Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

satan.

Ita kuwa Maman Yusuf ita da Aunty suka d'auki nasu Abba suka kai,
kana suka dawo kitchen d'in a tare da sauri Maman Yusuf tace.
"Wai baki sawa su Ibrahim ba."
murmushi Aunty Amarya tayi kana tace..
"Yoh bakiga tun d'azu suka tafi gidan Jafar ba, Ibrahim harda cewa bari yaje ya tsagalgali Aunty Dija sai ta mishi d'anwake, shiyasa banyi rabiya na dasuba?."
itama Mama murmushi kana tace.
"aifa Ibrahim da Aunty Dijanshi sai Allah, ba matsala ai abincinsu Abban nasu da yawa ko mutun biya zasuci su bari in sun dawo in zasuci saje can."

Haka dai sukaje sukayi sallah kana sukazo sukaci abinci,
hajja ina sai santin tuwo da miyar gandarnan takeyi koda ta fito tai ta sawa Maman Yusuf da Aunty Amarya al'barka harda cewa.
"Kun samu ladana yau naci tuwo,
dama kwana biyu dan mugunta sai a dafa shirmen abincin yan gayu wanda ni ba dad'i yake minba,
haka dama yauda safe banci wannan wannan soyayyiyar shinkafarba dan ni ba kaza bace."
ta k'arishe mgnar tana hararan Ummu dan da ita take.
Nanda suka zauna sunata hira.

Yusuf kuwa dama yana fita part nashi ya wuce tare da Adnan,
kan gado ya kontar dashi tare da bashi wayarshi d'aya kana ya d'auki d'ayar kuma,
Aryan ya fara kira kana ya kara woyar a kunnenshi tare da zare hallabiyar jikinshi,
jin sallaman Aryan ya sashi zama bakin gadon cikin happy yace.
"Wa alaikassalam." sai ya kuma ci gaba da cewa.
"Al'bishirin ka."
cikin d'oki da zak'uwa Aryan yace.
"Goro fari k'al."
murmushi yayi cikin kara irin ta aminai ya shafa kanshi tare da cewa.
"Toh yau dai Allah yayi yaranka sun fito duniya an samu tagwaye, Aryan ya tafi Aryan ya dawo tare da Yusrah."
cikin tsananin farin ciki Aryan yace.
"Alhamdulillah Alhamdulillah Masha Allah mashaaa Allah kai Allah na gode maka, Allah ya raya mana su bisa imani, kuna wanne asibiti yanzu?."
mik'ewa yayi ya gyarawa Adnan konciyarshi dan yayi bacci kana yace.
"Yoh ai a gida muka haihu."
dariya sosai Aryan yayi kana yace.
"Kuka haihu ko ta haihu watoma tare kuka haihu."
cikin fidda numfashi yace.
"Kai Aryan wlh tare muka haihu kakuwa san azabar danasha, shak'a mari yagushi naushi duk saida Zahra tamin kafin ta haihu kaga ko ai tare muka haihu wlh yanzu haka duk jikina ciwo yakeyi."
cikin dariyar shak'iyanci, Aryan yace.
"Toh gamu nan zuwa yanzu?."
suna gama waya da Aryan ya kira Affan ya shaida mishi inda Affan yace mishi.
"Yoh ai makara domin mu gamu ma a hanya Aunty ta gaya mana tun d'azu."
dariya yayi kana yace.
"Toh Allah kawoku lfy."
daga nanfa ya kira Sultan ya shaida mishi sannan ya kira Abdul-kareem inda yace ai ya makara domin Aryan ya gaya mishi,
ya k'ara da cewa ya turo mishi hoton yaran,
yana katse kiran ya kira shugaban tuzurai inji Affan da fad'i M Jabeer inda yace mushi.
"Yoh ai Abba ya rigaka ya gaya min tun d'azu."
cikin jin kunya yace.
"Malam yaushe zaka zo ka gansu ka musu Addu'a?."
cikin kamala yace.
"Sai zuwa jibi."
Cikin jin dad'i yace.
"Allah ya kaimu."

So daga nan ya kira Safwan ma ya gaya mishi shima ya tayashi murna,
kana yana katse kiran ya shiga bathroom a gurguje ya wonke towel d'in daya d'an b'aci kana yayi wonka mai rai da lfy sannan,
ya fito ya kimtsa cikin wata d'anyar voyel mai azabar tsada da kyau da shek'i kana ya feffesa turare,
tare da kafa hular zanna mai tsunami kyau kana ya d'auki carbinshi ya nufi masallaci,
nan ya samu Aryan da iyalanshi ya iso hakama Affan.
so su Nana da d'iyarta Anisa da Rayi' da yan tagqayenta suka wuce part d'in Mama.
Su Ibrahim da Sadiq ma duk sun fito daga gidan Jafar zuwa nan
tare sukayi sallah a matsallacin gidanshin inda Abba ne ya limancesu.

kana fitowa masallacin suka wuce parlour Abba nanfa,
suka zauna sukayi lunch tare sai Affan da yak'i shigowa parlour sabida kunyar surkan nashi.
Ibrahim kuwa da Sadiq kajin suka d'anci kad'an kana suka shiga gari,
shi kuwa Affan parlour Yusuf ya tafi inda Nana ta kai mishi abincin a can ta nace sai yaci so a k'oshe yake kawai sai ya d'ansha kunun gyad'an.

Dija kuwa tana samun ta sallami su Ibrahim ta shiga bedroom nata wasu set d'in kayan jarirai ta kwaso kusan kala shida na mace da namiji a Dubai Jafar ya sayesu domin cikin Zahra,
tana gama had'a kayan ta zari hijabinta kana ta suri woyarya tare fitowa ta nufi gidan Zahra d'in da cikinta daya fara d'an fitowa.

Tana shiga cikin gidan ta samu su Mami sun rigata zuwa,
kai tsaye bedroom ta wuce inda ta samu su Rafi'a da Mami,
dasu Adda Amira da Zulaihat jiki na rawa ta kalli Zahra dake zaune Mama ta tasata a gaba tamkar ta bata abincin a baki,
cikin tsananin farin ciki ta karb'i jaririyar da Ummi tayiwa wonka yanzu jiki na rawa ta karb'eta tare da nad'eta cikin tattausan shawul da ta zaro cikin kayan da tazo dashi,
"Wow Masha Allah, kai Allah mun gode maka yau gamu ga d'iyarmu."
sai ta kuma kalli Zahra dake murmushi tace.
"Sannu Matar Hamma." dariya sukayi baki d'aya dan sun san Dija da tsiya,
Hajja inna kuwa sai murmushi takeyi kun san tana son Jafar shiyasa take son matarshi over tafi tsargan Sakina cikin kula tace.
"Saura ke da Rukayya Allah ya sauk'eku lfy."
cikin jin kunya Dija ta d'uk'ar da kai dan ga surkanta,
Adda Zulaihat kuwa mik'ewa tayi tare da cewa Amira.
"Ke tashi mu shiga kitchen kinji fa Mama cewa tayi mai aikinta ta huta yau mune da kitchen."
cikin sauri Amira ta mik'e tare da mik'awa Aunty Amarya d'iyarta k'arama Arifa, da sauri Aunty Amarya ta amshi Baby cikin wasa ta d'an ja kumatun Arifa tare da cewa.
"Kishi ban haushi zata karya min sawu."
Mami ce tai dariya tare da cewa.
"Kai Aunty Amarya kishi dai kinga ta fiki gashi."
dariya sukayi baki d'aya kana Zulaihat da Amira kana Rafi'a tabi bayansu suka fita suka shiga kitchen.
Ummi kuwa taci gaba da yiwa jaririn wonka cikin kula da amana.
yayinda Dija ke kimtsa macen.
Mama kuwa ta dage tana bawa Zahra kula data dace da masu jego.

Yusuf kuwa suna fitowa parlour Abba ya nufi parlour Mama da kanshi ya shiga cikin wai zai d'auko yaran ya kaiwa su Aryan su samusu al'barka,
yayinda Aryan kuma ya nufi parlour Yusuf d'in wurin Affan.

Da sallamanshi ya shiga,
ganin suna cike a d'akin sai ya d'an koma gefen Mamanshi ya zauna,
domin ba wanda yakejin kunya a cikinsu dan Dija surutu gareta dole ya saki jiki da ita,
Mama kuma uwace hakama Ummi Aunty Amarya kuwa matsayinta nada yawa a gurinshi,
so bai wani jin kunyarta sosai bugu da k'ari suma kowa Harkar gabanshi yakeyi.
ido ya zubawa Zahra kana ya k'ara matsota hannunshi yasa bisa wuyanta,
idonta ya kallah bisa dukkan alamu baccin bai ishetaba.
a hankali yace.
"Kici abinci kizo muje kiyi bacci nan surutun Dija ma kad'ai zai hanaki bacci."
murmushi Dija tayi kana tace.
"Kai Hamma Yusuf nifa kafin in zoma a zaune na sameta."
shima murmushi yayi kana yace.
"A a gwara fa in tafi da abata yafi min konciyan hankali,
gwara in bata kulawa sabida tsaro badon tsoroba."
Mami kam baki ta bud'e tana kallon Hamman nasu tana mmki ashe Hamma Yusuf yana tsurutu mai tsawo yau harda wasa da dariya lallai kam.
itama kanta Dija tayi mmki don tabbas ya sake in tazo gidansu suna gaisawa a mutunce amman ba irin fara'ar yau d'innan ba.
Aunty Amarya kuwa murmushin jin dad'i kawai taketayi,
yayinda Ummi ma take binsu da kallon sha'awa,
kana Hajja inna ko ita ke taya Dija kimtsa jaririyar,
ita kuwa Maman Yusuf kofin kunu ta mik'awa Yusuf tare da cewa.
"Bata ta shanyeshi."
da sauri ya amshi kofin kana ya kai matashi har baki ganin dafa gaske yakeyi dole ta shanyeshi kana ya barta.
sai ya kuma kalli Ummi jin yaron nata kuka cikin kwab'e fuska yace.
"Ummi barshi haka wonkannan yayi yawafa kawoshi yasha nono."
cikin dariya Ummi ta kalli Mani tare da cewa.
"Kinga ke jeki zunda ruwannan ki k'aro ruwa na uku in tsulleshi in dai ba so suke ya zama saurayi mai warin k'ashiba."
cikin sauri yace.
"Kai Ummi har wonka uku yunwafa yakeji ayi hak'uri a kawoshi yasha nono sai ayi na ukun."
Cikin sanyi Dija tace.
"Toh ai nononma ba'a wonkeshi bako?."
kai ya jujjuya cikin subutar baki yace.
"Ohh hoo nononmu ba tatti fes yake, kullum sai n...!"
sai ya kumayi maza ya taro harshenshi jin zaiyi katob'ara,
ita kuwa Dija Mami ta kalla sai kuma suka sunkuyar da kai don sunfa lura yau Hamma Yusuf sai a slow,
Ummu kuwa da Aunty Amarya yi sukayi kamar basuji ba.
shi kuwa tsare gida yayi kamar ba shiba kana ya mik'a hannu ya amshi jaririyar da Dija ta gama kimtsata cikin wasu tattausan kayan sanyi pink color kasancewar ana cikin yanayin sanyin huturu yarinya sai k'amshi takeyi yana amsarta ya ruggumeta tare da wanna mata kiss a goshi.
daga nan aka gama kimtsa na mijinma.

Nan Mama ta shigo dabino da Zam-zam ta mik'a mishi, gyara rik'on babyn yayi kana ya amshi robar dabinon ya watsa a bakinshi ya tattauna kana ya tattara yawunshi da d'and'anon dabinon ya bata a baki irin yadda yayiwa marigayi Aryan saida ya gama bata na dabino bakwai sannan ya bawa namijin ma.
kana Mami ta rik'e macen suka tafi part nashi inda su Affan suke nan sukayiwa yara addu'a,
zata fitane sukaji muryar Adnan da sauri Yusuf ya shiga bedroom nashi ya d'auko Adnan ya batashi tare da cewa.
"Ki bashi abinci ki mishi wonka ki dawo min dashi?."
toh tace kana ta amsheshi.


Kai wannan rana dai wannan zuriya ta cika da farin ciki,
yan uwa da abo kan arzik'i duk sunji social media ta ciki da hotunan Yusuf da jariranshi tako ina Aryan ya turawa Abdulkareem da Sultan kunfa san Sultan shi hoto nada daraja a wurinshi shiyasa lokaci d'aya haihuwar ta ratsa ko ina,
Su Ummi kuwa har sun gaji da ganin rawan k'afar Yusuf.
Ranar dai nan suka wuni.


Washe gari Sakina ma tazo hakama Raihana da Hajjia Kaka, da Zeenat
Safwan ma yazo da Rukayyanshi,
Kana Tatti ma tazo ita da matar Uncle Sani,
mak'otansu Mama na Girei duk sunzo yiwa Mama barka.


Kwanaki sun tafi suna yazo tuni Zahra tafa murje tayi ras kunsan cikan satin sunannan mai jego takanyi wani sihirtaccen kyau da fitinennen shak'i da k'amshi.

Toh hakance ta kasance da Zahra tayi ras da ita sai shek'i tamkar tauraruwa Zahra.
Hamma Yusuf kuwa tun Mama na korarshi har ta zubawa sarautar rabbi ido.


Gobe suna Mutan sokotoma Sun zo Sultan da Nana hakama,
Abdul-kareem da matarshi haka bashir abokin Yusuf d'an liman shima daga Gombe yazo, Jafar ma da ya dowo dan baya nan akayi haihuwar yana Abuja to washe gari suna ya dawo

Washe garin suna yara sukaci sunansu Namijin aka meda sunan Aryan mace kuwa akasa mata Yusrah


Anyi hidama da shagalin bikin suna cikin wadata da salama.

Bayan suna da kwana biyu duk bak'i sun watse,
Abdulkareem ya wuce Sokoto shida Sultan da matansu.


******************************

Kwanaki sunja makonni sun ja ya juye eh zuwa wattini yanzu watannin Aryan da Yusrah biyu.
Abubuwa da yawa sun faru cikin watannin nan,
a ciki kuwa harda magiya da nacin da Yusuf yayi ta yiwa Mama akan tunda Zahra ta gama Araba'in ta koma side d'inta amman ina Mama ta kafa ta tsare tace wai sai yara sunyi wata uku to yau dai Yusuf ya shiryawa kanshi mafita.




by
*GARKUWAR FULANI**HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 30*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



Da sauri ya k'ara jawota jikinshi tare da ruggumeta da kyau,
kana ya rumtse idanun shi sabisa ganin jinin da ta zubda ya bashi tsoro.
Lafewa tayi a jikinshi cikin maida numfashin gajiya da d'an rad'ad'in dake addabarta sabida ratsowar yara har biyu,
cikin kad'uwa da tsananin tausayinta sabida tabbas yaga zallar wahalar da tasha kana ga wani jini da yaga ta zubda wanda shi a zatonshi in shine ya rasa wannan jinin ai macewa zaiyi,
Cikin tsantsar kulawa ya sunkuyo kanta tare da tallab'eta ya ajiyeta cikin bath tub d'in ruwan d'umin da ya had'a mata. Ita kam Zahra rumtse ido tayi da k'arfi kana rik'o hannunshi tare da kallonshi cikin rauni murya a sanyaye tace.
"Wach Allah na Hamma Yusuf zafee."
gaba d'aya ta karya mishi zuciya tausayinta da rauni ya rufemishi zuciya da dukkan sasan jikinshi,
ji yake girma da darajar iyaye mata ya k'aru a idanunshi yayinda tausayin k'anne da 'yaya mata ya rufeshi,
a ranshi yake kitsima shin duk matar data haihu dama haka take fuskantar azabawa hawala zafi k'una suka kana da k'etare tsirad'i tabbas ya yarda da mgnar mutane da ake cewa duk mai ciki k'afa d'aya na duniya d'aya na lahira ne,
wasu zafafan hawayene suka fara tsastsafo mishi cikin diddigin jijiyoyin ida nunshi yana jin tausayin Mamanshi da k'aunarta da jink'anta na ratsa dukkan jini da jijiyoyin jikinshi.
jin Zahra ta kuma rik'o hannunshi tare da manna kanta bisa cinyarshi dan shi yana zaunene bakin bath tub d'in.
ina zuwa yanzu ya kasa danne hawayenshi,
haka yasa ya zame ya tsuguna ta wojen bath d'in kana ita tanata ciki,
hannunshi yasa ya tallabo kanta cikin tsananin tausayawa murya na rawa hawaye na kwaranyowa a fuskarshi yace.
"Am so sorry My dear sis bansan irin wannan azaba mata ke shaba,
da bazanyi tunanin na fiki son Aryan ba,
da da hali da na karb'a miki zafin jikinki."
sai ya kuma manne goshinshi da nata still hawaye na zubo mishi,
murmushin k'arfin hali tayi kana girgiza mishi kai murya a hankali tace.
"Hamma Yusuf hawayen kuma na menene?."
cikin rawan murya yace.
"Zahra duk fa mai imani dole ya tausawaya mace in har yasan irin wannan wahalar kuke sha yayin haihuwa,
toh ni ya zanyi in hana zuciyata tausayawa miki ya zanyi in hana idanuna zubda hawayen da tausayinki ne ya samar dashi."
dolefa Zahra ta aro jarumta ta koma a Zahranta mai dauriya sabida taga zuciyar d'an uwanta mijinta kuma ta kareya sosai,
ko rasuwar Aryan bataga Hamma Yusuf yayi irin wannan kukanba.
janye kanta tayi daga nashi cikin k'arfin hali tace.
"Abban Yusrah yaufa ranar farin cikine ba kuka ba,
taimaka min inyi wonka muje inyi kolliya in kafa d'auri in ruggume yaranmu suji d'umin Amminsu."
lips inshi ya taune dan yafa lura dauriya takeyi,
so ganin akwai gajiya tare da itane yasashi mik'ewa.
sosai ya taimaka mata tayi wonka kana,
ta d'auro towel suka fito.
A bakin gado ya ajiyeta kana ya nufi side d'inta da sauri,
doguwar rigar atamfa ya d'auko mata tare da bra and pant kana ya had'a da pand kunsan ita Zahra dama in tanada ciki take jini.

Sauri-sauri ya dawo shida kanshi ya manna mata audugar a jikin pant d'in kana ya saka mata shi sannan ya mak'ala mata bra d'in kana ya zira mata rigar tare da janye towel d'in cikin mmki ya kalleta ganin har towel d'in ya fara b'aci a hankali yace.
"Mu tafi asibiti a dubaki."
cikin sanyi tace.
"No Hamma ba komai fa."
da sauri yace.
"Ya zaki cemin ba komai bayan kinata zubda jini kin san ba abinda ke saurin d'auke mutun kamar rashin jini."
cikin lumshe ido tace.
"Toh Hamma tsoro kake kar ka rasani ne?."
da sauri yace.
"Sosai ma kuwa baki san cewa in na rasakiba nima za'a rasani."
murmushin jin dad'i tayi kana ta sha sajenshi ba tare da tace komai ba,
shi kuwa bathroom ya bud'e ya cilla towel d'in kana ya fito,
da kanshi ya tada ita zaune kana ya tallabeta suka nufi parlour,
cikin k'arfin hali tace.
"Hamma zan iya tafiya ba tare da an rik'eni bafa."
bai kulata ba sai ajiyeta yayi bisa kujera,
kana ya fita sauri-sauri gudu-gudu ya tafi harabar gidan tafiyar kusan 5 minutes yayi kana ya isa parking lot nasu da sauri ya shiga cikin wata farar mota,
kana ya fito da ita,
yayinda tuni mai gad'i ya bud'e mishi gate,
shi kuwa Yusuf part nashi ya nufa da motar saida ya kaita har bakin parlour kana yayi parking sannan ya d'an meda kujerar gefen shi baya tare da d'an kontar da ita kad'an sannan ya fita da sauri,
parlour shi ya koma ba tare da yace mata komaiba ya ciccib'eta ya nufi cikin motar,
kunfa san Zahra ba k'atuwa bace kana Yusuf ya fita nesa ba kusaba kuma shi k'ak'k'arfane da yake iya sarrafa linzamin dawakai,
so Madam karkiji nace an d'aga Zahra wata k'il kin kai Garkuwa k'iba kana mijinki dan hutune ba aikin k'arfine sana'arsaba,
ki haihu ki sake kice ai Garkuwa nata nuna Yusuf ne ya d'aga Zahra kice kema sai an d'agaki,
yaseen in kin fasa zuciyar mijinki babu water na, kana kina son mijinki ya rink'a miki yadda Yusuf kewa Zahra na tabbar babu wacce zatayiwa kanta fatan shiga k'alubaken rayuwa irin yadda Zahra ta shiga kuma wacce zatayi fatan mijin da zata aura ya fuskanci matsalolin rayuwa irin yadda Yusuf ya fuskantar,
na kuma tabbatar duk wad'anda suka fuskanci irin rayuwar,
so irin zaman da zasuyi da juna kenan...!

Cikin motar ya ajeta kana ya rufe marfin sannan ya shiga tare da jan motar suka nufi Yusrah Hospital.

Bayan yan dube-dube da doctor Asiya tayi mata ta tabbatarwa Yusuf cewa ba matsalar komai dama normal masu haihuwan kule bayan haihuwa da minti 10 ko 15 wasu minti 7 jinin zai fara zubowa,
so in kasan haka kana haihuwa sai kayi maza ka gyara yadda jinin zai zubo ba tare da ya b'ata miki gidaba.
allurar rage rad'ad'i dana bacci ta mata kana dana ciwon ciki.

So daga nan suka nufi gida,
shi dai kam Yusuf harga Allah ta Zahra yakeyi yafi kula da lmarinta kan na yaran,
suna hanya ne ya d'an kalleta ganin ta fara lumshe ido alamun zatayi bacci dan allurar baccin ta fara aiki,
hannunshi yasa ya kamo nata kana yana driving da hannu d'aya cikin kula yace.
"Zahra."
a hankali ta kalleshi dan sam bai fiye kiranta hakaba sai Ummu Aryan,
ido ya d'an lumshe kana yace.
"Bacci ko?."
kai ta gyad'a mishi tare da d'an roggofowa jikinshi,
hannunshi yasa ya gyara mata konciyarta a jikin nashi kana yaci gaba da tuk'i.


Kafin su isa gida tuni tayi bacci,
har bakin parlour shi yaje yayi parking kana ya fita ya koma ta inda take tare ruggumota ya nufi k'ofar parlour,
sai ya kuma tsaya da sauri sabida sunyi kicibis da Maman Yusuf,
cikin tsoro tace.
"Na shiga uku Yusuf meya sameta daga ina kuke bata da lfy ne?."
da sauri ya girgiza mata kai kana cikin kontar mata da hankali ya mata bayanin komai, ya k'ara da cewa.
"Yanzun baccin tayi."
ajiyan zuciya ta sauk'e tare da tsuke fuska kana tace.
"Ni ka bani tsoro na jira na jira in ganku shiru har na gaji na taho sannan nazo ban sameku ba zan fitone nayi kicibis da ita,
toh juya muje ka kaimin ita d'akina."
cikin sanyi yace.
"Toh Maman Yusuf yadda kikace duk haka za'ayi."
ya k'arishe mgnar tare da juyawa ya nufi part d'insu Mama,
gashi tafiyar da d'an rata kana kuma jikin mai bacci da nauyi,
sosai hannunshi sukayi tsamifa,
ita kuwa Maman Yusuf binshi tayi a baya tana jin tausayinshi dan ta lura yafi son ta zauna a d'akinshi amman tsananin biyayyarsa tasa bai nuna mata rashin jin dad'inshi ba.
shiko Yusuf ji yake kome zata sashi zai aikata matuk'ar bai sab'awa umarnin Allah da manzonsa ba.

Kai tsaye bedroom d'in Mama ya kaita kan gado ya kontar da ita tare da jan blanket ya rufeta zuwa k'irjinta kana ya sumbaci goshinta sannan ya kuma matso inda yaga an kontar da yaran,
zama yayi cikin gadon sannan ya d'aukosu duka biyu ya ruggumeshi tare da lumshe ido yanajin so da k'aunar yaran na ratsa mishi jiki da zuciya,
murmushi yake tayi tare da yiwa Allah godiya daya nuna mishi tsatsonshi.

Yana zaune a haka Mama ta shigo da sallama yayinda Abba ke binta a baya wanda jin haihuwarne ya sashi baro wurin aiki yazo yaga jikokinshi kafin bayan azahar ya koma ya gabatar da shariyar da zaiyi.

da sauri ya isa gefen YUSUF kawai sai ya zauna bakin gadon,
tare dasa hannu ya jawo Yusuf da yaranshi ya ruggumesu duka,
wani irin mashahurin farin cikine ya dabaibaye zuciyar Yusuf ji yake duk duniya babu wanda ya kaishi farin ciki.
Mama kuwa wasu hawayen dad'ine suka rufeta,
jiyo muryar Hajja inna na sallama ne yasata nufi parlour da sauri,
inda ta samu suna cike a parlour don Abba tun kafin ya baro office nashi ya kira Daddy da Hajja inna ya sanar dasu,
aiko sai gasu duk sun taho Daddy da Hajja inna da Ummi da Aunty Amarya sai Ibrahim.


A bedroom kuwa Abba ya kasa sakin Yusuf don ji yake tamkar ya maidashi cikin cikinshi,
sai d'an bubbuga kafad'an Yusuf d'in yakeyi tare da cewa.
"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah Yusuf mun godewa Allah da kyautar da ya mana dama dukkan tsanani yana tare da sauk'i Yusuf Allah ya raya min kai da ahlinka, ni ku biyu rak Allah ya bani gashi kai kuma Allah ya baka biyu a lokaci d'aya."
misalta farin cikin Yusuf fa bazai fad'uba.

Suna cikin haka Su Daddy duk suka shigo don shima kanshi Daddy ai k'anine ga Maman Yusuf tunda ita yayarshi ce yar Goggonshi k'anwar mahaifinshi kuma matar yayanshi,
so babu wani nauyi dan ya shiga bedroom nata bare kuma Hajja Inna da take uwarsu bare su Ummi da suke faccalolinta kuma matan k'aninta so ba wani nauyi duk suka shiga,
so ganin Abba ne yasa Ummi da Aunty Amarya sukayi sairin komawa parlour sabida ai su kam shi surkinsu ne yayan mijinsu.

ita kam Maman Yusuf tama rasa me zatayi dan farin ciki.

Shi kuwa Abba hannun Daddy ya jawo,
hakan yasa Daddy ya rusuno tare da matsowa garesu,
cikin farin ciki Abba ya manna jikin Daddy da nashi ta gefen hagunshi yayinda Yusuf yaketa gefen damanshi cikin sanyin murya yace.
"Dukkan farin ciki daya samu zuriyarmu Aliyu kaine sanadi yayinda nine nayi sanadin dukkan bak'in cikin da muka shiga a baya Aliyu ina al'fahari da kai a matsayinka na d'an uwana ngdewa Allah daya azurtani da k'ani kamarka."
cikin rauni Yusuf yace.
"Abba nine silar bak'in cikinmu ba kaiba baka cutar damu da komaiba."
da sauri Daddy yace.
"Babu laifin kowa wannan hukunci ne na Allah, gashi yanzu komai ya wuce ai."
Hajja inna kuwa hannu tasa ta karb'i yaran kana ta fara shaga gashin kansu zuwa goshinsu sai ta kuma d'ago hannunta ta manna a goshinta,
wai tanayi musu maraba da zuwa duniya saida yayi musu haka sau bakwai-bakwai kana ta mik'awa Daddy su,
cikin happy yace.
"Kunga wannan d'a da komanshi irin na Aryan."
cikin tsananin farin ciki Yusuf ya d'an lek'o fuskar yaron yana cewa.
"Nima dai haka nagani."
dak'uwa Maman Yusuf ta mishi tare da cewa.
"Ba kunya 'yam fari nefa."
K'eya ya sosa tare da cewa.
"Maman Yusuf 'yan na biyu dai ko, wato har kin mance Aryan d'inki."
murmushi sukayi baki d'aya cikin sanyi,
duk sukayiwa yaran addu'a.

A parlour kuwa Aunty Amarya zame hijabinta tayi ta shiga kitchen,
ta ci gaba da aikinda Maman Yusuf ta fara, tare da taimakon Abu mai aikin Maman Yusuf d'in,
Ummi kuwa zaune tayi a parlour ruggume da Adnan tana bashi costac enshi don da yar jakarshi take tafiya,
tunda ba nono yake shaba.

a tare Daddy da Abba suka fito suka nufi parlour Abba,

Maman Yusuf kuma parlour ta dawo,
ta zauna kusa da Ummi kana ta karb'i Adnan yaro yayi k'ato gashi fari k'al kekkyawa don sak yayi kama k'anin ubanshi Ibrahim babban d'an Aunty Amarya yayan Zahra kenan
koda yake Ibrahim na kama da Suleiman over hakan yasa ake ganin kamannin Adnan da Ibrahim.
rawa take mishi yayinda yaketa b'ank'ala baki yana mata dariya ita kuwa Maman Yusuf sai biye mishi take don tana matuk'ar son Adnan tana addu'ar Allah ya rayashi kamar sauran yara wad'anda ba sheguba sabida

Please Login or Register in order to submit comment