Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Page 1⃣6⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


*Zakeeyata tana sona, shiyasa nake jinta a raina fiye da sauran yarana, Zakiya malleri nake nufi in taga nayi shiru sai hankalinta ya tashi tayi ta cemin. "Yafend'o baki da lfy ne? meya sameki? waya b'ata miki rai?." duk amsar da zan bata sam basata gamsuba sai taga na saki rai muna hira da dariya, in ta dawo school daga bakin gate take fara kirana, in ta iso tsakar gida zuwa corridor kuwa bata ganniba sai ta k'ara d'aga sautin muryarta tare da fara lek'a kitchen tana cewa. " Yafendo! Yafendo!! Yafendo!!! in taga bana kitchen sai ta shigo parlour in bata ganniba sai ta shigo bedroom, wani lokacin har corridor bathroom take matsowa wai ko zataji motsina a ciki, in bata jiniba sai tayi maza ta nufi d'akinsu dan tasan ina buya a d'akinsu inyi typing lokacin da nake rubuta mi'wasmiti, in ta sameni sai tayi dariya tare da cilla jakarta tace. "ai har naji haushi ina zaton ko kin tafi unguwa ne, nakan yi shiru bana kulata sabida ina typing, ita kuwa sai ta zumbura baki wai dole in bar typing ai lokacinta ne tunda ta dawo daga school so dole in bar typing sabida diyartawa tana but'atar in bata lokacina, in ko dare yayi bayan sun taso hadda, tofa sai taje kitchen d'in tsakiyar gida tayi ta girke-girke in ta kawo min na karb'a naci sai tayita jin dadi tana cemin, "Yagendo na iya girki ko? yayi dad'i ko Yafendona." sai ince mata sosaima kuwa Zakeeyata kin iya girki, aifa sai ta cika da farin ciki, inko ran jumma'a da al'hamis ne tofa ranar wonka da kolliyace tayi ta bina wai in kefta mata pictures, inko ina kitchen to tana gefena duk wasu yan yanke-yanke ita zatamin ina girki muna hira kamar k'awaye, takan cemin, "Yafendo kina da kyau wlh da na samun kyawunki da farinki da gashinki da na more, kujifa duk da munin nan nawa ita bata ganin munina ko kad'an, tana gaya min dukkan damuwarta dan tanada yak'inin ina sonta a raina, koda duk duniya zasu tsaneni su juya min baya ina da yak'inin Zakiyata zata soni, bata cemin Yafendo kawai sai tace Yafendona, mukan kwana bisa gado d'aya tana jin dadin mu kwana tare shiyasa sai ta baro d'akinsu ta dawo d'akin Mamanta, ina sonki Zakiyata kinfi sauran yarana soyuwa a zuciyata sabida kin fisu kulafashi a kaina, Allah ya raya minke ya baki miji na gari salihi mai rikeki da amana da gsky mai yin hakuri da kuruciyarki, ina miki fatan shiga S s 3 Lfy ki gama lfy dama kince kingaji da saka uniform kina mararin ki fara kabta jami'a diyata yar albarka ki gaida min bestynki yar garinmu Saddik'a Cholli dama duk k'awayenki dama d'aliben makarantar Hayatu baki d'aya ina gaidasu sabida kee!*


```Free page```
*GA masu niyar biyan kud'in shiga group d'in Hukuncin Allah domin samun damar karantawa to k'ofa a bude take, turo katin MTN na 200 kacal ta wannan layin 09097853276 ko kuma ku turo ta asusuna 0005388578 jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar kinyi screenshot kin turo min shaidar kin biya*

~ohohoh ni Shatu Alhamdulillah masoya rahama ne, kuyi haquri dani mosoyana nace ku dena min transfer ta etisalat, in kinmin naqi saki sai kice na cuceki fa ko? Kuma nace miki bana so dan Allah ku bari katin Mtn nake so~


Da sauri Yusuf ya saka hannuwan shi duka biyun ya toshe kunnuwan shi saboda sowa da kiraye-kirayen sunashi daya ciki illahirin farfajiyar, da sauri ya juyo ya kalli window d'in inda Safwan yake zaune gun-gun matasa ne da sukazo wucewa suka hangosu zaune cikin motar, sanadin glass din window d'in motar da suke ciki a sauk'e yake sannan kuma number d'in jikin motar an rubuta *Adamawa polo team jahan*.
Sosai suke murna da hargagi tare da fad'in
" Kaga *BARADEN* Adamawa d'an na koya ya zarta d'an na gada".
kafin mai gadi ya bud'e musu gate su shiga cikin gamjin tuni sun zagaye motar sunata ihu shine dalilin daya saka Yusuf toshe kunnensa.



Matasan kuwa k'ok'arin gaisawa da Yusuf suke inda wasu ke mik'a mishi wayar shi ya saka musu phone number d'inshi wasu kuwa user name d'inshi da yake using a face book da instagram da You tube and snap chat suke tambaya.

Malam Jabir da yake Motar baya shiya fito danya duba meke faruwa saboda motar su Yusuf d'in daban tasu Malam jabeer d'inma daban da yake yau harda abokanan shi da suke cikin Kadunan suke tare, Aryan kuwa shi yake k'ok'arin sakawa masoyan Yusuf phone number d'inshi a wayarsu yana fad'a musu user name d'inshi danshi Yusuf ya kasa komai sai kallo da ido ya tsuke fuska tare da kamo lip enshi na k'asa yana cizawa a hankali tare da tsare fuska cikin cikar haiba da zumunci, a zuciyar shi kuwa yana tasbihi ga ubangiji dan tabbas shine mai yiwa dan adam baiwa a lokacin da yaso in banda ubangiji waye zai mishi wannan baiwar rana tsaka,
Aryan ne ya d'an harareshi tare da cewa.
"Banza masifeffe ka saki fuska mana kanaga harda yan mata ke yayinka".
fuska ya kuma tsukewa tare da jan d'an guntun tsaki had'i dayin k'asa-k'asa da murya yace .
"Toh kuma sai inyi ta b'are baki kamar zaucecce kenan, tunda dai ku kuna musu dariyar ai ya isa ba sai mun taru duk mun zama zararruba."
ya k'arishe maganar cikin tsokana tare da nunawa Aryan Affan da baki,
kai Aryan ya rink'a juyawa tare da yin dariya ganin yadda Affan ke rawan kai shi tuni ya bud'e motar ya fita yana tsakiyar matasan yayinda duk hankalinshi ke kan yan matan,
tsaki Yusuf yaja had'ida tab'e baki ganin yadda Affan yabi wata yar budurwa tare amsar wayarta da alama number sa yasa dan jin wayarsa dake cikin motar tana ringing kuma sabuwar number ya nuna ba suna.
dak'yar aka samu matasan suka basu hanya suka shiga cikin gamjin.

Safwan kuwa tuni ya cika yayi tam da bak'in ciki da tsananin kishi da tsanar Yusuf da yakeji, ranshi na soyuwa matuk'a in yaji anawa Yusuf kirari da kaga d'an na koya ya zarta d'an nagada ji yake kamar dashi akeyi tunda shi d'an gadone, tsaki yaja ganin shi Affan ko a jikinshi sai rawan kai da yakeyi,
suna isa dai-dai inda Affan ke tsaye yarinyar na gefenshi cikin tsuke fuska Yusuf yasa hannu ya jawo hannun Affan d'in tare dayin k'asa da murya yace.
"Toh Namamajo ya isa haka zo mu tafi gacan Malam na isowa."
ido ya zaro tare da juyawa ya kalli inda Malam Jabeer yake, da sauri yabi bayan Yusuf d'in tare da cewa.
"Baby sai kinji ni, ki ajeyi wayarki kusa."
"ok bye ". tace mai tare da d'aga mishi hannu,
shi ko Affan sai cewa Yusuf yayi.
"Kai meya kawoka gunmu banza mai farin jini zakasa ta ganka tace ta fasa dani sai kai".
dariya Aryan yayi tare da cewa.
"tsoro kakeji karya rushema gomnatinka ko."
Safwan kam sai tsaki yaketa ja,
shiko Yusuf tuni ya saki hannun Affan yabi bayan Malam Jabeer dake juyowa yana kallonsu da alamar gargad'i su rik'e mutuncinsu.


Gurine na shakatawa sosai gurin yake da kyau a ido da kayatarwa saboda yadda aka k'awata gurin da fulawoyi da grass carpet ga wani sweaming fool da ruwa yake zubowa ta jikin duwatsu yana shiga cikin sweaming fool d'in, wani k'awataccen guri special Malam Jabir ya kama musu d'an k'aramin garden ne da aka k'awata shi da kujeru kamar na kaba amma masu kwari sai rumfa da take yanayi data bunu amma duk abubuwan an sarrafasu ne cikin zamani da burgewa gaba d'aya k'asan gurin grass carpet ne inda wasu fulawoyi green da pink suka kawata gurin sosai gurin zai saka nishad'i da farin ciki kukan tsintsaye da k'amshin furanni kawai ke tashi a cikin gurin ga yanayin iskar damuna dake kad'awa tana ratsa jiki da zuk'atan ma zauna wurin, cikin rumfar kujeru ne kusan guda 8 nan Yusuf, Safwan, Aryan, Affan, Malam jabir sai abokanan sa guda 3 suka zazzauna nan aka fara kawo musu kayan tab'a ka lashe su drinks da snacks cikin nishad'i sukecin komai da farin ciki,
Malam Jabir ne yayi gyaran murya tare da maida hankalinshi gasu Yusuf yana nazartan yanayin jin dad'i da suke ciki cikin kulawa yace.
"Na zab'i gurinnan ne na kawoku saboda da in sama muku farin ciki dan nima ba k'aramin farin ciki na samu kaina ba a bisa nasarar da muka samu a wannan gasar, ban tab'a zato ko tsammanin zamuci gasar nan ba in mukayi duba ga wad'anda aka gwabza gasar dasu amma Alhamdllh cikin *HUKUNCIN ALLAH* wanda shike baiwa bawan sa nasara a lokacin da yaso saiya nufe mu da lashe gasar". murmushi sukayi baki d'ayansu sannan Yusuf ya nisa tare da sad'a kanshi k'asa cikin sanyi murya da girmama abokin maganar tasa yace.
"Lallai Allah shine abin godiya a ko wanne yanayi wanda k'ok'arin ka ko dabarar ka baya saka ka samu abinda kake nema har saida ikon sa lallai Allah shine gagara misali sarkin buwaya da d'aukaka".
murmushi Malam Jabir yayi da gyad'a kansa abokanan Malam Jabir ma maganar da Yusuf yayi ya birgesu saboda gashi shine yayi k'ok'ari yaci gasar amma baya danganta nasarar da kanshi ya yarda Allah ne ya bashi ba wayon shiba lallai Allah yayiwa Yusuf baiwar daba kowa yake yiwa ba sai wanda ya zab'a acikin al'umma Safwan kuwa babu abinda yakeyi sai sak'e-sak'en yadda zai sa taurarin Yusuf su disashe a idon duniya.



Basu suka bar cikin Gamji ba sai gabanin Magrib kuma sun samu nishad'i da nutsuwa a cikin zuciyar su.



Washe gari 10:00am su Yusuf suka fito da shirin komawa garinsu Adamawa Yola inda dafifin jama'a sukayi musu rakiya harda *Kaduna Polo Team* saboda duk wanda zasu tafi inhar jirgi zasu hau sai sunyi musu rakiya har airport.




A can garin Adamawa kuwa
tuni labarin nasarar ta riskesu ko ta ina ka gifta posters d'in Yusuf ne da tambarin doki tare da kirarinshi Baraden Adamawa gidajen radio da TV duk an sanar da dawowarsu yau d'in.

Cikar matasa da wasu daga fadar mai martaba sarkin ADAMAWA sukazo tarbar su Yusuf jirgin su yana sauka bayan kamar minti 5 da saukar shi passengers suka fara sakkowa a hankali daga cikin jirgin a sannu Yusuf ya fara ziro k'afar shi ta dama sanye yake da rigar polo pink colour inda yake sanye da wando jeans black sai idonshi rufe cikin glass baki sai takalmi boot black sanye a kafar shi kanshi babu hula sai kwantaccen gashin sa na asalin fulani dake kyalli saboda yasha gyara hannun sa d'aure da agogon Gucci baki hannunshi d'auke da hand logadge yana ja, wani doguwar ajiyar zuciya yaja jinshi cikin garin shi a sannu yake sakkowa bayan shi Aryan ne sanye da irin dressing d'inshi sai dai shi yaja glass d'in idon nashi zuwa saman kanshi, sai Affan Safwan na binshi sai Malam Jabir a bayan shi suna gama sakkowa motar cikin airport ta kwashe su zuwa k'ofar da zasubi sujen wajen airport d'in.



Sanya k'afar Yusuf a k'ofar fita keda wuya nan yan jarida suka fara d'aukar su a video ba kakkautawa cikin farin ciki d'aya daga cikin 'yan jaridar ya saka loudspeaker a bakin shi yace.
"Wanne irin farin ciki kake ciki a bisa wannan nasara daka samu na wannan gasa da kukaje?".
sai kuma yayi maza ya maida loudspeaker d'in saitin bakin Yusuf murmushi Yusuf yayi had'i da shafa sumar kanshi da taune lips d'inshi na k'asa sai daya ja ajiyar zuciya cikin sanyi da tattausar lafazi yace.
"Alhamdulillah , Allah shine abin godiya mai bawa bawan sa nasara a lokacin da yaso tabbas farin cikin da muka samu kanmu nida 'yan uwana bisa nasarar da muka samu ba zata fad'u ba amma bahaushe yace labarin zuciya a tambayi fuska nagode".
zai k'ara masa wata tambayar ya d'aga hannun shi ganin yawan matasan da sukazo tarbar su.
yana gab da shiga motar da aka zageyeta da posters enshi yaji wani d'an jarida ya jefo mai wata tambayar daya kamata ya bashi amsa, ganin yadda ya juyo yasa dan jaridar k'arisawa gabanshi da sauri tare da cewa.
"Shin kanaga k'orewarka da iyawarkata kai matsayin da zaka iya wakiltan Nigeria a gasar da akeyi da South Africa?".
murmushi yayi tare da taune lip enshi cikin iya sarrafa harshe yace.
"Eh zan iya amman ba dan k'orewata da iyawa na ba".
da sauri wata kekyawar yar jarida mai suna Rahmatu Aliyu Garkuwa (Autarmu) ta matso tare da jefamar tabbayar.
"Toh me yak'ininka da kace zaka iya, bayan kuma kace baka yarda da iyawarka ba so me madogarka?."
cikin sanyin murya yace.
"Allah! dashi na dogara domin shike bada nasara kuma duk inda nake yana tare dani, sanna inada yak'ini da Addu'ar Mahaifiyata wacce take k'are ko wani motsinta da ambaton Allah tare da yiwa Yusuf d'inta Addu'a, sannan inada tabbacin ink'ataccen horasawa daga shugabana Malam Jabeer so ina kyautata zaton iya shiga gasar ko wacce k'asa."
murmushi yar jariar tayi dan jin dad'in amsar shi da gamsuwa cikin sauri ta kuma magana dan ganin ya bud'e marfin motar ya shi da sauri ta sunkuyo tare da cewa.
"Me zaka cewa masoyanka da suke ganin ka a akwatunan talabishen ensu a gida a halin yanzu da ake nunaka live da kuma masu jinka a radio."
murmushi yayi jin ance live ake ganinshi glasses insha ya cire cikin sanyi ya d'an sunkuyo tare da cewa.
"Mamah! Mamah!! Maman Yusuf nasan kina ganina yanzu haka na kuma san duk duniya kinfi kowa sona kuma kinfi kowa farin cikin wannan nasarar da muka samu."
sai kuma ya lumshe ido tare da cewa.
"Ana uhubbuki hubban azeem ya Ummi Maman Yusuf kinga Addu'arki tana bibiyar Yusuf d'inki ko? Ngd matuka Mamana."
cikin jin dad'i da matuk'ar burge yan jaridan suka had'a baki wurin cewa.
"Sauran masoyan kafa?".
murmushi yayi tare da cewa.
"Ina godiya a gareku masoya na Ngd Ngd Ngd matuka Allah bar zumunci da qauna."

koda akaje kansu Aryan, Affan, suma sunyi nasu jawabin amman Safwan ko kulasu baiyiba,
malam Jabeer kuwa sai jinjinawa yaran nashi yayi.



Mama dake gaban t. v tana kallon abinda ke faruwa a airport d'in saboda live ake nunawa batasan lokacin da hawayen farin ciki ya wanke fuskar taba tace.
"Alhamdulillah Allah ka karawa annabi daraja, Allah ka kara d'aukaka min Yusuf na kasa ya ya zarta duk tunanin mai tunani".
tsakin da Abba yaja shiya ankarar da ita ashe yana gurin dan ita tama manta shauk'i da mararin ganin shalelen idanuwan ta ya rufe mata ido.

Zulaihat ma sai murmushi takeyi a parlour ta ita d'aya ganin d'an k'aninta a tv

Su Ummi da Anty Amarya ma duk suna gani hakama Daddy a office nashi yake gani da yake shi tun randa aka gama gasar ya dawo kasancewar ana nemanshi a asibitinsu dan wani aiki da zasuyi na dashen zuciya,
su Goggo Aisha ma duk sun gani dan Goggo Madina cema ta kira Maman Yusuf d'in a woya tace ta kunna TV .

Ci gaba da nuna abinda ke faruwa akayi inda su Yusuf suka shiga motar da zata kaisu fadar mai martaba sarkin ADAMAWA Yola sukai gaisuwa daga can kuma kowa ya tafi gida,
motacin dake bin bayansu na samari yan tarosu sunfi 40 ga da wakai sama 50 yan sauran teams na polo na jihar ga wasu daga masarautar sai kad'e-kad'e da bushe-bushen algaita da sarewa dake tashi har fadar mai martaba sukayi musu rakiya inda sukuma suka kai gaisuwa fada daganan aka kai kowa gida.



Zaune su Yusuf suke a parlourn Hajiya Kaka suna d'an tab'a abincin data shirya musu, dan a k'oshe suke sunci abinci a fadar jiha,
tsakura suke d'anyi suna hira da bata labarin yadda gasar ta kasance Aryan ne ya takarkare yake bata labarin irin yadda Yusuf yayi musu bajinta sukaci gasar dan harsun fidda rai dad'i sosai takeji a ranta.



Ganin dare ya farayi ya sakasu Yusuf yiwa Hajiya Kaka sallama suka mik'e zasu fita, ido Kaka ta tsura musu tare da cewa
"Yusufa har yanzu cinyoyin ciwo suke makane".
kai ya gyad'a mata alamar eh,
Aryan ne ya d'an juyo tare da cewa.
"Kaka ai duk wanda yasan hawa doki to yasan akwai wuya bayan ka sauk'a duk cinyoyinmu sai suyi ta cowo." sannu tace musu tare da cewa susha mgnin gajiya, toh kawai suka ce mata
suka tafi part d'insu.



Sanadin wannan nasara dasu Yusuf sukayi ya saka sunanshi yad'uwa a cikin ADAMAWA dama Nigeria ko ina cikin gungun samari labarin Barde akeyi dan yayi k'wazo ya nuna kwarewar shi wajen sarrafa doki da polo stick da polo ball.



Saida sukayi sati da dawowa yau Jummu'a ya kama ranar k'warya-k'waryar liyafar ban gajiya da Malam Jabir ya had'a musu tare da sauran teams gaba d'aya dan zaburar dasu.

Shiga ta alfarma Yusuf da Aryan sukayi cikin brown rigar polo da milk jeans sai takakmi boot brown inda suka saka milk din P-cap agogon hannunsu brown sai turarukan da sukayi bari a jikin su sosai wankan yahau da fatar jikin su kai tsaye Hajiya kaka sukaje suka yiwa sallama,
cikin k'aunar jikokin nata Hajja Kaka tace.
"Kai Masha Allah kunyi kyau, amman dai da manyan kaya kuka saka da kunfi hakayin kyau da kamala".
dariya Aryan yayi had'i da had'a hannushi ya tafa yace.
"Kajimin Hajiya Kaka wannan wankan shi ake kira da wankan sukari yanzu zakisa Yusuf ya fasa dan dama da keret nashi ya yarda".
hab'a Hajiya Kaka ta kama tace.
"iyeee kajimu dan ja'irin yaro" dariya sukayi suka fita kai tsaye machine d'insu suka hau Yusuf na tuk'awa Aryan yana baya kana kallonsu zakayi tunanin 2wice ne sai dai inka zuba musu idanu zakaga basa kamanni dan kowa da irin kyanshi.



Cike hall d'in Lamid'o sinima da suka kama cike yake da jama'a dan harda masu fad'a aji na cikin ADAMAWA aka gayyato bayan bud'e taro da addu'a jawabin godiya Malam Jabir ya gabatar na kokarin dasu Yusuf sukayi har suka ciyo musu kofi nan aka raba musu a word tare da kyaututtukan da suka samu bayan an nutsa Malam Jabir ya k'ara d'aukar loudspeaker tare yin gyaran murya cikin sanyin yanayinshi yace.
"Dangane da bajinta da k'wazon da Yusuf ya nuna an samu wani bawan Allah daya nemi a sakaya sunanshi ya d'auki nauyin karatun shi duk k'asar da yakeso tare daduk wasu kudaden da zaiyi amfani dasu a k'asar da zaije, sannan kuma da damar yin karatu a kan ilimin polo na shekara d'aya ,in ya gama sai ya karanci duk abinda yake so".
tafi aka k'ara d'auka sosai Daddy yayi farin cikin nasarar da d'an d'an uwannashi ya samu zaiso ace Abban shi yana gurin yaga irin abin alkhairin da yake bibiyar d'an nasu nan taro ya watse cikin farin ciki da annashuwa kowa yana san barka banda Safwan da yake ganin kamar da biyu akayi abinnan babu wani daya d'auki nauyin karatun Yusuf shugaban team d'inne,
gaba d'aya hasada tasa ya manta *HUKUNCIN ALLAH* rubutacce al'amarine shine mai bawa wanda yaso a kuma lokacin da yaso.




Lokacin da Daddy ke bawa Mama labari batasan lokacin da kukan farin ciki ya b'alle mata ba cikin rawar baki tace.
"Yauwa kiramin shi nayi mishi murna".
wayarshi ya d'auka ya kira Yusuf a lokacin suna tsaye suna shirya kyaututtukan da suka samu acikin show glass din da suka siyo dan adana kyautar su ganin Daddy ke kiranshi da sauri ya ajiye karamin cup mai tambarin doki d'in dake hannun shi ya d'aga,
jin muryar da yake tsananin kewa da marmarin ji a koda yaushe shine ya saka shi jan ajiyar zuciya yace.
"Maman Yusuf?" dariya Mama dake manne da waya a kunnenta tayi ta dad'a k'ank'ame wayar tamkar za'a kwace mata ita,
Daddy dake kallonta kuwa tausayinta ne ya kamashi yasan tana kewar Yusuf dan duk da yana d'a namiji shak'uwar da sukayi tafi shak'uwar da Mama da Zulaihat sukayi saboda ita Zulaihat a hannun Hajja Inna ta tashi,
cikin farin ciki tace.
"Yusuf d'ina kun dawo lafiya?".
gashin kansa ya shafa sosai yakejin soyayyar Maman nashi na shiga k'ashi da b'argon shi cikin lumshe ido yace.
"Lafiya k'alau Maman Yusuf sai tsabar kewar ki data dabaibaye ni".
murmushi tayi tare da cewa.
"Maman Yusuf ma tananan tana kewar shi kuma har yanzu bata bar kai kukanta wajen Allah ya dawo mata da Yusuf dinta gareta ba................" sai kuma kuka ya kwace mata cikin tashin hankali da tausayinta Yusuf yace.
"Haba Mama har yanzu baki bar kukan nanba nifa lafiya ta k'alau kuma ina samun kulawa kamar ina tare dake, ba kin ganni a tv ba nayi k'ato na k'ara tsawo ko?."
murmushi tayi had'i da share hawayen tace.
"A a kam kadai yi kyau kam matuk'a amman ba k'atoba,
ai in kayi k'ato ka tsufa kenan."
maganganu masu dad'i ya dinga fad'a mata har saida yaji kukan nata ya koma dariya,
anan take sanar mishi itama zasuje Umrah in sha Allah zatayi kokari su hadu kafin su tafi,
addu'ar zuwa lafiya dan dawowa lafiya yayi musu da nuna mata shima zaiso su had'un domin ya ganta.



Bayan gama wayar tasu komawa yayi ya kwantar da kanshi ajikin kujera had'i da lumshe idon shi abubuwa da yawa ne suka dinga dawowa cikin rayuwar shi yasan tabbas da ace yana gida tare da iyayen shine tom da dashi zasuje Umrah nan tom amma dokin zuciya ya kaishi ya baroshi.



Zaune suke a parlourn Hajiya Kaka cikin murna Aryan ya kalli Kakarta tasu yace.
"Hajiya Kaka mun samu abin farin cika fa saboda k'wazon da Yusuf ya nuna a gurin gasar nan ya samu wani ya d'auki nauyin karatun shi duk k'asar da yakeso zai je cikin k'atsashe ukun nan da
America, Argentina, ko South Africa".
cikin sanyin jiki da rashin jin dad'i Yusuf yace.
"Kai nifa na fad'a maka bazani ba gwanda ka daina maganar nan dan ba inda zanje".
cikin mamaki Hajiya Kaka ta kalleshi tare cewa.
"A'ah Yusuf ya kake irin wannan maganar abin alkhairi ya tunkaro ka kace bakaso a a kar kayi haka kul dama ba'a meda hannun kyauta baya".
langwabe kai yayi cikin sanyin murya yace.
"Bazan iyaba Hajiya Kaka ya za'ayi ace saini kad'ai za'a biyawa ba dasu Aryan Safwan Affan d'in mukayi gwanintar ba in biyanne a biya mana gaba d'aya mana saini kad'ai ni babu inda zani nabar Aryan".
murmushi Hajiya Kaka tace. "In saboda wannan ne ka kwantar da hankalin ka kawun Aryan yasha min maganar ya kamata ya tura Aryan kasar waje karatu amma saboda shak'uwar dake tsakanin ku ya sakani dakatar dashi amma tunda haka ya faru zance na amince yanzu sai ku

Please Login or Register in order to submit comment