Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wayar da sauri ya mik'awa Mama daketa binsu da ido tana jin farin ciki na ratsata tako ina,
wayar na hannunshi ya nuna mata,
sai ya kuma juya a guje yayi parlour Mama gaban Zahra ya tsaya tare da mik'a mata wayar yana fad'in.
"Ammi kalli Abban Yusuf yamin hoto a wayarshi."
cikin tsananin mmki ta karb'i wayar tare da zuba mata ido yau wacce rana Abba dai ya sakarwa Aryan fuska har da d'aukarshi hoto kuma harda bashi wayar,
kai ta jinjina tare da jawoshi jikinta ruggumeshi tayi tare da sauke ajiyan zuciya,
dan haka nan take jin fargaba tsoro takeji dan tana ji a jikinta kamar za'a rabata dashi,
shi kuwa Aryan da sauri ya zame yana cewa.
"Ammi sakeni bari inje in nunawa Daddy."
sakeshi tayi shiko ya fice da gudu abinshi.

Hajja inna kuwa da Ummi da Goggo Maimuna,
a radio Hajja Inna dukeji,
lbrin dawowar Yusuf jin haka yasa Goggo Maimuna tashi da sauri ta kunna tv d'ai-dai lokacin da wani d'an jarida ke bin bayan Yusuf tare da cewa.
"Masoyanka sun zak'u suji ta bakinka,
fatansu kar kayi ma al'ummar k'asarka cinikin goro."
murmushi Yusuf yayi domin shi dai ba bahaushe bane ba fullatanine,
shiyasa bai gane mgnarba,
hakan yasa ya juyo tare da gyara tsayuwanshi jikin motor dake bayanshi yayinda Affan da Sultan ke gefenshi sai Aryan Babba da Matawalle.
cikin sanyin murya yace.
"Hausar tayi min tsauri,
menene cinikin goro?."
cikin jin dad'i d'an jaridar ya matso tare da cewa.
"Ma'anar cinikin goro, masoyanka na tsoro kada kayiwa al'ummar k'asar taka kallon duk mak'iyanka ne duba da abinda ya faru da kai shekaru hud'u da suka gabata."
Gyara tsayuwanshi yayi tare da lumshe ido sai ya kuma bud'esu a hankali murmushi yayi har saida hasken hak'oranshi ya baiyana,
murya ya gyara tare da cewa.
"Toh in dai zanyi tunanin bani da masoya a k'asata ,
asheko zanyi tunanin bani da masoya a duniya baki d'aya."
cikin sauri d'an jaridar yace.
"Masoyan naka zasu so k'arin bayani daga gareka?."
kanshi ya rusunar tare da cewa.
"A k'asata nakeda masayon da zasu zubda hawaye domin rashin nasarata,
a k'asata nakeda masoyan da sukeyi min addu'ar Allah ya tsareni ya bani nasara a dukkan sallolinsu,
a k'asata nakeda masoyan da son da sukemin baya hanasu hukuntani duk girman laifina dana aikata."
sai ya kuma rumtse idonshi tare da cewa.
"Duk fad'in duniya bani da inda nakeda masoya masu rufa min asiri da boye laifina koda zasu rasa martabarsu sai a k'asata Nigeria."
ido d'an jaridar ya lumshe tare da cewa.
"Zako muso sanin suna yensu."
kai ya rusunar tare da cewa.
"Wani sunan bazai fad'uba domin yayiwa harshe na nauyi,
amman a sashin forko a k'asata nakeda mahaifiya Maman Yusuf da mahaifi Abban Yusuf kaga duk duniya bani da masu sona sama dasu,
kunga kenan babu dama in yiwa Al'ummar k'asata cinikin goro."
da sauri ya matso da nufin zai k'ara mishi wata tambayar sai ya kuma komawa baya sabida tuni masu tsaron Yusuf sun tareshi,
Affan kuwa mota ya shiga tare da cewa Yusuf ya shigo,
haka kuwa akayi Yusuf na shiga yaja marfin ya rufe,
Sultan kuwa da Jafar mota d'aya suka shiga,
Aryan da Matawalle suma mota d'aya suka shiga sai sauran tawagar,
da suka shisshiga sauran motocin,
yayinda masu dawakaima tuni suna harabar Airport d'in,
kai tsaye Dou Girei suka nufa,
inda gidajen manya suke,
anguwace ta algarma,
tafiya sukeyi a jere a jere yayinda tawagar matasan gari ke musu rakiya uwa uba yan polo,
dole suna isa cikin unguwar aka fara tagiyar nitsuwa sabida,
nistsiyar unguwace da take cike da tamfatsa-tamfatsan gidaje na alfarma,
ko ina tsif sai wani irin sanyi da k'amshi furanni da unguwar keyi kasancewar mafi akasarin gidajen akwai lammu a cikinsu,
ga yanayi na damu ko wane ganye yayi kore shar yanata k'awanya,
yayinda iskar damuna take kad'awa tana ratsa jiki da zuciyar duk wanda yake wurin.
wani tamfatsetsen gida naga sun tsaya a bakin gate d'in wanda bayan ya dak'ik'u kad'an sai gashi ya bud'u da kanshi bisa dukkan alamu da na'irar masarrafi yake aiki,
a jere motocin suka kutsa kai cikin harabar gidan inda sukayi gefen parking lot,
inda a k'alla zai d'auki motoci 16,
daga gefen dama kuwa wani k'aton wurine bisa dukkan alamu tirken dawakaine,
hakan yasa wani daga cikin buzayen dake zaune a gefen gate d'in,
sukaje suka bud'e musu wata y'ar k'ofa nanfa masu dawakan suka rink'a shiga ciki.

Su Affan kuwa bayan sun gama shiga,

Bada jimawa ba,
aka kira sallan la'asar a masallacin cikin gidan Yusuf d'in,
nan wasu sukayi al'wala a pompunan dake jere a harabar,
su Affan kuwa a ciki sukayi al'awala sannan duk suka fita sukaje masallacin da yakeda girma nan sukayi jam'i,
bayan an idar da sallan ne duk suka shiga cikin gida cikin wani tabkeken parlour duk suka shiga inda daba an tsareshine dan irin haka,
liyafa me zaman kanta akayi, wacce take gauraye da walima,
Yusuf kuka duk ta inda ya juya masoyane keyi mishi son barka,
yayinda shiko duk hankalinshi na kan Jafar,
hannu yasa ya yafito Sultan tare dayin k'asa da murya yace.
"Kira min Jafar."
hararanshi Sultan yayi tare da cewa.
"Ni da kai wayafi kusa dashi."
tsaki ya d'an ja tare da cewa.
"Ni bazan iya ihuba bakaga yadda yake ta fama da surutuba in ba ihu akayiba ba ji zaiba."
cikin dariya sultan yace.
"OK wato nine zararre mai ihu."
Murmushi ya d'anyi tare da taune gefen lips enshi na k'asa cikin sanyi yace.
"Please kira minshi."
Affan ne ya kallesu tare da cewa.
"Abu mai sauk'i a kirashi ta waya mana."
cikin d'an tab'e baki Yusuf yace.
" ai ni nabar phone d'in a bedroom."
shi kuwa Sultan tuni ya kira Jafar,
har ya iso inda suke,
kai ya sunkuyar gab da Yusuf yace.
"Hamma Yusuf gani ya Sultan yace kana kirana."
jingunuwa yayi da jikin kujerar tare da cewa.
"Kaje ka kawo min Aryan."
toh yace tare da mik'ewa,
cikin abokan nashi ya juya ba jimawa kuma ya fita.

Su kuwa nan akaci gaba da hark'alla yayinda shugannin teams da dama suka nemi sa hannun Yusuf,
shi kuwa cikin mutuntaka yake samusu,
ya kuma bada kyautukan girma ga dukkan wakilan teams d'in.

Jafar kuwa,
yana isa gida ya samu dama tuni shi Aryan ke jira,
cikin happy yace.
"Yauwa b'ingel zomu tafi da sauri."
mik'ewa yayi tare da cewa Zahra.
"Ammi na tafi."
cikin sauri ta kalli Jafar tare da cewa.
"Ya Jafar ina zakuje?."
kamo hannun Aryan yayi tare da juyawa suka kama hanyar fita cikin sauri-sauri yace.
"Zamuje unguwa ne anjima zamu dawo."
kai ta gyada alamar to duk da cikin tanta bataso hakanba,
a sanyaye ta kalli Dija dake gyara mayafinta,
"Dan Allah ki bari sai munyi sallan isha kafin nan Ya Jafar ya dawo Wlh zamu rakaki har gida."
Kai ta juya tare da cewa.
"Tab ai Hajia ta zatayi fad'a,
ke dai sai munzo shagalin birthday."
murmushi tayi tare da cewa.
"Hmmm bafa wani shagali."
"Saifa anyi shagali kam".
cewar Dija lokacin da suka fito tsakar gida,
inda ta samu su Mama,
sallama tayi musu sannan Zahra ta rakata har bakin gate kana ta dawo.

Hajja inna kuwa sai k'ada kai take tana cewa.
"Yanzu dai babu inda Yusufa zai kuma fita k'asashen turawannan ya isheni haka ace kullum yaro shi baya cikin yan uwanshi."
tab'e baki Zahra tayi tare da girgiza kai tace.
"Jita kamar gaske yo koma menene ai ke kika jamishi,
tunda kece kikasa aka koreshi,
dan haka kece kika fiddashi dangi."
cikin hayagaga ta bi bayan Zahra tare da cewa.
"Shegiya mai tsiwar tsiya zanyi mgnunki kedashi baki d'aya."
shigewa part d'in Mama tayi ba tare da ta kuma bin ta kan hajja innaba,
Ummi kuwa yanzu haushin Hajja inna takeji yadda take nuna tana son Yusuf,
shiyasa taja tsaki tabar wurin
Goggo Maimuna kuwa dariya tayi tare dayi musu sallama ta tafi,
Mama kuma da Aunty Amarya hirarsu sukaci gaba dayi kan Yusuf.


A can Girei kuwa bayan duk an watse saura makusanta,
dole Aryan babba ma ya tafi dan Affan ya kasa ya tsare,
motsi kad'an sai ya gaya mishi mgna,
Jafar kam babu abinda yafi d'aure mishi kai kamar ganin yadda Aryan ke tare da Matawalle,
shi kuwa Sultan idi ya sawa ido,
yana mmkin yadda Yusuf ya saki jiki dashi,
bayan Aryan da Matawalle sun tafine shima idi ya mik'e tare da kallon Yusuf yace.
"Toh nima bari in wuce gida dan dare ya fara nisa."
jin haka yasa Yusuf mik'ewa tare da kamo hannun Aryan dake kan cinyarshi,
juyowa yayi wurin Affan yace.
"Yauwa Affan bani key d'aya na wad'an can motocin."
mik'ewa shima Affan yayi tare da zaro key d'in a aljihunshi amsa Yusuf d'in yayi tare da bawa Aryan k'arami yace.
"Yauwa Aryan jeka bawa bappa idi key d'inna ko."
ai da sauri yaje gaban idi tare da mik'a mishi yace.
"Bappa idi gashi inji Abeeh."
cikin mmki Idi ya kalli Yusuf tare da cewa.
"Yusuf mota guda."
Kai ya jinjina mishi alamar ba komai,
cikin jin dad'i yace.
"Ngd Ngd Ngd matuka Allah ya bar zumunci da qauna Yusuf Allah ya k'ara bud'i."
sai ya kuma kalli Affan da Jafar yace.
"Dan Allah ku tayani godiya."
cikin sanyi Affan yace.
"Mune da godiya idi, Allah ya bar k'auna."
Amin Amin sukace baki d'aya kana Jafar yaje ya nuna mishi motar.

Nan sukaci gaba da hira,
sai kusan k'arfe sha d'aya Affan ya kira fadawanshi sukazo daukarshi,
tare suka fita harabar gidan har ya shiga mota sai ya kuma fito tare da cewa Yusuf.
"Kafa kula da sabon abokinka maci amanar nan,
ni tsoro yake bani."
cikin sakin fuska Yusuf yace.
"Toh naji Abban Yusuf."
dariya sukayi baki d'aya sabida yadda yayi mgnar ya nuna Affan na mishi fad'a kamar shine mahaifinshi,
bayan Affan ya tafi Jafar ma yace zai tafi da Aryan ai kuwa Yusuf ya hana,
wai su kwana nan shi kuwa Jafar yasan sarai yau Zahra bazatayi bacciba gashi tun d'azu sai kiranshi take.
dole ya hak'ura ya tafi ya bar Aryan a wurinshi yasan in ya kwana a nan bai komaba Umminshi sai ta kusan tsine mishi yanzuma zaginshi takeyi waishi shi baida zuciya
ya nacewa yan iska.

So dole ya koma.

Gida ya rage daga Yusuf sai Sultan da Aryan k'arami,
sai can gefen masu kula da gidan kuma buzayen su biyu yaya da k'ani sai matar yayan,
su dama sun dad'e a gidan.
shi kam Sultan tuni ya tafi makoncinshi,
shi kuwa Yusuf,
shida Aryan bayan ya mishi wonka ya canza mishi kaya kana shima yayi wonka,
konciya Yusuf yayi tare da jawo Aryan cikin sauk'e ajiyan zuciya yace.
"Zo muyi hira in baka jin bacci."
kai ya jinjina cikin yin rau-rau da ido murya na rawa yace.
"Ammi, Ammi na."
da sauri ya tashi zaune tare da cewa.
"Karkayi baka ga Abeehnka ba,
gaya min me kakeso?."
cikin share hawayenshi da suka zubo yace.
"Abeeh ka kira min Ammi na,
zan ce mata tayi bacci ni yau a nan zan kwana,
nasan yanzu tana can tana jirana."
gyara zama yayi tare da cewa.
"Oho ai na gayawa Uncle Jafar ya gaya mata kuma,
har tayi baccin ma,
tama ce a gaya maka kaima kayi baccinka lfy."
kai ya jinjina cikin yarda sai ya kuma jujjuya kai tare dayin k'asa da murya yace.
"Abeeh."
cikin jin k'aunar yaron na k'ara ratsashi yace.
"Na'am Aryan."
cikin fidda ido yace.
"Abeeh kaima baka da matane."
ido ya zubawa yaron cikin tsananin mmki tare da mutuwan jiki,
muryar yaronne ya kuma katseshi da maimata tambayar,
cikin sanyi ya gyad'a mishi kai alamar eh baida mata.
Shi kuwa Aryan gyara zama yayi tare da cewa.
"Malamin isilamiyarmu ya tab'a ce mana,
wai darajar mutun bata cika har sai in yayi aure,
to shine ranan nacewa Ammina tayi aure ko za'a dena ce mata karuwa,
sai tayi ta kuka,
kuma kaga Uncle Affan ya d'auki Anty Mami Anty Zeenat ma tayi aure hakama Anty Nana,
duk basa gida sai Ammi na kawai kullum Ummi tayi ta ce mata yar iska,
kuma Uncle Jafar yace min in ka dawo zaka d'auke Ammina za'a dena zaginta."
sai ya kuma yi shiru tare da zubawa Yusuf ido cikin zubda hawaye yace.
"Abeeh dan Allah ka d'auki Ammi na,
kasata ta dena kuka."
ganin shiru Yusuf bai kulashiba sai ya fara zubda hawaye tare da cewa.
"Kaima baka sonta irin Uncle Suleiman ko?."
ido ya k'ara zuba mishi tare da nazartan kalaman yaron,
shi kuwa Aryan cikin muryar
kuka yace.
"kullum Ammina sai tayi kuka,
in munzo konciya tana cemin,
kowa baya sonta harda Aunty Amarya,
Ammi na tana cemin mahaifina.........



By
*GARKUWAR FULANI*


[23/01 2:38 PM] My 2nd Mtn: [1/20, 1:22 PM] sbp eh
ddwl



*HUKUNCIN ALLAH*



*PAGE 12*




"Ba d'an iska bane, shi tsarkakkene mai kakykyawar zuciya shi muminine mai cikar nagarta.
Allah ne ya ya jarabceshi da jarrabawa mai zafi,
Ammi na tana yawan cewa kada in tuhumi mahaifina domin bisa dole da kaddara ya samar dani ta wannan hanyar."
Ruggumeshi yayi tare da lumshe idanunshi wata iriyar ajiyar zuciya yake sauk'ewa a jere a jere,
Sannan ya rink'a gyad'a mishi kai alamar gamusuwa,
shi kuwa Aryan ganin yanayin Yusuf ya sauya sai yace.
"Abeeh zanyi bacci "
kai ya jinjina tare da gyara pillows d'in ya kuma kwantar dashi tsakiyarsu,
sannan ya sunkuyo kanshi ya manna mishi kiss a goshi tare da cewa,
"Good night my Aryan."
da sauri ya mik'e zaune tare da cewa,
"Nida Ammina in zamiyi bacci tare muke kwanciya kuma a jikinta nake bacci,
sai tayi mana addu'a ta shafa mana nida ita."
jin haka yasa Yusuf kwanciya tare da jawo Aryan bisa k'irjinshi,
cikin sanyi da kalaman yaron ya sakar mishi murmushi yace.
"Zo nan ka konta jikin Abeehnka,
zan maka duk abinda kakeso matuk'ar baifi k'arfina ba."
kwanciya yayi luf a jikinsa, yayi musu addu'a tare da jawo musu blanket ya rufesu.




Zahra kuwa gaba d'aya ta gaza bacci sai juyi takeyi,
tunda take Ya Jafar bai tab'a mata abinda ya k'ona mata raiba sai yau,
shima kuma yaga haka domin tunda yazo yace mata ai Hamma Yusuf yace a bar Aryan a can bata kuma ce mishi komaiba,
sai juyawa tayi ta shiga bedroom tana sherte hawayenta.

Ido ta lumshe tare da yin juyi a kan gadon tare da share hawayenta,
so take taga gudan jininta kusa da ita, kuma gashi ya mata nisa,
cikin sanyi tace.
"Aryan meyasa ka yarda ka kwana a can,
alhalin bamu tab'a raba makonciba."
sai ta kuma tashi zaune ta jingina da jikin gadon tare da jawo pillow ta ruggumeshi,
sannan ta lumshe idonta,
addu'a ta rink'ayi a hankali har dai ta samu bacci ya d'an fizgeta,
batafi 40 minutes ba dayin baccin sai ta kuma farkawa jiki na rawa sabida mafarki da yayi,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi yayinda hawaye ke bin fuskarta,
kai taketa jujjuyawa alamun a a,
ganin hakan bazai ficcetaba ta mik'e ta shiga bathroom al'awala tayi kana tazo tayi ta nafilfili,
daren ranarda bata samu tayi bacciba har zuwa asuba.

Bayan an idar da salla,
sai ta fito parlour ta zauna ta zubawa k'ofar shigowa ido kamar zata shigowar Aryan d'in kamar kullum,
ganin babu alamarsa sai ta mik'e jiki a mace ta shiga kitchen ta fara aikin breakfast,
ta shiga bada jimawaba Mama tazo nan take cewa.
"Yauwa Zahra kin tashi ko."
Kai ta gyad'a mata kana tace.
"Ina kwana Mama."
"Lafiya lau ya kewar Aryan?."
kai ta sunkuyar tare da k'ok'arin maida hawayenta tace.
"Mama banyi bacciba wlh,
ko yanzu sai in rink'aji kamar mgnarsa."
cikin yin murmushi Mama tace.
"Kinga ni banyi zaton zai yarda bama,
yanzu maza ki had'awa Hammanku breakfast in Jafar ya kai mishi sai ya dawo da Aryan d'in."
To tace cikin jin kwarin guiwa,
sannan ta fara aikinta da d'an sauri ta had'a mishi abinci kusan kala 3 sannan ta dama mishi kunun gyad'a,
bayan an gama komai Jafar yazo d'auka,
cikin sanyi da d'an kawaici tace.
"Ya Jafar ko baka kira inji muryarshi kafin kaje."
dariya ya mata tare da cewa.
"Hmmmm kin san Hamma Yusuf ba mmki baima bud'e wayarba ki dai bari sai naje."
Kai ido ta d'an rufe tare da cewa.
"Ai in kaje tare zaku dawo ko?."
mik'ewa yayi tare da cewa.
"In Hamma ya yardaba."
jin haka sai ta tsuke fuska tare dayin cikin d'akinta ,
Mama kuma dariya ta d'anyi kana ta kalli Jafar tace.
"Kafa dawo tare dashi."
to yace tare da ficewa ya tafi.


Yana isa gidan tun a harabar gidan ya hango Yusuf kan doki yayinda Aryan ke gabanshi,
amman shi Aryan ya fuskanci Yusuf d'inne kuma ya ruggumeshi gam-gam da hannu bibbiyu,
shi kuwa Yusuf hannunshi d'aya rige da linzamin d'aya kuma yasa ya tallabe Aryan d'in,
sai sukuwa yakeyi da dokin,
yayinda yake cewa Aryan.
"Bud'e idonka kaji bazaka fad'iba,
kaga kalli can Uncle Jafar yazo."
jin haka yasa Aryan cewa.
"Abeeh mu sauka."
dariya yayi tare da cewa.
"Toh Aryana Abeeh sauk'o."
tsaida dokin yayi tare da saukowa sannan yasa hannu ya saukoda Aryan,
dariya ya kyalkyala tare da nufan inda Jafar yake da gudu yaje wurin Jafar,
yana isowa Jafar ya d'agashi sama tare da rungumeshi,
cikin meda numfashi yace.
"Uncle Jafar ina Ammi na bata zo bane?."
medashi yayi kan wuyanshi tare kallon Yusuf daya iso gunsu kana yabawa Hamma Yusuf d'in hannu suka gaisa.
bayan sun gaisa ne ya sauko Aryan,
sannan yaja hannunshi sukaje wurin motar,
kulolin abincin ya firfitarta,
k'aramar kular Aryan d'in ya mik'a mishi tare da cewa.
"Ga breakfast naka inji Ammin ka."
amsa yayi da sauri tare da cewa.
"Jazakallahu khairan."
sai ya kuma kalli Yusuf dake mik'o mishi hannu alamar ya bashi kular.
mik'a mishi yayi tare da cewa.
"Zakaci ko Ammi na tafi Maman Yusuf iya girki."
dariya yayi tare jawo hannunshi sukayi cikin gida sunkuyowa yayi ya kalleshi tare da cewa.
"A a wlh bazan yardaba Aryan Amminka batafi Maman Yusuf iya girkiba."
had'e fuska yayi ina dalili za'ace Amminshi bata iya girkiba,
suna isa a tsakiyar parlour suka zub'e bisa carpet,
yayinda Jafar keta shigo da abincin,
jafar na zama sai ga Affan da
ba jimawa sai ga Aryan kamar had'in baki kuma saiga Faisal,
lokaci d'aya parlour ya cika nanfa suka cikawa Yusuf gaba da abinci iri-iri
shi kuwa Yusuf kulan Aryan k'arabi ya jawo tare da fuskantar shi,
ganin har yanzu fushi yakeyi,
bud'e kular yayi,
murmushi yayi tare da kallonshi yace.
"Eyeh duka wannan kai kad'ai,
lallai Amminka na sonka,
to ni ina nawa?."
cikin jin dad'i ya matsoshi tare da cewa.
"Ai namune mu biyu,
muci zai ishemu kaji ko Abeeh."
kanshi ya shafa alamun gamsuwa sannan ya zare d'an filas d'in dake manne da yar kular,
bud'ewa yayi dan ganin menene a ciki,
ido ya lumshe jin k'amshin citta da kanamfarin da aka tafasa tea d'in dashi,
kana sai ya bud'e yar kular indomi ce a ciki wacce aka tafasata kana aka tsalub'e nawan kaza,
sannan aka jajjaga attaruhu da albasa,
sai aka had'eshi da daddageggen naman kazarnan sai aka fatsa kwai aka saka kayan had'i sannan aka juye indomin a ciki aka soyashi felle-felle kamar yadda ake soya kwai,
gaba d'aya parlour ya cika da k'amshi,
cup ya yawo sannan ya zuba mishi tea d'in shi kuma ya d'an tsiyayi kunun gyad'an,
sannan ya Jawa kular gabansu yace.
"To muci inji iya girkin Amminka d'in."
aifa da sauri ya matso suka fara ci,
Affan kuwa sai harar Aryan Babba yakeyi,
shiko Aryan abincin yaketa zuzzuba musu,
nan suka zauna sukayi breakfast yayinda kowa kecin abinda ranshi keso,
Affan ne ya mik'awa Yusuf kofi tare da cewa samin kununnan,
Jafar kuwa cewa.
"Aini bani ba sake shan kunun gyad'a wlh."
cikin mamaki Yusuf yace.
"Meyasa?."
kai ya jujjuya tare da cewa.
"Uhummm kawai dai tunda nasha wani lokaci daya wuce irin haka,
sai ya jaza min matsala a ranar wuni nayi bani da sukuni."
dariya Affan yayi tare da cewa.
"Wannan kai kenan aini yanzu inada masauk'i bani da fargaba."
Kauda kai Yusuf yayi tare da nitsawa alamar,
shiga dogon nazari,
Sultan kuwa cewa yayi.
"Hmmm ni daman can kunu ba cimata bane."
Aryan kuwa ido ya zubawa Yusuf cikin alamun mgna da ido,
kai Yusuf d'in ya jinjina mishi tare da cewa.
"Ya dai?."
ido ya lumshe kana yace.
"Ba komai nazari nakeyi."
Aryan k'arami kuwa ganin Yusuf bai fara ciba yasashi sa hannunshi ya jawo na Yusuf yasa a cikin kularshin,
ganina haka ya d'an yagi gefen indomi yasa a baki,
wani irin lumshe ido yayi tare had'iye yawun daya tsinko mishi,
shi kuwa Aryan k'arami dariya yayi tare da cewa.
"Abeeh yayi dad'i ko?."
ina Yusuf ya kasa mgn sabida sai yawunshi keta tsstsafowa,
dad'in abincin na ratsa mishi harce,
ganin haka Aryan yayi dariya tare da cewa.
"Kaji girkin Ammina ko ai tafi Maman Yusuf iya girki?."
Yusuf dai har yanzu babu baki sai jinjina mishi kai yake,
hakan yasa su Affan dibkewa da dariya,
yoh shi dai Yusuf baibi ta kansuba saida yayi hanik'an
wata sassanyar gyatsa yayi kana ya kalli Aryan k'arami tare da cewa.
"Eh na yarda Amminka ta iya girki,
amman fa batafi Maman Yusuf ba."
dariya yayi irin ta yara kana yazo ya konta jikin Yusuf d'in yana cewa.
"Hum-uhm ni dai Ammina tafi tsohuwa iya girki."
aifa duk ya sasu darawa shi kuwa Yusuf sai gyara zamanshi yayi tare da tallabe Aryan d'in da kyau nan sukaci gaba da hira.


Zahra kuwa wunin ranar kamar bata da lfy haka ta wuni.

Wasa-wasa kwanan Aryan k'arami 3 a wurin Yusuf,
yaro ya sake dashi sun saba wani sabo da shak'uwa mai k'arfi ya shiga tsakaninsu,
duk inda Yusuf yake yana tare da Aryan d'inshi,
yayinda Zahra kuwa yau dai ta gaza hak'ura,
tun sanyin safiya taketa yiwa Jafar mita ita a dawo mata da yaronta.

Sultan kuwa ya koma Sokoto jiya,

Aryan kuwa ya kawo Hajia Kaka da Rafi'a wurin Yusuf nan suka wuni kasancewar ranarne Adda Zulahat da Amira da Mami da Raihana ma sukaje,
ranar kam Yusuf ya wuni da yan uwanshi sai dare suka tattafi,
Adda zulaihat ce k'arshe har zata kira mijinta yazo ya d'auketa sai Yusuf d'in yace ta bari shi zai maida ta.

Suna cikin motane suna tafiya Yusuf na driving Aryan na bisa cinyarshi yana d'an
jigine da kanshi jikin kirjin Yusuf d'in,
yayinda yake rik'e da wayar Yusuf d'in yana daddannawa,
shi kuwa Yusuf tuk'i yake amman gaba d'aya hankalinshi na kan game d'in da Aryan keyi.

Cikin kula Adda Zulaihat ta kalleshi tare da cewa.
"Hmmmm shin yanzu kam menene shirinka na gaba a kan rayuwarka ta gaba?."
juyowa yayi ya d'an kalleta,
sai ya kuma meda kanshi ya fuskanci titi,
kai ta kuma juyowa gareshi tare da cewa.
"Da kaifa nake kayi shiru."
murya can k'asa yace.
"To me zan ce miki?."
fuska ta tsuke tare da cewa.
"Haka zamuyi da kai?."
kafad'unshi ya bud'a alamar oho.
ganin haka sai ta juya kanta tare da tsuke fuska,
daga nan bata kuma yi mishi mgna ba,
har suka isa,
da sauri tasa hannu ta bud'e marfin motar tare da niyar fita,
jin muryarshine ya sata komawa ya zauna,
cikin sanyin murya yace.
"Kiyi hak'uri Adda na,
gaya min ya zanyi?."
murya na rawa tace.
"Kayi aure shine cikar darajarka."
meda kanshi yayi ya jingina da kujerar kana ya gyarawa Aryan kwanciyarshi,
murya can k'asa yace.
"Wa zai bani yarshi in aura baya duk duniya suna min kallon d'an isaka,
kuma kin sani na gaya miki bana son abinda zai takura rayuwar Aryan,
shiyasa fatana in gina rayuwarshi tukun."
ficewa tayi daga motar tare da cewa.
"OK ba matsala Yusuf kayi ta zama a haka."
tana fad'in haka tayi cikin gida,
shi kuwa balance yayi kan driving sit d'in,
sam baya son fushin Adda Zulaihat dan shi madadin Mama yake ganinta.

Ita kuwa Zulaihat tana shiga cikin gida ta samu Faiq a a tsakiyar gidan,
hand bag nata ya karb'a tare da cewa.
"Mommy kina fita Aunty Zahra tazo,
tun lokacin taketa kuka wai tazo tace miki ki kira Uncle Yusuf ya bawa uncle Jafar Aryan su dawo tare,
wai yau kwana uku bata ganshi ba,
Allah ko Mommy sai kinga yadda tayi ta kuka."
da sauri ta kalleshi tare da cewa
"Yanzu tana ina?."
"tana d'akinki tace bazata tafiba zata jiraki in kin dawo ki sashi ya kawo mata shi."
bata tsaya bin ta kanshi ba tayi bedroom nata.

Tana shiga sai ta kuma yi saurin isa inda Zahran ke zaune tare da cewa,
"Zahra."
ita kuwa jin muryar yayartata yasa tayi saurin mik'ewa tare da cewa.
"Dan Allah Adda Zulaihat ki kira Hamma Yusuf kice mishi ya bada Aryan a kawoshi,
wlh kwana ukunnan duk bana iya bacci."
cikin sauri ta kamo hannunta tare da cewa.
"Zo maza kiyi sauri karsu tafi dan Yusuf d'inne ya dawo dani."
da sauri take janta suna fitowa parlour sukayi kicib'is dashi yana ruggume da Aryan tamkar jariri yayinda Abubakar ke gabanshi,
wanda har Yusuf zai fitane sai yaga shigowar moyarshi shiyasa ya tsaya su gaisa,
to shi kuwa dama Sharifa ta gaya mishi Zahra tazo tanata

Please Login or Register in order to submit comment