Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

na d'aukeka, a raina, ai ko yadda duk duniya ban nufi ko inaba da Abba ya koreni sai gidanku yaci kasan tsakaninmu mun zama uwa d'aya uba d'aya".
Kafad'ar Aryan d'in ya dafa tare da son gamsar dashi yaci gaba da cewa.
"Ina kewar ahalina ne Aryan dama ace Abba zai bani dama naje nayi sallama dasu tunda ita tafiya kai kake da ita dawowa kuwa sai Allah yayi ban sani ba zan dawo a raye ne ko a mace Allah masani".
wani irin hawaye ne mai zafi da k'una ya ziraro masa, cikin sanynn jiki ya saka bayan hannu ya goge ,
ajiyar zuciya Aryan yaja yace.
"Nima na dad'e ina wannan tunanin amma shawara mezai hana tunda gobe juma'a in mun dawo daga masallacin juma'a kawai mu wuce gidan tunda kaga gobe zamuje gidan sarki kuma ranar lahadi zamuyi tafiyar nan muje kila wala Allah Abba ya saurare mu koya kace?".
shiru Yusuf yayi saboda yasan kafiya da taurin zuciya irinna Abba in yahau babu mai iya tank'wara shi sai Hajja Inna shima yana hak'ura ne kawai dan zamowarta mahaifiyar shi danba k'aramin biyayya da soyayya yake yiwa tsohuwar nan ba tom shi kuma ita ya daka da wanine ma da yasan da tuni an wuce gurin Hajja Inna ta saka Abban ya yafe mishi Aryan ne ya katse mishi tunanin nashi da cewa. "Kayi shiru bakayi magana ba?".
firgigit ya dawo daga tunanin daya tafi yace.
"Hmmm anya kuwa Aryan kana ganin wannan shawara ce Abba zai Yadda?".
cikin shakku Aryan yace. "In sha Allahu zai amince muci gaba da addu'a".
daga haka sukayi shiru har suka k'arasa gida hirar da suka saiba zuwa taya Hajiya Kaka ma yau basuje ba saboda kowa da kalar damuwar da take cikin zuciyar sa.




2:15am Yusuf ya tashi sai nafila yake yana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar mahaifin nashi ya janye fushin da yakeyi dashi, bashi ya kwanta ba saida suka dawo daga masallaci sallar asuba.



1:30pm Yusuf sanye yake cikin Shadda fara pitet irinta samari kanshi sanye da hula bak'i hannunsa daure da agogo sai bak'in takalmin dake sanye a kafarshi shigarsu iri d'aya da Aryan sallama sukayi da Hajiya Kaka tayi musu addu'ar dawowa lafiya,
sam jikin Yusuf bai bashi zuwanshi shine maslaha shiyasa yau suku-suku ya tashi sam bashi da kuzari Aryan nema ke bashi karfin gwiwa haka suka hau machine din Aryan ya tuk'asu kai tsaye masallaci suka nufa bayan sun idar da sallah Yusuf yace.
"Allah Aryan tsoro nakeji tun jiya da mukayi maganar nan inna tuno zamuje gida kirjina saiya buga da sauri ina tsoron bansan me zanje na tarar ba, bansan me zuwana zai jazawa Mama ba". murmushi Aryan yayi duk da shima yanajin tsoron amma danya karfafawa Yusuf gwiwa sai yace.
"Haba Yusuf in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi kana karanta Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" shiru Yusuf yayi had'i da girgiza kansa, sanan suka nufi gidan.



Dai-dai k'ofar gidansu Yusuf,
Aryan yayi parking d'in machine d'inshi nan suka nufi gidan Yusuf na gaba Aryan na biye dashi a baya, suna isa bakin k'ofar gidan cikin fargaba da tsoro Yusuf yasa hannunshi tare da turo k'ofar yayinda bakinshi ke dauke da addu'o'i a hankali ya tura k'ofar had'i da d'aga k'afa d'aya niyyar shiga gidan,
Abba kuwa da dawowar sa kenan yana sama yana zaune cikin yar barandar saman gidan hannunshi rik'e da carbi, jin k'aran bud'e k'ofar gate d'in yasashi d'ago kai tare da zubawa mai shigowan ido,
da sauri ya mik'e cikin tsananin fushi da zafin zuciya ganin Yusuf cikin fad'a da tsawa yace.
"Kaaai...! Yusuf karka sake k'afarka ta taka cikin gidanan maza juya kabarmin gidana ,in ka kuskura nazo na sameka anan to sai dai uwarka ta haifi wani d'an."
shi kuwa Yusuf da Aryan a firgice suka d'aga kai sama suna fuskantar inda sukaji muryar Abba gaba d'aya jikinsu b'ari yakeyi,
ganin yadda Abba yake musu hargowa da son tara musu jama 'a yasa Yusuf rumtse idonshi cikin tsananin k'unan rai da zafi ya tsaya a wurin kamar wanda aka dasa ya kasa yin baya bare gaba, hatta k'afarsa da ya d'ago da niyar shiga cikin gidan ya kasa sauk'eta haka yasa yake tsaye da k'afa d'aya,
sai jikinshi dake bari kamar mazari idanunshi sunyi jazir,
a cikin gida kuwa duk abinda Abba ya fad'a duk sunji, shiyasa gaba d'ayan suka fito harabar gidan a guje,
suna isa farfajiyar gidan Abba ya daka musu tsawa cewa kada wanda ya kuskura ya isa inda Yusuf yake,
gaba d'aya suka tsaya yaran sai suka saki kuka suna kiranshi,
shima Yusuf kukan yakeyi ganin Mama na kuka kamar ranta zai fita,
cikin zafin rai taci gaba da tafiya zuwa inda Yusuf d'in ke tsaye,
ganin haka Abba ya buga mata tsawo tare da cewa.
"Hafsa kada ki kuskura kije inda yake, wallahi in kin isa inda yake akan igiyoyin aurenki duka uku,
kuma wallahi babu ke babushi a cikin gidannan.!."
cikin kuka Mama tace.
"Zanje..! wallahi!! zanje!!! gareshi na hak'ura da auren naka! na yarda zamu barmaka gidanka ni dashi ni zanbi d'ana."
tana fad'in haka ta juya cikin kuka ta d'aga k'afarta tare da yin taku d'aya ta nufi inda Yusuf ke tsaye yana zubda hawaye,
ido ta zaro tare da tsananin firgita jin wani irin k'ara da Yusuf ya saki sabida...!





*BY*
*GARKUWAR FULANI*
[02/01 1:06 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣4⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*




🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





*GA masu buk'atar shiga group na k'ofa a bud'e take, turo katin MTN na 200 kacal ta wannan layin etisalat d'in 09097853276 ko kuma ku turo d'ari biyun ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar kinyi screenshot kin turo min shaidarkin biya kud'in shiga group d'in HUKUNCIN ALLAH*

~Free page~

*IN KUKE NE AMARE, MANYAN MATA DA YAN SAFFA-SAFFA DA 'YAN MATAN DA AKE SHIRIN AURAR DASU, KADA KU MANCE MACE SAIDA GYARA, TO GA NESA TAZO KUSA. MANHAJATA TANA BUD'E CIKE DA ABABEN GYARA KAYAN MARMARI, AKWAI TSUMI MAI KYAU HAD'IN FULANIN GEMBU SANNAN AKWAI DAKA HADIN BUZAYEN NIGER AKWAI GARIN MAD'I MAI TAKEN MAIDA TSOHUWA YARINYA YANA CIKO MACEN DA HAIHUWA YASA TA SAKE KO KUMA YAWAN SHEKARU YASA TA BAJE YANA TSUKETA TA CIKO, AKWAI GUMBA DAKAN MALI MAI TAKEN SUSUTA MAI GIDA, INA MATAN DA MAZANSU SUKAYI SANYI, TO AKWAI TSUMINSU MAI GYARA MAI GIDA YA ZAMA TAMKAR MATASHI SABON BALAGA, HAKAZALIKA AKWAI MAGUNGUNAN INFECTION SADIDAN, AKWAI ZUMAR BABBAR MACE AKWAI AUDUGAR MATSI AKWAI BITA ZAI-ZAI AKWAI MAN AYU DA KITSEN DAMO AKWAI MAGANIN NARKARWA AKWAI NA GYARAN NONO SANNAN AKWAI SABULAI DA MAYUKA MASU GYARA JIKI DASA K'AMSHI INA MUKU AL'BISHIR DA AKWAI SABULUN KANKANA DOMIN MONKE HQ YANA GYARA MACE SHI DAMA MUSAMMAN DAN WANKE CAN AKAYISH KAI ABINDA BAZAI K'IRGUBA, BAHAUSHE YACE. "GANI YA KORI JI". DOMIN GANIN ZAHIRI MAI SAYAN DADDAYA KO SARI KU TUNTUBENI TA WANAN NUMBER 09097853276 IN TURA MIKI KI ZAB'I IRIN WANDA KIKESO. DUK GARINDA KIKE ZAN AIKA MIKI , SAYAN NAGARI MAIDA KUD'I GIDA, IYAYE KARKU AURAR DA YARANKU BA GYARA SAI KUNZO*




Cikin firgici da tsoron Mama ta d'ago kanta tare da kallon inda Yusuf yake dan jin sautin muryar Yusuf da ya fara zubda hawaye sabida ganin ta d'aga k'afa da niyyar tahowa gurin shi da sauri ya rab'a jikin Aryan dan gudun kar ya taka k'afarsa a harabar gidan dan furucin da Abba yayi na yana taka k'afarsa kan auren Mama, kanshi ya rink'a jujjuyawa cikin rawan murya yace.
"Noo...! Mama karki zo dan Allah ki rufamin asiri! dan Allah Mama kar ki yanke wannan hukuncin, karke d'auke min sauran farin cikina wallahi in haka ta kasance na zama sanadin mutuwar aurenku bazan tab'a yafewa kaina ba, kuma nayi asarar rayuwata, Mama wanne hali kike tunanin zan shiga randa za'ace bakya tare da Abba, please karki k'ara ko taku d'aya kuskuren da nayi a baya ma ina danasani ina neman hanyar da zanbi danna gyara kuskurena in dawo gareku ina gudun kar wata masifa tayi ta bibiyar rayuwata...".
sai kuma muryarshi ta carke wani irin rauni da tausayin mahaifiyarshi ya rufeshi ganin yadda ta tsaya cak tana wani irin kuka mai tsuma zuciya,
tuni kukan ya kwace masa da k'arfi hannunsa duka biyu ya saka ya rufe fuskar shi yana gurzar kuka,
Aryan ma dake tallabe dashi kuka yake iya k'arfin shi.

Cikin zubda hawaye Aunty Amarya ta rik'o hannun Mama tare da cewa.
"Kada ki aikata wannan kuskuren Maman Yusuf wannan hukuncin da zaki yanke bashi ne maslaha a garemu ba, hakuri shizai magance komai zamanki tare da Abba da mu kici gaba da lallami da lallashin Abban Yusuf shine zai saka mu cinma burin mu dan Allah kiyi hak'uri karki k'arawa Yusuf zafi bisa zafi".
cikin shesshek'an kuka Mama ta fara share hawayenta tare da k'ak'alo murmushin dole dan kontar da hankalin d'an nata, kallonshi tayi cikin tsantsar k'auna da bege sai ta kuma yimishi murmushi,
shima murmushin yayi mata tare da jujjuya ya mata kai da kad'a mata yatsunshi hud'u alamar kartayi kuka kuma su duka hud'u suna tare Abba da ita da Zulaihat dashi d'in, ma'anar kad'a mata yatsu hud'un kenan,
murmushi ta kumayi yayinda hawaye ki tsirarowa a fuskarta, cikin sanyin murya tace.
"Allah yayi maka albarka ya karemin kai rabbi ya tsare min imaninka da gab'b'anka."
sai ta kuma d'aga kai da hannunta sama tare da cewa. "Ya hayyu ya k'ayyum ya zirjalali wal ikram ya Allah kai nake rok'o ka tsare min Yusuf ka tsaremin idanunshi daga ganin haram ya Allah ka tsaremin kunnenshi daga jin zance na haram ya rabbil izzati ka tsaremin k'afafunshi daga zuwa ga haram ya rabbi ka tsaremin hannunshi daga tab'a haram ya Allah ka tsaremin Al'auransa daga kusantar haram, Allah ka had'ashi da halal d'inshi ka bashi nasara kan dukkan lamuranshi."
sosai Yusuf yake dariya yayinda kuma hawaye ke bin fuskarsa yaso ace hannun Mama na tsakiyar kanshi yayin da take mishi irin wad'annan addu'o'in da ni Garkuwa nake yiwa yarana, ya kuma kamata ko wacce uwa takeyiwa yaranta,
murmushi yakeyi sosai tare da cewa.
"Amin Amin, Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati, zadakillahu ilman wa fikhran wa yatta k'inallahu jami'aaan ya ummee, ana uhubbuki hubban azeem ya mu'allima, laisa li misluki abadan ya habibati."
ita kam Mama dariya takeyi sosai tana jin dad'in yadda d'an nata ya shiga farin ciki, tana alfahari dashi yadda yake iya sarrafa harshensa.

Zahra kuwa da yanzu ta fito da niyar ta sad'ad'a ta gudu shagon telan daya dawo shagon idi dan ta d'ebo k'ellayen wasanta, tsalle tayi
ganin Hamma Yusuf d'inta dan tunda ya daka mata Hajja Inna take Al'fahari dashi da gudu ta kwasa sai gurin Yusuf d'in k'afafunshi ta rungume tana.
" Oyoyo Hamma Yucuf na a dawo."
cikin zubda k'ollah yasa hannun ya d'agota sama sannan ya jingina kanshi da jikin Aryan goshinta ya d'aura kan nashi hancinta na gogar hancinsa, murmushi yayi mata tare da lumshe idonshi wanda sanadin haka hawayen dake tare a idonshi suka zubo,
Ita kuwa Zahra tana ganin haka da sauri takai hannunta kan hab'arshi tana sharemai hawayen tare da cewa.
"Sorry Hamma Yucuf ka daina kuka kayi shiyu, zan baka sweet in kayi shiru kaji ko? kana son cakuleti ko?".
kai ya gyad'a mata tare da yin dariya,
ita kuwa sai ta saka hannunta tana goge mishi hawaye,
"Yauwa Hamma Yucuf an baka da yawa amman sai kayiwa Hajja Inna duka irin na ancan ranan."
rungumeta yayi tsam a k'irjinsa yanajin wani k'unan rai da tausayin yarinyar nabin jini da bargon shi,
duk da akwai hawaye a idanuwan shi murmushi yayi mata yace.
"Toh Zarah amma kina zuwa makaranta dai ko kina karatu sosai ko?".
'kanta ta gyad'a had'i da fara biya mishi karatun nata.
Daddy daya fito shima saboda time d'in da Yusuf yazo shigarshi bathroom kenan kuma yanajin duk abinda ke faruwa umarni ya bawa aunty Amarya yace.
"Maryam kije wurin Yusuf kiji dame yazo nine mijinki kuma nine na baki umarni zo muje". ai da sauri tabi bayan Daddy daman aunty Amarya dan babu yadda zatayi ya saka ta hakura da gudu-gudu sauri-sauri ta karasa gurin Yusuf k'afarshi dake d'ankale a harabar gidan ya fitar ya tsaya ta woje dan hango Abba na sauk'owa daga saman gyara tsayuaarsa yayi had'i da gaida Daddy da Anty Amarya da suka k'araso,
cikin tausasa zuciya sukayita lallashin sa da kalamai masu dad'i da sanyaya zuciya,
ita kuwa Mama ganin Abba ya fito a zafafe yasa ta juya ta koma part d'inta
cikin gunjin kuka da bak'in ciki.
cikin sanyin murya fuska d'auke da murmushi Yusuf yace.
"Aunty ga Amanar Mamana nan da k'annena please ki kulamin dasu nabar amanar su a hannunki ko bayan raina ina fata ki rikemin su da duk kulawar da zaki iya, sannan Anty karki manta Zahra amanace Allah ya baki kuma abar tambayace".
kuka ne ya kwace mata,
shi kuwa kai ya juya mata had'i dayin wani murmushi ya juya sannan ya kama hannun Aryan suka juya suka tafi.
kuka Aunty Amarya ta saki da k'arfi had'i da kwalawa Yusuf kira amma ina ko juyowa baiyi ba Aryan ne ya tashi machine d'in Yusuf yahau baya yaja cikin sanyin jiki suka bar layin.



Hajja Inna kuwa dake tsaye tana kallon duk abinda ke faruwa ajiyar zuciya tayi had'i da gutsirar goron ta ta afa a baki tare da taunawa tace.
"Wai Allah na gode maka tab! yauda Yusuf ya shigo gidannan da babu abinda zai hana na tattara kayana nabar gidan".
harara Amira ta buga mata da jan tsaki tace.
"aikuwa sai dai ki mutu insha Allah sai Yusuf ya dawo gidannan ko kuma kema ki koma gidanku ai shi dai nanne gidansu".
harara Hajja Inna ta buga mata tace.
" Hegiya gantalalliyar yarinya nasan maganin ki aure zan saka uban naki yayi miki".
daga nan ta juya ta shige part d'inta,
Aunty Amarya kuwa Daddy ne yaje ya kamota suka koma part d'insu.



Yauma gaba daya farin ciki da nutsuwar cikin gidansu Yusuf ya kau kowa ka kalli fuskar sa tsantsar damuwa da bakin ciki ne aciki.



Koda su Yusuf suka isa gida ta k'ofar gaba suka shiga cikin part d'insu suna gudun kada Hajiya Kaka ta fahimci abin daya faru, wunin ranar gaba daya basu yishi cikin farin ciki da walwala ba gaba daya Yusuf ya wani zama wani iri Aryan nema yake tausar shi,
koda mangirb tayi suka tafi masallaci basu dawoba saida sukayi isha,
bayan sun dawonma part nasu suka koma jiki duk a mace, badan sunso ba suka tashi suka shiga cikin gida saboda Raihana da Hajiya kaka ta aiko ta kirasu.

Ganinsu gaba d'aya ba cikin walwala ba nan hankalinta ya tashi ta fara tambayar su me yake damun su cikin yak'e sukaso danne damuwar su badan ta yarda badai ta hakura ganin basason sanar mata, dole ta tasasu gaba sukaci abinci sannan suka d'anyi hira sai da sukaga Yusuf ya d'an sake sannan suka koma part nasu kowa ya konta.



Washe gari asabar misalin 10:00am coach Fu'ad ne tsaye a gaban su Yusuf a filin sukuwar dake cikin masarautar Adamawa, cikin kula yace.
"Ina gargad'in ku akan bama son a samu rashin nasara akan wannan gasar kada ku manta wannan karan ne team d'in Jahan zai fara zuwa wakiltar jahar mu kuma kinfi kowa sanin irin kud'in da Malam Jabeer ke kashewa a kanku, kun dai san polo wasane me zaman kanshi shiyasa yakeda tsada, sannan kuna ganin wani lokacinma da kanshi yake horar daku, so dan haka ya kamata ku karowa jahar mu k'ima da mutunci a idanuwan jama'a."
kai suka jinjina cikin gamsuwa da bayaninshi tare da cewa.
"In sha Allah bazamu kunyatashi ba."
daga nan yace su taso suje suga dokunan da aka tanadar musu dan zuwa gasar,
Yusuf ne a gaba dan haka a sannu ya fara zagaye dawakan dukan su yana k'are musu kallo wani jan doki ya gani jikin shi har kyalli yake ga wani gashi daya kwanto a goshin shi sai d'an farin d'igo a tsakiyar goshin dokin a sannu dokin ya dinga masa gizo da badsha d'inshi saboda komai da komai iri d'aya ne murmushi yayi had'i da shafar kwantaccen gashin goshin dokin had'i da sumbatar shi bakin shi yakai dai-dai kunnen dokin hadi da rad'a mishi sunan.
*"Guramm...!".* haniniya dokin yayi had'i da d'age kafafuwan shi duka biyun na gaba, alamar sarawa murmushi Aryan yayi a ranshi yace.
"Barde kenan kasan sirrin dawakai ciki da bai".
Safwan kuwa wani irin takaici da haushin abinda Yusuf yayi yake ji shi ko ina sai yayi abu fiye dasu yan gadon alhalin shi Kuma d'an taka haye ne.
coach Jabeer da Fu'ad suma sosai Yusuf ya burgesu, daga nan suma su Safwan, Aryan, Affan, suka zabi nasu dawakan suka fito.




Nasiha mai shiga jiki Malam Jabeer yayi musu yace.
"Kada ku d'auka gasar nan iya haka zata tsaya kuce ai babu komai tom ku sani duk wani motsin ku akan idanuwan wasu suke dan haka ina muku nasiha ku rik'e mutuncin ku da darajarku da tarbiyarku dan kune maduban da suke nunawa duniya irin tarbiyar jiharmu, kuna kuma sane da cewa ni Jabeer zan barranta da kowa da komai matuk'ar zai shafi daraja da mutuncin masarautarmu da gwamnatin mahaifina dan haka ku tsare mutumutuncin addininmu shine gaba da komai,
sannan dangane da gasa ku sani ita gasa kwarewa da samun lafiyayyun dowakai shine sirrin cin gasa dan haka na shirya muku wadannan lafiyayyun dawakan kosassu wadanda suka horu a harkar tsere dan dawakan ma bananan bane tafiyayyu ne nayo order dinsu daga England dan haka ina muku fatan sa'a da nasara mai amfani".
godiya sukayi masa na nuna masa kwarin gwiwar su akan zasuyi kokarin ganin basu bashi kunya ba, nan suka fito kowa ya tafi gida da niyyar gobe 4:00pm jirgiin su zai tashi zuwa kaduna.



Motar kuma da zata kwashi dawakan tana tsaye dama tana jira su gama zab'a driver dazai kwashesu yana cikin motar shima, a sannu fadawa suka taimaka wajen saka dawakan a mota aka tafi dasu.



Koda su Yusuf suka koma gida Aryan ne yayi kokarin had'a musu kayan nasu dan har zuwa lokacin babu wani kuzari a tattare da Yusuf, wayar Yusuf d'ince tahau ringing ganin Daddy ke kiranshi d'agawa yayi bayan sun gaisa yace.
"Yaushe ne tafiyar taku?" cikin sanyi Yusuf yace.
"Gobe ne in sha Allah".
cikin kulawa Daddy yace. "Toh shikenan nima in sha Allahu zanyi k'ok'ari na halarci gasar taku dan haka karka damu muna tare kaji ko?".
ajiyar zuciya Yusuf yayi dan sosai yaji dadin abinda Daddy yayi cikin jin dad'i yace. "Yauwa Daddy nagode nagode,
Daddy Allah ya k'ara girma ya saka da alkhairi". murmushi Daddy yayi yace.
"Ameen ya Allah amma dan Allah inaso ka cire damuwa daga cikin ranka saboda ka samu damar wining a gasar taku".
murmushi Yusuf yayi yace. "insha Allah Daddy na gode". so sanadin wayar da Yusuf sukayi da Daddy shine ya saka shi jin damuwar shi kashi 50 daga cikin 100 ta tafi, hakanne ma ya bashi damar samu sukeyin hira jifa-jifa shida Aryan d'in.



washe gari bayan sun gama shirinsu tsab suka shiga part d'in Hajiya Kaka suka yimata sallama,
tana tayi musu addu'a ta rakasu har bakin gate inda driver ya daukesu ya kaisu masarautar ADAMAWA daga nan aka kwashe su a mota sai airport tare da yan rakiyar su daga fadar mai martaba.



Jirgin su na sauka olready motar da zata kwashe su ta kaisu hotel din da zasu sauka tazo tana jiransu suna sakkowa daga cikin jirgi suka fito daga cikin airport d'in motor ce ta kwashe su sai masauk'insu, olready yan Jos da Lagos da katsina sun karaso birnin Kaduna nan suma aka basu masauki bayan sunyi wanka sunci abinci nan suka fita masallaci saboda kiran sallah da akeyi, bayan sunyi shirin baccinsu dan tunda suka iso corch insu ke koyar dasu, sanan yanzuma d'aki-d'aki ya bisu yana k'ara k'arfafamusu guiwa.




Washe gari ran Monday misalin 4:00 pm *MURTALA MUHAMMAD SQUARE POLO CLUB KADUNA* ne cike da yan kallo da masu fada aji na cikin garin kadunan yan kasuwa da kuma k'usoshin gwamnati dan har mai girma gwamna da mai martaba sarkin zariya ma sunje, gefe kuma alk'alan wasa ne zaune gaban ko wanne alkali akwai laptop da loudspeaker can gefe kuma likitoci ne saboda kota kwana, sannan akwai dawakai lafiyayyu daga gefe ko bukatar canjin doki gad'an wasa zata tashi.



Can gefe kuwa Wasu k'ofofine masu kamar gate a k'Alla sun kai (25) suka Bud'e wasu k'osassun lafiyayyun dawakai ne suka fito ko wanne da mahayin sa a kanshi, ko wanne team daya wakilci jahar shi kamar *Kano Polo team* da *Kaduna polo team* da *Katsina Polo team* da *Adamawa polo team* da *Lagos Polo team*
*Jos Polo team* jahohi dai da dama,
rigace sanye jikin ko wanne mahayin doki daga gaban rigar sunan team din da yake wakilta ne daga bayan rigar kuma sunan mahayin dokin ne Yusuf dake sanye da yeluwar riga gabanta an rubutu *JAHAN TEAM* bayan rigar kuma an saka *BARDE 3* daga sama a tsakiya kuwan an saka Jahan polo team,
dukkansu hannunsu rike da s Polo sticks with polo balls , zaune suke akan dokin cikin kwarewa da d'okantuwar abinda zasu gabatar ko wanne ya rike linzamin dokinsa cikin bajinta.



*Adamawa Polo team* ne zasuyi tsare tare da *Katsina Polo team* inda a cikin su gari 1 zai cire d'aya daga gasar,
bindiga aka saki durumm alamar suyi ready nan suka k'ara dai-daita zamansu kan dawakan da dad'a rik'e sandar tasu da kyau minti 2 tsakani aka kara sakin bindiga ta 2 nan ko wanne d'an wasa ya k'ara rike linzamin dokin sa dummmmmmm! K'arar bindiga ta uku ta biga tamkar walkiya suka saki lizamin dawakan nasu da zungurar cikin su cikin abin da bai wuce k'iftawar ido ba dawakan suka take gudu suke tamkar k'afafuwan su basa tab'a k'asa inda mahayan suke dad'a zaburar su da zungurar cikin su sannan kowa na sarrafa sand'arsa dan samu egg d'in ya dawo gareshi,
tsere ya mik'a gudu dawakan suke iya k'arfin su a sannu wasu dawakan suka fara rage gudu amma banda dokin Barde da Safwan 2 da d'aya daga cikin yan Katsina polo team prince kusan a jere suke gudu dan koya dokin 1 ya wuce na d'aya zakuga mahayin shi ya zungure shi ya k'ara gudu saura daf su k'arasa cikin kwarewa da sanin sirrin doki Yusuf yayi wani tsalle da dukan cikin had'ida

Please Login or Register in order to submit comment