Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*41.*
_#Jealousness_

Bayyanannen murmushi yayi lokacin daya tuna da maganganun Daddy lokacin daya kirashi bedroom d'insa,ko da yake bai bada hankalinsa a gurin ba,amma tabbas yaji da kunnensa lokacin da Daddy yake shaida masa lallai² yaje yaga yarinyar a yau kafin nan da ranar d'aurin aure,sai dai kuma bayan fitowarsa daga gurin san sai ya iske abunda ya tada masa hankali,wanda shi ne batun tafiyarta gida,a lokacin ya fito yana mitar dalilinsa zaisa Dad ya tashe shi daga zaman jiranta sannan kuma yanzun yace zai tilasta masa yin abunda bai yi niyyaba,wannan dalilin yasa ko daya fita sai bai zame ko ina ba ya nufi gurin tsuntsuwarsa,itama d'in kuma duk da marmarin ganinta da yake da yaje d'in ta nemi chaja masa hankali,dan ma dai Allah yaso bai biye mata ba ya maida ita kamar wani abun wasan yara,,murmushi ya sake yi a hankali ya kai hannunsa saman short sides with side swept haircut da aka masa tun a U.S yana shafawa,bayan wucewar kamar mintuna biyu kuma sai ya sake d'age kai zuwa sama cikin yanayi na mai tunani kafin yayi magana a fili yana mai fad'in
"Yah rabb.! Kai kake bayarwa,kuma kai kake hanawa,mu bayinka ne gajiyayyu kuma mak'ask'anta,rok'o na a gare ka a kowane lokaci na tsinci kaina a gareka shi ne ka amince min,ka datar dani ta hanyar wadata rayuwata da abunda ya kasance mafi alkhairi a gare ni,,yah ubangijina yadda ka tsara shi ne dai² mu banyinka ne,a koda yaushe k'addarawarka da hukuncin ka a garemu shi ne dai² kuma shi ne abun binmu,,na tabbata kai kad'ai ka barwa kanka sanin dalilin da yasa ka dasa soyayya a tsakanin wad'annan bayin naka,dan haka kai kake da ikon juya dukkan lamuran su kasance a yadda ka tsarasu,,ya rabbi a wannan karon ina rok'on ka kamar yadda na sabarwa zuciyata da yi maka biyayya,daka amince min ta kasance mallakina.!"
Sai da yayi addu'o'insa kafin daga bisani ya kama hanyar bathroom jikinsa babu wadataccen kuzari,,bayan yayi wanka ya shirya kansa tsaf cikin pajamas d'insa masu matuk'ar kyau sannan ya d'auki d'aya a cikin wayoyinsa ya fara dialing number Badra,wacce a lokacin tuni tayi nisa a duniyar bacci,kiransa ya farkar da ita,lalubawa tayi kusa da ita daga inda take ajiye wayar ta d'auko ta,ba tare data iya bud'e idanunta ba tayi answering call d'in cikin muryar bacci tace
"Hello.! Wane ne a kan layi..!?"
Shiru ya d'anyi yana nazartarta kafin yace
"Bacci kike yi ne Yallab'iya..!?"
Muryarsa ce tasa ta mutsike idanunta da sauri ta tashi ta zauna tana waige²
"Yah Hammad..!"
Ta fad'a da muryar tsoro
"Ya akayi..!?"
Ya tambaya cikin wannan husky voice d'in nasa na asali,bata iya bashi amsa sai dai tayi saurin cewa
"Babu komai."
Siririn tsaki yayi sannan yace
"Ok.. Ki turomin number k'awar ki yanzun..!"

"Toh" tace masa dan ta fahimci wacce yake nufin,tun kafin tayi wani abu tuni har ya katse kiran daga b'angarensa,zugum Badra tayi tana bin wayarta da kallo,yayin da ta zabga tahumi da duka hannayenta tana kallon kiran wayar daya katse,cikin ranta take ayyanawa ita kam ayinin yau gaba d'aya ta kasa fahimtar abunda yake shirin faruwa a tsakanin yayan nata da kuma k'awar tata,sannan gashi bata san wane ne ya dace ace ta tunkara da batun ba a cikin su biyun,shin haka kenan zata yi ta zama cikin duhu,ko kuwa zata yi k'ok'arin tambayar d'aya a cikinsu ne.? Saurin girgiza kai tayi a fili tace
"Gaskiya duka babu wanda zai yiwu,,nasan halin yah Hammad,babu ta yadda za'ayi ma na iya masa maganar."
Saurin d'aga kai tayi da fad'in
"To.! ko princess d'in zan tambaya ne tayi min bayanin abunda yake tsakaninsu.?"
Shiru ta sake yi tana tunani,a cikin wannan yanayin na damuwa wani kiran ya sake shigo mata,k'arar da wayar tayi shi ya taimaka mata wajen dawo da ita daga tunanin data tafi,,Yah Hammad shi ne sunan da mai kiran ya bayyanar,cikin sauri ta sake answering call d'in nasa
"Da Allah kin san ke nake jira,shi ne zaki tsaya b'ata min lokaci..? Mene ne yasa baki turo min bane har yanzun,,ko kuma dai so kike nazo da kaina na amsa.?"
Cikin b'arin jiki da murya tace
"A'a A'a,, yah! Ba sai ka zo ba.."

"In banda iskanci ma nace kiyi min abu da sauri shi ne sai kin sani jiranki..?? Da me kike yi da baki turo ba har tsayin mintuna uku..?"
A sanyaye tace
"Kayi hak'uri.."

"Ki rik'e hakur'in ki ni kiyi min abunda na saki.. Saura ki bari na sake kira,kin san dai abunda zai biyo baya.."
Tana niyyar bashi hak'uri,ya sake kashe wayar ba tare daya jira cewarta ba,,contact lists d'inta ta shiga tana duba number,bayan ta duba d'in tayi masa sharing via text message,sak'on yana nuna mata ya tafi ta sauke ajiyar zuciya da fad'in
"Alhamdulillah alaa kulli halin..!"
Idanunta ta d'an runtse a hankali ta d'aga kanta zuwa kan agogo
"Ohh.! Ashe har yanzun dare ma baiyi ba..!"
Ta fad'a tana yamutse fuska kafin ta koma ta sake kwanciya.

Yana tsaye har lokacin da wayar a hannunsa sak'on ya fad'o,da azama ya bankad'e shi dan dama shi yake jira,sunan da ya gani ne yasa shi yin murmushi a fili yayi magana da fad'in
"Wow..! Kid sis,,lallai kin cancanta da ayi miki kyauta."
Bai k'arasa maganar ba sai da wayar a jikin kunnensa,,yadda kiran yake sounding haka zuciyarsa taje bugawa,amma har kiran ya katse ba'a d'auka ba sai daya sake maimaita kira kafin ta d'auka muryarta a nutse tayi sallama without tasan waye mai kiran sai dai tana jin fad'uwar gaba,kamilalliyar ajiyar zuciya yayi a lokaci guda yana had'awa da lumshe idanunsa ya amsa mata,a bazata taji muryarsa,cikin tsantsan mamaki tace
"Kai ne..!?"

"Ehh! Nine mana,,yaya akayi ne..? Kin yi mamakin jina ne kike tambaya.?"

"A'a.! To akan mene ne ma zanyi mamakin.?"
Lafiyayyen murmushi yayi wanda sai da taji sautin fitarsa har cikin kwakwalwarta yace
"Abunda zance kenan ai,mene ne daga jina zaisa kiyi mamaki..?"

"Uhhuumm.!" Tace ba tare da tayi magana ba,jin yanayin yadda tayi masa response yasa cikin d'aga muryansa kad'an amma ba cikin yanayin hayaniya ba yace
"Hey Lady.! Speak ur mind.."

"Nace me kenan..!?"

"Duk abunda yake ranki.."

"Ni kam babu abunda yake raina bare asani na fad'a.."

"Akwai.." Yace mata cikin sauri

Tace "babu" sake cewa yayi "akwai" itama tace "babu",ya sake fad'a ta maimaita masa "babu",murmushi ya saki mai sauti wanda yasa numfashinta tafiya yajin aiki ya dawo a lokaci guda,kafin ta farga kuma ya watso mata tambayar
"Ni d'in kuma ina kika ajiye ni ma'am.??"

"Da a ina nace na ajiye ka ne..!?"
Kamar mai son tunawa ya d'anyi jim sai kuma yayi saurin cewa
"Cikin zuciyarki.."

"Ban fad'a maka haka ba,ni kada kayi min sharri kace na fad'a.."

"Da gaske baki fad'a ba..?"

"Ehh!" Tayi saurin bashi amsa

"Mene ne kike wani bani amsa a gaggauce ne..!?"
A zahiri tayi murmushi sai dai ba mai ba saboda yadda taji yayi maganar kamar wani soko sai taji kamar yana ganinta ta daure tace
"Mene ne kuwa daya wuce son kwanciya da nake yi."
Siririyar ajiyar zuciya yayi har cikin ransa sai da yaji batun son ajiye wayar da tayi bai masa ba,amma a hakan duk dan baya so ya takurata sai yace
"Bacci..!?"
Tace masa "Ehh!",d'an lumshe idonsa ya sake yi yana rik'o lower lip d'insa zuwa cikin na saman ya danne da hak'oransa,slowly bayan yayi masa wani irin tsotsar daya bada sauti mai ma'ana kafin yace
"Ok.. A huta gajiya ko.. Sai na zo..?"
Cike da zolaya bcos ita kanta bata gaji da sauraren muryarsa ba kuma bata shiryawa rabuwa da shi da gaggawa ba tayi caraf tace
"Mene ne zai kawo kane..??"

"Kina tambayata me zanzo na yine..!?"

"Ehh! Ai dole nabi ba'asi ne.."

"Uhhuumm.!" Yayi ajiyar numfashin da yasa ta lumshe ido saboda tsigar jikinta da taji ta fara tashi
"Ki jira idan nazo sai ki sake kallona ki maimaita tambayar ki,,na tabbata zaki samu amsar daya dace.. Kin ji ko..?"

"Toh" ta amsa,daga nan suka yi shiru duka har na tsayin lokaci,suna sauraren fitar numfashin juna,,shirun ne ya d'an dame shi,muryarsa kamar yana mata rad'a ko son yin bacci yace
"Lady..! Anya kina sona har yanzun kamar yadda nake yi..!?"

"A'a.. Bana yi ni dai.!"
Amsar yaji kamar fitar kibiya daga bakinta,duk da yasan fad'a kawai tayi amma take yaji jikinsa yayi masa wani iri kamar ana watsa masa narkakken ruwan dalma
"Me yasa kika daina..??"

"Saboda baka yiwa zuciyata adalci ba,a lokacin daya dace ace ta samu y'ancin kanta.."
Idanunsa yayi saurin bud'ewa yana kallon sama
"Me yasa zaki ce haka.?"

"Me yasa bazan ce ba,bayan abu ne daya riga ya faru.."

"Mene ne ya farun..??"

"Kaima ai kasan ko mene ne d'in ya faru.. Mene ne na tambaya ta.? Ko zaka cene baka sani ba..?"

"Ban sani ba,,d'an taimaka ki fad'a min,kin jiiii ladyyy..!"
Yadda yaja sunan sai daya sata sakin wahalalliyar ajiyar zuciyar da sai da taji inama ace yana kusa da ina,a hankali ta rufe itanunta had'e da fad'awa da baya a saman k'atuwar katigarta ta k'arasa kwanciya flat
"Mene ne ya faru lady..??"
Idanunta har lokacin a lumshe tace
"Me ka gani..??"

"Tambayarki nayi,,nd baki bani amsa ba kina min wata tambayar.. Fara bani amsar tambayata first,,sai ki tambaye ni.."
Murmushi tayi saboda yadda take jin dad'in firar,a hankali tace
"Babu abunda ya faru.."

"Ban yarda ba."

"Ka yarda babu..!"

"Ok.. Tunda baki yi niyyar na sani ba.. Amm baki bani amsar tambayar da nayi ba."

"Yaushe..??"

"D'azun." Ya fad'a yana sauraronta

"Mene ne ka tambaya ban fad'a maka ba..?"

"Kince banyiwa zuciyarki adalci ba,,shin wane irin adalci ne na kasa yi mata.?"

"Uhhuumm.! Mu bar wannan maganar."

"Me yasa za'a barta..?"

"Haka nan naji bana son ayi.."
Murmushi yayi k'asa² bayan yayi wani tunani sannan cikin zolaya yace
"Ok.. An barta tunda bakya buk'ata,,,buh nace za dai kizo aurena ko.?"
Wani haushinsa ne ya sake kunno mata wuyar kishinsa a zuciyarta,musamman kuma daya tuna mata da batun da take k'ok'arin mantawa a dai² lokacin da giyar soyayyarsa ta fara watangariri da ita cikin iska,a hasale ta taso masa tace
"Nazo nayi mene ne..??"

"Ki tayani farin ciki mana.. Ai zaki zo ko..?"

"Bazan zo ba.."
Ta sake bashi amsa a hasale
"Me yasa to..? Baza ki taya ni farin ciki ba kenan..?"

"Kada Allah sa kuyi farin cikin,,to ni inama ruwanna da aurenka..?? Kaje kayi tayi mana sai me.? Sauk'in nima dai ina da mai sona..!"
Tana fad'a tsabar takaicin maganar dake sussukar ta a zuciya duk da kasancewar ta bashi amsa ji tayi hakan bai mata ba sai data had'a d'a kashe wayar,a fusace tayi cilli da ita gefe had'e da fashewa da kuka.

A b'angaren Hammad yadda ya kunnota lokaci guda tana masifa ba k'aramin burgeshi ta sake yi ba,shi dai yana son yaga tana magana da shi babu kunya babu komai musamman kuma akan idonsa a cikin yanayin fushi abun sosai yake k'ayatar da shi,,lumshe idanunsa ya sake yi yayin da ya tafi tunanin moment d'insu daya gabata a d'azun da yaje gurinta,,murmushi ya sake yi mai sauti a hankali ya mik'e yana sosa k'eyarsa da aka babu gashi a gurin saboda yanayin haircut d'in da aka masa,sanda ya gama duk abunda yake kafin ya ajiye komai da yake ya fita zuwa bedroom d'in Mamma'nsa,,lokacin daya shiga a sanan gado ya sameta cikin shirinta na bacci har tama kwanta sai dai da alamun kamar akwai muhimmin aikin da take yi akan waya,sannan duka kamar bata da niyyar ziyartar d'akin Daddy'nsu,da sallama ya k'arasa inda take,bayan ya gaisheta ta amsa masa da kulawa sosai kana ta ajiye wayar a gefe ta fuskance shi
"Ba dai sai yanzun ka dawo ba ko..!?"

"A'a Mah.! Na d'an jima da shigowa,akwai dai aikin dana tsaya yi ne shi yasa ban samu damar shigowa da wuri ba.."
K'ayataccen murmushi tayi masa had'e da tambayarsa yaya ya baro su,ya bata amsa dai² abunda idanunsa suka gane masa,,daga nan suka fad'a hira kafin ya tambayeta yadda suka yi da Daddy,,ranta ne ya d'an b'aci tunawa da yadda suka k'are ta da shi,duk da dai ta nemo mafita kafin lokacin amma tana jin babu dad'i game da halayyar da yake gwadawa akansu,,a nan ta kwashe duk yadda sukayi ta sanar masa,sai dai ta b'oye masa batun Dad da yace mata dole ne Hammad d'in ya rabu da ita ko da kuwa da zinare aka k'erata ya haramtawa maaa aurenta tunda har akanta yake neman yayi jayayya da shi,haka nan batun kiran Malam da tayi shima ta kyale akan gobe idan yazo duka sa ganshi gudunma kada a samu matsala,bawai don tana zargin za'a samu wani ya kaiwa Daddy gulmar ta kai k'ararsa gurin Malam d'inba,sai dan gudun abunda zai faru kafin wayewar garin.
Godiya sosai Hammad yayiwa Mamma cikin tsananin farin ciki ya kwanta a jikinta yana sanar mata murmushi,kansa ta shafa tana masa murmushi itama,ba ita ta kyale shi ya tafi ba sai data tabbatar ta sake kwantar masa da hankali ta hanyar nuna masa amincewarta akna kada yaji tsoro wajen yin abunda zuciyarsa take so,itan zata tsaya masa,sannan suka yi sallama ya tafi bedroom d'insa cikin tsananin farin ciki da goyon bayanta akan neman auren nasa daya taso da shi gadangadan.
Lokacin daya dawo tsabar farin ciki ne yasa gaba d'aya ya manta da abunda ya faru tsakaninsu d'azun kafin ya tafi gurin Mamma,kai tsaye ko daya shigo sai ya sake d'aukar waya ya kirata,sai dai har yayi mata misscall uku bata d'auka ba,,haka yayi ta kira tana kallo saboda tsabar fushi da kishin daya rufe mata ido tak'i amsa masa,dan kansa ko daya kira bata d'auka ba sai ya hak'ura bai sake kira ba ya ajiye wayar bisan bedside drawer,,saman bed d'insa ya haye yana sakin murmushi da fatan ganin wayewar gari lafiya bcos yasan goben nan akwai kafcen da za'ayi a gidan.
(Ni kuwa dai nace danma wasu ya sani bai san wasu ba).

Lokacin daya gama zama yana k'ok'arin d'age bedspread ya rufe k'afafunsa kira ya shigo masa,,bai d'ago ya kalli wayar ba sai da yayi murmushi sannan ya ajiye bedspread d'in yana d'aukar wayar a zatonsa itace take kiran nasa,sai yayi gamo da *NEW NUMBER* yana yawo saman screen d'in wayar,haka nan ya sawa number ido kamar mai nazari shi bai d'auka ba kuma bau katse ba,har sai da kiran ya katse,siririyar ajiyar zuciya yayi yana niyyar ajiye wayar ya kwanta wani kiran ya sake shigo masa,kamar kada ya d'auki wayar haka yaji,nan take nasihar Mamma ta dawo masa cikin kwakwalwarsa akan babu kyau wulak'anci,d'aukar kiran yayi yasa wayar a hands free had'e da yin sallama,cikin siririyar muryarta kamar ta k'ananun yara sosai tace
"Hello..!"
Shiru yayi yana nazartar muryar,kafin yayi magana ta sake maimaita fad'in "hello" muryarta kamar ta mutumin dake shirin yin kuka,siririn tsaki ya saki a ciki ya katse kiran wayar,yana niyyar ajiyewa aka sake kira,d'agawa yayi da sallama cikin yanayin son rashin magana,amsawa tayi tana sakin sanyayyar ajiyar zuciya da fad'in
"My hero.. Ya kake..?"
Jimm yayi yana tunanin wace ce ita kafin ya ce
"Wace ce ke d'in..??"

"Kaii.! Yah Hammad,ko number na ma baka da shi..??"

"Ehhh!" Yace kai tsaye yana sake tambaya
"Wai wace ce ke d'in da kike magana.??"
Duk da taji haushin tambayar amma haka nan ta daure tace masa
*"FALISHA* ce.."

"Daga ina kenan..??"
Ji tayi jikinta ya hau rawa,alamun daya tabbatar mata ko sunanta ma bai sani ba,bare kuma itan kanta,to wai ita kenan wane irin aure ne za tayi,al'halin mijin ma ko saninta bai yi ba.?? Hawaye taji suna gangaro mata a hankali cikin dauriya tace
"Ur wife to be..!"

"Uhhuumm..! Yayi,to ya kike..?"

"Lafiya k'alau.. Kai fa.? Fatan kana lafiya..?"

"Lafiya." Yace cikin alamun gajiya da magana kafin yace
"Sai da safe..??"
Cikin sauri ta tare shi da fad'in
"Haba Yaya,,me yasa zaka kashe wayan tun yanzun..?? Bayan kai ne ma ya kamata ace ka fara kira na amma kak'i,shi ne kuma na kira zaka min wulak'anci.!?"

"Koh..!"
Ya tambaya babu damuwar komai a kan fuskarsa daga maganar da tayi
"Ehh.! Kuma ma dama kasa nayi ta jiranka amma kaki zuwa.."

"Waye yace miki da zanzo..??"

"Daddyna ya fad'a min zaka zo,amma baka zo ka ganni ba.. Me yasa haka to..? Nayi ta jiranka shiru,kuma nayi jiran ka kira shima baka yi ba,sai nice da na gaji da jira na kira.?"
Kai tsaye yace
"Naje zance ne.."

"Zance fa kace Yaya.."

"Ehh! Haka nace mana.."
Yawun azabar damuwa da bak'in kishi ta had'iye tana sake tambayarsa
"Ina ne kaje.."

"Gurin uwar gidan ki na fara zuwa na gano ta.."
A zabure tace
"Whatttt.!?"
Kyakykyawan murmushi ya saki da fad'in
"Mene ne..?? Kika tsorata..??"
Muryarta cikin alamun dake bayyanar da a kowane irin lokaci kuka yana daf da zuwa mata tace
"Yaya.! Wai har mu nawa ne,naji kana maganar uwar gida..??"

"Biyu." Ya bata amsa kai tsaye ba tare daya jira ba

"Amma ni Yaya ai ba haka aka cemin ba.."

"Ni kuma haka na tsara,,ko zaki hana ni yin tsarin da zuciyata take so ne..??"

"A'a..! To amma Yaya mene ne yasa zaka auremu mu biyu..??"

"Saboda ita nake muradin yin rayuwa da ita,,,ke kuma...!"



*Tofaaa..!😱 Lallai Hammad anyi sarkin masu fad'ar magana kai tsaye.. Dan Allah fan's idan ba rainin wayo ba,da raina ajin y'ar mutane,kujifa wani irin response daya bata,,shin dan Allah idan kece a matsayin FALISHA me zaki aikata a dai² irin wannan lokacin da kike tsammanin farin ciki,kika tsinci sab'anin sa...??*

*Ni dai gaskiya idan nice yadda komai yazo min k'arshe nan,duk abunda zaka yi bazan yi zuciya da kai na barwa wata geluwa ba..To amma kefa..?? Ku fa me kuka ce..?* 🤣

*#Reply as FALISHA...* 🧘🏻‍♀

*Aradu bani da isashen chaji sosai,sai dai kuyi managed da wannan...*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*42.*
_#Marriage seeking_

Shiru yayi saurin yi dan yasan idan har ya fad'a mata abunda yake zuciyarsa,aka yi rashin sa'a bakinta babu linzami maganar ta komawa Daddy za'a samu gagarumar matsala a tsakaninsu
"Ni kuma mene ne nawa matsayin Yayana..??"
Ta sake tambayarsa,banza yayi mata ba tare daya amsa mata tambayar da tayi ba,jin yadda yayi shiru yasa ta sake maimaitawa,a zatonta ko bai ji bane shi yasa yayi shirun,ajiyar numfashi yayi a hankali kafin yace
"Manta kawai..!"

"Yah.! Me yasa zan manta..?? Ni dai gaskiya ka fad'a min.."

"A'aahh.."
Takura masa ta nemi yi akan lallai ita tana so sai ya fad'a mata abunda yayi niyyar fad'an shi kuma yak'i,da yake dama tana kan hanya wannan dalilin yasa ta fashe masa da kuka da tunanin zai tausaya mata ya fad'a tunda taji k'awayenta na fad'a mata maza da yawa basa son kuka,wannan dalilin yasa tayi zaton shima Hammad yana cikin wannan ajin,amma sai taga ya nuna he don't care da kukanta ko shirunta,k'arshe ma yaji haushi ya kashe wayarsa ya rabu da ita tana aikin rusa kuka,,yana kashe wayar ya kai hannunsa saman forehead d'insa yana matsawa da sakin wahalallen numfashi kamar wanda yayi aikin k'arfi a fili saboda takaicin data bashi ya furta
"Huh.! Headache..!"
Ko gama rufe bakinsa bai yi ba wani kiran ya sake shigowa,a hankali ya saki dogon tsaki,cikin jin haushi ya d'auka yana cewa
"Yaa aka yi ne..?"
Sheshshek'ar kuka tayi cikin muryar ban tausayi tace
"Yah Hammad,,me yasa zaka min haka..?? I think duk mutumin dake k'aunarka bai kamata ace ka saka masa ta wannan hanyar ba.. Mene ne laifina dan ina sonka.? Don kawai ina sonka sai ka wulak'anta ni.. Ahhh..??"

"Wulak'ancin na mene ne..!?"

"Kana kashemin waya al'halin baka bari mun gama magana ba.."
Idanunsa ya tsayar guri guda yana sauraren yadda take magana da muryar kuka,cikin zuciyarsa banda haushin ta babu abunda ke mak'ale a cikinta,k'arin haushin ma yadda ta sashi gaba tana tuhumarsa,shi fa gaba d'aya a rayuwarsa yak'i jinin yaga ana kuka a kusa da shi,saboda tayar masa da hankali yake,buh idan kayi masa abun da ba dai² ba kuma ya hukunta dan kayi wannan ba zai sa yaji tausayin ka

Please Login or Register in order to submit comment