Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

"Waye ya zo Hameed..!?"
Yar dariya ya saki mai sauti sannan cikin salon jan rai yace
"Kai Yayah.. Wai baki san wanda yazo ba d'in..!?"
Ahanakli ta kad'a masa kai alamun haka ne,ficewa yayi saurin yi a guje yana fad'in
"Yayah Muhammad nake nufi Yaya..!"
A hankali sunan ya fara zagayawa ta cikin duka veins d'inta har ya kai ga ya samu damar bugun zuciyarta,nan take ta fara jin wani irin fad'uwar gaba na bijiro mata a sakamakon ambaton sunansa kawao da Hameed d'in yayi,har ta daina ganinsa bata fasa bin hanyar daya bi da kallo ba,bayan wasu yan mintuna kuma sai tayi zugum sannan ta koma ta zauna tana tunani a zuciyarta,saboda wasu irin mix-feelings da suka had'u suka cure mata a guri guda,a lokacin jinta take tamkar anyi mata albishir da zuwa hajji,bata motsa ba sai ma sake dunk'ulewa da tayi ta zura kanta a tsakanin kafafuwanta tana surutai ita d'aya
"Ya Allah shin nayi murna ko kuwa mene ne ya kamata nayi yanzun.!? Da gaske ne shi d'in ne ya zo..!? Ohh! Ya rabb help me..!"
Duka farin ciki da jin labarin zuwansa gaba d'aya yasa ta kasa samun sukuni,idan ta motsa nan sai ta sake dawowa duk ta rasa inda ya kamata ta nufa dan tsananin murnan da take yi.

Yadda suka shiga a guje haka wajen dawowa su labarta masa sak'on baffan na cewa da yayi ya shigo,suna tafe suna ture-turen juna su a dole sai d'aya ya riga d'aya fad'an sak'on duk da ba tare suka je gurin baffan ba,tun kafin su k'arasa kusa da shi Hamudan duk da ba shi ne yaje gurin baffa ba cikin karad'i yace
"Yace wai ka shiga..!"
Hararan sa Sule yayi yana cewa
"Dillah tafi can,,ai naga di ba haka baffa yace na fad'a ba.."
Murmushi Hammad yayi musu duka kafin yayi magana tuni Sule ya riga shi
"Cewa fa baffa yayi wai ba yace ka dunga shiga ba idan kazo..Shi ne ka tsaya a waje kamar bak'o."
Still murmushi ya sake yi kafin ya ce
"Ok..Ok.! Na gode duka,,yanzun maza kuyi sauri ko...Sai kun dawo zamu had'u,amma banda fad'a kunji ko..?"

"To Yayah.."
Suka amsa masa,daga haka kuma sai suka juya cikin sauri² duk da anayi ana tsokanar juna suka d'auki hanya,shima kansa Hammad bayan da yaga tafiyarsu sai ya juyawa ya nufi hanyar da zai sada shi da cikin gida kamar yadda baffa ya bashi izini,,tun daga bakin k'ofa yayi sallama nd ko da zai shiga ciki ma sai daya sake yin wani sannan ya shiga,a tsakar gidan ya iske tsiraru daga jama'ar gidan suna ta hidin-dimunsu na yau da kullum,sai da suka gaisa da su tukun kafin ya nufi d'akin saukar bak'in na baffa,da sallama ya iske shi a kishingid'e da alamun kamar bai jima da shigowa sosai ba duba da yadda yake fifita jikinsa a jik'e da zufa.Kok'arin tashi baffan ya shiga yi ko daya zauna fuskarsa cike da fara'a yake fad'in
"Mai babban suna,, kai ne tafe da wannan ranar..!?"
Murmushin shima yayi masa kafin ya amsa da cewa
"Ni ne baffa,,fatan na same ku lafiya..!?"

"Alhamdulillah..! Kam ya ka baro manyan naka..!?"
Dai² yana zama ya sake amsawa da
"Lafiyarsu k'alau baffa.."

"Masha Allah..! Haka kullum muke fata."
D'an jimm dukansu suka yi kafin baffa ya kalleshi yana sake murmusawa da fad'in
"Kada dai ace har hutun daka ce d'in ya k'are..??"

"A'a baffa,,hutu kam da saura.."

"Aihoo toh..! Nayi zaton ai ko har hutun naka ne ya k'are,nace lokaci babu wahala.."
Murmushi kad'ai yayi kafin ya sake sunkuyar da kai k'asa,kallonsa baffa ya sake yi kad'an kafin yace
"Amma mai babban suna,,tafiyar nan bata maka nisa ba,ka taso tun daga Kano har nan..!? Ai daka jira k'arewar hutun naka ko..?"
Gajeran murmushi ya saki a ransa yana fad'in
"Haba..! Baffa taya za'ayi zuwa nan yayi min nisa..!? Ai ko kullum ya kama nazo na taho..Bare dan nazo yau kad'ai.."

"Amm! Baffa ai da yake na lek'o makaranta ne,shi ne nace bari na k'araso mu gaisa,, nasan idan na tafi zai d'auke mu tsayin wasu kwanakin kafin mu sake ganawa.."
Tsintae kansa kawai yana fad'awa baffa hakan ba tare daya shiryawa yin hakan ba
"A'aahh! Ai kam ka kyauta sosai,,yadda ka rik'e zumunci da mu haka,babu abunda zamu ce dakai sai godiya da fatan alkhairi.. Allah kuma ya saka maka da mafificin alkhairinsa.."
"Ameen" ya amsa yana ci gaba da sunkuyar da kai dan wani irin kunyar baffan daya tsinci kansa ciki a sakamakon k'aryar daya gindaya masa wacce yake gudun ace ya gano hakan,,baffa kam bai san me yake k'issimawa aransa ba sai dai ya mik'e cikin sauri ya fita yana fad'in
"Mai babban suna,,Ina dawowa yanzun kaji ko..?"

"Toh baffa Allah ya tsare hanya.."
Ya bishi da addu'ar fatan alkhairi har ya fice.

Kamar wacce aka cillo daga d'akin ta fito tsakar gidan sai raba idanu take,burin ta duka a lokacin bai wuce ta gano shin da gaske Hamudan yake yi shi d'in ne yazo ko kuwa k'arya ne irin nasu..! Fitowarta dai² lokacin yayi dai² da k'arasowan baffa k'ofar d'akin nasu yana kwallawa Innarta kira
"Mairo..! Kina ina ne..!?"
Baffan ya sake fad'a yana dudduba tsakar gidan,daga cikin d'akin ta Inna tayi masa gyaran murya alamun tana sallah kenan,jinjina kai yayi sannan ya juya ga Sabina dake tsaye sai sunkuyar da kai k'asa take
"Yawwa uwata..! Maza zo ki samo ruwa mai d'an sanyi ki kaiwa MUHAMMADU..!"
Cikin sauri ta d'ago ta kalli baffa,duk da da farko tunaninta ya gama tafiya ne akan Hamudan yayi mata k'arya,sai dai ko da jin sunan da baffan ya fad'a yanzun take ta fara jin nutsuwarta tana dawowa jikinta a 360,da hanzarinta ta amsawa baffan kafin ta juya cikin tsantsar murna ta koma d'akin,tsallen murna da doka kafin ta fara rawa tana yi tana dariya kamar wata sabon kamu,wanda jin fitowar Inna daga d'aki shi ne yasa ta dakatawa da dawar da take ta fara neman kofin da zata kai masa ruwan sannan ta fita daga d'akin,ko data fito kallo d'aya Inna tayi mata ta d'auke kanta daga gareta ta koma ciki tana girgiza kai,tabbas ba sai wani ya fito ya fad'a mata abunda ke faruwa ba a cikin y'an kwanakin,itama da kanta ta fara fuskantar damuwar y'ar tata,ba tare data ce mata komai ba ta juya ta koma cikin d'akin tunda ta fito bata ga baffan ba,ita kanta SABINA ganin irin kallon Inna ke yi mata sai daya sata shan jikin jikinta,amma to yaya ta iya..?? Idan har bata yi zumud'i da zuwansa ba mene ne ya kamata tayi..?? Wucewa ta sake yi ta kinkimo madaidaicin tray ta d'ora mug d'in akai,bayan ta kawo k'aramin cup ta d'ora ta nufi hanyar d'akin da yake cikin.
Bakinta d'auke da sallama ta tsaya a k'ofar d'akin,,,shi kansa gogan tun daya zo gidan yake cike da son ganin ko da wucewar ta amma sai yaji shiru ko d'uriyarta bai babu sai yanzun da tayi sallama a bakin k'ofar shigowa d'akin,k'ayataccen murmushi ya saki kamar ance masa tana gani kafin ya amsa mata,,tsaiwa taci gaba da yi har kusan mintuna biyu kafin ta jiyo muryansa nan mai cike da nutsuwa yana amsa mata,sai dai yaji shiru tak'i shigowa dalilin da yasa shi maida idanunsa ga kallon hanyar da zata shigo d'in kenan nd cikin ransa yana ji kamar ya tashi ya janyota cikin d'akin tunda yaga bata da niyyar shigowa,,,ita kanta da take tsaye a gurin yanayin shirun data ji yayi bayan amsa sallamarta ba tare daya bata izinin shiga ba yasa nan da nan ta fara jin jikinta ya d'auki rawa,bayan a kullum tun daya tafi bata ganin shi take cikin damuwa,buh yanzun daya kasance yana kusa da ita nd take jin son ganinsa sai duk taji ta diririce tunma kafin suyi ido hud'u,da kyar ta samu ta saita nutsuwarta kafin ta kai hannunta ta d'age curtains d'in d'akin ta shiga tana sake yin sallama a ciki,,idanunsa kyar akanta tun data shigo har ta k'araso gabansa ba tare daya iya daina kallonta ba,duk da tana jin idanunsa akanta a hakan itama taci gaba da tafiyar,ko data zo dai² gabansa a hankali ta sunkuya tana niyyar ajiye tray d'in,a lokacin ne kuma taji zuciyarta tana fad'a mata ta d'aga kai ta kalleshi
"Shin yaya ya koma a cikin y'an kwanakin da bai zoba.?"
Ta tambayi kanta,,duk da tana kissima yanda ya koma d'in a ranta yanzun sai take jin kamar ya zartar yadda duk zuciyarta take sanar matan,dai² ta d'ago kai tana shirin kallonsa suka had'a ido da shi,cikin k'ank'anin lokaci tuni jikinta yaci gaba da rawa tamkar wacce aka jonawa shock,,sam bata kula da abunda take yi ba,sai muryansa data tsinto yana fad'in......





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
_Devoted to my lil 6ters *Real hafsy & Mamah Zee.*_
_Bestowed to *Sis Hubbeey.*_

*Bismillahir-rahmanir-rahiim.*

*13.*
_#Prejudices_

"Easy young lady..!"
Ya fad'a da wannan husky voice d'insan while yana kallon cikin idanunta,ita kam saurin janye idonta tayi daga kallonsa,sannan ta maida hankalinta zuwa kan hannunta,a lokaci guda shima Hammad ko da ganin tana neman juye masa ruwan ajiki sai yayi saurin rik'o gefen tray d'in nd still yana sake kallonta,sai a lokacin ta fahimci dalilinsa nayin magana dan yadda ta kusa kifar masa da tray d'in a jiki a dalilin kallonsa data tafi yi har bata san lokacin data kusa yin b'arin ba
"Sorry..!"
Ta fad'a tana gyara rik'on tray d'in a hannunta sai dai ya kasa zama stable saboda yadda duk jikinta yake rawa sannan ga shi sun kusanci juna wanda hakan yasa yanayin da suke ciki d'in yake neman yin tasiri akanta,kan tray d'in ya maida hankali ba tare daya sake kallonta ba ganin ta kasa tab'uka komai ya ce
"Uhhuumm! Saki..!"
Hannayenta tayi saurin janyewa daga rik'on da tayima tray d'in sai dai ta kasa motsawa a gurin,yadda ta girke ita bata yi gaba ba kuma bata yi baya ba,nd still tana nan a tsugunen tamkar wacce akayi sculpturing nata (sassak'a) sai yasa shi d'an kallonta kad'an,ko daya ajiye tray d'in a hankali ya sake d'agowa ya bita da wani shu'umin kallo,har ya bud'e baki kamar zai yi magana kome ya tuna kuma sai yaja baki yayi shiru,,har lokacin tana gabansa kamar mai d'aukan darasi ba tare data iya motsawa ba,haka shima bai ce mata ko ci kanki ba bare tayi tsammanin zai ce ta matsa,dan kanta ko data gaji da tsugunon sai ta d'an koma baya kad'an kafin ta mik'e duka ta juya da niyyar ficewa,,a hanakli yasa hannu ya d'auki ruwan yana k'ok'arin sha,har yasa kofin a bakinsa yaga ta mik'e tana shirin fita,kofin yana jikin bakinsa bayan ya kalleta sai ya d'an zame shi kad'an cikin wani murya yana fad'in
"Where do u think to go..!?"
K'yam ta tsaya a gurin ba tare data sake iya motsawa ba,shi kansa Hammad bai zato ba yaji maganar yayi escaped a bakinsa,a hankali ya d'an datse harshensa had'e da runtse idanunsa sabofa yadda maganar yayi masa fitar bazata,ta d'auki lokaci a tsaye a gurin ba tare data juyo ba,ko da ganin bata juyo d'in ba nd ya san bawai ji ne bata yiba sai yasa shi basarwa cikin shan k'amshi kuma yana sake cewa
"Kin manta sharad'in dana fad'a miki..? Ko kuwa kina sane ne,ganin daman bani amsa ne baki yi ba..??"
Still tana tsaye a gurin ta kasa juyowa bare ta kalleshi sai dai jikinta duka ya gama mutuwa,yadda yake magana da kowane motsawar second a duk lokacin da zasu had'u ita kam duk da tak'i jinin a dunga nuna mata isa nasa yanayin yana bala'in tasiri a cikin jini da b'argonta,musamman na yau data ganshi a lokacin da bata zata ba,ji take kamar ta koma gabansa ta tsaya nd ta bud'e baki ta tambaye shi shin ya dawo kenan ko kuwa zai koma..? Saboda yadda a y'an kwanakin da suka gabata taji wani irin kewarsa a tare da ita duk da bata san yaushe ne har tayi irin wannan sabon da shi ba da har zaisa taji rashin irin hakan a tare da ita,,buh a yanzun kam tana jin guiwoyinta a sanyaye duka da al'amarin sa,nd haka nan yanayinsa data sake gani yanzun a cikin idanunta sam bai mata kama dana mutumin da zata tsaya a gabansa tayi masa irin wannan shirmen bane,mutumin da ganinsa a daf da ita kad'ai yasa ta shiga razani,shin yaya zata kasance idan har aka ce tsaya gaba da gaba tayi masa irin wannan tambayar..?? Wannan tambayar shi ne ya fara zuwa mata arai,wannan dalilin yasa nan take sai ta sake tsintar kanta ciki wani irin zarani kenan wanda ta rasa gano dalilin da yasa take shiga irin wannan yanayin a wasu lokutan,tayi nisa a cikin tunanin abunda ya kamata tayi,nan ta sake jiyo shi yana fad'in
"U can go..Tunda haka kika zab'a.."
Daga haka bai sake magana ba ya shiga wasa da car keys d'insa,yanayin yadda yayi magana ya tabbatar mata bai ji dad'in abunda tayi masa ba,a hankali nd cikin rashin kuzari ta d'an waiwaya kad'an ta kalleshi kafin ta juyo dukanta,shi kam bai ko kalleta ba har ta fara takowa dan yadda ta sa shi jin wani iri har cikin zuciyarsa,cikin sigar jin haushi taga ya sake tab'e baki sai dai bai yi mata magana ba har ta koma ta zauna,shiru ne ya ziyarci d'akin na wani lokaci daga shi har ita babu wanda yace da kowa komai,a hakan har baffa ya dawo ya tarar dasu,lokacin ko daya shigo ya tarar da su duka sunyi zugum wa juna babu mai cewa komai,a hankali sai ya girgiza kai yana fad'in
"Uwata..! Ke kuma haka akeyi sai ki bar mutum shiru babu wani magana,ke kinyi shiru shima kin barshi shirun..Dad'in samarina kenan da su ne nasan yanzun da tun shigowa ta najiyo karad'in su.."
A hankali ta sake nutsewa cikin jikinta dan kunyar da kalamanta baffan suka sata ji tana d'an murmushi sama²,shi kuwa gogan d'agowa yayi ya kalleta sai daya sake tab'e baki kafin ya kalli baffa dake neman gurin zama yana cewa
"Baffa wai dama tana magana ne..!? Ni tun da nake zuwa ban tab'a jinta tana hira da kowa ba..I thought ma she's a deaf..!"
Sarai taji me yace sai dai baffa da bai gane me ya fad'a a last ba,buh duk da hakan sai yayi murmushi
"A'aahh! Sosai ma,,ai kuwa uwata tana magana sosai,sai dai ko da yake baku yi sabo ba shi yasa take zama shirun.."

"Uhmm! Ai kuwa dai baffa sai dai idan ku take iya yima magana,,,amma ni ina tunanin tunda na santa bana jin zan iya tuna abunda na tab'a jin daga gareta."
Dariya baffa ya sake yi shi kuma hakan sai yasa yayi amfani da sautin dariyar baffa wajen furta
"Shi yasa nayi zaton ko kurma ce ai..!"
Saurin d'agowa tayi ta zuba masa ido jin abunda yake fad'a,sam bata yi tsammanin idanunsa suna kanta ba a lokacin dan haka sai ta shagala wajen kallonsa,muryarsa ta tsinto k'asa² kamar na mutumin dake son yin rad'a
"Kallon fa..Na mene ne.!?"
Saurin sunkuyar da kai tayi k'asa dan ko kad'an bata yi tsammanin ita yake kallo ba,cikin k'unk'unin masifar abunbuwan da yake mata tun zuwansa duk da ta kasa gane ma'anar hakan ta furta
"Kaii..! shi wannan ya cika baud'ad'd'en hali,,yanzun yayi magana kamar ba shi yayi ba..huh.!"
Wani mugun smirk ya saki ba tare daya kalleta ba ya furta
"Baffa..! Ni kam wai mene ne asalin sunanta ne..!?"
Murmushi baffa yayi kafin ya kalle su duka
"A'aahh! Wannan kuma ka tambayeta gata nan gama nan,kasan ance wak'a a bakin mai ita yafi dad'in sauraro ko..?"
Jinjina kai yayi yana murmusawa,ba tare daya kalleta ba ya furta
"Y'an mata..! Mene ne ainihin sunan ki ne..!?"
Sai data harare shi kafin ta furta
*"HAFSAH..!"*
Jinjina kai yayi kafin yace
"Suna mai dad'i.. Buh mene ne ma'anar sunan naki ne..I hope dai kin sani ba wai sunan kawai su baffa suka sa miki,ba tare da kin san ma'anar saba..!"
Wannan karon sai data d'ago ta kalleshi kafin ta harare shi tana girgiza kai a hankali,aaboda yadda yayi tambayar gani tayi kamar da rainin wayo a cikin maganarsa,baffa kuwa yana jinsu yana kishingid'e sai murmushi kawai da yake yi
"Malama kada ki k'ara yimin wannan abun daga yanzun,,,dan haka wannan ya zama na k'arshe da zance kinmin wani abu..A kiyaye ko dan gaba..!"
Kallonsa tayi saurin sake yi a tunanin ta zata ga yana kallonta,amma sai taga hankalinsa kamar yana kan keys d'insa,d'auke kainta tayi itanma sannan ta bud'e baki da kyar tace
"Origin of name Hafsa,was the name of prophet Muhammad (P.B.U.H) wife,nd a daughter of sayyadina Umar bin khattab (R.A),,in English HAFSAH has different meaning first of it,beautiful,moon,young lioness nd...!"
Jinjina kai yake tayi tunda ta fara magana,haka nan jin yadda take furta ko wane harafi a muhallinsa kai kace ita ne asalin grammar
"Masha Allah.. That's great..Bravo alaik..!"
Yadda yayi maganar yana lumshe ido tare da jinjina kai ba tare daya bari ta k'arasa fad'an abunda ke bakinta ba yasa ta sakin d'an murmushin jin dad'i itanma,a hankali kuma jin tayi shiru sai ya sashi d'agowa,shi kansa lokacin ko daya d'ago ya ganta tana murmushi har cikin ransa sai da yaji dad'in hakan,a nan ne har ya shagala da kallonta na tsayin lokaci,while deeply kuma yana tambayar kansa
"Ohh.! Ashe dai da gaske tana da baki har haka..? Why to ni a lokuta da dama take min shiru..!? Kenan hakan yana nufin laifina ne ko me..??"
D'an murmushi yayi kafin ya sake yin magana a zuci
"Lallai kuwa zanyi ta saki magana a duk lokacin da muka had'u,,imma kin shirya ko baki ahirya ba..!"
Cikin dabara ya d'ago ya kalli baffa dake kishingid'e idanunsa a kulle,sannan a hankali ya maida kallonsa kanta cikin hikima irin nasu na Psychologist ya shiga watso mata tambayoyi kan abubuwan da suka shafeta,duk da ba kowanne yake samun amsa ba dan yadda take magana,amma dai yana samu ta amsa wasu kai tsaye wasu kuma sai ta d'an yi jim,nd wasu ma shiru kawai take bata amsaau sai dai ya tsallake su,,wannan lokacin kam duka k'in barinta yayi ta motsa a gurin,nd wani abu daya d'aure mata kai shi ne,lokacin da yake yiwa baffa wani magana,wanda yasa ta binsa da kallon mamaki sai dai bata fahimce shi ba,abunda ya faru kuwa shi ne a lokacin suna magana da baffa sai taji shi yana cewa
"Baffa..Ni kuwa ina son fad'a maka wani magana,,ko tambaya zance nema i dunno know how ya kamata ace nayi maka maganar,buh tun tuni nake son ace nayi ta,amma dai..!"
Sai kuma yayi shiru yana kallonta k'asa²,murmushi baffa yayi yana gyara zamansa daga kishingid'a zuwa zama sosai da fad'in
"Toh..! mai babban suna..Ina sauraronka,,zaka iya fad'a min ko wane magana ne kada kaji shakka,ni ai matsayin d'a kake a gurinmu,mene ne abunda zaisa ka kasa sanar min kuma..?"
Murmushi yayi cikin hikima kafin ya furta
"Wollahi baffa,wata na gani ne a cikin garin nan,,to amma kuma ni abunda ban sani ba shi ne,shin ko zata iya zama dani..??"

Murmushi baffa yayi irin nasu na manya kafin ya amsa masa
"A'aahh! Mai babban suna,,dama wannan ahi ne maganar da kake jin nautin fad'a,amma kuwa anya yanzun akwai yarinyar da zata kalli saurayi kamarka ace ta nuna bata ra'ayi..? Ai wannan abun a duba ne..Na tabbatar duk macen da zaka ce kana so bawai iya nan garin ba,a ko ina take a fad'in duniyar nan,ko da ace y'ar wani mai muk'ami ce,na tabbata ba zata tab'a k'inka ba..Sai dai kuma dan wani dalili nata can..Amma bana jin za'a samu.."
Murmushi ya sake yi mai k'ayatarwa kafin ya ci gaba da kallon reactions d'inta ta k'asan ido
"To amma baffa,,idan kuma aka samu akasi fa iyayenta suka nuna basa ra'ayin na,a matsayina na wanda ya fito yak'in neman aurenta..!?"

Dariya baffa ya sake yi sannan ya ce
"Shi yasa tun farko ai na fad'a maka,yadda na fahimci halayenka gaskiya bana zaton za'a samu wani uba da bazai so mutum irinka ya kasance suruki a gurinsa ba,yadda na d'auke ka a zuciyata bana tunanin akwai wata yarinya da sata fito tayi da'awar ta fi k'arfin kana,yo ko k'asar masu jajayen kunnuwa idan da zaka je a gujema zasu dunga kawo kansu bare mu a nan..Saboda haka ina son ka fad'a min ko y'ar gidan waye in dai har a cikin garin nan take,na yi maka alk'awarin ni da kaina zan shige maka gaba har sai na tabbatar da ka sameta.."
Murmushin jin dad'i yayi saboda yadda kalaman baffa suka gama faranta masa,,ga *SABINA* kuwa duk wannan surutun da yake yiwa baffa tuni nutsuwarta ta jima barin gangar jikinta,dan a wannan lokacin bana jin ta fahimci akan mene ne suke tattawar bare har ta iya gano wani abu ko kuma inda maganar tasu ta dosa,,though ma dai duk da bawai ace ya ambaci suna ba ne,amma haka nan sai ta fara jin zuciyarta tana tsinkewa,runtse idanunta ta d'anyi a hankali yayin da take jin wasu irin bak'in yanayi suna ziyartar ta,cikin sauri ta mik'e ta nufi hanya ba tare data yi musu magana ba,har ta isa bakin k'ofar fita baffa ya kallota yana fad'in
"Uwata ina kuma zaki je,,naga kin tashi..Ko kuwa har kin gaji da hiran..!?"
Ba tare data juyo ba sai dai yanayinta zuwa lokacin gaba d'aya ya sauya
"A'aahh! Baffa zan jene na sha magani,,naji kaina yana min ciwo..!"
Ta gefe ya kallota yana sakin murmushi dan gaba d'aya ya gama fahimtar inda ta nufa da dalilin da yasa ta tashi
"Subhanallah! Amma uwata yanzun nan fa lafiyar ki k'alau kuna ta hira..!"

"Ehh! Baffa nima yanzun ne naji kan nawa yana sarawa..Shi yasa zanje na duba magani,kafin ya dame ni.."
Ta karashe maganar had'e da dafe goshinta da take jinsa kamar zai fad'o k'asa
"Sannu uwata Allah ya baki lafiya,,maza to ki hanzarta ki samu magani ki sha kinji ko..sai ki d'an kwanta ki huta..!"

"To baffa.."
Tana fad'a tasa kai ta fice ba tare data jira taji me zasu sake tattaunawa akai ba,idanunta cike da damuwa take tafiya wanda yasa ko ganin inda take jefa k'afafunta ma bata iya tantancewa,a haka har ta k'arasa shigewa d'aki,da shigarta ciki ko data tsinci kanta a tsakiyar d'akin kan gado ta kife had'e da sakin wani marayan kuka mai tattare da ban tausayi.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥


Please Login or Register in order to submit comment