Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suna shiga parlour Mama kiran Yusuf na shiga wayar Jafar.

Shi kuwa Aryan da gudu ya isa inda Zahra ke zaune cikin sanyi da alamun rauni ya fara kici-kicin kwab'e rigarshi tare da cewa.
"Ammi kalli bayana, Bappa Njangirde ya dakeni, yace wai ni najasace wai mahaifina d'an iska ne."
jawoshi tayi tare da d'aga rigarshi,
shi kuwa Jafar amsa kiran yayi tare da matsowa kusa dasu ta yadda Yusuf zaiji me suke fad'i,
itako Zahra tuni hawaye sun cika mata ido cikin muryar kuka tare da rauni tace.
"Allah zai saka maka, kuma mahaifinka ba d'an iska bane, kai kuma ba najasa bane."
sai ta kuma saki kuka mai rauni tare da cewa.
"Kowa sai ya rink'a jifarshi da kalmar d'an iska,
al'halin babu tsohon da zaice ya b'ata mishi yarshi,
ina dai ni yayiwa kuma ni na sani ba d'an iska bane Daddy na ma ya shaida shi ba d'an iska bane,
ina dalili dan k'addara ta fad'a kanmu zasuyi ta zaginshi,
gashi sun sashi ya shiga uwa duniya ya barmu cikin k'uncin rayuwa,
yayinda bamu san shima wacce iriyar k'una yake jiba."
cikin sanyi Aryan d'in yasa tafin hannunshi yana share mata hawaye tare da cewa.
"Ammi yau in mahaifina yazo min a mafarki zan ce mishi yazo ya d'aukemu mu tafi mu bar gidannan ko?."
d'agoshi tayi gaba d'aya ta ruggumeshi tare da cewa.
Y...!








By
*GARKUWAR FULANI*

Sbpwl


HUKINCIN ALLAH

PAGE 10






"Ya isa haka, kayi hak'uri kaji ko babana?."
kai ya gyad'a mata tare dasa tafin hannunshi ya share hawayenshi,
sannan ya zame daga gareta yayi wurin Mama data zuba musu ido cikin tausayawa.
gaba d'aya shiru sukayi kowa da abinda ke ranshi.
Shi kuwa Jafar ya nitsu yana jin Yusuf cikin sanyi da tausayin Aryan yace.
"Zan zo zan d'auke shi ya bar k'asar gaba d'aya,
domin na lura mutane suna mance shariyar musulunci suna bin son zuciya,
har zasu kirashi najasa ko a ina sukaji ance d'anda aka samar ta hangar da ba'ayi aureba shi najasa ne,
In sha Allah zan zo nan kusa zan d'aukeshi ya huta da izayar azzalumai."
cikin tsananin jin dad'i Jafar yace.
"Gskya kam gwara ka zo d'in domin abin gaba-gaba yakeyi."
shi kuwa Jafar da Affan dama yanzu burinsu kawai Yusuf ya dawo shiyasa Affan yake janshi da cewar Mama ba Lfy,
so ya k'ira Jafar yaji ya jikin nata sai ya kuma ci karo da abinda akewa Aryan,
gaba d'aya sai hankalinshi ya tashi duk tunaninshi ya dawo gida.

Mama kuwa ido ta zubawa Jafar cikin kula tace,
"Anjima ina son mgna da kai."
kai ya rutsunar tare da cewa.
"Toh."

Shi kuwa Yusuf bayan ya katse kiran Affan ya kuma kira,
lokacin suna zaune a parlour shida Mami na konce tayi pillow da cinyoyin Affan d'in yayinda Asina kuwa ke gefensu tana ta rarrafenta,
tattaunawa sukeyi a kan batun Zahra ita Mami tana son Safwan ko dan yace ya amince zai auri Zahra duk da tabon dake tare da ita,
shi kuwa Affan yanada nashi burin da fata,
duk da yasan babu haka a zuciyar Yusuf,
jin tanata mgna bai tanka mata bane ya sata mik'ewa zaune tare da meda hankalinta kanshi cikin sanyi tace.
"Lafiya kuwa inata mgna kayi shiru."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Toh me zan ce miki,
ni dai na sani Safwan bai dace da Zahra ba,
shiyasa ban ji zafin Hajia yabi ba,
don ni dad'intama naji data hana abin,
nasha gaya miki komai lokaci ne ki kontar da hankalinki Zahra zatayi aure,
kamar yau itama zatayi farin ciki."
kai ta d'an jinjina tare da cewa.
"Toh Allah ya nuna mana,
amman Abban Asi kafa sani bata da ma nemi ko d'aya,
hasalima ko mutun ya fara zuwa gunta in yaji abinda ya faru sai ya bari kagafa,
Zeenat k'anwar bayanta ma an aurar da ita."
jawota yayi jikinshi ganin alamun rauni da karaya tuni ida nunta sun cicciko da hawaye,
cikin yak'ini yace.
"Karkiyi kuka kiyi mata addu'a domin dukkan tsanani yana tare da sauk'i in sha Allah wata rana sai labari."
kai ta manna a kafad'arshi tare da lumshe idonta.
ya bud'i baki da niyar yin mgn kenan,
sai ya kumayi shiru tare da jawo wayarshi data fara ringing,
ganin Girei,
Yusuf kenan domin yanzu shine inkiyarshi a duniyar shahara tuni ya watsar da Baraden Adamawa,
yana amsa kiran ya juya harshe zuwa larabci duk da bai wani iya sosaiba,
ganin haka sai Mami tayi zaton ko wani sirrinashi na dabanne ko abinda ya shafi masarautarsu ne,
shiyasa baya buk'atan taji,
dan haka ta mik'e tare da d'aukan Asina tayi bedroom don yi mata shirin bacci.
shi kuwa Affan ganin ta tafi ya sauk'e numfashi tare da gyara zama da murya yace.
"Eh ina jinka."
a can sashin Yusuf kuwa zaune yake cikin shigar k'anan kaya bisa dukkan alamu yanzu ya shigo gida,
dan da alamar gajiya tare dashi,
wayar yakeyi laptop nashi kuma yana gabanshi,
a nan gida Nigeria ma,
shima Affan laptop d'in ya jawo tare da bud'eshi,
cikin gajiya Yusuf ya d'an gyara zama tare da cewa.
"D'azun nayi mgna da Sultan ya gama had'a sunayen teams da muke dasu a Nigeria bak'i d'aya,
ya kuma yi min k'arin bayani akan irin tainakon daya dace a musu."
gyara zama Affan yayi tare da cewa.
"Eh lallai munyi mgnar dashi,
ya kuma cemin,
wai harda masarautun k'asar kasa a cikin kyautar."
Kai ya jinjina mishi tamkar yana gabanshi,
gane bazaiyi mgna bane yasa Affan yin d'an tsaki tare da cewa.
"Wai kai wanne irin mutun ne kam,
bafa ganinka nakeyi ba,
so ka dena min boddy language d'inannan ka."
tab'e baki yayi tare da jan gajeren tsaki murya can k'asa yace.
"Anyi d'in."
dariya Affan yayi tare da cewa.
"Toh ci gaba."
zamanshi ya gyara tare da cewa.
" Yaufa tunda gari ya waye ban dawo gidaba sai yanzu,
ga zirga-zirgan da shirye-shiryen zuwa gida,
ga yawan practical da mukeyi a kan gasar nan da za'ayi,
dan ma an d'an k'ara kwana kine da gobene za'ayi."
sai ya kuma ci gaba da cewa.
"Sultan yace teams 47 muke dasu a fad'in k'asarmu ,
yace 27 na arewa ne yayinda 20 kuma na kudu ne,
yace akwai wad'anda basu da safitiken,
to su na sama musu,
sannan ko wanne team za'a basu dawa kai 25.
sai kofunan da za'a had'a musu,
sannan kuma,
ko wanne team an had'awa yan cikinta sabbin uniform kala bibbiyu,
an kuma fad'ad'a abun."
shi kam Affan kai kawai yake gyad'awa tare da cewa.
"Hakan yayi."
A can cikin zuciyarshi kuwa tunani yake,
kan tsarkakan zuciyar Yusuf,
dubi miliyoyin da ya ware zai kashesu wa k'asarshi data tozartashi,
yana sane lokacin da abin nan ya faru dashi duk teams d'in babu team d'aya da yazo ya nuna tausayinshi gareshi ko kulawa ko kareshi,
muryar Yusuf ce ta katse mishi tunani.
"Kana ji ko?."
gyaran murya yayi tare da cewa.
"Eh ina jinka."
jin haka Yusuf d'in yaci gaba da cewa.
"An gama ginin filin polo na kaduna Kano Adamawa Lagos da kuma ginin masallacin jummar da akayi a Girei,
amman shi sai next two weeks za'a bud'eshi kafin nan na dawo,
sai kuma masarautun mu,
gaba d'aya za'a basu dawakai talatin-talatin masarautun arewa kenan,
na kudu kuma za'a basu shabiyar-biyar,
sai fad'ar shugaban k'asa ta'a basu dawa kai 200
sannan masarautarmu."
murmushi Affan yayi domin yasan in Yusuf yace masarautarmu to yana nufin Adamawa kenan,
kai ya jinjina tare da cewa.
"Oh ni babu ruwana kaida uban gidanka M Jabeer,
in kaga dama ka bashi ranka ma wannan ya rage naka,
tunda ka mance ya gujeka lokacin da kake tsananin son makusanta,
ni babu ruwana da batun masarautar."
cikin murmushi Yusuf ya gyad'a kai domin yasan Affan yana son Hamma Jabeer d'inshi kamar ranshi amman kuma yana nuna kawaici wai sabida kar Yusuf d'in yayi tunanin yanada son kai,
ya kuma san yana son ci gaban masarautarsu,
hakan yasa darajarshi k'aruwa a idon Yusuf cikin kula da salon wasa yaci gaba da cewa.
"Yoh ai shiyasa nace masarautarmu, sabida nasan yanzu kai d'an adawarmu ne."
shima Affan cikin wasa yace.
"Na yarda."
dariya sukayi baki d'aya sannan Yusuf yaci gaba da cewa.
"Masarautarmu itama dawakai 100 ne nata,
sai 50 da zasu rarrabawa k'ananun masarauta,
sai masarautarsu Safwan masarautar Jimeta kenan suma za'a basu dawakai 10."
cikin tab'e baki Affan yace.
"Oh ni dai bana hana mutun yin al'khairi,
amman kuma bazanwa mak'iyana kyauta ba."
murmushi Yusuf ya kumayi dan yasan hakane bazai hanashi yiwa kowa al'khairiba amman bai so yayiwa su Safwan wani al'khairin ba,
numfashi ya d'an furzar tare da cewa.
"An kuma gama d'iban d'alibai a makaranta *YUSRAH*."
da sauri Affan yace.
"Nawa ne school fees?."
kai ya jinjina tare da cewa .
"Hmmmm baza'a biya ko asi ba kyauta ne har sai randa Aryan ya gama primary,
sannan za'a fara biya."
kai Affan ya jinjina tare da gamsuwa cikin sauk'e numfashi yace.
"Hakan yayi dama ina son canzawa Aryan makaranta ko dan wannan yaro Salim dan Atynsun nan,
kaga abi yazo da sauk'i."
lips enshi ya d'an taune kana yaci gaba da cewa.
"Kawai ka bada dama a fara rarraba dawakan da uniform na teams d'in,
sannan ko wacce masarauta a had'a musu da kud'in abincin dawa kan,
wannan ka bada yadda kaga ya dace,
ni yanzu ban fiye zamaba so duk abinda ya dace kayi,
akwai kuma motoci guda 10 suna hanya ina kyautata zaton zuwa jibi sun isa,
ka adanasu."
mik'ewa Affan yayi tare da cewa.
"Toh Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a."
Amin Amin yace tare da katse kiran,
ruwa ya d'an watsa sannan ya d'anci abincin daya shigo dashi,
karatu ya d'anyi kafin ya konta.


Affan kuwa da Sultan tuni sun bada damar raba dawa kan yayinda ko wacce masarauta ta yaba da nagartar Yusuf,
Polo teams na k'asar kuma jin Yusuf sukeyi tamkar wani tsagi na jikkunansu ne,
wasu State da dama dake kusa da Abuja yan teams d'insu a kan dawa kansu suka kokkoma garuruwansu
kamar yan Jos kaduna da Nasarawa lafiya,
yan nesa kuma sai abinda manyan motoci sukayi,
nan kallo ya koma sama inda ake ganin sabbin samfurin tireloli wad'anda keda tambarin Polo sai harufan Y M U a k'arshe kuma a saka Girei da tambarin doki a jiki,
masha,
ma'ana Yusuf Muhammad Usman Girei kenan,
lokaci d'aya ko wanne lungu da sak'o na k'asar Nigeria ta shaida,
ihsanin Yusuf ga k'asarsa mu samman matasa da kusan abin yafi raja'a kansu domin a cewarsa matasane tushen al'umma in sun gyaru to al'umma ta gyaru,
shiyasa ya ware kud'e na musamman domin matasa.

Ko ina ka gifta zaka tsinkayi ihsanin Yusuf kidajen radio da jaridu da TV kuwa ko ina sunashi ake kira,
ana ta kuma bibiyar Affan da Sultan da Jafar dan jin shin yaushenene Yusuf zai shigo k'asarshi ta haihuwa Affan dai baya ko sauraronsu hakama Sultan sai Jafar ne yayi k'ok'arin amsa tambayar Matawalle da cewa.
nan bada jimawa ba zasu shaida musu.

Tofa zo kaga ko wanne team yadda suketa neman kusanci dasu Jafar ko sa samu shiga wurin Yusuf.


Wai ko ina Aryan babba da Sulaiman suka shigane.
Maji ma gani dai


Alhamdulillah Yusuf yayi nasara a gasar world polo da akayi na 2019 inda duniya ta d'auka domin tun kafuwar Polo ba'a tab'a samun mutun d'aya da yayi nasarar cinye world polo sau biyu ba,
sai gashi Yusuf bak'in fata d'an Nigeria yayi winning world polo a karo na uku kuma a jere-a jere,
wannan abu ya girgiza duniyar turawa,
Argentina tayi shahara ta sanadin Yusuf dake jagorantar team ellistiner johor,
haka yasa sukayi zarra da fice,
duk duniyar polo suke son had'a hannu dasu,
yayinda Yusuf kuwa yace yanzu zaman kanshi yakeyi yabar Argentina domin yayi aiki dasu na tsawon shekara uku zuwa hud'u,
ba musu suka saki Yusuf domin dama America ta fara uzzura musu,
matuk'ar sukaci gaba da rik'eshi zasuyi musu zagon k'asa,
tohhh bahaushe dai yace,
wai mugu dai shi yasan makoncin mugu,
toh Argentina ko dai kuma akwai wad'anda kuka tinke ne ganin zasuyi nasara a baya.
hmmm madai ji ma kuma gani.


Alhamdulillah bayan komai ya lafa Yusuf ya tattara nashi ya nashi ya kamo hanyar k'asarshi.


Yau Jumma'a kuma yaune ranar da Yusuf zai dawo,
a tak'aicema tuni jirginshi ya sauk'a a babban birnin taraiya.
inda ya samu tarba daga fadar shugaban k'asa,
garin Abuja ta shaida Yusuf Muhammad Usman Girei ya iso,
hakama sauran jihohi,
domin madadin yawaitan motoci a fad'ar garin sai dawakai,
domin ko wanne team wakilanta sun zo tarbar Girei,
bayan an karramashi iya karramawa,
dashi akayi sallan jumma'a a masallacin fadar shugaban k'asa.
Sannan ya kuma nufi jiharshi ta haihuwa wato Adawama,
nanfa al'amari ya girmi tunanin magauta har suka sare tare da yin mubaya'a ga Yusuf,
domin dafifin dawakaine sukayi tawaga-tawaga daga Abuja zuwa adamawa domin yiwa Yusuf rakiya,
sanadin wannan lamari duniya ta cika da al'ajabi domin wannan abu daya faru ya had'u da nasarar da yayi tayin winning a world polo shakaru uku a jere,
sai ga sak'o daga majalisar wakilan shahara ta duniya inda sunan Yusuf ya samu shiga cikin world book records.


K'arfe biyar dai-dai jirginsu ya sauk'a cikin birnin Adamawa,
cikin nitsuwa da cikar haiba parssinges suka fara fitowa yayinda wasu daga ciki yan rakiyar Yusuf ne,
saida a k'alla mutun 38 suka fito sannan Yusuf ya fito.

Cikin nitsuwa da cikar haiba yake taku,
yayinda shigar da yayi ta k'ara mishi daraja da kima da cikar zati,
sanye yake cikin wani azabebben d'anyen voyel mai kalar sararin samaniya wanda yakeda azabar kyau riga da wondone tare da babbar riga malum-malum kenan ko ince gariya irin ta matasa masu mutunci,
yayinda ya kafa hular zanna mai tsunami kyau wanda aka sarrafa da surfani mai shek'in gold sai takalmin k'afarshi irin half cover d'innan suma masu kalar gold,
sai agogon hannunshi dake d'auke idanun magauta domin sai shek'i yakeyi yayinda yatsarshi ta gefen yar kurin nan yake sanye da zoben azurfa wanda wannan dottijon ne ya bashi,
shiyasa duk iya ganinka zobe a duniya baka isa kace ka tab'a ganin makamancin wannan zobenba,
zobene mai masifar kyau da d'aukan hankali,
ido ya lumshe a dai-dai lokacin da ya sako k'afarshi a kan step d'in jirgin,
hannu yasa a hankali ya shafa sajen fuskarshi daya konta yayi lib-lib dashi,
a hankali ya cusa yatsunshi cikin tattausar sumar dake konce a k'eyarshi,
sai ya kuma gyara sakun hular ya d'an medashi baya kad'an ta yadda ana iya ganin konceccen sumarshi ta goshinshi da yabi sajenshi yayinda bak'in gashin ya k'ara fito da farin fatar fuskarshi d'an bakinshi dakeda lips masu d'an fad'i sirara da suke jajaye sai shek'i sukeyi cikin zageyen sajenshi.

A hankali yaci gaba da taku yayinda yake shak'ar sassayan iskar damina da take busawa bisa dukkan alamun hadari ne ya watse,


A can harabar Airport d'in kuwa cike yake mak'il da taron bani Adam,
yayinda yan jaridu sukayiwa su Affan caa a kansu,
shi kuwa Affan burinshi yaga Safwan,
shiyasa bai bi ta kan sauranba,
shiko Safwan sanin halin Affan sarai ya sashi kaucewa ya nufi wurin Sultan bai saniba yayi gudun garane ya tadda zago,
cikin taron jamar ya jefawa Sultan tambaya.
"Shin yau wanne irin farin ciki kake ciki duba da yadda jama'a ke cike suna dakon isowar abokinka Girei?."
da sauri Affan ya d'an janye Sultan kana ya matso gaban Safwan murya ya gyara tare da cewa.
"D'an adam d'in kenan mai mantuwa,
kaga yadda Allah yayi ikonshi yau Yusuf ya taka matakin da duniyace tasan dashi,
duniyace baki d'aya ke al'fahari dashi yayinda ya zama mutun na biyu cikin mutanen Nigeria da suka samu damar shiga world book record,
hakan yasa masoyansa darawa a madadin kukan da sukayi a baya,
magautanshi kuwa yanzu sun zama fadawanshi."
ya k'arishe mgnar yana yiwa
Safwan wani irin murmushi tare da d'aga mishi gira d'aya da bud'a kafad'unshi alamar ya ka gani.
shi kuwa Safwan kauda kai yayi tare da barin wurin domin yasan tuni mutane sunga hakan ta akwatunan tv nansu,
Sultan kuwa sai godiya yakewa masoya,
lokacin da tawagar Yusuf ta iso inda taron jamar suke kuwa,
gaba d'aya wirin ya rud'e sabida abinda tambura da keyi wanda aka kawosu daga masarautar Yola,
Affan ne ya fara zuwa inda Yusuf yake ruggumeshi yayi tare da cewa.
"Alhamdulillah barka da zuwa,
Sultan ma ruggumeshi yayi tare da fara surutunshi,
sai kuma duk suka tsaya cike da mmki ganin Aryan da Abdul-karerm sai kuma Matawalle suna bayan Yusuf da irin shigarshi komai iri d'aya kamar yadda suma Affan da Sultan da Jafar irin shigar Yusuf d'in sukayi komai iri d'aya,
cikin mamaki da tsuke fuska Affan ya cillawa Aryan mugun kallo tare da janye Yusuf,
Matawalle da Sultan kuwa ruggume juna sukayi yayinda Aryan yabi bayan Yusuf,
Affan kuwa ya kasa ya tsare ya hana yan jarida isowa inda Yusuf yake,
har sukaje inda motocinsu suke,
sam shi Affan gani yake ko dai Aryan yazo kashe Yusuf ne.


A cikin gari kuwa ko ina mgnar Yusuf akeyi masoyanshi na murna magautanshi na cika da kunya.


Haka abin yake a gida kasancewar babu wanda yasan da batun dawowar Yusuf sai Abba da Daddy, kuma basu gayawa kowa ba.


A gefen Zahra kuwa yau k'awarta Dija ta kawo mata ziyara so suna parlour Mama yayinda Aryan k'arami ke zaune tsakiyarsu Dija na yanke mishi farce.
gyara zamanshi yayi tare da kallon Dija cikin d'an kwab'e fuska yace.
"Anty keyi sauri,
uncle Jafar fa yace in shirya yana zuwa d'aukata zamuje wurin Abeeh."
cikin tsuke fuska Zahra tace..
"Kai wlh ni na gaji da wannan batu na Aryan wai waye ne Abeeh d'innan da kuka buwayemu da batunshi tun jiya."
dariya ya d'anyi irin ta yara sannan ya janye hannunshi tare da cewa.
"Uncle Jafar yace sirrine kar in gaya miki,
kuma Abeeh d'in a woyar Uncle Jafar nake ganinshi ai."
share zancen tayi domin ganin zancen shirmene,
shi kuwa Aryan kan kujera ya hau tare da kai bakinshi saitin kunnen Dija yana cewa.
"Yauwa Anty Dija zo kiji."
murmushi tayi tare da kamo kuma tunshi ta d'an jijjiga,
shi kuwa hannu yasa ya jawo kanta cikin rad'a yace.
"Kin ga ko Uncle Jafar yace yau da Abeeh na zan kwana amman yace kar in gayawa Ammi na,
wai zatayi kuka zata hanani zuwa."
sai ya kuma zare ido tare da cewa.
"Karfa ki gaya mata, kema na gaya mikine dan yau karki koma ki kwana da Ammina bana son barinta ita d'aya nasan zatayi kuka kuma bana son tayi kuka."
Cikin dariya da son yaron Dija tace.
"Toh naji yanzu dai zo in k'arisa maka yankan farcen kar Abeehnka yace ana barinka da dotti."
sai ta kuma juyo ta kalli Zahra data zuba musu ido tana murmushi dan tana jin dad'in yadda Dija ke son gudan jininta,
shi kuwa Aryan zama yayi gaban Dija ta karishe mishi yankan farcen,
ita kuwa Zahra cewa Dija tayi,
"Wai ya batun Salisu ne kam?."
Salisu saurayin Dija ne ita kuma bata sonshi,
cikin tab'e baki tace.
"Wlh in kika kuma min mgnar wannan gaulan tafiya zanyi."
cikin dariya Zahra tace.
"A a meda wuk'ar hajiyata, ni dai gani nayi muna tsufa ba aure karfa ki manta nima na kusa shekara ashirin cib,
bare keda kin fini,
ke badon wannan larurar tawaba ai Wlh da tuni nayi aurena,
amman ke kin samu dama kuma kink'i,
in karatun nema yanzu dai kin gama,
iri nafa ba aure ba karatu ba daraja ba budurci."
sai ta k'arishe mgnar cikin zubda kollah,
da sauri Aryan ya koma gefenta tare dasa hannunshi ya share mata hawayen,
ita kuwa Dija cikin son kauda zancen tace.
"Yaushe ne zaki cika 20 d'in kinsan Allah wannan karon sai anyi shagalin birthday enki."
kai ta jujjuya tare da cewa,
"Saura kwana biyar nefa."
cikin d'an murmushi ganin ta samu ta kauda kukan Zahra tace.
"Wlh inaji a jikina komai yazo k'arshe."
ita kuwa Zahra numfashi ta sauk'e tare da cewa.
"Ni kuwa duk kwana nan ina yawan jin fargaba da tsinkewar zuciya,
ga mafarkan da nake yawan yi marasa dad'i."
cikin sanyi Dija tace
"In sha Allah babu komai sai al'khairi."
Haka sukaci gaba da tattaunawa,
Mama kuma tana parlour Abba suna kallo yayinda Mama keta sanya Abba nitsad'i dan haka nan mama take jin farin ciki,
shiyasa take d'ebe mishi kewa,
a wani sashin kuwa shima Abba yana cikin tsananin happy,
Ummi da Hajja inna kuwa suna Parlour Hajja inna suna hira da Goggo Maimuna da tazo yanzu,
sai Aunty Amarya kuwa da ta lek'o yanzu ta kira Aryan cewar Daddy na kiranshi yaje yana sama,
bayan ya fita
bada jimawa ba ya dawo wurin Zahra cikin mmki suka bishi da ido ganin ya shigo cikin wani shiri shima ashe dashi akayi d'inkin Daddy ya shiryashi cikin riga da wondo da gare irin nasu Yusuf hatta d'inkin shi nashi irin na Yusuf ne,
hakama takalmi da hula da agogo.
cikin happy yaje gaban Zahra yace.
"Ammi kalli nayi kyau ko?."
sunkuyowa tayi tare kissing nashi a goshi tace.
"Masha Allah kayi kyau Allah ya yiwa Daddy na al'barka."
cikin wayo yace.
" A a Allah ya yiwa Abeeh na al'barka dai
Daddy yace shine ya aiko min."
dariya tayi tare da amsa kiran wayarta dake suwa cikin kula tace.
"Salamu'alaikum ya Jafar ya akayi ne?."
cikin d'an d'aga murya dan hayaniyar mutane yace.
"Ki cewa Mama ta kunna tv."
kafin tayi mgna tuni ya katse kiran.
ido ta d'an juya tare da jawo rimot d'in tv ta kunna tare da komawa zaune da nufin ta kira Mama a waya ta kagaya mata,
tv yana kawowa yayi dai-dai da lokacin da aka nuno fuskar Yusuf cikin kyawun haiba,
Ido ta zubawa tv tare da komawa bisa kujeran tana fesar da sassanyar numfashi cikin sanyin murya tace.
"Hamma Yus........!




By
*GARKUWAR FULANI*

Sbp eh gowl

*HUKUNCIN ALLAH*


*PAGE 11*







Numfashi ta sauke a hankali jin mgnar ta kasa fitowa gaba d'aya,
Dija kuwa Aryan ta kalla da kyau ta kuma juyo ta kalli tv,
kai ta jinjina tare da sak'a abubuwa da yawa a ranta,
Zahra kam jin iska nata cika mata ido ta kasa k'ibtasu,
sai tayi k'arfin halin lumshesu a hankali,
wani irin yanayi takeji wanda yafi kama da tausayi.
Aryan k'arami kuwa
da gudu yayi parlour Abba yana zuwa bakin k'ofa ya tsaya tare da yin sallama,
cikin son yaron Mama ta amsa mishi sallamar tare da cewa.
"Aryan shigo."
yana shiga ya samu Mama ta tsare tv da ido cikin maida numfashi yace.
"Maman Yusuf kalli Uncle Jafar da Daddy mai suna, a tv."
sai ya kuma matsota tare da juyo kanta gareshi yace.
"Maman Yusuf kalli nima irin kayansu aka samin,
kinga ko dinkina irin na Abeeh."
sai ya kuma yi murmushi tare da cewa.
"Laah ga Uncle Affan ma kusa da Abeeh,
kinga harda Uncle Matawalle."
jawoshi tayi gabanshi tare da tsurawa tv ido sai ta kuma meda idonta kanshi,
cikin lumshe ido tace.
"Na gani Aryan kayi kyau sosai duk ka fisu kyau ai."
murmushin jin dad'i yayi tare da kallon inda Abba yake ganin ya zuba musu ido,
sai lips enshi daya taune ga idanunshi sunyi ja,
sai yaron ya juya kanshi gabanshi yaje ya rusuna cikin sanyi yace.
"Abban Yusuf baka da lfy ne?."
karo na forko da Abba yaji k'aunar yaron,
domin ko ba komai shi dai ya zama mishi wajibi yaso yaron,
hannunshi ya kamo tare da cewa.
"Wato kai ba Abbanka bane sai Abban Yusuf ne kad'ai ko."
kai ya jinjina mishi tare da cewa.
"A a nima kai Abba nane mana,
amman ba haka Maman Yusuf ke kiranka ba Abban Yusuf ai take cewa bata cewa Abban Aryan."
Dariya Abba yayi tare da jawoshi gabanshi,
nad'in hannun garen ya gyara mishi tare da cire hulan ya gyara mishi ya d'an tura hulan baya kad'an irin yadda Yusuf yayi,
murmushi yayi tare da lumshe ido wayarshi ya jawo sannan ya tura Aryan baya kad'an kusa da tv hotuna yayi mishi guda uku,
shi kuwa Aryan sai taune lips enshi yayi ina dalili zai b'ata mishi sa hulanshi to shinefa dalilin taune lips shi kuwa Abba sai murmushi yakeyi,
hotunan ya kalla tare da cewa.
"Zo ka gani."
da sauri yazo ya gani sai ya kuma karb'i

Please Login or Register in order to submit comment