Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tattausan jallabiya ya zaro tare da zurawa a jikinshi kan k'ananun kayan dake jikin nashi,
hula ya d'auko tare da murzashi bisa kanshi,
kana ya tako zuwa gaban dressing mirror turare ya d'auka tare da fesawa a jikinshi sannan ya d'auki Qura'anin dake kan mirror da carbi dake gefen wurin,
sannan ya juya ya kalli wani sashi na d'akin inda bisa dukkan alamu nanne keb'antaccen wurin da ya ware dan yin ibadunshi,
domin ga sallaya a shimfid'e a wurin.
kai ya d'an juya ya kalli inda take har yanzu a zaune take ta had'a guiwowinta da girjinta,
tunani yayi ko ganinshi ne yasata takurewa wuri d'aya,
dan haka sai ya koma gaban durowar bud'ewa yayi ya d'auki wani d'an madaidaicin sallaya kana ya juya ya fita ba tare da yace mata ko k'alaba.

Ita kuwa duk abinda yakeyi tana kallonshi ta gefen ido,
ido ta lumshe lokacin daya fito don gaba d'aya k'amshinsa ya cika d'akin,
ganin alamun nafila zaije ya fara sai ta d'anji k'arfin guiwa sannan ta koma ta kwanta.


Yusuf kuwa yana fitowa parlour nafilfili yayi tayi har zuwa k'arfe d'aya da rabi sannan ya zauna tare da bud'e Qura'n d'in yayi ta karatu har zuwa k'arfe biyu sannan yayiwa Aryan d'inshi addu'a tare da konciya a k'asa a tsakiyar parlour inda yayi nafilfilin,
kana ya fara can carbi, lokaci d'aya ya koma baccin.


Itako Zahra kusan a haka ta kwana yanzu bacci ya saceta anjima kad'an ta farka.


Koda Asuba tayi,
Yusuf tashi yayi ya koma bedroom,
cikin mmki ya kuma kallonta ganin har yanzu tana zaune inda ya barta a yadda ya barta,
ita kuwa ajiyan zuciya taketa sauk'ewa dan kukan da tayi sakamakon tuno Aryan d'inta.

Kai ya jujjuya alamar Allah ya kyauta don shi a zatonshi shi take tsoro,
bathroom ya wuce,
yana shiga yayi wonka kana ya kuma wani Al'walan sannan ya fito,
riga da wondon wani yadi mai laushi yasa kana ya fesa turare sannan ya juya ya fita.
Bayan fitarshi da kamar 6 minutes taji yayi kiran forko,
haka yasa ta mik'e tare rumtse ido ta sauk'a kan gadon bathroom d'in ta shiga inda nan tashaa mmkin yadda tsarin bathroom d'in yake,
cikin muryar bacci tace.
"Auho ashe shiyasa yake kwana wonka,
bini-bini yazo ya shiga ruwa kamar wani kifi,
ashe bathroom d'inma mazaunine."
wonkan tayi kana tayi al'wala sannan ta tsane jikinta tare da shafa turarenshi,
tana fitowa band'akin masallatai nata kiran assalatu,
so kayan jikinta ta meda kana tasa hijabin sannan taje sashinda aka ware danyin Sallan da fara yin rak atul fajir,
sannan daga bisani tayi sallanta tare dayin azkar.

a wurin ta mik'e bayan taga gari yayi haske wani dadd'an baccine ya saceta.

Shi kuwa Yusuf bayan sun idar da salla shida ma'aikatan gidanshi dana maqocinsa na gefen dama,
sai zauna yayi ta karatu.

7:12 Am ya shiga cikin gida yana tafe yana hamma da yar mik'a domin shi dai ya saba bacci dai-dai wannan lokacin bare kuma irin jiya da baccin bai isheshiba.

Kai tsaye bedroom ya nufa,
zare kayan jikinshi yayi,
ya zauna dagashi sai boxer da vest,
ita kuwa Zahra motsinshi ne ya tadata daga baccinda ya saceta,
da sauri ta tashi ta zauna tana mai gyaran wuyan hijabinta.
cikin sanyin murya tace.
"Ina kwana Hamma Yusuf."
juyowa yayi ya kalleta cikin lumshe ido ya kuma juyowa gaban durowar,
yakai 4 minutes yana sunkuye kan durowar,
ita kuwa Zahra har ta cire tsammanin zai amsa mata,
shiyasa ta mik'e da nufin zata fita ta bashi wuri,
tazo dab dashi zata wuce kenan taga yasa hannunshi ya tare,
ido ta sunkuyar ganin abinda yake mik'a matan,
irin dogayen rigunarnanne da wond'onsu na larabawa masu azabar kyau,
kalarta orange sai d'an gyalenshi,
cikin tsuma ta kuma d'ago ido ta kalleshi,
da sauri ta sunkuyar da kanta ganin shima ita yake kallo,
sai ta kuma d'ago kai ta kalleshi jin yana cewa.
"Lfy lau Alhamdulillah. meya hanaki bacci?."
cikin inda-inda tace.
"Nayi fa."
kai ya gyad'a mata alamar to kana ya k'ara mik'o mata kayan alamar ta karb'a
da sauri tasa hannunta ta karb'a kana tace.
"Ngd."
da sauri ta juya zata fita har taje bakin k'ofar fita sai ta kuma tsayawa jin yana cemata.
"Waya baki damar samin turarena?."
juyowa tayi cikin k'arfin hali tace.
"Ni kam bansa turarenka ba."
baki ya tab'e kana yace.
"Uhummm Allah ko?."
kai ta gyad'a mishi sannan ta fita gudun karya sake tuhumarta da wani abun,
k'ofar shiga side d'inta taje da nufin ta bud'e ta koma amman still har yanzu bata bud'uwa,
fita tayi na harabar wajenma still itama bata bud'uwa dole ta dawo parlour nashi,
abinda bata saniba shima daya dawo masallaci ya gwada bud'ewa amman k'ofar tak'i bud'uwa.
Dole ta canza kayan a parlour nashi sosai kayan sukayi masifar amsarta ta fito ras sai dai idanunta dake d'an kumbure alamar kuka tayi,
ninke kayan da ta cired'in tayi kana ta shiga bedroom d'in a hankali murya can k'asa tayi sallama,
cikin sanyi ya amsa mata yayinda tuni ita kuma ta ajiye kayan gefen gadon,
har ta juya zata fita sai ta dawo jin yace.
"Zoki d'agemin su a gado, turasu can."
ya k'arishe mgnar tare da nuna mata inda zata ajesun.
kana ta fita.
a parlour ta konta inda ta samu tayi baccinta,
shima tuni yayi baccin.

K'arfe goma saura ya farka,
kai tsaye bathroom ya fad'a wonka yayi mai rai da lfy, kana yayi shigar k'ananan kaya wanda sukayi matuk'ar amsarshi,
daga bisani ya d'auko woyoyinshi ya fito parlour inda ya samu Jafar ya kawo musu breakfast kamar yadda suka saba tunda ya dawo daga gida ake kawo mishi abinci,
kuma koda akayi auren har yanzu daga gida ake kawo musu.
gefen Jafar ya zauna kana suka gaisa daga bisani sukaci abincin,
yayinda ita kam Zahra ta gaza sakewa.

saida suka kai shabiyu a gidan sannan Yusuf da Jafar suka fita tare.

Kai tsaye gidansu Aryan babba sukaje,
inda a can sukayi sallan azahar kana sukayi lunch,
daga bisani Yusuf ya tara Kaka da Rafi'a inda yace dole Aryan ya koma bakin aikinshi domin shi dai yasan wannan aiki shine burin Aryan.
shi kuwa Aryan ya kafe yace ina shi yayi hannun riga da aiki tunda aikinshi zai zama madafar magautan Yusuf har su samu galabar tozartashi.
to abu dai saida Yusuf ya nuna fushinsa kana Aryan ya yarda,
dama kunsan Aryan baida zafi shiyasa in Yusuf ya kafe kan abu sai shi ya hak'ura.
To Alhamdulillah Aryan dai ya koma bakin aikinshi.


Ummi kuwa ta dawo maiduguri,
sai daifa lamura sun tsaya mata domin ta lura Daddy fushi mai tsanani yakeyi da ita.

Dija kuwa washe garin randa Aryan ya rasu tayi tafiya zuwa,
Gembu shiyasa bata samu damar zuwa ta'aziyaba raduwarma sai bayan har ta isa Gembu tajita.


Affan kuwa shike kula da lamuran Yusuf a matsayinshi na lawyer.


Haka dai kwanaki suka d'an ja,
Zahra da Hamma Yusuf d'inta kuwa har yau tafiyarsu bata sauya zaniba,
shi yana parlour ita tana bedroom in gari ya waye kuwa tana parlour yana bedroom.
Yana kuma yawan shiga bedroom da dare in zai alwala sai ya sameta tana zaune,
so shi dai bai sake tambayarta make hanata bacciba,
abinci kuwa daga gida ake kawo mata,
a cewar Mama sai randa ta cika kwana goma zasu dena aiko musu abinci.


Yau kwanan Ummi uku da dawowa amman koda tayi girki tun kafin tazo Daddy ke rufe k'ofarshi,
so abu dai yaci tura,
gashi yau dai shine girkinta na biyu amman ko ganinshi da ido batayiba.
shiru tayi lokacin da taje bakin k'ofar ta samu yana rufe,
jikin fargaba ta fara bubbuga k'ofar,
yana daga cikin parlour yace.
"Waye ne?."
cikin iya makirci tace.
"Doctor kayi bak'ine."
jin yayi bak'ine ya sashi zuwa bakin k'ofar ya bud'e,
wuf tayi ta fad'a cikin parlour kana ta juyo tana karya wuya kamar mutumiyar kirki,
shi kuwa Daddy cikin had'e fuska da kaurin murya yace.
"Maza zoki ficemin da gani,
kiyi maza ki bar inda nake tun kafin ranki ya b'aci."
ido ta d'an zaro cikin tsoro tayi k'asa da murya tare da cewa.
"Please Doctor kayi hak'uri dan Allah ka sanar dani laifina gareka na lura fushi kakeyi dani,
yayinda ni kuwa bansan laifin da nayi makaba."
wani irin tsuke fuska Daddy yayi kana ya tako zuwa tsakiyar parlour cikin tsananin bacin rai yace..
"Eh ya za'ayi ki sani tunda ke a zatonki bansan mugun nufi da muna furcin dake rankiba ko Asiya,
kin d'auka bansan ha'incin da kikeyiwa makusanta na bako?."
cikin rud'u ta dafe hannunta a k'irjinta tare cewa.
"Innalillahi Doctor ni Asiya me nayi?."
wani irin tsaki yaja kana ya wuce bedroom nashi,
ita kuwa Ummi jiki na rawa tabi bayanshi domin kalamanshi sun razanata.
zaune ta sameshi gefen gado yayi tagumi da hannu bibbiyu ,
fuskarnan ba walwala ko kad'a,
cikin tsoron kar igiyoyin aurenta su raunata ta durk'usa gabanshi tare da yin k'asa da murya tace.
"Dan Allah doctor ka gafarceni ka gaya min laifina sai in baka hak'uri."
da hannu ya dakatar da ita kana yace.
"Kada ki bani hak'uri domin Allah ya nuna miki ikonshi,
kina hasada ga d'an d'an uwana,
kina shirya mishi mugayen kalamai dan ki zubar da kimarshi a idanun duniya, kina dariya da farin ciki akan k'addararshi,
kin yiwa Zahra abubuwa da dama,
yayinda kika mance kema kinada baya,
kina ta gayawa duniya Yusuf mazinaci ne Zahra karuwace,
baki raga musuba ko dan kashin kaina Jafar Amira da Zeenat yaran cikinki sun fiki hankali,
kece kika gurbata zuciyar Sulaiman da Nana kika cusa musu tsanar yan uwansu,
to duk wannan kanki kikayiwa,
Yusuf da Zahra dai nasu ya wuce,
sai kuma na Sulaiman d'an naki da yaje yayiwa Sakina yar gidan A S Butu ciki ta hanyar yaudararta wai zai had'ata da Yusuf,
duk kina zaton ban sani bako,
har yunk'urin zubda cikin da kukeyi duk kina zaton ban saniba,
baki san cewa doctor da kukaji wurinshi yarona bane,
ha kazalika Sulaiman yana Nigeria kika cemin ya tafi Dubai akan wani aikinshi duk wai kina b'oye laifin d'anki ne ko kin mance sanda kikayi ta tonawa wasu asiri,
to ta yaya kike tunanin Allah zai rufa miki asiri?."
cikin tsananin fargaba da tashin hankali ta fara kuka tare da magiya da bashi hak'uri amman ina Daddy bai wani saurareta bama korata yayi daga d'akinshi tare da cemata ta shirya rainon jikanta shege.


A gidan Yusuf kuwa kamar kullum,
yana parlour,
ita tana bedroom, sam gaba d'aya daren yau bata rumtse idontaba kona 10 minutes,
domin wasu kulullukane suka addabi rayuwarta da koke-koke,
kukanda sautinshi ya hanata jin motsin komai,
yayinda shi kuwa Yusuf yana parlour bai kuma ji kukan kullukanba.
K'arfe d'aya dai-dai ya farka dan tashi yin nafilfilin daya sabayi.
cikin sanyin jiki da kasala ya shiga bedroom d'in.
bai wani damu da ganinta a zauneba domin tsawon kwana uku da tayi a d'akinshin kullum haka yake samunta,
bathroom ya wuce tare dayin buk'atunshi kana yayi al'wala sannan ya fito ya kimtsa kamar yadda ya saba,
turare ya fesa sannan ya juya ya fito parlour,
nafilfilin yayi tayi har zuwa k'arfe d'aya da rabi kana ya zauna ya fara karatu,
k'arfe biyu dai-dai ya rufe Qura'anin kana ya sha addu'a sannan ya mik'e a tsakiyar parlour lokaci d'aya bacci mai dad'i ya saceshi ga k'amshi da sanyin AC na ratsashi.

Zahra kuwa yana fita, taji gaba d'aya filin bayan ya hautsine da koke-koken magunan tamkar zasu d'aga gidan,
kuka sukeyi tamkar kukan jarirai,
uwa uba sai yagunin windows d'in sukeyi,
ga alamun sararin samani ta hautsine da hadari mai tsananin k'arfi wanda ya keto daga k'asa,
ji kukeyi garin sit alamun dare ya tsala,
babu abinda takeji sai kukan magunan,
yayinda sama ta hautsine da walk'iyoyi masu tsananin haske,
lokaci d'aya kuma wata iriyar iska mai tsananin dad'i da sanyi ta sak'o yayinda sanyinta ke ratsa jiki da zuk'atan dukkan abin halitta dake yankin nahiyar.
ajiyar zuciya ta fara sakewa akai-akai dan gaba d'aya bacci ya addabeta,
ido ta lumshe kana ta d'an jingina kanta da jikin kan gado.
fiw bacci ya d'an safceta,
kamar daga sama can cikin baccin taji tamkar cikin kunnuwanta kullukan nan suke kuka,
wata iriyar zabura tayi tare da mik'ewa a firgice,
gaba d'aya jikinta rawa yakeyi,
jin kulullkan nan tamkar kukan jaririyai.
sai hauww hauww suketa cewa sunata fad'a da juna.

Dai-dai lokacin kuma wutar nepa ta d'auke duhu ya mamaye d'akin tsoro mai tsanani ya rufeta,
yayinda ta farajin tamkar kullukan nan suna kan gadon ne,
juyowa tayi a guje ta nufi hanyar fita da taimakon hasken walk'iya, parlourn ta fito a guje cikin tsananin rawan jiki kana tana lalube tare da cewa.
"Hamma Yusuf! Hamma Yusuf!! Hamma Yusuf!!! kululluka sun shigo ta window."
cikin wani daddad'an baccin da yakeyine yaji ta taka mishi yan yatsun hannunshi garin laluben da takeyi kana gashi tanata zabga mishi kira.
wayarshi ya jawo tare da danna haskenta,
ba tare da ya tashi zauneba.
ita kuwa juyowa tayi a guje ganin zahiri wani na bayanta,
cikin azabar tsoro da firgita ta fad'a kanshi har saida yace.
"Wash Allah na, ki nitsufa babu komai."
ina ai batama san yanayi ba gaba d'aya jikinta rawa yakeyi kamar mazari,
hatta numfashinta sama-sama yake fitowa,
wani irin k'wak'uma da zazzafan rugguma tayi mishi jin kukan kule cikin kunnenta kana cikin kuka tace.
"Wayyo Allah na wayyo Hamma Yusuf kule a kan wuyana."
bashi da zab'i dole yabita a yadda tazo domin tana gab da suma sabida tsoro,
birkitata yayi ta kinta gefenshi kan hannun hagunta yayinda Shima ya konta ta gefe kan hannun damanshi ya zama suna fuskantar juna,
Kwak'umeshi ta kumayi tare da rumtse idanunta da k'arfi kana ta cusa kanta bisa k'irjinshi,
jin gaba d'aya jikinta rawa yakeyi,
shine yasa Hamma Yusuf d'in nata sa hannu duka biyu ya ruggumeta da k'arfi wai ko zai samu ta nitsu ta bar karkarwa,
ina saima kamar k'aruwa yayi shegewa jikinshi takeyi tamkar zata koma cikinshi domin har yanzu tana jin kukan kulullukan yayinda shi kuwa Yusuf baya jin komai.
jin yadda ta manne mishine ya sashi lumshe idonshi tare da jan wani shid'ed'd'en numfashi kana ya manna mata......!












By
*GARKUWAR FULANI*


By
*GARKUWAR FULANI*



[01/02 5:46 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*



*PAGE 20*



NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*






Tafin hannunshi ya manna kan wuyanta tare gyara konciyar tasu ya kanainayeta tako ina,
hakan yasa karkarwar da jikinta keyi d'in ya bari,
kana tayi luf a jikinshi,
tare da lumshe idanunta tana jin yadda zuciyarshi ke bugawa a 360 yayinda ita kuma numfashinta ke korar juna,
shi kuwa cikin jin baccin ya bud'e idanunshi a hankali kana ya gyara konciyarshi ta yadda ita kuma ta samu damar yin balance a jikinshi,
tayi pillow da damtsen hannunshi na dama kana ta manna fuskantar a k'irjinshi,
har tana jiyo yadda sautin zuciyarshi ke farbawa dib-dib.
idanu ya lumshe kana ya bud'i baki a hankali cikin sanyin murya ya fara karanto addu'o'i yana tofawa tsakiyar kanta zuwa goshinta.
idanu ta lumshe tare da sauk'e numfashi,
lokaci kad'an bacci yayi awon gaba da ita,
shima Hamma Yusuf tuni kasala mai k'arfi ta rufeshi da ker yake addu'o'in muryarshi tayi k'asa can cikin mak'oshi,
sauk'owan ruwan sama ya k'ara sanyayaya nahiyar Adamawa yayinda mazauna cikinta suka wadatu da shauk'i da nishad'i bacci mai dad'i ya suri Yusuf.


Yanayin sanyi da garin yayi yasa sanyin yafara musu yawa,
gashi nepa sun dawo da wuta kunsan mu Adamawa yanzu Alhamdulillah bamu da matsalar wuta shiyasa shagunan masu saida janareto farashinsu ya fad'i k'asa.
tuni AC ya fara feso musu nashi sanyin,
cikin bacci Zahra ta fara jin sanyi na mata yawa,
hakan yasa ta k'ara ruggumeshi tana jin d'umin jikinshi na ratsata.
shi kuwa Hamma Yusuf numfashi ya sauk'e tare da yin mgnar zuci.
"Wannan kam wai cikina zata shiga ne kuma?."
ita dai bata san yana yiba domin baccin da ta kwana biyar batayi ba take ramakinshi.
Shiko Hamma Yusuf yana sane da dukkan matsinta,
domin baccin ya gagareshi tunda ta tadashi da k'ara mak'aleshi da tayi,
hannunshi ya janye daga rik'on da tayi mishi kana ya jawo woyarshi fuskantar ya d'an haska kana ya tsura mata ido tsawon 45 second sannan ya juyo fuskar wayar ya kalli time ganin k'arfe hud'u da rabine,
yasashi fara janye jikinshi dan lokacin tashinsa har ya wuce dan kullun k'arfe hud'u yake tashi.
janye jikinshi yayi kana ya mik'e zaune tare da cewa.
"Wash Allah na."
sai ya kuna karkad'a hannunshi da tayi pillow dashi,
"wash". ya kuma cewa tare da mik'ewa yana yarfa hannun domin hannun yayi tsami ya tara jini ji yakeyi kamar ba'a jikinshi ba hannun yake.

Tsaki ya d'an ja kana ya juyo tare da watsa mata harara,
sai ya kuma sunkuyo ya d'auki Qura'an d'inshi dake killace a gefe,
kana ya taso ya nufi bedroom kai tsaye bathroom ya shige yayi wonka kamar yadda ya saba kana ya canza kaya tare da fesa turare sannan ya d'auki carbinshi ya fito,
lokacin tuni wasu masallatan sun fara kiran assalatu,
kai tsaye masallacin ya wuce.

Ita kuwa Zahra baccifa takeyi sosai kamar yanzu dare yayi,
sai juyi takeyi bisa carpet d'in,
can cikin baccin taji sautin muryarshi yana kiran assalatu,
ido ta bud'e a hankali kana tayi juyi tare sauk'e gauron numfashi.
sosai takejiyo sautin muryarshi yana kiran sallan tamkar balarabe,
cikin kasala da mutuwar jiki,
ta mik'e zaune kana ta zubawa wurin idanu tana tunano meya kawota parlour,
mik'ewa tsaye tayi tare da yin mik'a sannan ta juya a hankali ta nufi bedroom tana hamma.

Bayan tayi wonka kamar yadda ta saba sai ta meda kayan jikinta,
salla tayi kana ta mik'e bisa sallayar,
tare da lumshe ido tana mai tuno Aryan da yanayin da suke kullum safiya,
idon yana rufe a hakan kuma hawaye na zubo mata,
a haka tayi bacci.

7:35 Am ya shigo cikin gidan kai tsaye bedroom ya wuce,
domin wani irin bacci yakeji yana fizgarshi.

Yana shiga bedroom d'in ya zare rigar jikinshi kana ya haura bisa gadon ya konta,
har ya fara baccin sai ya kuma mik'ewa ya kashe hasken d'akin ko ina yayi lub sai sanyi da k'amshin turaru kanshi,
cikin kasala ya koma ya konta tare da lumshe ido,
tuni baccin yazo.


Ummi kuwa abin duniya fa ya isheta domin,
Allah ya nuna mata ikonshi.

Dan Sulaiman dai tunda ya samu Yusuf ya bar k'asar sai ya fara cin karenshi babu babbaka da Sakina AS butu,
wacce d'iyace ga marigayi A. S butu wanda hamshaqin mai kud'ine yanada gidajan mai a dukkan sak'ok'in Nigeria,
so yara biyu rak Allah ya bashi Sakina sai yayanta wanda lokacin da sukaje ummarah suka had'u da Yusuf da Sulaiman,
ita kuwa Sakina dama ta tasawa ranta burin auren sanannan mutun wanda duniya keji dashi,
shiyasa ta nacewa Yusuf wanda shi kuwa baima san tanayiba,
dan bayan sun bar saudia sunje Dubai sun kuma had'uwa amman shi Yusuf ya yayi kamarma bai tab'a ganintaba domin shi dai baya son mace mara aji.
To kunsan bayan dawowarshi Nigeria kuma da kwana uku wannan tsautsayin ya rufta dashi k'arshe ya k'are shekarar a furzin,
yayinda hakan ya kara sanuwarshi a duniya,
yana fitowa furzin kuma ya bar k'asar.
toh da wannan damar Sulaiman ya yaudareta,
domin shi yana son shine ya aureta kasancewar yar masu hannu da shuni ne,
ita kuwa ta nuna Yusuf take so ba shiba,
so da zumar zai kaita wurin da Yusuf yake ya yaudareta domin dama Suleiman namamajone shi yana nan tamkar bunsuru in dai yaga mace to shi dai yasha ya tafi,
babu wanda yasan wannan d'abi'a ta Sulaiman sai Yusuf kuma shike taka mishi birki,
so ya samu Yusuf bainan sai ya sake,
kana yayi farin ciki da butulcin da Aryan yayiwa Yusuf a cewarsa Yusuf d'an hana ruwa gudune.

Zama yayi zama ya samu ya yaudari Sakina tuni ya tsumata ya mantar da ita Yusuf da yake dama shahararshi takeso,
sosai suka fara soyayyar shan minti har ya kaisu ga soyayyar rijiya da guga,
cikin ikon Allah suka dad'e suna holewarsu
kaaancewar Sakina bata da mafad'i shima kanshi yayanta sa'an Yusuf ne yana kuma fama da tarin dukiyar da mahaifinsu ya bar musu,
shiyasa baya wani tsareta,
so tunda Sulaiman yaji Yusuf zai dawo,
sai ya kwasheta sukayi Abuja,
inda sukecin karensu babu babbaka,
yayinda yayiwa Daddy k'aryar cewa ma'aikatarsuce ta turashi Dubai,
tofa sunje Abuja da kwana biyune suka gane tanada ciki sabida zazzab'in da tayi tayi,
kana asibitin da sukaje doctor yaron Daddy ne ganinta tare da Suleiman ne ya sashi yiwa Daddy bayanin duk da sukayi mishi.
kana ita Sakina kai tsaye ta gayawa Yayanta,
so ya nemi Daddy sunyi mgnar inda suka yanke hukuncin tana haihuwa za'a d'aura musu aure da Sulaiman.

To abin shiya buwayi Ummi tana tsoron randa magnar zata bazu,
abinda bata saniba tuni su Mama sun san da mgnar kuma abin bai musu dad'iba.


Ga kuma Nana da tuni Sultan ya gyara mata zuckyarta da kyawawan d'abi'unshi,
tuni ta juyawa Ummi baya,
dama tana son yan uwanta.


Ganin fushin da Daddy keyi da ita yayi tsauri dole ta kira Sulaiman tace maza ya dawo.

Aryan kuwa komawarshi bakin aiki keda wuya,
tuni nasabarshi ta taso,
sanadin abinda yayiwa Yusuf yasa duniya ta d'aukeshi mai tsananin gskya da rik'on amana ya nunawa duniya duk kusancishi da mutun babu ruwanshi in aiki yabi ta kanshi ba sani ba sabo gskya zaibi duk d'acinta,
haka yasa darajarshi d'aguwa domin ai ita gskya nasabarta nada yawa.

Affan kuwa yanzu sai bud'awa Hamma Jabeer d'inshi hanci yakeyi.
domin wai suna son Yusuf ya dawo Jahan polo team,
dan sunada burin shiga gasar world polo 2020 gashi an meda gasar a forkon shekara tsabin da baya a k'arshen shekara akeyi,
shi kuwa Affan yak'ima ya sauraresu.
shiko M Jabeer yace yafi son Affan yayiwa Yusuf d'in mgnar,
shi kuwa Affan bai kuma bin ta kansuba.

Idi kuwa shima hark'alla taci gaba domin Yusuf ya fad'ad'a mishi kasuwancinshi.

Jafar ma ya fara zuwa aiki a yau da Aryan ya cika kwana biyar da rasuwa.

Zahra da Yusuf kuwa tafiya dai tayi tafiya,
tun daga wannan ranar har yau in dai dare yayi kuliyoyin nan ke zuwa su hanata bacci kuma sai sun tabbatar da Yusuf ya idar da nafilfilinshi yayi bacci sai su tasota gaba,
dole ta fito parlour wurinshi,
so daga nan kuma sai su tafi,
kuma shi Yusuf baya wani jin kukansu da take cewa.


Yau wuni yayi da bacci a idanunshi dan ta hanashi bacci daran jiya kana da gari ya waye kuma ya fita dan anata shirye-shiryen bud'e wani babba kamfani mai suna Yusrah.


Ita kuwa Zahra ranar bayan sallan azahar k'awarta Dija ta kawo mata ziyara inda Zahra tayi mmkin ganinta ita da Jafar ne suka zo,
bayan sun gaisa Jafar ya mik'e tare da kallon Dija cikin yin wani yanayi da ido yace.
"In kin gama ki kirani."
cikin yin fari da ido tace.
"Toh Ya Jafar."
ita kuwa Zahra ido ta zuba musu ganin yadda suke ta wani rausayar da idanu,
shi kuwa Jafar tuni ya fita.
cikin cikin fuska Zahra ta kamo hannun Dija tare da cewa.
"Taso mu tafi can d'akin ki gaya min sirrinku keda ya Jafar."
sunkuyowa Dija tayi ta d'auki wata babbar lada data shigo dashi kana tabi bayan Zahra.

nan shige wani corridor dake gefen dinning area d'in, sai gasu a wani d'an madaidaicin parlour da bedroom dinshi,
zamewa sukayi kan 3 str cikin wasa Dija tace.
"K'awas ko dai yanzu kam Aunty Dija zan cemiki ne,
naga wani kallo da ya Jafar ke miki please gaya min menene sirrin?."
cikin dariya Dija tace.
"Hahaha ke kin gaya min sirrinki da Hamma Yusuf ne?."
cikin lumshe ido tace.
"To ai mu mata da mijine haramunne in gaya miki sirrinmu."
dariya Dija tayi tare da d'aka mata dukan wasa kana tace.
"Zahra kina iya hege yaseen to nima bani son jin sirrinku,
kuma muma namu bana ji bana."
sai ta kuma gyara zama tare da cewa.
"Hmm kinsan

Please Login or Register in order to submit comment