Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da rashin fahimta
"Broah! Wai lafiyar ka kuwa..!? Ya za'ayi ka dunga magana kai kad'ai ne..?? Wace ce kake magana akanta..?? Ya kamata ka sanar dani abunda yake faruwa.."

"Ban san ta ina ne zan yi maka bayani ka fahimce ni ba,,buh ina cikin rud'ani d'an uwa,,kwakwalwata ta kasa fahimtar abunda ke shirin faruwa..! Ka fad'a min inda zan ganta.."
Ajiyar zuciya Sultan ya sake yi kafin ya d'an bubbuga kafad'arsa
"No Broah..! Ya kamata dai ka nutsu kamin bayanin da zan fahimci damuwarka,,kasan bani da sani akan abunda kake magana,duk na shiga duhu wollahi..Ka fitar dani daga wannan k'angin.."

"Ban sani ba..! Ban san ina ta tafi ba..?? Ka fad'a mata ta dawo gare ni,nayiwa Baffa *ALK'AWARI* zan kula da ita..! Me yasa to bata jira ni ba.. Me yasa tayi tafiyarta ta barni bayan na fad'a mata da ita kad'ai zan iya rayuwa..!!"
Runtse idanu Sultan yayi,ko da ace Hammad bai sanar da shi dukkan abunda ke faruwa ba,lallai ne zuwa yanzun a matsayinsa na Psychologist ya iya fahimtar *AKAN SO* ne Hammad ya shiga damuwa
"To amma meya janyo faruwar *AL'AMARIN..??"*
Ya k'arashe zancen da tambayar kansa
"Ban san dalilin da yasa ta iya tafiya ta barni ba..D'an uwa ka fad'a mata ta dawo,nayi mata *ALK'AWARI* da *JININ* jikina zan kula da ita fiye da yadda zan bawa kaina kulawa,ka fad'a mata ta zo gare ni..!"
Yadda yake surutai yasa Sultan gyara tsaiwarsa yana binsa da kallon tausayi cikin k'ank'anin lokaci duk ya fita hayyacinsa kamar wanda yayi jinyar shekara,to wai shi shin ta ina ne zai fara bashi hak'urihar su samu damar binciko abunda yake faruwa..?? Allah ya san zuciyarsa bashi da masaniya kan abunda abokin nasa yake magana,kafad'ar Hammad ya sake rik'owa duka biyu yana fad'in
"Relax broah..! Let us leave.."

"Babu inda zani,,har sai na gano inda ta tafi..!"

"A'a broah baza ayi haka ba,,ya kamata fa ka nutsu sosai,,idan ka duba yanayin gurin nan,kaima kanka zaka gane hakan,, gurin nan baiyi kama da gurin da mutane suke rayuwa ba,koma mene ne yake faruwa ya kamata muyi bincike kafin mu tabbatar da abunda ya faru,in sha Allah zamu gano gaskiyar abunda ya faru.."
Tunda ya fara magana yake kallonsa da jajayen idanunsa masu cike da tsoro,,girgiza kai yayi yana sakin ajiyar zuciya
"Babu fa inda zani..Kawai kayi tafiyarka ka kyale ni,,ko dama ace na bika damuwar rashin ta shi zai zame min *AJALIN SO..!"*

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.. Allahumma ajirna fiy musibatin wa'aklufna khairan minha..!"
Addu'ar da Sultan ya fara yi kenan a fili,yi yake yana sake maimaitawa,har ya samu Allah ya taimake shi Hammad d'in ya cafka suka ci gaba da maimaitawa tare,,dama dalilinsa nayi kenan a fili,bcos yana ganin idan cewa yayi masa kace kaza,yasan yadda yayi spark lokaci guda d'in nan zai yi wahala bai zazzage shi ba,shi yasa ya gwammace yayi a filin,idan ya dace sai ya karb'a,hamdala yayi a ransa na jin dad'i kafin ya dafa shi da muryan rarrashi
"Let us move Broah,,in sha Allah zamu binciko komai,kada ka damu,kai dai ka bar komai a hannu na,da yardar Allah babu abunda zai same ta,,nayi maka *ALK'AWARI..!"*
Tsare shi yayi da kallo kamar mai neman wani abu akan fuskarsa,cikin d'agawar sauti ya furta
"K'arya ne..! Ba zaka ganta ba,,,ta yaya ne zaka ganta..? A ina..?? Nima fa bata sanar dani dalilin da yasa ta tafi ba..? Kai d'in ta yaya zaka gano inda take..?? Eyyy!?? Ka fad'a min..!"
Lumshe idanu Sultan yayi sannan ya sake rik'e shi
"I promised.. Zan nemo,,saboda kai..Buh kayi hak'uri yanzun mu koma gida.."
Da kyar badon Hammad yana so ba,sai dan ganin yadda Sultan d'in yake ta bashi baki ga fuskarsa cike da damuwa sannan ya sakko akan su koma d'in,,lokacin da suka fito daga surk'uk'in hanya dai² suna fitowa bakin titi inda suka bar mota,suna niyyan shiga su wuce cikin gari,sai ga wani dattijo bisa tsohon keke yazo wucewa,da ganinsa zaka kasan ya gaji sosai dan kallo d'aya zaisa mutum fahimtar ba iya talauci ne kad'ai yasa shi tsufa ba,har da rashin kyakykyawan muhalli da cima mai kyau,wannan ne dalilin da yasa tsufansa yayi saurin bayyana,,ganin yana niyyar wuce su a gurin cikin sauri Sultan ya matsa daga jikin motar yayi masa sallama,,har ya d'anyi gaba da inda suke duk sa keken ba wani sauri yake da shi ba,sai kuma ya dawo yana amsawa,gaisawa suka fara yi da Sultan dan shi kam Oga Hammad tuni ya shige cikin mota bcos bazai iya ci gaba da jurewa tsaiwa ba,,kallon Sultan dattijon yayi bayan ya sauko daga saman antique bike d'insa,dan daga dukkan alamu akwai magana a tare da shi,sai da Sultan ya juya ya kallo hanyar da suka baro sannan ya furta
"Baba dan Allah idan babu damuwa tambaya nake da,,ban sani ba ko Allah yasa ka sani.."

"In sha Allahu samari,, idan har na sani me zai hana na sanar da kai..?"
Jinjina kai yayi cikin farin ciki sannan a hankali yaci gaba da magana
"Baba.! Dama Baba tambaya nake sonyi game da k'auyen dake a ta wancan hanyar..!"
Shiru dattijon yayi yana bin inda Sultan d'in yake nunawa da hannunsa
"Eehh! Toh! Samari,gaskiya ban san wane k'auye ne kake magana akansa ba,da yake yanzun gaskiya abubuwa sun sauyawa sosai,ta iya yuwuwa abunda kake son tambayar ko na sanshi ko akasin haka,,amma shin kuna neman sani ne akan wani abu..??"

"Ehh! Baba...Dama dai akwai wad'anda muka zo nema ne,saboda kasancewar mu bak'i,to kuma dai mun d'auki lokaci bamu zo ba,,shi ne yanzun da muka zo mun tarar babu kowa sai filin gurin kawai..Shin ko kana da sani akan abunda ya faru da jama'ar garin,ko kuma dai canja gari suka yi,shi ne abunda muka gaza fuskanta.."

"Allah sarki..! Kai kuwa yaro,,shin baka samu labarin irin abunda ya faru da mutanen wannan gari ba da jimawa..??"
Girgiza kai sultan yayi alamun bai sani ba,dattijo cikin jimamin yaci gaba da magana
"Ai kuwa samari idan har akan mutanen dake zaune *RUGAR MALAM SHEHU..!?* Kake magana da jimawa suka bar wannan gari sakamakon iftila'i daya fad'a musu.."
Shiru Sultan yayi yana sauraron labarin da yake bashi kan bala'in daya faru watannin da suka gabata,,jikinsa yayi wani irin sanyi da jin irin k'addarar data same su,har dattijon ya gama bashi labarin bai daina jimanta *AL'AMARIN* a zuciyarsa ba,godiya yayi masa gami da alkhairi,sannan yayi masa sallama ya juya ya bar gurin da sanyayyun guiwoyi.
A mota ya tarar da Hammad kwance a kan seat na mai zaman banza,,yana shigowa ya tada motar suka kamo hanyar dawowa gida,tun da suka d'auko hanya babu wanda ya iya cewa komai,tun bama Hammad ba da damuwa tasa shi yin shirun dole,shima kuma Sultan dalilin da yasa yak'i yi masa magana kenan saboda yasan idan yace zaiyi masa magana ma a yanzun ba lallai ne ya iya tsayawa ya fahimci abunda yake son sana shi ba,,,har suka shigo cikin gari kalma d'aya bata had'a su ba,sai karatun da Sultan d'in ya musanya musu a maimakon cool music da suka sa a tafiya su da yake tashi.
Tun kafin su k'araso gida tsananin damuwar da yake ciki tuni ta haifar masa da zazzafan zazzab'i baya ga ciwon kai da yayi masa mugun kamu,lokacin da suka shigo gidan ma a daddafe ya fita daga mota,da tainmakon Sultan suka shigo cikin parlor,da Mamma suka fara arba,,tunda suka shigo tana kallonsu jikinta ya bata akwai matsala,hankalinta ta tattara akan Hammad dake wani irin tafiya rik'e a jikin Sultan tana tambaya
"Son..! Lafiya..!? Sultan me yake faruwa ne..!?"

"Mah relax..! Am fine.."
Cikin dauriya yana rik'e forehead yayi maganar
"Sultan,,me yake faruwa da shi wai..!?"
Ta sake tambaya,sai daya tabbatar ya zaunar da shi sannan ya d'ago yana kallon Mamma da fuskar damuwa
"Mamma..! Wollahi i dunno how..!"

"A'a sultan,,kaima kasan babu yadda za'ayi na yarda da abunda zaka fad'a min,,tunda na san tare kuka fita.."

"Wollahi Mamma ban san komai akan abunda yake faruwa da shi ba,buh a yadda dai na fahimta koma mene ya janyo shigarsa wannan yanayin baya rasa nasaba da *SO..!"*

"So kace..! Soyayya kake nufi ko kuwa..!?"

"Ehh! Mamma..Tabbas soyayya ce silar faruwar komai.."

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un.."
Abunda ya fara fitowa daga bakin Mamma kenan tana kallon Hammad daya kwanta rik'e da kansa
"To yanzun kun je hospital ne.. Ko kuwa gida kawai kuka nufo kai tsaye..!?"

"A'a Mamma dawowarmu kenan yanzun.."
Inda tabar wayarta ta nufa,ko data d'auka line Daddy ta soma kira cikin damuwa,,sai da wayar tayi ring kamar zata katse kafin ya d'auka,bata iya jiran su gaisa ba ko amsa sallamar da yake mata ba ta hau fad'in
"Daddy...Please ka turo mana doctor gida yanzun.!"
Jin abunda ta fad'a ne ya sashi saurin mik'ewa a kid'ime daga saman kujeran da yake kai har yana neman yin tuntub'e
"Asiya..! Me kike fad'a..!? Me kuma ya faru.!?"

"Please daddy,, ni dai kawai nace ne kasa doctor yazo yanzun,koma mene ne sai bayan yazo nefa duka zamu sani..Amma dai akwai matsala.."

"Ok..Ok.! Ina zuwa.."
Yayi saurin katse kiran,hannunsa har karkarwa yake gurin neman number doctor'nsu, ba tare da shima ya tsaya b'ata lokaci gurin amsa gaisuwar saba cikin tak'aita magana yayi masa bayanin iya abunda ya fahimta,,cikin gaggawa kamar yadda Daddy ya sanar da shi ya shirya kayayyakin aikinsa da yasan zai buk'ata sannan ya fice daga hospital d'in.A ta gefen Daddy kuwa tun kafin k'arasowar doctor ya sake kiran Mamma dan jin abunda ke faruwa suke neman likita da gaggawa haka,da kyar Mamma ta d'an samu nutsuwar da har ta iya fad'awa Daddy iya abunda ta sani cikin damuwa, shima dai jimamin ya shiga yi kamar yadda take,a lokacin suna tsaka da magana likitan ya k'araso,da hanzari ta yiwa Daddy sallama saboda tana son bada nutsuwarta akan bayanin da zaiyi,,da taimakon ma'aikatan gidan suka samu suka maida Hammad bedroom d'insa bayan nan likita ya shiga aikisa,,duk wani binciken da gwaje² kusan babu wanda baiyi masa ba,,bayan dogon lokaci daya d'auka yana bincike yayi masa alluran da yasan zasu taimakawa jikinsa kafin ya buk'aci yin magana da Mamma,shi kansa likitan lokacin da yake nufin sanar da ita ciwon nasa jikinsa a sanyaye yake da *AL'AMARIN* na Hammad,,amma saboda k'arfin hali a hakan bayan ya sharce gumi ya kalli kafin ya sake yin shiru yana nazari,Mamma kam ko da taa yayi shiru ita da kanta ta bud'e baki tana tambayar sa
"Doctor..! Har yanzun baka ce min komai ba,,matsalar tasa ba babba bace ne..!?"
Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya d'ago kansa daga kallon takardun sakamakon gwajin da yayi masa,yana niyyar yin magana kuma kiran Daddy ya shigo wayarsa,da hanzari ya d'auko wayar yana fad'in
"Afuwaan Hajiya,,alhaji ke kira."
Da kai ta amsa masa,sannan ya d'auka muryan Daddy cike da tashin hankali akan rashin sanin abunda ke faruwa da gudan jininsa yake tambayar likitan
"Doctor..! Wai shin mene ne actual na abunda ke damun Hammad ne..? Na jira² tun d'azun amma shiru har yanzun banji ko wane irin magana ba dangane da larurar tasa..Me yake damunsa ne..!?"
Ajiyar zuciyar dai ya kuma yi,murya a sanyaye cike da rashin hope ya fara magana
"A gaskiya ranka ya dad'e,,Hammad na cikin mawuyacin hali,,dan a maganar nan da nake yima,kamar yadda bincike ya tabbar,a ko wane irin lokaci zuciyarsa zata iya bugawa.."

"Whattt..!? How dare u.!? Ta yaya ne wannan problem d'in zai faru da shi..!?"
Ga Mamma kuwa kalmar "Innalillahi wa'inna ilahi raji'un",taci gaba da maimaitawa a zuciyarta,yayin da take kallon Hammad dake kwance saman bed a kwance kamar gawa

"Sir..wannan matsalar fa ba laifina bane,sannan kaima ba naka bane..Kawai dai abunda zan iya cewa ko nace na fahimta game da shi shine,akwai abunda yake so,ko kuma dai ta iya yiwuwa yayi loosing wani abu mai muhimmanci a rayuwarsa da yake expecting samu.."
Shiru Daddy yayi daga gefensa banda zagaye tamfatsetsen office d'insa babu abunda yake tamkar mai safa da marwa
"To yanzun doctor mene ne matsalar kenan..!?

"Ehh to matsala dai a yanzun shi ne mu samu zazzab'in dake tare da shi ya sauka,matuk'ar ba haka ba kuwa,,zan iya cewa sai dai kawai muyi hak'uri.."
Murya a d'age Daddy ya tambaya
"Kamar yaya muyi hak'uri doctor.!? Kana son fad'a min ne Hammad zai mutu ko me kalamanka suke nufi..!?"

"A'a ranka ya dad'e,, sam Ba haka nake nufi ba,,amma dai abunda yafi a yanzun shi ne zamu yi k'ok'arin ganin zazzab'in ya sauka,kafin mu yanke hukuncin abunda zai iya faruwa da shi nan gaba.."
Hankalin Daddy idan ya kai million a wannan lokacin tofa ya kai mak'ura wajen tashi,ko da yaji likitanma yana fad'ar wannan maganar guiwoyinsa tuni suka sake yin sanyi
"Shi kenan doctor,, duk abunda ya dace ayi kana tare da shi kayi masa,sannan abunda nake so shi ne ina son ka bawa Hammad kulawar data dace,matuk'ar zata warware matsalar Yarona,fatana shi ne ace ya kasance cikin k'oshin lafiya.."

"In sha Allah, ranka ya dad'e za muyi iya k'ok'arin da zamu iya wajen ganin munyi duk yadda kace.."
Godiya sukama juna sannan cikin damuwa Daddy ya kife wayar bisa table,saman armchair da aka tanada domin ganawarsa da guest ya zauna yana aza chin d'insa bisa hannayensa daya dunk'ule,yayin da damuwa mai girma ta bijiro masa a dalilin ciwon Hammad.
(Ni kuwa dai da nake gefe nace Daddy kenan,,ai ina tunanin bai kamata ka shiga damuwa akan ciwon Hammad ba,tunda tun asali kai ne mutum na farko daya bada gudunmawar assasa dukma abunda ya faru,,shin fan's kunga laifina a nan dan na fad'i gaskiya..?)

A can gida kuwa,bayan da likitan ya ajiye wayar Daddy, da kyar Mamma ta iya kallon shi saboda tashin hankalin da bayaninsa ya jefata,ta jima tana tunani kafin ta samu k'warin guiwar tambayarsa
"To yanzu likita,meya kamata muyi masa wanda zaisa shi fita daga halin daya shiga..!?"

"A gaskiya ina ganin dai tabbas a yanzun,abunda yafi kamata ace anyi masa shi ne,kamar yadda na fad'a tun farko,wato ayi k'ok'arin ganin zazzab'in dake tare da shi ya sauka,bayan shi kuma sai dole mu kasance masu yin taka tsantsan da duk abunda zai iya maida shi halin daya tsinci kansa a ciki,ta hanyae kwantar masa da hankali,saboda ta haka ne kad'ai nake ganin zamu iya yin nasarar yak'ar duk wata damuwa dake tare da shi.."
Sun jima sosai itama suna tattaunawa da likitan akan matsalar tasa kafin likita yayi prescribing magungunan da zasu taimaka masa jikin yayi kyay,daga nan yayi sallama da Mamma bayan ya sake duba jikin nasa ya ta batar lafiya saman ya tafi.

Tun daga wannan ranar ak'alla zan iya cewa sai da Hammad ya shafe sama da sati biyu kwance yana fama da jikinsa,kafin cikin hukuncin ubangiji sauk'i ya fara samuwa,sai dai d'an abunda ba'a rasa ba ta fannin tunani da damuwa da yakan shiga a wasu lokutan,duk da likita ya sanar masa ya daina sa damuwa a ransa,buh mun san dama abune mai matuk'ar wahala a gare shi ace lokaci guda ya iya cire tunanin da yake damun zuciyarsa,sai dai ko a hankali yau da gobe,dum da kasancewar kullum yana tare da Mamma,Sultan,Bassam nd BADRA da a kullum d'in suke k'ok'arin ganin sun sashi farin ciki,,sai dai kuma a duk lokacin da zasu yi abun dariya ko da su d'in ya basu dariyar ba lallai ne idan ka kalli fuskarsa ka fahimci wane irin yanayi ne yake ciki ba.....




#Follow:@jeeddahmu898
#Real Smasher.
💠💠💠💠💠
*©® 2019.*



*AL~K'AWARIN JINI..* 💥
_(Blood pledged)_



*NA.*
*_HAWWA MUH'D USMAN._*
*~(REAL SMASHER).~*
*WATTPAD@JEEDDAHMU898.*
••••••••••••••••

*26.*
_#Surprisal_

Yana zaune saman bed yayin da bayansa ke jingine a jikin pillow saboda gajiyar da yayi da kwanciya,Sultan ya shigo da sallama,d'aga kansa yayi ya bishi da kallo har ya k'araso kusa da shi ba tare daya samu damar bud'e baki yayi masa magana ba,sai dai ya amsa sallamar a k'asa²,,zama Sultan yayi daga gefensa ta wajen k'afafunsa yana kallon yadda cikin y'an kwanaki duk ya zama wani pale
"Dude..! Ashe ka farka..!"

"Ummmhh!" Yace yana motsa k'afarsa kamar zai tashi,kallonsa Sultan d'in ya sake yi da hanzari yana tambaya
"Tashi za kayi ne..!?"
Wannan karon da kai ya amsa masa alamun "Ehh",Taimaka masa Sultan yayi har ya sauka daga saman bed d'in,a hankali sai ya furta
"Thanks dude..!"
Murmushi Sultan yayi masa yana girgiza kai alamun babu komai,sannan ya juya yana tafiya a hanakli har ya isa bathroom,alwala ya d'auro bayan ya wanke bakinsa ya fito, pray mat ya shimfid'a sannan ya daidaita a kai,ya kabbara sallah,duk da bawai lokacin sallah ne yayi ba dan duka a lokacin bazai wuce 11am ba na safe,raka'a biyu yayi a daddafe masu sauk'i,sannan yayi tahiya ya sallame,ya d'auki lokaci yana addu'ah,yayin da Sultan ya zuba masa idanu kawai yana kallonsa da tsantsar tausayawa irin rayuwar da yake ciki,,,idanunsa da hawaye kwance a cikinsu,sai dai basu samu damar saukowa ba,,ya shafe tsawon mintuna kafin ya mik'e a gurin,bayan ya maida pray mat d'in muhallinta ya koma ainihin inda ya taso,har lokacin bakinsa na motsawa alamun yana ci gaba da addu'ah hannunsa rik'e da counter,,fuskar serious Sultan yayi wearing yana kallonsa
"Dude..! Ina da magana fa.."
Ba tare daya kalleshi ba,muryansa cikin sanyin da kana ji kasan tsabar jin jikin da yake yine yasa ta koma haka
"Uhhuumm..! Kana iya fad'in duk abunda ka so.."

"A'a broah..! Ba haka nake so naji ka fad'a ba,,idan har dan zan iya fad'ar duk abunda na so ne,ai da ba saina tambayi izininka ba.."

"Kada ka damu,,kai dai ka fad'a kawai ina sauraron ka.."
"Uhhuumm" Sultan yace kafin ya sake kallonsa yana fad'in
"Barshi ma kawai.."
D'agowa yayi da idanunsa ya kalleshi kafin ya tab'e baki
"Ok..good.."
Sake kallonsa Sultan d'in yayi jin abunda ya fad'a
"Baka son ji kenan..!?"

"Tunda baka yi niyyar na sani ba,mene amfanin na takura ka fad'a..!?"
Murmushi Sultan yayi yana jinjina kai
"Kai dai kam wollahi zanga ranar da zaka chanja.."

"Baza ka tab'a ganinta ba kuwa..Idan har ita kake jiran gani,,bana tunanin zata zo.."
Surin taron numfashin sa sultan yayi da cewa
"Zata zo..Kuma zaka ce na fad'a maka..Da idanunka zaka ganta..!"
Shima Sultan d'in yayi saurin katse masa maganar,sake tab'e baki yayi while yana fad'in
"I don't think so.."

"Ok.. Ni dai naji a jikina kuma nasan zai zo,,buh bama wannan ba,,,tun wancan ranar da muka baro Wudil naso yi maka maganar,to kuma dai yanayin da kake ciki sai yasa na kasa yi maka bayanin abunda naji tun a ranar.."

"Akan mene ne..?"

"Labarin abunda ya faru da mutanen garin mana ai shi naso sanar maka lokacin.."
Idanunsa ya zuba akan Sultan yana jiran yaji abunda zai fad'a,yadda yaga alamunsa take ya fahimci lallai akwai labari a tare da shi,sai dai baya jin zai iya fahimtarsa,a hakan kuma sai ya bada nutsuwarsa akan Sultan d'in bawai dan ya damu da son jin abunda zai fad'a masa ba,ga Sultan kuwa ko da yaga yasa nutsuwa a lamarin take ya kwashe kaf yadda suka yi da dattijon nan ya sanar da shi,,tun daya fara bashi labarin banda gumi na tsabar tashin hankali babu abunda Hammad keyi,bakinsa yana fad'in "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un,,Laa ilaha illah anta subhanaka inniiy kuntu minaz'zalumiiyn",har zuwa lokacin da Sultan ya rufe labarin da fad'in
"A gaskiya d'an uwa ina ganin *AL'AMARIN* soyayyarkan nan sai Allah,then muci gaba da addu'ah,,idan har Allah yasa kuna da rabon ganin juna to..Amma duk ta yadda kake zato wollahi lamarin nan naku ya wuce haka,ni kaina ban tab'a tsammanin *AL'AMARIN* ya kai nan ba.."
Idanunsa da suka fara rikid'ewa ya sauke k'asa daga kallon da yake jifan Sultan da shi na jin irin fatan da yake masa,,a k'asan zuciyarsa kuma yana ci gaba da tasbihi ga Allah da yi masa kirari akan ya jib'inci *AL'AMARINSA* idan har da rabon su ga juna a rayuwa ya had'a su da gaggawa
"Bana tunanin akwai wani da zamu samu wanda yasan inda suke rayuwa gaskiya a yanzun,tunda nayi tambaya nd nayi bincike amma har yanzun shiru bamu samu wani gamsashiyar amsa ba.."
Lumshe idanun dai ya sake yi,yana gyara kwanciyarsa yayin da yake jin zuciyarsa na masa wani iri,sam babu dad'i a yanayin da yake ciki yanzun,,kula da Sultan yayi da halin da yake neman shiga shi yasa shi yin shiru daga maganar da yake
"Dude..! Kana lafiya dai ko..??"
Idanunsa ya d'an bud'e a hankali ya kalli Sultan ba tare daya amsa ba
"Dan Allah broah..! Kada kasa damuwar wannan *AL'AMARIN* a zuciyarka,,ya kamata ace zuwa yanzun komai ya canja,ka cirewa kanka damuwa,idan fa wani abu ya sameka Mamma da mu dukanmu zamu shiga damuwa,,,idan muka maida lamuranmu gurin Ubangiji zai isar mana,amma damuwa babu abunda zai haifar sai k'aruwar ciwo."
Murmushin takaici ya saki,ba tare daya iya cewa da shi komai ba ya sake maida idanunsa ya kulle,har Sultan ya gama fad'ar abunda zai fad'a bai sake daga ido ya kallkalle shi ba,sai daya tashi tafiya da yayi masa sallama sannan ya bud'e idanunsan suka yi sallama ya tafi.
Tunda Sultan ya saka k'afa ya fita ya barshi a gidanyake cikin damuwa a dalilin jin irin iftila'in daya cafkawa al'ummar garin wanda shi ne dalilin daya sake d'aga masa hankali,,musamman kuma da yaji ance bayan nan sama da mutum ashirin sun rasu,duk sai zuciyarsa ta kasa samun sukuni,tunanuka da dama suna sake bijiro masa,tayin da zuciyarsa ke hasko masa wasu faruwar lamarin tamkar a gaban idanunsa ne suke kan faruwar,,wayer garin ya tashi jikinsan da sauk'i sosai amma zuwa yanzun tsananin tashin hankali yana neman ya maida komai baya,ciwo yana neman dawowa sabo,da taimakon addu'o'in da yake yi Ubangiji ya taimake shi tun kafin ciwon yaci k'arfin jikinsa ya janyo drawer da magungunansa ke ciki,bai jima sosai da shan maganin ba bacci ya d'auke shi.

Kwanaki sun dad'a tafiya har lokacin Hammad yana cikin wannan mawuyacin halin,,jinyar da duka yayi

Please Login or Register in order to submit comment