Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

azabar da takeji tace.
"Innalillahi'wa'illaihiraji'un Hamma Yusuf zan mutu wayyo Hamma na zan mutu."
sai ta kuma yarfa hannu tare da tashi zaune kana ta fuskanci inda yake sai ta kuma komawa baya kad'an ta jingina da allon gadon,
ido ya zaro ganin ta bud'e mishi jikinta, irin yadda bata tab'a yiba,
cikin wahala ta rumtse idonta tare da yin nishi mai k'arfi kana cikin d'aga sauti tace.
"Hamma Yusuf ka duba yana fitowa ne?."
cikin tsoro da daburcewa yace.
"waye d'in a ina zai fito?."
nishi ta kumayi tare da cewa.
"Waye kuma banda d'anka da ka lik'amin yake neman kasheni,
kasa hannu ka fito min dashi."
Kan jarfa aiki ja a gaban Yusuf,
gaba d'aya jikinshi b'ari yakeyi tamkar mazari,
ido ya zazzaro ganin yaro ya danno kai.
da sauri ya matso tare dasa hannunshi gabanta cikin rashin sanin madafar da zai dafa kawai sai yace.
"Kiyi nishi yi nishi."
kai ta juya tare da rumtse ido zufa mai azabar k'arfi ta kayo mota,
zamewa tayi ta konta a rigingine kana ta matso gabanshi cikin k'arfi ta rink'a nishi a jere-a jere
wuk'i-wuk'i Yusuf yayi da idanunshi lokacin da ta daddage ta yarfa mishi mari tare da danno nishi sai ga k'atuwar jaririya fara k'al ta fad'o gabanshi,
babu jini ko d'igo,
ita kam Zahra meda kai tayi ta konta cikin sauk'e nannauyan numfashi,
shi kuwa Yusuf cikin tsananin farin cikin da bai tab'a shigaba a rayuwarshi ta duniya yasa hannunshi ya tallabo jaririyar,
tare da ruggumeta a k'irjinshi jikin farar jallabiyar nan tare da cewa.
"Alhamdulillah ya Allah na gode maka da wannan kyauta da yayi min Zahra Allah ya miki albarka Ngd Ngd matuka my dear sister Allah ya miki al'barka Zahra na kin haifo mana Yusranmu."
dai-dai lokacin Mama kuwa ta iso,
dan akwai tazara tsakanin part nasu danasu Zahra d'in.
ganin Zahra na konce haihuwar uwarta ga zariyar cibiya manne da jikinta,
ga Yusuf kuwa ruggume da jaririyar da sai tsala ihu takeyi.
"Inyahh-inyahhhh inyararai inyararai."
cikin rawan jiki ta k'arisa gunsu ita kuwa Zahra sai tayi maza ta had'e cinyoyinta kana ta kalli Hamma Yusuf d'in cikin had'e rai tace.
"Oga ka jamin rigata."
da sauri ya mik'a Mama yarinyar tare da cewa.
"Mama karb'eta dan naga haushinmu takeji."
cikin dariya da tsananin jin dad'i Mama ta amshi yarinyar tare da mannata da cikin Zahra kana tace.
"Ikon Allah Goggon Abba kin yi irin haihuwar Hajja inna ita ke bamu lbrin ita haihuwar kule takeyi babu jini ko ruwa kinga 'yayanta basu gadota ba sai ke Jakarta."
sai ta kuma kalli Yusuf cikin tsananin jin dad'i tace.
"To ai dole taji haushinku kaida d'iyarka mai tsamin murya,
kun sata wahala,
sai ta kuma jawo d'an kwalin Zahra ta rufe mata jikinta kana tace.
"Toh ai mabiyiya bata fad'oba yanzu tashi zakiyi ki zauna ko Goggon Abba."
"toh". tace kana ta mik'awa Yusuf hannu tace.
"Tadani."
to yace tare da kashe mata ido ganin hararanshi takeyi.

To fa ana wata sai ga wata yana ajiyeta zaune sai ga wani sabon nak'uda,
damk'eshi tayi da tsananin k'arfi jin k'ugunta yana rabka da k'arfi k'ad-k'ad takeji yana sarawa,
cikin firgici tace.
"Wayyo Allah na Hamma Yusuf ciwon ya dawo."
sai ta kumayi maza ta ture jaririyar dake kan ruwan cikinta tare da zaburowa da k'arfi jiki na rawa murya a hard'e tace.
"Mama k'uguna cinyoyina Mama bayana sarawa yake zai b'alle sai ta kuma damk'o wuyan Hamma Yusuf d'in cikin karkarwa tace.
"Ciro min shi ciro yayanka da basu da adadi a jikina mugu kawai ka cuceni ka had'ani da wahala Allah ya isana."
cikin sauri Mama tace.
"Zahra ki nitsu karki tsinka cibiyar yarinyar."
cikin kuka tace.
"Mama wallahi wannan ma nak'uda ne ai shi ya sani yara biyu ne ko gomane na ya d'irka min waya sani."
dariya ce sosai ta kama Yusuf a wani sashi na zuciyarshi kuwa tausayinta ne fal zuciyarshi.
hannu ta yarfa tare da taune lips enta kana ta barbarza gashin kanta cikin rawan murya tace.
"Ka duba ka fito min dashi karya kasheni."
dariyar da yake dannewa ne ta d'an kubce mishi,
ai kuwa Zahra na ganin haka tayi sauri ta rarumo wuyanshi.
cikin tausayinta da dariya yace.
"Maman Yusuf kina tsaye zata kashe miki Yusuf d'inki da jikokinki ko?."
ita dai Mama Yusuf janye jaririyar tayi gudun kar Zahra ta danneta,
shi kuwa Yusuf ido ya zaro jin shak'arshifa tayi da gaske,
yasa hannu zai bambaro hannunta kenan sai ya kuma ji ta saki wuyanshi ta ruggumeshi shi yana zaune ita kuma tana durk'ushe,
nishi ta farayi da azaban k'arfi tanayi tana fizgar mgna kunsan matsiwaci in yayi ciwo,
cikin mutuwar baki take cewa.
"Hamma Yusuf k'arfina ya k'are."
wannan furuci yasa Yusuf firgici janyeta yayi ya kontar da ita kana ya bud'a k'afafunta ya waresu,
ita kuwa Mama baya ta basu,
shi kuwa Yusuf cikin zubda zazzafan hawaye yace.
"Daure kiyi nishi gashi ya kawo kai."
cikin tattaro dukkan sauran k'arfinta ta yunk'uro tare da kai mishi wawura a wuya kana tayi nishi da tsananin k'arfi saiga santalelen jariri fari k'al ya fad'o yana cillara kuka.
cikin tsananin jin dad'i ya d'ago yaro tare da cewa.
"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Allah Ngd matuka rabbi mai kyauta da k'ari."
sai ya kuma kalleta dan har yanzu tana cakume da wuyan rigarshi cikin sanyi yace.
"Madam a sake min wuyana haka mana, ai naga zahiri kin iya ressilin nausukan da kika shayar dani haka kuma sai kin k'ara da shak'eni."
cikin jin kunya ta sakeshi tare da cewa.
"Yanzu kam sun kare ko?."
dariya yayi tare da cewa.
"LA LA ni ban saniba dan banyiwa Allah shisshigi cikin lamarinshi ba,
kinga ke zan tambaya koda saura?."
kai ta kauda cikin maida numfashi ta kalli Mama dake cike da farin ciki tace.
"Mama sun k'are ko?."
gyad'a kai Mama tayi tare da cewa.
"Ina ga sun k'are tunda gama mabiyiyarsu ta fad'o,
kai Yusuf maza kaita bathroom ka ajiyeta kan toilet dan ba mmki jinin ya fara zubowa yanzu."
to yace kana ya d'agata cid'ak ya nufi bathroom yana shiga ya ajiyeta kan toilet.

Ita kuwa Maman Iya shatu ta kira tace tazo part d'in Yusuf da reza da lalle.

Ba jimawa tazo nan suka yanke cibiyar yaran kana suka shafe jikin jariran da lalle sannan suka nad'e macen cikin d'an kwalin Zahra na mijin kuma cikin jallabiyar da Yusuf ya cire lokacin da Zahra tazo.
daga nan suka tattara mabiyiyar suka gyara musu shimfid'an gadon da zara ta birkitashi amman babu jini ko ruwa ko d'igo sai d'an aman da tayi kuma shima a jikin Yusuf d'in tayi, saida suka kimtsa gadon
kana suka tafi part d'in Maman Yusuf da yaran


Shi kuwa Yusuf a bathroom ruwan d'umi ya had'a mata kana ya kamo hannunta ya taimaka mata ta taso.
Ido ya zaro ganin......!





By
*GARKUWAR FULANI*
[20/02 7:36 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 30*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



Da sauri ya k'ara jawota jikinshi tare da ruggumeta da kyau,
kana ya rumtse idanun shi sabisa ganin jinin da ta zubda ya bashi tsoro.
Lafewa tayi a jikinshi cikin maida numfashin gajiya da d'an rad'ad'in dake addabarta sabida ratsowar yara har biyu,
cikin kad'uwa da tsananin tausayinta sabida tabbas yaga zallar wahalar da tasha kana ga wani jini da yaga ta zubda wanda shi a zatonshi in shine ya rasa wannan jinin ai macewa zaiyi,
Cikin tsantsar kulawa ya sunkuyo kanta tare da tallab'eta ya ajiyeta cikin bath tub d'in ruwan d'umin da ya had'a mata. Ita kam Zahra rumtse ido tayi da k'arfi kana rik'o hannunshi tare da kallonshi cikin rauni murya a sanyaye tace.
"Wach Allah na Hamma Yusuf zafee."
gaba d'aya ta karya mishi zuciya tausayinta da rauni ya rufemishi zuciya da dukkan sasan jikinshi,
ji yake girma da darajar iyaye mata ya k'aru a idanunshi yayinda tausayin k'anne da 'yaya mata ya rufeshi,
a ranshi yake kitsima shin duk matar data haihu dama haka take fuskantar azabawa hawala zafi k'una suka kana da k'etare tsirad'i tabbas ya yarda da mgnar mutane da ake cewa duk mai ciki k'afa d'aya na duniya d'aya na lahira ne,
wasu zafafan hawayene suka fara tsastsafo mishi cikin diddigin jijiyoyin ida nunshi yana jin tausayin Mamanshi da k'aunarta da jink'anta na ratsa dukkan jini da jijiyoyin jikinshi.
jin Zahra ta kuma rik'o hannunshi tare da manna kanta bisa cinyarshi dan shi yana zaunene bakin bath tub d'in.
ina zuwa yanzu ya kasa danne hawayenshi,
haka yasa ya zame ya tsuguna ta wojen bath d'in kana ita tanata ciki,
hannunshi yasa ya tallabo kanta cikin tsananin tausayawa murya na rawa hawaye na kwaranyowa a fuskarshi yace.
"Am so sorry My dear sis bansan irin wannan azaba mata ke shaba,
da bazanyi tunanin na fiki son Aryan ba,
da da hali da na karb'a miki zafin jikinki."
sai ya kuma manne goshinshi da nata still hawaye na zubo mishi,
murmushin k'arfin hali tayi kana girgiza mishi kai murya a hankali tace.
"Hamma Yusuf hawayen kuma na menene?."
cikin rawan murya yace.
"Zahra duk fa mai imani dole ya tausawaya mace in har yasan irin wannan wahalar kuke sha yayin haihuwa,
toh ni ya zanyi in hana zuciyata tausayawa miki ya zanyi in hana idanuna zubda hawayen da tausayinki ne ya samar dashi."
dolefa Zahra ta aro jarumta ta koma a Zahranta mai dauriya sabida taga zuciyar d'an uwanta mijinta kuma ta kareya sosai,
ko rasuwar Aryan bataga Hamma Yusuf yayi irin wannan kukanba.
janye kanta tayi daga nashi cikin k'arfin hali tace.
"Abban Yusrah yaufa ranar farin cikine ba kuka ba,
taimaka min inyi wonka muje inyi kolliya in kafa d'auri in ruggume yaranmu suji d'umin Amminsu."
lips inshi ya taune dan yafa lura dauriya takeyi,
so ganin akwai gajiya tare da itane yasashi mik'ewa.
sosai ya taimaka mata tayi wonka kana,
ta d'auro towel suka fito.
A bakin gado ya ajiyeta kana ya nufi side d'inta da sauri,
doguwar rigar atamfa ya d'auko mata tare da bra and pant kana ya had'a da pand kunsan ita Zahra dama in tanada ciki take jini.

Sauri-sauri ya dawo shida kanshi ya manna mata audugar a jikin pant d'in kana ya saka mata shi sannan ya mak'ala mata bra d'in kana ya zira mata rigar tare da janye towel d'in cikin mmki ya kalleta ganin har towel d'in ya fara b'aci a hankali yace.
"Mu tafi asibiti a dubaki."
cikin sanyi tace.
"No Hamma ba komai fa."
da sauri yace.
"Ya zaki cemin ba komai bayan kinata zubda jini kin san ba abinda ke saurin d'auke mutun kamar rashin jini."
cikin lumshe ido tace.
"Toh Hamma tsoro kake kar ka rasani ne?."
da sauri yace.
"Sosai ma kuwa baki san cewa in na rasakiba nima za'a rasani."
murmushin jin dad'i tayi kana ta sha sajenshi ba tare da tace komai ba,
shi kuwa bathroom ya bud'e ya cilla towel d'in kana ya fito,
da kanshi ya tada ita zaune kana ya tallabeta suka nufi parlour,
cikin k'arfin hali tace.
"Hamma zan iya tafiya ba tare da an rik'eni bafa."
bai kulata ba sai ajiyeta yayi bisa kujera,
kana ya fita sauri-sauri gudu-gudu ya tafi harabar gidan tafiyar kusan 5 minutes yayi kana ya isa parking lot nasu da sauri ya shiga cikin wata farar mota,
kana ya fito da ita,
yayinda tuni mai gad'i ya bud'e mishi gate,
shi kuwa Yusuf part nashi ya nufa da motar saida ya kaita har bakin parlour kana yayi parking sannan ya d'an meda kujerar gefen shi baya tare da d'an kontar da ita kad'an sannan ya fita da sauri,
parlour shi ya koma ba tare da yace mata komaiba ya ciccib'eta ya nufi cikin motar,
kunfa san Zahra ba k'atuwa bace kana Yusuf ya fita nesa ba kusaba kuma shi k'ak'k'arfane da yake iya sarrafa linzamin dawakai,
so Madam karkiji nace an d'aga Zahra wata k'il kin kai Garkuwa k'iba kana mijinki dan hutune ba aikin k'arfine sana'arsaba,
ki haihu ki sake kice ai Garkuwa nata nuna Yusuf ne ya d'aga Zahra kice kema sai an d'agaki,
yaseen in kin fasa zuciyar mijinki babu water na, kana kina son mijinki ya rink'a miki yadda Yusuf kewa Zahra na tabbar babu wacce zatayiwa kanta fatan shiga k'alubaken rayuwa irin yadda Zahra ta shiga kuma wacce zatayi fatan mijin da zata aura ya fuskanci matsalolin rayuwa irin yadda Yusuf ya fuskantar,
na kuma tabbatar duk wad'anda suka fuskanci irin rayuwar,
so irin zaman da zasuyi da juna kenan...!

Cikin motar ya ajeta kana ya rufe marfin sannan ya shiga tare da jan motar suka nufi Yusrah Hospital.

Bayan yan dube-dube da doctor Asiya tayi mata ta tabbatarwa Yusuf cewa ba matsalar komai dama normal masu haihuwan kule bayan haihuwa da minti 10 ko 15 wasu minti 7 jinin zai fara zubowa,
so in kasan haka kana haihuwa sai kayi maza ka gyara yadda jinin zai zubo ba tare da ya b'ata miki gidaba.
allurar rage rad'ad'i dana bacci ta mata kana dana ciwon ciki.

So daga nan suka nufi gida,
shi dai kam Yusuf harga Allah ta Zahra yakeyi yafi kula da lmarinta kan na yaran,
suna hanya ne ya d'an kalleta ganin ta fara lumshe ido alamun zatayi bacci dan allurar baccin ta fara aiki,
hannunshi yasa ya kamo nata kana yana driving da hannu d'aya cikin kula yace.
"Zahra."
a hankali ta kalleshi dan sam bai fiye kiranta hakaba sai Ummu Aryan,
ido ya d'an lumshe kana yace.
"Bacci ko?."
kai ta gyad'a mishi tare da d'an roggofowa jikinshi,
hannunshi yasa ya gyara mata konciyarta a jikin nashi kana yaci gaba da tuk'i.


Kafin su isa gida tuni tayi bacci,
har bakin parlour shi yaje yayi parking kana ya fita ya koma ta inda take tare ruggumota ya nufi k'ofar parlour,
sai ya kuma tsaya da sauri sabida sunyi kicibis da Maman Yusuf,
cikin tsoro tace.
"Na shiga uku Yusuf meya sameta daga ina kuke bata da lfy ne?."
da sauri ya girgiza mata kai kana cikin kontar mata da hankali ya mata bayanin komai, ya k'ara da cewa.
"Yanzun baccin tayi."
ajiyan zuciya ta sauk'e tare da tsuke fuska kana tace.
"Ni ka bani tsoro na jira na jira in ganku shiru har na gaji na taho sannan nazo ban sameku ba zan fitone nayi kicibis da ita,
toh juya muje ka kaimin ita d'akina."
cikin sanyi yace.
"Toh Maman Yusuf yadda kikace duk haka za'ayi."
ya k'arishe mgnar tare da juyawa ya nufi part d'insu Mama,
gashi tafiyar da d'an rata kana kuma jikin mai bacci da nauyi,
sosai hannunshi sukayi tsamifa,
ita kuwa Maman Yusuf binshi tayi a baya tana jin tausayinshi dan ta lura yafi son ta zauna a d'akinshi amman tsananin biyayyarsa tasa bai nuna mata rashin jin dad'inshi ba.
shiko Yusuf ji yake kome zata sashi zai aikata matuk'ar bai sab'awa umarnin Allah da manzonsa ba.

Kai tsaye bedroom d'in Mama ya kaita kan gado ya kontar da ita tare da jan blanket ya rufeta zuwa k'irjinta kana ya sumbaci goshinta sannan ya kuma matso inda yaga an kontar da yaran,
zama yayi cikin gadon sannan ya d'aukosu duka biyu ya ruggumeshi tare da lumshe ido yanajin so da k'aunar yaran na ratsa mishi jiki da zuciya,
murmushi yake tayi tare da yiwa Allah godiya daya nuna mishi tsatsonshi.

Yana zaune a haka Mama ta shigo da sallama yayinda Abba ke binta a baya wanda jin haihuwarne ya sashi baro wurin aiki yazo yaga jikokinshi kafin bayan azahar ya koma ya gabatar da shariyar da zaiyi.

da sauri ya isa gefen YUSUF kawai sai ya zauna bakin gadon,
tare dasa hannu ya jawo Yusuf da yaranshi ya ruggumesu duka,
wani irin mashahurin farin cikine ya dabaibaye zuciyar Yusuf ji yake duk duniya babu wanda ya kaishi farin ciki.
Mama kuwa wasu hawayen dad'ine suka rufeta,
jiyo muryar Hajja inna na sallama ne yasata nufi parlour da sauri,
inda ta samu suna cike a parlour don Abba tun kafin ya baro office nashi ya kira Daddy da Hajja inna ya sanar dasu,
aiko sai gasu duk sun taho Daddy da Hajja inna da Ummi da Aunty Amarya sai Ibrahim.


A bedroom kuwa Abba ya kasa sakin Yusuf don ji yake tamkar ya maidashi cikin cikinshi,
sai d'an bubbuga kafad'an Yusuf d'in yakeyi tare da cewa.
"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Yusuf mun godewa Allah da kyautar da ya mana dama dukkan tsanani yana tare da sauk'i Yusuf Allah ya raya min kai da ahlinka, ni ku biyu rak Allah ya bani gashi kai kuma Allah ya baka biyu a lokaci d'aya."
misalta farin cikin Yusuf fa bazai fad'uba.

Suna cikin haka Su Daddy duk suka shigo don shima kanshi Daddy ai k'anine ga Maman Yusuf tunda ita yayarshi ce yar Goggonshi k'anwar mahaifinshi kuma matar yayanshi,
so babu wani nauyi dan ya shiga bedroom nata bare kuma Hajja Inna da take uwarsu bare su Ummi da suke faccalolinta kuma matan k'aninta so ba wani nauyi duk suka shiga,
so ganin Abba ne yasa Ummi da Aunty Amarya sukayi sairin komawa parlour sabida ai su kam shi surkinsu ne yayan mijinsu.

ita kam Maman Yusuf tama rasa me zatayi dan farin ciki.

Shi kuwa Abba hannun Daddy ya jawo,
hakan yasa Daddy ya rusuno tare da matsowa garesu,
cikin farin ciki Abba ya manna jikin Daddy da nashi ta gefen hagunshi yayinda Yusuf yaketa gefen damanshi cikin sanyin murya yace.
"Dukkan farin ciki daya samu zuriyarmu Aliyu kaine sanadi yayinda nine nayi sanadin dukkan bak'in cikin da muka shiga a baya Aliyu ina al'fahari da kai a matsayinka na d'an uwana ngdewa Allah daya azurtani da k'ani kamarka."
cikin rauni Yusuf yace.
"Abba nine silar bak'in cikinmu ba kaiba baka cutar damu da komaiba."
da sauri Daddy yace.
"Babu laifin kowa wannan hukunci ne na Allah, gashi yanzu komai ya wuce ai."
Hajja inna kuwa hannu tasa ta karb'i yaran kana ta fara shaga gashin kansu zuwa goshinsu sai ta kuma d'ago hannunta ta manna a goshinta,
wai tanayi musu maraba da zuwa duniya saida yayi musu haka sau bakwai-bakwai kana ta mik'awa Daddy su,
cikin happy yace.
"Kunga wannan d'a da komanshi irin na Aryan."
cikin tsananin farin ciki Yusuf ya d'an lek'o fuskar yaron yana cewa.
"Nima dai haka nagani."
dak'uwa Maman Yusuf ta mishi tare da cewa.
"Ba kunya 'yam fari nefa."
K'eya ya sosa tare da cewa.
"Maman Yusuf 'yan na biyu dai ko, wato har kin mance Aryan d'inki."
murmushi sukayi baki d'aya cikin sanyi,
duk sukayiwa yaran addu'a.

A parlour kuwa Aunty Amarya zame hijabinta tayi ta shiga kitchen,
ta ci gaba da aikinda Maman Yusuf ta fara, tare da taimakon Abu mai aikin Maman Yusuf d'in,
Ummi kuwa zaune tayi a parlour ruggume da Adnan tana bashi costac enshi don da yar jakarshi take tafiya,
tunda ba nono yake shaba.

a tare Daddy da Abba suka fito suka nufi parlour Abba,

Maman Yusuf kuma parlour ta dawo,
ta zauna kusa da Ummi kana ta karb'i Adnan yaro yayi k'ato gashi fari k'al kekkyawa don sak yayi kama k'anin ubanshi Ibrahim babban d'an Aunty Amarya yayan Zahra kenan
koda yake Ibrahim na kama da Suleiman over hakan yasa ake ganin kamannin Adnan da Ibrahim.
rawa take mishi yayinda yaketa b'ank'ala baki yana mata dariya ita kuwa Maman Yusuf sai biye mishi take don tana matuk'ar son Adnan tana addu'ar Allah ya rayashi kamar sauran yara wad'anda ba sheguba sabida da yawa sai kaga yaran shegu basa nisan kwana wanda hakan yasa ake zargin kashesu akeyi,
shiyasa sukeyiwa Adnan addu'ar nisan kwana domin suma shegu 'yaye kamar saura.

A bedroom kuwa Hajja inna ce ta Kontar da yaran kusa da uwarsu kana ta tasa Yusuf a gaba suka fito parlour.
Suna fitowa Adnan ya rink'a tsalle yana dariya tare da mik'awa Yusuf hannu dan sun saba yakanje gida dan ganin yaron.
da sauri Yusuf ya mik'o hannu zai karb'eshi sai ya kuma juyo da sauri ya kalli Hajja inna da tayi mgna cikin d'aga sauti tace.
"Kai Yusuf kul ina kai ina tab'a d'an shege d'an najasa d'an mazinata,
kada ka kuskura ka d'agashi in d'aga yara kakeso gacan naka Allah ya baka har biyu tsarkakekku."
sai ta kuma harari Ummi da tuni hawaye ya ciko mata ido domin sam Hajja inna ta hanata sukini akan Adnan ta lura kuma tanayin hakane dan ta k'untata mata.
ita kuwa Hajja inna cikin k'udurinta na ramawa su Zahra da Maman Yusuf ta kalli Maman cikin tsuke fuska tace.
"Maza bata jikanta, karki sake d'agashi in kina son inci abincin gidanki."
ganin Maman Yusuf tak'i mik'awa Ummi yaron yasa ta buga mata tsawa.
"Maza ki bata nace, ko ban isa in saki abuba ne?."
cikin sanyi Mama ta mik'awa Ummi yaron,
da sauri Yusuf ya karb'eshi dan har yanzu yaron yanata mik'o mishi hannu,
ruggumeshi yayi tare da watsawa Hajja inna harara,
kana cikin kaushin murya yace.
"Wallahi Allah ko in baki daina tsoggomar rayuwar Adnan ba na rantse miki da Allah zaki had'u da fushina, kinfa sanni sarai ni ba'a min gwaninta karkiga kina wani shige min ina d'an sake miki fuska yaseen kinsanni ba mutuncine da niba in raina ya b'aci."
ido Hajja inna ta zazzaro woje don wlh ita dai bata mance na jakin daya bata, ta kuma sani sarai bashi da M in ranshi ya b'aci kamar yadda ya fad'ad'in ta kuma sanshi ba'ayi mishi gwaninta yanzu zai gwatsaleta.
gefen kujera ta rab'a tayi tsuru-tsuru da ita,
shi kuwa cikin danne dariyarshi da tsuke fuska ya nunata da yatsa yace.
"Wallahi ki kiyayeni tsohuwarnan ki bari ki mutu da kanki karki jazamin in zanek in karki d'anki ya karni,
kinfa san had'uwata dake ba dad'i b'ab'b'allaki zanyi ba ruwana da tsufanki kin sanni sarai."
ita kanta Maman Yusuf ta tsinke da lamarin dan tsoron zuciyar Yusuf takeyi, tana tsoron kada tarihi ya maimaita kanshi, haka yasa ta mik'e tare da cewa.
"Kai Yusuf ka nitsu."
ita kuwa Ummi dad'i takeji tamkar ta goya Yusuf a bayanta
ita kuwa Hajja Inna cikin dakiya da tsoro tace.
"Yoh ni da kai nakene uban yan rashin mutunci darkin k'arfi,
babu ruwanka da ita nake itama taji abinda su Mamanka sukaji lokacin da tayi ta zugani ina yarfa musu rashin d'a'a."
kai ya jinjina tare yin koffa kana ya juya ya fita dan jin anata kiran sallah.

Yana fita Hajja ina ta d'ora daga inda ta tsaya,
saida tasa Ummi kuka kamar yadda ta saba,

Mama kuma kitchen taje, nan ta samu tuni Aunty Amarya da Abu sun kammala aikin komai.

har Aunty Amarya ta rarraba abincin,
ta sawa Abba shida Daddy da Yusuf dan tasan a irin haka in suna had'e tare suke cin abinci,
sai ta kuma sawa Hajja inna uwar rigima, kana ta sawa mai Jedi, sannan tasawa Iya shatu da Baba mai gadi,
sannan tasawa sharifa da yanzu ta dawo school sai tsalle takeyi,
sai kuma tasa musu ita da Ummi da Maman Yusuf d'in.

D'aya bayan d'aya Maman Yusuf ta bud'e kulolin,
tuk'ek'ken tuwon shikafane dayasha tuk'i yayi lugub sai miyar gand'a ta fatar sa da bindi datashaa man shanu da su cittah da kanamfari da kayan d'an-d'ano tsokokin sunyi tibis da d'an kamewarsu baiyi irin lugub d'innanba, miyar masu jego Kennan tayi kyau sai kanshi take zubawa,
kana sai couscous da miyar daddageggiyar hanta da ganyen liwashi,
kana sai zazzafan ferfesun kayan ciki.
kana sai kunun gyad'a da akayiwa Abba da Daddy da Yusuf,
sai kuma kunun kanwa dayasha citta kanamfari da masoro, yayi kyau sai k'amshin geren da kayan had'in.
cikin mmki Maman Yusuf tace.
"Kai Auntyn yara sannu sannu da aiki ya akayi gandarnan ta tuna da wuri haka?."
cikin tattara kulolin su Abba tana jerasu kan wani babban tire tace.
"Ai in dai kina son gand'a ta nuna da wuri kawai ki cefa spoon a ciki."
tayata jerawa ta fari tare da cewa.
"Aifa naga zahiri."
sai ta kuma kalli Abu tare da cemata.
"Yauwa Abu kwashi na Hajja inna ki kai mata d'akin sharifa kana kizo ki kai na Zahra d'akina,
sannan ki kai nasu iya shatu sai kizo ki d'auki naki,
in kinci kiyi baccinki ki huta dan Amara da Zulaihat suna zuwa su zasu mana aikin dare."
cikin jin dad'i tace to kana ta fara yin Aiken da aka

Please Login or Register in order to submit comment