Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da yawa sai kaga yaran shegu basa nisan kwana wanda hakan yasa ake zargin kashesu akeyi,
shiyasa sukeyiwa Adnan addu'ar nisan kwana domin suma shegu 'yaye kamar saura.

A bedroom kuwa Hajja inna ce ta Kontar da yaran kusa da uwarsu kana ta tasa Yusuf a gaba suka fito parlour.
Suna fitowa Adnan ya rink'a tsalle yana dariya tare da mik'awa Yusuf hannu dan sun saba yakanje gida dan ganin yaron.
da sauri Yusuf ya mik'o hannu zai karb'eshi sai ya kuma juyo da sauri ya kalli Hajja inna da tayi mgna cikin d'aga sauti tace.
"Kai Yusuf kul ina kai ina tab'a d'an shege d'an najasa d'an mazinata,
kada ka kuskura ka d'agashi in d'aga yara kakeso gacan naka Allah ya baka har biyu tsarkakekku."
sai ta kuma harari Ummi da tuni hawaye ya ciko mata ido domin sam Hajja inna ta hanata sukini akan Adnan ta lura kuma tanayin hakane dan ta k'untata mata.
ita kuwa Hajja inna cikin k'udurinta na ramawa su Zahra da Maman Yusuf ta kalli Maman cikin tsuke fuska tace.
"Maza bata jikanta, karki sake d'agashi in kina son inci abincin gidanki."
ganin Maman Yusuf tak'i mik'awa Ummi yaron yasa ta buga mata tsawa.
"Maza ki bata nace, ko ban isa in saki abuba ne?."
cikin sanyi Mama ta mik'awa Ummi yaron,
da sauri Yusuf ya karb'eshi dan har yanzu yaron yanata mik'o mishi hannu,
ruggumeshi yayi tare da watsawa Hajja inna harara,
kana cikin kaushin murya yace.
"Wallahi Allah ko in baki daina tsoggomar rayuwar Adnan ba na rantse miki da Allah zaki had'u da fushina, kinfa sanni sarai ni ba'a min gwaninta karkiga kina wani shige min ina d'an sake miki fuska yaseen kinsanni ba mutuncine da niba in raina ya b'aci."
ido Hajja inna ta zazzaro woje don wlh ita dai bata mance na jakin daya bata, ta kuma sani sarai bashi da M in ranshi ya b'aci kamar yadda ya fad'ad'in ta kuma sanshi ba'ayi mishi gwaninta yanzu zai gwatsaleta.
gefen kujera ta rab'a tayi tsuru-tsuru da ita,
shi kuwa cikin danne dariyarshi da tsuke fuska ya nunata da yatsa yace.
"Wallahi ki kiyayeni tsohuwarnan ki bari ki mutu da kanki karki jazamin in zanek in karki d'anki ya karni,
kinfa san had'uwata dake ba dad'i b'ab'b'allaki zanyi ba ruwana da tsufanki kin sanni sarai."
ita kanta Maman Yusuf ta tsinke da lamarin dan tsoron zuciyar Yusuf takeyi, tana tsoron kada tarihi ya maimaita kanshi, haka yasa ta mik'e tare da cewa.
"Kai Yusuf ka nitsu."
ita kuwa Ummi dad'i takeji tamkar ta goya Yusuf a bayanta
ita kuwa Hajja Inna cikin dakiya da tsoro tace.
"Yoh ni da kai nakene uban yan rashin mutunci darkin k'arfi,
babu ruwanka da ita nake itama taji abinda su Mamanka sukaji lokacin da tayi ta zugani ina yarfa musu rashin d'a'a."
kai ya jinjina tare yin koffa kana ya juya ya fita dan jin anata kiran sallah.

Yana fita Hajja ina ta d'ora daga inda ta tsaya,
saida tasa Ummi kuka kamar yadda ta saba,

Mama kuma kitchen taje, nan ta samu tuni Aunty Amarya da Abu sun kammala aikin komai.

har Aunty Amarya ta rarraba abincin,
ta sawa Abba shida Daddy da Yusuf dan tasan a irin haka in suna had'e tare suke cin abinci,
sai ta kuma sawa Hajja inna uwar rigima, kana ta sawa mai Jedi, sannan tasawa Iya shatu da Baba mai gadi,
sannan tasawa sharifa da yanzu ta dawo school sai tsalle takeyi,
sai kuma tasa musu ita da Ummi da Maman Yusuf d'in.

D'aya bayan d'aya Maman Yusuf ta bud'e kulolin,
tuk'ek'ken tuwon shikafane dayasha tuk'i yayi lugub sai miyar gand'a ta fatar sa da bindi datashaa man shanu da su cittah da kanamfari da kayan d'an-d'ano tsokokin sunyi tibis da d'an kamewarsu baiyi irin lugub d'innanba, miyar masu jego Kennan tayi kyau sai kanshi take zubawa,
kana sai couscous da miyar daddageggiyar hanta da ganyen liwashi,
kana sai zazzafan ferfesun kayan ciki.
kana sai kunun gyad'a da akayiwa Abba da Daddy da Yusuf,
sai kuma kunun kanwa dayasha citta kanamfari da masoro, yayi kyau sai k'amshin geren da kayan had'in.
cikin mmki Maman Yusuf tace.
"Kai Auntyn yara sannu sannu da aiki ya akayi gandarnan ta tuna da wuri haka?."
cikin tattara kulolin su Abba tana jerasu kan wani babban tire tace.
"Ai in dai kina son gand'a ta nuna da wuri kawai ki cefa spoon a ciki."
tayata jerawa ta fari tare da cewa.
"Aifa naga zahiri."
sai ta kuma kalli Abu tare da cemata.
"Yauwa Abu kwashi na Hajja inna ki kai mata d'akin sharifa kana kizo ki kai na Zahra d'akina,
sannan ki kai nasu iya shatu sai kizo ki d'auki naki,
in kinci kiyi baccinki ki huta dan Amara da Zulaihat suna zuwa su zasu mana aikin dare."
cikin jin dad'i tace to kana ta fara yin Aiken da aka satan.

Ita kuwa Maman Yusuf ita da Aunty suka d'auki nasu Abba suka kai,
kana suka dawo kitchen d'in a tare da sauri Maman Yusuf tace.
"Wai baki sawa su Ibrahim ba."
murmushi Aunty Amarya tayi kana tace..
"Yoh bakiga tun d'azu suka tafi gidan Jafar ba, Ibrahim harda cewa bari yaje ya tsagalgali Aunty Dija sai ta mishi d'anwake, shiyasa banyi rabiya na dasuba?."
itama Mama murmushi kana tace.
"aifa Ibrahim da Aunty Dijanshi sai Allah, ba matsala ai abincinsu Abban nasu da yawa ko mutun biya zasuci su bari in sun dawo in zasuci saje can."

Haka dai sukaje sukayi sallah kana sukazo sukaci abinci,
hajja ina sai santin tuwo da miyar gandarnan takeyi koda ta fito tai ta sawa Maman Yusuf da Aunty Amarya al'barka harda cewa.
"Kun samu ladana yau naci tuwo,
dama kwana biyu dan mugunta sai a dafa shirmen abincin yan gayu wanda ni ba dad'i yake minba,
haka dama yauda safe banci wannan wannan soyayyiyar shinkafarba dan ni ba kaza bace."
ta k'arishe mgnar tana hararan Ummu dan da ita take.
Nanda suka zauna sunata hira.

Yusuf kuwa dama yana fita part nashi ya wuce tare da Adnan,
kan gado ya kontar dashi tare da bashi wayarshi d'aya kana ya d'auki d'ayar kuma,
Aryan ya fara kira kana ya kara woyar a kunnenshi tare da zare hallabiyar jikinshi,
jin sallaman Aryan ya sashi zama bakin gadon cikin happy yace.
"Wa alaikassalam." sai ya kuma ci gaba da cewa.
"Al'bishirin ka."
cikin d'oki da zak'uwa Aryan yace.
"Goro fari k'al."
murmushi yayi cikin kara irin ta aminai ya shafa kanshi tare da cewa.
"Toh yau dai Allah yayi yaranka sun fito duniya an samu tagwaye, Aryan ya tafi Aryan ya dawo tare da Yusrah."
cikin tsananin farin ciki Aryan yace.
"Alhamdulillah Alhamdulillah Masha Allah mashaaa Allah kai Allah na gode maka, Allah ya raya mana su bisa imani, kuna wanne asibiti yanzu?."
mik'ewa yayi ya gyarawa Adnan konciyarshi dan yayi bacci kana yace.
"Yoh ai a gida muka haihu."
dariya sosai Aryan yayi kana yace.
"Kuka haihu ko ta haihu watoma tare kuka haihu."
cikin fidda numfashi yace.
"Kai Aryan wlh tare muka haihu kakuwa san azabar danasha, shak'a mari yagushi naushi duk saida Zahra tamin kafin ta haihu kaga ko ai tare muka haihu wlh yanzu haka duk jikina ciwo yakeyi."
cikin dariyar shak'iyanci, Aryan yace.
"Toh gamu nan zuwa yanzu?."
suna gama waya da Aryan ya kira Affan ya shaida mishi inda Affan yace mishi.
"Yoh ai makara domin mu gamu ma a hanya Aunty ta gaya mana tun d'azu."
dariya yayi kana yace.
"Toh Allah kawoku lfy."
daga nanfa ya kira Sultan ya shaida mishi sannan ya kira Abdul-kareem inda yace ai ya makara domin Aryan ya gaya mishi,
ya k'ara da cewa ya turo mishi hoton yaran,
yana katse kiran ya kira shugaban tuzurai inji Affan da fad'i M Jabeer inda yace mushi.
"Yoh ai Abba ya rigaka ya gaya min tun d'azu."
cikin jin kunya yace.
"Malam yaushe zaka zo ka gansu ka musu Addu'a?."
cikin kamala yace.
"Sai zuwa jibi."
Cikin jin dad'i yace.
"Allah ya kaimu."

So daga nan ya kira Safwan ma ya gaya mishi shima ya tayashi murna,
kana yana katse kiran ya shiga bathroom a gurguje ya wonke towel d'in daya d'an b'aci kana yayi wonka mai rai da lfy sannan,
ya fito ya kimtsa cikin wata d'anyar voyel mai azabar tsada da kyau da shek'i kana ya feffesa turare,
tare da kafa hular zanna mai tsunami kyau kana ya d'auki carbinshi ya nufi masallaci,
nan ya samu Aryan da iyalanshi ya iso hakama Affan.
so su Nana da d'iyarta Anisa da Rayi' da yan tagqayenta suka wuce part d'in Mama.
Su Ibrahim da Sadiq ma duk sun fito daga gidan Jafar zuwa nan
tare sukayi sallah a matsallacin gidanshin inda Abba ne ya limancesu.

kana fitowa masallacin suka wuce parlour Abba nanfa,
suka zauna sukayi lunch tare sai Affan da yak'i shigowa parlour sabida kunyar surkan nashi.
Ibrahim kuwa da Sadiq kajin suka d'anci kad'an kana suka shiga gari,
shi kuwa Affan parlour Yusuf ya tafi inda Nana ta kai mishi abincin a can ta nace sai yaci so a k'oshe yake kawai sai ya d'ansha kunun gyad'an.

Dija kuwa tana samun ta sallami su Ibrahim ta shiga bedroom nata wasu set d'in kayan jarirai ta kwaso kusan kala shida na mace da namiji a Dubai Jafar ya sayesu domin cikin Zahra,
tana gama had'a kayan ta zari hijabinta kana ta suri woyarya tare fitowa ta nufi gidan Zahra d'in da cikinta daya fara d'an fitowa.

Tana shiga cikin gidan ta samu su Mami sun rigata zuwa,
kai tsaye bedroom ta wuce inda ta samu su Rafi'a da Mami,
dasu Adda Amira da Zulaihat jiki na rawa ta kalli Zahra dake zaune Mama ta tasata a gaba tamkar ta bata abincin a baki,
cikin tsananin farin ciki ta karb'i jaririyar da Ummi tayiwa wonka yanzu jiki na rawa ta karb'eta tare da nad'eta cikin tattausan shawul da ta zaro cikin kayan da tazo dashi,
"Wow Masha Allah, kai Allah mun gode maka yau gamu ga d'iyarmu."
sai ta kuma kalli Zahra dake murmushi tace.
"Sannu Matar Hamma." dariya sukayi baki d'aya dan sun san Dija da tsiya,
Hajja inna kuwa sai murmushi takeyi kun san tana son Jafar shiyasa take son matarshi over tafi tsargan Sakina cikin kula tace.
"Saura ke da Rukayya Allah ya sauk'eku lfy."
cikin jin kunya Dija ta d'uk'ar da kai dan ga surkanta,
Adda Zulaihat kuwa mik'ewa tayi tare da cewa Amira.
"Ke tashi mu shiga kitchen kinji fa Mama cewa tayi mai aikinta ta huta yau mune da kitchen."
cikin sauri Amira ta mik'e tare da mik'awa Aunty Amarya d'iyarta k'arama Arifa, da sauri Aunty Amarya ta amshi Baby cikin wasa ta d'an ja kumatun Arifa tare da cewa.
"Kishi ban haushi zata karya min sawu."
Mami ce tai dariya tare da cewa.
"Kai Aunty Amarya kishi dai kinga ta fiki gashi."
dariya sukayi baki d'aya kana Zulaihat da Amira kana Rafi'a tabi bayansu suka fita suka shiga kitchen.
Ummi kuwa taci gaba da yiwa jaririn wonka cikin kula da amana.
yayinda Dija ke kimtsa macen.
Mama kuwa ta dage tana bawa Zahra kula data dace da masu jego.

Yusuf kuwa suna fitowa parlour Abba ya nufi parlour Mama da kanshi ya shiga cikin wai zai d'auko yaran ya kaiwa su Aryan su samusu al'barka,
yayinda Aryan kuma ya nufi parlour Yusuf d'in wurin Affan.

Da sallamanshi ya shiga,
ganin suna cike a d'akin sai ya d'an koma gefen Mamanshi ya zauna,
domin ba wanda yakejin kunya a cikinsu dan Dija surutu gareta dole ya saki jiki da ita,
Mama kuma uwace hakama Ummi Aunty Amarya kuwa matsayinta nada yawa a gurinshi,
so bai wani jin kunyarta sosai bugu da k'ari suma kowa Harkar gabanshi yakeyi.
ido ya zubawa Zahra kana ya k'ara matsota hannunshi yasa bisa wuyanta,
idonta ya kallah bisa dukkan alamu baccin bai ishetaba.
a hankali yace.
"Kici abinci kizo muje kiyi bacci nan surutun Dija ma kad'ai zai hanaki bacci."
murmushi Dija tayi kana tace.
"Kai Hamma Yusuf nifa kafin in zoma a zaune na sameta."
shima murmushi yayi kana yace.
"A a gwara fa in tafi da abata yafi min konciyan hankali,
gwara in bata kulawa sabida tsaro badon tsoroba."
Mami kam baki ta bud'e tana kallon Hamman nasu tana mmki ashe Hamma Yusuf yana tsurutu mai tsawo yau harda wasa da dariya lallai kam.
itama kanta Dija tayi mmki don tabbas ya sake in tazo gidansu suna gaisawa a mutunce amman ba irin fara'ar yau d'innan ba.
Aunty Amarya kuwa murmushin jin dad'i kawai taketayi,
yayinda Ummi ma take binsu da kallon sha'awa,
kana Hajja inna ko ita ke taya Dija kimtsa jaririyar,
ita kuwa Maman Yusuf kofin kunu ta mik'awa Yusuf tare da cewa.
"Bata ta shanyeshi."
da sauri ya amshi kofin kana ya kai matashi har baki ganin dafa gaske yakeyi dole ta shanyeshi kana ya barta.
sai ya kuma kalli Ummi jin yaron nata kuka cikin kwab'e fuska yace.
"Ummi barshi haka wonkannan yayi yawafa kawoshi yasha nono."
cikin dariya Ummi ta kalli Mani tare da cewa.
"Kinga ke jeki zunda ruwannan ki k'aro ruwa na uku in tsulleshi in dai ba so suke ya zama saurayi mai warin k'ashiba."
cikin sauri yace.
"Kai Ummi har wonka uku yunwafa yakeji ayi hak'uri a kawoshi yasha nono sai ayi na ukun."
Cikin sanyi Dija tace.
"Toh ai nononma ba'a wonkeshi bako?."
kai ya jujjuya cikin subutar baki yace.
"Ohh hoo nononmu ba tatti fes yake, kullum sai n...!"
sai ya kumayi maza ya taro harshenshi jin zaiyi katob'ara,
ita kuwa Dija Mami ta kalla sai kuma suka sunkuyar da kai don sunfa lura yau Hamma Yusuf sai a slow,
Ummu kuwa da Aunty Amarya yi sukayi kamar basuji ba.
shi kuwa tsare gida yayi kamar ba shiba kana ya mik'a hannu ya amshi jaririyar da Dija ta gama kimtsata cikin wasu tattausan kayan sanyi pink color kasancewar ana cikin yanayin sanyin huturu yarinya sai k'amshi takeyi yana amsarta ya ruggumeta tare da wanna mata kiss a goshi.
daga nan aka gama kimtsa na mijinma.

Nan Mama ta shigo dabino da Zam-zam ta mik'a mishi, gyara rik'on babyn yayi kana ya amshi robar dabinon ya watsa a bakinshi ya tattauna kana ya tattara yawunshi da d'and'anon dabinon ya bata a baki irin yadda yayiwa marigayi Aryan saida ya gama bata na dabino bakwai sannan ya bawa namijin ma.
kana Mami ta rik'e macen suka tafi part nashi inda su Affan suke nan sukayiwa yara addu'a,
zata fitane sukaji muryar Adnan da sauri Yusuf ya shiga bedroom nashi ya d'auko Adnan ya batashi tare da cewa.
"Ki bashi abinci ki mishi wonka ki dawo min dashi?."
toh tace kana ta amsheshi.


Kai wannan rana dai wannan zuriya ta cika da farin ciki,
yan uwa da abo kan arzik'i duk sunji social media ta ciki da hotunan Yusuf da jariranshi tako ina Aryan ya turawa Abdulkareem da Sultan kunfa san Sultan shi hoto nada daraja a wurinshi shiyasa lokaci d'aya haihuwar ta ratsa ko ina,
Su Ummi kuwa har sun gaji da ganin rawan k'afar Yusuf.
Ranar dai nan suka wuni.


Washe gari Sakina ma tazo hakama Raihana da Hajjia Kaka, da Zeenat
Safwan ma yazo da Rukayyanshi,
Kana Tatti ma tazo ita da matar Uncle Sani,
mak'otansu Mama na Girei duk sunzo yiwa Mama barka.


Kwanaki sun tafi suna yazo tuni Zahra tafa murje tayi ras kunsan cikan satin sunannan mai jego takanyi wani sihirtaccen kyau da fitinennen shak'i da k'amshi.

Toh hakance ta kasance da Zahra tayi ras da ita sai shek'i tamkar tauraruwa Zahra.
Hamma Yusuf kuwa tun Mama na korarshi har ta zubawa sarautar rabbi ido.


Gobe suna Mutan sokotoma Sun zo Sultan da Nana hakama,
Abdul-kareem da matarshi haka bashir abokin Yusuf d'an liman shima daga Gombe yazo, Jafar ma da ya dowo dan baya nan akayi haihuwar yana Abuja to washe gari suna ya dawo

Washe garin suna yara sukaci sunansu Namijin aka meda sunan Aryan mace kuwa akasa mata Yusrah


Anyi hidama da shagalin bikin suna cikin wadata da salama.

Bayan suna da kwana biyu duk bak'i sun watse,
Abdulkareem ya wuce Sokoto shida Sultan da matansu.


******************************

Kwanaki sunja makonni sun ja ya juye eh zuwa wattini yanzu watannin Aryan da Yusrah biyu.
Abubuwa da yawa sun faru cikin watannin nan,
a ciki kuwa harda magiya da nacin da Yusuf yayi ta yiwa Mama akan tunda Zahra ta gama Araba'in ta koma side d'inta amman ina Mama ta kafa ta tsare tace wai sai yara sunyi wata uku to yau dai Yusuf ya shiryawa kanshi mafita.




by
*GARKUWAR FULANI*




[2/20, 5:50 PM]
*HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 31*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


*WANNA SHAFI NAKU NE HUKUNCIN ALLAH fan's 1,2,3,4 inayi mana fatan al'khairi*





Bayan sallan isha ne ana fitowa masallaci, Yusuf ya nufi part d'in Mama,
a parlour ya samu Mama tana rik'e da Aryan tana sauya musu pampers ita da sharifa da Abu,
gefen Mama ya zauna tare da sa hannu ya karb'i Yusrah da ita aka fara canzawa kana ya rugguemata a k'irjinshi tare da cewa.
"Mama zafi dai ake d'anyi kika sa musu k'aya mai d'an kaurin nan."
murmushi tayi tare da cewa.
"Yoh uwarsu tace dole ita da AC zata kwana wai zafi na damunta su kuma inaga da sauransu da wannan sanyin."
kai ya jinjina alamar gamsuwa kana ya kalli sharifa data amshi Aryan,
murmushi yayi tare da cewa.
"Adda shari nafa lura kinfi ji da Aryan akan my Yusrah."
shafa kan Aryan tayi kana tace.
"Uncle ita Yusrah ta fiye koke-koke shiyasa ba ruwana da ita shi kuwa Aryan bawan Allah yanada hak'uri."
Zahra da yanzu ta fito ya d'an kalla a sace kana yace.
"Ita Yusrah tsiwar Mamanta ta kwaso ai shi kuwa bawan Allah Aryan ya gado hak'urin Abeehnshi da yayanshi marigayi."
kallon hadarin so tayi mishi kana ta zauna gefen Mama tana shan tea da ake tafasashi da had'in gyara.
shi kuwa da sauri ya mik'e dan jin yake tamkar ya rarumota jikinshi.
amsar Aryan yayi kana ya fita dasu ya nufi part nashi.

Yana shiga ya kontar dasu kan gado,
kana ya kunna karatun qura'an a woyarshi ya ajiye musu a tsakayirsu sannan ya shige bathroom wonka yayi mai rai da lfy, yana fitowa ya kimtsa cikin tattausan kayan bacci,
kana yaje ya hada madararshi da zuma yasha sannan,
ya kira Ado yazo ya bashi key d'in mota tare da bashi kud'i yace yaje ya saye mushi burger da fries shawarma da kifin margi special.

saida ya tabbatar Ado yaja mota ya bar gidan sannan ya kuma parlourshi ya zauna tare da zaro wayarshi Mama ya kira tana d'agawa yace.
"Maman Yusuf Zahra taje side na ta d'auko su Aryan na barosu suna bacci karsu tashi suyi ta kuka ba kowa a wurin su kad'ai."
da sauri tace.
"Hhhhhhh ina kaje wannan wanne irin ganganci ne zaka tafi ka barsu su kad'ai?."
gyara zama yayi tare da yin murmushin jin dad'i ganin game nashi zai tafi yadda yakeso, ya d'an hura iska tare da cewa.
"Oh sorry Maman Yusuf na bar miki jikokinki su kad'ai wlh Aryan ne ya k'irani sauri-sauri wai ya samu matsala da Rafi'a tana can ta kafe wai zata tafi gidansu."
cikin sanyi tace.
"Ashsha! to Allah kiyaye hanya hamzarta kaje."
toh yace kana yace.
"Bawa Zahra wayar taki."
ba tare da ta tuna komaiba ta bawa Zahra wayar tana amsa yace.
"Mik'e maza kije ki d'auko su Aryan."
toh tace kana ta mik'e da wayar a kunnenta,
tana tafiya suna mgna koda ta iso ta tura k'ofar ta shiga wayam parlour,
sai ta kuma juyowa da sauri jin an rufe k'ogar parlour,
tsaye ta ganshi ta bayan k'ofa alamun a bayan k'ofa ya b'uya shiko ya b'uyane a zatonshi ko zata zo da Sharifa ganin ita d'ayane ya dashi rufe k'ofar tare da tahowa inda take,
ita kuwa ido ta zuba mishi murmushi yayi tare da cewa.
"Yarinya ba wayo, na zauna inata binku Allah manzo kizo kingi gashi hikimar 2 minutes ta kawo min ke."
murmushi tayi tare da cewa.
"Toh me zan maka?."
kamo hannunta yayi suka zauna kan kujera yayi mgna cikin rad'a yace.
"Ihu nake so ki sani, dan yauma ton d'inki ne."
kissing nashi tayi dan ita kanta tana kewan mijinta.
a hankali tace.
"Abba da Mama zasu jiyo kafa."
hannu yasa cikin rigarta tare da cewa.
"ai da rata tsakaninmu bafa zasuji ba."
sai kuma shafo k'irjinta tare da lumshe ido yace.
"Ban tab'a kewar wani a duniya ba kamar wannan."
kumatunshi ta d'an kama tare da ja kana ta d'an jijjiga tace.
"Gasu gareka ai."
cikin yi mata sigana yace.
"Madam kema dama kinyi missing nafa kike wani shassharewa."
ruggumeshi tayi tare da cewa.
"Ba dole ba inyi kewar santalelen mijina ba kwana sittin da biyu fa ai ba kusaba."
wani irin dad'ine yaji yana ratsashi,
sai ya kuma mik'e ya nufi bakin k'ofa dan yaji muryar Ado
ledojin ya karb'a kana ya sallameshi da sauran kud'in yace yaje ya sayo duk abinda yakeso dashi,
cikin jin dad'i Ado ya juya kana shi kuma ya rufe k'ofar.

Bisa dinning table ya ajiye ledojin kana ya dawo ya sameta zaune inda ya barta,
hannu yasa ya kamo nata ya saida iya kana ya zauna shi sannan ya jawota kan cinyarshi,
cikin rad'a tace.
"Mu tafi bedroom wlh nasan zakayi ta zund'uma ihu har a jiyoka in dai bisa kujera ne."
dugure goshinta ya d'anyi tare da cewa.
"Uhummm wato ni dai kin maidani a koke,
amman bari ki gani."
woyarshi ya jawo ya kira Ado yana d'agawa cikin bada umarni yace.
"Ado a canza layin wuta a medashi na inji."
da sauri Ado yace.
"Abban biyu akwai wutan fa."
kai ya manna a k'irjinta tare da cewa Ado.
"Eh na sani kayi abinda na saka ka medashi inji sai kaje ka kunna injin d'in."
cikin bin umarni yace.
"Toh yanzu kuwa."
ido ta zuba mishi saida taga ya ajiye woyar tace.
"Meyasa kace a kunna inji baya ga wuta?."
igiyar rigarta ya fara kuncewa kana yace.
"Sabida ina son jin dad'i inyi ihuna son raina babu mai jina sautin injin zai yi mana tsakani dasu ai,
sai ki kontar da hankalinki babu mai jin ihun mijinki, kimin da kyau yadda zan sa miki al'barka da kyau."
murmushi tayi tare da sa hannu tana zuge zip d'in k'ugunshi.
wata iriyar rugguma sukayiwa juna wacce tayi dai-dai da kunna injin d'in da akayi,
cikin zazzafar fitina suka fara shigewa jikin juna,
ji take tamkar ta maidashi cikinta dan shauk'i,
a hankali tace.
"Hamma in nayi cikifa?."
hannunshi yasa ya d'amk'i k'ugunta tare da dannata kan cinyarshi cikin kware murya da rumtse ido jiki na tsuma ya fizgo mgnar da k'arfi yace.
"Ohhhh Karki damu zan tayaki nak'uda."
jin yadda yake mgna ne yasata bud'a wuta,
aifa Hamma Yusuf tuni ya susuce yake kwarara sambatu da zurma ihu iya son ranshi.

Maman Yusuf kuwa tana can tana jiran dawowar Zahra yaune gobe ne shiru,
abu har tsawon awa biyu har zuwa uku babu Zahra babu dalilinta.
toh Mama dai kam ta rasa abin fad'i dole ta tashi taje tayi shirin bacci ta konta a d'akinta tana tsumayinta dan tunda Zahra ta haihu ta dena zuwa d'akin Abba sai ta kwana can acewaeta yanzu da sabon ango takeyi,
to dole dai shima Abba ya hak'ura, sai da rana ake kai mishi ziyara koda safe.

Toh fahimtar yau dai Yusuf wayo ya musu sai itama ta fece d'akin Abban Yusuf abinta.

Shi kuma Yusuf lamarin fa ya girmama fad'in yanayin da yake ciki sam yafi k'arfin al'k'alamin Garkuwa.

Bayan komai ya lafane,
Zahra tayi rau-rau da idanu kana tace.
"Kace zaka tayani nak'uda ko?."
k'eyarshi ya shafa tare da d'aga mata girarshi d'aya kana yace.
"Yoh ai ni na saba tayaki nak'uda."
cikin narkewa a jikinshi tace.
"Kai Hamma Yaushe ka tayani nak'uda."
gyara mata kwanciyarta yayi bisa jikinshi tayi balance da kyau kana cikin fidda numfashi yace.
"Uhumm kin manta haihuwar su Yusrah ko da kikayi ta dukana kina shak'eni da yayyarfa min mari, harda ce min mugu sabida kinji bone kin manta sanda kike d'aga k'afa sama kina irga silin."
tsune kanta tayi tare da cewa.
"Uhummm Hamma Yusuf iya ruwa fidda kai ko."
bayanta ya shafa tare da cewa.
"Fad'in gskya dai."
fuska ta kwab'e kana tace.
"Hamma yunwa nakeji."
mik'ewa yayi da ita kana yace.
"Muje muyi wanka kafin kici abincin a cici kawai ke dai ba daman a tab'aki kamar zazzage abincin cikinki akeyi sakaliyar Hamma."
k'eyanshi ta d'an shafa kana tace.
"To ai zazzagar ne kakeyi min."
suna

Please Login or Register in order to submit comment