Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

harshe ya gabatar da kanshi sannan ya buk'aci,
Idris daya fito yazo gaban kotu,
cikin sanyi Idi ya fito gaba d'aya kunyar duniya ta rufeshi tsanar kanshi da kanshi yake,
tafiya yakeyi kamar mara Lfy,
cikin saib'i ya iso inda ake tsayuwar,
ba tare da b'ata lokaci ba Affan ya fara jefo mishi tambayoyi.
"Kotu zata so sanin sunanka?."
cikin jin kunya Idi yace.
"Sunana Idris Kabiru."

kai tsaye Affan yace.
"Kasan Zahra Aliyu Usman Girei?. "

"Eh na santa."

"Kotu zata so sanin yaushe ka santa,
kuma me alak'arka da ita,
sannan yaushe k'arshen ganinka da ita kuma a wanne yanayi kayi mata ganin k'arshe."

Jiki na rawa idi yace.
"Nasan Zahra tun tana k'arama,
domin nine idi Mai caji na k'ofar gidansu,
Alak'ata da ita kuwa,
soyayyace,
gani na da ita na k'arshe ranar 4 ga watan d'aya shekara ta 2015 da misalin 4:29 pm.
ya kama kenan yanzu wata uku da mako biyu rabona da ita."
sai ya kuma yi shiru yana mai zubda hawaye,
cikin salon iya aiki Affan yace.
"Uhum ina jinkata a wanne yanayi ka barta?."
murya na rawa idi ya rumtse idonshi tare da cewa.
"Cikin mawuyacin hali."
rai a b'ace Affan yace.
"Kaine kayi mata fyad'e amman kanaji an d'aurawa wani laifin kuma kayi shiru,
meyasa ka zab'i kayi mata fyad'e?."
cikin d'aga sauti Aryan yace.
"Objection!!! My lod,
a dena tirsasawa idris amsan laifin da bashi ya aikata ba."
cikin nitsuwa maishariyan ya kalli Affan tare da cewa.
"Barrister Affan ka kikaye."
kai Affan ya rusunar tare dayi godiya sannan yace.
"Kotu na son ganin Raihana Usman jada."
da sauri Raihana ta taso tazo ta shiga d'aya wurin cikin nitsuwa Affan yace.
"Kotu zata so sanin waye ke me alak'arki da Zahra?."
cikin kuka mai cin rai Raihana tayiwa kotu duk bayanin abinda ya faru ranar d'aurin aurenta a lokacin da aka zo d'aukar amarya,
ta k'ara da cewa.
"Ni naga idris da idanuna kuma gashi nan in dai zaiji tsoron Allah zai fad'i gskya,
shine yayiwa Zahra fyad'e,
wlhi ba Hamma Yusuf bane,
d'an uwana sharri yakeson yiwa abokinshi."
shi kuwa Affan murmushi yayi tare da komawa gaban idris cikin sanyi yace.
"Kaji abinda Raihana ta fad'a shin hakane ko ba hakaba."
ido cike da k'walla yace.
"Tabbas hakane."
gaba d'aya court sai ya rud'e anata tsinewa idi yayinda ya kife kanshi yana zubda hawaye,
Yusuf kuwa tunda yaji idi ne idris
da kuma jawabenshi kawai sai ya kife kanshi a kafad'un Jafar ya saki wani irin kuka mai cike da ciwo da k'una kuka yakeyi tamkar ranshi zai fita,
jin kotun ta rud'e yasa al'k'akalin cewa za'a tafi hutun rabin lokaci.

Nima Garkuwa a guje na mik'e dan yin sallan la'asar.


Bayan an dawo hutun rabin lokacin sai aka d'ora daga inda aka tsaya.

Affan ne ya kalli taron jamar sannan ya juyo ya kalli maishariyar cikin rusunar da kai yace.
"Ina neman izinin gabatar da shaiduna na gaba."
cikin kula maishariyar yace.
"An baka."
kai ya rusunar tare da cewa.
"Nagode ya mashariya."
sai ya kuma juyowa ya kalli taron lawyers d'in dake zagaye da wani babban teburi,
Kai ya jinjina ya kuma juyowa ya kalli jamar gari dake cike mak'il a kotun,
gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"Kotu na buk'atar Jafar Aliyu Usman Girei a gabanta."
cikin sauk'e numfashi Jafar ya d'an janye kan Yusuf daga gareshi sannan ya mik'e ya nufi wurin tsayuwa domin bada shaidar,
bayan ya tsaya ne Affan yace.
"Mishi kotu na buk'atar sanin sunaka,
da kuma alak'arka da wanda akayiwa fyad'e?."
A nitse Jafar yace.
"Sunana Jafar Aliyu Usman Girei ni wa ne ga wacce akayiwa fyad'e ubanmu d'aya,
sannan kuma ni k'anine ga wanda ake zargi Yusuf Muhammad Usman Girei,
wanda ya kasance d'an wan mahaifina nane."
cikin gamsuwa da jawabin Jafar Affan yace.
"Ranar 4 ga watan d'aya da mitsalin k'arfe hud'u na yamma xuwa har biyar da rabi kana ina? kuma me kakeyi?."
cikin nitsuwa Jafar ya gyara tsayuwarshi tare da cewa.
"04-01-2015 daga misalin 4:00 pm har zuwa 5:49 pm ina cikin gidan man A S Butu inda nake bin layin shan mai kasan cewar lokacin ana d'an wuyan samun mai?."
taku d'aya zuwa biyu Affan yayi tare da cewa.
"Kotu zataso tasan kaida waye ne kaje kuma wacce iriyar motace a gabanka kuma waccece a bayanka?."
nisawa Jafar yayi tare da cewa.
"Motar dake gabana Audi-Rs6 ce bak'a,
wacce a jikin pilet number d'in ansa Baraden Adamawa tare da tambari doki a gefen,
ganin hakane yasa na gane mai motar,
motar bayana kuma gskya bazan shaidata ba."
cikin salon iya aiki Affan yace.
"Toh amman ai baka da tabbacin wayene a cikin motar Baraden Adamawan ko? tunda gata can yanzuma a woje naga gileshenta masu duhune."
cikin sauk'e numfashi Jafar yace.
"Inada tabbacin waye a cikinta."
daga nan ya basu lbrin yadda sukayi da Yusuf a wurin,
har kiranshi da akayi a waya,
da irin yadda ya figi mota suka tafi,
cikin gamsuwa al'k'alin yake gyad'a kai.
Bayan Jafar ya bada shaida
sai Affan ya nemi fadawanshi da sukaje wurin Yusuf lokacin da zaisa hannu a takardun da M jabeer ya bashi ya kai
in baku manceba har Affan yasa d'aya daga cikinsu yaja motar Yusuf ya medata gefe kuma duk Yusuf na ciki,
bayan fadawan sun bada shaidar lallai dai-dai lokacin da abin ya faru suna tare da Yusuf,
sai kuma Affan ya kira mai gadin gidansu Aryan,
shima yazo yayi bayani,
shi da kanshi ya bud'ewa Yusuf gate ya bar gidan ya kuma k'ara da cewa kuma Aryan d'inma yasan Yusuf ya fita dan ya rakashi har bakin mota,
ya sake jaddada shi tunda Yusuf ya fita bai ga ya sake shigowaba saida,
suka taho tare da Jafar,
ya kuma bada tabbacin yaga Idris ya shigo gidan ya kuma fita a rikice
kuma bayan fitarshi kad'an gida ya rud'e.

Bayan mai gadi ya gama shaidarsa
aka kira Rafi'a da Adda Zulaihat suma duk suka bada shaida,
yayinda idi kuwa yake jaddada duk jawabansu.
cikin nitsuwa Affan ya d'an rok'ofo tare da kausasa murya yace.
"Ya mai girma mai shariya ina rok'on wannan kotu mai adalci,
data duba hujjojinmu da shaidunmu,
su wanke Yusuf Muhammad Usman Girei daga zargin da ake mishi,
a kuma hukunta Idi bisa laifinshi na fyad'e sannan,
a hukunta Aryan kan laifin k'age da yayiwa Yusuf."
sai ya kuma sunkuyowa tare da cewa.
"Nagode."
Aryan ne ya taso da zummar yin magana sai ya koma zaune sabida,
alamu da mai shariyar yayi mishi da hannu alamar ya zauna.

Bayan kamar 3 minutes, Al'k'alin ya d'ago kansa daga kallon books d'in gabanshi da yakeyi,
gyaran murya yayi tare da cewa.
"Bisa la'akari da duba eh zuwa ga shaidu da hujjojin da Lawyer wanda ake k'ara ya kawo,
Court ta wonki Yusuf Muhammad Usman Girei bisa zarginshi da akayi a kan laifin fyad'e,
sannan Court ta yankewa Idris hukuncin zama gidan maza na shekara goma sha biyar da horo dai-dai laifinshi,
sannan babu batun beli,
har ila yau kuma Court ta gargad'i Aryan kan duk k'arar da zai shigar ya tabbatar da bai b'ata sunan waniba."

Sai ya kumayi shiru tare da kallon fuskokin mutane sannan ya kalli Aryan da bisa dukka alamu bai gamsuba,
cikin nitsuwa al'k'alin yace.
"In akwai wanda bai gamsuba da wannan shariyar ko hukunci toh k'ofa a bud'e take zaku iya d'aukaka k'ara."
yana fadin haka ya buga wannan guduman sau uku tare da mik'ewa ya fita mai tsaronshi na binshi a baya.

Cikin kotu kuwa gaba d'aya kowa ya mik'e ya nemi hanyar fita,
sauran lawyers kuwa sai hannu suke bawa Affan suna tayashi murynar yin nasara,
shi kuwa Aryan tattara takardunshi yakeyi yana mai cike da takaici,
bayan ya gama kimtsa takardunshi ne,
ya matso wurin Affan wanda keta murmushi yana tattara takardun gabanshi,
hannu Aryan ya mik'a mishi musabaha sukayi,
cikin wani irin yanayi Aryan ya kalli Affan tare da cewa.
"Congratulation,
ka d'aiyi nasara a nan,
amman nanda sati biyu zamu sake had'uwa a HUKUNCIN ALLAH COURT,
ina mai tabbatar maka ni zanyi nasara."
cikin mmkin Affan ya kalli Aryan yana mamakin bak'ar zuciyar irin ta Aryan,
cikin k'arfin hali yace.
"Muna nan muna jiran sammaci Barrister Aryan."
yana fad'in haka ya juya ya fita.

A harabar wurin kuwa dafifin yan jarudune sukayiwa Yusuf caa,
amman yaki yin mgn haka Affan yak'iyin mgna tunda yasan da sauran rina a kaba tunda Aryan zai d'aukaka k'ara
Haka dai aka tashi mafi akasari suna farin ciki,
Aryan da Safwan kuwa kamar su mutu dan bak'in ciki a wani sashi na mutanena da yan uwan Yusuf sunso a tozartashi,
domin burin magautan nashi ya hallaka,
abin takaici kuwa harda yan uwanshi.

har gida Affan yazo yayiwa Mama bayanin yadda komai ya tafi da kuma k'udurin Aryan.

Abu dai kowa da saqin da zuciyarshi keyi.


A ranar Aryan ya shigar da k'ara a court d'insu Abba,
kafin zuwa dare takardar sammaci ta riski Yusuf.

wannan abu ya bawa mutane mmki,
musamman Raihana ita gani take ko dai an canza mata d'an uwanta ne.


Haka dai abun yayi ta tafiya yau da dad'i gobe akasin haka,
yau saura kwana d'aya tak a shiga zaman sauraron case d'insu Zahra inda Abba ne Al'k'alin,
Affan dai duk ya had'a dukkan baya nanshi har takardar da wancan Court suka basu,
yanata dai yiwa shariyar tanadi,
yayinda har yanzu M Jabeer bai dawoba,
Yusuf kuwa a cikin watanninna
komai ya cukushe masa.


Yau asabar da yamma,
Maman Yusuf ne tsaye a bedroom nata,
tana kallon Zahra dake konce kan gado tayi luf wani irin bacci takeyi wanda bisa dukkan alamu tana jin dad'in baccin,
a hankali Mama ta k'ara matsowa gaban gadon tana mai tsurawa saitin cikin Zahra ido,
matsowa ta kumayi cikin tsananin fad'uwan gaba da firgici mai tsanani k'irjinta sai duka yakeyi a 360 lokaci d'aya zufa ta keto mata,
cikin rawan jiki tasa hannunta kan cikin da taga yayi k'ui dashi,
wata iriyar razana tayi lokacin da taji alamun motsin yaro a cikin uwarshi,
cikin rawan murya da razana ta rink'a cewa.
"Innalillahi wa innailaihi raji'un,
ya ilahi ya mujibat da'awati la haulawalak'uta illabillahi aliyu axeem,
Zahra cik....!!!




*By*
*GARKUWAR FULANI*





Nybl



Uhmmmmm gashi dai ina ta baku 2-2 page a rana,
ban kuma san ya zata kaya ba randa ban samu damar yin posting ba,
duk da nasan akwai masuyi min uzuri, to haka kuma akwai masu manta nayi bibniyun su rufe ido suyi ta fesa k'warafin ba'ayi musu posting.

Duk da haka dai ga page na biyu sabida naga kun shiga tsananin tashin hankali da rud'ani.
Dan haka gashi ku rege powd'um



34

Mik'ewa tayi cikin rawan jiki,
hawayen fuskarta suka k'i tsayuwa,
kai tsaye part d'in Aunty Amarya ta nufa,
tana shiga ta fara kiranta cikin yanayin tashin hankali,
da sauri Aunty Amarya ta fito daga kitchen ganin Maman Yusuf a firgicenne yasata matsowa inda take da sauri,
ita kuwa Mama hannun ta kawai ta kamo tare da juyawa suka fita,
Aunty Amarya ido kawai ta zurawa Mama tare da binta kamar rak'umi da akala,
kai tsaye ta wuce da ita har bedroom bakin gado ta zauna tare da nuna Aunty Amarya Zahra dake baccinta cikin nitsuwa,
matsowa Aunty tayi cikin rawan jiki da tsananin tashin hankali dan gani tai kamar Zahra bata numfashi ne shiyasa k'ara matsota tare da cewa.
"Meke faru da Zahra?."
cikin sanyi da tsoro da kad'uwa Mama ta bud'e baki a hankali tace.
"Ciki...! Ciki...!! Cikifa take dashi bamu saniba bamu tab'a ankara ba sai yanzu da tana bacci nazo zan tada ita tayi salla naga kai cikin ya girmi saninmu dana zuba ido sai naga yaron cikin yana motsawa...!!!."
kukane ya kufce mata ta rumtse idonta da k'arfi wasu zazzzafan hawaye suka zubo.
Wannan shine fa ana wata sai ga wata.
Da mugun sauri Aunty Amarya ta haura kan gadon cikin d'an d'aga sauti ta fara kiran Zahra tare da sa hannu a giggice tana bubbuga cinyoyinta tana cewa.
"Zahra..! Zahra ....! Zahara... ! ki tashi."
cikin bacci taji ana d'aka mata duka,
ido ta bud'e a hankali tare da juyowa tana kallon ta inda taji sautin magana,
cikin sanyin da nitsuwa da rayuwarta ta sauya,
ta mik'e zaune murya can k'asa tace.
"Aunty meya samu Mama?".
ta kuma juyo kamta gefen Mama cikin sanyin sauti tace.
"Mama meya sameki? menene yasaki kuka?."
ita kam Mama sai hawaye,
Aunty Amarya cikin fargaba tace.
"Zahra!!."
juyowa tayi ta kalli uwar tata,
alamun tana jinta
cikin rud'ani Aunty ta matsota tare da dafa kafad'arta murya na rawa tace.
"Zahra menene ya samu cikinki ya naga ya d'an k'ara girma? me kikeji a cikin?."
fuska ta d'an kawar tare da lumshe ido sai ga hawayen da suka cika idon sun zubo,
lips enta ta had'e ta matse murya can k'asa tace.
"Nima ban san meyasa yake k'ara girmanba,
kuma yanzu kullum sai inji wani abu na yawo a cikin cikina d'in,
ko jiya da Dija chiroma tazo,
na gaya mata sai tace min wata k'il ko k'abane,
kuma cikin yana d'an min nauyi."
wata iriyar zabura Aunty tayi cikin d'aga sauti ta saki kuka tare da cewa.
"Na shiga uku Zahra cikin shege,
wayyo ni Maryam ina zansa wannan abun kunya."
Da takaici ta hade da bakin ciki ta kai mata duka tako ina tana cewa.
"Ke mahaukaciyar inace, meyasa tun yana k'arami baki gaya min kina da cikiba,
to wlh tallahi zubdashi za'ayi ! ko zaki rasa ranki ne wurin zubdashi sai an zubar."
cikin kid'ima da tsantsar mamaki Mama ta mik'e tare da shiga tsakiyarsu,
ita kuwa Zahra sai idanu ta tsurawa Aunty yayinda take jin zuciyarta na harba da tsananin k'arfi har saida d'an cikinta ya juya,
ita kuwa Aunty Amarya kuka takeyi sosai tana cewa Mama.
"Wlhi sai an zubda cikin nan ni dai baza'a haifamin jika d'an dakan kuka ba."
sai ta kuma saki kuka.

A cikin gida kuwa Ummi dake rakub'e a window Mama ce ta juya da sauri kai tsaye parlour Hajja Inna taje har tana tuntub'e,
jiki na rawa ta iso gaban Hajja inna dake d'aura lalle cikin rawan baki tace.
"Hajja Inna kinji wai ashe Zahra ciki gareta."
zabura tayi tare da mik'ewa tsaye cikin wani irin yanayi tace.
"Hahaha ai dama ni na jima ina ce muku tanada ciki,
amman kukak'i yarda,
yanzu waya fad'i miki tanada cikin?."
cikin azama tace.
"Yoh d'azu naga uwar korton taje ta kamo hannun uwar karuwar,
sunyi d'akin uwar Namajon shiyasa naje na rakub'e a window to nan naji abinda suke tattau nawa,
yanzu gacan uwar Zahra tanata haushi wai dole a zubda cikin ita ba'a haifa mata jika d'an dakan kuka ba."
ai kafin ta k'arishe baya ninta tuni shegiyar tsohuwarnan tayi waje,
kai tsaye sashin Mama ta nufa,
a guje Itama Ummi tabi bayanta,
babu sallama ta kusa kai cikin bedroom d'in Mama inda take jiyo sautin kukan Aunty Amarya,
tana shiga tayi wani irin saurin ture Aunty Amarya da Mama ta matso gaban Zahra da ta mana tamkar gunki sai hawayen dake tsiyaya a hab'arta,
ita kuwa Hajja Inna hannu tasa ta shafi cikin Zahra wanda,
dai-dai lokacin yaron cikin yayi wutsul-wutsul tare da harba k'afafu,
ai tana jin haka ta koma da baya tare dayin zaman yan bori baki ta kware tare da kurma ihu da iya k'arfinta
tana ihu tana surutai.
"Cikin shege a zuriyata,
wallahi Allah bazata sab'u ba,
sai dai Aliyu yazo ya koreki kibar gidannan kije can ki had'u da shegen daya d'irka miki cikin,
d'an iskan yaro mai jajeyen kunnuwa,
Wlh sai nasa an koreki bazaki haifa mana cikin shegeba a tsarkakken gidanmu."
Mama kam zama tayi gefen Zahra da ta fara wani irin kuka mai cin rai,
ita kuwa Aunty Amarya parlour ta fito tana kuka tare da cewa.
"Wallahi sai dai a zubda cikin nan."
ita kuwa Hajja Inna ihu da kururuwa take kurma,
wanda yasa gaba d'aya mak'otansu na kusa na jinsu,
hakama mutanen dake k'ofar masallaci duk sunji,
jiyo hayaniya a cikin gidane yasa Jafar da Sulaiman shigowa da sauri,
Daddy dake sama wanda wonka yakeyi,
tunda ya jiyo ihu da kururuwar Hajja Inna,
sai jikinshi ya fara b'ari,
sauri-sauri ya fito wonka a gurguje ya kimtsa,
sannan ya fito har yana taka steps d'in bibbiyu,
yana sauk'owa Jafar da Sulaiman suna isowa,
a tare suka shiga part d'in Mama,
yayinda Mami kam da Zeenat tuni suke rakub'e a jikin k'ofar parlour suna kuka mai cike da tausayawa yar uwarsu,
Daddy kuwa dasu Jafar kai tsaye suka wuce bedroom,
suna shiga Hajja Inna ta k'ara sakin ihu tana cewa.
"Aliyu ka gani ko cikin shege a jikin Zahra to,
Wlh ni bazan zauna da ita a gida d'aya ba."
wani irin murmushi Daddy yayi,
murmushin da yafi kuka ciwo,
matsowa yayi gaban Zahra hannu yasa ya kamo hannunta ya mik'ar da ita tsaye,
cikin tsananin tsoro da tashin hankali ta kalli Mahaifin nata cikin tsananin kuka murya na rawa tace.
"Daddy kayi hak'uri wlh nima bansan ciki bane dani sai,
yanzu Daddy dan Allah ka gafar ceni."
wani irin suya da d'aci zuciyar Daddy keyi gaba d'aya fuskarshi tayi jazir,
ita kuwa Hajja inna sai cewa tayi.
"Yauwa Aliyu fitar mana ita daga gidanmu mai tsarki, kai zuriyarmu ma baki d'aya kada ta k'ara tunomi."
Zahra najin haka ta zame ta durk'usa gaban mahaifin nata cikin tsananin kuka tace.
"Dan Allah Daddy kayi mini rai,
karka koreni, in ka koreni ban san ina zan shigaba,
Daddy ni dai daka koreni gwara a zubar da cikin in na mutuma kun huta kamar yadda Aunty na tace."
sunku yowa yayi ya sake kamo hannunta ya tsaida ita,
dai-dai lokacin kuma Aunty Amarya ta sake shigowa d'akin cikin kuka tace.
"Eh wlh ni dai a zubda cikin, inma ta mutu mun huta da ganin bak'in ciki."
ita kuwa Zahra jin furucin majaifiyarta yasata sakin wani irin marayan kuka tana zamewa,
a k'asa ta konta tare da cewa.
"Daddy kada ka koreni,
Daddy kainefa kake yiwa Abba fad'a akan korar da yayiwa Hamma Yusuf,
Daddy ban san ina zan shigaba a duniyar nan,
gwara kusa a zubda cikin in yaso in mutu kawai,
tunda babu mai sona a duniya."
sai ta kuma saki kuka tare da rik'o k'afafun Daddyntan
Mama kuwa yau sai aka fama mata ciwon ranta aka tuno mata randa aka kori Yusuf,
Jafar kuwa kuka yakeyi kamar macce,
Suleiman ma kukan yakeyi yana cewa.
"Daddy yanzu haka zakuyi ta korarmu da d'd'ad'aya akan biyewa Hajja Inna shin ina zamusa kanmu?".
Mama kam ta gaza magana sai kuka takeyi tare da rik'o hannun Zahra alamun bazata saketaba,
Mami da Zeenat da Ibrahim da Sadik kuwa had'e kai sukayi a wajen suna kuka,
kukansu da ihu da kururuwar Hajja Inna shiya jawo hankalin mutane har yara suka taru suka cika gidan,
yayinda tsaffin cikin matsallacin nan suketa sallama a bakin gate suna kiran Abba a waya dan son jin meke faruwa.

Aunty Amarya kuwa cikin d'aga sauti tace.
"Ni dai gwara a zubda cikin ta mutu kowa ya huta a kan ace an koreta."
cikin tsananin fushi da zafin zuciya Daddy ya kikkifa mata wasu zafafan marukan da saida taga taurari k'agarshi yasa ya tad'e k'afafunta ji kakeyi tim ta zube k'asa,
cureta yayi da k'afarshi ya matsar da ita daga gabanshi,
hannun Zahra ya jawo da k'arfi,
ya tsaida ita sannan ya fara janta hanyar fita,
Jafar kuwa cikin kuka yace.
"Daddy in dai an kori Zahra a gidannan wlh wlh nima zan bar muku gidanku."
da sauri Daddy yasa hannunshi d'aya ya kamo na Jafar ya nufi hanyar fita tare dasu,
Ummi ce tayi tsagal cikin rashin tausayi tace.
"A a wlh bazata sab'u ba,
ina dalili d'ana ba d'an iskaba ace za'a koreshi dan yan iskan gidan sunyi laifi,
ai kawai kubi shawarar uwarta a zubda cikin in ta mutuma an huta."
cikin tsananin fushi Daddy ya saki hannun Jafar sannan ya juyo kan Ummi maruka ya rink'a zuba mata a gigice cikin muryar kuka yace.
"Kunyi asarar imani da raunin zuciyar da aka san mata suna dashi,
a gabana kuke cewa in 'yata ta mutu an huta,
ido da ido kuke cemin inyi kisan kai,
Maryam kinji kunya kinyi asara Allah ya wadaranki in dai haka iyaye mata suka zama a wannan zamanin to an shiga uku,
ni kuke cewa in kori d'iyata dan tayi cikin da tsautsayi da k'addarane ya batashi."
Sai ya kuma jawo hannun Jafar ya had'a dana Zahra cikin rauni yace.
"Wallahi Allah kenan kunga Jafar da Zahra to nafi sonsu duk cikin yayana,
Zahra na ko yara dubune a cikinnan babu mai zubdashi,
mu mun yarda da k'addara kuma bazamuyi kisan kaiba."
sai ya kuma juyowa ya kalli Aunty Amarya daketa kuka kamar ranta zai fita cikin daka tsawo yace.
"Wallahi wallahi in kika kuskura kika sake cewa a zubar da cikin nan ta mutu a huta,
toh wlh kan igiyoyin aurenki guda biyu da suka rege,
ke kuma Ummi kika sake kuskura kika sake yunk'urin shiga tsakanin yarana wlh zaki bar gidannan bari na har abadan."
sai ya kuma jawo hannun Zahra suka zo gaban Hajja Inna durk'usawa yayi cikin zubda hawaye yace.
"Hajja Inna ki gafarceni,
zanbi umarninki zan kori Zahra,
amman nima zan bar cikin zuriyarnan bari na har abadan in d'ai kince Zahra ta bar gidan,
na yarda zamu tafi."
cikin tsoro da razani tace.
"A a Aliyu ka tafi kuma to ni kuma inyi yaya,
ya za'ayi ka tafi niko ina zan shiga d'en?".
Kai ya juya tare da cewa.
"Toh kince bakya son ganin Zahra,
so kike in koreta kamar yadda Yayana ya kori Yusuf ko?."
cikin kuka tace.
"A a ni kam barta tayi zamanta ita da abin kunyarta
haka kawai dansu zan rasaka,
to na amince ta zauna."
mik'ewa Daddy yayi ya jawo hannun Zahra da jafar suka nufi parlour,
a dai-dai bakin k'ofar bedroom d'in suka ga Abba yana tsaye ya zuba musu ido karo na forko da Daddy yaga tsantsar tausayi da tashin hankali a fuskar d'an uwan nashi,
ganin hawaye nabin fuskar Abba yasa Daddy zuwa gareshi yana cewa.
"Yaya ka gani ko?."
ruggumeshi Abba yayi tare da rumtse ido wasu zafafan hawayen nadama na zubo mishi,
ganin sun ruggume juna suna kuka yasa,
Hajja inna zuwa ta rarrashesu tare da jawosu suka fito,

Suna zuwa tsakiyar gida suka samu d'and'azo yaran unguwa harda matan aure kad'an,
cikin zafi Jafar ya koresu,
amman a take a wurin wata yarinya ta d'aga murya tare da cewa.
"Tayi cikin shege,
uwarta tace a zubar in ta mutu ai sun huta,
Zahra ta zaro tsiya."
jin haka Jafar yayi kansu a guje suka fita suna ihu suna maimaita abinda yarinyar nan tace.



( Tsugunne Bata K'are ba). Wasa farin girki!!!!!!

A wannnan ranar a wannan yammacin labarin cikin Zahra ya karad'e ko wanne lungu da sak'o dake cikin Girei,
duk gidan da kashiga mgarta akeyi,
duk inda zaka wuce taron jama'a mgnarta akeyi,
yayinda in anji wanda ake zargin ya mata cikin da yawa musawa sukeyi suna tausayawa k'addarar da Yusuf ya rufta ciki.

Adda Zulaihat kuwa da Amira wanda Ummi ce ta kirasu ta gaya musu,
sunyi kuka tamkar su mutu,

A lokacin Adda Zulaihat ta shirya sai gidansu Aryan.
bayan taje sun gaisa da kaka ce,
ta gaya mata meke faruwa,
itama Kaka kuka tayi tayi sannan tawa Zulaihat jahora sukaje part d'in Yusuf,
suna shiga suka samu Jafar da Affan sun tasa Yusuf a gaba rarrashinsa sukeyi amman ya gaza dena kukan,
tunda Jafar ya gaya mishi abinda yake faruwa,
yana ganin Zulaihat sai kuka kukanshi ya k'aru,
zuwa tayi gabanshi ta durk'usa cikin kuka tace.
"Na rok'eka da Allah Yusuf ka zama gatan Zahra ka rufa mata asiri,
ka zama Garkuwarta wlh Zahra tayi k'ank'anta da wad'annan jarrabobin rayuwar,
kai na mijine Yusuf zaka iya jure wani abun,
dan Allah ka taimaki rayuwar Zahra."
cikin kuka yace.
"In sha Allah zanyi abinda ya dace."
cikin sauri Affan da Jafar suka had'a baki wurin cewa.
"A a dan Allah Yusuf karkayi haka,
zaka zubda mutuncinka a idon duniya,
jama'a zasuyi ta tsine maka."
Kai ya jinjina tare da mik'ewa ya dafa kafad'ar Affan yace.
"Affan karka damu kaine da nasara a kan Aryan."
yana fad'in haka ya nufi bedroom nashi,
Affan da Jafar kuwa tare suka fita,
Adda Zulaihat kuwa Aryan ne ya meda ita.


washe gari da sanyin safiya Abba ya tara mutanen gidan yayi musu nasiha mai ratsa jiki kan d'an adam ya rik'e gskya duk zafinta,
bayan an tashi taron ne yace Jafar da Zahra su tsaya yanada mgna dasu,
jin haka suka dawo gabanshi suka zauna,
cikin sanyi yacewa Zahra.
"Toh Goggo kinga yadda kalar taki jarrabar tazo."
kai ta gyad'a mishi cikin zubda hawaye,
shi kuwa kanshi ya kawar daga kallonta domin tana matuk'ar bashi tausayi cikin sanyin murya mai cike da rarrashi yace.
"Kinsan gobene za'a shiga Court d'inmu dan sauraron k'arku ko?."
kai ta gyad'a mishi alamar eh,
cikin sanyi da alamun neman alfarma yace.
"Dan Allah na rok'i al'farmaki gobe kije Court,
sannan in rok'onki daki fad'i gskyar abinda kika sani domin shi zai kawo sauk'in shariyar,
sannan yanzu ko ba komai ko dan cikinki kya fito ki gayawa court waye ubanshi."
cikin sanyi da rawan murya tace.
"Toh Abba Ngd."
cikin sanyi yace.
"Allah ya miki al'barka."
murya na rawa tace.
"Amin."
shi kuwa Abba sai ya juyo kan

Please Login or Register in order to submit comment