Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

game da Haddi na Mazinata yana cewa;

الزَّانِيَةُ وَالزَّانِي فَاجْلِدُوا كُلَّ وَاحِدٍ مِّنْهُمَا مِائَةَ جَلْدَةٍ وَلَا تَأْخُذْكُم بِهِمَا رَأْفَةٌ فِي دِينِ اللَّهِ إِن كُنتُمْ تُؤْمِنُونَ بِاللَّهِ وَالْيَوْمِ الْآخِرِ وَلْيَشْهَدْ عَذَابَهُمَا طَائِفَةٌ مِّنَ الْمُؤْمِنِينَ
Mazinaciya da Mazinaci, kuyiwa kowane d'aya daga cikin su bulala 100, kuma kada tausayin su ya kamaku cikin zantar da *Hukuncin Allah,* indai kun kasance kunyi i'mani da Allah da ranar Alqiyama. sa'annan kuma wasu jama'a daga cikin Muminai su halarci wajen da ake musu hukuncin.
gaba d'aya kotun mafi akasarin mutanen ciki hawaye suke zubdawa sabida tausayin uba da d'anshi domin Abba ya gaza tsada hawayenshi,
yayinda muryarshi keta rawa,
Safwan kuwa jin fad'in Allah kan cewa a samu halartan wasu mutane daga cikin muminai a inda za'a yanke haddin,
sai farin ciki mai tsanani ya rufeshi yanafa ganin yanzu dama tashi,
gashi ya nadi muryar Yusuf da hotonshi inda yake jaddada shi yayiwa Zahra fyad'e ga kuma damar da zai samu ta zuwa inda za'a tsustsulawa Yusuf bulalin Hukuncin Allah.

Shi kuwa Abba kanshi ya kuma sunkuyarwa tare da cewa.
"Kamar yadda kuma yazo a littafin "Muwad'd'a" na Imam Malik ibn Anasin Allah ya k'ara yarda da shi Juzu'i na 2, shafi na 734 yake cewa "Dangane da wanda yayiwa mace fyaɗe Budurwa ko wacce ba Budurwa ba,
idan 'ya ba baiwaba ce zai biya sadaki dai dai da na mace mai daraja irin tata. Idon kuma baiwa ce, zai biya kwatankwacin darajar abinda duk ya tab'a a jikin ta.
Sannan kuma akwai haddi ga shi wanda yayi fyaden amma babu haddi ga wacce yayiwa. Indai har wacce yayiwa fyaden ba baiwar shi bace ba."
gyara zama yayi tare da ci gaba da cewa.
"Wannan shine hukunci daya rataya kan Yusuf Muhammad Usman Girei,
sai kuma hukunci da court zatayi mishi a matsayin horaswa,
zaiyi zaman gidan kaso na shekara d'aya."
sit court d'in sai sautin masuyin kuka,
shi kuwa Abba
gilashin shi ya goge tare da medashi kan fuskarshi,
kanshi ya d'ago tare da zuwa mutanen cikin court d'in idanu na tsawon 25 seconds sannan ya gyara zama tare da gyara murya ya fara yin wata iriyar nasiha mai ratsa jiki da zuciya inda yake cewa.
"Jan hankali ga iyaye da malamai masu koyarwa! da manyan anguwanni,
wato Allah ya kawomu wani zamani mai hatsarin gaske,
lalacewa tayi yawa,
sabubban hallaka sun fantsama ko ina,
akwai bukatar sanya ido sosai akan yara,
musamman game da mu'amalar da take gudana atsakanin su.
Kamar yadda iyaye dole anisanta yara daga fina finai, musamman Masu koyar da alaqar jinsi,
soyayya da rungume rungume,
sumbanta juna, taba jikin juna da, wasa da jikin juna, furta kalamai masu motsa sha'awa,ajiye hotunan jinsi da video a wayoyi ,fyade ko kuma yin zina afili.

duka wa'innan babban kuskure ne barin yara sukai garesu.


munanan misali sunanan da yawa inda zaka sami zina tsakanin wa da qanwa, ko yaro ya sanya hannu awando dan uwansa ko yar uwansa ko akasin haka,
ko su dinga kwabewa juna wando, ko kaga suna sunbanta junansu, ko kuma furtawa juna kalaman soyayya ba tare da yaran sun kai wani mataki ba arayuwa,
ko kuma baiwa juna kyaututtukan na soyayya da wasiqu masu kashe zuciya. da dai sauransu
Wato ataqaice dai wayon yaran nan ya wuce tunanai mai tunani,
alokacin da muke musu kallon yarinta ai tuni su kuma sun riga sun wuce tunaninmu.
Saboda haka iyaye asanya ido kwarai akan yara, soyayya tsakanin ma'aurata ta halatta amma akula da irin wasannin da za'a yi agaban yara domin gudun koyar dasu abinda lokacin shi agaresu baiyi ba,
kamar yadda shara'a ta koyar damu raba tsakaninsu hatta akan shimfida da wurin wasanni,
kuma lalle akiyaye tarawa ko wasanni agaban yara, ko cikin daki guda dasu, domin kuwa wasu yaran ba bacci sukeyi ba lamau sukeyi ko likimo,
kunga komai agaban idanunsu yake faruwa kenan, kamar yadda dole akiyaye barin yara kanana cikin wa'inda sun d'arasu wayau da shekaru ,domin wannan ma nada nashi hatsarin ababin tarbiyyah."

Numfashi yaja tare da kauda kanshi gefe domin ji yakeyi baya son k'ara ganin fuskar Yusuf a rayuwarshi,
taron jamar kuwa duk an nitsu anajin nasiharshi da tunasarwarshi,
cikin sanyin sauti yaci gaba da cewa.
" Muna yawan fuskantar matsalolin rayuwane tun lokacin da *KUNYA !!!* tayi k'aranci a tsakaninmu,
mun mance cewa
kunya wata d'abi'a ce daga cikin dabi'un musulunci wanda ake kwadaitar da musulmi na gari ya siffantu da ita.
yayinda ba'a damu da MATSAYIN KUNYA A MUSULUNCI BA
an mance kunya a addinin musulunci d'abi'a ce dake sanya mutum aikata kyawawan ayyuka ababan so ga ma'abocin ta,
ta kuma hana shi aikata munanan ayyuka.

Manzon ALLAH ( ﷺ ) Yace.
"KUNYA wani rassa ko yanki ne daga cikin Imani.” [Sahihun Nasa'i 5020]

Manzon ALLAH ( ﷺ ) ya kuma cewa.
“Kunya bata zuwa da komai sai alkhairi."
a wani wajen kuma yace: "Kunya dukkanta alkhairi ce." Sahihaini.

Manzon ALLAH yace. "Lallai ALLAH mai yawan Kunyane kuma mai son suturtawa ne, yana son suturtawa da kunya.”. [Abu-dawud da Nasa'i
Manzon ALLAH yana kuma cewa.
"Yana daga abunda mutane suka riska daga cikin kalaman Annabawan farko, idan baka jin kunya to ka aikata abunda kaga dama." (Bukhari)
A wani wurin kuma Manzon ALLAH yace.
"Lallai kowanne addini yana da wani hali mai kyau, halin Musulunci shine kunya."
(Muwadda Malik da Sunan Ibn majah)
Ibn Sa'adiy (Rahimahullah) yana cewa.
"Da Kunya ake samun rayuwar imani, wato imani yana rayuwa ne idan akwai kunya acikinsa, da kunya ne bawa yake barin dukkan abunda zai janyo masa zubar da mutumci da matsayi, da kunya ne aka tabbatar da dukkan halaye masu kyau, domin kunya itace tushen dukkan hali mai kyau abun yabo, kuma ita ke korar da dukkan hali mummuna abun zargi."
(Attaudihu wal bayan: 95)
sai ya kuma yi shiru tare da kallon gefenda Yusuf yake cikin k'unci yace.
"Kaga yanzu kai sanadin babu kunya tare da kai,
ya zama rasa kimarka da martabarka ya kuma jazama zubewar mutuncinka."
jin haka yasa Yusuf rumtse idanunshi da k'arfi yayinda kunya me tsanani ta rufeshi
shi kuwa Abba ciga yayi da cewa.
"Ibn Uthaymeen (Rahimahullah) Yace:
"Kunya wani sifface ko dabi'ace da take sanya mutum ya aikata dukkan abunda zai sanya masa yabo da daukaka da mutunci da matsayi, kuma take hanasa aikata abunda zai zubar masa da matsayi da kima da daraja." (Sharh Riyadus-saliheen 4/42)
Nisawa yayi tare da ciga da cewa.
"Abu-Tamaam Yace:
"Wallahi babu wani alkhairi acikin rayuwa, har ma acikin duniyar baki daya idan kunya ya gushe! Idan har baka tsoron abunda zai je ya dawo, matukar baka da kunya, ka aikata duk abunda kaga dama.
Wani Magabaci yake cewa: “Duk Wanda kunyarsa tayi Karanci, Toh takatsantsan dinsa zai yi kadan.
Kunya na da matukar amfani da muhimman ci ga rayuwar dan adam mace ko namiji.
Hak'ik'a mata sune wadanda akafi siffantawa da d'abi'ar kunya. Sai dai abun takaici ayanzu suna nema su saki wannan d'abi'a ta kubuce musu a wannan rayuwa badan komai ba sai dan bin rudin duniya da mai halakarwa wato shaidan,
domin ayau mun wayi gari dayawa daga matayen cikinku da mazajen mu basa jin kunyar Ubangijinsu wajen aikata sabo kowanne iri ne amma abin takaici zaka samu yana tsoron mutane akan wani aibi nasa.
Hakika rashin kunya alamace ta raunin imani ga ma'abocinta.
Wani daga cikin magabata yana cewa:
"imani tsirara yake tufafin sa shine tsoron ALLAH adonsa kuwa shine kunya!"
Wani kuma yana cewa:
"Duk wanda ya mai da tufafin sawarsa ya zamo kunya to mutane baza su ga aibin sa ba."
Wannan magana tana nusar damu cewa kunya da imani tafiyarsu daya.
.IRE-IREN KUNYA: atakaice Kunya ta kasu kashi hudu:
JIN KUNYAR UBANGIJI: wannan nau'in kunyar shike hana bawa sabawa ubangijinsa,
aduk lokacin da bawa zai aikata mummunan aiki matukar akwai kunya atare dashi to lallai zaiyi gaggawar tuna cewa ALLAH yana ganinsa aduk inda yakasan ce kuma zai tambayeshi akan abunda ya aikata.
JIN KUNYAR MALA'IKU: ALLAH (SWT) Yana cewa: "Lallai akan ku akwai matsara masu daraja marubuta suna sanin abunda kuke aikatawa.
Ansamu daga sahabbai wani na cewa lallai atare daku akwai wadanda basa rabuwa daku saboda haka kuji kunyar su ku girmama su.
JIN KUNYAR MUTANE: Huzaifa bin yaman (R.A) yana cewa.
"Babu al'kairi ga wanda baiji kunyar mutane ba.
Ashe yan uwa kunya alkairi ce."
JIN KUNYAR KAI,
aduk lokacin da mutum zai aikata mummunan aiki dazarar yatuna Ubangijinsa kuma yaji kunyar kansa to lallai zuciyar sa zata nutsu kuma ta tsoraci ALLAH ta hana shi aikata mummuna tayi masa umarni da kyakkyawan aiki."

Kanshi ya sunkuyar tare dasa tafin hannunshi yana goge hawayenshi dake bin hab'arshi har zuwa kan gemunshi.

Mutanen wurin kuwa kowa zuciyarshi ta cika da kunya da tausayin dottijon
Yusuf kam yasan cewa dashi Abbanshi keyi,
yayinda Aryanma ya tsargu yakega kamar dashi Abba keyi,
Mama kuwa wani irin kallo take bin Yusuf dashi.

Shi kuwa Abba cikin zubda k'walla yaci gaba da mgna murya na rawa yace.
"Yanzu Allah ya kawomu wani zamani da fyad'e ya zama ruwan dere,
duk court in zaka lek'a sai ka samu case d'in fyad'e shi yafi yawa,
shiyasa dokar k'asa ta tsananta hukuncin masu laifin fyad'e."
kanshi ya d'an d'ago yayinda hawaye ke bin fuskarshi yace.
"Kada kuyi zaton yara kawai akewa fyad'e har hakan ya saku yin sakaci da kawunanku,
domin shi fyad'e ya kasu kashi iri daban-daban domin ko wanne da yadda yake riskar mutum,

*Shi dai Fyade* yana nufin aikata ko saduwa da mace ko namiji, ta amfani da hanyar karfi, ba tareda amincewar dayan bangare ba. Fyade yakan iya faruwa namiji ya yi wa mace, ko ita mace ta yi wa namiji, ko yanzu da zamani ya lalace, namiji ya yi wa namiji ko mace ta yi wa mace yar uwarta.
Ba shakka wannan mummunan aiki ne da ba addini ko al’ada da suka aminta da shi.



Fyade yanada nau’ukansa kamar haka da dama wad'anda suke haddasa matsalolin rayuwa.

*Fyade na kai tsaye*. Wanda galibi yakan faru ne tsakanin mutane da wata kila ba su san da juna ba, haka kawai namiji zai ji ya kwadaitu da mace ko ita ta ji haka, sai fyaden ya auku.


*Fyade tsakanin masoya*. Wannan nau’in yana faruwa ne tsakanin masoya da suka shaku da juna, wata kila ma sukan sadu a tsakaninsu, amma kasancewar yanayi na ita ta hana shi ko shi ya hana ta sai fyade ya auku tsakaninsu.


*Fyade na abota ko shakuwa*. Wannan yakan faru ne tsakanin mutane da suke a unguwa daya, wata kila kan yanayi na shigar mace har ya sa a ji ana so a mata fyade kasancewar ana wuri daya ana kallon motsinta,
shiyasa a kullum muke kira ga iyayen yara da su saka ido kan irin shigar da yaransu sukeyi.

*Fyade na taro*. Wanda aka fi sani da gang rape, shi wannan fyaden mutane da dama ne za su taru kan mace daya, ko wannensu ya yi amfani da ita, galibi irin wannan fyaden har rasa rai ake yi.



LAIFIN WA YE?

Kai tsaye ba za mu iya ayyana wasu al’umma muce laifinsu ne ba kan fyade da ke faruwa, amma ba shakka faruwar fyade a cikin jama’a akwai laifin.
IYAYE, sau da yawa bahaushe kan ce, sakacin daga gida yakan fara iyaye musamman mata, su tarbiyyar mata take a hannunsu, su ake tunani sun san shiga da fita na ‘ya’yansu mata, saboda galibi yanzu fyade ya fi aukuwa kan mata ne. amma sai ka ga uwa yarinyarta budurwa ta fita tun safe ba za ta neme ta ba har dare lokacin yarinyar za ta dawo, ina taje, oho! a ina ta ci abinci, oho! wasu ma sai ka ga ba a gida suke kwana ba. A bangaren kananan yara kuwa, sai ka ga uwa ta bar yara k'anana mata suna fita ba ko wando a jikinsu, a haka za su dinga gararanba kan titi da lunguna suna wasa cikin yara suna giftawa gaban miyagun unguwa, kafin uwa ta ankara ankai ta anbaro, sai ta dawo ta d'ora hannu a kai tana kurma ihu, bayan tun farko laifinta ne. laifin uba anan shi ne, an ji ya fita aiki ko neman abinci, idan ya dawo me yasa ba ya bincikar wanne hali yaran nasa suke ciki? ko ya dinga dan dawowa daga wurin aiki domin duba yanayin gidansa, gaskiya ni a wurina laifin iyaye ne ta 70%.


*Gwannati*.

Jin ya ambaci sunan Gwannati ne yasa gaba d'aya rabin yan jaridun sukayi gabanshi,
domin suma wannan damace ta isar da sak'on al'umma zuwaga Gwannatin jiha dama k'asa baki d'aya,
shi kuwa Abba cikin taune lips enshi alamun yana cikin tsananin bak'in ciki yaci gaba da cewa.
"An ce gwannati an kafa ta ne domin ta kare hakkin duk wani dan k'asa nata, idan haka ne kuwa yanada kyawu a tarar a kowacce unguwa akwai tsaro daga gwannati ta yadda fyade zai ragu a cikin al’umma, amma gaba d'aya gwannati hankalinta ya karkata kan jin dad'in kanta dan morewa rayuwar duniya, wanda ba karamar barazana ba ce a tsaro na kasa ma baki d'aya.


Suma kansu yaran da akeyiwa fyad'en.
da yawa za su yi mamaki idan nace da laifin yaran da ake yi wa fyade, idan muka duba yanzu zamani ya yi lalacewar da wasu d'inkunan da ake yi, gaba d'aya sai ka ga jikin mace ya bayyana kama daga k'irjinta har kafad'unta, wanda kai tsaye idan cikakken namiji ya kalla zai ji ya kwadaitu, hakan na janyo yawaitar fyade ainun. Wasu yaran sukan yaudari samari sosai, su kuwa samarin domin ramuwa kan yaudara da aka yi musu, sai ka ga sun yi wa yarinya fyade. Wasu matan kuma su da kansu ke kai kawunansu a dakin samari. Wasu matan kuma shaye-shaye suke yi wanda zai sa su fita hayyacinsu, sanadiyyar haka, sai ayi musu fyade.


DATTAWA DA MUTANEN UNGUWA.
Idan iyaye sun yi sakaci, gwannati ta kasa, bai dace mutanen unguwa suma su koma ‘yan kallo ba, ba shakka mutanen unguwa dole suna ganin abubuwa da ke wakana a unguwanni, tun daga fita da mata ke yi na banza da sauransu, da za su tsawatar,
da tuntini abun ya ragu,
amman dadin a tsawatarwa yaran mak'otan juna sai aka koma gulmar mak'otan kuma dan haka suma mutanen unguwanni sunada nasu laifi suma.

Daga cikin mafita akwai:

Addu’ah ita addu’ah takobin mumini ce kuma ba ta faduwa k'asa banza

Iyaye su dage susan cewa ‘ya’yansu hakki ne a kansu, kuma idan basu kula da tarbiyyarsu ba wallahi ubangiji zai tambaye su ranar gobe k'iyama


Gwannati ta dage wurin ganin ta saka tsaro domin dakile wannan mummunar akida, haka ta dage wurin ganin an hukunta duk wanda aka kama da wannan laifin, a kuma kafa kwamiti da zai dinga yawatawa yana fadakar da mutane illar fyade da bayar da misalai, misali yanzu da can baya jihar Adamawa an kafa kwamitin TABITAL PUUKAKU, inda kuma akaji dadin a lokacin ya zama duk k'ananun masarautu an basu umarni su kafata a shi'o'insu inda a wancan zamanin tayi tasiri sosai a wasu wurare misali kamar Mayo balwa,
Allah ya jik'an lamid'o Aliyu Mustapa da rahama daya assasa wannan tsari, to yana da kyau a sabunta wannan tsarin a kuma kafa kwamiti da zai dinga kulawa da wadanda tsautsayin fyade ya afka musu

Mutane su daina kyamatar wad'anda tsautsayin fyade ya farwa, domin hakan kan janyo matan su shiga uwa duniya.


Mutanen unguwa su kafa kwamiti da zai ba wa unguwanninsu tsaro, su dinga lura da masu shiga da fita a unguwanninsu.

Yara su ji tsoron Allah su dinga amfani da abinda ake karantar da su a islamiyya, su dinga shiga irin wacce musulunci ya tanadar.


A dinga yi wa mazaje auren wuri idan aka lura ba za su iya kame kawunansu ba.

Daga cikin illolin fyade.

Mafi akasari masu yin fyade za ka tarar suna yin masha'arsu a gefe, wasu ma sai a tarar suna dauke da munanann cututuka irin HIV Gonorrhea, Hepititis, sai kuga an rab'awa wad'anda aka yi wa fyaden, domin hakan ta sha faruwa

Ksancewar da karfi ne ake yi wa mace ko namiji, a yayin aikatawar wasu akan ji musu ciwo sosai, da wasu a
larurai dai inda har jini ya dinga fita musamman yara kanana.


*RIKITA MUTUM DA FITAR DA SHI A HAYYACINSA*
Kamar yadda Zahra ta fuskanta
wasu da ake yi wa fyade, sai ka ga har abin ya taba kwakwalwarsu, wasu ma sukan sami tabin hankali da shiga tsoro mai tsanani.


*ZUBAR MUTUNCIN SHI WANDA YA AIKATA FYADEN*
Kamar yadda Yusuf ke ciki a yanzu,
duk wanda aka ce ya taba yin fyade, za ku ga mutuncinsa ya ragu a idanun mutane zai zamo abin gudu kuma abin kyama, wanda har zuri’arsa ba za su tsallake abin fada ba kan fyaden.
SHAFAWA WANDA TSAUTSAYIN YA FAR WA TABO wasu suna rike mata da yawa da wannan tsautsayin ya far wa, bacin ba laifinsu ba ne, amma a haka wasu har ba’a ake musu, wasu kuma ana musu dariya da nuna musu kyama wasuma sai a rasa mai aurensu. Wanda sam hakan bai dace ba."
Cikin zubda hawaye murya na rawa yayinda wani kukan k'unci ya kubcewa Abba cikin rawan murya yaci gaba da cewa.
"Ta hanyar fyade ake samu ciki ya shiga har a haihu, wanda ta sanadiyyar haka yaro ya tashi cikin zuriah ga shi ba wanda ya san mahaifinsa bare asalinshi.

Ga jawo mace-macen aure Wasu mazajen da dama idan aka yi wa matansu fyade, sai ka ga sun rabu da su.


*HANA AURE*. Wasu kan wannan tsautsayi ya far musu sai ka ga kowa na gudun ya aure su, wasu ma daga karshe dole sa'an kakansu ne za su aura, shima kuma sai mai k'arfin imagine zai yadda ya auri wacce akawa fyad'e."

Sunkuyar da kanshi yayi ya saki wani sassayan kuka mai cike da k'unar zuciya,
kukan Abba yasa mafi akasarin mutane kuka,
jin Court d'in ya rud'e yasa Abba tsagaitawa tare dayin gyaran murya yace.
"Gobe da hantsi anason Yusuf yazo nan inda za'ayi mishi Hukuncin da Allah ya umurcemu da muyiwa mai laifi irin ya nasa,
ana kuma buk'atar taron mumanai a wurin,
sannan kotu ta wonki Idi daga zargin da akayi mishi."
yana fad'in haka ya mik'e tare da juyawa ya fita ta k'aramar k'ogar daya shigo,
yana tafiya yana zubda k'ollah.

Daga nan mutane sukayi ta fita,
yayinda yan jaridu sukayi caa kan M Jabeer da yakejin bak'in ciki kamar ya mutu,
tun kafin ya fito cikin Court d'in Safwan yayi saurin tareshi tare da cewa.
"Jama'a zasu so su san matsayin Hukuncin da Team Jahan zata d'auka kan laifin da abin kunyar da babban d'an team d'in ya aikata."
Affan ne yayi sauri ya mik'e yaje gaban Safwan cikin kuka yace.
"Akwai wani Hukunci ne bayan Hukuncin Allah?."
kai Safwan ya jujjuya tare da yin murmushin mugunta yace.
"Kaima zanzo gareka inji matsayin laifin wanda kake karewa in kuma jajanta muku rashin nasarar da kukeyi."
yana fad'in haka ya juya tare da bin bayan malam Jabeer cikin d'aga sauti yace.
"Ko dai laifin da d'an team Japan yayi ba laifi bane,
ba hukuncin da za'a d'auka a kanshi,
sannan an bawa duk sauran yan team d'in suci karensu babu babbaka, tunda uban gidansu baya ganin laifinsu?."
cikin tsananin takaici da bak'in ciki M Jabeer ya fuskanci camera da Safwan ya saita fuskarshi dashi,
cikin kaushin murya yace.
"Yusuf Muhammad Usman Girei ba d'an team Jahan bane a yanzu,
team bata tare dashi,
duk laifi da abin kunyar da yayi babu ruwan team Jahan ko mahukuntanmu, an koreshi daga team Jahan, in kuma hanashi damar shiga ko wannne team in d'ai a fad'in k'asarnan team d'in take, kuma bashi da damar kafa tasa team d'in,
domin in an bashi dama ya tara yaran mutane bazai koya musu d'abi'ar k'waraiba,
kuma daga yau ba shine barad'en Adamawa ba!."
yana fad'in haka ya fice a fusashe idanun nan nashi sunyi jazir,
Affan kuwa zamewa yayi kan kujera ya zauna yasa hannu bibbiyu yana dukan kanshi yana kuka tare da cewa.
"Ga abinda nan nake gudu ya kasance Hamma Jabeer ya zakayi min haka, wlh ka raunata team d'inka."
Aryan kuwa ido ya zubawa Mama wacce ta mik'e ta nufi inda Yusuf ke d'urkushe yana wani irin kuka mai cike da toskun rayuwa ganin yadda Abbanshi ke kuka a kanshi shi yafi komai d'aga mishi hankali,
Raihana kuwa fizge hannunta tayi daga rik'onda Faisal ya mata gaban Aryan d'in taje ta tsaya tare dasa hannunta duka biyu tana d'an dukan k'irjinshi tare da sakin kuka tana cewa.
"Shi kenan ko Ya Aryan burinka ya cika ka zubda mutuncin Hamma Yusuf kasa an koreshi a masana'antarshi kasa an tozartashi maza sai ka zubda ruwa a k'asa ka shanye."
sai ta kuma zame gabanshi ta d'urk'ushe tana kuka,
hakama Kaka tazo tana d'agata tana kuka,
Adda Zulaihat kuwa fad'awa tayi jikin mijinta ta saki kuka mai cin rai,
shima Abubakar kuka yakeyi domin yasan duk abinda ya faru k'aninshi Garzali shine sila, ganin Zulaihat d'in ta birkice mishi yasashi janta suka fita,
Zahra kuwa kanta ta kife kan bencin gabanta tana wani irin kuka,
Mama kuwa tana zuwa inda Yusuf yake tsaye ta d'aga hannunta duka biyu ta rink'a kikkifa mishi maruka tanayi tana kuka tare da cewa.
"Ka cuceni ka tozartani ka ha'inceni ka watsar da tarbiyar da nayi maka,
Yusuf kaci amanar Daddynku ,
Yusuf tsakanina da kai Allah ya shir.......!


By
*GARKUWAR FULANI*



Jwddbl













Cikin tsananin firgici da tsoro Yusuf ya d'ago kanshi tare da zazzaro jajayen ida nunshi da sukayi tamkar garwashi ya rink'a jujjuya kanshi tare dasa hannunshi duka biyu yana toshe kunnuwanshi cikin tsananin tashin hankali murya na rawa hawayenshi suka tsananta kwaranya a idanunshi baki ya bud'e da kyar ya fara mgna.
"Maman Yusuf na tuba ki gafarceni kada ki jamin Allah ya isa,
in kinyi fushi dani ina zansa raina? ya rayuwata zata kasance? kinga ko abinda ya faru dani a yanzu,
ni na tabbatar fushin da Abba keyi danine sanadi,
shiyasa Allah ya jarabceni da jarrabawa mafi muni da zafi ki gafarceni kimin rai ki dena zubda hawayenki a kaina."
cikin jan guiwowinshi ya kuma fara matsowa gareta
tafin hannunta ta ware da iya k'arfinta ta yarfa mishi mari tare da nunashi da yar yatsarta manuniya cikin muryar kuka tace.
"Karka sake kirana Maman Yusuf! daga yau bani ba kai! kaje can ka nemo wata uwar banda ni,
dan ni banyiwa d'ana irin wannan tarbiyar ta lalata 'ya'yan mutane ba,
ni Yusuf d'ina tsarkakkene salihin bawan Allah ne, mai tausayi ne! mai rik'on amana ne! Yusuf d'ina ba fasik'i bane,
shi bama zinaci bane,
kada ka sake ko a mafarki kace ni uwarka ce,
ni Yusuf d'ina ya rigada ya mutu baya duniya."
tana fad'in haka ta juya tana zubda hawaye,
hannun Zahra ta kamo wacce itama kukan takeyi har numfashinta na fizga,
suna fita motar Jafar suka shiga,
ganin yadda Zahra ke tsananin kuka yasa Mama jawota da nufin ta rarrasheta amman abin yaci tura kawai sai suka ruggume juna suna kuka,
yayinda kowa da abinda yakewa kuka,
a cikin kuwa,
Daddy yak'i ya dakatar da Mamana da abinda takeyi domin in ya barta ta amayar da abinda ke zuciyarta wala Allah ta d'anji sanyi,
shiyasa saida ta fita, shi kuma
Daddyn ya mik'e cikin tsananin k'unci yana zuwa inda suke ya sunkuyo tare dasa hannu ya d'ago Yusuf dake kuka yana bubbuga kanshi a jikinshi katakon wurin,
ruggumeshi yayi tare da kontar da kanshi a kafad'arshi bayanshi ya rink'a d'an bubbugawa cikin kukan shima ya fara mgna.
"Dukkan tsanani yana tare da sauk'i,
muminai salihan bayi su Allah ke jarabta domin ya gwada k'arfin imaninsu,
komai yayi zafi mgninshi Allah,
Allah yasani ba kaine kayiwa Zahra fyad'eba nima na tabbatar ba kai bane,
kada ka damu,
Mamanka bata cikin hayyacinta,
domin na sani ko duk duniya zasuyi fushi da kai to tabbas Maman Yusuf bazatayi fushi da Yusuf d'intaba,
tsananin bak'in cikine ya sata fad'in wad'annan kalaman dani da ita da Abbanka da duk wanda ya sanka yasan kai ba fasik'i bane kai bamazinaci bane,
kayi ta addua a madadin kuka in sha Allah burin Aryan bazai cikaba bazaka tozartaba in sha Allah darajarka zata d'agu fiye da- dacan baya."
wani irin kuka Yusuf ya saki domin jin tausayin kanshi da kanshi ya rufeshi,
Aryan kuwa shima zamewa yayi a wurin yanayin wani irin fitinennen kuka mai cike da k'unci da k'una a zuciya,
Jafar ma kukan yakeyi yayinda yaje ya ruggumi Yusuf ta baya,
Affan kuwa tuni yasa fadawanshi sun kora Safwan woje,
sai lokacin yaga Matawalle a bakin

Please Login or Register in order to submit comment