Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kad'an,,to kuma lokacin ma dai bayan da wa'adinsa ya cika,daya fito a haka ya koma gudanar da rayuwarsa,mutum mai jaye²n fad'a gaba d'aya sai gashi ya dawo mutum mai sanyin hali,,abokansa da komai ada tun daya fito bai sake neman kowa a cikinsu ba ya keb'e kansa,dan kuwa babban burinsa a kullum a yanzun shi ne ya samu yaga Sabina don yana son neman yafiyarta sosai,kuma yayi mata godiyar halaccin data yi masa a rayuwa.

*TANI* ma dai ba'a barta a baya ba,dan tun bayan da taga yadda Allah yayi da d'an da take ta yiwa mutane rashin mutunci dalilinsa,hankali ya shigeta tsarin rayuwarta da komai duk ta watsar ta koma mutuniyar Allah,a kullum idan tana tuno yadda suka rayu a k'auyen KAUSANI lokacin da suke ruga har zuwa dalilin dawowarsu birni sai tayi dana sani,,mutanen da take ganin basu da komai basu mallaki komai ba a rayuwa daya wuce *Y'A MACE* guda d'aya sai ga shi Allah ya d'aga darajarsu a dalilin samuwarta,har ta zame musu abar alfaharin da ita kanta suka mata rana,,haka nan idan ta tuna lokacin da suka dawo unguwar KAWO da zama bayan gwamnati ta basu gidajen zama da yadda ta asassa tada wutar lallai sai dai su raba muhalli da su Sabinar,da yadda ta tadawa su Baba hankali lokacin akan rabon diyyar Baffa da gwanati ta basu,wanda har ya janyo tasa Baban su LADO ya karb'i kason Hameed duk dan kada a zauna lafiya,sai taji duk yanzun bata san da wane irin ido ya kamata ta kallesu ta basu hak'uri ba,,a haka rayuwa taci gaba da tafiya musu idan sun had'u da Inna duk sai ta kasa sakewa tayi ta nok'ewa tana kauda kai cikin jin kunya,Inna kuwa ko data fahimceta nuna mata tayi ai babu komai tunda har Allah yasa ta gane gaskiya,shi yasa dama ake cewa duk abunda mutum yake tak'amar yana da shi to kada yayi wulak'anci akansa bcos wata rana baka san yaya rayuwa zata juya maka ba. Lokaci duk ya tafi da wasu damuwoyin da suka addabi family'n,yayin da farin ciki da k'aunar juna,yafiya da maida komai ba komai ba ya maye gurbin duk wata damuwar da take tattare da su fiye da shekaru.

A b'angaren Sabina ma zuwa wanman lokacin tuni cikinta ya fara girma,yanayin kulawar da take samu daga b'angaren Hammad da yaranta zuwa gudunmawar su Badra akanta abun na yi mata dad'i sosai,wani lokaci idan ta zauna tana kallonsu yadda suke tsara taron baby'n sai dai tayi ta dariya,dramar su da Hammad wanda yanzun bayan samuwar yara yasa ya sake sosai idan suna lissafi sai tayi ta dariya,shi kuma dama abunda yake buk'ata kenan a kullum ta kasance bata da wata damuwa a rayuwa.

*NIGERIA...*
Zuwa yanzun ko da lokaci yayi nisa,akalar rayuwar Hameed da Sulaiman gaba d'aya ta koma gidan su Sabina,dan tun bayan da aka kama LADO Baba ya tattara su ya maida su hannunsa,a yanzun shi yake kula da su da duk wasu al'smuran rayuwarsu,,sannan a bayan dawowarsun kasancewar tun da suka kammala secondary basu samu ci gaba ba sai buga² da suke duk da Baban lado yaso su ci gaba Tani ce ta hana shi yasa suke zaune haka nan,to yanzun kuma ko da suka dawo hannun Inna,sai ta nemi shawarar Sabina akan yadda take gani game da ci gaban kannen nata,bayan sunyi shawara ta sanar da Inna akan ta fara yin magana da Bana tukun abunda duk yace sai suyi magana akansa,to bayan sunyi maganar da Baban k'ima data fad'a mata anan take fad'awa Inna tana ganin kawai gara su baro k'asar,cos tana tunanin hakan zai sa su fi maida hankali sosai a kan karatun,amma idan suna zaune gida wata k'ila su saka shirme,,a lokacin bayan sun gama maganar hakan yasa sai ta shaidawa Innar zata sa a nema musu makarantar a nan U.S d'in,,,cikin hukuncin ubangiji kuma duka y'an kwanaki aka d'iba tsakanin maganar su tasa aka kammala musu komai,da yake ta can 9ja ma suna da Chamber k'ark'ashin Daddy sai basu sha wahala ba aka musu komai daya dace akan lokaci,bayan y'an satittika kuma suka taho bakin karatunsu inda su d'in suke k'ark'ashin school of science a nan KANSAS STATE UNIVERSITY.

LADO ma dai a nasa gefen lokacin daya ji labarin su Hameed zasu tafi k'asar waje karatu kuma k'ark'ashin kulawar Sabinar yayi kuka yayi dana sanin k'in tsayawa yayi karatu a lokacin da kowa yake bashi shawarar yayi wata rana zai amfaneshi amma sai yayi biris yak'i ji,sai gashi yanzun da lokacin da ake fad'a masa zai zo d'in yayi ya tashi a zero,,haka nan ko da yake tunawa da irin nasihohin baffa akansa yayi kuka sosai kuma yayi tir da irin rayuwar da yayi a baya,,to a irin ranakun da yake zuwa gurin Inna gaisheta ne,da yake tun bayan fitowar sa daga gidan kaso duk jumu'ah bayan sakkowa daga masjeed can yake wucewa ya yini,sai yake shaida mata damuwarsa a lokacin na son komawa yayi ilimi to amma kuma bai san yaya zai yi ba,nan Inna ta zaunar da shi ta sake yi masa fad'a da bashi shawarwarin da zasu taimaki rayuwarsa,,a nan d'in nema har ta sake k'arfafa masa guiwa akan ya nemi ilimin tunda su dai shekaru basa hana ilimi.
Tun daga ranar kuwa bayan ya tafi gida yake ta tunani da neman hanyar da zai inganta rayuwarsa,lokaci kad'an tsakani da kansa sai ya samu Baban Sabina ya fad'a masa batun son komawarsa makaranta,Baba ya bashi goyon baya had'e da yi masa nasiha sosai,,bayan wani lokaci LADO ya fad'a neman ilimin addini dana boko sosai,kuma cikin hukuncin Ubangiji da komawarsa karatun hakan sai yasa ya dage sosai saboda burinsa a yanzun shi ne ya inganta rayuwarsa ta yadda zai shafe duk wani tsatsa da bak'in painting daya b'ata masa rayuwa a baya.


*SOME YEARS LATER...*

Lokaci ya tafi yayin da rayuwa tayi kyau a ko wane gefe,,a b'angaren su Sabina da suke U.S yanzun kam tuni ta haife d'anta namiji wanda aka mayarwa da sunan Baffa wato *IBRAHIM* suna kiransa da *KHALEEL*,, soyayyarsu a yanzun da zaman da suke gudanarwa tsakaninta da Hammad harma da yaransu abun gwanin burgewa ne,kowa yana bawa kowa girma gami da mutunci dai² gwargwado,babu wulak'anci ko tozarci a zamansu,kullum ka gansu suna cikin farin ciki da nunawa juna kulawa.
A b'angaren su Badra,Jannat da Zeeharis ma haka rayuwa ta kasance musu,dan a wannan lokacin Badra yaranta biyu bayan Meenal,ta samu Daddy wato *ALIYU* (Ayman) da *MUHAMMAD* (Mukhtar) mai sunan Daddy'nsu Sultan,da yake tsakanin Ayman da Mukhtar bata samu tazara mai nisa ba shi yasa duka sai ta wuce su Jannat,,haka ma Jannat d'in itama ta sake haihuwar namiji wanda aka sa masa sunan Daddy'nta,Zee ma a yanzun haka tana tare da yaranta biyu Bayan Little Hammad ta samu mace mai sunan Mamanta,,rayuwa tayi musu dad'i,zamansu a NEW YORK gwanin burgewa,duka da yake zamansu a can yafi yawa shi yasa su da 9ja sai lokaci² idan sun samu hutu,ko k'arshen shekara su tattaro gaba d'aya.

Da yake duk weekend idan ya zagayo a zamansu sun saba ba a gida suke yinsa ba yasa tun da safiyar ranar Saturday d'in suke ta shirin fita,kasancewar duk zagayowar sati a irin wad'annan ranakun da kowane ma'aikaci yake hutu zaka ga ya tattara iyalinsa su fita shak'atawa,to suma din hakan sai ya zsme musu sabo,wani lokacin kuma maimakon shan iskar sai su shiga malls yin shopping kasancewar arean fifth avenue it has many luxury goods,fashion da kuma sport brand boutiques wad'anda suka had'a da irin su Louis vuitton,tiffany & co,gucci,prada,armani,salvatore ferragamo,nike,escada,rolex,lindt chocolate shop da kuma irin su oxford clothes.Idan kuma batun gurare ake na shan iska bayan Central park zoo,akwai irin su museum of modern art,washington square park nd Bryant park,,to yau d'in ma dai kamar kullum ne bayan duk sun gama kammala abubuwan da zasu buk'ata yaran su da suka girma,da iyayen maza suka fita da komai suka sa a motocin da zasu fita,kasancewar tuni sun jima da barin Trump Tawer,yanzun suna zaune ne a *KANSAS* duka dai a cikin New York d'in,,,lokacin da suka firo cikin ado suke matansu da maza irin na mutumin da hutu,gata gami da naira suka zaunawa,,daga nan kai tsaye sai suka d'auki hanyar *BRYANT PARK* dake 6th avenue,bcos yau can suka fi buk'atar zuwa.
Suna tafe a motocinsu kowa da nasa iyalin har suka shiga cikin park d'in,bayan duk sunyi parking sun fito,can daga gefe k'asan wasu irin bishiyu da suka bada inuwa sai suka shimfid'a k'aton mat da zai d'auke su,duk da a yanzun ak'alla jimillar su a 20 abunda babu kad'an ne kawai,to lokacin bayan sun zo kuma babu jimawa sai ga su Hameed nan suma sun k'araso da yake a cikin *KANSAS STATE UNIVERSITY* suke karatun su,kuma dai duk weekend idan za'ayi irin wannan fitar gaba d'ayan su suke had'uwa,nan jimillar su ya tada mutum ashirin cif daya bada family guda mai ban sha'awa.

Rayuwa tayi kyau ga kowa bayan tsayin lokaci,inda yanzun Hammad ya taka matsayin Ass. director a cibiyarsu,haka Sultan da Sadeeq suma sun k'ara samun matsayi mai girma bayan da suka kammala karatun PhD d'insu,a yanzun haka kuma so suke su sake taka zuwa matsayin Proffs,,Sabina da su Badra ma duk sun koma sunyi Master's d'insu,,,ko wane ahali suna cikin farin ciki,jin dad'i da nutsuwar rai wacce ta wanzu a tsakaninsu bayan irin k'alubalen da suka fuskanta a baya... They all lived happily ever after...

*KARSHE...*

Alhamdulillah..! Alhamdulillah alaa kulli halin.. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah (S.W.T),daya bani ikon zuwa k'arshen wannan labari nawa dana kira da *ALK'AWARIN JINI,* tsira da amincin Allah suci gaba da tabbata ga farin jakada babba dan Abdullah Annabi Muhammad (S.W.A) tare da ahalinsa da sahabbansa.

Ina mik'a sak'on jinjina da ban hak'uri ga mabiyana kuma mabiya wannan littafi,bisa jumurin saurarona da kuka yi babu dare babu rana,,fatan ubangiji yasa muyi koyi da dukkan wasu darussan da labarin yake d'auke da su,kura²i kuma muna fatan rabb ya yafe mana.
Bayan dogon lokacin dana d'auka na ganin na nishad'antar da masoyana,yau Ubangiji ya bani damar ajiye alk'alamina domin na huta. Abisa wannan damar dana samu nake sake godewa Allah (S.W.T) da irin baiwar da yayi a gare ni,Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat..👏

*YABON GWANI...*
Hassan Atk
Hussain Atk
Itz B.Y Ebraheem
Hayat Baba Zubair
Ku d'in ku ne gwanaye na,kuma abun alfahari na,idan har ina da mutanen daya kamata ace na ambata,a wannan dan tak'aitaccen rubutun nawa,tabbas ku ne farko,,bisa d'awainiya da kuke da litattafaina a social media,bani da bakin da zanyi muku godiya,sai dai har kullum ina yi muku fatan rabb ya saka muku da mafificin alkhairinsa ameen.

*FATAN ALK'HAIRI..*
Y'an uwana marubuta a duk inda kuke ina yi muku fatan alkhairi, ban cire ko mutum guda,wanda na sani da wanda ban sani ba,ina muku fatan alkhairin Allah ya ci gaba da kasancewa tare da ku.

*GODIYA TA MUSAMMAN GA...*
Alk'awarin jini fans 1&2,Smasher nd hubbeey novels,Novel's comment only,Leema fan's group,Aeshab Novel group,Xumunta novella,Sawwama Novels da sauran dukkanin groups da nake ciki na social media both Whatsapp,Facebook nd Wattpad wanda nake ciki da wanda bana ciki,wanda na ambata da wanda ban ambata ba,duka ina mik'a sak'on godiya ta gare ku da fatan alkhairi,ubangiji ya sake had'a fuskokinmu da alkhairinsa ameen.

Masoya rubutun Smasher a nan nake fatan sanar da ku zan barku ba don ina so ba,sai dan zuwan lokacin da ya zama lallai saina barkun,,A duk inda masoyana suke a fad'in duniya ina yi muku fatan alkhairi,sai Allah ya sake had'a mu a cikin labari na gaba da yardar Allah wanda na yiwa lak'abi da...

*'DAN MACE..!!*

Da haka nake fatan mu sake kasancewa tare da ku a cikin labarin *'Dan Mace* idan Allah ya ara mana rai da lokaci na ganin shigarmu sabuwar shekara lafiya..

*BISSALAAM...*


#Ur's Hawwa Muhammad Usman.
#Jeeddahmu898.
#Real Smasher.
#Oum Janan.
#Alk'awarin Jini.💘
#Blood pledged.❣
#Saturday 23/Nov,2019.
#End's @7:00pm GMT.

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Please Login or Register in order to submit comment