Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Idanunta ta d'ago dake cike taf da hawaye tana kallon Badra,a hankali kuma ta maida su ta lumshe hawayen dake kwance ciki suka samu damar gangarowa,,a kid'ime Jannat da Zeeharis suma suka dawo gefenta
"What's going wrong princess..?? Me zai saki kuka ke kuwa a dai² lokacin da kike rayuwar farin ciki.??"
Cikin muryar kuka tace
"Sam ba yadda kuke zato bane.."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Dan Allah kiyi hak'uri ki bar kuka,bai kamace ki bafa,,kuma kema kin sani.."

"Ba haka bane.. In dan damuwa ne,na jima a cikinta,kawai dai baku tab'a fahimta bane,amma tun zuwa na k'asar nan da abuna na zo,,nasan kuma da shi zan koma ga mahaliccinmu,matukar ban ganshi ba..."

Shiru suka yi gaba d'aya kowa cikinsu da abunda yake sak'awa a zuci
"Dan Allah to princess ki bar kuka,,in sha Allah,ubangiji zai kawo mafita.."

Sai data ja numfashi sannan ta ce
"Allah yasa.. Amma ni kam ina ji a jikina,wannan ranar bazai zo...!"
Saurin rufe mata Badra tayi tana girgiza kai
"Zai zo da yardar Allah,,kuma zaki ce na fad'a miki,in sha Allah duk abunda ke damunki ubangiji zai miki maganinsa,,kin sani fa,kuma ke musulma ce,saboda haka ki daina yanke tsammani,sannan ki bar munanawa Allah zato,wata rana komai zai zama tarihi.."

"Dear.. Tsayin shekaru nawa zan d'auka kenan ina jiransa..?? Kullum fa cikin tsumayinsa nake,,yaushe zai dawo,a ina zan ganshi..?? Wad'annan sune damuwata a kullum.. Amma ban sani ba,bani da amsa kuma bani da wanda zai fad'a min inda zan ganshi.."
Idanu suka ware akanta suna kallon yadda take sharce hawaye,cikin tsananin mamakinta da damuwa dukansu suka sake had'a baki
"Wa kike jira ne princess..??"
Sai lokacin ta fahimci abunda damuwa tasa ta aikatawa,sam bata shirya sanar da kowa damuwarta ba a dai² wannan lokacin,da sauri ta shiga goge fuskarta ta mik'e a gurin,har ta fara tafiya ta waiwayo fuskarta da wani irin tsoro ta ce
"Mene ne wai kuka wani sakani gaba haka..??"
Kallonta suka ci gaba da yi har ta fara zargin kanta
"Wai ku dan Allah mene haka ne,kun samin ido ina magana duk kunyi shiru,,ku bani amsa mana..??"
Ajiyar zuciya suka yi duka,kowa da mamakinta fal zuciyarsa mace kamar ba ita ba,yanzun tayi abu kuma ta sake birkicewa
"Uhhuumm..! Labari fa kike bamu,shi ne zaki wani nuna kamar baki sani ba.. Dillah dawo ki k'arasa mana mu..!"

"Labari..!? Na waye..? Akan mene nake baku labarin..??"

"Ur Prince mana.. King of ur heart.."
Zaro ido tayi hannunta dafe da k'irjinta dake duka da sauri²,tana ci gaba da kallonsu taci gaba
"Da gaske na fara baku labarinsa..??"
Ta tambaya tana raba ido,,Zeeharis ce taci gaba da magana,dama kuma tunda ta tashi da itan suke maganar
"Ehh! Mana,to wai ina ya tafi ya barki ne,mu kin samu a duhu.. Nd kukan ki ya tada mana hankali sosai.."
Fuskarta da damuwa mai girma ta dawo kusa dasu ta zauna
"Da gaske na baku wannan labarin..??"
Tayi tambayar cikin rashin yarda
"To banda abunki idan ba kin fad'a mana ba,ta yaya za'ayi mu sani mu..??"

"Haka ne,,amma ni ai ban san yaushe ne nayi maganar ba.."

"Uhhuumm..! Ai shi kenan tunda baki yarda ba,amma dama ta yaya zaki sani tunda kina b'oye mana,mu kam bamu sam matsayin da kika d'auke muba,,amma na tabbatar duk cikinmu nan babu wanda yake tare dake da wani zuciyar na daban.. Ko akwai..?? Idan akwai ku fad'a mata gata nan..!"
Duka suka tabbatarwa Zeeharis babu,kallonta tayi fuska fal damuwa
"Kin gani ko princess.. Wollahi gaba d'ayanmu nan,da zuciya d'aya muke tare dake,na tabbata idan ace a cikinmu ne,wani yake tare da damuwa zai sanar kuma har muyi sharing nasa wa juna,,amma me yasa zaki mana haka..?? Ya kamata ki sanar damu matsayinmu a gurinki.. Ko ba haka ba guys..??"
Tamkar had'in baki duka suka rud'e da cewa
"Gaskiya ki sanar damu..!"
Kunnuwanta tasa hannu ta toshe,dan yadda suke maganar ihunsu sake hawa mata kai yake,su kuma da basu san me yake faruwa ba maimakon su dakata sai suka ci gaba
"Ehh! Ki sanar damu,,kawai ki fada mana..! Mu dai ki fad'a.!!"
Yadda taga basu da alamar dainawa yasa cikin tsawa tace
"Yaa isaaa..! Enough..!!"
D'if sukayi duka lokaci guda suna masu binta da kallon mamaki,cikin sheshshek'ar kuka mai tafe da damuwa ta fara magana
"Zatonku na d'auke ku wani matsayi ne na daban.. Ko ba haka kuke tunani ba..??"

"K'warai kuwa,haka muka gani,kuma haka kika nuna mana.."
Kanta ta shiga girgizawa
"Baza ku tab'a fahimtata ba,haka nan baza ku tab'a fahimtar dalilin da yasa na kasa sanar daku ba,,kuna tunanin saboda ban yarda daku bane yasa nak'i sanar daku damuwa ta..?? Shi kenan na amince nayi laifi,na kuma karb'i duk wani abu da za kuce matuk'ar akai nane,,shi kenan zan sanar daku,komai ya wuce..??"
Ci gaba suka yi da kallonta sai dai wannan karon kallon nasu yana k'unshe ne da ma'anoni da dama,a hankali ta maida idanunta ta rufe kana ta fara zayyano musu labarin soyayyarta tun daga farkon had'uwarsu tamkar yanzun ne komai yake wakana,har ta dasa aya babu wanda ya iya yin ko da tari,tana yin shiru ta bud'e idanunta sannan ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya,,d'akin gaba d'aya ya d'auki shiru baka jin komai face sheshshek'ar kukanta cikin tsananin damuwa.
Yayin da gaba d'ayansu dake saurarenta jikinsu yayi wani irin sanyi,tausayin ta gami da jinjinawa k'ok'arin ta yasa suke mata wani irin kallo na daban,,kafad'arta Jannat ta dafa cikin tausasa murya tace
"Princess.. Amma shin kina ganin laifinsa ne cikin abunda ya faru..??"
Sai data goge fuskarta sannan ta gyad'a mata kai
"Idan banga laifinsa ba,shin laifin waye kike zaton zan gani..??"
Caraf Badra tayi ta amshe zancen
"A gaskiya princess,, ni kam duka cikin labarin nan,laifin mutum d'aya na gani.."
Waiwayawa duka suka yi kanta suna kallo
"Waye kike nufi..??"
A hankali tana k'ik'k'ifta idanu tace
"Dad d'insa.. Gaskiya shi ya janyo rabuwarku,idan ba don haka ba,ai da duk ba'a zo wannan matsayar ba.."
(Uhhuumm.! Lallai Badra zaki tafka KUSKURE idan kika ci gaba da magana.. Fan's ya kamata ku bata shawara tayi shiru hakan nan,dan kada allura ta tono garma)
Saurin kallonta Zeeharis tayi tana cewa
"A'a Badra.. Kada kiyi saurin yanke hukunci..!"

"Haba friend,idan ba shi bane ba to waye ne za'a kira mai laifin..??"

"I knew,,yayi ba dai² ba daya k'i zuwa nema masa aurenta,bayan nan kuma ya tura shi MUHAMMAD d'in karatu.. Amma kada ki manta da cewar,ita rayuwa da muke yi gaba d'ayan ta ubangiji ya tarawa kowane bawa yadda yake son nasa ya kasance,nd kuma daya tashi duk da hakan ya tsara rayuwarmu ta tafi ne a bisan doron *K'ADDARA* komai tsarin Allah ne,so kinga kenan idan yaso ko a yanzun sai ya had'a su,tunda tun da fari shi yaso rabuwarsu ko ba haka ba..??"

Shiru ta d'anyi kafin ta gyad'a kai
"Yeah..! Haka ne maganar ki.."

"Kun gani ba,,sannan idan kuka duba ko cikin labarin data bamu yanzun tace sun samu matsala a garinsufa,after kuma suka samu canjin gurin zama,kunga kenan idan kun duba nan ba tsarinsa bane kuma bana Daddy'nsa ba,akwai dalilin da yasa Ubangiji yayi haka,,ni ina ganin lokacin had'uwarsu ne bai yi ba,amma idan har lokacin yayi ba kamar yadda ubangiji ya raba su babu shawaran d'aya daga cikinsu,zai had'a su ba tare da d'aya a cikinsu ya sani ba.. Kuyi nazari mana..!"

"Yeah! Kin fad'i gaskiya.."
Duka abunda suke fad'a kenan,ita kanta da take tunanin kamar ya ajiyeta jiransa sai duk jikinta yayi sanyi,cikin k'ank'anin lokaci tauhidi ya sake shiga zuciyarta
"Tabbas.! Kunyi gaskiya,, ubangiji shiya raba tsakaninmu,,amma dole akwai Sila.. Shin waye ne silar a nan..??"
Shiru tayi da yake a zuci tayi maganar,nan wani gefe daga zuciyarta ya bata amsa da
"His Dad..!"
Idanunta ta lumshe a hankali tana sake zurfafa tunani cikin zuciyarta,ta d'auki lokaci mai tsayi sannan ta fara addu'ah
"Yah rabb..! Kai ne magani da abunda ke b'oye kuma kai ne masanin abunda ke sarari,ya ubangijin samman bakwai,da kuma k'assan bakwai,,ya ubangijin al'arshi mad'aukakiya,tabbas kai kad'ai ka barwa kanka sanin dalilin da yasa ka raba wad'annan zuk'ata,,yah Allah..! idan har kayi nufin had'a wad'annan gajiyayyun bayi naka,ina rok'on ka yah Allah,daka had'a fuskokinmu da alkhainka..!"
K'aran thunderstorm daya ratsa kunnuwanta yasa ta saurin bud'e idanunta tana kallon windows d'insu
"Heeyy! Guys muyi maza mu rufe windows kada ruwa ya jik'e mana room.."
A gurguje duka suka watse a gurin,itama Sabinar sai ta mik'e tana nufar hanyan toilet zuciyarta cike da nufin yin alwala.

*NIGERIA..*
Cikin aminci da nutsuwar rai,bayan dogon hanyar da suka kwaso jirginsu ya sauka a katafaren filin saukar jirage na Malam Aminu Kano,shi kad'ansa kamar yadda ya fito haka ya sauka daga shi sai halinsa sai kuma wayoyinsa,,hire cab ya d'auka daga airport d'in har k'ofar gidansu,,bayan ya sallami mai cab,ya tasarma k'ofar shiga gidan kai tsaye,,babu wanda ya san da zuwansa a lokacin,buh ya k'udurce dama sai dai kawai su ganshi tunda duk lokacin daya sanar yace zaizo sai an samu matsala,shi yasa ko da yayi niyyar zuwan yak'i sanarwa,,Mamma ita kad'ai zaune a parlour tana watching TV ya shigo da sallama,,cikin tsananin mamakin ganinsa lokacin da yake shigowar take fad'in
"Hammad..!? Kai ne..??"



*Wahh! Aradu na rubutu yau kam.. Nasan ya wuce nace kuyu manage,buh nasan baza'a rasa wanda zasu ce manage suka yi ba,,toh! Ku k'ara hak'uri,kunsan idan da lafiya babu abunda ba zanyi ba dan na faranta muku.*





#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*34.*
_#Distressful_

Kai ya gyad'a mata fuskarsa k'unshe da kyakykyawan murmushi har ya shigo cikin parlor'n,lokacin daya k'araso daf da ita still Mamma bata daina binsa da kallon tsantsar mamaki ba,gaba d'aya gani take kamar ba da gaske take ganinsa a kusa da itan ba,,murmushi ya sake yi ganin irin kallon da take masa,har yayi niyyar zama sai kuma ya fasa ya k'arasa inda take,warm hug ya bata da yasa ta sauke doguwar ajiyar zuciya,da kyar tana k'ik'k'ifta idanu ta dago hannunta ta shafa kansa,har k'asan ranta tana mai jin dad'in ganinsa
"Baby.. Yaushe ka taho ne..? Amma baka sanar min kana hanya ba..!?"
Murmushi yayi mata yana k'ifta idanunsa
"Mamma..! Nayi nufin baku surprise ne,shi yasa ban sanar ba..Amma ayi min afuwa.."

"Uhhuumm! Aifa kam gashi nan ni kam ka bani,, ya gurin aikin naku..?"

"Alhamdulillah..! Mah ina mutanen gidan suka yi ne..?"
Harararsa tayi kafin ta amsa masa
"Sau nawa ne zan fad'a maka ni kad'ai na rage a gidan..??"
Sai daya dafe bakinsa yana mata murmushi sannan yace
"Ohh! Am sorry Mah,, na manta ne munyi wannan maganar tuni.."
Still yana shafa sumar kansa
"Kai dai ka sani.."
Murmushin k'arfin hali ya sake yi mata sannan ya nemi guri ya zauna yana fad'in
"Wahh! Mah Daddy fa.. Yana gari..?"
Jimm Mamma'n tayi cikin wani irin yanayi na b'oyayyen tashin hankali ta kad'a masa kai,tunda yayi tambayar yasa mata ido yana kula da duk wani motsinta,yadda tayi reaction lokacin da take masa response yasa take ya fahimci akwai damuwa,kusa da ita ya dawo ya kwantar da kansa a jikin shoulder d'inta
"Mah.. Did something went wrong..??"
Still bata yi magana ba saima kanta data kawar gefe,saurin mik'ewa yayi ya zauna
"Please.! Ki fad'a min abunda yake faruwa,,u know bazan iya juran ganinki a damuwa ba.. Please Mah.!"

"Hammad.. Akwai damuwa ne,,idan na fad'a maka babu abunda zai k'are mu da shi daga ni har kai,haka ma idan na b'oye bazai yi mana maganin komai ba,bcos dole ne nan da d'an lokaci nasan zaka san komai.."

"Haka ne Mah. Buh ki sanar dani damuwan.."
Kallonsa tayi idanunta taf hawaye,a hankali tasa hannunta a saman kansa tana shafawa kamar mai rarrashin sa
"Baby ina cikin damuwar hukuncin Daddy'nku ne a wannan karon,saboda ya sanar dani a kowane irin lokaci zai yi maka aure..!"
Bai tsaya jiran mene ne zata sake fad'a ba ya rungume ta cikin tsananin murna
"Thank u Mah,buh wannan ai ba abun damuwa bane.. Ya kamata ne ace kinyi farin ciki,coz nima ina cikin farin ciki."
Kallonsa kawai take yadda taga yana zumud'i akan maganar da take yi d'in,without ya jira yaji k'arshen inda maganar zata tsayaya hau murna
"Thank u Mah.. Da kika bani wannan kyakykyawan albishir d'in.. I love u Mah..I love u ³..! Mu'aaahh.!"
Ya d'ora mata peck a chicks,nd cikin sauri ya mik'e a gurin yayi sama itan kuma ya barta tana aikin binsa da idanu,a gurguje ya watsawa jikinsa ruwa sannan ya fito cikin shirinsa,ko tsayawa ya fad'a mata inda zashi a time d'in bai yiba ya fita da sauri,a baya ta biyo shi tana kira don ta k'arasa sanar masa inda k'arshen zancen yake amma ina har yayi mata nisa,kiransa ta shiga yi sai dai kash nan d'inma bata yi nasara ba don kuqa hannu kad'ai ya d'aga mata da alamar yana dawowa yanzun,,tun kafin ta k'arasa inda yake tuni har ya fizgo mota yayi waje,dafe kai tayi cikin takaicin rashin samunsa tana fad'in
"Yah rabb..!"
Shi kam cikin ziciyarsa gaba d'aya farin ciki yake da jin maganar aurensa da Daddy ya yanke yanzun,ba tare daya damu da tambayar Mamma wace ce ko y'ar waye ba,bare a inda take yasa kai ya fice nd without tunanin abunda zai biyo baya,,haka nan kuma bayan fitowarsa daga gidan sai yake jin zuciyarsa ta kasu kashi²,yayin da yake jin wani sashin ya cika da zumud'in ganin lokacin ya gabato,d'ayan gefen kuma sai yake jinsa cike da damuwa,sai dai farin cikin da yake cikinta yafi k'arfi ta yadda har yake neman danne damuwar sa,d'an dafe gefen chest d'insa yayi,dai² saitin inda zuciyarsa take k'aik'ayi,a hankali ya d'an cije lips d'insa ya fara magana
"Me yasa ke kuwa zaki shiga damuwa al'halin mammalakin ki yana cikin tsananin farin ciki..??"
Kamar wanda yake magana da mutum ko yake sauraron amsa,sai yayi jimm shi kad'ai yana sakin numfashi,ya d'auki y'an mintuna shiru sannan a hankali ya lumshe idanunsa da fad'in
"Haba ke kuwa,,ki kasance cikin farin ciki mana,,yanzun fa ba lokacin shiga k'unci da damuwa bane,,ya kamata kiyi farin ciki kamar yadda mammallakin ki yake yi.. Let's cheer up.! Lokacin farin ciki ne,so muyi farin ciki gaba d'aya.."
A hankali kuma ya saki sihirtaccen murmushi,cikin tsananin gudu ya ci gaba da cin taya,dai² lokacin yana shiga kwanar gidan maggi,ya samu gefe yayi parking a inda ya saba tsayawa,sai dai wannan karonma bai fito ba ya zauna cikin motar yana tunanin hanyar daya kamata yabi,shin zai fita ne yayi tambaya ko kuwa haka zai ta zama cikin motan da saka ran zai ganta..??

A kan idanun Mamma ya fita a gidan,duk da taso tsayar da shi bcos tana son ya sanar mata inda zashi,buh abu ya gagara har ya fice ba tare daya saurareta ba,cikin tsananin damuwa bayan taga fitarsa ta koma parlor ta zauna tana mai buga tagumi da duka hannayenta biyu,lokaci guda zuciyarta ta kasu da mugayen tunanuka,cikin tsananin tashin hankali kuma suka fara tafka muhawara
"Shin yanzun tunda ya iso k'asar zan sanar masa hukuncin Daddy ne ko kuwa zan b'oye masa zuwa nan gaba sannan na fad'a masa..??"
Ta yiwa kanta tambayar,,saurin girgiza kai tayi alamun "A'a" sannan ta sake zurfafawa cikin tunani yayin da wani sashin na zuciyarta yake cewa
"Kada kiyi haka,,gara kawai ki fad'a Masan,bcos duk abunda zai faru a yanzun na d'an lokaci ne,daga kin sanar masa komai zai wuce,,kema kin huta da ganin tashin hankali a gaba..!"

"To amma idan yak'i amincewa fa sai nayi yaya kenan..??"
Bijirarriyar zuciyarta ta saje watso mata amsa
"Shi kenan.. Sai ki sanarwa Daddy'nsa,,dan Hammad yak'i amincewama da zab'insa ai ba wani abun damuwa ba ne..!"

"A'a bazai yiwu ba,,dole ne nayi k'ok'arin rarrashinsa,,bai saba yiwa mahaifinsa musu ba kan duk hukuncin daya yanke masa,,so yanzunma dole ne yayi hak'uri yabi maganarsa.."

"Babu dole..! Kawai dai kiyi k'ok'arin lallab'a shi idan ya amince shi kenan,,idan kuma ya nuna baya so..!"

"A'a ba haka ba,,dole nayi k'ok'arin fahimtar da shi,wannan umarnin mahaifinsa ne,ya kamata ne ace ko yana so ko baya so ya karb'e shi da dukkan zuciyarsa."

"To wai da kike batun dole³! Ke haka aka miki.?? Ko kuwa shi Daddy'n anyi masa dole wajen aurenki..?? Shin ku bakwa tunanin jefa rayuwar yaron ku ahalaka ne..??"
Shiru tayi tana jan ajiyar zuciya
"Yeah! It's true,,dole ne na lallab'a shin kafin ya koma.. Buh ina jin tsoron kada yak'i amincewa fa.."

"Uhhuumm..! Kina wasa ne kema.. Ta yaya ne kike zaton zai amince d'in.? Al'halin ke da kanki kin sani tun a can baya ya shaida miki akwai yarinyar da yake so..!"
D'if tayi tana tuna irinbmaganganun da suka yi a bayan wanda a dalilin hakan har sai data kaishi da kwanciya jinya,da kyar² ta fara twitching breathe had'e da goge zufar dake karyo mata tamkar wacce tayi tseren gudu
"Shin yaya kenan za ayi idan yaji wannan batun..?? Hakan yana nufin akwai damuwa kena..? Yah rabb! Ka kawomin tallafi wannan lamarin yana neman juyarmin da tunani.."
Kamar za tayi kuka haka reaction d'in dake shimfid'e saman fuskarta ya nuna,amma saboda dauriya irin nata da k'arfin halinta ko silin hawaye bata bashi damar sauko mata ba.

*PENNSYLVANIA CITY..*
Tana fitowa a toilet saman bed d'inta ta koma ta zauna ba tare data yiwa kowa cikinsu magana ba,daga can k'asan zuciyarta kuma tana ci gaba da kai kukanta gurin ubangiji,har gabanin lokacin sallar magrib tana zaune bata motsa ba,duk da irin ihun da suke yi a room d'in,a haka har lokaci ya shiga ta mik'e tayi sallah,bayan ta idar ta ci gaba da zama a gurin tana addu'o'i,ba ita ta shi a gurin ba sai data tabbatar tayi sallar isha'a sannan ta sake d'orawa da addu'o'i,tana idarwa sai ta d'auke abun sallah ta koma saman gadonta,yadda garin yayi sanyi sakamakon ruwan saman da suka samu da yunwan dake sasikar cikinta yasa ko da su Jannat suka gama shiryawa zasu fita tace su jirata,da mamaki duka suka tsaya kallonta,Jannat kam ko da taga baza ta iya yin shiru ba tace
"Amma! Princess kefa kika ce baza ki fita ba..!? Why kuma yanzun zamu jira ki..??"
Baka kalleta ba taci gaba da shirinta cikin sauri²
"Ra'ayi na canja.."
Tana fad'ar haka ta mik'e,bayan ta gyara fuskarta ta d'auko pencil trouser na mata da long sleeve na mata ta saka,after kuma taja blazer d'inta dake ajiye a gefenta,bayan ta sakaye k'afarta cikin wani had'ad'd'en women's chunky heels mai zip ta gaban,tana mik'ewa ta sab'a blazer d'inta ta rufata a saman kananan kayan dake jikinta,tana takowa kusa da su ci gaba da rolling vail a saman kanta,cikin sauri² duk tayi komai ta gama
"Wah..! Princess..!! Gaskiya da kinyi zamanki,kinga kuwa yadda kika yi kyau..!?"
Murmushi kad'ai tayi ta kuma tab'e baki ba tare data ce dasu komai ba ta wuce ta barsu tsaye a gurin
"Ni kam gaskiya ina kishi princess,, wannan ai sai kisa masu jan kunne suyi ta biyo mu.. Kunga fa dan Allah,ni kam gaskiya duka yau bazan jera dake ba,salon ace masu Aikinki ne mu.."
Cewar Zeeharis da take kallon Badra,dariya suka yi mata suna fad'in
"Gara miki ma ki wuce muje kawai,,idan ta wannan matar zaki biya ina jin daga yau baza ki sake fita ba.."

"Haba sisters,, kuna kallo fa,matar nan da fari kamar bata san komai ba amma yanzun fa..? Ku duba uban gayun data d'auka.. Ni dai ina kishi.."

"O'o! Kada ki damu mana sisi,maybe da tsarinta ne haka,yanzun kuma ta canja,so muje kawai kada mu b'ata lokaci.."
Hararar wasa tayi musu sannan suka fice daga room d'in,cike da tsokana Badra da suke binta ta kallo ta tana dariya
"Nifa Sisi tuni nayima Yayanah kamu.."
Bata juyo ba bare ta kalleta ko tasan da ita take magana suke tafiyar,duk inda suka wuce sai dai suga ana binsu da kallo,tun basu wani damu ba,har suka fara tsarguwa.
Wani had'ad'd'en eatery suka shiga dake kusa² da skul d'insu ne dana kuma basu cika yin nisa ba idan sun fito gudun samun matsala,bayan sunyi order abunda suke ganin zasu iya ci,Badra ta sake yin magana
"Princess nayi magana d'azun amma shi ne kika share kamar ba dake nake yi ba..!"
Bata kalleta ba tace
"Mene ne kika ce..??"
Kallon sauran tayi tana murmushi sannan tace
"Cewa nayi nayi ma big Bross nah kamu,,sai kuma kika share ni.."

"Na meye ne kamun..?? Biki za kuyi ne..??"

Cike da rashin fahimta duka suka bita da wani irin kallo
"Kamar yaya..??"
Idanunta ta d'ago ta kallesu
"Ehh! Mana tambaya ne nayi ai,kamun na mene ne..? I thought sai ana bikin aure ake cewa ana

Please Login or Register in order to submit comment