Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya k'ara sannan ya fito a motar dai-dai gate d'in ya tsaya had'i dayin knocking mai gadi ne ya fito d'an risinawa yayi yace.
"Baba ina wuni".
d'an sakin fuska yayi ya amsa da.
"Lafiya qlau dan saurayi lafiya dai ko? wa kake nema".
shiru ya d'anyi dan tunowa da yayi ko sunanta bai saniba sai ya kuma dan nisawa yace.
"Bak'on yarinyar gidannan ne data shogo yanzu".
murmushi ne ya fad'ad'a fuskar Baba mai gadi yace "Auho Raihana?".
cikin zumud'i saurayin yace.
"Eh ita dai Baba". nan ya matsa masa ya bashi hanya yace.
"bismillah ka shigo".
nanya shiga kirjin shi na bugawa yana addu'ar Allah yasa Raihana ta karbi soyayyar shi duk dama sai yanzu yaji sunan ta.



Wurin mai gadi ya bashi inuwa kan benci yace.
"Zauna anan bari naje na fad'a mata".
saurayin yace.
"toh Baba" nan Baba mai gadi ya k'arasa cikin gidan tsaye yake a k'ofar da zata sadaka da ainahin cikin gidan Raihana data fito daga kitchen hannunta d'auke da plate ta zubo d'an wake ta kalli mai aikin su tace,
"Juli jeki duba mana kina jin ana knocking k'ofa?".
Nan Juli ta bud'e mai gadi yace.
"Kije ki sanarwa Hajiya k'arama tayi bak'o".
Juli ta amsa mishi lokacin Raihana harta zauna ta fara cin d'an waken ta Julin tace "Aunty wai kinyi bak'o".
Raihana ta maimaita "b'ako kuma? Kuma yace gurina yazo?".
Hajiya Kaka ce data fito yanzu da carbi a hannunta tace.
"Toh gurin wa zaizo banson shirmen banza Juli je kicewa Bala ya bude mishi k'ofar parlour Aryan ya shiga,
ke kuma kikai mishi ruwa".
da to Julin ta amsa inda ta sanarwa Baba mai gadi abinda Hajiya Kaka tace sannan itama ta nufi kitchen dan aiwatar da abinda aka sakata.



Raihana kuwa hankalinta kwance taci gaba dacin abincin ta ganin a k'allah da zuwa kiranta da kaiwa bak'on ruwa zaiyi minti 10 Hajiya Kaka tace.
"Ba kina da bak'o a parlour ba amma kike zaune har yanzu".
tunzura bakinta gaba tayi tace.
"Toh Hajiya Kaka nifa ban sanshi ba kuma kiga dawowata daga makaranta kenan ko wanka ma banyi ba".
Hajiya Kaka tace.
"Toh me kike nufi so kikeyi yayita zaman jiranki har sai kinyi wanka zakije kiji dame yazo in kuma zancen kice baki sanshi bane kije ai zakiga ko wanene".
cikin tura baki tace.
"Toh amma.....".
da sauri Hajiya Kaka ta katseta.
"Amma me? kinsan dai banason musu ko?."
mik'ewa Raihana tayi taje kitchen ta ajiye plate d'in d'an waken ta wanke hannunta fitowa tayi ta shiga d'akinta ta d'auko wankakken hijab tad'an fesa mishi turare ta saka hijab d'in dogo ne danya wuce gwiwarta nanta shige Hajiya Kaka tana k'unk'uni ta murd'a handle d'in k'ofar ta cikin parlourn su da sallama a bakinta.



Saurayin yana zaune shiru kanshi a k'asa da alamun tunani ya tafi jin murd'a k'ofa ya sakashi d'agowa ganin tauraruwar tashi ya sakashi sakin ajiyar zuciya Raihana kuwa d'an tsayawa tayi dimmm tunawa tasan fuskar amma a ina cikin abinda bai gaza second 30 ba ta tuna inda tasan fuskar da mamaki ta nunashi tace.
"Kaine?".
Murmushi yayi had'i da lumshe ido yace.
"Alhamdulillah naji dad'i da kikayi saurin tunani kinga hakan ya nuna min bazan samu wahalar fad'in abinda nazo dashi ba".
gujerar dake kallon tashi ta zauna had'i da gaishe shi amsawa yayi cikin sakin fuska sai yaci gaba da magana.
"Tun safiyar yau da idona yayi tozali da naki Allah ya jarabci zuciyata da fad'awa tarkon sonki ina fatan babu kowa cikin taki zuciyar yadda zan samu d'amar kundumbala cikin ta nayi shukar fure daban ruwa?". Raihana batasan sa'in da murmushi ya kufce mata ba sai ta saka hannu ta rufe fuskarta.
shi kuwa hannu biyu ya saka ya tallafe fuskar shi yace "Masha Allah fatabarallahu Ahsanul kalikin, ashe haka murmushi yake miki kyau d'an k'ara na gani" .
k'ara rufe fuskarta tayi shima sai yayi murmushi cikin sigar tsokana yace.
"Shikenan tunda rowar murmushin ake mini zan rama".
shiru ne yad'an ratsa parlour a hankali ya kira sunanta "Raihanahhh!". har zuciyarta saida ta buga saboda yadda ya kira sunanta da wata irin siga yaja k'arshen sunan "uhmmm".
kawai ta iya cewa,
shi kuwa cikin nitsuwa yace.
"Bawai da shirme ko shiririta nazo miki ba kamar yadda na fad'a miki ganin farko da nayi miki Allah ya jarabce ni da k'aunar ki ni dai sunana Faisal kuma ni ma'aikacin banki ne ni haifaffen garinnan ne ina zaune da mahaifiyata da kannena biyu a gdanmu Allah yayiwa Mahaifina rasuwa shekara biyu kenan sakamakon had'arin mota banzo miki da k'arya ba inhar kin amince inaso na kasance cikin manema auren ki kuma ina fatan na zamo miji a gareki in Allah yasa na miki".
Ajiyar zuciya taje tace.
"Nima sunana Raihana kamar yadda ka fad'a ina da Yayana ya Aryan muna zaune da kakarmu Allah yayiwa iyayenmu muma rasuwa".
sai kuma hawaye ya fara bin fuskarta,
cikin rikicewa da tausayawa yace.
"Subhanallah sorry My dear kar kiyi musu kuka ai Addu'a ce ta dace dasu ba kuka ba Raihana kici gaba dayi musu addu'a Allah ya jaddada Rahama kabarin su a , insha Allah nida Kaka da Yaya Aryan zamu zame miki madadinsu."
haka dai ya dinga rarrashinta da kalamai masu dad'i har sai data d'an sake dashi take maida mishi da martani wata maganar kuma in yayi tayi murmushi badan Faisal yaso ba yayi mata sallama sai dan yaga bata dad'e da dawowa makaranta bane kuma akwai alamun gajiya a tare da ita.


Cikin watannin 8 Faisal da Raihana suka shaqu da juna soyayya mai k'arfi ya shiga tsaka ninsu kowa nata yasan Faisal haka Shima duk yan uwanshi sun santa, shi tuni ya matsa da son zai turo iyayenshi itace ke dakatar dashi dan tana son sai ta gama digirinta, amman shi ya nace kullum sai yayi mata magiya.

***************** ************

Lokaci ya d'an ja yanayi ya sauya zuwa yanzu su Zahra ana s, s 3 tuni su Mami da Nana sun murje sun zama cikekkun yan mata masu nitsuwa da kunya, yayinda tuni sunyi nisa a karatunsu na islama dan duk sunyi sauk'a sai bitar littatafai da sukeyi.

Zahra kuwa duk da ita k'arama a kansu amman ta fisu cika da murjewa uwa uba gyara da manyance ga gayu da yawan ado da kolliya tuni yawanci yanzu yanayin abubuwanta al'adun shuwa'arab takeyi sabida zama da Anty Fadwa.

Zeenat ma yanzu tana primary 6.
Sulaiman kuwa tuni ya zama cikekken d'an jarida inda Allah ya bashi sa'a ya samu aiki a k'ark'ashin BBC, shine d'an rahotonsu, yana karb'ar albashishi mai gwab'i,,
yayinda kuwa shi ke kula da al'amuran Yusuf nan cikin k'asa,
Ibrahim dan Jafar da Sadik ma duk sun gama secondary sun zama yan matasan jami'a,

Daga nesa naketa mamakin ganin wani mashahurin canji da ci gaba a cikin garin Girei, gidansu Zahra ya zama tamkar fadar masarauta,
an gyara gidan sannan da alama an sayi filin dake kudu da gidan duk an hadeshi da cikin gidan anyi part-part masu rai da lfya, gida dai yayi kyau,
daga bakin gate kuwa har yanzu wad'an nan pompunan suna nan
inda yaran mak'ota keta zirga-zirgan d'iban ruwa suna kaiwa gida jensu,
masallacin k'ofar gidansu ma an k'ara girmanshi da fad'inshi ya zama sabo dal, gashi yanzu anguwar ta k'ara cika over.

Da sauri na kutsa kai cikin gidan dan ganin zahirin ya rayuwa ke tafiyar musu ina shiga naji muryar Anty Amarya tana cewa.
"Zahra..! Zahra..!.
shiru bata amsaba, Mama dake gefenta ne ta kalketa tare da cewa.
"Tafa shiga onka."
da sauri tace.
"To ta gama miki aikin ne?."

"Uhumm ai kin santa in tanada wurin zuwa yin aikinta da sauri takeyi ta samu ta rabu da mitata."

dariya suka d'anyi Hajja inna dake gefensu kan kujera yar tsuguno hannunta rik'e da jarbine tace.
"Wannan yarinya Allah yayita da shegen yawon tsiya kamar k'ork'ota akan mutun."
Dan guntun murmushi Anty Amarya tayi hadi da cewa.
"Ai zata bari duk randa tayi aure."

Ummi ce ta tab'e baki hadi da cewa.
"Uhum Allah dai ya kyauta ya kuma rufa mana asiri mu samu mu aurar da ita Lfy."

Shiru sukayi baki d'ayansu dan mgnar Ummee tazo da wata sigar.

wani irin k'amshi naji yana ratsani da sauri kuwa na juyo, ido na k'ara warewa a kanta,
Zahra ce ta fito a Zahranta sai wani irin k'yalli da shek'i takeyi, tasa wasu irin k'anan kaya wadanda tamkar in tayi nishi zasu fashe, dogon wondone Blue Jeans sai yar k'araar riga mai dogon hannu green color, takalminta mai d'an karen tsini lemon green da jakarshi sai wani yadi da na gani a hanunta shima lemon green,
gaban Mama ta tsuguna tare da juya mata baya tana mai mik'a mata ribbons har uku tare da cewa.
"Ayyah Mama tubke min gashin nan, sauri nakeyi ni kad'aifa ake jira."
sa hannu tayi ta amsa tana tattaro gashin da tsulbinshi yayi yawa tare da cewa.
"Anya kuwa Zahra kinsa abinda kikeyi yanzu da wannan shigar zaki fita?."
mik'ewa tayi tare da tura baki tace.
"Kallifa Mama laffaya fa zan d'aura akai, wa zaiga wannan shigar?".

Cikin dan fad'a tace.
"Keda zakije yiwa Amarya da k'awayenta k'unshi da kolliya mai zai hanaki cire wannan laffayar?."
da sauri tace.
"Yaseen yau banda k'unshi makeup kawai zan musu."

Shiru sukayi baki d'ayansu suka meda kallonsu kan Sulaiman daya shigo yana woya,
ita kuwa Zahra part d'in Mama ta nufa
kai tsaye ta shiga har cikin bedroom,
ita kuwa Mama da sulaima a tare suka shigo parlour dan Yusuf na yake son yin mgna da Maman,
suna zama Zahra na fitowa da kud'i a hannunta,
kai tsaye gefen Maman ta tsaya hadi da cewa,
"Mama ni zan tafi na d'auki kud'i 5k."
ido ta d'an waro tare da cewa.
"Ke Zahra me zakiyi da kud'i har dubu biyar?."
baki ta tura tare da cusa kudin cikin Jakarta tace.
"Turarukana fa duk sun k'ara."
kai ta jinjina mata alamar taje,
yayinda d'aya gefen kuwa Yusuf najin duk abinda sukeyi,
Sulaiman kuwa sai harararta yakeyi,
ita kuwa ko a jikinta dan kunsan tun tana k'arama bata tsoron Sulaiman,
d'an tsalle tayi had'ida, sunkuyowa ta sumbaci goshin Mama tare da cewa.
"Allah ya barmin ke Mamana."
sai kuma ta juya tana shirin barin parlour tare da cewa.
"Bye Mama sai na dawo."
har taje bakin k'ofa Mama tace.
"Zahra zoh mana ga Hammanku ku gaisa."
baki ta tura had'ida cewa.
"Kawai kice na gaidashi."
kafin Mama tayi wata mgnarma tuni ta fita,
ita kuwa tana tafe tana k'unk'uni,
"Haka kawai sai kuyi ta cewa a gaisa dashi,
al'halin shi ba gaisuwar zai amsaba sai yayi ta kindayawa mutun wasu dokoki da sharud'a kamar wani ubana, yanzu hakama in yaga dama sai ya hanani fitar."
Ummi dai da Hajja inna baki suka tab'e suka bita da harara.

Ita kuwa tana tafiya tana mita har gidan Anty Fadwa,

Cikin dariya ta kalli Zahra hadi da cewa.
"Ke kuma keda waye."

cikin yatsine fuska ta gaya mata sannan ta d'aura da cewa.
"Kuma wallahi babu manyan munafukai sai Adda Mami da Nana,
sune kome zasuyi sai sun gaya mishi kamar shine ubansu, mutumin da baya k'asar ni dadintama bai sanniba ban sanshiba, shiyasa bana kula babinsa zalina da yaci a yarintama ina nan! da cikinshi daram wata rana sai na haifeshi."
ta k'arishe mgnar cikin tsiwa,
Anty Fadwa kuwa dariya sosai takeyi hadida daukar hang bag dinta tare da cewa.
"Mu tafi to, Uwar Yusuf,
harda wai kinada cikinsa."
mik'ewa tayi tabi bayanta tare da cewa,
"Allah kuwa Anty randa duk Allah ya kawoshi gani gashi zan rama. "
ita dai Anty Fadwa mamkin Zahara da k'arfin halinta da tsiwarta takeyi, duk da kullum cikin yi mata nasiha takeyi kan ta rege tsiwarta,
juyowa tayi ta kalli Zahran jin tana tambayarta wacce unguwace gidansu amarya?
"Cikin Yola gefen masarauta."
ta bata amsa dai-dai lokacin da suka shiga cikin motar Anty Fadwan,
suna fitowa gidan a bakin masalkaci suka wuce taron dottawan dake zama a wurin,
suna wucewa wani farin dittijo ya girgiza Kai hadi da cewa.
"Kai ya Allah ka shirya mana ahlinmu."
da sauri wani daga cikinsu yace.
"Amin Amin dai malam Liman,
domin lamarin yarinyar nan sai du'a'i."
wani daga cikine ya kuma cewa.
"Yoh aini yarinyar nan har tsoro take bani, domin tana nan kamar iyalan dujal duk wurin biki tana nan, ga dan karen yawo kamar da kariyar farauta akayi ragon sunanta."
Malam liman ne ya nisa tare da cewa.
"Yoh ai duk sakacin iyayenta ne."
cikin kula d'ayan yace.
"A a wallahi babu laifin iyayenta ka duba mana sauran yaran gidan duk a nitse suke, itan ce dai tafi k'arfinsu."
Haka dai tsoffin nan sukayi ta mgnar Zahra.


A cikin gidansu kuwa,
tana fita Mama taci gaba da wayarta da Yusuf, inda yake ce mata.
"Maman Yusuf."

"Na'am Yusuf ya akayi ne?."

murmushi ya d'anyi had'i da cewa.
"Yauwa Maman Yusuf, kinga k'arshen shekara yazo ko?."

"Eh lallai kuwa nima jiya nake tunanin ina son yi maka mgnar gidan marayun nan da asibiti."

Ajiyar zuciya yayi tare da cewa.
"Yauwa Alhamdulillah jiya na turowa Sulaiman kud'in,
toh na gaya mishi ya sayi duk abinda ya dace abinci suture sannan ya biyawa yara 50 kudin makaranta,
sannan zakuje asibiti kuje layin yan yoyon fitsari ku dauku nauyin tiyatarsu,
sai kuje gidan marayun tare a nuna miki asibitin da nasa a gina a cikin in akwai gyaran da kikeso sai ayi,
sannan akwai wani masallacin juma'a da za'a gina a unk'uwarsu Aryan Bayan P, Z na dauki nauyinshi duk dai Sulaiman zai miki k'arin bayani."
sai kuma yayi shiru jin abinda take cewa.
"Duk yayi ba matsala zamuje asibitin da gidan marayun amman kasan sai da hikima zan samu fitan,
Allah ya maka al'barka ya k'ara wadata ya baka mata ta gari."
cikin jin dad'i yace.
"Amin Amin Ameeeeeeeeen ya rabbil izzati."
sannan yaci gaba da cewa.
"Sai kuma cocin L, C, C, N sun nema tai maka kona, kan gyara cocin nasu me kikace a kai."
ya k'arishe maganar cikin tsigar neman izini,
ita kuwa Mama cikin bada umarni tace.
"Ai kai ba d'an siyasa bane bare ace kana son k'uri arsu, dan haka zaka iya binsu da ihsani domin ta kyautatawa musulmi kan iya juya ra'ayin arne."
cikin gamsuwa yace.
"Yadda kikace za'ayi."
haka sukayi ta zanta yadda aiyu kan al'khairinshi zasu isa ga jama'a suna cikin hirar ta jefo mishi tambayar.
"Wai Babana kam sai yaushe zaka dawone? shin baka kewata ne shekaru nawa ban gankaba baka ganniba sai a woya."
cikin sauk'e numfashi yace.
"Mama ina son dawowa amman ina tuna Abba sai inji zuciyata ta tsinke gaba d'aya sai inji tsoro ya rufeni jakina sai ya rink'a bani babu al'khairi a dawowata."
da sauri tace.
"Subahanallahi kul! Yusuf karka sake fad'an haka, kuma kayi k'ok'arin dawowa tunda ka gama kara tunka tintini."
Ajiyan zuciya ya sauk'e tare da cewa.
"Haka Aryan ma yace kuma ya matsamin dole wai sai nazo auren Raihana, sabida banzo banema aka d'aga bikin da a watannan za'ayi, Aryan yasa aka meda bikin forkon shekara mai zuwa,
amman insha Allah zan zo."
Cikin jin dadi tace.
"Yaushene bikin Raihanan".
"Saura wata uku ne kacal."
"Kacal nema kai ka gani aini ji nake kamar in jawo watannin, Allah ya kaimu ya kawo min kai lfy."
Cewar Mama,
"Amin Amin."yace mata daga nan sukayi sallama
sannan ta tattauna da Sulaima in da anan yake ce mata Yusuf din yace.
"Ya mishi list d'in mutun 12 da suka dace zai biya musu zuwa aikin haji."
to nan suka tsara wadanda suka dace.

Bikin raihana dai nata gaba towa anata shirye-shirye Yusuf yasa an gyara gidan komai yayi tsab.


********
Sound Africa
Shiru garin yayi sabida tsananin sanyin da akayi saka makon ruwan sama da aketa tsugawa harda k'ank'ara, ga dere ya tsala,
Duk da yawan hada-hadar da daliban U, C, T, amman yau babu sabida ruwan da akeyi sannan ga dere ya tsala babu motsin komai sai sautin ruwan,
Yusuf da ke konce sai yanzu ya samu baccin azaba da wuya ya d'an saceshi,
cikin baccin da baiyi nisa, kamar a mafarki kamar a ido biyu,
yake ganin abun,
ganinshi yayi cikin wani gida mai kyau inda yake tafi da kyar dan mararshi dake mushi azabebben ciwo,
wani part ya nufa wanda yafi ko wannen kyau a gidan,
kai tsaye cikin parlour ya kutsa kai, ido ya lumshe jin wani irin sassanyar iska da k'amshi mai tsananin dadi, lokaci d'aya sha'awarsa ta k'ara k'arfi ji yake kamar yayita kurma ihu, konciya yasa yayi kan 3 str amman sai ya fasa,
ya nufi cikin bedroom kai tsaye bakin gadon yaje
kayanshi ya fara cirewa dan niyarshi na son yayi wonka ko zai samu sassaucin abinda ke d'akinshi,
gaba d'aya ya cire kayan dagashi sai boxes,
ido a rufe ya bude k'ofar toilet d'in,
ba tare daya bude idoba ya zare boxes dinma ya rege dashi sai fatar jikinshi,
a hankali ya bud'e ido jin motsin ruwa,
da sauri ya k'ara waro idonshi waje dan gani wata kekyawar budurwa mai cikar haiba,
matsota yayi da sauri yayinda ita kuwa take matsawa da baya-baya, har ta isa jikin ginin inda shima ya iso gareta,
ruwa na sauk'a a kansu,
mannan k'irjinshi yayi da nata tare da sauk'e wani nannauyan ajin zuciya, hannunshi yasa ya ruggumota,
ita kuwa sai kiciniyar kwace kanta takeyi, amman ina kasa,
juyoya yayi bayanta na manne a k'irjinshi cikin rawan jiki ya dora hannunshi kan k'irjinta a tare suka saki k'ara ita ihun tsorone shikuwa na jin dadin abinda bai taba samun ya gani bama bare ya tab'a,
murza k"irjinta ya farayi da sauri-sauri yayin Yusuf d'inshi ke harbawa kamar zataci babu,
zamewa budurwar tayi da niyan zata sunkuya ta gudu, amman sai hakan ya bashi damar matsota sai yake ganin kamar goho tayi mishi,. ai kuwa cikin rawan jiki ya matsota tare da ratsa birnin budurcinta,
wani irin ihu budurwar tayi tare da kururuwa da fadar wasu maganganu.

A firgice ya farka daga mummunan mafarkin nan da bai tab'a yin makamancishi bama,
"Wa iya zubilla suhanallah ya Allah ka tsareni."
ya rink'a fada,
ido ya zaro lokacin daya kai hannunshi ya shafi boxes d'inshi da yaji a d'an jik'e ,da sauri ya mik'e cikin rawar jiki ganin tabbas rlxng yayi abinda bai taba yiba duk da k'arfin sha'awarsa,
Ido ya rumtse da k'arfi yayinda zufa ke tsatstsafowa duk ta inda hudar gashi yake a jikinshi,
a zabure ya mik'e tare da bud'e idonshi da jin abinda budurwarnan ke gaya mishi,
da k'arfi yasa hannunshi duka biyu ya.......!





*By*
*GARKUWAR FULANI*
[01/01 9:13 PM] My 2nd Mtn: 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

*Page 2⃣3⃣*

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




Yatsunshi yasa cikin kunnenshi ya toshe da k'arfi,
tare da jujjuya kai cikin rawan jiki da tsananin firgita murya na rawa yake girguza kai tare da cewa.
"Kiyi hak'uri ki gafarce ni."
Sai ya kuma rumtse ido, lokaci d'aya kuma ya bud'esu tare da cusa kanshi cikin cinyoyinshi,
dan har yanzu in ya rufe idonshi ganin abin yakeyi kamar a majigi, ga sautin muryarta dake ratsa zuciyarsa har yanzu yana jin sautin kukanta da kalaman da take gaya mishi lokacin da yake kusantatarta a mafarkin.

Haka ya zauna cikin wannan yanayi har saida asubar fari ta gabato,
sannan ya samu bacci ya fara saceshi,
baccin 40 minit yayi mai cike da mafarkai kuma duk da waccar budurwar yadda take cikin halin wuyar abinda ya mata,
da kyer ya samu ya mik'e jiki duk a mace, wonko yayi da ruwan d'umi wai ko zai samu kuzarinshi ya dawo jikinshi amman sam abin yaci tura haka yayi wunin wannan ranar sukuku sai tarin bak'in cikin da yakeji.


Zaune suke cikin bedroom din Abba,
ita tana ninke yan k'ananun kayanshi data wonke mishi shi kuwa yana duba wasu takardune da ta rula duk hankakinshi a kansu yake,
dan haka ta barshi saida ya gama,
taga ya jawo cup ya zuba tea din data ajeyi mishi,
ganin haka yasa ta mik'e tare da karb'ar cup d'in ta k'arisa hada mishin,
sannan ta zauna gefenshi,
cikin kula ya maida hankalinshi gareta ganin alamun tana buk'atar lokacinshi,
ido ya tsura mata,
da sauri ta d'ago kanta jin alamun idanunshi na yawo a jikinta,
suna had'a ido ya d'aga mata girarshi duka biyu tare da cewa.
"Ya dai Maman Yusuf me kikeson gayawa Abban Yusuf ne?."
kallonshi tayi cikin sauri da tsananin mamaki a d'aya sashin zuciyarta kuwa farin cikine kamar ya kasheta,
dan tun da ya kori Yusuf bai sake kiranta da Maman Yusuf ba duk da dama can sai in yana cikin shauk'i yake mata irin wannan salon,
toh gashi yau kuma har yana kiran kanshi da Abban Yusuf,
lokaci d'aya taji mikin zuciyarta ya tashi ido ta lumshe tana jin hawaye masu zafi yana tsatstsafo mata,
gaba d'aya sai yanayinta ya sauya,
shi kuwa Abba ido ya lumshe tare da jawota jikinshi dan a zatonshi ko kunya taji dan sigar da yamata mgna dan sigace ta musamman a tsakaninsu,
itama tana jin ya jawota ta lafe a jikinshi tana mai cewa.
"Abban Yusuf."
"Na'am Maman Yusuf ya akayi ne?."
cikin tsananin farin cikin gani wani gagarumin sauyi ya samu tace.
"Sulaiman ya gaya maka cewa ya biya mana umrah nida Anty Amarya ko?."
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Hakk'un ya gaya min,
yace har ya gama muku komaima,
da zai hada da Umminshi to yace Aliyu ya hanashi sabida kar abar gidan ba kowa,
ya bari ita ya biya mata aikin hajji."
cikin jin dadi da tsarin da Sulaiman ya fitowa Abban,
ta yadda bazai gane Yusuf ne yake musu komaiba,
dan in ya sani zai hana.

"Eh haka dai nima yacemin."

"Toh kin gama shirinki kenan tunda yace min tafiyar saura kwana 5."

"Eh na gama yanzu kam ranar kawai muke jira."

kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan yaci gaba da cewa.
"Naso ace tare zamu tafi,
domin kin sani sam bana jurar kiyi nesa dani,
sai nayi ta faman azumi nake samun nitsuwa,
toh har nayi niyar zan biya kud'in mu tafi tare sai kuma aka turomin wani case daga Sokoto kuma murd'iya akaso yi shiyasa aka turoshi har nan,
to tafiyar dole ta kamani zuwa sokoton shiyasa kawai na hak'ura."
kai ta jinjina tare da cewa.
"Abban Yusuf baka sufa yaci ace yanzu dai kam ka samu canji a irin yanayin halittarka ta k'uruciya,
amman ina kai dai kullum kar ayi nesa da kai, mutun harda jikokinshi,
ai yanzu sai kabarwa yara."
Ido ya lumshe tare da cewa.
"Toh ya zanyi haka Allah yayini lafiyeyye."
ya k'arishe maganar cikin sigar jawota zuwa gareshi.


washe gari kuwa tana komawa bank'arenta ta samu Zahra tana ta kiciniya a kitchen,
da yake Anty Amarya ta bawa Zahra Maman Yusuf d'in ita keyi mata duk wani abinda y'a zatayiwa uwarta, tunda ita ga Mami na tayata, Ummi kuwa ga Nana da Zeenat,
tana shiga bedroom Zahra na biye da ita a baya,
bakin gado ta zauna ita kuwa Zahra konciya tayi gefenta tare da jawo wayar Maman tana wasa dashi,
"Goggon Abba kin gama mana breakfast din ne? kin san yau Jumma'a Abbanku zai fita da wuri."
gyara konciyarta tayi tare da lumshe ido cikin muryar shogob'a tace.
"Eh na gama Mama tun k'arfe hudufa na tashi."

kai ta jinjina tare da cewa.
"Sannu Goggon Abba dadina dake aiki baya baki tsoro, me kika dafa mana ne?."
da sauri tace.
"Doya da k'wai na soya

Please Login or Register in order to submit comment