Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

mata k'awanya, ga wani irin ruwa mai hasken garai-garai da yake tsatstsafowa a sassa da yawa na jikin dutsen da yake shimfid'e a nahiyar ga beneye masu kyau da tsari da jan hankali ga wasu irin tituna dake shimfid'e a lungu da sak'o na cikin jami'a ga wasu fulawowi masu furannin orange and blue and pink colors da sukayiwa ko wanne wuri k'awanya, bugu da k'ari ga bani adam da suke rayuwa a wurin mafi akasarinsu fararene masu kyau da haiba, kai dolema mutun yaji shauk'i da nishad'i a wannan wurin.

Kai tsaye har ma kwancin daliban yaje yayi parking inda suka raka Aryan tsakiyar taron jama'ar da suke tsaye gaban allon da aka lik'a sunayen sabbin d'alibai da numbers d'in d'akunan su,
kutsawa cikin Aryan yayi inda yana sa ido yayi arba da sunanshi da number d'akinshi,
juyowa yayi tare da cewa Yusuf.
"room C murder 160, baturen yana jin haka yaje ya bud'e motar ya d'auko jakar Aryan d'in yayi hanyar d'akin inda wani d'an matashi kuma yabi bayan Aryan yana yi mai magana ina kayanshi zai kai mishi,
baturen na ganinshi ya mik'a mishi jakar, sannan sukaci gaba da tafiya, sunyi tafiya mai d'an nisa kad'an suka riski d'akin.
One bedroom ne sai kitchen insu a manne a wurin sai d'an wani wuri da yafi kama da parlour dan an k'awatashi da kujeru ga fulawowi sai d'an masakaicin dinning area wanda kamar glass ne katangar wurin, k'asan kuma anyi mishi dab'e da katakon k'asashen waje, cikin bedroom en kuwa komai akwai kama daga tv fridge da gadaje biyu masu kyau durowa ma biyu toilet ensu babba mai kyau,
a wojen su kuwa can gefe kad'an dasu kuma ruwa ke tsatstsafowa ta jikin dutsen,
wuri dai yayi kyau sosai
nan suka taya Aryan ya shirya komainshi wannan d'an matashin ya gabatar da kanshi a matsayin shike yiwa duk sabbin students yan aikace-aikacensu da yan aikensu kamarsu wanki da guga da share musu d'aki da kitchen ana d'an biyanshi mutsabbai.

Shima Aryan sake bin Yusuf yayi har bakin mota, ganin yana k'ok'arin shiga yasa Yusuf cewa.
"Aryan bazaka hutaba."
kai ya jinjina cikin jin kewar zasu d'an rabu na wani d'an lokaci har tsawon shekara yace.
"Hutu kuma kamar wanda yazo da k'afa, kuma yama zanyi in huta banje naga makarantarku ba naga masauk'inka ai bazai yiwuba."
kai ya jinjina tare da cewa.
"OK muje."


Daga nan makarantarsu Aryan zuwa Jurassic Park polo tafiya ce mai zaman kanta,
shiyasa suka d'anyi kusan 25 minutes suna tafiya,
dai-dai sanda motar ta kusa kanta cikin jami'ar polo wani irin zabura Aryan yayi gani wani abu kamar a mafarki, daga bakin gate d'in ya ishi mazaunin birnin taraiya abuja kallo in yaje,
duk tsaruwa da kyawun university of Cape Town, sai da Jurassic Park polo ta tafi da nitsuwarsu Aryan , ko dan shi private school ne mai zaman kanshi wanda kuma 'yayan manyane da k'usoshin gwamnati ke ciki inda ko wacce k'asa na kawo shahararrun yan tserensu dan sama musu ink'antacciyar horaswa,
Aryan kam sakin baki yayi ganin irin yadda aka shek'e wuyan dollars aka dannesu a cikin filin,
gaba d'aya makarantar kan kogi take yayinda ruwane yayi mata k'awanya sai tsaunuka da fulawowi kamar a k'asar India, wasu irin shahararrun tituna ne masu zaman kansu, daga farfajiyar wurin in ka wulga ida nunka ba abinda zaka gani sai beneye masu tsananin kyau da shek'i sai hasken gilasai can gefen dama kuwa wani irin k'aton filine da manyan rufuna inda wurin yafi kama da forens sai dawakai da suke shimfid'e a wurin iya ganinka,
murmushi mai fad'i Yusuf yayi ganin ababen sonshi dawakai dirka-dirka dasu k'osassu sai shek'i sukeyi,
can hannun hagu kuma wurine da yafi kama da wurin shak'atawa sai dai da alama wurin kamar kasuwace da kuma dan cikar wurin, can gefe kuma da suka juya wani k'aton bene ne da aka rubuta Jurassic Park theme polo hospital ,
k'asan illahirin farfajiyar makarantar kuwa anyi mata dab'ene da glass mai tsananin k'arfi da shek'i wanda sanad'in haka kana iya ganin duk mutsin ruwan da halittun dake cikin in sunyiyo sama suna mink'aya
ajiyan zuciya sukayi ganin direban ya nufi can,
cikin zumud'i suka fito tun bai k'arisa yin parking ba, jakar Yusuf d'in ya d'auko tare da cewa su biyoshi, dan su direbobin sune kuma suke yi musu komai shiyasa wurin yake cike da motocin duk ko wanne an rubuta Jurassic Park polo car suma hukumar makarantarce take biyansu sukewa students d'in komai kama daga wonki guga share-share da kad'e-kad'e da aikensu duk inda suke buk'ata,
shiyasa kai tsaye ya dauki jakar Yusuf kuma dama key d'in d'akin Yusuf d'in yana hannunsa tunda hukumar makarantar ta san da zuwansa kuma an biya mishi makudan kud'in da ake biyawa ko wanne d'alibi shiyasa komanshi yake intak kasancewar yana da babban jigo, malam Jabeer tuni yasa an gama mishi komai.

Su dai kam Aryan da Yusuf binshi a baya kawai sukeyi, wani babban holl ya shiga inda suka bishi a baya,
ai cikin sauri Yusuf yasa hannunshi cikin aljihun wondonshi dan jin wani irin fitinennen sanyi dake ratsashi,
lifter suka hau irin mai steps d'in nan,
sosai Aryan ke baza ido,
shi kuwa Yusuf kallon komai na wurin yake yana mamakin komai na wurin yanada tamb'arin doki da sunan makarantar,
kutsawa yayi tayi dasu cikin kyawawan benayen glasses d'in har suka isa wani d'an hanya suna shan kona suka fara hango asalin farfajiyar makarantar da illahirin birnin da kogin dake shimfid'e k'asan makarantar, k'asan farfajiyar kuwa da glass mai k'arfi akayi mishi k'awanya inda aka jera kujerun zama
sai hada-hadar ababen hawa,
a bakin wani k'ofa ya tsaya tare da sa key d'in daya zaro a aljihunshi ya bud'e k'ofar sannan ya shiga tare da cewa su shigo,
ajiyan zuciya suka sauk'e da suka shiga wani irin tamfatsetsen parlour ne mai cike da kujeru ga k'aton tv and fridge sai dinning table mai kujeru shida, sai 3 bedroom with bathroom parlour yana zagaye da wasu manyan labulaye kyawawa masu kauri,
kai tsaye ya nufi bedroom d'in dake tsakiyan corridor d'in key yasa ya bud'e sannan suka shiga, nanma d'aki ne mai samawa mazaunin cikinsa salama da nitsuwa komai yana nan intak lafiyeyyen gado da durowa sai d'an madaidaicin tv da d'an k'aramin fridge durowar kawai abin ganine cikin zumud'i Aryan ya bud'e, murmushi yayi tare da cewa.
"Wow Yusuf kalli harda Polo ball and polo stick with polo boots and leans with shirts, komai naka a shirye kai anci gaba anan."
hannu yasa ya zaro riga d'aya cikin rugunar yace.
"Tab,! kalli komai da sunanka dana Team d'inmu, gaskiya makarantar nan ta had'u."
murmushin yayi tare da cewa.
"Ba yadda anyi da kaiba muyi tare tunda dudu in one year d'ai mun gama, kace min ina kai low kake mararin kaga ka fara kabtawa."
zama yayi kan 2 seeter dake gaban gadon sannan ya d'ora k'afafunshi kan stool dake tsakiyar gadon da kujerar,
yace.
"Hmmm Yusuf kafa sani ni bani ma da ra'ayin polo kusan kai kasani nake dan gwadawa, bani da buri daya wuce inga yau na zama lawyer mai kare hakk'in mata da k'wata musu encinsu."
Kai Yusuf ya jinjina tare da fara rege kayan jikinshi, dan tuni driven nashi ya fita samo musu abinda zasuci,
bud'e k'ofar toilet d'in yayi tare da shiga,
samun komai a ciki kama daga soso sabulu makilin burosh towel komai sabo dal yana cikin ledarsa hakane ya sashi k'arisa cire kayansa,
wanka yayi mai rai da lafiya yana fitowa,
yaje gaban dressing mirror ya fara tsane jikinshi sannan ya shafa mai turare ya fesa sauri-sauri dan jiyo muryan Aryan a parlour yana kwab'a hausar sokotawa,
riga da wondon polo da aka cika mai durowa dusu ya dauki d'aya ya saka sannan ya nufi parlour.

Aryan ya samu zaune bisa sofa sai wasu matasa su biyu d'aya balarabe d'aya ba haushe,yaga sunayensu sanadnn rigunan dake jikinsu na polo d'in na balaraben ansa saudia polo team sai k'asan kuma akasa Abdulkareem 2 sai ba haushen kuma ansa Nigerian polo team
Sultan 4 ,
murmushi Aryan yayi tare da nuna musu inda Yusuf yake,
a tare suka juya cikin sakin fuska suka nufeshi har suna had'a baki cewa.
"Yusuf 1 team Jahan ko?."
hannu ya mik'a musu fuska d'auke da murmushi suka gaisa yana mamakin yadda balaben nan ya iya hausa, hausarma kuma ta sokotawa,
sai kuma ya bar mamakin jin yadda wannan basokkocen yakeda dan banzan surutu sai zuba yakeyi kamar carbin daya tsinke bisa tayis,
tsakiyar parlour suka koma wasu kan sofa wasu bisa carpet cikin farau-farau basokkocen nan ya kalli Yusuf yace.
"Kai baAdamawe zancema ko bayole, ni dai basokkoce ne, ba kuma balarebe, ganan d'akinmu mu mun kusa shekara da zuwa Jurassic da yake mu daga hawa doki muka fara shekara biyu zamuyi kafin mu gama."
Yusuf kam sai murmushi yake jin wannan sokotancin, bare kasancewarshi ba fullatani ba fullataninma bayole ,so kunsan hausa kanta wani sabon abu mukejinta, Aryan kuwa ya zage ala a dole sai ya koma basokkoce, Abdulkareem kam shi tuni ya d'an iya, shi kuwa Yusuf dad'i yakeji a ransa daya samu musulmai yan uwansa ne mak'otanshi, cikin yin murmushi yace.
"kirani bayole."
Abdulkareem ne ya amshe maganar da cewa
"Ko dai Baraden Nigerian."
Aryan ne ya mik'a mai hannu suka tafa tare da cewa.
"Kaji hausafa wannan balaraben wato har ka fahimci zancen da nayi muku na shine baraden Adamawa."
Sultan basokocen ne yace.
"Yoh ai dole yasan Baraden Adamawa tunda duk yana ganin komai naku a facebook page naku da instagram yana kuma ganin videos naku a YouTube channel d'inku."
sosai suka sake da juna suke d'an hirarsu, akan abinda ya shafi harkartasu yayinda suke k'ara yiwa Yusuf bayanin komai akan makarantar nan Sultan yake shaida mishi matsayin Arsar direbansu ne kuma d'an aikinsu da aikensu, duk abinda yake buk'ata ya kirashi a waye, sannan ya bashi number shi,
anan sukayi sallah magrib da isha, sannan Abdulkareem ya kira musu Arsar yazo ya d'aukesu dan ya kaisu filin cin abincinsu, suyi dinner in sun gama ya d'aukesu d'an zaga gari sannan su maida Aryan makarantarsu.

Lokacin da suka isa wurin cikin abincin nasu, anan kallo ya sake bud'uwa ga Aryan wurine na gani na fad'a babu k'asar da za'a kira a duniyar nan ace ba mutuminta a wannan wurin, shiyasa suke girka ire-iren abincin ko wacce k'asa , iya had'uwa Jurassic ta had'u nan sukaci abinci kowa yaci abinda ransa keso, sannnan suka shiga zagaye cikin makarantar, sai misalin 11:00 pm suka meda Aryan har d'akinshi sannnan suka dawo gida.


Washe gari suna idar da salla asuba, Abudukareem ya lek'o d'akin Yusuf ganinshi yana zaune yana karatun qura'an ya sashi komawa d'akinshi,
bayan yan mintuna talatin Sultan ya shigo tare da sallama, hannu ya mik'a mishi suka gaisa sannan yace.
"Ka hanzarta shiryawa cikin shigar polo, yanzu zamu sauk'a k'asa dan yau shugaban makarantar zai zo yin bayani gareku sabbin d'auka da kuma mu da zamu tafi tare daku,
sannan za'a fara nuna mana tsare-tsare da dokokin aikin da zamu fara."
"Toh ganin nan fitowa."
yace tare da mik'ewa ya fara shiri,
shi kuwa Sultan ya koma parlour wurin Abdulkareem suka zauna suna jiranshi.

Shi kuwa Yusuf irin shigar da yaga sultan yayi shima shi yayi sai dai babbancin color
rigar polo ce yellow ya saka sai ratsin rubutu da akayi da red color inda aka rubuta Nigerian polo 2015
a k'asa kuma akasa hajan team a gabanshi kuwa aka rubuta Yusuf 1 , sai wondonshi red color, sai danarshi yellow sai takalma shi na boot suma yellow, sosai kalar tayi mishi kyau ya fito kamar balarabe,
polo stick with polo ball d'inshi ya d'auka sannan ya fito,
"Wow gaskiya bayole shigar polo tana matuk'ar yima kyau."
Cewar Sultan lokacin da suke fita.


Gaba d'aya students maza da mata na Jurassic Park polo sabbin zuwa da masu tafiya next level suna hallare a babban filinsu da yake tsuburine
sai tsirrai da bishiyoyi da farin yashi sannan da ciyayi masu laushi da sukayiwa wurin k'awanya ga taron dawakai masu yawan adadin daliban,
jawabi sosai shugaban makarantar yayi musu, tare da zaburar dasu, ya kuma shaida musu yana alfahari dasu yana kuma fata da farin ciki ace d'aya daga cikin d'aliban Jurassic yazo na d'aya a gasar polo ta duniya baki d'aya, shi bawai sai d'an k'asarsa yakewa fataba shi duk d'alibin Jurassic Park polo to ya zama nashi.

Sosai ya zaburar dasu tare da k'arfafa musu guiwa, ya kuma musu nasiha sosai,
sannan sauran duk Malamansu suka fito aka gabatar dasu,
sannan aka fara rarraba musu wuraren da kowa zai fara d'aukar darasin,
komai daki-daki yake inma kana so daga yadda mutun zai fara koyan hawan doki da rik'e linzamin.

Haka dai suka shiga cikin abinda ya kawosu gadan-gadan komai yana tafiya dai-dai da tsarin zamani, Yusuf ya meda kai da hankali baki d'aya kan abinda ya kawoshi k'asar inda yake Allah-Allah ya gama one year d'in da zaiyi a Jurassic ya koma can university of Cape Town inda Aryan yake suci gaba da karatunsu duk da yasan Aryan zai tsere mishi da shekara d'aya,.

Can a b'ank'aren Aryan shima ya maida hankali kan karatunshi.


Mama kuwa da Abba sunyi umransu lfy, yayinda duk motsin Mama Addu'a da fatan shiriya da albarka take nema Yusuf d'inta da dukkan yan uwa musulmai,
sunyi satinsu biyu a saudia sannan daga nan suka ratsa Dubai inda Abba ya zage yake sabunta soyayyarsa don samawa matarsa nitsuwa ya kuma cire mata kewar Yusuf,
Alhamdulillah ita kuwa Mama yanzu ta sadakar ta hak'ura ta dena tasashi gaba tana mishi kuka da magiya kan Yusuf, tunda tasan yanzu baya Nigeria kuma ko ta dawo bazata ganshiba so sai kawai take ji da ganin kamar ba abinda ya faru kawai ya tafi karatune sai take gani kamar daga gida ya tafi.


Tafe suke rik'e da polo stick d'insu suna kad'a polo ball d'in da Yusuf ya cilla musu tsakiyarsu,
saida suka hau lifter suka bar kadata, yayinda Sultan ke rik'e da wayarsa yanata kashe musu selfie duk motsinda sukayi, Yusuf yayi kyau sosai cikin shigarsu ta polo riga pink da ratsin farin rubutu sai pink bandana wond'o fari tare da farin takalmin boot, sosai yayi kyau gashin kanshi ya konto kan bandanan,
Cikin tsuke fuska Yusuf ya juyo tare da cewa.
"Kaifa banza ne Sultan me haka kullum kayi ta addabarmu da d'auke-d'auken hoto kamar wasu mata ko birirrukan gidan gona."
Cikin wasa Abdul-kareem ya matso tsakiyarsu yayinda k'aton tambarin Jurassic yake bayansu da dawakai zageye dasu, ga tarin turawa dake bayan tambarin,
murmushi Yusuf yayi ganin yadda Abdul-kareem ke kallonshi,
shi kuwa Sultan da sauri yace.
"Yauwa tsaya-tsaya kai wannan hoton yayi kyau."
shi kam Yusuf sharesu yayi ya haura tare da shigewa d'akinshi, kai tsaye bathroom ya shiga wonka yayi tare da kimtsawa,
sannan ya fito parlour, nan ya samesu suma sun shirya sun fito,
Kan sofa ya zauna tare da jawo stool ya mik'e k'afafunshi a kai, sannan ya d'aura laptop d'in kan cinyarshi yayinda ya aje woyoyinshi gefe,
Shima Abdul-kareem laptop yake dannawa,
sai Sultan maganad'isun basokkoce,
daya matso Yusuf tare da mik'amishi wayarsa cikin kula yace.
"Kalli pictures enka sunfi d'ari biyu a wayata harda wad'anda nayi ta daukarmu randa muka fara fita randa kayi shigar yellow and red color, kaga yadda sukayi kyau fa,
ga wasu kana kan doki wasu kana cikin yahudawannan ga yadda ka saje dasu, wasu kana cikin tsuburin can, kalli wani inda shugan makarantar ke baka takardun ka na zama cikekken dalibin Jurassic, in an ganka dashi za'ace kaima farar fatace."
karb'ar wayar Yusuf yayi tare da kallon pictures d'inshi daki-daki ba k'arya sunyi kyau, murmushi yayi tare da cewa.
"Dan Allah na tub'a."
da sauri Abdul-kareem yace.
"A kan me?."
cikin dan sakin fuska yace.
"Yoh tsoro nakeji kar wata ran ya bini bathroom ya d'aukeni, dan naga aljanin d'auke-d'auken hotone gareshi."
Dariya sukayi baki d'aya sannan a take Sultan d'in ya turawa Aryan hotunan, aiko shiko yana gani ya hau yanar gizo-gizo ya turasu duk inda suke da page.

suna zaune a wurin wayar Yusuf tayi ringing da sauri ya d'aga ganin Malam Jabeer ke kiranshi yana d'agawa yace.
"iyeh Masha Allah Yusuf ya zama balarebe irin wannan kyau haka." cikin jin kunya yace.
"Malam barka da yamma."
dariya ya d'anyi tare da cewa.
"Barka dai Yusuf, abu yayi kyau naga pictures naka duk sun nuna alamun kana abinda ya kaika, kuma dan Allah ka k'ara kula ka rik'e mutuncinka ka kare martabar addininka."
cikin jin dad'in nasihar yace.
"In sha Allah zan kula Ngd matuka Allah ya k'ara girma."
"Amin Amin."
yace tare da katse kiran,
yana ajiye wayar Aryan ya kirashi yana d'aga sai cewa yayi.
"Baraden Adamawa dan Allah lek'a facebook page naka and instagram da YouTube channel d'inka."
tsaki yaja yace.
"OK wayasa pictures na?."
"Ni nan Aryan na saka dan d'azun nan Sultan ya turomin su, love kana da maga ne a kai, banza mai nuk'u-nuk'u."
dariya yayi dan jin k'arfin halin Aryan, katse kiran yayi tare da lek'a social media, yasha mamin dubban masoyan da suke k'aruwar masa a kullum, Allah ya godewa dan ai jama'a rahamace.

Satinsu Mama d'aya a Dubai suka dawo Nigeria,
ranar da zasu dawo tun safe Zulaihat tazo ita da Amira suka gyara part d'in Mama komai nit Anty Amarya kuwa ta shirya musu abinci kala-kala,
k'arfe 12 jirginsu zai sauk'a,
yayinda yaran gidan kuwa duk sun tafi makaranta sai Sulaiman da yanzu ya dawo daga Modibbo Adamawa university, dan shima tuni ya fara zuwa jami'ar, sauri-sauri ya shirya sannan ya d'auki key d'in motar da Abba ya saya mai kafin ya tafi,
Zulaihat da Amira da Zeenat sai yaron Zulaihat d'in ya d'auka suka tafi d'auko su Abba a airport.


12:35 Am su Mama suka k'araso inda su Suleiman d'in suke, da gudu Zeenat da Amira sukaje suka rungume Mama shiko Sulaiman jakar hannun Abba ya karb'a tare da rusunawa ya gaidashi, Zulaihat kuwa sai murmushi takeyi tare da gaidasu.

Abba shida Sulaiman suna gaba ita kuwa Mama ita dasu Zeenat da Zulaihat suna baya hira sukeyi sosai.

Suna isa gida Hajja Inna, Anty Amarya, Ummi, Daddy, duk suka shigo har parlour Mama suna mata barka da dawowa lafiya,
Ranar kam wuni sukayi a parlour Mama sai salla da cin abinci yake tadasu,
6:00pm yan makaranta suka dawo nanma wani sabon hira aka dasa.

Bayan sallan isha duk suna cike a parlour Zahra na gefen Mama tana shan ruwan zam-zam da cin dibino, saura kowa na sungullarsa kowa ga tsarabarsa duk suna cikin nishad'i, sai Abba da Daddy take can parlour bak'i inda ake zuwa musu sannu da dawowa.

Cikin happy Suleiman ya kalli Mama tare da matsota ya fara nuna musu pictures d'in Yusuf.
"Masha Allah."
sukace baki d'aya, Amira kuwa cewa take.
"Wow Sulaiman turamin su ta what's app dan Allah zan saka a status na."
dariya yayi tare da cewa.
"Wallahi Allah ko Mama ban tab'a k'aunar harkan polonnan da Yusuf yakeyi ba sai yau, ya mark'ar burgeni, amman wallahi da kullum in naga Yusuf mak'ale saman doki yana tsalle dashi tsoro ke rufeni, sai idona ya rink'a nunamin ya wurgar da Yusuf k'asa ya bi ta kanshi ya wuce amman yau ya burgeni matuk'a."
cikin jin dad'i Mama tace.
"Kirawo min shi mana tunda na tafi bamu gaisaba."

video call ya kirashi,
shi kuwa Yusuf dai-dai lokacin suna cikin babban mall dake cikin Jurassic d'in suna zab'an turarukan da mayukansu yaga kiran,
da sauri ya d'aga,
ido ya lumshe tare da sauk'e ajiyan zuciya ganin fuskar Mamanshi,
itama dariya tayi cikin jin dad'i tace.
"Babana nayi kewarka."
cikin dariya ya kamo hannun Abdul-kareem da Sultan yace.
"Hi guys ga Maman Yusuf fa."
sai ya kuma kalli fuskar wayar yace.
"Maman Yusuf, ina kewarki kullum sai na kira Daddy yace min baku dawoba, har na gaji nace ya bani number Abba ta can, daga nan kullum sai na kira Abbana naji muryarshi yana sallama sai inyi shiru, dan nasan in ya gane nine zai iya yin komai."
sai ya kuma kauda mgnar ganin fuskar Mama ta fara canzawa I zuwa k'unci cikin sauri yace.
"i really miss you sweet Mama."
murmushi tayi tare da samishi albarka tare da tambayarsa su waye wad'annan.
"Abokai nane Mama."
suma murmishi sukayi mata tare da gaidata,
suma albarka tasa musu,
sai kuma duk su Anty Amarya suka dawo bayan Mama yadda duk zasu ganshi zai gansu, sai Zahra kawai da tuni ta b'ink'ire tayi bacci.

Hira sukeyi sosai yayinda suke d'an zagayawa har suka gama tsintar abinda sukeso suka koma gida, hakan yasa su Mama sukaga inda yake rayuwa Amirace ta kalleshi tare da tab'e baki tace.
"Hege Yusuf ka samu duniya kallifa yanzu ka fini fari."
hararta yayi cikin tsigar yar tsamarsu da sukeyi yace.
"Harda kyauma duk na fiki ai mummunar gidanmu mai k'aton goshi kawai."
baki ta tura tare da cewa.
"Mama kin jishi ko? wato har a gaban abokanshi sai yace min mai k'aton goshi."
Suleiman ne yayi saurin cewa.
"To k'arya yayi?."
duka ta kaimai cikin tsuke fuska tace.
"Oho dai duk da haka nice babba dani akeji shekara biyu cur nake baku."
dariya Yusuf yayi tare da cewa.
"Toh a gwada tsawo mana, kina nan kamar wada kuma kin manta Sulaiman kike bawa shekara biyu cur, ni dai bai cika biyu kika baniba d'aya da rabine."
sosai suke dariya Sulaiman har da mata gwalo,
Ummi kuwa cewa tayi.
"Kai yaran nan kun raina Anty Amiran nanfa da yawa."
Anty Amarya kuwa cewa Yusuf tayi.
"Yusuf Tattina tace tayi fushi da kai kafin ka tafi bakaje kunyi sallama ba."
"Oh my Tattile Anty turomin number ta in kirata in lallashi yar tsohuwa."
dariya tayi tace.
"kaima Mamarka yar tsohuwa."
haka sukayi ta hira ita kam Mama sai dariya da samusu albarka takeyi,
su Mami da Nana, Jafar, Ibrahim, Sadik, kuwa sai tambayarsa suke yaushe zai dawo, in zai dawofa ya kawo musu tsaraba, basu bar wayarba saida kud'in Sulaiman suka k'are sannan Yusuf d'in ya kira shima saida kud'inshi ya k'are.

bayan dawowarsu da kwana Biyu Hajia Kaka da Raihana sukazo sukayiwa Mama sannu da dawo dan tun randa ta dawo Yusuf ya gaya mata kuma shiyasa Sulaiman yaje ya kawosu kuma ya meyardasu,
k'annen Abba ma da family baki d'aya sunzo musu sannu da dawowa.


***************

Haka rayuwa tayi ta juyawa tana tafiya, Yusuf karatu yayi nisa haka nan Aryan da Sulaiman,
shak'uwa da zaman amana Sultan da Abdul-kareem sukeyi da Yusuf.

Rayuwar Zahra kuma da telen shagon idi tafiyar bata sauya zaniba,
dan shima telan d'an iska ne, kullum yana janta da k'ellayen da take zuwa karb'a wai zata d'inkawa Babynta, sannan yakan sayi sweet da cakuleti dominta,
Anty Amarya kuma ko a jikinta,
kai tsaye Zahra kan ce mata bari taje shagon tela karban kayan Babynta,
sai tace.
"To maza jeki da gudu karki dad'e ko Tinana."
shi kuwa tana zuwa sai ya d'aurata kan cinyarshi wai zai koya mata taka keke, ita kuwa tayi ta murna zata d'inke kayan Babynta da haka yake d'an lallatseta.

Haka dai rayuwa ke shud'ewa kullum telan nan fatanshi ya samu dama kadaicewa da ita a layin ya samu gamsuwa da ita.


*South Africa*
Lokaci yaja yanzu Yusuf ya kusa wata 9 da shiga Jurassic Park polo, tuni sun shiga zongon k'arshe kullum suna cikin d'aukar darusa.


Ranar wata Asabar,
Haka nan yau Yusuf ya tashi jiki a mace dan wani mafarkin da yayi,
so kasancewar weekend ne yasashi komawa ya konta tare da rufuwa da blanket,
a hakali ya fara jin ciwon mararsa na kartarshi jikinshi sai k'ara macewa yakeyi yayinda zuciyarshi ke k'ara tsinkewa tana duka uku-uku.


*Girei Adamawa Yola Nigeria*

kasan cewar yau asabarne weekend yasa garin shiru kowa na cikin gida ga yanayin sanyin huturu da aka fara,
Zahra kuwa da yake an basu hutun maulidin da za'ayi a makarantarsu yasa yau tana gida,
tana tashi kitchen ta nufa inda Ummi ke aikin breakfast,
tana zuwa tace.
"Ummi zansha tea."
"To." tace tare da had'a mata tea mai kauri ta bata tasha tana gama shanyewa ta wurgar da cup d'in ta fita a guje,
cikin d'aga murya Ummi tace.
"Ke Zahra ina zakije!?."
ba tare da ta juyoba tace.
"Parlour Hajja Inna zanje."

tana fita madadin taje inda tace zata jed'in sai kawai ta nufi gate, cikin sa'a ta fita bataci karo da kowa ba,
kai tsaye shagon tela ta nufa,
inda ta sameshi shi kuwa yayi sammako ya fito dan yin d'inkin anko d'in 'yan maulidi.

Yana ganita ya washe baki tare da mik'ewa tsaye ya kunce tazugenshi sannan ya koma ya zauna,
ita kuwa da sauri ta shigo har yasa hannu ya d'agota sai ya kuma ajiyeta tare da cewa.
"Jeki

Please Login or Register in order to submit comment