Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zatona ne a kanku Allah ya bamu ikon rik'e amanar juna*




*Cikin* razana da tsoro Zahra ta saki ihu da kururuwa, sanadin wani irin fizgota da Yusuf yayi, wanda ya shigo shagon a 1000,
gefe ya tureta tare da nufan Idi, wanda tsoro da razani ya rufeshi, dan kofar da Yusuf ya buga da karfi gaba d'aya jikin idi rawa yakeyi, danshi a zatonsa, tsawan aradu ne ya sauk'o kanshi,
ido ya zaro gami dasa hannunsa duka biyu ya rik'e jelarsa , gaba d'aya tsuma yakeyi zufa na tsatstsafo mai tako ina, k'ara matse abar tasa yayi dan ganin Yusuf yake kamar zakin daya fito farauta, gani yake sam bai siraba Yusuf zai tsinke mai mazakuntan nasa.
Shi kuwa Yusuf cikin fushi da tsananin tafasar zuciya gaba d'aya jikinshi b'ari yakeyi, kamar zaki ya nufi idi,
yayinda shiko idi ya kware baki iya k'arfinsa ya rink'a zurma ihu da kwarara kururuwa,
wuyanshi Yusuf ya damk'o tare da wujujjugashi ya mannashi da jikin gini, ya rink'a gwara kanshi, yayinda yasa guiwarsa yana dandatsa mazakuntan idin da jikin ginin, shak'eshi yayi da iya k'arfinshi, har sai da yaga ida nunshi sunyi zuru-zuru yana kakarin mutuwa,
sannan ya jawoshi tare da tik'ashi da k'asa ya rink'a tattakashi yana bol dashing, ya gorishi tanan ya gorashi ta can, d'agoshi ya kumayi ya hankad'ashi baya ya bugashi jikin kantar har yana rikito da kayan daya jera su alewa da biscuit a ciki ganin Yusuf, ya tsaya yana nannad'e hannun rigarshi alamar zai mishi bugun k'aton gardi, ai da sauri yaja wandon shi yana niyar mayarwa yana shirin zura k'afarsa,
yaji Yusuf cikin ihu da gurnani tamkar namijin zaki ya danko kwalar rigar shi ya buga da bango nan yahau jibgar shi tamkar an aiko shi Idi kuwa dama babu karfi sai tantagayyar iskanci, ihun yake tana.
"Wayyo!! jama'a taimako zai kasheni wayyo lilina ya tsinke ya kama da wuta, ku firfito kuzo ku ceci rai mana".
ihun da yake zurmawa da kururuwar, ganin haka yasa Zahra zurmawa da gudu ta fice a shagon tayi gida.




Yusuf kuwa ya ware iya karfin da Allah ya hore masa sai jibgar Idi yake dan idonshi ya rufe hankalinshi ya bar jikinshi,
jibgarsa kawai yakeyi tuni ya dad'e da hada mishi jini da majina.
A hankali dattijan da suke zaune cikin masallacin dake kofar gidansu Zahra, suka fara jiyo ihu da kururuwar jikin yanayin azabebbiyar wahala, da sauri suka fito nan sukayo hanyar shagon Idi jin ihun daga nan yake fitowa, ganin Yusuf ke dannak'ar Idi tamkar Allah ya aiko shi duk yaji masa rauni ga wandon shi sai kokarin sabulowa yake nan sukayi tunanin wani abune ya afku dan dama sun dade suna zargin Idi haka kuma sun tsane shi saboda kid'an da yake cika musu a layi gashi bayajin maganar kowa baya girmama kowa.
Dakyar suka kwaci Idi a hannun Yusuf ai Idi na ganin haka ya fice daga shagon da gudu wando a hannu zigidir haihuwar uwarsa,
cikin tafasar zuciya Yusuf ya naushi gini idanun sa sunyi jajazur kuka ya saki mai cin rai tare da yin bakin k'ofar fuuuu shima ya fice daga shagon yayi gida daga bakin gate yake kwazawa Zahra kira.



A zafafe ya tura kofar part din Aunty Amarya ita kanta Aunty Amarya saida ta zabura jin irin bugowar da Yusuf yayi,
kai tsaye gurin da Zarah take ya nufa ya kwashe ta da wani gigitaccen,
mari ihu ta cillara tamkar ana cire mata rai da sauri Aunty Amarya ta tashi taje ta rike hannunsa, yau daya data nuna bacin ranta akan dukan da Yusuf yayiwa Zarah wata uwar harara ya banka mata da jajayen idanuwan shi sakin hannun shi tayi,
shi kuwa da hanzari ya fice daga part dinta gaba daya ma ficewa yayi daga gidan yabar unguwar.




Aunty Amarya kuwa Zarah ta d'aga daga kwanciyar da tayi sakamakon marin da Yusuf yayi mata Mama da Ummi ne suka shigo suke tambayar meya faru murmushi ta kakalo kana tace.
"Ita da Yusuf ne ya mareta" Mama ce taje ta zauna kusa da Aunty Amarya ta dauki Zarah ta daura akan cinya saboda har zuwa lokacin sai hadiyar zuciya takeyi, a sannu ta fara shafa mata baya a take baccin wahala ya kwashe ta.



Abba ne ya fita k'ofar gida wajen 12:00pm yaji ana labarin dukan da Yusuf yayiwa Idi da mamaki yake tambaya.
"wanne Yusuf din". wani dattijo d'aya daga cikin wadanda suka kwaci Idi yace "Yusuf naka". kan Abba ne ya daure a take ya ciro wayar shi ya kira number din Yusuf lokacin yana kwance akan 3 sweater a parlourn gidansu Aryan,
Aryan sai tsinewa Idi yake yana dama yana gurin su dandak'e d'an iska yaji wayarshi na ringing d'aukota yayi ganin Abba ke kiranshi ya mike ya d'aga ko gaisuwar da yakewa Abba bai amsa ba cikin fushi yace.
"Kana ina!?"
"ina Jimeta ne gidansu Aryan."
a hatsale yace.
"To kayi maza kazo ina jiranka".
diff ya kashe wayar kallon-kallo sukayi da Aryan tashi yayi Aryan ma ya tashi yana cewa.
"Muje tare", nan suka fita a machine din Aryan,
dan sai 4:00pm zasu fara gasar tseren dokin.



Abba ko borkono sarkin zafi da fad'a ya shiga yana. "Kawai yaro ka kama mutum baiyi maka komai ba kayita duka".
Mama ce ta tareshi tana.
" Wa aka daka kaida wa?" cikin fushi kamar zai kai mata duka yace.
"Waye kuwa banda Yusuf ya kama yaron nan da duka duk ya farfasa masa jiki".
cikin salon miji na mgna mace na tanka mishi Mama tace.
"Yusuf kuma anya kuwa waya daka?".
zabura Abba yayi kamar zaikai mata duka yace.
"Nayi miki karya to, sharri nayiwa d'anki, gwara ki musa min ai, to Idi ya daka".
shiru Mama tayi dan ganin yadda ya dauki dumin nan sai su raba hali ana haka sai gasu Yusuf da Aryan sun shigo, cikin fada Abba yace. "Uban me Idi yayi maka kayi mishi duka harda fitar mishi da jini?".
shiru yayi ya sunkuyar da kai nan fa Abba yahau banbamin fada "Watako ka girma ka rika zaka zama tantiri har ka fara zuwa shagon mutane kana dukansu da fidda musu jini tom bari kaji yanzu-yanzu kaje ka nemi Idi ka bashi hakuri."
a dimauce Yusuf ya mike cikin kunar rai ya rink'a juya kai alamar Abba yayi hak'uri yace.
"Hakuri Abba kasan me yayi ne, Wlh Abba ji nake a raina idona idon idi sai nayi ajalinsa".
ya k'arishe maganar yana komawa bayan Daddy daya fito yanzu,
fuuuu Abba yyi kanshi tare da cewa.
"A gabana kake inkarin zakayi kisan kai to da sauranka, inma d'an daba kake son dawowa".
da sauri Daddy ya tareshi tare da jawo hannun Yusuf da Aryan suka haura sama.

da kallo Abba da Mama suka bishi tabbas akwai wani babban Al'amari daya faru dasu basusan dashi ba dan Yusuf Mahak'urcine ba'a tab'a jin yayi fad'a da kowa ba, Mama ce cikin fushi tace.
"To kaima haka akeyi daga shigowar yaro babin ba'asi ka haushi da fada".
nanfa Abba ya ware ya zabzabga mata mari ya fanshe fushinsa a kanta kuka ta hauyi sai da tayi mai isarta sannan tayi shiru.



Zarah kuwa bayan ta tashi har shatin hannun Yusuf ya fito a fuskarta wanka Aunty Amarya tayi mata ta bata abinci taci sai da ta tabbatar ta koshi da wayo da dabara ta tambayeta me tayi a shagon Idi yaro babu ruwanshi nan ta fada mata. "Anty Idi ya fito da abinshi a wando ya saka min a, yasa hanunnushi cikin wondo na, cine Hamma Yucut a kasheshi , ya bani a baki a Hamma Yushuf yaje bum-bum ya daki Idi". cikin tsoro da firgici Aunty Amarya taja hannunta sai part din Mama tana kuka nanta fad'a mata abinda Zarah ta fad'a mata itama sosai ta shiga tashin hankali duba Zarah sukayi sosai ganin babu abinda ya sameta shine ya saka musu nutsuwa suka hau tsinewa Idi da yiwa Allah godiya.



Allah sarki Mama haka ta shiga dakin Abba ta labarta masa abinda ya faru, shiru cikin tsoron lamuran duniyar, oh d'an adam abin tsoro, sai kuma ya janyota jikinsa ya fara lallashinta daban hakuri.


Daddy kuwa cikin nitsuwa yasa Yusuf ya mishi bayanin dalilin dukan da yayiwa idi,
cikin kid'ima da firgici Daddy ya mik'e da tsananin fushi da firgici ya taso Yusuf da Aryan a gaba, kai tsaye gidan da Idi yake haya yaje ya gayawa mai gidan a take aka koresa a unguwar gaba d'aya, sannan aka tattara mai komatsanshi aka korashi dan dama d'an cin ranine.


Alhamdulillah yanzu hankalin Yusuf ya konta tunda ya kauda idi a unguwar,
sai dai abinda bai saniba, mai gadin gidan mak'ocinsu yafi idi Illa, kuma tuni yaja hankalin yaran unquwar duka da kyaututtukan da yake basu,

A hanyarsu ta dawowa gida ne Yusuf ya kalli Daddy cikin sanyi yace.
"Daddy sauk'emu a kofar gidan Anty Zulaihat mana zamu gaidata. "
to yace dai-dai lokacin da suka tsaya sannan ya zaro 5k ya basu yace.
"gashi Ku kai mata kuce ina gaidata ta kuma ci gaba da hak'uri ko."
"To " suka amsa tare da kutsa kai cikin gidan, suna shiga tsakiyar gidan,
cikin tsananin firgitada gudu suka kutsa cikin...!





*By*
*GARKUWAR FULANI*
[02/01 1:06 PM] My 2nd Mtn: πŸ“πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 9⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*





πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡


*GA masu buk'atar sayan littafin Hukincin Allah zasu biya d'ari biyu kacal, turo katin MTN na 200 ta wannan layin 09097853276 ko kuma ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar ka/kin turo shaidar ka/kin biya kafin in saki a group*



*Free page*


*😭😭😭😭😭😭ABOKIN K'ANINA NE, Sunanshi muhammad Seyo MAHAIFINSU BASHI DA LFY BABBAN YAYANSU YA KASANCE D'AN SHAYE-SHAYE K'ANWARSA MAI BINSHI TAYI AURE MIJINTA YA RASU YA BARTA DA YARA BIYU TA KOMA DASU GIDANSU TANA DA K'ANNE KUSAN 8 BASU DA GATAN KOWA A DUNIYA SAI ABOKIN K'ANIN Nan NAWA MUHAMMAD WANDA AKE KIRANSHI DA *SEYO* *YARO K'ARAMI ALLAH YA D'ORA MISHI NAUYIN RIK'E ZURIYARSHI SHINE KOMAI NASU NA DUNIYA, KWANANNAN NAJE NA DUBO MAHAIFIN NASU NASAMU KO MIK'EWA TSAYE BAYA IYA YI.CIKIN IKO NA ALLAH DA K'UDURARSA SAI GASHI SEYO YAYI HATSARI YA FAD'I YA MUTU YA BAR DUNIYA😭😭😭😭😭😭😭Wayyo Allah Ayyah Su Sadiya sun zama basu da bongo abin jingina a duniya basu da wani mai kula da rayuwarsu. k'arshen had'uwata da Seyo bai kai sati biyu ba, ina tuna yadda yake yafitoni da hannu yana min mgn da ido cikin salon wasa dan shima ya zama tamkar Adamu k'anina, me zanyiwa Seyo, dan Allah Dan Allah dan Allah masoyana ina barar k'ulhu k'afa uku-uku ga wannan bawan Allah Seyo, Allah ya jik'anshi da rahama yasa ya huta, Ya Allah ka bawa yan uwanshi hak'uri da dangana ya rabbi kaine gatansu Sadiya*






Tun daren jiya sanater ya karaso gidansa, kamar yadda ya saba, da yake shigowar dare yayi, shiyasa ba kowa yasan yazo ba, sai abokanan shed'anan cinsa.



11:15 Am. Yusuf da Aryan ne suka fito daga gidansu Yusuf d'in, suna hira ta kofar gidan senator sukazo zasu wucewa Baba me gadi dake zaune yanajin radio suka yiwa sallama har zasu wuce sai yace.
"Y'an samari kuzo mana!". cikin girmamawa suka dawo dan sosai Yusuf yake ganin mutuncin tsohon, baisan biri bane da fatar kura.



Shi kuwa tsohon najadu Baban mai gadin, saida yadan jujjuya kanshi gabas da yamma yaga alamun babu wani da yazo wucewa cikin yin k'asa-k'asa da murya yace.
"Yan samari mezai hana na hadaku da uban gidana ya taimakeku?".
cikin mamaki Yusuf da Aryan suka hada ido tare da kuma maida dubansu gareshi, cikin rashin fahimtar maganar Yusuf yace.
"Baba meyasa kace haka? ko kaga kamar munyi maka Kama da masu buk'ata neman wani taimako ne?". cikin dariya kasa-kasa Baba tsoho yace.
"Ina yaro ai ganinku a koshe alamun kudin lafiyayyu ne ya sakani fadar haka ganinku zakuyi farashi sosai a gun maigida na,
zakuji dad'in harka dashi zai biya muku dukkan but'atunku na rayuwa".
maganar shi kara daure musu kai yayi Aryan ma kasa magana yayi, sai Yusuf ne yiyi magana cikin alamun k'osawa yace.
"uhm hmmm muna jinka". kara kallon hagu da damarsa Baba tsoho yayi sannan yayi kasa da murya yace.
"Yan samari ko bakwa burin ku fantama irin yadda samarin wannan zamanin sukeyi ne kuga yaro karami da zungureriyar mota".
cikin jin haushin batun tsohon da sai kwane-kwane yake musu yaki magana d'aya a hatsale Yusuf yace.
"Aryan mu tafi inaga bai shirya fad'a mana abinda zai fada ba yake bata mana lokaci".
da sauri Baba mai gadi yace. "Haba-haba 'yan samari banso fad'a mukuba kuma na tsaidaku".
shikuwa Baba dagewar da yayi saboda yasan inhar ya hada uban gidansa da samarin nan ba karamar kyauta zaiyi masa ba.
"Kuna jina ko zan had'aku da uban gidana, had'in kai kawai zaku bashi ina mai tabbatar muku kuda talauci kunyi hannun riga".
wata uwar harara Yusuf ya bankawa Baba mai gadi cikin zafin zuciya jikin shi har rawa yake yace.
"Wallahi kaci darajar furfurar ka duk da baka girmama furfurar taka ba da babu abinda zai hanani na faffalla maka mari na hada maka jini da majina dattijon banza dattijon hofi, tsohon najadu kawai".
saboda yadda Yusuf ke daga murya har mutane sun fara taruwa Baba tsoho kuwa yayi tsilli-tsilli da ido da kyar Aryan yaja hannun Yusuf suka tafi da yaketa kumfar baki tamkar zai kaiwa dattijon duka.



Tun daga ranar Yusuf ya gargadi kannensa akan kota ta kofar gidanma yaga yaro ya wuce saiya babballasa, ya tsoritasu da kalmar tsohon najadu ne shi, aiko daga nan Zahra ta samu kalma harda rerewa tsohon wak'a, kunsan dama Zahra uwar rawa da wak'ace.



Tun daga ranar da abinnan ya faru Baba mai gadi ya daina zaman k'ofar gida dan yana tsoron wataran Yusuf yazo wucewa ba kowa yayi masa dukan tsiya dan ya lura yaron dan tijara ne,
ga Zahra dake zuwa har bakin gate d'in ta rink'a mishi wak'a.

Yauma kamar kullum in Zahra ta samu damar fitowa gida sai tayi gun mai gadin,
a guje ta fito dan tsifar da akeyi mata take gujewa, har zata tsallaka titin da nufinta zata gudu gidan Bappa jangirde malamin makarantar allon da take zuwa da can baya,
da sauri kuma ta kayo ganin yau Mai gadin gidan senater d'in ya fidda yar kujerarsa ta wojen gidan yana zaune, da tarin biskin, sweet, a gefenshi wanda dashi yake jan yara zuwa gareshi, sai kuma ruwan kud'i da yakewa yan k'ananan matasan unkuwar,, kamar daga sama ya jiyo muryar Zahra na cewa. "Tiri Baba tiri aralle, masifa sai an koma gidan baba mai gadi, bala'i sai a d'akin Baba mai gadi, Baba Mai gadi yasa han hanamu wasa a waje, Baba soho mai farin gemu ba fari bane ko alline ubansan zanci".
kai ya juya tare da watso mata sweet , cikin tijara da rashin kunya tasa hannun ta tsinci sweets d'in,
cikin son jan ra'ayin yarinyar yace.
"Zahra yan mata ki rink'a zuwa d'akina zan rink'a baki minti."
kafad'a ta mak'e tare da cewa.
"Bazan zoba Hamma Yusuf yace kai tsohon Najadu ne". tana fad'in haka ta juya ta tafi tana shan sweet d'in tare da cewa.
"Gobema zanzo in karb'a".
har ya bud'i baki zai kira wota sai kuma yayi shiru sabida hango,
yarinyar da take kawowa mishi tallan zogale ce ta iso wurin, saida ta duba gabas da yamma kudu da arewa bataga kowa ba sai tayi wuf ta fada gidan, Baba mai gadi ne ya washe jajayen hakwaran sa yace.
"Inno kece a tafe".
saida tayi fari da idanuwanta tace.
"iyi nice kaga muyi maza-maza kayi ka gama ka bani kudina na tafi kaga innar mu harta fara ganewa, tace ina nake kai zogale ina fita bana dadewa na dawo mata da kudin nace na siyar".
bakin shi ya kara washewa hadi da mikewa yana kunce tazugen wando,
dama Inno tuni ta dade da shigewa dakin nanya mara mata baya anan suka fara shed'ancin su.



Dan dazon yara ne da suke buga kwallo a bakin titin, suna bugawa ball d'in ya fad'o gidan kai tsaye suka shiga dauko ball din tasu da yake baba mai gadi har mangwaro yake tsinkowa ya raba musu, dan haka kai tsaye dakin shi suka tafi suna "Baba Ball dinmu ta fad'o munxo dauka".
ganin Baba turmi da tab'arya shida Inno ai sai suka saka ihu Baba mai gadi kuwa zabura yayi ya daga Inno yana kokarin maida tazugen shi.



Yara kuwa yadda suka fita da ihu shiya janyo hankalin samarin dake zaune akan wani dandamali tambayar su sukayi meya faru nan sukace Baba mai gadi suka gani yana yiwa wata yarinya wani abu ai a 100 suka shiga gidan Baba mai gadi da fitowarshi kenan daga dakin shi jikin shi sai rawa yake ganin gungun samari sun shigo a guje yayi ainahin cikin gidan senator wasu samarinne suka mara mishi baya wasu kuma sukayi cikin dakin shi wadanda suka shiga dakin nashi Inno suka gani a rakube jikinta sai rawa yake wasu ne suka fara dukanta inda wasu sukace su kyaleta aje a kamo Baba mai gadi a hadasu a mikawa hukuma.




Tofa akace ana wata ga wata wani babban tashin hankalin lokacin da Baba mai gadi yayi cikin gidan samarinnan suka mara mishi baya ai sai sukayi turus tarar da senator da wani matashin saurayi suna aikata masha'a a parlour tsirara haihuwar uwarsu (wa'iyazu billah) ai nan samarinnan sukayi kansu da duka baji ba gani ai jin duka shiya dawo da senator da saurayinnan daga duniyar shed'ancin da suka lula ihu suka fara da kokarin kwace kansu da gudu saurayin da senator sukayi daki suka saka sakata inda samarin suka mara musu baya sai dukan k'ofar suke suna saisun ballah, baba mai gadi ganin haka ya sulale da niyyar guduwa yana fita samarin dake waje suka cafke shi suka turashi dakinsa suka hada da inno suka kulle.



Senator na shiga daki yayi hanzarin daukar wayarshi ya kira commissioner of police yace ya turo mishi yan sanda matasa sun shigo har gidansa sun tayar mishi da hatsaniya.



Matasan nanne na cikin gidan suka fito suka bawa na waje labari nanfa wasu sukace kawai a kona gidan wasu sukace su kira hukuma cikin tsananin zafin rai da bak'in ciki Yusuf yace.
"Haba kamar bakusan hukuncin Nigeria ba ai yanxu ana kiran yan sanda ayau za'a sakesu ba zasu kai gobe ba kawai mu kona gidan komai zai faru sai dai ya faru, mu dai munsan mun rege mugun iri!".
da wannan shawarar suka fita wasu suka tsaya jira wasu suka tafi siyo fetir.



Dawowar samarin yayi dai-dai da isowar yan sanda ganin abinda samarin suke shirin yi da hanzari yan sandan suka tare gidan suka koro na ciki ganin da gaske samarin keson kona gidan senator sai suka sakar musu tiyagas har kofar part din senator yan sanda suka kai mota senator da saurayin nan suka fito suka shiga motar yan sanda suka hada da Baba mai gadi da yarinyar suka fita dasu ganin haka samarin da duk da tiyagas din da ake buga musu baisa sun gudu ba suka marawa motar baya da tofin Allah tsine.



Koda Yusuf ya dawo gida ji yake kamar ya mutu dan takaici da ba'a hadu an k'ona gidan ba an rage mugun iri, partrool aka saka a unguwar su Yusuf na kwana 3 babu shiga babu fita zuwa tsakankaninnan senator ya gama tattara inashi-inashi yabar garin. (Ya ubangiji dan girmanka dan zatinka ka kawo mana dauki da sauki a cikin al'ummar mu da kasar mu Nigeria me kudi zai iya komai ya kwana lfy ya taka wanda yaga dama ya cuci wanda yaga dama amma ba za'a iya kwatarwa wanda aka zalunta ba saboda ana ganin wannan mutumin mai fada ajine a gari Allah ya kyauta).



Tun faruwar abinnan senator bai k'ara dawowa gidanshi ba saboda tabbas yasan duk randa yazo sai dai uwarshi ta haifi wani dan labarin ya gama karade ADAMAWA gaba daya.

***********


A sannu tafiyar su Yusuf ke gabatowa dan baifi saura wata 1 ba inda harsun kammala Neco dinsu inda dama tuni sun zana jamb.


Bayan an idar da sallan asuba Abba, Daddy, Sulaiman, Yusuf, Ibrahim, Sadik, suka shigo gida kai tsaya suka nufi parlour Hajja Inna dan ak'adar su Abba kenan, suna dawowa sallan asuba sai sun shiga sun duba lfyar mahaifiyarsu,
zaune suka sameta bisa sallaya, cikin tsananin so da kulawa Abba ya zauna gabanta tare da karb'ar maganin dake hannunta tare da fara shafa mata, cikin tsananin kula da lalla fatar, shafa mata maganin yake kamar yana tsoron fameta.
"Sannu Hajja ya k'afafun naki?."

"Alhamdulillah da sauk'i. "

"Da sauk'i sosai ko, in fa kina jin ciwo duk k'ank'antarsa ki gaya mana. "

Daddy ne ya katsesu tare da cewa.
"Abba yadda kake shafa mata maganin namfa baiyiba so ake a murza maganin da kyau."

"A a haka ma yayi in an murza ai sai taji zafi."
sulaiman ne yayi dariya tare da cewa.
"Kai Abba kana ji da wannan tsohuwar ji yadda kake lalla b'ata kamar k'wai".

"ai tafi k'waima wannan".
Yusuf ya fad'a tare da ficewa, ya nufi part d'in mamanshi ya gaidata daga nan yaje part d'in Anty Amarya suka gaisa sannan ya tada Zahra daga baccin da take tana mak'ale da babynta saida tayi salla sannan ya fita.

A parlour Hajja inna kuwa Abba da kanshi ya had'a mad'a tea tasha, sanna Daddy ya bata maganinta tasha, hira suka yi sosai har gari ya k'ara washewa sannan suka fita kowa yayi part d'inshi, ita kuwa Hajja inna sai samusu albarka takeyi, suna tafiya matansu kuma duk suka zo suka gaidata.


***

Ranar wata Jumma'a da yamma,
Zulaihat ce zaune a parlour sai gurzar kuka take fuskarta duk a kumbure saboda dukan da Garzali ya samu dama ya lakad'a mata Mama sai fada take tamkar ta ari baki yau kome za'ayi sai anje an musu tsakani da Zulaihat da Garzali ko itama tayi hayar yan daba suje su daddatsa shi.
cikin takaici tace taje tayi wanka ta kwanta ta huta shigewarta kenan Abba ya dawo bayan Mama tayi masa sannu da zuwa ya shiga daki binsa tayi kayansa ya rage ta kai mishi abinci yaci saida ya koshi take fada mishi abinda ya faru.

A

Please Login or Register in order to submit comment