Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sakamako,zuwa k'arewar drip d'in daya jona mata,, godiya Hammad yayi masa sosai sai ya juya kad'an inda take yana sauke wasu irin wahalallun numfashi,murmushi tayi masa mai sanyi tana lumshe idanunta,shima sai yayi k'ok'arin k'irk'iro murmushin ya mayar mata,,bayan wucewar wasu lokaci masu d'an dama nurse d'in data d'auki jininta ta dawo da result,ta mik'awa Dr JABEER,kallo daya yayiwa takardar ya sauke ajiyar zuciya mai tafe da kyakykyawan murmushi,then ya mik'awa Hammad d'in hannu suka yi musabaha while yana fad'in
"Congratulations dude.!"
Kansa a d'aure yabi Dr JABEER da kallon mamaki kafin yace
"Akan me kenan Dr.?"
Takardar Dr ya mik'a masa sai yayi hanyar fita daga office d'in cos akwai round off da zaije yi a time d'in nd yana tafiyar yake fad'awa nurse d'in ta kula da ita,cos yana tunanin kafin ya dawo drip d'in zai iya k'arewa,cikin girmamawa ta amsa masa,sai ya fice ya barsu,itama nurse d'in fita tayi da nufin duba wasu aikin da take kafin ya k'are d'in,,,zubawa takardar ido yayi,zuciyarsa cike da wani irin mix-feelings da suka had'e guri guda suka bada wani irin bold expressions,ko gama nazartarta bai jira yayi ba ya damk'e ta a hannunsa,yana sakin murmushin da shi kansa bai san daga inane yake zuwa masa ba
"Alhamdulillahillaziiy bii ni'imatihi tatimmus'salihaat..!"
Yake ta jerawa har ya iso bakin gadon,daga gefenta kad'an ya zauna,while yana rik'o d'ayan hannun nata da babu komai a jiki ya damk'e shi da kyau,cikin k'arajin murna ya furta
"Thank u helpmate,,thank u so much for making my day extra special..Ana ahabbuk-thtiir."
Sai ya sunkuya k'asa² ya bata wani irin light kiss a saman lips d'inta,,murmushi ta sake yi masa mai taushi da fad'in
"Shhh! Wa'ana kamaan habibiiy,,anaa ahabbak-thtiir,,buh why are u thanking me,,am always ur's fa ko har ka manta ne.? nd u are mine,,wannan kuma kyauta ne daga ubangijin mu daya azurta mu da shi,so gare shi ne kawai yafi cancanta muyi godiya duka ko ba haka ba.!?"
Kai ya d'an gyad'a mata yana murmushi,a hankali sai ya d'ora palms d'insa ya shafi gefen fuskarta while yana cewa
"Allah ya bamu ikon kula da shi,from now till lokacin zuwansa duniya,,nd ya bamu ikon yi masa tarbiyya akan tafarki madaidaici..."

"Ameen" tace tana masa sihirtaccen murmushi before ta sake maida idanunta ta lumshe,from deepest na zuciyarta tana jin wani sanyin rahama na ratsata da yasa take jin kamar tafi ko wace mace sa'a a duniyar..Almost 2 hours suka d'auka a hospital d'in bayan an cire mata k'arin ruwan an sake dubata an tabbatar komai lafiya,sannan Dr JABEER d'in ya sake d'ora su akan shawarwarin yadda zasu kula da cikin,after kuma sai ya sallame su,sun masa godiya sosai sannan suka d'auki hanyar komawa gida,,fitowarsu babu jimawa suna tafiya cikin mota hannayensu mak'ale da juna cos suna cikin farin cikin da baya tab'a misaltuwa nd kanta na kwance a jikin shoulder d'insa,duka sunyi wani irin shiru amma kowa da tunanin da yake a ransa,a hankali murya can k'asan mak'oshi ya d'an kalleta kafin yace
"Helpmate.! Ina muka nufa yanzun.!?"
Idanunta a lumshe tace masa "Gida"
Murmushi yayi yace "kin fasa rakiyar amaren.!?"

"Um'um.! Ai nasan ko naje ma lokaci ya k'ure min,tuni an kaisu ma yanzun kam,,na je musu daga baya.."

"Okay.!" Yace sai yaci gaba da tuk'i abunsa,,daga cikin asibitin Nassarawa sunyi y'ar tafiya sosai,a lokacin jin tafiyar tak'i k'arewa har take masa k'orafin har yanzun basu iso ba.? Sai yace mata "saura kad'an" ba tare data bud'e idanunta ba sai tace "toh",basu jima da yin maganar ba suka iso bakin get d'in gidan,yana tsayawa da mota a hankali aka yage masa get,ya shige ciki yana d'agawa get man d'in nasu hannu cos glasses d'in motar duka suna rufe,har ya isa carport bata bud'e idanunta ba,sai data ji motar ta tsaya ne a hankali sai ta d'ago kanta ta kalleshi,murmushi yayi mata mai sanyaya zuciya sannan yace
"Welcome to ur palace my Lady.."
Y'ar dariya tayi sannan ta juya tana k'ok'arin fita while tana fad'in
"Baka gajiya da zolaya wollahi.."
Murmushi yayi yace
"Kema haka..!"
Fitowarta daga mota bayan ta kalli inda suke sai ta tsaya cak tana sake k'arewa ilahirin farfajiyar gidan kallo,tabbas ba gidan Mamma bane nan d'in,"shin ina ne to nan d'in ya kawo su.!?" Bata gama tunanin ba taji ya bata wani irin wawan rungumar da sai data so firgita,da yake ta bayanta yake tsayen sai ta d'aga ido a hankali ta kalleshi while tana furta
"Ina ne nan d'in muka zo..!?"

"It's our new home."
Ya bata amsa a tak'aice,gyad'a kai kawai tayi sannan tace
"Toh ai naga ba nan ka d'auko ni ba,,shi ne zaka taho da ni.?"
Wani irin kallo yayi mata mai d'auke da sak'onninsa sannan yace
"Da na tambayeki me yasa baki min specifying ba.!?"
Jimm tayi tana sake bin ilahirin gurin da kallo gaskiya ta ko ina gidan yayi mata ita kam,yadda tun daga haraba gidan ya tsaru tamkar wanda aka kwafo daga k'asar turawa ko aka d'auko hayar masu ginin daga waje,duk inda ta kalla sai ta ganshi gwanin burgewa,duk girman gidan kuma ta side's dinsa an wani k'awata shi da wasu irin shuke² masu matuk'ar kyau da dad'ad'an k'amshi,,hannunta ya rik'o a hankali sai ta d'aga kai ta kalleshi sannan suka fara tafiya slowly daga carport d'in zuwa ainihin k'ofar da zai sada su da cikin gidan,suna fara tafiya daga gurin da suke tsayen amma ji take inama ya kyaleta ta gama k'arewa gidan kallo,a cikin zuciyarta kuwa banda addu'ah babu abunda take musu da godiya ga Allah akan yaci gaba da kare su daga sharrin masu sharri sannan ya sawa zamansu albarka tare da kad'e musu dukkanin wani abun k'i,har suka iso bakin k'ofar da zata sada su da cikin gidan bata bar kalle² ba,ko bakin k'ofar ma dai shi kansa abun kallo ne,haka taita kalle² abunta yana tsokanarta,nuna masa tayi ko a jikinta,da taje wani gurin tayi gara tayi a nata,a haka har ya janyeta suka shige ciki yana rik'e da ita yana mata dariya,shi kansa parlor'n abun kallo ne dan ta ko ina ya gama had'ewa,fad'ar irin dukiyar da aka zuba a gurin kuwa zai zama kauyanci ne da b'ata baki just imaging,sai da ya d'an zagaya da ita saura gurare daga bedroom d'inta zuwa su kitchen da master bedroom,d'akunan yaransu da suke fatan haifa,,ko ina ya kaita ta gani kuma ta yaba,tsabar murna har kasa magana tayi sai k'ank'ame shi da tayi tana ihun murna da yi masa addu'o'i iri²,bayan d'an lokaci sun gama kewayensu a nan cikin gidan da yake dare ya dan fara yi sai ya janyeta suka nufi master bedroom d'insa,,kada kuso ganin k'auyancin mutuniyar a time d'in da suka shigo,saboda yadda taga an tsara d'akin gaba d'ayansa cikin adon white daga kayan ciki har paint komai fari ne zallah babu sirkin colour,sai ta shagala da kallonsa tana kuma mamakin yadda aka tsara gidan,iskar daya busa mata a fuska ita tasa ta kallonsa da sauri,cos lokacin duka ita har ta manta ma jinya take sai ya kamo hannunta ya zaunar gefen bed sannan ya kwanta a saman laps d'inta,hannunta ta kai saman kansa tana shafa kwantaccen sumarsa da ya d'an d'aga,idanunsa a cikin nata suna kallon juna da wani irin shauk'i a cikin idanunsu,sun d'auki lokaci suna ma juna kallon tsakiyar ido kafin suka sauke ajiyar zuciya,,k'afafunta ta fara motsawa a hankali saboda wani irin yamm da taji suna yi mata sai ya d'ago ya kallota da fad'in
"Lafiya..!?"

"Ummm! K'alau."
Tace tana ci gaba da motsa k'afar,tashi yayi ya zauna sosai a hankali ya kamo k'afafun ya d'ora saman nasa da yayi flexing ya fara matsa mata su,lumshe idanunta tayi a hankali sau ta zame ta kwanta tayi wani irin luf kamar tana bacci,sai duk d'akin ya d'auki shiru sai kukan A.C dake fita,tafiyar tsutsa ya d'an yi mata a tafin k'afa,sai tayi saurin lankwashe su,tana shirin janyewa ya sake damk'e su da kyau,still yana ci gaba da mata matsar k'afar yana kuma had'a mata da tafiyar tsutsa,dariya tayi tana fad'in
"Please habibiiy.! Ka bari babu dad'i fa."
Murmushi yayi mata mai sauti yace
"Babu dad'in kike dariya.!?"

"Ehh! Babu wani dad'i kam,buh kawo k'afarka kaji."
Sai ya sake yin murmushi kawai yana mak'ale mata kafad'a,cikin salon son ya canja musu hiran kuma sai yace
"Yaya kika ga gidan naki..!?"

"It was nice nd very massive.."
Ta bashi amsa cike da zumud'i
"Umm! Yayi miki kyau ne.!?"

"Ehh! Sosai fa yayi matuk'ar tafiya da ni" har ta yi shiru kuma sai ta kalle shi da fadin "Umm! Shud i ask.!?"
Yace "Mene ne.!?"
Juyawa tayi ta hango gefen had'ad'd'en reach-in closet d'insu while tana fad'in
"Waye ne yayi illustrating d'insa.!?"
Murmushi yayi mata da fad'in
"Ohh.! Yanzun baki san aikin waye wannan ba..!?"
Gyad'a masa kai tayi saurin yi tana kallonsa,sai da sake yin murmushi then yace
"Sai na fad'wa Bassam nace kin manta aikinsa.."
Y'ar dariyar tayi irin ta mantawa d'in nan da fad'in
"Please habibiiy banyi tunanin shi yayi bafa."
Ba tare da ya sake cewa wani abu ba sai ya ci gaba da mata tausar yana yi yana dariya k'asa²,daga nan kuma sai suka zarce da wasanni wanda ya kaisu ga bawa juna kulawar data dace.

A gidan amare da angwaye kuwa a wannan daren sun raya shi ne da nuna tsantsar godiya ga mahalicci wanda shi ne ya ara musu rana da kuma ganin nasu lokacin suna masu tsayin rai,daga nan kuma sai suka k'arasa raya shi da nunawa juna tsantsar k'aunar da aka jima ana ginawa..Tun daga wannan ranar haka ko wace rana da zata zo ta wuce sai ya zama suna cike ne da nunawa junansu kulawa ta musamman tare da sake k'arfafa alak'ar dake tsakaninsu,,ko wane b'angare dai² gwargwado suna iya k'ok'ari wajen girmama junansu,babu raini bare wulak'anci,a haka rayuwa ta ci gaba da tafiya.

Bayan wucewar wasu kwanaki da yin bikinsu,tun a gida Nigeria suka gurji sadakinsu son ransu,daga nan sai suka fara shirin komawa bakin aikinsu,cikin d'an tak'aitaccen lokaci da zuwan sun samu damar zagaye dangi yayin da suka cika y'an uwa da alkhairi,bayan nan kuma suka bi jirgi zuwa k'asar ta U.S cike da nasarori da a kullum suke fatan samu,ma'ana su kasance k'ark'ashin inuwa d'aya.
Tun a Nigeria kafin su koma New York da incidence d'innan ya faru a ranar da za'a kai su Badra,tsakanin Sabina da Fauzah,shi kenan sai ciki ya fallasata,tun daga nan tsurfar yau da ban na gobe da ban,sai dai bata wani laulayi mai zafi,bacci ne dai take yawan yinsa bayan shi ko sai d'an banzan kwad'ayi,idan ta samu lime juice ta tsiyaya shi cikin cup sai ta kawo zuma ta zuba akai,haka za tayi ta shan abunta,yayin da tsamin ke mata dad'i har ranta,Yallab'ai dai tun yana nuna baya so har ya gaji ya rabu da ita,cos yayi ko daya tuntub'i Likitoci da dama suka ce masa babu matsala sai ya zuba mata idanu,wani lokacin ma shi yake had'a mata,tun abun bai shiga jikinta ba har ta saba ko me zata ci sai ta sha had'in lime juice d'inta take samun kwanciyar hankali,,a b'angaren skul ma dai tunda suka dawo d'in suna zuwa babu fashi kuma ko kad'an babu abunda ya tab'a karatunsu,kullum suna kan mai da hankali da duk abunda ke faruwa,,a hankali kwanaki suka ci gaba da tafiya yayin da a kullum take cikin samun kulawa ta musamman daga gare shi dama su Badra da tun bayan da suka san tana d'auke da juna biyun suke kulawa da ita sosai cikinta kuma yana k'ara girma.

A wani wayer gari lokacin cikinta yana da wata biyar dan har ya d'an kumburo ana iya ganewa,kasancewar safiya ce suna kwance manne da juna,tun bayan da suka idar da sallah sai suka koma baccin safe kasancewar yace fad'a mata ranar ba zai fita ba,sai ga kira around 6:00am ya shigowa Hammad d'in daga office d'insu,cikin gaggawa bayan ya amsa kiran ya fara shirin fita,tana daga kwancen ta kalle shi ranta a d'an had'e tace masa
"Amma fa cewa kayi babu inda za ka yau d'in.! Yanzun kuma fa.!?"
Waiwayowa yayi yana kallonta shi kansa ba'a son ransa zai je ba,amma saboda ance masa it was urgent,kuma kiran yana da muhimmanci ne yasa zai je d'in
"Aasiif my Lady.! Ya zama dole ne sai na fita,buh kinsan tunda nace bana fita yau,idan ba irin wannan kiran ba babu dalilin da zai fitar da ni..Zan je na duba naji kiran da ake min,,amma ba zan dad'e ba sosai kinji..!? In sha Allah yanzun zan dawo.!"
Yadda yayi mata magana cikin taushi sai ta d'age zpread d'in da take rufe da shi ta sauke k'afafunta k'asa,a hankali ta taso zuwa inda yake cikin tafiyar ta mai jan hankali,yana tsaye yana buttoning shirt d'in jikinsa har ta iso sai ta rik'e hannunsa,bayan ta taimaka masa ya k'arasa shiryawan sannan cikin sauri tayi making masa 1 cup na coffee da toast,a tsaitsaye ya ci sannan suka yi sallama ta masa rakiya har bakin k'ofar apartment d'in nasu,,yana fita apartment d'in sai ya d'an tsaya a bakin door d'insu yana kallonta da wani irin yanayi masu wahalar fahimta a tare da shi yace
"Bye Lady,,ki kula min da kanki kinji,,nd kada kiyi aiki mai wahala,in sha Allah i will be back soon.."
Murmushi tayi masa mai k'arawa zuciya nutsuwa sai ta d'an rausayar da kai cike da kewarsa tace
"Tamm!"
Sai yace "kinyi ALK'AWARI baza kiyi ba ko.!?"
Kai ta gyad'a masa tana lumshe idanunta,a hankali sai ya matso jikinta ya bata warm hug slowly ya had'a da bata peck chicks d'inta zuwa forehead d'inta,stilltana kwance jikinsa ya kai hannunsa ya shafo cikinta yana sauke ajiyar zuciya yace
"Please Lady,, kada ki bawa baby wahala,idan kinji ba zaki iya zaman ba,please ki nemi su Badra su taya ki zaman kin ji..!? Amma kada kiyi aikin da zai gajiyar da ke."
A tare sai suka sake sakon siraran ajiyar zuciya then ya wuce yana waving d'inta,tana tsayen tana kallonsa ya fara tafiya,fitowa tayi kad'an ta tsaya jikin k'ofa tana kallon bayansa har ya kai bakin elevator yana niyyar shiga,,haka nan bata san mene ne ya faru ba taji wani irin mummunar fad'uwar gaba ya ratsa mata zuciya har bata san lokacin da ta kwalla kiran
*"HAYAT..!"*
Slowly ya tsaya yana sakin wani irin murmushi mai narka zuciya kafin ya d'an juyo gently,inda yake tsayen ta fara tahowa zuciyarta a raunane har ta iso,tana zuwa sai ta shige jikinsa ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi,haka nan sai take jin cikin k'ank'anin lokaci tafiyar tasa ta tsaya mata a rai kamar tace masa ya fasa zuwan,buh k'arfin hali irin nata sai yasa ta kasa bud'e baki ta sanar masa yanayin da take ciki,,holding d'inta yayi tight suna nan tsaye har wayarsa ta sake yin k'ara,yana dubawa ko da yaga kiran daga Sultan ne,sai ya mayar da wayar silent a hankali bayan sun more tsayawa rungume da junan yayi ta jero mata kalaman da yasan zasu k'ara mata k'warin guiwar zama har yaje ya dawo d'in,sannan ya zareta a jikinsa yana goge mata hawayen,,sai da suka sake yin sallama yana niyyar tafiya ta rik'e shi gam,still tana kallonsa d'in sai ta masa alama ya d'an rage mata tsayinsa,hannayenta ta kai saman wuyarsa bayan ta zagaye shi da su,a habakli sai ta kai bakinta kan nasa,cikin salonta passionately tayi kissing d'insa,almost five minutes suna mak'ale da juna kafin tasake shi a hankali ta koma baya tana masa d'an murmushin k'arfin hali,cikin mutuwar jiki shima yayi saurin shigewa cikin elevator d'in,amma deeply ji yake kamar ya fasa,buhbaabu yadda zaiyi dole ne yaje shi yasa ya bawa kansa k'warin guiwar tafiyar,sai data ga tafiyarsa sannan ta juya a hankali tana sauke nauyayyun ajiyar zuciya,,ko data koma cikin apartment d'in jikin glass curtain wall d'insu ta nufa tana hangen waje,almost 5 minutes da tsayawarta a gurin sai ta hango fitarsa daga cikin Tawer d'in,hannunta ta sauke jikin wall d'in ta dafe sosai while d'ayan yana dafe da cikinta,cikin muryarta mai tattare da rashin kuzari ta furta
"Good luck for all ur efforts habibiiy,may u get what u truly deserve,,my good wishes are always with u,go for it HAYAT.!"
Tamkar ya jiyo me tace a dai² lokacin sai ya d'ago kansa slowly ya kallo location d'in da dark glass wall d'in yayi masa shamaki da gamo abunda ke ciki had'e da yin kwantaccen murmushi,cikin wani irin sanyin rahama shima sai ya furta
"U might not be with me,but u are always in my mind..The way u walk,fight,smile nd cry,is all am dying to see...I miss u baby,cos u are my life.."
Sai daya d'an jima yana kallon gurin sannan a hankali ya k'arasa carline ya shige motarsa had'e da barin harabar gurin....



*#Mene ne yake shirin faruwa ne wai haka.!?*



#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*


*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••
*So much happiness that u could see on my face was because of ur loving grace,ur wishes truly made my day nd all the things that u wished to say,,just a big heartfelt thanks from me.💔*
*Thank u all for making my heart smile 💕...I love u..♥*


*51.*
_#Fairyland_

Direct yana barin gurin 26 Federal Plaza ya nufa da yake a nan branch d'insu yake a cikin 23rd floor,kasancewar shima d'in a cikin fifth avenue d'in yake shi yasa sai bai wani d'auki dogon lokaci ba ya k'araso,,tun daga fitowarsa daga elevator wad'anda ke k'asansa a matsayi suke ta aikin gaishe shi,amma da yake yana cikin sauri ne sai dai ya d'aga musu hannu kawai ya wuce,buh baya tsayawa har ya iso office d'in director d'in sun kasancewar shi ne ya kira shi,,a bakin entrance ya tsaya after yayi knocking door d'in,aka bashi izinin shiga daga ciki,sai ya tura k'ofar a hankali yana shiga,,zaune ya iske Director d'in sun Moses Clinton da Assistant dinsa,sai Sultan,Sadeeq sannan da wasu fuskokin da dama duka daga cikin ma'aikatan sun,wanda duka a k'iyasin da yayi daga shigarsa baya tunanin za su wuce twenty a yawa,shi kansa sai da yayi gaisuwar tukun ya koma saman meeting table d'in daya tarar da su a zaune
"Have ur seat please.!"
Mr Moses Clinton ya fad'a cikin tsadadden turancinsa yana masa nuni da kujerun dake gurin wanda babu mutane samansu
"Thank u sir.!"
Ya fad'a shima sai ya nemawa kansa gurin zaman,,gurin yayi remaining silence na wucin gadi,before Mr Moses Clinton ya fara koro musu jawabin dalilin taruwarsu,wanda duka ya ta'allak'a akan wani workshop da zasu gabatar,kuma duk wanda akayi selecting d'in fuskarsa tana gurin,cikin zallar turancinsa da babu sirki ko algus yake musu bayanin yadda ake so aikin ya gudana,nd abu ne na sirri da dole sai sun keb'ance kansu har na tsayin 1 month,ba tare da fita ko nan da can ba,besides kuma aikin duka a nan cikin branch d'insun zasu gabatar da shi,,tunda Mr Moses ya fara koro musu bayanin Hammad yayi wani irin shiru yayin da fad'uwar gaba da wasu irin gumin tashin hankali suka fara ziyartarsa,,inwardly kuwa tunanin yadda zai iya barin Lady d'insa yake har na tsayin wata gudan ba tare daya ganta ba,yasan a irin situation d'in da take dole tana buk'atar kulawa sosai,matuk'ar aka ce zaiyi one month ba tare da ya ganta ta ganshi ba yaya kenan.? Wane halin zata shiga saboda rashin zamansa kusa da ita.? Shi d'in wane halin zai shiga shima,nd waye zai tallafe shi ya kula masa da ita.? Besides kuma yanzun duk suna tsakiyar semester ne bare yace zai maida ta 9ja zuwa lokacin da zai kammala d'in yasan hankalinsa indai ya kaita can ba zai tashi sosai ba nd shima d'in yasan idan dan ta shi ne zai iya bada hankali kan aikin har su gama,tunda yasan bata tare da shi,,ko gama tunani bai bari yayi ba akan wannan shawarin sai yayi saurin katse tunanin kaita wani 9ja,cos ya san ma abune da bazai tab'a iya faruwa ba,he want's her by his side,shi yasa da wuri yayi cancelling batun komawarta gida,,after some prolong da aka d'auka ana ta shawarin yadda aikin zai tafi sai Mr Moses d'in ya sallame su,,after taron ya watse duka jikin Hammad a matuk'ar sanyaye ya iya mik'ewa a gurin sai ya bi bayan su Sultan da tuni suka fita,suka d'auki hanyar komawa gida kowannensu yana cikin motarsa,,buh a side d'insa tunanin yadda zai sanar mata batun workshop d'in duk ya hana masa sakat har ya k'araso carline na wajen ginin Tawer d'in,,dai² yayi parking tsakiyar carline zuciyarsa cike taf da taraddadin yadda zai fuskance ta da batun ya fito ya fara tafiya har ya isa entrance,shi ya fara shigewa cikin elevator d'in sannan su Sadeeq cos ya riga su k'arasowa ma duka,,tun da suka shiga babu wanda ya iya magana a haka suka yi sama,,can daga k'arshen elevator d'in ya koma had'e da jingina spine d'insa a gurin ya runtse idanunsa while fuskarsa na bayyana damuwa sosai,,Sultan daya kula da sauyin da aka samu a tare da shi sai ya kalleshi yana tambaya
"Dude.! Are u ok..!?"
Gyad'a masa kai kawai yayi,bai iya yace masa komai ba,sai shi Sultan d'in daya tsaya kallonsa bakwai har na d'an wani lokacin kafin yace
"Ko dai kana tunanin aikin nan ne..!? I mean yadda zaka barta a gida ita d'aya har na tsayin 1month.."
Idanunsa yayi saurin bud'ewa sai ya sauke su akan Sultan d'in while yana sakin ajiyar zuciya,Sadeeq dake gefe kasancewar su uku ne a cikin gurin kawai sai ya dafa shi slowly yace
"Buh dude! I think yanzun ba ita kad'ai bace ko.? Besides kuma ya kamata ace ka godema Allah da yasa muna da yawa a nan d'in,,don't bother ur self mana man,tana fa da y'an uwan da za su d'ebe mata kewa ko da baka kusa.."
Sake sauke ajiyar zuciya yayi still sai bai ce da su komai ba har suka iso floor d'insun,elevator yana tsayawa shi ya fara ficewa duk da shi ne a ciki,ya wuce jikinsa duk a sanyaye har ya kai entrance na apartment d'in su,doorbell ya danna a hankali then ya tsaya jiran a bud'e masa,sai daya d'auki

Please Login or Register in order to submit comment