Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 5⃣

*NA*

*AYSHA ALIYU GARKUWA*




🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



```WANNAN SHAFIN NAKUNE MASU HALIN KWARAI KUD'IN NA DABANNE A CIKIN WRITERS TABBAS KUNYI DACE DA TSARKAKEKKUN ZUK'ATA WANNAN RAHAMACE ALLAH YAYI MUKU,
TABBAS NI DAI INA KYAUTATA MUKU ZATON, KUD'IN ZUK'ATANKU BABU HA'INCI MUNAFURCI CIN AMANA ANNAMIMANCI K'ASHI HASADA KUSHE ZAMBA CIKIN AMINCI GULMA DUK ALLAH YA TSAREKU NIKAM AYSHA ALIYU GARKUWA DA FARAR ANIYA NAKE KALLONKU Safiyya Abdullahi musa Huguma Batool Jottko```






Ya rumtse idanun shi dan hayaniyar da yaji iyayenshi nayi,
So yake ya juya ya fice daga gidan Amman ya kasa d'aga k'afarsa,
yunk'uri yayi dan d'ago hannayenshi dan yasa yatsunshi ya toshe kunnen shi amman hakan ya gagareshi,
k'ara rumtse idonshi yayi da k'arfi jin masifar da Abba keyi Mama kuma na kuka k'asa-k'asa tana kuma bashi amsa
sunata fad'i in fad'a,
cikin tsawa Abba ke magana.
"Ina gaya miki in ina magana ki dena bani amsa,
in har bazaki iya bani hak'uri ba."

Ido ya d'an bud'e jin maganar Maman shi.

"Eh ai in dai kana son dukana ko ya nayi sai ka dakeni,
ya rigada Ka saba,
kai zaka ajiye takardun ka
in kazo ka nema baka ganiba sai kahau kaina kayita min fad'a
kuma ba ajiyarsu ka baniba."

a hatsale yace.
"Eh ban baki ajiyar sun ba,
amman a d'akin nan na ajiyesu,
kuma dagani sai kene a cikin d'akin,
in banda rashin tattali ai ko watsar dasu nayi zaki tattara min,
waddan nan takardu ne masu mahimmanci ne,
domin na shariya ne akan *Fyade* kuma duk hujjojin suna ciki,
dan haka nemomin su."

Mik'ewa tayi zata fice daga d'akin,
shiko Abba sai jawota yayi ya turata kan kujera,
sannan yace.
"Ba inda zaki fita sai kin nemomin su."
dole a haka ta tashi ta fara neman ajiyar da ba ita tayishi ba,
abin mamaki kuwa ashe a k'asan sallayan da Abba ke nafila a kai a nan ya ajeye takardun,
tana mik'amai tace.
"Ba gashi a wurinda kake nafila ka ajiyesu ba."
hannu yasa ya karb'a tare da cewa.
"Toh ai ban gansu bane."

Yana karba yafito,

shiko Yusuf har yanzu yana tsaye yana jin duk yadda sukayi,
Abban na fitowa yayi sauri ya d'an rusuna tare da cewa.

"Abba ina kwana."

"lafiya lau Yusuf, baka tafi bane har yanzu?
ko ka fasa zuwan ne? ."

"Eh yanzu zan tafi."

"toh zomuje in sauk'eka tunda nima yanzu zan shiga cikin Yola".

"To Abba bari in sallami Mama."

daga nan yayi cikin parlour,
shiko Abba yayi woje.

Yana shiga ya sameta a zaune tana b'are Parasitamol da rili extra zata sha,
gefen ta ya zauna cikin sanyin murya yace.
"Mama baki da lafiya ko?."
murmushin k'arfin hali tayi dan ji take kanta kamar zai tsage,
cikin kulawa tace.
"kayya kainane ke d'an ciwo."

"Toh shirya mu tafi asibiti,
tunda yanzu zamuyi cikin Jimeta."

"a a da sauk'ifa kuje kawai."

mik'ewa yayi yana kallonta jin Abba na dannamai hon,
fita yayi tare da cewa.

"Na tafi."

"Allah kiyaye hanya ka gaida min Aryan da Kakarsa. "

"zasuji. ".


A cikin mota shiru yayi yana tunanin irin halin da mahaifiyar shi take ciki da zaman wahala da take da mahaifin shi har suka iso inda Abba zai ajiye shi baisan sun karaso ba har sai da Abba yayi mishi magana firgigit yayi, amma da yake kan Abba ya dauki zafi akan shari'ar da sukeyi a kotun nashi bai wani damu da halin da yaron nashi yake ciki ba shidai burin shi ya isa kotu inhar maganar fyaden nan ta tabbata ya yankewa wanda ya aikata hukunci dai-dai da abinda yayi, haka Yusuf ya fita a motar jiki a sanyaye yana mai yiwa mahaifin nashi fatan sauka lafiy, har saida motar mahaifin nashi ta kule sannan ya gangara ya shiga layin gidansu Aryan.

Saida suka gaisa da mai gadin gdansu Aryan sannan ya shige ciki asalin gdan,asalin mai gadin sune da yake musu gadi tun iyayen su Aryan suna raye, katon gdane na gaske mai dauke da wajen parking din motoci da akallah zaici motoci kamar guda hudu kuma su sakata su wala wata bata matsi wata ba, daga can gefen bangaren hannun hagu wani katon daki ne na dawakai, dokuna ne a ciki guda hudu manya lafiyayyu sai harbin iska suke, sai shikokin fulawoyi da suka dadawa gidan kyau, wata katuwar kofa ce da zata sadaka da dukanin bangarorin gidan amma akwai wani corridor dazai sadaka da bangaren mata kawai duk da akwai kofar da zata sadaka da bangaren matan inka shiga kofar farkon.



Knocking yayi Aryan da tun dazu banda duba agogo dajan tsaki da yake ganin tun 10:00am sukayi da Yusuf zaizo amma har 12:00om bai karaso ba ya saka shi mikewa yaje ya bude ganin Yusuf ne cikin murna ya bugi kafadar shi irinta abokan da suka yadda da juna murmushi Yusuf din yayi amma dai da gani kasan na yake ne karasa shiga ciki sukayi,katon parlour ne mai dauke da manya-manyan kujeru hadi dasu electrics dasu AC da fridge da duk wani kayan kawa dake kawata parlour akwai kofofi guda 2 a cikin parlour daya wadda zata sadaka da asalin main part na cikin gdan dayar kofar kuwa bedroom ne.


Zama yayi akan kujera 2 seater hadi da balle boturan gaban rigar shi a sannu yake sauke numfashi a hankali Aryan ne ya kawo mishi ruwa da lemo akan try da karamin cup zama yayi kusa da Yusuf hadi da dafa kafadar shi a hankali Yusuf ya bude idanuwan shi kai Aryan ya girgiza yace "har yaushe ne zaka dauke ni dan uwa da zamuna tattauna matsalar mune a duk lokacin dana fahimci kana cikin damuwa na tambaye ka sai kace babu komai why? Ko matsayin dana dauke ka akwai banbanci da yadda ka dauke ni ne?"


Murmushin karfin hali Yusuf yayi tom ta ina zai fara abin kunya da takaici yace mahaifin shi na dukan Maman shi ina bazai iya ba sai shima ya dafa kafadar Aryan yace.
"Yadda kasan Sulaiman haka na dauke ka Aryan babu wata damuwa dazan boye maka yauna tashi da matsanancin ciwon cikine kasan ina fama dashi kusan shekara biyu kenan tom shine ya tasarmin yau shiyasa kajini shiru banma yi niyyar zuwa ba amma ganin ina tayi maka alkawarin zanzo na kasa zuwa ya saka nazo yanzu ma Abba ne ya sauke ni ka yadda dani Abokina".
ya wani kafeshi da ido yanaso ya tabbatar ya yarda din dariya Aryan yayi yace "Ohoho abokina kawai kace kai din dai sai a hankali inaga kawai aure zamuyi maka tun wuri...... " hadi da kyalkyalewa da dariyar shakiyan ci dukan wasa Yusuf yakai mishi a kafada yace "karasa mana" murmushi Aryan yayi tare da cewa.
"Ko dai aure kake son a maka, in aure kakeso ka gaya min tun wuri in aurar da kai."
Dariya sukayi baki d'ayan su, haka dai Yusuf ya saka sukayu ta hira da Aryan bawai dan damuwar dake cin ranshi ta tafi ba a'ah sai don son ya cire shakku acikin ran Abokin nashi.



Har time d'in sallar azahar yayi sukayi alwala sukaje masallaci sukayi sallah saida suka dawo daga masallaci. Kai tsaye suka shiga part din granny, watako kakar su Aryan suka gaishe ta ta amsa suka taba barkwanci Rayhana k'anwar Aryan ta gaida Yusuf a nutse babu rawar kai babu hargagi irinna Zahrah a tattare da ita a cikin ran Yusuf saida ya tuna da Zahrah a ranshi yace.
"Allah ka nutsar da Zahrah kamar sauran yara Ameen."



Saida sukaci abinci suka koma part din Aryan kana suka taba karatu sannan sukaci gaba da hira, wunin yau gaba daya Yusuf a gidansu Aryan yayi shi Aryan kuma yaji dadi sosai, wajen 5:00pm Yusuf ya kalli Aryan yace "Abokina ni zan wuce gida".
da mamaki Aryan ya kalleshi yace.
"Aina zata yau zamu hau doki muje kayi sukuwa kasan gasar nan da zakuyi sai da practicing, fatana ka zama cikin nasara kamar kullum, bare wannan karon harda mai Martaba zai halacci taron gasar fa."
kai Yusuf ya shafa yace.
"Ka bari abokina yau banajin dadi, marana tana matsamin sosai,ka bari idan na dawo sai muyi."
"OK" Aryan yace sannan ya tashi sai da suka je Yusuf yayiwa granny sallama Aryan ya rakoshi bakin titi ta gefen round about mai doki, ta gefen PZ, sannan suka tsallako gefen titin by past yahau taxi da zai nufi geere.

Tafiyar yan dak'ik'u sukayi suka, isa,
a bakin layin gidansu ya sauk'a sannan ya gaggara titin dazai kaishi gida.

Daga nesa yake jiyo sautin kid'e-kid'en da idi ke sawa kullum yamma da safiya, tsaki yaja tare da kauda kanshi ya rumtse idanshi, bakin gate d'in gidansu ya nufa tare da tura k'aramar k'ofar ya kutsa kanshi cikin gidan,
Ita kuwa Zahra a guje ta nufo bakin gate d'in dan sautin kid'in da taji idin ya saka, gudun da takeyi yasa sam bata lura da shiba, shi kuwa idonshi a rufe, dan gaba d'aya baijin dad'in yanayi,
yana sa jiki cikin gidan ita kuma tana kutso kai a guje, karo sukaci yayinda kanta ya bugi dai-dai kan mararsa da ke azalzalarsa da ciwo, ba zato ba tsammani yaji wani irin azaba da rad'ad'i ido ya rumtse da k'arfi tare da sa hannu ya damk'i marartasa, dan ji yayi kamar dutse aka kima mishi, zuface ta ketomai tako ina, idon ya bud'e da sauri cikin azabtuwa dan jin wani irin...!




By
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*HUKUNCIN ALLAH*

page 6⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*Assalamu alaikum, masoya na masoyan littafaina, ina mik'a sak'on gaisuwata a gareku tare dayi muku Al'bishir d'in gani na dawo gareku da sabon littafina mai suna HUKUNCIN ALLAH, wanda na shiga Nazari tunani bincike hangen nesa na zak'ulo matsalolinmu a yau tare da kuma samo Garkuwar da zata tsira damu da yaranmu k'annenmu daga fad'awa halin dana sani,*
*HUKUNCIN ALLAH*
littafine dake tafe da sak'onni masu tarin yawa. *tuna sarwa, tsorotarwa, jan hankali, fadakarwa, tare da zaburarwa da bada k'arfin guiwa da zamu had'u mu yak'i k'alubalen dake addabar al'ummar mutanen wannan k'arni da muke ciki. sannan akwai nishad'antawa tare da ban dariya hakan kuma* kunsan salo nane ban tausayi mai ratsa zuciyar ma abocin imani da tausayi, duk suna cikin wannan littafinawa mai suna *HUKUNCIN ALLAH,* domin samun damar karantashi zaku iya bibiyata a manhajar what's App a number wayata kamar haka 09097853276 kan farashi mai sauk'i yi register da naira d'ari biyu kacal damin samun damar karantashi daga forko har k'arshe littafin *HUKUNCIN ALLAH* ko katin waya na layin MTN wanda za'a turo shi ta wannan number 09097853276 ko tur'a d'ari biyun ta asusuna na 0005388578 JAIZ BANK AISHA ALIYU GARKUWA,
kada ka/ki manta turo min shaidarki na tura kud'in a dai wannan number 09097853276 ina maraba daku masoyana tare da kuma yi muku al'bishir da yin posting a kai a kai kada ka/ki sake a baki labari, sai kunzo.......!!!

Dan Allah banda kira
*HUKUNCIN ALLAH


Free page








Kallonta yayi da idanuwansa da suka rine sukayi jajawur lokaci daya dan azabar dake ratsashi har cikin k'ahon zuciyarsa,
ita kuwa Zahra da hanzari tayi baya tana tsitstsillah idanu, tabbas wannan abin da Zarah tayi mishi dabadan gaba daya karfin shi da kuzarin shi sun gudu ba to da babu abinda zai hanashi babballata a wajennan.



Wani irin damk'a marar tashi tayi masa ritse ido yayi hadi dabin bango ya fara tafiya a sunkuye hannunsa d'aya dafe da marar shi daya hannun dafe da bango.



Ita kuwa Zarah ganin haka saita kyalkyale da dariyan dadi dayi mishi gwalo, ta fita waje a guje dan sosai kidan gurin Idi mai chaji ke tsumata.



Haka ya karasa part din Aunty Amarya a daddafe kan doguwar kujera ya karasa ya kwanta yana murkususu dan jinshi yake tamkar zai mutu saboda azaba da radadin da mararshi take masa, dan ba karamin buga mishi katon kanta Zarah tayi ba, yana cikin halinnan Aunty Amarya tazo ta taddashi nanta rikice da tambayar shi.
"Yusuf lafiya Kuwa?".
kai ya rink'a juyawa tare da rumtse idonshi, Zeenat dake gefeshi ya kalla cikin rawan murya dakyar ya hado kalmomi ya yace mata.
"Kije shagon Idi ki cewa Zahra maza ta dawo".
K'ara matsoshi Anty Amarya tayi tare da cewa.
"Ana maganar lafiyarka kana batun shirmen Zahra, meke damunka? ka gaya min ko in in kira Daddynku mu tafi hospital yanzu."
cikin rumtse ido yace.
"Maaaa-raaaa-taah". shima dan ganin yadda ta tada hankalin tane dan sosai suke shiri da Aunty Amarya, ita kam da hanzari tajuya ta shiga kitchen ta zuba ruwan Lipton a cup ta matsa lemon tsami da yawa, fitowa tayi da sauri ta kamashi ta dago kanshi, saboda zuwa lokacin jikin shi har rawa yakeyi, a sannu ta saka mishi cup din a baki ya farashan tea din a hankali yasha da yawa sannan ya ture hannunta.
Yana gama shan tea din yaji marar shi tayi wani irin kullewa zabura yayi gami da damke marar ya rumtse ido tare da cije lips enshi, a sannu yaji wani sanyi da sauki lokaci daya ya nemi ciwon ya rasa tamkar an zare gashi daga cikin nono gumi ne ya fara karyo mishi tako ina a sannu ya koma ya kwanta yana sauke numfashi, yana jin damshi a jikin cinyoyinshi, ido ya lumshe dan sai yaji kunya ta rufeshi, gani yaje kamar Aunty Amarya tasan abinda ke sashi ciwon da kuma abinda yaji na fita daga jikinshi.
ita kuwa Anty Amarya in banda sannu babu abinda take jera mishi,
zumbur ya mike tamkar wanda aka aka mintsina da sauri Aunty Amarya tace.
"Menene, Yusuf lafiya kuwa?"
Ina ko sauraronta baiyi ba ko takalmi babu a kafarshi da gudu-gudu sauri-sauri yayi waje Aunty Amarya na binshi a baya dan ita ta dauka wani abinne ko ciwon ne ya gigitashi.



Tun daga nesa ya hangota tana kada kugu da siket dinta tayani tsalle duk inda ta juya yana bita bata damuwa sai dirkar rawa take gun-gun samarin dake zaune kan benci kofar shagon idi mai caji kuwa sai ihu suke suna dada zaburar ta.
Yana isa kunnenta yaja,
ita Kuwa jin anja kunnenta kiiiii, a firgice tayi baya k'ara ta kwallah tana.
"Ayyo kunne a ciye sh............" ganin Yusuf ne ya janyota saita had'iye ragowar maganar bakin ta, hadi da kifkifta idanu,
Yusuf kuwa wani mugun kallo ya jefi gun-gun samarin irinna ku shiga taitayin ku suka juya shida zarah sukayi gida hannun shi rike da kunnenta yanayi yana murza mata shi ita kuma saita saka tsalle kan sukai gida har tayi fitsari a wando fuskarta duk ruwan hawaye da majina.




Aunty Amarya data ganshi rike da kunnen zarah dariya tayi tace.
"Oh ni Maryam wataran dai Yusuf saika cire kunnen zarah zakaji dadi ko? ni kuwa haka zanta maka ajiyarta da cirarren kunne sai dai kaika aureta, dan babu wanda za'a bawa ita da kunne daya yanayi mata gori".
Siririn tsaki yaja hadi da sakin kunnen Zarah yayi cikin gida fuuuuu.



Zarah kuwa da gudu taje ta rungume Aunty Amarya kukan da bata samu damar yiba sai yanxu take baje kolinsa tuni ta fito da matan gidan Mama da Hajja Inna Mommy saboda kukan Zarah shegen kara gareshi kamar jiniya data baci, tambayar meya faru sukayi nan Aunty Amarya tace.
"Inaga kofar shagon Idi mai chaji Yusuf ya ganota tana sana'ar tata, dan wanka nake shirin mata tanajin ya saki kida ta fito a guje".
ta karashe maganar da dariya alamun abin baya damunta tsaki Hajja inna tayi tace.
"Kai wannan yaro anyi tantiri tak'adiri duk ya maida mana unguwa kamar wani gidan gala yana shirin maida min jika iyalin dujal".
harara ta bankawa Zarah ta koma bangaren ta, Mommy uwar gidan Anty Amarya kenan karasawa tayi ta dafa kafadar Aunty Amarya tace "Wlh Auntyn su gata Yusuf yakewa Zarah ba zaki gane illar sangarcin da kike mata ba sai nan gaba shi duk wani gata da zaka yiwa danka inba na ilimi bane shirme ne" daukar Zahrah Aunty Amarya tayi hadi da dariya tace.
"kai Mommy kuruciya cefa wataran da kudi akace zarah tayi ba zatayi ba".
hadi da kallon zarah tace.
"ko Tinana na".
dariya Zarah tayi hadi da gyada kai dan bata gane me Auntyn take cewa ba,
ita kuwa Maman Yusuf kanta ta girgiza a ranta tana fatan Aunty Amarya ta gane tun kafin duniya ta ganar da ita itama ta juya ta tafi part dinta.




Aunty Amarya ma part dinta suka shiga dakyar da wayo da dabara ta samu tayiwa zarah wanka anayi tana zillewa a haka dai aka gama.



Yusuf kuwa cikin kunar zuci ya k'arasa d'akin sa da yake part din Kaka amma shi a upstairs dakinshi yake kullum burinshi k'annenshi su zamo nagari abin koyi ga kowa amma ina a komai sai an fidda zakka ga Zarah nan da tata kalar kuruciyar,
ya yarda da kuruciya amma yana tsoro saboda ance icce tun yana d'anye ake tankwara shi kada ya barta yanxu yana ganin yarinya ce saita girma kuma ta gagaresu a haka yana tunanin yadda zaiyi da Idi mai chaji ya cire kayansa ya shiga toilet dan yayi wanka ya tsarkake jikin shi.



Washe gari tsaye yake a bakin k'ofar Aunty Amarya 7:45am yana muzurai Zarah da ake sakawa socks sai matsar hawaye take dan ita a rayuwarta in anaso a kuntata mata a takura rayuwarta ace taje makaranta yau kuma gashi Hamma Yusuf da kanshi yazo yace a shiryata shine zai kaita makarantar da kanshi, haka aka gama shiryata da sauran yaran suka dauki launching box dinsu suka yiwa Aunty Amarya sallama suka tafi,
suna tafiya yau Zarah babu halin tsokana ko taki tafiya tace saisun goyata su kuwa duk dadi ya cikasu,
har cikin class ya rakasu sannan ya cewa
"Aunty dinsu dan Allah yau ko fitsari in Zarah ta tambaya a hadata da wani suje su dawo dan guduwa take".
tace "toh" sannan ya tafi.



Da aka tashi ma Yusuf shi yazo ya koma dasu gida saboda sun fara shirye2 fara WAEC yanxu ba kullum suke zuwa school ba, kuma yau a zaman da yayi a gida ya fita ya binciko wata islamiyya can nesa da gidansu dan sai an hau napep ko mota ma dan zaiyi tafiyar 25 to 30 minutes tsakanin suda makarantar 3:00pm ake shiga a taso 6:30pm nan yayi niyyar yakai zarah ya kwammace in bayanan ya saka a dauko masa ita gwanda ta daina wunin gidan gaba daya.



Hakance kuwa ta kasance 2:15pm suka dawo daga school da kanshi ya shigo ya cewa Aunty Amarya tayi mata wanka yana tsaye akayi mata wankan bayan an shiryata har Aunty Amarya ta dauko mata kayanta na sawa vest da siket dinta tayani tsalle saboda zafi da ake fama dashi saboda gabatowar damuna amma har yanxu ruwan bai sakko ba yace.
"Aunty Amarya ki saka mata kayan mutunci islamiyya zan kaita fa".
kuka Zarah zata saka Yusuf ya zare mata idanu Aunty Amarya kuwa dariya tayi dan ita tanada kawaici da kara koda zaka dakar mata yaronta a gabanta ba zata daga ido ta kalleka ba balle tayi magana, bayan ta gama saka mata kayan da kanshi ya bata abinci tayi tana gamawa ya saka mata hijab ya rike hannunta suka fita a gidan,
napep sukaje suka hau dama yaje yayi mata registration duk ya biya kudin komai interview akayi mata amma Zarah bata iya komai ba saboda yadda take gudun makarantar allon in an kaita, dama makarantar tahfiz ce daga dan shekara 3 suke fara daukar yara zarah kuma yanxu tana shekarunta sun zarta haka ta nan suka kaita aji biyu Yusuf yayi signing akan shine zaina zuwa daukarta in an tashi in kuma ba zaizo ba zaiyi waya ya fadi wanda zai dauko ta yayiwa head master sallama ya tafi.





Tun 6:00pm Yusuf yana cikin islamiyyar su Zarah har aka tashi yara ita ta fara fitowa daga aji a guje ganin Yusuf saita dan nutsu ta karaso tanata washe baki nan ta fara bashi labari "Hamma Yushuf Malam ayi mana kayatu shoshe, ayifun ta'un jimun Alhamdu lillahi labbli alamin" cikin farin ciki Yusuf ya dauke ta ya daurata akan cinya rabon da Yusuf yayiwa Zarah wannan daukar harya manta cikin sakin fuska yaja kumatun ta yace "Yauwa kanwata kinga kin fara zama good girl ko kiyi karatu sosai kinji".
dariya ta kyalkyale da ita tace "yauwa Hamma Yushuf inna jama gud jel jaka shiyamin alawa ko?".
Murmushi yayi hadi da sauke ta ya mike hannu ya saka ya d'auke ta yace.
"Eh in kika iya karatu kika zama good girl babu rawa babu tsokana da rashin ji har Baby zan siya miki".
cikin zumud'i tace.
"Hamma Yucuf baby mai gashi zaka sayamin ko sai in mata kitso."
"eh." yace mata a tak'aice
murna tayi-tayi har suka karasa titi suka sami napep ya kaisu gida.



Yaufa duk wanda ya shigo part dinsu sai Zarah ta biya mishi karatun da aka mata,
d'ad'i sosai Aunty Amarya taji har part din Ummi da Mama da Hajja Inna sai da Zarah taje ta biya musu karatun data koyo duk da batayi dai-dai amma sunji dadi haka Daddy da Abba ma da suka dawo saida Zarah ta biya musu karatun, Daddy kam yaji dad'in abin sosai, cewa yake.
" iyeh Goggon Daddy ta girma".

Tun daga ranar Zarah ta daina wunin gida dan tana dawowa daga boko Yusuf zai dauketa ya kaita Islamiyya in kuma bayanan zai barwa Aunty Amarya sallahu yace in Sulaiman ya dawo yaje ya dauko ta, har zuwa lokacin da suka fara rubuta exam dinsu ta WAEC.


Idi mai chaji kuwa tun yana zuba idon ganin Zarah dan har tambayar yaran gidansu yake in zasu wuce makarantar Allo sai suce Hamma Yusuf ya kaita Islamiyya kullum zuba ido yake yaganta amma babu hali dan ya kulla

Please Login or Register in order to submit comment