Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da aka bata abubuwan da suka faru da ita a yarinta,
cikin ranta take cewa,
na shiga uku ni Zahra meyasa Allah ke yawan k'adartamin had'uwa da mutane marasa d'a'a shin menene a jikina dake jazamin wannan masifar,
sai ta kuma saki kuka maicin rai ta yadda su Raihana basa jinta a haka bacci ya saceta suma su Rafi'a tuni sunyi bacci.

Aryan kuwawa rai a b'ace ya shiga wurin Yusuf konce ya sameshi cikin blanket dan tuni ya gama cin abinda zai iya ci yayinda kofin kunun ke kan bed side alamun kunun ne k'arshen shansa,
ido ya d'an bud'e tare da kallon Aryan daya d'auki kulan pepper chicken d'in ya juya zai fita yaji Yusuf na cewa.
"Kai kazo mu kwana a nan mana tunda akwai bak'i a side d'in naka."
cikin k'ok'arin danne b'acin ranshi dan baya son Yusuf yasan abinda ke faruwa sabida yanaga zai magance abin yace.
"A a ba komai ai basu da yawa su 4 kawai ne wurin zai ishemu."
ido ya mayar ya lumshe tare da cewa.
"Allah kiyaye hanya."
shiko Aryan juyawa kawai yayi ya koma part d'inshi inda sukayi ta hira da yan uwan Mamansu.

A Girei kuwa
Abba ne zaune yayinda Mama ke gefenshi cikin shirin bacci,
cikin sanyi Mama tace.
"Yau gidan ba dad'i wallahi tunda yarannan suka tafi bikin nan."
cikin tsuke fuska Abba yace.
"Ba dai kunyi yadda ranku ke soba,
in banda sakaci ya za'ayi ku tura yaranmu wani wurin da baku da tabbacin tsaronsa. "
ita dai Mama shiru tayi sabida itama taso hanasu yaran ne nacinsu ya fiye yawa.
shi kuwa Abban gyara zama yayi tare da tsura mata ido cikin,
kamo hannunta yace.
"Maman Yusuf kenan kina bani mamaki wasu lokutan."
ido ta d'an zuba mishi tare da cewa.
"Abban Yusuf me nayi?."
ido ya d'an fitar waje tare da taune lips enshi yace.
"Bakya son laifin yaranku sannan kuma son kanki yayi yawa fa."
fuskantashi tayi da kyau tare da cewa.
"Son Kai kuma?."
ta fad'i haka dan kauda batun laifin yaran,
shi kuwa kai ya gyad'a alamar eh,
cikin mamaki tace.
"To a kan me nayi son kai d'in?."
kamar a mafarki taji yace.
"Akan Yusuf d'ina mana."
wani irin kallo Mama ta bishi dashi yayinda shi kuwa ya kamo hannunta sukayi cikin bedroom ganin dare ya fara nisa,
ita kam wani irin farin ciki takeyi kamar ta zubda ruwa a k'asa tasha sai binshi da ido takeyi rabon da ya alak'anta Yusuf da d'anshi tun kafin ya daki Hajja Inna,
ido ta zuba mishi jin yana cewa.
"Kin sashi yaje ya gaida kowa amman banda ni,
al'halin kin san ina begen ganinshi,
shekara 7 ban ganshiba bai ganniba,
wata k'il shi ko begena baya yayi."
ina ai ita kam Mama tuni hawayen farin ciki da tausayin kanta da d'anta takeyi,
cikin kuka ta rab'a kanta jikin kafad'an Abba murya na rawa tace.
"Ba son kai bane,
ka manta kai kace karya sake zuwa gidannan in ya shigo kuma a bakin aurena,
to wannan dalilin shiyasa bai zoba sabida baya son ya zama sanadin mutuwar auren da aka d'aura tun ba'a san da shiba."
kanta ya d'an k'ara mannawa a kafad'arshi tare da cewa.
"Toh yaje office na mana ya sameni a can."
hamdala Mama tayi tare da cewa.
"In sha Allah zai je,
amman kafin nanma ina zakaje d'aurin auren Raihana k'anwar Aryan?."
kai ya d'an jinjina tare da cewa.
"Naso inje amman lokacin da za'ayi d'aurin auren lokacin ina Jada wurin jana'izar abokina M Saraki don shima da hantsi za'ayi jana'izarsa,
sai dai in Allah ya kaimu ran Monday d'in."
cikin farin ciki tace.
"Toh Allah ya kaimu."
"Amin Amin."
yace tare da kashe musu wutan d'akin.


Washe gari ana idar da salla Zahra taci gaba da kitse kan Amaryar,
kafin 8:00 Am sun gama,
yayinda zuwa 11:00 Am farfajiyar gidan dama can wojen gidan ya cika mak'il da jama maza manya mutane domin harda mai martaba sarkin Adamawa yazo sabida dalilin Yusuf yan uwansu na Chadi ma wasu sun k'ara isowa yanzu.
Daddy, M Jabeer, Affan, Bashir, Sulaiman, Jafar, Sadik, Ibrahim,
yan uwan ango Faisal duk sunzo,
Sha d'aya da rabi dai-dai aka gama d'aurin auren Faisal da Raihana bisa sadaki dubu hamsin.


Bayan masu d'aurin aure sun watsene manyan duk sun fita a babban parlour inda nan waliyai suka zauna,
cikin fargaba Aryan ya kalli Yusuf dake zaune gefenshi sai zufa dake tsatstsafo mishi ta goshinshi,
cikin kula yace.
"Yusuf!."
ido ya bud'e da kyer tare da taune lips enshi sai ya kamo hannun Aryan ya mik'e da k'arfi sannan ya mik'e yayinda hannunshi d'aya ke dafe da kirjinshi.
cikin sauri Aryan ya bishi ganin ya nufi part d'inshi,
a parlour suka tsaya cikin kula Aryan ya k'ara gudun A.C. dan ganin yadda zufa ke tsatstsafowa Yusuf d'in gabanshi ya dawo tare da cewa.
"Yusuf me ke damunka ne?."
cikin taune lips enshi tare dayin mik'a a Jere a jere yace.
"Aryan zuciyata ke tsinkewa yau tunda safe nake ta jin wani irin azabebben tsinkewar zuciya da fargaba bacci ma ya gagareni."
cikin kula da bashi k'arfin guiwa Aryan yace.
"Haba dai broz kamar bana mijiba,
in sha Allah babu komai,
ka samu kayi bacci
bari inje wurinsu Affan kasan duk suna part na."
Kai ya gyad'a mishi dan shima yana son kadai cewa,
sabida wani irin zillo da yakeji gabanshi nayi,
ganin ya gyad'a mishi kai yasa Aryan fita.


Shi kuwa Yusuf tun 11:00 Am ya fara jin gabanshi na wani irin zillo da harbawa wani irin shauk'i yakeji duk da mararshi bata mishi ciwo amman sai zufa ke keto mishi ga tsinkewar zuciya,
ga sanyin A.C. na k'ara mishi sha'awa kuma in ya kashe wani irin zafi yakeji kamar zai kasheshi dole ya bar sanyin A.C. na ratsashi.
lips d'inshi na k'asa ya taune tare da rumtse idanunshi,
kanshi ya jingina da jikin kujerar da yake,
yanajin wani irin bak'on yanayin da bai tab'aji a rayuwarsa,
haka nan kuma yake jin tsinkewar zuciyarshi na tsananta a duk bugawar zuciyarshi,
idonshi ya bud'e a hankali tare da mik'ewa zaune,
ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa tamkar wanda yayi kuka mai tsanani,
lokaci d'aya kuma yaji tsikar jikinshi na tashi,
mik'ewa tsaye yayi tare da cewa.
"Innalillahi."
dan tsakiyar kanshi yaji yana wani irin 'yam-'yam,
tafin hannunshi ya kife kan tsaitin k'ahon zuciyarshi,
juyawa yayi ya nufi bedroom d'inshi yayinda yake jin bugun zuciyarshi na tsananta yanajin du- dumdum bakin gadonshi ya zauna dan wani irin azabebben sarawa da yaji kanshi nayi tamkar zai tsage gida biyu,
konciya yayi cikin wani irin yanayi,
ga azabar zufan da yakeji kuma ga rawan da jikinshi ya fara a take,
shiru yayi cikin blanket d'in daya yaketa goge zufan jikinshi dashi,
duk k'ank'antan motsin da zaiyi sai yaji kamar zare ranshi ake shirin yi,
ido ya lumshe tare da k'ara ambaton sunan Allah dan shi kam Yusuf gaba d'aya ya saki inda ya rik'e ya gama karaya kan mutuwa zaiyi dan bai tab'ajin makamancin wannan abin da yakeji ba.

Aryan kuwa dasu Affan suna cike a parlour shi da sauran yan uwan Ummansu wanda sai gobe zasu koma Cadi tunda wasunma yau suka iso,
hirarsu suketayi irin ta abokai ,
Sulaiman ne ya d'an kalli Aryan tare da cewa.
"Bari inje in duba Yusuf ko."
mik'ewa Affan yayi tare da cewa.
"Yauwa muje nima akwai sak'on da M Jabeer ya bani in bashi yasa hannu."
Aryan d'inne ya mik'e rik'e da hannun Rabi'u d'aya daga cikin yan uwan Ummansu,
binsu a baya yayi tare da cewa.
"Eh muje."
sam Yusuf a d'abi'arshi bai fiye rufe k'ofar d'akinshi ba shiyasa mafi akasarin lokuta za'a samu k'ofar d'akinshi a bud'e,
hakan yasa kai tsaye suka shige har bedroom,
yana jin shigowarsu yana kuma sauraron maganganunsu can sama-sama,
sabida zuwa lokacin ko idonshi bazai iya bud'ewa ba,
Sulaiman ne ya matsoshi tare da lek'a fuskarsa,
sai ya kuma juyo gasu Affan d'in cikin yin k'asa da murya wai dan karya tadashi a bacci,
ya kalli Aryan tare da cewa.
"Alhamdulillah ya samu yayi bacci,
kuma bisa dukkan alamu zazzab'in ya sauk'a dan sai zufa yaketa tsatstsafomishi tako ina."
kai Aryan ya jujjuya tare da matsowa ya kife tafin hannunshi kan goshin Yusuf d'in,
ido ya d'an zaro jin yadda jijiyoyin gishin nashi suke harbawa,
cikin tausayawa yace.
"Anya kuwa Sulaiman damafa tun d'azun ma yake had'a wannan uwar zufar,
kuma kaji yadda jijiyoyin kanshi ke harbawa ko dai zamu kira doctor yazo ya dubashi ne?."
yana jin duk mgnar da sukeyi amman ya gaza motsi,
Affan ne yayi d'an mik'a tare da yin hamma yace.
"Eh yana da kyau a nemo doctor yazo ya dubashi.
Rabi'u ne ya d'an matso tare da cewa.
"In sha Allah babu komai tunda yanzu ya samuyi yin bacci,
a barshi zuwa azahar in ya farka sai in dubashi."
Sulaiman ne yace.
"Alhamdulillah ashema muna tare da doctor."
Aryan Kuwa goshinsa ya d'an buga tare da cewa.
"Kaga ni nama rud'e na mance gamu ga doctor."
Sulaiman ne ya maso gefen gadon tare da k'ara gudun A.C. sannan suka juya suka fita tare da jamishi k'ofar,
shi kam Yusuf lamarinshi ya girmi zatonshi sam yau baya jin ciwon mararshi ko kad'an
amman jinshi yakeyi kamar doki dan wani irin shauk'i da azabebbiyar buk'ata yakeji tamkar in bai samu maceba zai iya rasa ransa,
haka yayi ta rayuwa cikin wannan yanayin a wannan wunin,
yayinda ciwon kai ya hanashi ko bud'e idonshi.

Bayan sallan azaharne Sulaiman ya koma cikin Girei,
parlour Umminshi ya wuce kai tsaye inda ya samu Amira tazo tun safe sai yanzu take shirin zata wuce gidansu Aryan d'in dan kai amarya,
nan suka zauna sunata d'an hira.
yayinda Aunty Amarya kuma take kitchen tana aikin abincin dare,
Ummi kuwa dama tun safe ta tafi gidansu Aryan tun lokacin da Daddy zaije d'aurin auren.

Mama ce ta fito daga part d'inta ta nufi part d'in Ummi,
bakin mashigar ta tsaya tare da d'an daga murya tace.
"Kamar Sulaiman nakeji ko?."
Amirace tace.
"Eh shine."
shi kuwa Sulaiman ruwan daya cika bakinshi da shine ya had'iye sannan ya mik'e tare da fitowa zuwa inda Mama ke tsaye,
yana rik'e da goran faron yace.
"Na'am Mama."
tsayuwanta ta d'an gyara tare da cewa.
"Daga ina kake ne?."
k'ara matsowa inda take yayi tare da cewa.
"Daga gidan su Aryan."
Kai ta gyad'a alamar gamsu sannan tace.
"Tun bayan sallan asuba da mukayi waya da Yusuf yake cemin yana cikin jama'a sai anjima zai kirani,
nayi ta jiran kiranshi bai kiraniba,
har dai zuwa 11:45 Am naga bai kiranba,
to tun d'azu nake kiranshi wayar na ringing amman baya amsa kiran,
shine da najika nace bari inji ko Lfy dai?."
Kai Sulaiman ya gyad'a tare da cewa.
"Laa ba komai Lfy lau,
ya dai ce kanshi na d'an ciwo kuma muna ganin rashin isashen bacci ne yasa,
to lallai tun da aka gama d'aurin auren ya shiga pat nashi,
toh kafin in taho d'innanma mun shiga muka samu yana bacci,
toh inaga shiyasa baya amsa kiran naki,
amman ba komaifa kan ya bar ciwon dama rashin baccinne shiyasa mukace a barshi kar a tasheshi sai ya samu isasshen baccin."
ajiyan zuciya ta sauk'e tare da juyawa tana cewa.
"Toh Allah ya k'ara sauk'i."
"Amin Amin."
yace tare da juyawa ya koma gun Amira da taketa kiran Jafar wai yazo ya kaita amman baya ansa kiran,
tsaki taja tare da cewa.
"Mitsssw wallahi Jafar ya iya rashin mutunci."
zama Sulaiman yayi tare da cewa.
"Meya miki?."
baki ta tura tare da cewa.
"Tun d'azu fa naketa kiranshi amman baya amsa kiran kuma shine da bakinshi yace shi zai kaini gidansu Raihana."
gyara konciyarshi yayi tare da cewa.
"A a ni karki wani huce a kaina dan wlh yanzu na dawo daga can bazan koma yanzuba,
nida can sai da dere."
tsaki taja tare da cewa.
"Allah yayi dai inada mijin da zan kira yazo ya kaini."
murmushi yayi sannan yace.
"A a dan Allah karki kirashi ai sai yace k'annen naki sun rainaki,
bari dai in kira miki Jafar d'in."
fita yayi tare da cewa.
"ai naga motarshi sai dai ko bacci yakeyi a d'akinshi."
tana biye dashi a baya har sukazo tsakar gida inda suka samu Mama da Aunty Amarya suna zaune yayinda Hajja Inna ke gefensu,
amman duk suna zaune shiru irin babu wani hira sosai a tsakaninsu,
shi Sulaiman kai tsaye d'akin Jafar yaje inda ya sameshi yana konce sai d'an daddamk'e cikinsa yakeyi cikin fad'a da bada umarni yace.
"Kai Jafar ai tunda kayi al'k'awarin kaita, sai ka tashi kaje ka kaitan."
cikin k'arfin hali Jafar d'in ya mik'e zaune tare da cewa.
"Ayyah Ya Sulaiman ka kaita mana."
cikin tsuke fuska yace.
"Kai tashi bana son iskanci da raini ai yanzu da yawon kankane da sai ka karad'e jimeta da yola a wuni d'aya."
yana fad'in haka ya juya ya tafi,
don dole Jafar ya fito yana tafiya yana ciccije baki,
ita kuwa Amira sai dungure kanshi tayi tare da cewa su Mama.
"Toh na tafi."
"Allah kiyaye hanya." sukace mata a tare,
Aunty Amaryace tace.
"Yauwa in kinje kicewa su Zahra kadafa su yarda su kwana gidan amarya su dawo gidansu Aryan d'in su kwana yafi tsaro hankalina zaifi konciya."
to kawai Amira tace tana mamakin yaushe Aunty ta fara jin tsoron yaranta su nesanceta.
Mama kuwa itama ido ta zubawa Aunty Amarya kamar yadda Hajja Inna tayi,
kusan a tare sukace.
"ikon Allah yau kuma kece da tunanin inda yaranki zasufi samun tsaro."
dariya kawai tayi tare da ci gaba da share tsakiyar gidan.





*By*
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

*Page 2⃣9⃣*

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Can cikin fadar masarautar Yola kuwa,
sai bayan sallan la'asar ne,
M Jabeer ya tura jakadiya da tayi masa kiran Affan,
bayan taje ta isar da sak'on kiran ta dawo ta shaidawa M Jabeer d'in cewa yace.
"To yana zuwa."
amman shiru-shiru bai zoba saida aka kuma tura d'an aike sannan yazo,
koda yazo da alamun rashin nitsuwa tare dashi,
shiko M Jabeer sam bai luraba sabida saurin da yakeyi,
takardun da Affan ya dawo mishi dasu d'azu ne wanda yace ya bawa Yusuf yasa hannu ya kuma mik'a mishi tare da cewa.
"Maza amshi ka kaiwa Yusuf yasa hannu a takardurnan,
ka kawo minsu dan bayan sallan isha'i jirginmu zai tashi."
shi kam Affan kafin yayi wata mgnarma tuni M Jabeer ya juya ya fice a wurin tare da zugar fadawanshi,
dogon tsaki Affan yaja tare da rumtse jajayen ida nunshi,
sanin bazai iya yin tuk'in bane ya sashi neman,
rakiyar fadawansa,
motoci 3 suka d'auka d'aya ta gaba ta fadawa ce ta bayama fadawanne a ciki ta tsakiyar kuma Affan d'inne yake konce a bayan motar sai direbanshi tare da bafade d'aya a gaban.


Sannan suka nufi cikin jimeta.


A gidan biki kuwa,
Zahra tun da ta shiga yin al'walan sallan la'asar tayi wonkanta,
dan an kusa zuwa d'aukan amarya kuma tuni wasu k'awayen har sunyiyyi wanka ita kawai suke jira dan tace sai ta shirya zata fara musu kolliyar.
tana fitowa ta shirya sauri-sauri tayi wa kanta d'an karen kolliya,
sannan ta sanya wasu riga da siket na wani yadi mai azabar taushi da shak'i mai color red white and blue sai ratsin yellow-yellow a cikin white d'in,
Siket d'in dogone har k'asan idon sawunta sai daifa yayi matuk'ar matseta sai rigar kuma mai d'an guntayen hannu daga gaban rigar kuwa wasu kyawawan igiyoyine kalar yellow ke sark'afe sai ribbons da ta kama himilin gashinta kanta dashi,
tudun breast d'inta daya k'arawa shigar tata armashi ta baya kuwa abin sai wanda ya gani,
wata cancad'ed'iyar laffaya ta fitar mai kala uku Red white and yellow,
ta yaneshi a jikinta,
turaru kanta ta feshe jikinta dashi sannan ta matso da Jakarta red wanda kalarshi d'aya da takakminta
covern wayarta ta canza daga pink ta saka yellow mai ratsin jaja.
Rafi'a ce tayi kabbara tare da cewa.
"Wow kai Masha Allah,
ALLAH yayi halitta a nan."
murmushi tayi cikin jin kunya tace kai.
"Aunty Rafi na kaiki kyau ne?."
Amina ce ta d'an harareta dan ita Amina haka nan taji ta tsani Zahra cikin tab'e baki tace.
"Toh in kin gama jamana rai d'in sai kizo ki farawa amaryar kam in ma mu bazaki manaba."
Kunfa san Zahra sarai ta lura da kallonda Amina tayi mata shiyasa,
ta murgud'a baki tare da cewa.
"Toh ni ba haka tsarina yakeba sai na yiwa k'awayen amarya kafin in yiwa Amarya wanda yafi na k'awayen kyau."
Rafi'a najin haka ta matso gaban Zahra tare da cewa "Toh ki fara dani."
haka ta fara yiwa k'awayen amaryar makeup d'aya bayan d'aya,
yayinda sai lokacin wasu kuma ke shiga yin wankanma.


Yusuf kuwa sai bayan la'asar d'in ya samu d'an sauk'in ciwon kan ya fara lafawa,
zafin da yakeji kuma sai k'aruwan yakeyi,
mik'ewa yayi tare da taune lips enshi duka biyu dan wani irin k'ullewa da yaji mararsa tanayi,
Bathroom ya shige tare da sakarwa kanshi shower ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa tare da jan numfashi dan jin yake kamar zai shid'e,
wata iriyar zalamemmiyar sha'awa yakeji kamar zata kasheshi,
sauri-sauri yayi wanka sannan yayi al'wala,
bayan ya fitone ya shafa mai tare da fesa turaruka,
sallaya ya shimfid'a sannan yayi sallan azahar da la'asard'in da bai samu yayiba sabida larurar ciwon dayake tare dashi,
ya idar kenan yana ninke sallayar,
Aryan ya shigo tare da Dr Rabi'u,
murmushi sukayi tare da saurin k'arasawa gunshi cikin kula Aryan yace.
"Masha Allah ka tashi kenan?."
ido Yusuf ya d'an rumtse tare da gyad'a mishi kai alamar eh,
bai damu da rashin amsa mishi da baiyi da bakiba,
sabida duk wanda ya zauna da Yusuf ya san yana dad'abi'ar body language shiyasa duk sun saba da hakan,
mutum biyu ne wad'anda baya yiwa body language a duniyar nan Abbanshi da Malam Jabeer sabida su kuma sun tsani hakan harma gwara Abba a kan M Jabeer, cikin kula Aryan d'in kalleshi tare da cewa.
"Toh ya kake jin tsinkewan zuciyar yanzu?".
murmushi ya d'anyi tare da cewa.
"Alhamdulillah."
Dr Rabi'u ne ya matsoshi tare da cewa.
"Ya kamata a gwada BP d'inka dan hawan jinima yana sa yawan tsinkewan zuciya."
Kai ya jinjina tare da juyawa ya bud'e durowarshi ya zaro wasu fararen kaya riga da wando rigar irin d'inkin da matasan yanzu ke bala'in son koikoyar samfurin sabida a gun Yusuf mafi aka sari suke ganin salon d'inkin,
bakin gado ya ajiye kayan tare da juyowa gunsu Aryan cikin k'arfin hali murya can k'asa yace.
"In sha Allah zanyi k'ok'arin zuwa asibitin,
amman yanzu da sauk'i sosaima."
ta kalmi da hula ya d'auko duk masu kalar sararin samaniya,
ganin haka Aryan yace.
"Fita zakayi ne?."
kai ya gyad'a mishi alamar eh,
"Ina zakaje".
Aryan ya kuma tambayarsa fuska ya d'an tsuke tare da cewa.
"Zan shiga cikin Yola ne."
"Me zakayi a Yola kuma?."
Aryan ya tambayeshi yayinda suka juya zasu fita dan bashi wuri yasa kayan.
wondon rigar ya d'ago yana warware karin gugur tare da cewa.
"M Jabeer ne ke son ganina dan ya kirani kusan sau 5 toh ban samu na amsa kiranba saida na tashi na samu ya turomin text,
wai inyi maza inje akwai wasu takardu dazan sa hannu yau zai wuce abuja dasu dan daga fadar shugan k'asa suke."
OK Aryan yace sannan suka fito parlour anan suka zauna suka jirashi.

Shi kuwa Yusuf sauri-sauri ya shirya cikin tattausan voyel d'inan
mai bala'in tsada yadin shara-shara tamkar gyale har ana iya ganin shatin ves d'in dake cikin rigar,
farin yadin da hularshi da takalminshi kalar sararin samaniya suka had'u da kalar fatarshi suka zauna ras ya fito gwanin sha'awa sai k'amshi yake zubawa,
yayinda bakinshi ke d'auke da addu'o'i dan ya fara jin tsinkewar zuciyarshi na dawowa ga k'amshin turaren daya fesa d'in ya had'u da sanyin A.C sai ya bada wani irin kalan yanayi da ya sashi jin jijiyarshi ta harba da k'arfi,
key d'in motarshi da woyoyinshi ya sura da sauri dan son barin d'akin,


A parlour ya samu su Aryan inda tare suka fita,
har gaban motarshi suka rakashi,
suna tsaye a wurin har ya fita,
sannan su kuma suka juya suka koma part d'in Aryan.

Motor Yusuf na fita,
motar Idi mai caji yayiwa harabar gidan dirar mikiya.

Shi kuwa Yusuf yana fitowa bakin titin rauon about mai doki ya d'an gangara cikin gidan mai d'in dake kallon layin shiga gidansu Aryan,
tsaki ya ja sabida sai yanzu ya tuna jiya sunyi ta yawo duk sun k'arar da man cikin motar,
tsaki ya kuma ja ganin layin dake gabanshi,
tsaki ya kuma ja tare da cewa.
"Nigeria kenan, duk bayan kwana biyu sai anyi wuyan samun mai ko sai yaushe za'a rabu da wannan matsalar."
dole ya fara bin layi dan ko ya wuce nan zaiyi wuya ya samu mai d'in a gaba dan mafi akasarin gidajen mai d'in a rufe suke babu mai.

Yana cikin motar yaji wayarshi na ringing,
da sauri ya amsa kiran ganin Affan ne yake kiranshi.
Affan kuwa jin Yusuf ya d'aga wayar ya sashi yin gyaran murya tare da rumtse idonshi sabida wani abu da yakeji yana addabar ruhinsa,
shiko Yusuf cikin k'arfin hali yace.
"Affan ya kayi shiru?."
idon da ya rumtse ya bud'e tare da cewa.
"Yauwa Yusuf Hamma Jabeer ne ya aikeni wurinka,
toh nazo dai-dai mashigar layin kunnan sai naga wannan gidan mai d'in suna saida mai shine na d'an tsaya in saka mai sabida na kwana biyu bansa maiba."
gyara zama Yusuf yayi tare da cewa.
"Yauwa nima ina wurin."
da sauri Affan yace.
"Ta ina kake?."
kanshi ya d'an d'an d'ago tare da kallon motar gabanshi sannan yace.
"Ina bayan wata tirela."
shima kuwa Affan tashi zaune yayi tare da yujo kanshi ya kalli bayanshi sannan yace.
"Yauwa ai to motocinmu ne a gabar tirelan ai."
ido Yusuf ya rumtse tare da taune lips enshi yace.
"OK kunma kusa kan layi kenan?."
d'an gajeren tsaki Affan yaja tare da yin mik'a sannan yace.
"Eh mun kusa, baifi mota 11 bane a gabanmu,
kai kuma in an had'a da motocinmu da tirelarnan wata k'il mota 15 ne a gabanka."
Shima Yusuf tsakin yaja tare da matse cinyoyinshi dan ji yake kamar joystick d'inshi zata faso wondonshi ta fito waje cikin jin zillo yace.
"OK toh sai kunsha maid'in kawai sai ka kawomin takardun,
tunda yace sai bayan sallan isha jirginsun zai tashi ko?."
cikin fidda numfashi Affan yace.
"Eh haka yace min shiyasa nima na tsaya shan maid'in."
"OK." Yusuf yace tare da katse kiran,
wani irin a azabebben sha'awa yaji ya taso mishi wanda yafi na d'azu,
gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi sai wata uwar zufa da yaji ta fara tsatstsafo mishi tun daga tsakiyar kanshi har zuwa kan babban yatsanshi
lokaci d'aya kuma yaji mararshi ta fara zuk'a da tauna,
ji yakeyi kamar ya fita yayi ta goga joystick d'in nashi a tsakiyar titi kan kolta d'in ko zata dena harbawan da takeyi,
mik'a yayi tare da rumtse ida nunshi da sukayi jazir cikin rawan murya yake mgn.
"Innalillahi ya Allah ka yaye min wannan jarabar Allah ka sauk'ak'amin ya rabbil ka bani mafita in samu sassauci."
sai ya kuma matse cinyoyinshi tare da taune lips enshi.


Shi kuwa Idi zama yayi cikin motarsa yana tsumayin ta inda Zahra zata fito,
yasa a ranshi tana fitowa duk yadda zaiyi sai yayi ta shiga motarshi ya samu damar kaita gidanshi,
dama yaune yaci al'washi karbe budurcinta,
bayan Idi ya shiga da kamar 12 minutes sai ga motocin d'aukan amarya sun fara shigowa cikin gidan.

Tsala-tsalan motocine na gani na fad'a sukayi ta shigowa harabar gidan har saida ya zama babu sauran inda wata motar zata shiga,
yayinda canma wajen gidan motocine kusan 10 a jere a layin unguwar duk na d'aukan amarya ne,
yayinda motar idi itace can cikin gidan duk sauran a bayanshi suke.

Su Aryan kuwa tuni sun kaure da hirar zumunci da yan uwansu.



Zahra kuwa dasu Raihana tuni Zahra ta gama yiwa k'awayen amaryar nasu makeup d'insu inda sukayi shigarsu iri d'aya,
zama ta gyara tare da yin mik'a tace.
"Wash Allah na gskya fa Aunty Raiha na gaji."
Adda Zulaihat ce da ta shigo yanzu tace.
"Dan Allah kiyi maza ki k'arisa mata,
tun d'azufa yan kususu suka zo,
ga motocin d'aukan amarya sun cika harabar gidan."
Amina ce tace.
"Shiyasa nace a fara da amarya amman da yake rashin kunya ne da ita tana ganinmu kamar sa'anninta sai tace min ita ba haka tsarinta yakeba."
murgud'a baki Zahra ta d'anyi sai ta kuma kalli Raihana da tayi rau-rau da ido alamar zata fara kuka murya na rawa tace.
"Shima me yake sauri da zai turosu tun yanzu,
ni ban gaji da Hajjia Kaka ba."
sai kuma hawaye shar-shar nabin hab'arta,
ai tuni

Please Login or Register in order to submit comment