Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'auko wayar cikin sa'a ya samu wayar ba security number,
dan haka kawai number Zahra ya fara sawa,
kasancewar ya haddace number kai tsaye ya kirata ita kuwa lokacin tana konce ta gaza bacci sai juyi takeyi jin wayarta na ringing ya sata tashi zaune tare da d'agawa ,
jin muryar Aryan ne ya sata wastsakewa shi kuwa da gudu ya kuma dawowa parlour cinyar Yusuf ya d'ale tare da cewa.
"Ammi."
"Na'am Aryan ya akayi ne?."
cikin sauri yace.
"Ammi albishir."
murmushi tayi tare da cewa.
"Goro."
cikin d'aga sauti yace.
"Abeeh na zai aureki,
zaki dawo gidanshi kema kamar Aunty Mami da Uncle Affan."
shiru tayi tare da had'e fuska,
shi kuwa Yusuf zare wayar yayi tare da katse kiran kana yace.
"Aryan ka rage yawan surutu kaji ko?."
kai ya gyad'a mishi tare da cewa.
"Toh zan rag."
zaunar dashi tare da bashi biro yace.
"En maza yi abinda na saka."
Kai ya jujjuya tare da cewa.
"Ni bana son gidannan dokuna kawai nakeso,
na baka gidan kaida Ammina,
ina tare zamu zauna a ciki ko?."
kai ya gyad'a tare da tattara takardun sabida ya gane Aryan bazai fahimci manufarshiba,
so dole ya bari zuwa wani d'an lokaci,
hira sosai sukayi tayi sun tattauna abubuwa da yawa anan Yusuf ya bawa Aryan sak'on mgna zuwa gun Zahra Amman yace ya bari sai ya koma ya gaya mata kuma karya fad'a mata a gaban mutane.
haka dai sukayi ta hirar sirri har zuwa k'arfe d'aya sannan Aryan ya fara Hamma kana ya kalli Yusuf cikin sanyi yace.
"Abeeh zanyi bacci, kaga gobene zamuyi musabaga kuma da safe za'ayi kar mu makara."
murmushi yayi tare da cewa.
"Allah ya kaimu ya baka sa'a kazo na d'aya."
cikin sanyi yace Amin kana ya kalli Yusuf tare da cewa.
"Daga Gobe dai zan bar makarantar har abadan ko?."
cikin gyad'a kai Yusuf yace.
"Sosama don jibi za'ayi train bud'e makarantarka Yusrah."
kai ya manna k'afad'ar Yusuf tare da cewa.
" Yauwa kaga Salim bazai sake ganinaba, bare yace min shege."
cikin lumshe ido Yusuf ya gyad'a mishi kai,
ganin haka yace.
"To muje mu konta."
dole ya mik'e duk da shi baya jin bacci domin wasu maganganun yaron sun tsaya mishi a rai,
bayan sun kontama saida sukayi yar hira kana sukayi bacci.

Ita kuwa Zahra magnar Aryan ta samata fargaba.


Washe gari da safe kuwa Yusuf ya shirya Aryan kana ya wuce dashi makarantasu,
inda Jafar ya kai Zahra da aminaryata Dija,
Aryan babbama yaje domin Yusuf ya gaya mishi hakama Affan Mami Adda Amira da Zulaihat tare da Sharifa,
Daddy yaso zuwa sai dai aikin tiyatar wota mata ta tsareshi dole bai jeba.


Anyi musabak'a an gama Lfy,
Aryan yayi nasarar zuwa na d'aya a yan aji biyu inda ya kawo haddar izu biyar, cikin tak'ib da cikar tajwid,
daga nan aka rarraba kyautuka inda Yusuf d'in ya bawa Aryan kud'i masu yawa yace yaje ya bada kyautarsu ga yan aji shida domin sunyi k'ok'ari sosai.
haka dai akayi komai cikin farin ciki,
nan Aryan ya rink'a yiwa abokanshi sallama tare da nuna musu Abeeh enshi yana gaya musu an gina mishi makaranta da ban zai bar makarantarsu,
da yawa malamai sai tausayin Aryan ya rufesu domin sun san basu kyautata mishi dan kawai yazo duniya ta hanyar da bata kyautatuba.
bayan duk an tashi har zasu shiga mota sai ya juya da gudu hannun Salim Adam ya jawo tare da kawoshi gaban Yusuf cikin jin dad'i yace. "Salim kaga Babana ko ga Abeeh nama yafi Abbunka kyau, kaga nima ba shege bane ga Ammina ga Abeeh na."
shiru Salim yayi dan ganin idanun su Yusuf badon haba kam da ya zagi Aryan,
shi kuwa Aryan cikin sanyi ya mik'a mishi hannu tare da cewa.
"Ni dai na yafe maka da kai da Mamanka,
dan Abeeh na yace in yafe muku tunda Allah yana son masu hak'uri to nayi hak'uri na yafe muku."
cikin jin kunya Amiran tazo taja Salim d'in tare da juyawa suka tafi.

Su kuwa cikin sanyi Zahra ta kalli Yusuf tare da cewa.
"Hamma Yusuf bani shi mu koma gida mana,
Mamace tace in kai mata shi wai tayi kewarshi jiya har mafarkinshi tayi."
ido ya d'an zuba mata yana ganin yadda k'aunar yaron ke bisa fuskarta,
ta wani rik'e hannunshi gam kamar tana tsoron kar Yusuf d'in ya kwaceshi,
Jafar kallonsu yake yadda sukasa yaron a tsakiyarsu,
Affan da har zai wuce ya lek'o ta window motarshi tare da cewa.
"Da ka kaisu gidanka ai sai ka zauna kayi ta kallonsu tunda sun zamar maka tv."
bai kula Affan ba shi kuwa Affan dariyar shak'iyanci yayi tare da mace,
hakama Aryan babba saida ya musu tsiya,
Safwan kuwa wanda shine wanda yazo ya d'auki shirin musabak'ar dan sawa a gidan TV insu,
sai saita camera yayi yana viewing ensu,
ganin duk sun tsaya sun tsurawa yaron idone yasa,
Dija fitowa tare da zuwa kusa tace.
"Zahra kizo mu tafi."
To nanfa Safwan kuwa ya meda akalarshi kan Dija gaba d'aya sai ya mance da haushin Yusuf da yakeji,
ita kuwa Zahra cikin sanyi tace.
"Please Hamma Yusuf barshi mu tafi."
kai ya gyad'a mata tare da cewa.
"To sakeshi zamuyi mgna zaizo ku tafi."
jin haka ta sakeshi sabida tasan ba k'arya zai mataba tunda yace to tofa to dinne,
juyawa sukayi ita da Dija suka shiga motar Jafar,
shi kuwa d'aga Aryan yayi tare ajiyeshi kan drawing sit kana ya bashi hannu,
murmushi Aryan yayi tare da bashi hannu shima,
rik'e juna sukayi na wasu dak'ik'u kana Yusuf yace.
"Kayi Al'kwari ko Aryan?."
Kai ya gyad'a tare da cewa.
"Eh Abeeh nayi al'k'awari."
murmushi yayi tare da cewa. "To Allah ya maka al'barka"
Amin yace tare da cewa.
"Abeeh dan Allah kaima kayi al'k'awari kaji ko my Abeeh?."
cikin sanyi da mutuwar jiki Yusuf ya gyad'a mishi kai tare da cewa.
"Aryan nayi al'k'awari."
cikin tsananin farin ciki yayi tsalle ya mak'ale wuyan Yusuf tare da cewa.
"Yauwa my Abeeh kaini wurin Ammi na."
juyawa yayi dashi a yadda yake mak'ele da wuyan nashi murmushi yaketayi sabida maganar da Aryan ke mishi a kunne,
a haka suka isa motar Jafar,
inda Zahra ke zaune,
ya bud'e kana ya roggofo ta yadda in Aryan ya saki wuyanshi zai zauna kan cinyarta,
shi kuwa Aryan cikin sauri ya saki wuyan Yusuf sai ya kuma rik'o hannunshi yayinda yasa hannu d'aya ya rik'o hannun Zahra,
kamar a mafarki sukaji ya had'e hannunsu wuri d'aya,
kana yayi rau-rau da ido alamun zaiyi kuka,
yayinda ita kam Zahra tuni jikinta ya mutu sai shak'i da idanunta keyi alamar hawaye sun ciko idon.
shi kuwa Yusuf cikin k'arfin hali ya murza hannunta dake rik'e dana Aryan murya can k'asan mak'oshi ya bud'i baki a hankali yace.
"i......!




by
*GARKUWAR FULANI*
[26/01 6:16 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 15*

*NA*

*AYSHA ALIYU GARKUWA*






Sisters ga page 15 da 16 amman ban samu damar yin Editing ba.





"Idan kukan yayi yawa zai
miki illa a zuciya da idanu,
zaki kuma sawa gudan jininmu rauni da ragwanta, ya isa haka ki dena kuka in dai ba so kike kisa Aryan ya tuhumeni da kasa cika mishi al'k'awarin da nayiba."
ido ta tsura mishi cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa,
shi kuwa Yusuf lumshe idonshi kana ya bud'esu a hankali tare da rege girmansu a hankali ya rink'a jujjuya mata kwayar idanun nashi,
ita ko Zahra komawa tayi ta jingina da jikin sit d'in tanaji gaba d'aya gabban jikinta na sakewa kasala mai k'arfi ya rufeta,
tuni idanunta suka fara lumshewa suda kansu,
da kyar tasa hannunta d'aya ta jawo Aryan ta ruggumeshi gam,
yayinda tuni bugun zuciyarta ya tsananta,
shi kuwa Hamma Yusuf k'ara rokwofowa yayi kan Aryan dake manne a k'irjinta,
a hankali ya manne lips nashi kan tsakiyar goshin Aryan,
wani tattausan kiss ya manna mishi kana ya d'ago kanshi tare da yin murmushi har saida dimple d'in tsakiyar goshinshi ya d'an lotse,
yatsarshi ma nuniya ya saka gefen kumatinshi yayiwa Aryan alamar shima ya sumbaceshi.
murmushi yayi tare sa hannunshi duka biyu ya sank'alo wuyan Yusuf kiss ya manna mishi a kumatunshi duka biyu kana ya mishi a goshi sannan ya koma ya zauna tare da cewa.
"Allah ko Abeeh gobe dai zaku tafi da Ammi na."
murmushi yayi tare da sa hannu ya sha kanshi kana ya d'aga mishi gira d'aya.
Shima Aryan sai ya koikoyi Yusuf d'in amman shi sai girar duka biyu suka d'agu,
dariya Yusuf da Jafar sukayi,
shi kuwa Aryan sai ya kamo lips enshi na k'asa ya tauna ganin yadda Abeeh shi yayi bayan ya bar dariyar aifa, sai Yusuf ya kuma d'aga mishi gira d'aya,
a haka dai sukayi sau uku ana hud'u sai gashi shima ya samu ya d'aga gira d'aya,
aifa sai yayi tsalle ya mak'ale wuyan Yusuf tare da cewa.
"Ehh Abeeh ya koya min, Ammi kema zai koya miki."
ita kam Zahra hannu tasa ta b'amb'aro Aryan daya mak'ale jin ta kasa janshi ne yasata sunkuyowa sai taga ashe shima Yusuf yasa hannunsshi d'aya ya zagaye bayan Aryan,
ido suka had'a sanda ta kalli fuskarshi,
bak'i ya tab'e tare da d'aga mata gira d'aya alamar,
ya dai jashi mana in zaki iya,
ai da sauri ta janye idanunta murya can k'asan mak'oshi tace.
"Hamma Yusuf barshi mu tafi mana."
ajiye Aryan d'in yayi tare da sunkoyowa kanshi kamar dashi yake mgna yace.
"Bana son rabuwa dashi ne ko na one second shiyasa."
shi kuwa Aryan murmushi yayi kana yace.
" Abeeh,
anjima kazo mu tafi tare."
kai ya gyad'a mishi alamar to,
Jafar ne ya gyara zama ganin sam Hamma Yusuf baida niyar barinsu su tafi,
cikin girmamawa yace.
"Ayyah Hamma Yusuf saurifa mukeyi."
jin haka sai ya matsa gefe tare dasa hannu ya rufe musu marfin motar,
har jafar ya tada motar kuma sai ya dawo kusa dasu tare da zura hannunshi bisa kan Aryan ya aza hannun tare da cewa.
"Sai nazo ko my happiness."
cikin jin dad'i yace.
"Toh Abeeh kazo da wurifa."
Kai ya jinjina kana ya matsa gefe tare da yi musu bye bye,
yayinda shima Aryan bye bye yakewa Yusuf d'in.



Bayan sun fita daga harabar makarantar ne,
Yusuf ya juya shima ya shiga motarshi ya tafi yanata murmushi tare da taune lips enshi.

Shi kuwa Safwan, tuni yama gama sarewa da lamarin Yusuf,
shiyasa yaketa gudurtawa zaije ya samu Daddynshi ayita ta k'are tunda dai dama Hajia Yabi cewa take sai dai bayan ranta,
toh kuma Allah yayi ikonshi yau kwananta biyar da rasuwa kenan,
don deren randa Yusuf ya dawo ta rasu,
shiyasa ma Safwan bai samu sukunin zuwa wurin Zahran ba.



Suna isa gida ko parking Jafar bai k'arisa yiba Aryan yace.
"Ammi fitar dani inje in gayawa Abba ni nazo na d'aya."
cikin kula tace.
"Toh ai dai duk saurinka ka tsaya a gyara parking."
cikin rauni yace.
"Dan Allah dai kinga zai fitane kar ya fita ban gaya mishiba,
kuma Abeeh nama ya aikeni wurinshi."
bata ko saurareshiba sabida tasan nacin Aryan shi kuwa Aryan sai lek'owa yayi ta window yana cewa.
"Abba jirani karka fita."
jawoshi tayi ta zaunarshi bisa cinyarta cikin fad'a tace.
"Wai Aryan lfyarka kuwa ai Abban ba Tabbata zai a wojenba zai dawo ko."
cikin rauni ya kalleta murya na rawa yace.
"Ammi ai kafin Abba ya dawa na tafi bazai dawo ya sameni ba shiyasa nake son gaya mishi aiken Abeehna kingafa Al'k'awari nayiwa Abeeh na."
cikin mmaki tace.
"Haaah to ina zakaje?."
bai bata amsaba ya ganin Jafar ya tsada motar ai a guje ya bud'e marfin tare da ficewa,
kai tsaye gaban motar da Abba ke ciki ya nufa.
cikin d'aga sauti Zahra da Dija suka had'a baki wurin kiranshi.
"Kai Aryan mota na tafiya zakaje kasha gabanta."
ai bai ko juyo ya kallesu ba,
ganin haka yasa Jafar fitowa da gudu yabi bayanshi da nufin kamoshi.
Shi kuwa Abba kamar daga sama yaga Aryan a gabanshi ya tsaya tare da ware hannu da k'afa alamar wai ya tare Abba,
cikin wani irin tsananin firgita da tsoro Abba ya taka birki har saida ya koma baya kanshi ya bugi majinginar sit d'in.
ido ya rumtse da k'arfi tare da cewa.
"Alhamdulillah."
Zahra kuwa d'aura hannunta tayi a kai tare da rumtse idanunta jikinta duk kerma yakeyi,
har saida taji Dija tace Alhamdulillah sannan ta bud'e idonta,
Jafar kuwa da sauri ya kamo hannunshi,
shi kuwa sai janye hannunshi yayi tare da cewa.
"Uncle Jafar Abeeh nefa ya aikeni, wurinshi."
jin haka Jafar ya sakeshi tare da bin bayanshi,
shi kuwa Abba ya kasa motsi sabida fargaba da tsoron da ya rufeshi,
kai tsaye Aryan ya nufi motar Abba yayinda su Zahra suka zuba mushi ido,
yana isa wurin sai ya koma gefen inda Abba yake,
cikin nitsuwa yasa hannu ya bud'e marfin motar,
ganin yadda Abba ya zura mishi ido sai yayi maza ya durk'usa tare da sa hannu ya kamo kunnenshi, kana cikin sanyi yace.
"Abba kayi hak'uri na tareka, nasan kafin ka dawo na tafi shiyasa nakeso in gaya maka ni nazo na d'aya a ajinmu."
ajiyan zuciya mai nauyi Abba yaja domin ganin Aryan yakeyi tamkar lokacin da Yusuf yake k'arami,
cikin sanyi da jin k'aunar yaron na ratsashi yace.
"Masha Allah, Aryan Allah yayi maka al'barka, to yanzu kyautar me kakeso in yi maka?."
gyara durk'usonshi yayi tare da yin k'asa da murya kana ya kalleshi ido cikin ido murya na rawa yace.
"Ni dai ka yafewa Abeeh na,
yace min ya maka laifi wai kana fushi dashi shiyasa ka hanashi zuwa ginka."
Sai ya kuma sunkuyar da kai hawaye na zubowa a idanunshi murya na rawa yaci gaba da cewa.
"Abeeh na yacemin ka haanashi ganin Maman Yusuf,
yana son ganinta,
shine yace in baka hak'uri ka yafe mishi,
yace nima in yafe mishi kuma ni na yafe mishi, Ammi nama zan rok'i ta yafe mishi."
cikin tsananin rauni da mutuwar jiki Abba ya mik'o mishi hannu Alamar ya taso yazo amman sai ya mak'e kafad'a kana yasa d'an tafin hannunshi ya goge hawayenshi murya na rawa yace.
"Abba dan Allah ka yafewa Abeeh na,
wlh yace in gaya maka shi bamazinaci bane k'addarashe tazo mishi a haka,
please Abba ka yafewa Abeehna."
gaba d'aya ya karya zuciyarsu tuni hawaye ke zuba a fuskar Zahra,
da sauri ta juya tayi cikin gida sai ta kuma tsaya tare da yin murmushi still hawaye na zubowa,
juyowa tayi jin muryar Abba na cewa.
"Aryan na yafewa Abeehnka nasan shi bamazinaci bane,
na yafe mishi duniya da lahira,
shima Allah ya raya mishi kai kayi mishi biyeyya fiye da yadda kamin."
sai ya kuma sunkuyowa ya d'agoshi tsaye tare da share mishi hawayenshi kana yace.
"Ka dena kuka jikan Abba da Daddy kayi dariya kaji abokina,
na yafewa Abeeh inka."
cikin murmushi yayi tsalle tare da cewa.
"Abba Abeeh na ya gode."

bai jira cewar Abba ba ya nufi cikin gida a guje.

ganin haka Jafar, Dija, Zahra suka bishi a baya suna dariya.

shi kuwa Aryan kai tsaye bedroom d'in Mama ya wuce,
tana parlour tana kiranshi ma sai cemata yayi.
"Ina zuwa dai Maman Yusuf."
dariyar jin dad'i tayi domin duk lokacin da yace mata Maman Yusuf tofa yana tuna mata k'uruciyar gudan jikinta.

Shi kuwa Aryan yana shiga ya fito da wayar da Yusuf ya samishi a aljihunshi tana nad'ar duk mgnar da sukeyi,
kana ya kawo woyar kusa da bakinshi cikin rad'a-rad'a yace.
"Yauwa my happiness kaji Abbanka ya yafe maka ko,
Toh bari in kirawo Mamanka kuma."
sai ya tura wayar gefe tare da d'aga murya yace.
"Maman Yusuf! Maman Yusuf!!!."
"Na'am tace tare da shigowa gefenshi ta zauna kana tace.
"Wanna kiranfa duka na menene?."
bai kulataba sai ya matso gabanta tare da rusunawa kana ya kama kunnenshi cikin sanyi yace.
"Dan Allah Maman Yusuf ki yafewa Abeeh na,
ki dena fushi dashi."
ido ta zuba mishi na wasu yan dak'ik'u kana tayi ajiyar zuciya tare da cewa.
"Waya ce maka ina fushi dashi?."
murya can k'asa yace.
"Shine ya gaya min jiya da dare da muna hira kuma yace in nema mishi yafiyarku to ni kuwa nayi al'k'awari shiyasa nakeson ku yafe mishi."
Numfashi ta furzar tare da kamo hannunshi kana cikin sanyi tace.
"Toh ka gaya mishi ni banyi fushi dashiba ba kuma zanyi fushi da shiba, na kuma yafe mishi duniya da k'iyama ina kuma yin addu'ar Allah ya huci Abbanshi."
cikin jin dad'i yayi dariya tare da cewa.
"Yauwa my Abeeh kaji ko Abban Yusuf ya yafe Maman Yusuf ma ta yafe."
ita dai Mama sai ido ta zura mishi shi kuwa Aryan sai d'auke wayar yayi ya nufi d'akin Zahra.

Inda ya samesu suna cin abinci,
gefenta ya zauna tare da cewa.
"Ammi kiyi sauri kiyi min wonka kar suzo su sameni da dotti."
kai ta jinjina mishi tare da cewa.
"Yanzu dai zoka ci abinci in ba hakaba kuma in hanasu zuwa d'aukarka."
murmushi yayi tare da cewa.
"Hmmmm Ammi ai ko ya zakiyi sai sunzo,
ni na k'oshi yau bana jin yunwa."
fuska ta had'e tare da ce mishi dolefa yaci abinci,
shi kuwa ya kafe wai bazaiciba harda cewa.
"Ammi babu rabona fa a ciki duk na gama cinye rabona ai,
kawai ni kiyi min wonka kinji an fara kiran sallan azahar ko."
dole ta hak'uri sabida tasan zumud'in Aryan kuma tasan in yaje Abeeh zai sashi yaci abincin a dole.
burosh ya farayi kana tayi mishi wonka,
sannan yayi al'wala,
suna fitowa ya kalli Dija cikin sanyin murya yace.
"Aunty Dija fito min da kaya kafin Ammina ta shafa min mai ko."
to tace kana ta matso durowarsu ta bud'e ta fidda mishi k'ananan kaya,
ruwan goro sai yace mata shi yau bazaisa k'ananun kayaba,
cikin d'an fidda numfashi Zahra tace.
"Toh sai wanne irin kaya kakeso."
turare ya mik'oma alamar ta fesa mishi sannan cikin sanyin sauti yace.
"Manyan kaya."
jin haka Dija ta fito mishi da wasu kayanshi green riga da wond'o na wagambari.
Murmushi yayi mata tare da cewa.
"Malamin yace wannan itace kalar da tafi yawa a aljannah,
shiyasa nake son kalar,
amman yau farin kaya zan saka."
ita kam Zahra gaba d'aya sai taji jikinta ya mutu,
sai ta zuba mishi ido,
Dija kuwa murmushi tayi tare da cewa.
"An gama bari in zab'o maka."
kai ya gyad'a tare da matsowa kusa da ita,
wani tattausan yad'i ta zaro yad'in fari kal kal sai shek'i da sulb'i yake,
kana ta fito mishi da boxer da vest suma farare,
hannu ya dunk'ula tare da mik'ar da babbar yatsarshi alamar jinjinawa kana ya matso ta samishi kayan,
sai ya kuma cewa.
"Aunty Dija bani farin hula da takalmi."
cikin k'aunar yaron ta d'auko ta bashi gaban Zahra ya dawo tare da cewa.
"Ammi k'aramin turaren da Abeeh na ya saya min yafi k'amshi."
ba mgna sai mik'a mishi turaten tayi aiko ya karb'a ya feffesa sannan ya juya ya fita tare da cewa.
"Ammi bari inje inyi sallah kafin su zo."
kai ta gyad'a mishi kana itama taje tayi al'wala hakama Dija.
bayan sun idar da sallane Dija ta sallami su Mama ta tafi gida.


Ita kuwa Zahra tana dawowa daga raka Dija sai ta koma bedroom d'in da nufin tayi d'an bacci kafin LA'asar in tayi salla ta shiga kitchen.

Ta konta bada dad'ewaba taji shiganshi,
gabanta ya tsaya tare da cewa.
"Ammi baki da lfya ne?."
cikin kula tace.
"A a lfyata lau Aryan bacci zan d'anyi."
gyara tsayuwarshi yayi tare da cewa.
"Ayyah Ammi bani 5 minutes zamuyi mgna."
cikin mutuwar jiki tace.
"Ka bari mana sai na sai nayi baccin na tashi."
kai ya rausayar alamar to amman kuma da alamar baiso hakamba ganin haka sai taji ba dad'i itama,
sai ta mik'e zaune tare da kamo hannunshi ta haurar dashi kan gadon kana ta zaunar dashi suna fuskantar juna cikin sanyin jiki tace.
"Toh muyi mgnar ina jinka."
murmushi yayi cikin jin dad'i kana ya gyara zama tare da cewa.
"Uhymmm Ammi kin san wani abu?."
kai ta jujjuya tare da cewa.
"Ya za'ayi in sani bayan baka gaya minba."
cikin sanyin murya kamar rad'a yace.
"Ammi! Abeeh na yace min wai duk duniya bayida abokin shawara sai ni."
kanshi ta shafa tare da cewa.
"Ni ai hakane bani da abokin shawara sai kai."
murmushi yayi cikin rauni yace.
"To keda Abeeh na ku zama abokan shawara,
tunda duk kuna sona."
kai ta gyad'a mishi cikin sanyin jiki,
shi kuwa hannunta ya kamo tare da cewa.
"Abeeh na yace in ce miki ya gode da hallacin da kikayi mishi."
cikin sauri tace.
"Hallacin me?."
idonshi ya rumtse da k'arfi tare da cewa.
"Halaccin rufa mishi asiri da kikaso kiyi,
yace min duk duniya kece suturarshi ta rufin asiri,
yace min bashi da Garkuwa sama dake,
yace min in ce miki kalaman bakinshi sunyi k'aranci wojen neman yafiyarki."
sai ya kuma lumshe ido sai ga hawaye car-car cikin rawan murya yaci gaba da cewa.
"Abeeh na yana kuka kamar yadda nakeyi yanzu,
yace min in nema mishi yafiyarki ki gafarceshi biza zalumcin daya miki,
yace min kiyi mishi uzurin baya haiyacinsa ya aikata komai gareki,
yace wai nima in yafe mishi."
sai ya kuma kalli Zahra da take rik'e da hannunshi sai kuka da takeyi mai sanyin sauti,
cikin rauni da rawan murya yaci gaba da cewa.
"Abeeh na yace ba halinshi bane,
Allah ne ya k'addara zai samar dani ta bahaguwar hanya,
yace in gaya miki ya gode da suturar da kikayiwa sirrinku,
yace min kece suturarsa, kece nasabarsa, kece garkuwarsa, kece mai kare mutuncinsa a lokacin da ke kika rasa naki mutuncin a silarsa."
sai ya kuma sa tafin hannunshi yana share mata zafafan hawayenta dake zubowa cikin kuka yace.
"Ammi ki yafewa Abeeh na ki rufa masa asiri kamar yadda yace kin tab'a rufa mishi asiri."
Ruggumeshi tayi da k'arfi tare da sakin kuka kana cikin rauni tace.
"Aryan na yafewa Abeehnka duniya da k'iyama,
ni na yafe mishi kuma na sani shi ba mazinaci bane,
ka dena kuka ka cewa Abeehnka shima ya dena kuka,
insha Allah wannan sirrinmu ne,
babu wanda zaiji daga bakina koda uwar data haifeni bakina bazai furta mataba,
kaima karka gayawa kowa kaji my happiness."
cikin kukan ya kuma yi murmushi still hawaye na zuba tafin hannunta tasa ta goge mishi hawayenshi,
shima hannu yasa yana goge mata hawayenta kana yace.
"Abeeh kaji ko duk sun yafe maka na cika al'k'awari sauran kaima ka cika min naka al'k'awarin daka d'auka."
murmushi tayi tare da jawoshi tace.
"Zo mu konta kafin Uncle Jafar yazo ya kaika wurin Abeehnka ko?."
"To." yace tare da konciya a jikinta.

Bayan kamar 13 minutes bacci ya sace Zahra da taketa ajiyan zuciya,
shi kuwa Aryan mik'ewa yayi a hankali ya fita tsakiyar gida,
gefen barandar ya zauna shiru kasancewar ba kowa a tsakiyar gidan,
idonshi ya rumtse da k'arfi dan murd'an da yakeji a take kuma sai ya fara amai,
gurkusawa yayi a wurin yayi aman da yawa sannan cikin sanyi da rawan jiki yaje ya wonke bakinshi da k'afafunshi a pompo sannan ya nufi part d'in Aunty Amarya,
a parlour ya sameta tana zaune ita da Uncle Ibrahim yayan Zahra kenan wanda yake karatu a ABU Zaria yanzuma hutu yazo,
gefenshi yaje ya zauna domin Ibrahim na sonshi sosai,
cikin tsura mishi ido Aunty Amarya ta d'aura hannunta kan wuyanshi tare da cewa.
"Aryan baka da lfya ne?."
kai ya gyad'a mata kana ya kalli Ibrahim daya jawoshi jikinshi,
sai kuma yayi maza ya mik'e ya fita a guje a bakin barandar Aunty Amarya ta tsaya tare da yin wani irin yunk'urin.....!







By
*GARKUWAR FULANI*


[26/01 6:16 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 16*

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



A mai ya farayi mai tattare da yunk'uri mai k'arfi,
da sauri Ibrahim ya mik'e tare da biyo bayanshi,
yana zuwa inda yake yasa hannu ya tallabeshi ganin ya durk'ushe a k'asa,
itama Aunty Amarya biyo bayansu tayi jin yadda yaketa kakarin gefensu ta tsaya

Please Login or Register in order to submit comment