Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

aika asayomin SIM inason fara amfani da waya".
Gyada mata kai malama tayi tana tunanin ky'an zuciya irin na RUWAIDA duk abinda ta mata har yawuce komi ita take tambaya kamar yanda suke da goge hawayen da batasan suna zubowa ba tayi tace "to Aisha glo da airtel da mtn ko?
sai asannan Ruwaida tasan mlm kuka takeyi aikin kenan kullum har tausaya mata take shiyasa take kokarin nuna mata komai ya wuce
komawa tayi ta zauna
"haba mlm sonawa zance kidena kukan shekarunki ya kai da zaki rage damuwa kar wani ciwon ya kamaki mlm kigodewa Allah wata nata lefin dashi aka minneta mutane nawane suka aikate lefi fiyeda naki basu nemi tuba ba amma ke kowa ya yafe miki mijin ki da matar aljannar yake k'iranki kullum sai yakiraki da matar aljanna ko yau nasan kafin ya fita ya fada to wannan ya isa abin godiya kuma mutanen duniya ba wanda yasan ga abinda kikayi kowa yabonki yakeyi kinsamu sheda mekyau ki gode Allah."
murmushi malama tayi tace "shikenan kije ki gaida Ummar sai kinemi izinin mijin ki zaki fara amfani da waya."
"haba mlm dan zanyi amfani da waya sai na nemi izininsa bayan shi ko damuwa bai yi dani ba ina ma zan ganshi."
Mlm tace ."koma ya yake yana da hakki akanki kuma ko a ina kika gansa de kinemi izini."
"to. Kawai tace
tafita k'aninta Umar dan dak'in ummusulem yace "Wow aunty beautiful kinyi kyau yawwa aunty ai kinfi Ya Abdullah kyau ko amma wai Barrat tace yafiki."
" au gulmana kuke kenan zonan bance kana cemata aunty Barrat ba? ."
cikin tsoro yaja da baya Aunty Kiyi hakuri wllh bantawa nayi ai kinji nacewa yaya Abdullah yaya."
tace shikenan ka kiyaye kaje kabawa mlm hadda."
Aunty nifa naba da tunda Abba zai fita Ifteesan da Habotee ne basu bata ba. "

Ok suna ina Sunna part din Ummul."
"to kace suje suba da kafin nafito."
tsalle yake yafita dan yasan sune basuyi hadda ba dan yaga kamar Aunty nasu zatafi mlm fada ita malama ba duka ba zaji
ahankali ta shigo duk da taji kamar k'amshi sa a parlour Umman amma bata ganshiba duk da kanta ba ak'asa yake ba
hankalin ta yana kan yaran da suke gaisheta tana amsawa
hakan ya bawa Mall daman shagala da kallon ta tayi wani mugun kyau sai da yaka kamar zata juyo ya maida hankalin sa akan Umma juyowan da zatayi taga mutum zaune taji wani mugun faduwar gaba ahankali ta k'arasa parlour ta durkusa kusa da Umma tace "Umma antashi lafiya.?
"Alhamdulillah Ruwaida ya jikin ki ? .
"naji sauki."
"Masha Allah".
juyowa tayi tabude baki zata gaisheshi sai dai dai lokacin wayan da yake gefen sa Yayi ringing komawa tayi ta zauna shima ya daga wayan yana cewa "Eh da yake tafiyar mota nayi shine na tsaya a kaduna gaida Ummata zan duba in sha Allah ok sai auren Mujja thanks.
ya kashe wayan
Ruwaida ko cika tayi fam ashe ba dan ita yazoba
awani gunya tashi ma
Itama Umma dan tak'ara kular da Ruwaida dan ance mata Ruwaida bata san yasaki Halima ba tace "ko deda surukar tawa kake ne."
shiru Mall yayi kamar zaice wacce surukar sai kuma ya harbor jirgin Umma yayi murmushi yace "ah ah Umma ba ita bace kinsan nace miki tana fushi dani akan sai nazo da ita."
Umma tace ai da kazo da ita kaga bata taba zuwa ba dole tayi fushi."
"Umma nafa fada miki bata da lafiya."
Umma tace" hakane Allah de yaraba lafiya."
shiru yayi kaman mejin kunya
itako Ruwaida sai da suka gama maganan su ta juyo ba yabo ba fallasa tace "Yamall ina kwana ya hanya.? duk tajera lokaci guda duk abin mutum bazai ce ga yanda fuskanta yake ba
shima d'agowa yayi ya kalleta ya sauke kallon akan wayan sa yace "kina lafiya.?
ata k'ai ce
bata sake cewa komai ba sai Umma ce tace "Hajja ta fito parlour ne .?
Ruwaida tace "eh
Umma ta mek'e tace" bari naje na gaida hajja.
Mall yace"ok .
tafita
Ruwaida ma mek'ewa tayi zata fita har tayi taku 3 ta tuno batun izinin amfani da waya bata juyo ba ahankali tace "inason zan fara amfani da waya."
Mall wani dadi yaji dan da yaga wayan a hannunta yazaci mata fara amfanin ne
Jin yayi shiru yasa ta juyo saurin dauke kansa yayi kamar ba ita yake kallo ba
tazaci bai ji bane yasa ta mai daita
yana cigaba da danna wayan sa cikin basarwa yace "neman izine kike ko umarni.
Ruwaida tayi mugun kulewa da yanda yake mata magana kamar wata kashi
cikin k'uluwa tace "dukka biyu.
shima cikin i sa yace "ok ba da izinina ba kuma ban yarda ba "
kallon sata tsaya yi kamar zatayi magana kuma tama rasa me zatace zata juya ya dago kai yana mata wani kallo ta dauke idonta
Murmushi yayi yace "kici gaba da kallonki halalinyan kine fa idan kina bukata kar ki cutar da gangan jikin ki dan akwai shisabi a tsakanin ku idan kin cutar dashi
Ruwaida tace "banga abin son ba kuma ban ga me hanani fara amfani da waya ba wllh."

hannu kawai ya d'aga mata alaman ya isa
tafita a fusace part din mlm ta shiga Dan tasan ita kadai ce zata sanyaya mata zuciya da kalamai masu gamsarwa
shiko mall ya zauna yana tuna randa Ruwaida zata sake shiga hannunsa yayi murmushi shide aduniya yasan bawani abu da zai so kamar Ruwaida ahankali ya furta lalle kincika INDON MATA.."
Umma tace "Allah Sama ilu.
da sauri ya bude idon sa dan bai san ta shigo ba murmushi yayi yace " sosai Umma kubani ita dawuri ko na taro gidan nan."
"haba kar ka badani mana."
sosa k'eyarsa yayi yace Umma Aisha cefa
bai de karasa ba."

Hajja sai bayan Mall yatafi taji labarin zuwansa tazo tayiwa Umma tatas har Ruwaida bata bari ba acewar ta meyasa bata kirata ba ita da take neman sa ta rama abinda yayi mata munafuka wato kina son mijin ki ko

Ruwa taga gata awajen Abban ta dan tafiya ya kamashi yatafi ba dan yasoba bayan yacika mata account fal da kudi amma
shirye shirye biki ya kan kama dan har anfara gudanar da biki tun Thursday Ruwaida da Ayya suka sauka Ruwaida ansha fama da hajja dak'er da alk'awarin lalle ba ita ba Ismail kuma ana gama biki kafin ma su Unma suzo ita zata zo

Ummm to bari muga ko malam ILU zai yar da yasaki wannan dama

*ADAMAWA*

*HAMRAH* me kwana biyu yakoma sati biyu dan ita ma yau din take shirin zuwa dan tana tafiya da kwana daya tafiya yasamu Sahal yazo sukayi sallama
Hajiya Hamrah wanda yanzu ta koma Auntyn family sarkin k'ira dan komai za ayi sai da shawaran ta yanzu haka ranan aure za a yanke agidan Hamra ceta tasa rana ta tambayi yaran kalan kayan d'akin da suke so da taga bawani sanin kan kayan da ake yayi sukayi ba kawai ta cewa Sahal ya saya musu irin nasu Kharajina
su baba Hamza tuni suka sa Baban hamrah ya taro gidan suna family yanzu kam son Kabiru kuruma ake sosai

Hamrah an mata rakiya har mota kowa sai da yafito har moton yafita agidan ta ga kamar zauren k'ira hayaki yana fitowa ta juya ta kalli Binta da Rabiya da zata wuce dasu Kano har sai angama biki su dawo tace k'ira har yanzu agidan nan wayake mana k'ira Binta tace " Ya Nura.
saukowa hamrah tayi zata shiga zauren amma zafi ya hanata shiya a koma ta tsaya "Yanura da sauri Nura yajuyo fuskan baki k'irin ga toka da gawayi da gumi yayi masa kace kaca ba wanda zai ce shine *Alhaji Nuraddin Hamza sank'ira*
cikin murmushi Hamrah tace "sannu Yanuri gaskiya k'ira akwai wahala dole kace kai baza ka dauwama a sana an k'ira ba amma gado ba karan bani bane k'ira ba sana an rago bane kuma sai wanda ya gada dariya tayi tace wayyo har na tuno min da CABALLIYA a gidan mu gidan dadi kullum sai tamin wannan wak'an
*wasan wuta wasan wuta da ciwo yake ne hamratu k'ira ta gada*
kasan fa sana an k'ira sai magajin sa saboda abune da rago bazai iyaba haka bakware ya gaji shiga ruwa idan ka bashi k'ira bai isa ba shiyasa nake alfahari da sana ar gadona YaNura Allah ya temaka tajuya zata tafi ahankali ya mek'e nadama afuskan sa ba zai misaltu ba yace "Hamrah kiyafemin Dan girman Allah ."
"YaNura na jima da yafe maka meyasa kullum ka ganni sai ka nemi yafiya ne ? bayan yawuce na yafe nima Allah ya yafemin kurena."

"Hamrah na cutar dake dayawa amma hamrah idan da gaskene kin yafe min ki bani documents dina wllh akwai wani abokina zai nema min aiki takaddun kawai ake jira

."shiru Hamrah tayi
shiyasa tun a lokacin tace a ajiye kar akona Ruwaida da zafin zuciya ta kona su bata soba tasan irin wannan ranan zai zo dan koya naka yake nakane
"yaNura sai de kayi hakuri nagaya maka ankona su wllh amma in sha Allah zanyiwa Aunty Ayya magana aiki bazai gagara ba ko a companyn ta kafin nan ka tambayi Habibullah na bashi sako ya baka inaga mantawa yayi....
jitayi abayanta ance "ba mantawa yayi ba nina hana.
atare suka juyo duk da sungane muryar me maganan
Hamrah tace Wassilim meyasa hake haka kudina ko naka."

Wassileem da yake jin kansa ayanzu kamar shine gaba da Hamrah kudi ya zauna masa kuma gashi mijin *AMMA SHIDDAS BARNO*
aboki ga
*AKKARAM SHID*
yayi gogaiyya da manya yana ma kanyi dan idan aka irga masu kudin adamawa zai iya zuwa na goma ga temako amma banda yan gidan su da yatashi da mugun haushinsu yanzu haka ban da sun kawo masa iyayensa ba abinda zai kawoshi kuma bayajin zai yafe

Hamrah tace "yanura taromin account number din ka tajuya shima Wassilm tsaki yayi yashige cikin gida tasan kafin ya huce sai tasha fama zuciya kamar shiya gaji kurmantan
*Kano*
shirin biki ya kan kama dolen sa yana dan shiga safgan bikin saboda abokin sa Mujjashid wanda zai aure Nafisa kanwar sa wamda suke daki daya da Sahal
ayau ne Tuesday za ayi match ball na bikin an sha fama da Mall akan bazai yi ba musamman da sunansa ya fito a Team amarya kamar ance yasake kallon takardar aiko caraf yaci karo da sunan ruwaida a Team na ango kan uba matar sada buga kwallo agaban dinbin jama a sai de idan fasa auren za ayi inde dole sai anyi March amma yasan bazai samu goyon baya awajen Ummi ba dan tana da son bidia Amma ceta fado masa dasauri ya jefawa matawalle rigan wasan da aka basa me sunan amarya gaba da baya nafi ajiki yafita sahal yace "ai dama nace muku shigen ba zai yiba shida yake ta fadan mujja ya zubar mana kima yaje yana wani soyayya da yara".
dariya matawalle yayi yace "koni sanda nake soyayya da Kharajina har nabar Kano bazai min magana ba sai gashi shima ashe yarinyar yajima yana nema sa arsu ce."
duk dariya sukayi sahal yace" sai ma kunga wahalan da yake sha tsohuwa ta hanashi matar sa." daga nan ya kwashe abinda yafaru ya gaya musu dariya sukayi tayi
Matawalle yace "randa yafara sa ruwaida a idon sa ya gigice nace masa ai itama yarinya ce batafi Kharaj ba haka yace tafi Shatima ma ".
Sahal yace "bawani ai shekara guda kharajina tabawa Ruwaida."

Umma ta Kalli Mall tace "to yanzu Samaila ya kake son namaka kabari kawai nasan ma Ruwaida ba zata ce zatayi wani Ball koda ba aure akanta."
nasani ita ustaziya ce amma Umma kisani idan irin wannan bikin ya taso wllh dayawa ajiye ustazancin akeyi kisamo min mafita shikenan zan hanata."

Ruwaida Umma ta hanata amma batace Mall ne yahana ba shima Mall bai zo wajen ba dan ya tabbatar bata jeba

Amma de anyi wasa me k'ayatarwa a inda Amarya Farida ta ciye angonta SadeeQ ita
ma Nafi ita ta ciye ango Mujjashid da mutanen bayan sa
Ita kuma kharajina Affan ya lashe Affan dan gatan mommyn sa harda ita awasan ba kunya ta zage tanayi wanda basu san ta bama yau ga alk'arin AK'alai afilin wasa auren d'an lele

haka ran kamu Friday akayi kamu Mall de bai jeba amma yacika fam da yanda aka dinga posting hotuna a media yawanci da ruwaida aciki dan sunyi kyau ita da Ayya da Hamrah har kaman zasufi amaren haka aka dinka tsokanan ruwaida kamun harda ke dama ba amiki ba status ko yau ranan sane duk da ransa bai so yada hotonan ta ba amma baya gajiya da kallon su kusan dare yaraba dawaya ahannu gani yake duk duniya ba wacce tafi Ruwaida

Shagalin sai yau ake yinta yau general
Paty
Matar da aka dauko takanas dan kwalliyar amare da k'irajen biki haka kawai taji tana son Ruwaida da Ayya da Hamrah dan haka makeup din su daban ayanda ta tsara musu kwalliyar dole su dauki hankalin jama a Ruwaida ta Kalli kanta yanda kayan ya kamata sosai ta kalli Abida tace "aunty abid anya zan iya fita haha gaskiya kayan sun kamaki sosai wai baki bada measurements din riganki bane. "
Hamrah tace "wllh aunty dai dai ni akayi kuma tsayis dinmu daya baki ga ta kara cika ta k'irji wllh Boobs dinta da Hips sun karu Zahariya tace "eh wllh sis me sirrin ne.? Abida tace amma gaskiya ba zaki canza ankon nan ba kiyi hakuri kawai ai bikine.
su ukku suka fito dan yawan ci an wuce suna fitowa kowa sai Masha Allah yake cewa iya wanda ba zasu je bane a gidan Ruwaida ce take ta dube duben wanda zai kai su dan wannan adon bata driver bane gwara su nemi me tuk'asu da k'er suka samu wani abokin lawan ya kai su har anfara gudanar da dinner hamrah ce afarko Ayya na binta sai Ruwaida da gabanta yake ta faduwa abaya dan taran abokan Affan suna wajen karsuyi abinda zai taba mutumcinta dan tasan yan tabara ne dukka sangartattu irinsa ne
duk angwayen kowa kusa da tasa amaryar Mall da kansa asunkuye yake acen gefi wani irin ihu yaji Hall din ya dauka
*kala abasu kala abasu kala* ko sautin kidan ba aji saboda ihon mutane juyowa yayi dai dai san da suka karasa tsakiyar filin wani irin zabura yayi ya mek'e


*saboda yanda labarin ya jima ne na dan kara yawan pages din in sha Allah a page 28 zamu tsaya kuyi min abuwa*


*08062383027*
[05/01 5:58 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

*Page 2⃣6⃣*

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇





"Zan fad'a a ko ina a koda yaushe a gaban kowa ina sonki Mama duk duniya bani da kamarki mahaifiyata."
cikin jin wani irin shauk'i akan shak'uwa tsakanin d'a da uwa Matawalle ya sarawa Yusuf tare dasa hannu ya rufe mishi marfin motar.
sauran jama'a kuwa wasu harda yar k'ollansu dan ganin tsantsar so na tsakanin uwa da d'anta.

Mama kuwa ido ta rumtse da k'arfi yayinda hawaye ke bin idonta a lokaci guda kuma tana dariya,
jin d'igon hawayen Mama kan hab'ar Zahra yasa ta mik'e zaune tare da zubawa Mama ido tana kallon wani irin wutar son Hamma Yusuf d'in cikin idon Mamanshi,
kai ta jinjina tare dasa hannu ta share mata hawayen dukansu ba wanda yayi mgna.
suna cikin haka suka jiyo Daddy yana cewa.
"Ikon Allah Maman Yusuf kinga Yusuf d'inki ko,
wai yanzu nake sauri-sauri zanje tarbarsu ina fitowa wanka naga tuni A T V suna nunasu tuni har sun iso,
kai Yusuf mai jama'a kenan."
mik'ewa Mama tayi tare da fitowa tsakar gidan inda Daddy da Ummi ke tsaye cikin shirin fita murmushi tayi tare da cewa.
"Ya kamata kam a sameka a kusa dashi."
gyara zaman hular kanshi yayi sannan yace.
"Eh ai yanzu zanyi maza inbi ayarin motocin in samu mushiga fadar masarautar tare."
"Toh Allah ya kiyaye a shafa min kan d'an autana."
Dariya Ummi tayi tare da cewa Zahra data fito yanzu.
"Yauwa Zahra kije ki k'arisa mana aikin nan nama gama komai miyar kawai zaku daura in tayi d'umi ki zubawa kowa,
sannan ki tafasa mana tea ki d'ura a filas,
sai ki haura d'akin Daddynku ki tattareshi."
to tace tare da matso Daddyn cikin nitsuwa kamar ba ita bace uwar rawar nan tace.
"Daddy kud'in dinkin namu?."
kai ya juya lokacin daya fara tafiya Ummi na binshi a baya.
Ummince tace.
"Ya bani kud'in ki duba cikin durowa,
harda kud'in gyalenku,
Isma'il d'inma munyi mgna dashi yace zai kawo muku kayan da kanshi wai akwai wanda bai k'arisa bane".
"Toh". tace sannan ta d'auki tsintsiyar kwakwa ta fara share tsakiyar gidan saida ta share ko ina tsab,
sannan taje ta k'arisa aikin da Ummi ta sakata,
bayan ta gama komai a can ta dawo kitchen d'in Mama nanma tayi mata duk aikin data saba,
sannan tayi wanka ta fito ta nufi gidan Aunty Fadwa dan Salima zata rakata kasuwa,
tana fita can harabar gate d'insu tayi part dinsu Iya shatu,
a tsakar filin ta samesu ita da Hajja Inna,
murgud'a baki tayi ganin Hajja Inna na hararanta gami da tab'e baki,
ita kuwa Iya shatu murmushi tayi dan inda sabo yaci ace kowa ya saba da halin hantara da Hajja Inna keyiwa yaran Aunty Amarya Especially Zahra,
cikin murmushin tace.
"Zahra'u k'arbo d'inkin ne zakije?."
Kai ta juya tare da cewa.
"A a kasuwa zanje,
zan sayo mana gyalullukan acobin auren Aunty Raiha ne,
kema zakije dinner ko kiga yadda akeyi?."
ta k'arishe mgnar da alamun tambaya kuma da iya gskyarta,
cikin dariya iya shatu tace.
"A a ke dai ki dauko min a wayarki in kin dawo kya nuna min."
ita kuwa Hajja inna sai cewa tayi.
"Amara k'irjin biki, in kinje kasuwan saya min goro mana ko na 200 ne."
juyawa Zahra tayi tare da fara tafiya tace.
"Bazan saya ba."
mik'ewa Hajja inna tayi cikin kumfar baki tace.
"Toh ai kud'in bana d'anki bane na d'anane inaji d'azu ya baku to dole ki saya min."
juyowa tayi cikin tsiwa tace.
"Ank'i a sayo d'in,
Ina dai kud'in na uba nane to kema sai ki nemo na ubanki."
wohoho ina wuta Hajja Inna ta fad'a ciki,
wai ai Zahra ta zageta,
ita kuwa Zahra ko a jinta ta fita ta tafi abunta bayan ta biya Salima suka tafi tare.


A fadar masarautar Adamawa kuwa sai bayan sallan la'asar su Aryan, Daddy, Sulaiman, da Bashir suka samu damar ganin Yusuf.
Suna fitawa masallacin su M Jabeer da Affan da wasu makusantasu sukayiwa Yusuf rakiya har inda su Daddy suke,
suna isa wurin motocin da sauri Yusuf ya k'ara garesu yana zuwa kawai sai ya ruggumi Daddy tare da gaidashi,
"Daddy barka da yamma."
murmushi Daddy yayi cikin jin dad'i marar misaltuwa yace.
"Alhamdulillah yarona yaje Lfy ya dawo Lfy."
sakin Daddy yayi da sauri jin Aryan na cewa.
"Oh Sulaiman mu kam ba'a bin ta kanmu."
cikin tsananin shak'uwa da kewan juna yaje gabansu tare da ruggumesu dukansu,
dariya suka saki sai suka kuma d'an tureshi tare da bashi hannu d'ad'd'aya shi kuwa ya mik'owa Aryan hannu d'aya Sulaiman hannu d'aya,
a tare suka tafa sai suka kuma ruggume juna.
cikin dariya da wasa irin na abokai Aryan yace.
"Masha Allah d'an yaro!
d'an saurayin nan ka ganka kuwa kamar wani balarabe sai shek'i kakeyi."
dukan wasa Yusuf ya kaiwa Aryan tare da cewa.
"Banza waye d'an yaron?."
kaucewa Aryan yayi tare da cewa.
"Bashir ai kaima ka yarda d'an yarone ko,
tunda tuzuru ne babu mata,
dan manyance kuma harda tara k'asumba."
shima Bashir dariyar yayi tare da cewa.
"Kwananna ai zamu aurar daku,
nima in samu in hau layi."
dariyar shek'iyanci sukayi tare da yin k'asa-k'asa da murya dan kar Abba da M Jabeer dake gefensu suna tattauna wata mgna tasu ta daban ,
karsu jisu,
Affan kuwa da yanzu ya gama mgna a waya harara ya d'an cillawa M Jabeer tare da meda kallonsa kan su Yusuf da suka zuba mishi ido cikin tsuke fuska yace.
"Mitseew ai wallahi ni badan wancan k'aton tuzurun gidan namuba yaseen da tuni nayi aure,
amman da yake shi gani yake kowama irinshine sai na tashi da nufin zan fire in wuceshi inyi aurena sai ya tsigemin fiffige."
ai kafin ma ya gama Aryan kam dariya yake mishi harda rik'e ciki,
Sulaiman ma sai dariyar yakeyi hakama Bashir,
shiko Affan hahara ya kuma watsawa M Jabeer tare da jan dogon tsaki.
"Mitsssw ganshi kullum yana fama da al'kebba sai kace limamin makka,
kana mishi mgn in yaga dama sai kaji ya fara karatu da tasbihai ya wani shareka da zancenka,
yana abu kamar waliyi shi baruwanshi da mata."
duka Yusuf ya kai mishi tare da cewa.
"Banza ya ishekafa da zagarmin uban gida,
ai dole ya tsige maka fiffige domin kai in ba tsigekan akeyiba akwai matsala banza jarabebbe."
wani irin kallo Affan yayiwa Yusuf sannan ya juya gasu Aryan dake dariya da baki ya nunawa su Aryan inda Yusuf yake tare da cewa.
"Kuji wannan *namijin Ayu* d'in wai shima har zai cewa wani fitinenne jara bebbe."
shi dai Sulaiman dariya yayi tare da cewa.
"Oh oh ai wannan hirar taku ta girmi shekaruna."
shiko Aryan cewa yayi.
"Kada ku damu zamu aura daku."
murmushi sukayi baki d'aya ganin yadda Affan ke watsawa Yayanshi M Jabeer d'in harara shi ala dole M Jabeer ya takurashi dariya suka kumayi lokacin da suka juya suka nufi inda su Daddyn ke tsaye jin Affan na cewa.
"In ka ganshi zakayi zaton mata hud'u gareshi harda k'wark'wara gashi da kamala da ilimi,
amman yak'i aure,
d'an hana ruwa gudu kawai shugaban tuzuran Nigeria."
shiru yayi lokacin da suka isa gabansu kamar bashiba ya nitsu abinshi,
duk abinda M Jabeer yace sai yace.
"Toh Hamma mun gode Allah k'ara girma."
shiko M Jabeer hannu ya mik'awa Daddy sukayi sallama sannan yayi musu addu'ar isa Lfy,
sannan yace Affan,
"Mu shiga ciki ko Aku."
baki Affan ya d'an tura sannan ya bawa su Aryan hannu sukayi sallama tare da cewa,
"Sai na shigo."
sannan yabi bayan yayan nashi suka tafi.

Wasu irin tsala-tsalan motoci nagi matsu azabar kyau daga ka gani kasan dala tayi kuka,
wata tsaleliya naga Aryan ya bud'ewa Yusuf
Audi-Rs6
sai kuma Range rover velar guda biyu masu d'an karen kyau,
cikin zaro key's d'insu al'jihu ya cillawa Sulaiman d'aya sannan ya kalli Yusuf tare da cilla mishi d'ayan shi kuwa ya rik'e d'ayan,
sannan ya kalli Daddy cikin girmawawa yace.
"Daddy wad'an nan sune motocin da Yusuf ya saya mana,
toh dama dunda suka iso na kawosu nan don lokacin ana gyaran gidan namu,
Range Rover d'in d'aya ta Sulaiman ce d'aya kuma tawa, tsohuwar tawa kuwa ni na bawa Bashir
shi kuwa Audi-Rs6 dince tashin,
sannan sai wasu guda biyu suna gida mu."
murmushi Daddy yayi cikin yabawa da dottakun Yusuf sannan yace.
"Toh Allah ya sanya alkhairi,
Allah yasa rai akayiwa."
"Amin Amin".
sukace a tare sai Yusuf daya d'an tsuke fuska yace.
"Ni dai motar Daddy na zan shiga."
cikin jin dad'i Daddy yace.
"A a ba matsala Yusuf duk kushiga motar ai zaifi mu tafi a jere rakiyar taka zatafi armashi,
gashi dama kaga M Jabeer ya bada motar fadawa 3 zasuyi maka rakiya to kaga bazamu so a gane cikin wacce motar kakeba kyai tsaye."

Haka kuwa sukayi suka jera yayinda motar fadawa ke gabansu sai d'aya da take bayansu ya zama motoci shidan suna tafiya a jere,
sannan ga yan Jahan polo team a k'alla su 30 su kuma kan dawakai da uniform d'insu suna zageye da motocin,
daga nan cikin fadar suke tafiya a jere har cikin jimeta,
yayinda suna fita kallo ya koma sama,
sabida wani irin gudu da suke tsulawa kamar masu tashi sama,
kunsan abu da matasa wad'anda jininsu ke harbawa da zafi-zafi sannan ga sabbin motoci ga k'uruciya uwa uba ga matsayi,
ai Aryan da Sulaiman kamar zasu tashi sama gwarama Yusuf d'in dan shi yana bayan
Daddy ne to shiyasa

Please Login or Register in order to submit comment