Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya dafa maka..Amma dai ka k'ara hak'uri da abunda ya faru d'innan.."
Sai daya kalli dattijon yayi murmushi zuciyarsa cike da mamakin wannan ban hak'uri haka da yake ta maimaitawa,sannan ya ce
"Babu komai baba in sha Allah,,komai ya riga ya wuce.."
Da kyar suka bar wajen baban Sabina dan yadda yake ci gaba da bashi hak'uri abun sai ya koma bashi kunya,daga nan kuma kai tsaye hanyar da zai fitar dasu zuwa ainihin babban titi suka nufa a sauk'ak'e,suna tafe baffa da Muhammad suna d'an tab'a hira musamman akan yadda harkar noma da kiwo yake a yanzun,,a cikin hiran ne baffa yake tsokanarsa yana cewa bazai iya noma ba,while shi kuma yana fad'awa baffa ai babu abunda zai gagare shi in dai a harkar noma ne,dariya baffa yayi kana yace
"Haba..! Mai babban suna,,kana kalloka nan ko fartanya ina jin baka tab'a rik'ewa ba bare ka gwada noma kunya guda,bare akai ga gona guda..Ai kai d'in bakayi kama da wanda suka san wahala ba.."
Murmushi yayi sannan ya ce
"Baffa ai duk abunda ake buk'ata ga cikakken namiji shi ne juriya da jajircewa akan duk abunda yasa a gabansa,haka nan duk wani abu sawa ne a rai,idan mutum dama ya riga yasa a ransa bazai iya ba,tofa babu yadda za'ayi ya iya,,amma ni kam baffa ina ganin babu abunda zai gagare ni matsawar nasa shi a raina kuma naji ina so.."

"Aaa! Da kyau sosai..! Haka ya kamata ace mu maza dama mun gina zuk'atanmu,a koda yaushe muji cewa duk abunda yazo mana zamu iya yinsa ba tare da fargaba ba,,amma abun haushin shi ne a wasu lokutan wai sai kaga namiji ya kwanta a gida yana jiran a dafa a bashi,,musamman ku can a maraya an fi samun irin wannan,,amma mu nan kam babu yadda za'ayi kaga namiji bai fita gona ba tunda mu har matan muma sukan fita zuwa gon.!"

"Haka ne dama baffa,,rayuwarce ta yanzun sai addu'ah kawai da fatan Ubangiji yasa mu cika da imani.."

"Ameen..! Wannan kam shi ne babban fatan da muke har kullum.."
Dai² nan suka iso bakin titin,,wanda ga Muhammad sai a lokacin ne ya tuna da bike d'insa daya bari a can gurin daya ga Sabina buh yasani kam zuwa yanzun babu tabbacin ace zai ganshi shi yasama bai ko yi nufin dubawa ba,,haka nan sai a lokacin daya sake laluba jikinsa ya tuna da cewar bai fito da ko anini ba,jim ya d'anyi yana tunanin yadda za'ayi ya koma skul,nd ga shi ko phone babu a jikinsa bare yayi kira a zo a d'auke shi,,,gefe ya juya can daga d'ayan gefen na bridge d'in,yana y'an tunanuka na neman hanyan da zai bi ya tafin,can daga tsallake ya hango wani d'an k'aramin shop dake da alamun daban² irin na masu sai da recharge card,ko daya hango gurin a bud'e sai yayiwa Allah godiya sannan ya kalli baffa yana fad'in
"Baffa da kun koma haka kada nayi ta janku da nisa,tunda mun fito hanya nima yanzun zan samu abun hawa ya maidani buh zan tsallaka can na kira waya kafin na wuce..."

"Toh mai babban suna,mun gode sosai ubangiji ya saukeka lafiya.."

"Ameen baffa sai kun sake gani na.."

"Toh Allahu ya kawo ka da alkhairi.."
Da "ameen" ya amsa masa sannan ya d'an kalle gefen ta yana cewa
"To *K'ANWATA* ni zan tafi ko,,amma ki dunga kula da lokacin daya dace ace kina fita,,ba kowane lokaci ake so y'ay'a mata su dunga fita ba,saboda hatsarin da zai iya samun su.. kinji ko..??"
Sai data d'ago ta kalleshi idanunta suna fidda k'yallin hawaye sannan ta girgiza masa kai tana cewa
"In sha Allah zan kiyaye..!"

"Yawwa to ni zan tafi,,sai na sake dawowa.."
Cike da rashin kuzari sai ta amsa masa da "toh" sannan ta bishi da fatan kiyayewar Ubangiji,,suna nan tsaye ita da baffa a gurin har ya tsallaka zuwa d'ayan side d'in ya nufi gurin shop d'in,,bayan da suka ga ya wuce d'in sannan baffa yace mata su koma haka nan,a lokacin rana har ta fara d'agawa,nan suka kama hanyar su ta komawa gida.

Kai tsaye bakin d'an k'aramin shop d'in ya nufa,yana yiwa mutanen daya iske a gurin sallama had'e da mik'a musu hannu suka yi musabaha,,a hankali ya juya ya kallo cikin shop d'in dan a zatonsa zai iske mai gurin a ciki,sai dai yaga babu kowa,ko da yaga babu mutum a ciki,da fari sai yayi kamar bazai magana ba,can kuma dai da yaga shirun bazai amfana masa da komai ba,nd zai sake b'atawa kansa lokaci,sai ya kalli na farkon dake zaune a saman bench d'in da fad'in
"D'an uwa dan Allah ina tambaya ne..??"
Da mamaki suka kalle shi kafin ya amsa masa
"To Allah yasa na san abunda zaka tambaya..!"
Jim ya d'an sake yi kafin yace
"Dan Allah ina mai wannan shop d'in..!?"
Sai da suka kalle shi duka,after sun tabbatar ba wani abu ne yasa shi neman mai shop d'in ba sai ya amsa masa da cewa
"Gani..! Amma lafiya MALAM kake tambaya.??"

"Ehh! To lafiya k'alau zance maka,,buh ina neman waya ne zanyi kira idan kuna bada rent.."

"Okay..! Babu matsala akwai,ammafa duk minti d'aya zaka bada naira #100.."
Sai da yayi murmushi nd yana fad'in
"Babu matsala,,damuwata dama nayi kiran.."
Sannan ya karb'i wayan da ake mik'o masa,a hankali ya d'an matsa gefe kad'an da su yana clicking phone d'in,bayan ya loda number ya danna kira had'e da k'urawa screen d'in idanu yana nazarin tafiyar kiran,,sai da wayan ya kusa katsewa sannan aka d'auki kiran,da sauri yasa wayan a kunnensa dai² lokacin da ya furta
"Hello.. Man..!"
Can daga d'ayan side d'in wanda aka kira d'in ya furta
"Man..! What's up..?? Kafa tada mana da hankali da yawa,tun safe sai nemanka muke a cikin skul amma bamu ganka ba..Where have u been ne..?? Gashi har prof ya shigo ya fita baka nan..Ina ka shiga ne..??"
Sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke sannan ya furta
"Yeah! Ina nan wajen bridge kazo ka d'auke ni yanzun..Ban fito da phone ba.."

"Ok.. Gani nan a hanya.."
Yana fad'in haka ya katse wayan sannan ya koma kusa da masu shop d'in ya mik'a musu wayan kana yace ma mai shop d'in yayi masa hak'uri babu kud'i ne a jikinsa idan anzo d'aukansa sai ya sallame shi,amsawa yayi da babu komai sannan yace
"Amma fa Yallab'ai zaka yi mana k'arin kan abunda muka yi da kai,,tunda sai mun jira,sannan lokacin daka ci minti d'aya ne da sakan ashirin da uku (1m 23secs).."
Murmushi yayi masa kana ya amsa masa da
"Babu damuwa,,bari wanda nake jira ya k'araso.."
Daga haka sai basu sake yin magana ba suka bashi guri ya zauna,,almost 10 minutes ya kwashe yana zaman jira,time to time kuma yana kallon hanya,buh still shiru bai ga zuwansa ba,haka nan idan yaga babu alamun zuwansa sai ya d'anyi tsaki,still wasu mintuna biyu suka sake shud'ewa,,har ya mik'e tsaye cikin yanayi na fara hasala kuma ya hango tahowar motan.
Da mugun gudu motan k'irar toyota tundra fara sol mai duhun glasses ta zo ta gifta su,,har motan ya wuce shi,a hankali kuma matuk'in yayi slow sannan ya fara k'ok'arin yin reverse zuwa hannun da Muhammad d'in yake,komawa yayi ya zauna yana jiran ya k'araso fuskar nan a had'e irin na mai jiran k'iris,lokacin daya iso inda suke zaune bayan ya gyara parking sai ya sauke glasses d'in side na mai zaman banza ya d'an sunkuyo da niyyan yin magana,,kyakyatawan matashi ne wanda duka bazai haura tsaran Muhammad a shekaru ba da komansa,,a hankali ya kallo inda yake ganin bai motsa ba yana fad'in
"Am sorry friend,,na d'an samu matsala ne wajen fitowa daga skul.."
D'agowa yayi ya zabga masa wani mugun kallo kafin ya mik'e yana tura hannayensa a cikin aljihun jacket d'insa,sannan ya nufi inda motan yake,bai bud'e ba ya d'an sunkuya ta window d'in yana fad'in
"Bani ni na sallame su..!"
Sai daya kalleshi yayi murmushi sannan ya furta
"Me kuma..!?"
Wani malalacin kallo ya watsa masa sannan yace
"MALAM idan zaka bani ka bani..I think na fad'a maka ban fito da kud'i ba.."

"Ehh! Ka fad'a min..Sai akayi yaya to..??"
Shahararren tsaki yaja cikin jin haushi yana fad'in
"Dan Allah malam bana son rainin hankali,,ai ka san bada wayana na kira kaba,,shi ne ina tambayan ka kana rainamin hankali,idan ka zone dan ka b'ata min lokaci kaja motan ka wuce..zan dawo da kaina ko baka zo ba..!"
Y'ar dariya matuk'in motan yayi sannan ya d'auko wallet d'insa yana dubawa da niyyan d'auko masa kud'in,fizgewa Muhammad yayi yana harararsa sannan ya matsa inda yabar su zaune,bai wani tsaya duba meye a ciki ba ya zare 5k ya mik'a musu after ya musu godiya ya juya ya barsu sai godiya suke masa shima,,bai tsaya kulawa ba kawai ya bud'e motan ya shige,sannan suka d'auki hanyan campus..

A b'angaren Sabina kuwa da baffa tunda suka kama hanyar komawa basu wani tsaya ba,abunka da mutumin daya saba da zuwa gona,haka nan tafiyar k'afa duk nisanta da yake ba jinta suke yi ba,nan da nan sai gasu har sun dawo gida,,a k'ofar gida baffa ya tsaya gurin abokansa dake zaune k'asan awning dake k'ofar gidan,Sabina kuwa suna zuwa bayan ta gaishe su sai ta wuce abunta zuwa cikin gida kamar yadda baffan ya bata umarni,,shigowarta a lokacin yayi dai² da lokacin da LADO yake k'ok'arin fitowa,nan a bakin k'ofa sai suka kusa yin karo da juna,,yadda ya taho kamar zai fad'o kanta sai yasa tayi baya da sauri tana fad'in
"A'uzhubillahi minashshaid'anir rajiim.!"
Wani wulak'antaccen kallo ya sauke mata cikin fusata yana fad'in
"Ke dan uwarki waye kike cewa shaid'anin.!?"
Bata tanka masa ba sai dai ta tab'e baki gami da juya idanunta,abunda Sabina bata sani ba shi ne a wannan lokacin wannan abu biyun da tayi ba k'aramin k'onawa LADO rai yayi ba,nan take ya taso kanta kamar zai dake ta,da sauri ta sake ja da baya har tana yi kamar zata fad'i,,shi kuma yaci gaba da binta har ta kai jikin bango,ganin yadda yake ci gaba da nufo ta duk da hakan sai yasa itama ta fara hasala duk da a tsorace take da lamuransa,amma sai tayi jarumta cikin d'aga murya ta yadda tasan za'a iya jiyota ko da a cikin gidane a kawo mata agaji,bayan ta watsa masa mugun kallo sannan ta ce
"Wai kai LADO dan Allah ni me nayi maka ne da kake son takuramin..?? Naga dai ni wani abu bai tab'a had'a ni da kai ba bare kace ko na ci maka bashi,,,so let me be..! Ka fita a hanyata,,idan ba haka ba kuma Allah zan maka rashin mutunci ai ba tsoranka ake jiba.."
Jinjina kai yayi cikin k'asa da murya hakama fuskarsa a daf da nata yake fad'in
"Ai wollahi yarinya kinyi kad'an na kyaleki,,dan kin ga yau kin tsallake wannan tarkon,aka ce miki zaki iya tsallake na gaba ne..? Wollahi tunda nayi niyya,,na lashi takobin had'e da yin *ALK'AWARIN* sai na d'and'anaki matuk'ar muuna raye nine zan fara d'and'anar zumanki,,idanma old man d'inki yana ganin yafi k'arfina ta wani hanyar to ni nan gagara badau nake...Allah wollah...!"
Bai kai ga k'arasowa ba yaji saukar lafiyayyen mari a both chicks d'insa,,cikin wani irin mugun mamaki ya d'ago had'e da fad'in
"Kan uban can..!? Ke har ni zaki mara..!? Kamar ni LADO..!? Kina mace kisa hannu ki mare ni..!?"
Cikin hucin masifa kamar wacce take filin yak'i itama cikin k'arajin masifa ta furta
"Na mare ka d'in.. Idan kuma kana ganin zaka iya ramawa bismillah,,shege ka fasa a tsakaninmu..!"
Hannu LADO ya ware zai tafka mata a fuska muryar baffa daya jiyo kamar ana haniya a zauren gidan ya lek'o ya furta
"Kada ka kuskura ka tab'a ta..Idan kuwa ka sake ko da gefen hijabinta ka tab'a yau zaka ga yadda zanyi da kai a gidan nan.."
Da sauri ya juya yana kallon inda ya jiyo muryan baffan,nan take kuwa suka yi ido hud'u da shi,k'wafa LADO yayi cikin gunagunin b'acin rai ya furta
"Ai dama duk kuke d'aure mata gindin ta dunga raina mutane..Amma wollahi bazan bazan fasa ba tunda na lashi takobin yi sai nayi.."
Sai dai fa bawai yayi ne ta yadda baffan zai jiyo shiba coz yasan gamuwarsu da juna ba zata tab'a masa kyau ba matuk'ar ya jishi
"Sha³n banza..zo ka wuce daga nan kafin na shigo na riske ka..!"
Sum² LADO ya bar kusa da ita bayan ya watsa mata kallon zamu had'u next time,sai kin raina kanki,,,itama gareta mugun kallon ta watsa masa had'e da yin tsaki sannan ta bar wajen zuciyarta k'al dan murnan yadda tayi jarumta wajen marin LADON,,wanda dama muryan su baffa da take ji ne a kusa da k'ofar shigowa shi ne dalilin daya bata k'warin guiwan d'aga muryan a sonta ko babu komai idan baffa ya jiyo zai masa fad'a,sai ga shi a b'agas ta samu damar marinsa,yadda take cike da jin haushinsa a yau d'in take sai taji wani gefe na zuciyarta ya cika da tsantsar farin ciki,,baffa da har lokacin yana tsaye ya juya kanta lokacin tana niyyar shigewa yana fad'in
"Uwata abunda zan fad'a miki shi ne daga yau kada ki sake wani abu ya kuma had'a ki da shi,,kin jini ko..?? Kinga dai abunda suka kusa yi miki d'azun shi da wannan kangararrun abokan nasa,saboda haka sai kin kiyaye kanki daga shiga duk wani abu da zai had'a ku..kin ji ko..??"

"To baffa..In sha Allah zan kiyaye.."

"Yawwa to..Maza jeki gida..Allah yayi miki albarka.."

Da "ameen ta amsa masa kana ta wuce cikin gida abunta..

A b'angaren Muhammad kuwa tun da suka d'auki hanyan komawa skul bayan ya mik'awa friend d'in nasa wallet d'insa bai ko sake kallonsa ba,yayi shiru yana kwantar da kansa a jikin seat,duk da yadda yake ta masa magana da tambayarsa inda yaje da safen amma ko kallo bai is he shi yi ba,,hasalima shi haushi ne ya kama shi jin yadda duk ya dame shi da surutu nd a time d'in duka ba abunda ya dame shi kenan ba,cikin alamun nuna gajiya da surutun da yake masa ya d'ago kai yana sauke masa wasu awful looks kafin ya furta
"Sultan..! Please dan Allah kaja bakinka ka rufe haka nan,kai wai baka gane lokacin da mutum yake cikin yanayin da zai saurari wannan zantukan naka..?? Ka kyale ni naji da damuwata mana,,amma kazo sai k'ok'arin k'ara min wani kake..!"
Murmushi sultan ya saki mai sauti,cikin alamun zolaya kuma ya ce
"Ohh! Friend kaifa matsalar ka kenan,,baka rabuwa da damuwa,nd idan za'a tambayeka kuma a banza,ba fad'a za kayi ba,,,ai sai kaje kayi ta fama da kayan damuwarka.."
Sake kallonsa Muhammad yayi sai dai bai ce masa komai ba ya juyar da kansa zuwa side yana kallon hanya had'e da sakin long crack,wanda yasa sultan yin murmushi sai dai bai sake ce masa komai ba a haka har suka shiga cikin campus.

*2 days leave...*

A gefen Sabina kam zuwa yanzun tun bayan tafiyarsa hankalinta a kwance yake,dan tun daga ranar da AL'AMARIN ya faru,bata sake barin wani abu ya shiga tsakaninta da LADO ba haka ma Innarsa wato Tani,,a yanzun kullum cikin taka tsantsan take dasu,hakama duk wani abu da tasan zai had'a su ko ya janyo a samu sab'ani,sosai sai ta shiga k'ok'arin guje masa,ga Innarta ma itama ta fita a lamuransu Tani d'in,sai dai wani abun mamaki kuma da yakr faruwa shi ne tun da baffa yace zasu had'u da LADO,gaba d'aya sai aka nemi LADON a gidan aka rasa ya gudu daga gidan,hakan sai yayiwa jama'ar gidan dad'i dan dama kullum cikin neman magana yake a garin.

Ga baffa da baban Sabina kuwa tun suna neman LADO dan yi masa hukunci akan abunda ya aikata har suka gaji suka watsar,dan kuwa sun san duk daren dad'ewa wata rana dole ne zai kawo kansa gare su idan ya gama guje²n,nd dama kuma baffa yasan za'a rina shi yasa ma a ranar da AL'AMARIN ya faru yace masa saura su nemeshi su rasa d'in.

Shigowarsa kenan cikin gidan da yammacin ranar yana tafe yana fito kamar wani d'an farauta,,ko da yake ina maraba tsakanin d'an shaye² da mafarauci..?? A wasu lokutan ai halayensu suna d'an kama da juna,,da baffa ya fara katari a hanyarsa ta shigowa gidan,,sai ya d'auke kai yayi kamar bai ganshi ba zai wuce,baffa da mamaki a fuskarsa ya bishi da kallo kafin ya ce
"Kai LADO kai..!? Zo nan dan uwaka..Ja'iri mai siffar jinnu..!"
K'eyarsa ya shafa yana sunkuyar da kai k'asa had'e da gunguni k'asa² ya d'an rage tsayin sa kad'an,wanda da kad'an yafi ace mutum yana tsaye da fad'in
"Aaa! Baffa barka da yamma..!"
Malalacin kallo baffa ya bishi da shi kafin ya girgiza kai cikin jimami da cewa
"Ka gama guje²n naka..??"

"Aaa! Baffa nifa babu inda naje,,kawai dai.."

"Kawai dai me..!? Ai tambayarka nayi ka gama guje²n yau ka dawo gida..??"
Bai iya bashi amsa ba,nan kuwa baffa ya juya yana fad'in
"Biyo ni to muje ciki,,,yau zaka ci uwaka wannan mai fuskar kamar faifai..."
Ba don LADO ya so ba sai don babu yadda za'ayi ace ya sake guduwa nd kuma sun riga sun had'u da baffan shi yasa kawai ya shiga binsa a baya,,a tsakar gida baffa yaja tunga ya tsaya,cikin d'aga murya yana kallon mutanen gidan da cewa
"Kuna ina ne kai..! Duk ku fito ina son ganin ku..!"
D'aya bayan d'aya suka fara fitowa daga d'akunansu wad'anda kuma suke tsakar gidan nan suka shiga matsowa gaba dan jin dalilin baffa na son tara su dukan.....



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

_Jinjinar ban girma gare ku *HASSAN ATK (79k) 😜,HUSSAIN ATK (80k),HAYAT BABA ZUBAIR & B.Y EBRAHIM* Alkhairin Allah yaci gaba da kasancewa tare da ku a duk inda kuke,,Real Smasher tana jinjina a gare ku,tare da fatan rabb yayi muku tukuici da mafificin alkhairinsa.✊_

*PROMO.💞*
_All for u guy's *ALK'AWARIN JINI FAN'S.😍*_

*7*
_#Travel around_

Saman traditional chair dake ajiye a gefen rumfar baffa ya zauna,yayin da su kuma gaba d'aya ahalin kowannensu ya nemi guri ya zauna duka suna zagaye da shi had'e da kasa kunnuwansu ga abunda zai fad'a,,kaf gurin sai da baffa ya kallesu bayan ya tabbatar da su wane ne a gurin da kuma su waye basa nan sannan ya juya ga y'an yara² dake wasa a gurin yana fad'in
"Kai Sule kai,,,zo nan maza kaje ka kiramin babanku Aminu a k'ofar gida..Kai kuma Hamudan je ciki kacewa Tani tunda ban isa na ce tazo ta amsa akan lokaci ba,,to taci gaba da zama,,amma ta kiyayi gamonmu da ita..!"
Da gudu yaran biyu kowannensu ya bar gurin cikin sauri duka suka nufi inda aka aike sun cike da son isar da sak'on baffa akan lokaci,mintuna biyu da aiken baban Sabina ya shigo gidan cikin sauri,yana zuwa bayan yabi ilahirinsu da kallo kuma sai ya nemi guri nan a kusa da baffa ya zauna saman d'aya kujeran da babu kowa akai,yana fad'in
"Yaya wannan taron fa..?? Ince dai ko lafiya aka taru duka gida a nan..!?"

"Lafiya k'alau..!"
Baffan ya fad'a yana mai kallon hanya da sauraren isowar Tani,,sai da d'an aiken baffa ya kwashe ak'alla mintuna biyar da dawowa,amma shiru babu ko alamunta,girgiza kai baffa yayi cikin takaici kana ya kalli inda LADO yake yana fad'in
"Kai LADO..! Ina son yanzun nan maza ka sanar damu gaskiyar abunda ya faru a shekaran jiya..!"
Ba tare da LADO ya d'ago ba haka nan k'asa² ya furta
"Toh..Baffa ai naga kun riga kun san komai,,mene ne amfanin na maimaita kuma.."
Da mamaki duka mutanen gurin suke kallonsa,dan a iya tsayin wad'annan shekarun da aka kwashe tun bayan mutuwar MALAM,kaf a gidan baffa shi ne ya koma lamba d'aya,duk wani hukunci ko al'amuran da suka shafi gidan gaba d'aya da hukuncinsa ake aiki,hakama duk lokacin daya zartar da magana tofa ba'a tab'a samun wani ya musawa maganar tasa,ko kuma a mayar masa da magana kai tsaye,, buh yau karon farko lado ya fad'i irin wannan maganar mai tattare da rashin d'a'a ga baffan,ba ga mutanen gurin kad'ai ba hatta da shi kansa baffa sai da maganar LADO ta bashi matuk'ar mamaki,sai dai sanin halin LADON a yanzun na rashin mutunci wanda kowa ma bai kyale ba sai yasa baffa jinjina kai kawai,ba tare daya sake bi takansa ba ya kalli jama'ar gidan duka yana cewa
"Alal hak'ik'a na san da yawan ku a shekaran jiya lokacin da LADO yazo da wannan magana game da Sabina,kun yarda da shi,sai dai wani abun ban haushi,takaici da kuma Allah wadai shi me,ko da yazo yace wani ya kamata yana k'ok'arin haike mata,,a gaba d'ayan wannan magana babu gaskiya a ciki,dan kuwa ba haka take ba.."
Nan take baffa ya shiha warware musu duka abunda ya farun,after kuma ya umarci SABINA data sake maimaita musu abunda ya had'ata da su LADON,,nan itama ta shiga zayyana musu komai kamar yadda ya faru,,ko data gama basu labarin take gurin duka suka d'auki salati,,yayin da wasu a ciki suka hau fad'in
"Ya kamata a hunkuta shi kada gaba ya sake maimaitawa.."

Dai² lokacin anata hayaniya Tani ta k'araso gurin tana yatsina fuska da kallon mutane d'aya da d'aya,,babu wanda ya kalli inda take bare ya kula da abunda take tambaya game da hayaniyar da ake,dan haka ko da taga babu mai tanka matan sai ta nemi guri ta zauna kamar sauran tana maida kunnuwanta ga abunda ake tattaunawa akai,,Baban Sabina ne ya kalli inda LADO yake cikin jin zafinsa kamar zai yi magana,ko me ya tuna kuma sai ya fasa ya rabu da shi,musamman ma dan gudun kada ace dan akan y'arsa ne abun ya faru shi yasa yake hakan,,baffa ne ya kalli LADO yana cewa
"Kai LADO shin yanzun zaka sanar damu dalilinka na gayyato abokanka ku tare ta a hanya ko kuwa..??"
Tsam Tani tayi wacce duka zuwanta gurinkenan bata wani jima ba,cikin hargowa ta fara fad'in duk abunda yazo bakinta
"MALAM wannan wane irin magana ce kuma haka kake yi..!? In ce wannan maganar ya riga da ya wuce tun a shekaran jiya..amma kuma shi ne har yau abu yak'i ci yak'i cinyewa sai kwan gaba kwan baya ake akan wannan y'ar maganar..!"
Zuba mata idanu duka suka yi har ta dasa aya kafin baffan cikin takaici

Please Login or Register in order to submit comment