Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da damuwar daya saurara,amma tunda sunyi shiru shima bari yayi musu bakam.

*PENNSYLVANIA CITY..*
Kwanaki kusan biyu kenan da take kwance jikinta yak'i dad'i,a y'an tsakanin duka kusan tana rayuwa ne amma cikin zuciyarta babu dad'i,tunda satin ya shiga ko wane yini da zai zo ya tafi kawai tana yinsa ne amma sam babu wadataccen lafiya a tare da ita,cikin skul d'inma idan sunje sai dai tayi ta bin komai da ido sai kwanciya kamar ruwa,magana idan ba ya zama dole ba ko ansaka da ita sai taga dama take amsawa,haka take shafe tsayin yini ba tare da tayi kwakwaran magana da kowa cikinsu ba,tun abun yana damun k'awayen nata har suka saba da halinta,sai dai su kansu suna tausaya mata musamman a lokacin da suka ga tayi rama,,yauma tun da suka dawo take kwance jikinta tun suna school ya sake rikicewa,wannan dalilin yasa ko da suka dawo su Badra ne kawai zaune,su uku kad'ai suke ta tattauna yadda zasu tafi 9ja,saboda halarta bikin Yah Hammad,kasancewar Daddy ya sanar mata da batun tun da suka yi waya kafin yanzun,shirin tafiyarsu 9ja kawai suke cike da zumud'i suna kuma hiran yadda bikin zai kasance da abubuwan da zasu yi idan sun koma,,kamar ancewa da Jannat ta d'ago haka nan tun data kallo inda take kwance idanunta rufe kamar mai bacci,cikin tausayawa ta sake kallonsu Badra,bayan tayi jim na wucewar wasu sa'o'i sannan tace
"Y'an uwa nifa ina da shawara..!"
Duka suka kalle ta suna sauraron suji abunda zata fad'a,shirun itama tayi tana tunanin abunda zata ce nd still tana kallonsu kamar yadda suke yi,cikin damuwa Zeeharis taja tsaki da fad'in
"Wai ke mene ne zaki fad'a ne..? Kince kina da abun fad'a kuma kin yiwa mutane shiru.."
Cikin jimami ta fara kad'a musu kai kafin tayi musu nuni da inda Sabina take kwance
"A gaskiya ni dai ina tunanin,,me zaisa wai ba zamu tafi dukanmu bane,idan yaso ko gidane sai mu rakata taga mahaifanta ko ya kuka ce,nifa ina tunanin har da alhinin su yasa ta kwanciyar nan,,kunga idan mun tafi mu biyu mun barku a nan baza kuji dad'i ba gaskiya saboda sabo,amma idan muka tafi duka ganin mahaifan ma rahama ne ai ko..??"

"Gaskiya ne Lady kin kawo shawara,nima dama tun ba yanzun ba nake wannan maganar,,dama kuma ko babu rashin lafiya yadda muke dai a cikin makarantar nan ya kamata ne ace mun tafi duka sai mu dawo idan an kammala hidimar biki ko ba haka ba..??"
Jinjina kai Jannat tayi tana amsawa da
"K'warai dear kinyi magana.."
Murmushi kawai Zeeharis tayi tana fad'in
"To ku da kuke wannan maganar haka akeyi.? Dan kawai kuna son zuwa biki sai kuce zaku janyemu duka mu tafi..??"

"Ehh! Mana ai saboda mun san mun zama d'aya ne mu duka shi yasa zamu tafi taren.."

"A'a gaskiya ba'a haka,kunga kawai ku tafi ku kad'ai kada mu tattara mu tafi wani abun ya faru a school."
Saurin tarar numfashin ta Badra tayi
"A'a Malama,kinga kawai dai kice zaki k'i zuwa ne,amma mene batun wani abu da zai faru..?? Sufa nan ba kamar k'asar mu bace,da zaran munyi report babu abunda zai faru har muje mu dawo.. Kuma ma ai naga babu wanda bai sanmu ba,dan mun tafi cikin tak'aitaccen lokaci ne zamu dawo,kuma duka ma Allah sa muyi one week zamu dawo.. Bcos Daddy ma bazai barmu mu jima ba sosai a can.."

"Haba friend ki fahimci abunda nake nufi mana,bikin nan fa na brother d'inki ne bawai naki ba,idan ace yau bikinki ake yi me zai hana baza muje ba duka,amma tunda biki ne na namiji ku d'in kuje mana ai ya wadatar mu sai mu zauna.."

"Kinga kawai kice min baza kije ba,zaki tsaya b'oye² ni gara da kika fito ma kika nunamin matsayina a gurinku.. Dama tun farko na fahimta wollahi yadda muke zaune daku ba haka ku kuke zaune da mu ba,,shi kenan tunda haka ne,Allah ya had'a kowa da masoyinsa na gaskiya.."
Yadda ta d'auki d'umi akan maganar yasa Zeeharis zuba mata idanu tana kallonta cike da tsantsar mamakinta
"Haba friend mene ne yayi zafi haka,da zai sa ki fad'i irin wannan maganar..??"

"Ai kema kin san ko mene zai janyo d'in.."
Ajiyar zuciya Zee tayi tana rik'o hannunta
"Allah ya huci zuciyarki k'awata,tunda kika fad'i haka Allah saina baki mamaki,in sha Allah daga wannan karon bazaki sake fad'ar makamanciyar wannan maganar ba,,zamu tafi tare amma ki sani bazan je gida ba,bcos nasan in dai Abbana ya san naje wollahi zai bani kashi ne,dan yana sane da abunda ke faruwa,zai ce me nazo yi al'halin ba lokacin hutu bane,,saboda haka ina so kiyi farin ciki ki kuma kore shakku akan zamanmu da ku,duka zamu tafi tare shi kenan hakan yayi miki dad'i..??"
Hararar wasa tayi mata sannan ta rungume ta tana fad'in
"Da kuwa naji dad'i wollahi mara misaltuwa..!"

"Shi kenan ai babu sauran k'orafi ko..??"

"Babu kam..!"

Duka suka yi dariya suna ci gaba da had'a kayan tafiyar tasu,juyi Sabina tayi a hankali cikin azabar damuwa ta kallesu duka,haka nan take ji a ranta inama ace tana da yalwataccen kuzari a jikinta da ta kasance a tsakaninsu itama anyi hiran da ita,sai dai babu yadda zata yi dole tasa ta keb'ance kanta a gefe guda kamar mai laifin dake tsoron kamu,,gefe guda kuma tunanin Innarta yana sukar zuciyarta,y'an siraran hawayen da suke sakkowa saman fuskarta tayi saurin gogewa tana sake shigewa cikin bedspread d'in data lullub'e jikinta had'e da sakin kuka mara sauti,,sai da tayi mai isarta sannan ta goge fuskarta ta fito a ciki,a hankali kuma ta mik'e ta nufi hanyar toilet da kyar²,dukansu suka sake binta da kallo mai cike da tausayawa.

*NIGERIA..*
Duka kwanakin biki da suka rage yau baifi kwana hud'u ba,amma Daddy tuni har ya kamo hanya ya dawo Kano,lokacin daya iso gidan ya iske shi kamar yadda ya tafi ya barshi,amma daga zuwansa nan aka ci gaba da shirye² dan ita Mamma kusan gaba d'aya ta zare hannunta a sabgar,Daddy dai shi yake ta shirya komai sai taimakawar ma'aikatan dake gidan,,kasancewar yau laraba nd tun kafin ranar yake saka ran ganin Hammad amma sai yaji shiru ba tare daya ji wani gamsashen bayanin zai zo ko A'a ba yasa shi ci gaba da kiran wayarsa dan yaji zai taho d'in ne kamar yadda ya shaida masa ko kuwa dan ya fad'a masa lallai² kada ya bari Friday ta riske shi a can,,yana kira ya riski y'ar baturiyar nan tana shaida masa duka layukan nasa a kashewannan yasa sai yayi zaton wata k'ila ko yana cikin jirgi ne shi yasa sai ya hak'ura bai sake kiransa ba,yaci gaba da zuba ido yaga ta inda zai zo k'asar,,duka sauran y'an uwa da duka abokanan arzik'i Daddy shi yayi ta bada goronsu aka kai musu,dan haka shi yake matsayin uban ango kuma shi ne uwar,k'ark'arin Mamma da shiga harkokin sai ya kama dole,amma ta wasu b'angaren gaba d'aya ta tsame kanta gefe bcos tana taya d'anta jimamin wannan auren k'addarar.


*NEW YORK..*
A can New York ma rikici ne ya b'alle tsakanin Hammad da su Sultan tun daren ranar talata suke ta abu guda har wayewar gari basu daina ba,kasancewar tun bayan da Daddy yaga Hammad yayi masa shiru da batun neman auren da yayi masa,ya kuma fahimci babu arzik'i a ciki,shi yasa kawai sai ya koma maganarsa da Sultan tunda shi angon yak'i bada had'in kai,duk wasu shirye² daga Sultan sai Sadeeq su kad'ai Daddy yake nema tun da kwanakin suka sake gabatowa ya ajiye Hammad gefe,,a cewarsa ya fahimci daga shi har Mamma'nsa so suke su saka wani ciwon ya kamashi shi yasa suka k'i amincewa su shiga sabgogin bikin,,rigima sosai suke tun da suka takura masa akan ya shirya su bar k'asar,yayin da shi d'in ya kafe kai da fata idan har ba'a gano masa inda his Lady take ba babu shi babu zuwa 9ja kuma aurenmu idan sunyi masa sa san inda zasu ajiye matar amma shi dai baya auren,sai dai koma mene ne zai faru ya faru,,rigima dai tak'i ci tak'i cinyewa tsakaninsu har sai da ta kai ga Sultan ya kira Daddy ya shaida masa a halin da suke ciki,bai nuna masa b'acin ransa ba har suka kammala wayar,,Daddy kuwa yana ajiye wayar ya shiga safa da marwa zuciyarsa cike da tunanin irin abubuwan da zasu faru idan har Hammad ya barbad'a masa k'asa a idanu,hanyar fita a d'akin ya kama har ya fita ko me ya tuna kuma sai ya dawo da sauri,waya ya d'aga cikin abunda bai wuce seconds talatin ba ya fara magana
"Ina kike..??"
Banji me aka ce daga d'ayan gefen ba sai dai naji Daddy ya sake yin magana cikin fushi da fad'a²
"Lallai² kizo bedroom d'ina yanzun ina son ganinki,,kada kuma ki b'ata min lokaci.!"
D'if sai ya kashe wayar yaci gaba da moving asides zuciyarsa tam da takaicin irin kunyar da Hammad yake k'ok'arin sashi yaji,,shigowar Mamma ce ta sashi dakatawa da sauri ya tare ta yana jifanta da wasu irin kallon da sai da taji jikinta ya bata babu lafiya,cikin dauriya bayan ta d'auke kanta daga kallonsa tace
"Yallab'ai..! Gani Allah yasa dai lafiya kayi min irin wannan kiran na gaggawa.."
Takaici maganarta ta k'arawa Daddy,nan ya shiga zazzaga mata ruwan bala'i ta inda ya shiga ba tanan yake fita ba,har sai daya tabbatar ya zazzage mata kaf b'acin ransa sannan ya d'ora da fad'in
"Awa d'aya kacal na baku daga yanzun zuwa lokacin da zata cika dake da yaronki wollahi ku tabbatar kunyi abunda nake so,idan ba haka ba wallahil'aziiym sai na b'ata muku ta yadda baku yi tsammani ba.."
Yana gama fad'an ya wuce abunsa ya barta nan tsaye,,hankalin Mamma idan ya kai dubu a yau ya kai k'ololuwa wajen tashi,musamman yadda taga Daddy yana tada jijiyoyin wuya lamarin ya sake firgita ta,tabbas shekaru basa k'arya sai dai sanin da tayi masa a da shekaru kusan talatin da aurensu basu tab'a samun sab'anin da zaiyi mata irin wannan maganar ba,sai dai tunawa da hausar nan ta malam bahaushe da yake cewa "sabo da kaza baya hana a yankata",,da kuma kasancewar yau da gobe wacce ke janyowa amarya tasha d'an banzan duka,take yasa ta sake gasgatawa tsayin zama baya hana a yiwa mutum rashin mutunci,addu'ah taci gaba da yi a zuciyarta akan Allah ya sauk'ak'a lamarin,dama kuma tun data shigo taga halin da yake ciki take yinta har ya fita bata fasa ba,da kyar² bayan ta gama saita nutsuwarta sannan ta d'aga k'afafunta ta baro d'akin gudunma kada ya sake dawowa ya tarar da ita tayi sauri ta nufi hanyar d'akin ta,cikin zuciyarta tana tunani akan lallai ne ya zamar mata wajibi ta kira Hammad ta rarrasheshi ya taho d'in dan idan har bata yi haka ba,tasan kanta komai zai koma,a hakanma kuma ba tsira zata yi ba indai a gurin mijin nata ne.
Ko mintuna talatin bata yi da fitowa a d'akin Daddy ba tana shiga nata bedroom d'in tayi k'ok'arin kiransa sai dai abun mamakin duka wayoyinsa a rufe,wannan dalilin yasa itama sai tayi amfani da line Sultan,bayan sun gaisa ta buk'aci ya bata Hammad d'in a waya,sun d'auki lokaci mai tsayi suna magana a waya kafin ta ajiye ta nemi guri ta zauna had'e da buga uban tagumi.

*SOME HOURS LATER..*
Around 9pm jirginsu ya sauka a 9ja,daga airport kai tsaye bayan sun samu cab suka nufo Mayangu road gaba d'ayansu,saboda tun tahowarsu Badra ta kafe akan sai dai su fara zuwa can idan yaso daga baya sai su wuce su kaita gida,bisa dole badon ta soba ta amince musu suka taho taren sai dai tunda suka d'auko hanyar haka nan gabanta yake tsananta fad'uwa,,duk hiran da suke tunda tayi shiru bayan sun baro airport d'in bata sake magana ba har suka k'araso cikin unguwar ta Nassarawa G.R.A,a dai² bakin get d'in gidansu mai cab ya ajiye su da kayansu,suna gama sallamarsa suka wuce ciki Badra da Zee a gaba suna janye da luggage's d'in kayansu,sai Jannat data rik'o hannunta su kuma suna biye da su,tun daga bakin get d'in gidan Sabina take bin ko ina da kallo,a iya tsayin zamansu duk da ta fahimci daga irin gidan da suka fito,ko kad'an bata tab'a sawa a ranta gidan da suka fito ya kai haka ba,daurewa kawai tayi taci gaba da binsu amma can k'asan zuciyarta tana sak'a dole ne ta d'an ja baya dasu matuk'ar sun koma lafiya,,tana tsaka da tunanin har suka k'araso k'ofar shiga parlor'n gidan.
Alamu Badra tayi musu da su wuce a hankali dan bata son Mamma ta gansu yanzun,a hakan duka suka lallab'a a hankali,sai da Badra ta fara lek'awa,ta tabbatar babu kowa a parlor'n dan haka duka suka wuce da sand'a duk dan suna so su bawa Mamma surprise,sanda suka gama shigewa da gudu² suka wuce Bedroom d'in Badran,,a gyare suka iske komai d'akin sai k'amshi yake had'e da sanyin AC dake busawa,tamkar tana gidan bata je ko ina ba,hakan yasa ta jin dad'i a hankali sai ta bud'e hannayenta tana shak'ar ni'imtacciyar isakar y'anci,sai data gama tukun tayi saurin juyowa ta kallesu tana dariya
"Hey! Guy's mene ne kuka wani tsaya kallo na ne..?? Ku nemi guri ku huta tukuna mana."
Girgiza kai Sabina tayi saurin yi tana fad'in
"Noo! Dear ya kamata na wuce gida,,amma muje na gaisa da Mamma sai na tafi ko..??"
Hararar ta Badra tayi tana fad'in
"Kin manta..! Daga zuwan namu shi ne zaki ce zaki tafi..?? Kije ina to da wannan daren.? Uhhuumm.! Lallaima Princess,wai da a zatonki da nace mu taho saimu rakaki gida,kin d'auka da gaske nake..? Ai wollahi kima sa aranki ko zaki fita a gidan nan sai da safe dan Mamma ma ba zata bari ba,bare kuma Dad da idan yaji zai fad'a.."
Tana maganar tana mata dariya k'asa² su Jannat suna taya ta,had'e rai tayi saurin yi tana kallonsu duka suna ta dariya,a hankali kuma sai ta kad'a kai kawai tana fad'in
"Ku dai wollahi kuna da matsala,in banda abunku ai ba sai kunyi min haka ne zan gane bakwa so na tafi ba,,idan kuka ce min mu taho tarema ya isa,tunda kun san bazan baku kunya ba.. Amma shi ne har sai kun had'a da min wayo kamar wata y'ar goye..??"
Dariya suka ci gaba dayi,itama sai ta samu damar darawa,,daga haka kuma sai suka fice duka zuwa bedroom d'in Mamma da niyyar gaida ita tunda basu same ta a parlor ba,,knocking suka fara,Mamma ta tambaya waye,amma sai suka yi shiru,izinin shigowa kawai ta bayar dan tasan wata k'ila d'an mulkin mijin nata ne shi yasa yak'i amsawa da yake yana kan fushi da ita itama sai bata damu ba da shirun da taji,bud'ewa sukayi suka shigo ciki,,tunda suka shigo cikin bedroom Sabina ta sake bud'e ido saboda daular dake shimfid'e cikin ko wane d'aki,duk dama dai d'akunan daga na Badra sai na Mamma kawai ta shiga.
Baki bud'e Mamma take binsu da kallo tun da suka shigo har suka k'araso kusa da ita,sai da suka zauna a gabanta ne sannan ta fizgo maganar da kyar
"My kiddo..! Saukar yaushe..!?"
Dariya suka saka dukansu dan yadda Mamma take kallonsu kad'ai ya isa ya basu tabbacin sun mata bazata
"Bamu dad'e ba Mamma..!"

"Uhhuumm.! Lallai yaran nan wato sai kuka kasa fad'a min zaku zo ko..!?"
Tsagaitawa suka yi da dariyar da suke yi Jannat tana cewa
"Mamma wollahi Badra ta hanani fad'a miki,amma har na d'auki waya zan kira ki tace wai mu bari kawai muyi muku surprise.."
Murmushin k'arfin hali Mamma tayi tana fad'in
"Lallai..! Ai kuwa gashi nan kunyi.. Saura ita Hajiya Aminar,na ga ya zata ji idan ta ganku,dan nima tunda ba'a fad'a min ba bazan fada mata ba,sai dai kawai ta ganku.."

"Eyy! Wollahi Mamma kada ki fad'a,kowa kawai sai dai ya ganmu."
Sake yin murmushi tayi mai d'auke da ma'anoni daban² sannan suka gaisa dasu,lokacin da tazo kan Sabina haka nan tunda idanunta suka sauka akanta take jin kamar ana yaye mata wani irin duhu daya lullub'e mata zuciya,a hankali take sake kallonta suna ta hira da sauran yaran,,itama kanta Sabinar tunda suka shigo d'akin kallo d'aya ta yiwa matar taji jikinta ya d'auki rawa kamar wacce ake kad'awa gangi,sai dai ba kowa zai fahimci halin da take ciki ba sai mai tsananin sa ido,zuciyarta ta shiga cikin wani irin yanayi tun a kallon farko.
Rashin sarkewar da Mamma taga tayi ne yasa ta yi murmushi sannan ta basu umarni da suje suci abinci idan sun gama kuma sai su kwanta saboda gajiyar hanya zuwa da safe sayi hiran,dukansu kuwa suka amsa sannan suka yi mata sallama,suna ficewa daga bedroom d'in dama Sabina ce akan gaba wajen fitowa,dan duka tun shigarsu take jinta a takure,ko gurin cin abincinma a gaggauce ta iya yin hak'uri suka zauna a dining daga nan kuma suka koma sama,shima d'in ta riga su komawa,tana shiga wanka ta shiga ta fara yi,tana fitowa bayan ta shirya tayi sallolin dake kanta ba tare data tsaya bi takan kowa cikinsu ba tabi lafiyar gado.

*03:00am GMT.*
Jirginsu Hammad ya sauka a filin tashi da saukar jirgi na Malam Aminu Kano,su kansu basu yi zaton zasu zo basu haura haka ba kafin ace su iso d'in,kai tsaye suma koda suka fito gida suka nufo kasancewar dare yayi nisa sosai,da yake titin babu traffic a lokacin yasa cikin mintuna ashirin suka k'araso bakin get d'in gidan,baiyi k'ok'arin kiran kowa ba dan ransa duka a jagule yake tunda Mamma tasa shi tahowa bisa dole,,get man d'inma Sultan ne ya masa knocking bayan ya bud'e musu suka shige ko gaisuwar da yake musu bai amsa ba,,tunda ya sako k'afarsa a cikin gidan yaji yanayin isakar dake shiga cikin jikinsa ta sauya,a hankali damuwar dake tattare da shi ta fara k'ok'arin raguwa,fargaba ta sake tsananta a gare shi,,a hankali yake d'aga k'afarsa yana tafiya tun daga bakin get har suka k'arasa shigowa cikin gidan.....

*Tofa.. Fan's ga dai HAMMAD ga kuma SABINA a cikin gida guda,,ko yaya zata kaya Allah shi kad'ai ya barwa kansa sani..*

*Masoyana a duk inda kuke a fad'in duniyar nan bani da kamar ku,dan haka samun ku abun alfahari ne a gare ni,addu'o'inku a kullum cikin riskata suke,godiya kad'ai na tabbata bazata wadatar ba,ina jin dad'in addu'o'inku sosai²,saboda a koda yaushe suna k'ara min nutsuwa da kasancewa cikin farin ciki,addu'ah itace kad'ai abunda zan yi muku naji nutsuwa har cikin raina,kamar yadda nake jin dad'in addu'o'in da kuke min,kuma ubangiji ya faranta muku,ya yalwata rayuwarku da kasancewa cikin haske duniya da lahira,,tabbas ban san haka littafin _ALK'AWARIN JINI_ ya samu karb'uwa ba,,abun alfahari nane da naga yadda kuke commenting,musamman mutane na y'an amana jama'ar FACEBOOK wollah na jinjina muku sosai,,ina mik'a sak'on d'umbin godiya ta a gareku masoya na,irin wacce bata da iyaka,fatan rabb ya bar k'auna tsakanina da ku..#1❤Mutane na.*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*37.*
_#Coincidence_

_Tsayin shekarun dana d'auka daga fara rubutuna har zuwa yau,babu wanda ya tab'a yi min irin abunda kika min,duk da nasan an sadaukar min da pages na litattafai a baya da dama da ni kaina ban san adadin su ba,amma cikin hukuncin ubangiji babu wanda yayi min kwatankwacin abunda kika yi,,na gode sosai² *MY FENERH (Matar Soja)* kece mutum ta farko data sadaukar da littafinta guda akaina,,dole naji daban a wannan lokacin,kuma dole kuma nayi alfahari dake saboda karamcin da kika nuna min,bazan gaji ba wajen nuna miki tsantsar farin cikina,haka ba zan gaji da binki da addu'ah ba,har sai ranar da numfashi ya yanke min,,dole na ne ni *REAL SMASHER* nayi alfahari da littafin *Y'AY'AN GATA* saboda kasancewarsa kyauta mafi girma kuma mafi soyuwa a gareni,,na gode³ sosai da sosai,ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairinsa dear,ya duba bayanki,ya hasakaka rayuwarki tare da yalwata farin ciki a tsakanin zuri'ar ki,,kin sani hawaye a lokacin dana ga kyautarki,yadda kika sa wannan bakwa farin ciki ina rok'on ubangiji daya dawwamar dake cikin farin ciki mara yankewa.🙏_
*Fisabilillah.! Nake miki son so habibtiiy..* 💞


A kulle suka tarar da k'ofar shiga parlor'n gidan,duk wata hanya da suka san zata sada su da ciki sun duba amma duka babu wacce suka tarar a bud'e,gefe suka ja gaba d'aya suka tsaya kafin a fara Kallon-kallo tsakaninsu da Hammad da shima yaja gefen fuska a d'aure kamar bai tab'a sanin yadda ake dariya ba,sun d'auki tsayin mintuna a tsaye shiru kowa da abunda yake tunani aransa kafin ya d'ago ya kallesu duka yana tab'e baki
"Dude's.! Wai mene ne muke yi a tsaye ne..??"
Fuskar Sultan da mugun mamaki ya kalle shi yana fad'in
"Ban gane me kake son fad'a ba,,me kuwa zamu tsaya yi a nan idan ba jira ba.!"

"Uhhuumm..! Jiran na mene ne..??"

"Ban sani ba..! Da Allah malam kada ka b'atawa mutane rai mana,sai kace baka san me muke jiran ba.."
Dariya ya d'anyi kad'an irin wacce ya jima baiyi irinta ba,cike da zolaya kuma ya fito da keys d'in dake tare da shi yana wasa da su a hannunsa yana ci gaba da dariya k'asa²
"Uhhuumm..! Zaka sani ne yayin da kuka yi ta tsaiwa a nan.."
Sarai Sultan ya jiyo me yace amma sai ya kasa fahimtar abunda yake nufi,bayan kamar mintuna biyar kuma da sauri ya dawo gabansa ya wafce keys d'in,,dariya Hammad ya sake yi yana jinjina kai,Sultan kuwa ko daya karb'e keys d'in a hannunsa kai tsaye ya nufi k'ofar shiga parlor,wad'anda yake tunanin ya fara gwadawa take k'ofar ta bud'e,juyowa yayi ya kalli Hammad da tsananin mamaki
"Lallai ma mutumin nan ka raina mana hankali,,da kasan kana da keys d'in amma kasa mu zaman jira..??"

"Hankalin naku nawa yake dama..?"
Yana fad'ar haka yayi wucewarsa ciki ya barsu nan tsaye da mamakinsa,gaba d'aya suka biyo bayan shi,ko da suka shigo hanyar bedroom d'insa suka nufa yana gaba suna tafe suna binsa a baya,,kasancewar babu wanda yasan da zuwansu a lokacin bayan get man d'in gidan,shi yasa har suka isa cikinma babu wanda ya gansu,,suna shigowa ko zama bai jira yayi ba ya wuce bathroom,,sai daya watsawa jikinsa ruwa bayan ya d'auro alwala sannan ya fito,nan ya iskesu duka sun baje saman bed d'insa,dariyar mugunta kafin ya k'araso inda suke,yana zuwa bai jira komai ba ya bisu da duka,a firgice duka suka mik'e suka zauna suna binsa da kallon tuhuma
"Haba dude,,wannan wane irin abune haka.? Kawai sai da kaga mun fara bacci zaka tada mu.."
Juyawa yayi ya barsu a gurin k'asa² yace
"Lokacin sallar ya kusa zaku kwanta..??"

"Amma dai ai baiyi ba ko..??"


Please Login or Register in order to submit comment