kasa had'uwa da ita,yayi nisa cikin tunaninta hoton fuskarta ya sake dawo masa kamar yanzun ne take gabansa,fuskar nan cike da fara'a,runtse idanunsa yayi saurin yi yana cusa yatsunsa duka a cikin sumar kansa,lokacin guda kuma tuna ko waye take ma murmushin ya sake haddasa masa jin babu dad'i,tsaki yaja mai sauti a lokaci d'aya ya kaiwa iska bugu
"Lallai akwai matsala duk ranar da na sake ganin kin sake yima wani makamancin wannan murmushin.."
Ya fad'a a fili lokacin da yake mik'ewa ya nufi hanyar bathroom,after some minutes ya fito jikinsa jik'e da ruwa alamun dake nuna wanka yayi,slowly yake tafiya jikinsa na motsawa,sai dai ba kowa zai gane hakan ba bcos motsawa ne yake yi irin ba sosai ba d'in nan yanayin dai cike yake da bada sha'awa,tamkar wani gawurtaccen jarumi,,a gurguje yayi shirin bacci saboda yadda zuciyarsa take a cunkushe,yana gama murza lotions ya feshe jikinsa da turarukan sa yabi lafiyar bed,damuwa na sake masa barazana,ba tare daya bi ko takan pyjamas d'insa daya ajiye ba,yayi kwanciyarsa daga shi sai boxes da armless,idanunsa a kulle damuwoyin da yake ta k'ok'arin kaucema suka fara kawo masa ziyara,baccinma ba dan kasancewarsa b'arawo ba,da sai yace bai san lokacin da yayi shi ba.

Wasa² tun daga wannan ranar ak'alla sai daya d'auki tsawon kwanaki uku yana zagaye a cikin unguwar *KWANAR MAGGI* ba tare da yaga wani daya san su ba,ko even su d'inma,,kullum ta Allah kuma idan yaje bai samu gano inda suke ba,baya tab'a hak'ura gobe ma haka zai sake d'aukan jiki ya tafi,sai dai kullum amsan d'aya ne,baya had'uwa da even a single man da yasan su,a haka har aka kwana uku.

A b'angaren Daddy kuwa tun bayan da suka yi magana da Mamma lokacin daya tambayeta dalilin da yasa Hammad ya kashe waya,tace masa bata sani ba sai dai tayi magana itama akan matsalar,sannan ta sanar da shi sak'onsa,wanda shi ne dalilin da yasa Daddy'n yake ta tsammanin ganin ya kira shi tunda shi idan ya kira baya samunsa,sai dai shiru har yanzun kamar an shuka dusa,nd itan kuma suk lokacin da yayi magana da ita tace ta sanar masa,saboda haka ne sai ya kasa gane waye mai gaskiyar a tsakaninsu,sh baiji daga gare shi ba,ita kuma tana sake tabbatar masa ta fad'i sak'onsa,wannan dalilin yasa ko daya sake kiranta,yadda Mamma bata zato haka yayi ta mata fad'an da bata san dalilinsa ba,shiru tayi masa sai da ta bari yayi ya gama sannan ta bashi hak'uri,,katse kiran yayi dan yadda tayi masa magana wisely nd calmly yasa shi jin bazai iya jurewa hakan ba,,yana kashe wayan itama Mamma a nata gefen,ajiyar zuciya ta saki,sannan ta k'udurce a ranta yau ko mene ne zai faru dole ne ta gwadawa Hammad jan ido,bcos tana ganin zai fi fahimtar abunda take son sanar da shi.....


*Aradun Allah kwanakin nan ciwon kasala ke damuna,dana fara typing sai na fara jin gajiya,dole tasa ni ajiyewa,,,buh kuyi hak'uri da ni,nd pray for me,Allah ya yaye min..Please.!*


#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*Alhamdulillah..! Am stepping toward shifa'a..👏 Masoyana a duk inda kuke ina matuk'ar godiya da addu'o'inku gare ni,fatan rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa. Na gode³ sosai.💗*

*29.*
_#Life alteration 2_

Washe gari da safe a parlor Mamma ta zauna gudun kada ya fice a gidan bata sani ba yasa ta zauna dakon fitowarsa,ko cikakkun mintuna biyar bata d'auka da zamanta a gurin ba sai gashi cikin sauri² yana shirin fita,a tsaitsaye ya gaida ita ba tare daya zauna ba ya kama hanyar fita da sauri,tana kallonsa tak'i yin magana har sai data bari yaje daf da k'ofa zai fita sannan ta kira sunansa,tsayawa yayi cak a inda yake kafin ya juyo a hankali cikin mutuwar jiki ya kalleta fuskarsa da alamun damuwa
"Mah.! Na zo ne..!?"
Kai ta girgiza masa,cikin sanyi ya dawo ya nemi saman armchair ya zauna yana fuskantarta da jiran jin me zata fad'a,duk jinsa yayi masa wani iri haka nan ya kasa d'aga kai ya kalleta
"Ina zaka je by this time around kake sauri..!?"
Maganarta ta katse masa tunanin da yake yi,saurin d'agowa yayi ya kalleta,sai dai ko inda yake bata d'aga kai ba bare yasa ran zata kalle shi,saima sake had'e rai da tayi coz bata son bashi fuska
"Kai nake sauraro,,ka tsaya kallo na..!"
Had'iye yahu ya fara yi da kyar sannan cikin sanyi ya furta
"Mamma..! Unguwa zamu je..!?"

"Kai da waye..!?"

"Amm! Tare da Sultan ne.."

"Uhmmm..! Ina ne unguwar da zaku je d'in..!?"
Shiru yayi yana nazarin inda zai ce,zuwa can dabara ta fad'o masa a rai
"Mah..! Gidan su Sadeeq nefa zamu je.."
Kallon rashin yarda da abunda ya fad'a tayi masa kana tace
"Ka tabbatar abunda ka fad'a haka ne..!?"
Shiru ya sake yi sannan ya d'an girgiza kai followed by
"Ehh Mah.."

"Ok..Allah ya tsare hanya,buh make sure ka kunna wayoyinka,idan kuma ba haka ba wollahi thumma billahi,kaji dai rantsuwa nayi ko..?"



Please Login or Register in order to submit comment