Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayi wani irin juyi tare da zaro ido cikin tsantsan mamakin wadda baiyi tsammanin zuwansa a dai-dai wannan lokacin ba ya gani Malam Jabir ne tare da Affan,
Affan kuwa murmushi yakeyi tare da karkad'a kafad'unshi kad'an-kad'an tare da wani kakkashe idanu ,
Cikin farin ciki Yusuf yayi kanshi had'i dayin dan k'aramin ihun murna lokacin yayi dai-dai da mik'ewar Affan suka wani rungume juna had'i da fashewa da dariya sannan suka zubewa kan kujera 3 seater.


Malam Jabeer kuwa kallonsu yake fuskar shi d'auke da yalwataccen murmushi daya k'arawa kyakykyawar fuskar sa haiba Sultan da Abdul-kareem ma yan kallo suka zama dama sunsan Malam Jabeer saboda yawan kawowa Yusuf ziyara da yakeyi dan sun saba dashi sosai kasancewar shi mutum mai sauk'in kai so silent gashi duk randa yazo ya dinga musu nasiha kenan akan suji tsoron Allah su kare mutuncin kansu da addinin su, shiyasa suke sonshi sosai,
amma basu san Affan ba gaishe da Malam Jabeer sukayi kamar yadda suka saba ya amsa cikin sakin fuska da kulawa.



Yusuf kuwa sai da suka gama murnar ganin juna shida Affan sannan ya juya yana gaishe da Malam Jabir murmushi Malam Jabir yayi yace.
"Aina zata murnar ganin abokin naka ta mantar dakai ni da nake zaune?".
Shima Yusuf murmushi yayi had'i da sosa k'eyar shi yace. "Ah haba Malam ashe zan iya mantawa dani kainama in dai zan mance da kai,
kawai dai Affan dinne ya shammace ni jiya mafa munyi chatting dashi sosai amma bai sanarmin da zuwan nashi ba dama kai nasan kana tafe tunda wata ya kare".
murmushi Malam Jabeer yayi had'i da gyad'a kanshi alamun gamsuwa da jawaban Yusuf d'in zamanshi ya gyara tare dasa hannu ya karb'i cup d'in ruwa da Abdul-Kareem ya kawo mishi, kirban ruwan yayi tare da d'an lumshe ido yace.
"Ai gashinan kasan Affan d'an rigima da naci ne tun last months yake min nacin zai biyoni yazo ya ganku kaida Aryan nak'i saboda exam d'in first semester da suka fara toh Alhamdulillah 1 week da gamawar su fa yanzu yak'i zuwa ko ina shine dai na yadda muka taho". murmushi Yusuf yayi da kallon Affan ya wani kashewa Yusuf ido d'aya tare da jujjuya ido alamar zamu zaga garifa,
cikin kula Yusuf yace.
"Aikuwa nayi farin cikin wannan ziyara na kuma gode Allah yabar zumunci".
anan ya gabatarwa Affan Abdul-kareem da Sultan suma ya gabatar musu da Affan.



Kasancewar Abdul-kareem mai k'aunar Hausa nan ya fara yiwa Affan magana cikin mamaki Affan ya kalleshi jin hausa bakin balarabe yace.
"Kai Hausa fa naji kanayi kamar jakin kano".
dariya suka bushe dashi gaba d'aya har Abdul-kareem cikin harshensa da bai gama kama hausarba yace.
"eh naci na da k'aunar yaren da nakeyi ne ya sakani damun Sultan har sai daya koya mini nima na zama basokkoce, yanzu kuma bayole sai ya koya min fulfude".
Hannu Affan ya bashi suka tafa tare da cewa.
"Uhmm ato lallai nima dole na koyi larabci kafin nabar k'asar nan".
dariya suka dad'a bushewa dashi,
Sultan ne ya gyada kai tare da cewa.
"Gskyar ka Affan dan wannan shine ribar zaman tare ka k'aru da abin mutun kedashi".
nan dai suka d'inga hira tamkar sun shekara da sanin juna ana haka Aryan ma yazo sabadin wayar da Yusuf yayi mishi Affan yazo shima yayi farin ciki sosai da zuwan nasu.



Bayan sallar isha'i dawowar su daga masallaci kenan duk suna zaune a parlour,
sai Aryan dake tattare wurin da sukaci abincin, bayan sun gama kimtsa wurin duk suna zaune gaban Malam Jabeer.
Yusuf,Affan,Abdul-kareem, Sultan sai Aryan dabai koma ba saboda yau a gurin su Yusuf zai kwana dama time to time in bashi da lecture yana kawo musu ziyara Malam jabeer ne yayi gyaran murya nan dukansu suka bashi hankalin su dan sau tari in Malam jabeer zaiyi magana mai muhimmaci zakaga yayi gyaran murya shiyasa da sunji hakan suke nitsuwa,
shi kuwa cikin halin girma da mutunci yace.
"Alhamdulillah inaga in lissafina yayi dai-dai Yusuf inaga saura baifi wata d'aya ba ku gama makarantar nan ko Yusuf?".
Kai Yusuf ya gyad'a cikin tonk'woshe k'afafunshi yace.
"Eh Malam wata d'ayan nema koma ince 3 weeks."
kai ya jinjina tare cewa. "Yauwa toh Allah ya taimaka yasa ku gama lafiya."
a tare suka amsa da "Amin Amin."
Nisawa yayi tare da ci gaba da cewa.
"To amman fa kai Yusuf zaka k'ara zama anan na d'an wani lokaci duk da ban nemi shawararka ba,
Kasancewar naga k'wazonka da jajircewar ka akan abinda kakeyi na yanke shawarar yankar maka foam already ma na cike maka shi har nayi submitting kasancewar ta online nayi maka komai za'a k'ara horar dakai dabarun tseren doki da hanyoyin da ake bi akai ga nasara domin jajircewar ka ta saka inaji a jikina bama Nigeria ko Africa ba nan gaba duk duniya zatayi alfahari dakai akan tseren doki".
yalwataccen murmushi ne ya mamaye fuskar Yusuf cikin jin dad'i yace.
"Nagode Malam Allah ya biya masa dukkanin buk'atun ka ya cika maka burinka kamar yadda kake k'ok'arin ganin nawa burin na tsahon shekaru ya cika ka gama min komai malam kasani duk abinda kakeso basai ka nemi izinina ko shawarata ba dan ni nasan bazaka sani abu mara kyauba, Ngd matuka Allah ya k'ara girma".
Sai kuma muryarshi ta fara rawa wani irin farin ciki da tausayin kanshi ya k'wace masa abinda mahaifinshi bai mishiba wani yake mishi su kuwa Affan da "Ameen". suka amsa had'i da taya Yusuf godiya shikuwa Malam Jabeer cewa yayk.
"Alhamdulillah Allah shine abin godiya, fatana Allah ya baku sa'a a cikin dukkan lamuranku".
Amin sukace baki d'ayansu haka dai sukaci gaba da hira bare da suka samu Malam ya tafi dan Affan yak'i ya bishi masauk'insu.



Washe gari kuma su Yusuf suka fita zagaye gari suka bar Malam Jabeer a hotel d'in daya kama musu inda wani abokinshi ya kawo mishi ziyara.
sukuwa suka fantama cikin birnin duk wani gurin shak'atawa na garin sai da suka kai Affan, sultan kuwa kamar jira yake duk inda suka tsaya saiya hau snapping d'insu danshi wannan d'abi'ar shi ce a rana yana d'aukar pictures sama da guda 50 balle kuma yaga abin d'auka sai dare suka koma makaranta.



Kwanan su Malam Jabir 3 suka tafi sosai Affan yayi kewar su suma haka musamman Abdul-kareem kasancewar Affan mai irin halinsa na rawar kai da d'an banzan surutu.



Haka rayuwa taci gaba da tafiya yau dad'i gobe akasin haka daga wajen Yusuf ma hakanne dan sosai training d'in da yakeyi yake masa dad'i uwa uba kuma yana samu yayi waya ko vedio call da Maman Yusuf shiyasa ya kwantar da hankalin shi.



Bangaren su Zarah ma an samu canji sosai dan ko kofar gda Baba mai gadi baya barinsu su fita haka zatayi ta masa tijara da rashin kunya akan saita fita amma yaki karshe nan zata zube a k'asa tana ihu da birgima harta gaji dan Baba mai gadi ma in yaga zata dameshi sai ya rufe gidan da kwad'o yayi shigewar shi gurin matar shi haka Zarah zata gaji ta tashi ta koma gida abinda da kuruciya kafin gobe ta manta da jiya an hanata fita haka zata k'ara dawowa.



Shi kuwa Baba mai gadi ganin yanzu asirinsa a rufe ga muhalli an bashi babu biyan kudin haya uwa uba abincin safe rana dare an d'auke mishi basu akeyi suci su koshi har suma suyi kyautar shi da kuwa da in an samu a gidanshi anci abinci sau biyu ma anyi sa'a so tari inya fita ya siyo musu koko da kosai shi da matar shi sukaci saiya fita nema in Allah yasa ya samu ya dawo a sayi na rana in ba'a samu ba kuma a hakura sai dare ayi tuwo wasaran in anyi tuwon da yawa sai ayi dumame aci da safe harda rana.



Iya shatu Matar Baba mai gadi ganin haka a sannu ta fara janye hankalin Zarah tana mata dabara tace Zahra ta karantar da ita, ita kuwa Zarah dama sarkin son wasa sai hankalinta ya d'auke daga fita tayi ta koyar da iya shatu abinda ake koyarda ita tana yiwa iya shatu dariya wai itace malamarta, shiyasa sam yanzu bata fita dan inhar Hamma Sulaiman ya kaita makaranta ya d'auko ta toh bata k'ara fita sai kuma gobe in zata koma dan ko a makarantar suma ba'a barin yaro ya fita dokar makarantar ce dole in an tashi sai sai azo a d'auki yazo ita kuwa iya shatu sosai take k'aruwa da Zahara dan dama ba wani karatu tayiba haka yasa yanzu take jin dadi don ko a alwala saida Zahra tayi mata gyara.



Sannu-sannu bata hana zuwa sai dai a dad'e ba'a jeba.


Tafi dai tayi tafi Zarah yanzu ta girma hankali ya fara zuwa sai dai har yanzu tana da rawar kai da tsiwa kuma kasancewar tarbiyyar da aunty Amarya tayi mata yasa Zarah sam-sam ta tsani atamfa tafi k'aunar English wears suma saisun kamata gata da jikin girma dan yanzu tana shekara ta 9 amma zakayi tunanin zatayi shekara 11 ko 12.



A b'angaren su Yusuf ma Alhmdllh sun gama karatun su na shekara d'aya Alhamdulillah komai yayi yadda akeso dan Yusuf ya samu nasara shine ya karb'i a word d'in dalibin da yafi kowa k'wazo Abdul-kareem yazo ana biyu Sultan kuwa shine yazo na 6 inda wasu indiyawa ne sukazo na 3,4,5 sosai bikin yaye daliban ya k'awatar dan har Malam Jabir da Affan da Daddy sunje kuma sunji dad'i ganin yadda duk inda Yusuf yayi camera ke haskashi wal-wal haka taro ya tashi cikin farin ciki inda ko wanne d'alibi zai koma k'asar shi yan k'asar kuma masu zaman hotel su koma gdajen sun, inda Yusuf kuma zaiyi joining course d'in dazai k'arayi na 9 months.



Hakan ce ta kasance ga Abdul-kareem da Sultan kowa zai koma k'asarsu inda Sultan zaiyi Nigeria shi kuma Abdul-kareem zai tafi Egypt danshi balaraben Egypt ne.

Harda kuka sukayi da zasu rabu har airport suka raka Sultan danshi zai fara tafiya Abdul-kareem kuma sai cikin dare ,
a cikin airport d'in kuwa gaba d'aya suna tsaye suna fuskantar juna harda Aryan jifa-jifa Abdul-kareem kan goge hawayen dake bin fuskarsa,
ruggumar Sulanta yayi wanda yaketa d'aukarsu hoto yana cewa na ban kwana ne, Yusuf kuwa lips enshi ya ciza da qarfi tare da ruggumesu su duka biyu cikin tsananin kewar su da mutuwar jiki yace.
"Abdul-kareem in kana kuka to ni kuwa inyi yaya? ai gwara ku gida zaku koma cikin ahlinku, ni kuwafa zaku tafi ku barni da kewa gashi ba yanzu zan koma university Cape Town ba, bare ince Aryan zai dawo min madadinku ni d'aya zanyi ta zama har tsawon wata tara fa."
sai ya kuma yin shiru ganin Sultan ma na zubda k'olla sannan Aryan ma tuni hawaye yakeyi danshi Yusuf ne ya bashi tausayi da yace su sultan zasu koma gida cikin ahlinsu sai ya tuno mishi da cewafa shi ko ya koma din bazai koma cikin ahlinshi ba,
cikin rawar murya yace.
"Brox zan rink'a kawo maka ziyara akai-akai kuma kamar yau zaka gama Jurassic Park polo mu koma Cape Town."
cikin kula Sultan yace.
"Please bayole ka rink'a shan maganinka kan lokaci karkayi wasa da lafiyarka. "
Kai Yusuf ya gyada alamar to,
Abdul-kareem kuwa ruggumeshi yayi dukansu uku yana kuka lokacin da yaji ana kiran matafiyan
da kyar suka rabu da sultan suna binshi da ido har ya b'ace musu,
jimawa kad'an shima Abdul-kareem jirginsu ya d'aga ananne saida Yusuf ya zubda k'walla, kunsa balarabe da saurin kuka kukan da Abdul-kareem keyine yasa Yusuf zubda k'walla dan baushe yace sabo tirken wawa ko?
sai da sukaga tashin jirgin Abdul-kareem sannan suka koma jikin su duk a sanyaye suna ganin kamar wannan rabuwar itace ta har abada.




Sosai Yusuf ya maida hankalin kan wannan training d'in dan yana da sarkak'iya da had'ari cikin shi sosai a cikin shine ake koya musu yadda in suna tsakiyar tsere doki ya fad'ar dasu a maimakon su zube a'ah zasu zabura su koma saman dokin aci gaba da tsere dan wannan practical d'in sai kwararru kuma shahararrun yan tsere suke iya zuwa su koyeshi sosai training d'in ke wahalar da Yusuf Amma saboda yanaso ya k'arfafawa Malam Jabeer guiwa ya saka yake jure duk wani wahalar da zai sha.

Yawanci kullum a Mowbray golf club ake kaisu Yusuf inda anan suke training in practical sosai Yusuf ke k'ara k'warewa.

A bangaren Aryan ma karatun shi ya mika dan sun shiga 2nd semester suma karatun ake da zafi-zafi.



Zarah ma anata rawar kai za'a zana comment entrance kasancewar private school ne dan haka a primary 5 ta samu damar zana comment entrance kuma dama Zarah wasa ne yake shamata kai amma yanzu da bata da lokacin wasa saita zama yarinya mai k'okari da ake alfahari da ita matsalarta kawai tsokana da tsiwa da rawa.



Yau a gajiye Yusuf ya dawo daga gurin training dan sau biyu doki na kayar dashi k'asa gaba d'aya jikin shi in banda ciwo babu abinda yake har wata yar rama yayi,
yana shiga cikin parlour su kira ya shigo wayar shi vedio call ganin Sulaiman ne ke kiranshi ya saka shi hanzarin d'auka dan yasan Mamanshi ce ai kuwa yana amsawa da fuskar Mama yayi tozali ajiyar zuciya yaja had'i da lumshe idanuwan sa Mama kuwa fuskarta d'auke da murmushi amma ganin d'an nata duk ya rame sai annurin fuskar tata ya gushe cikin tsantsar damuwa da kula irinna uwa da d'anta tace.
"Subhanallah! Yusuf d'ina jinya kayi ne? baka da lafiya ne? Meke damunka?".
Duk cikin lokaci d'aya ta cillo mishi wannan tambayar cikin damuwa da tsantsar tashin hankali murmushi Yusuf ya k'ak'alo cikin sauk'e numfashi yace.
"Ayyah Maman Yusuf, Yusuf d'inki ko ciwon kai baiyi ba lafiyar shi k'alau".
cikin tsantsar tausayawa tayi magana tace.
"Ai naga dukka rame ne kamar baka da lafiya gaya min to make damunka?". Dariya yayi tare da cewa.
"Rama kuma kai Maman Yusuf wanne irin rama kina ganin Yusuf d'inki ya zama d'an lukuti ya fara ajiye k'aton tumbi".
a tare suka kyalkyale da dariya Mama tace.
"A'ah ni dai bangani ba".
d'an zaro idanu waje Yusuf yayi had'i da tattaro cikin shi ya turo shi gaba shi a dole yayi k'aton tunbi cikin wasa irin yadda yake mata in yana son kontar mata da hankali yace.
"Ah gashi kuwa Maman Yusuf, kallifa da kyau."
sai ya kuma kallonta cikin salon wasa yace.
"Ya dai ya to ko dai idon naki ne ko sai na yanko miki medical glass ne Maman Yusuf?".
dariya sukayi a tare cikin jin dad'i Mama tace.
"Zanci gidanku Babana ka maidani kakar ka ko?". Hannuwan shi duka ya saka ya kama kunnen tare da tonk'oshe wuyanshi yace. "Afuwan Maman Yusuf,
tuba nake".
sai ya kuma lumshe ido tare da sauk'e ajiyan zuciya yace. "Wallahi Maman Yusuf ina jin matsayin ki a cikin raina kin had'a dukkan darajar duk shak'ik'aina ke kad'ai in ina dake kin isar min, Kaka, Yaya, K'anwa, kawu, Bappa goggo, kai da komai ma!".
murmushi Mama tayi tace. "Menene koman kenan?." Hannun shi ya saka ya rufe duka idanuwan shi biyu yace "Uhmm?".
Murmushi tayi tace.
"Eh ina jinka bani amsa". bakin shi yad'an tura gaba yace.
"To Maman Yusuf dole saina fad'a ne?".
cikin dariya Mama tace.
"Eh dole ne ka bani amsa."
Kai ya sunkuyar tare da sosa k'eya yace.
"Toh kin fimin matar dazan aura da yaran dazan haifa nan gaba ma".
dariya sosai Mama ta tuntsire dashi tace.
"Eh lallai Yusuf dina ya girma har yana zancen aure ko an samomin surukar tawa ne? tunda naji harda batun jikoki". hannunsa ya saka ya rufe duka idanuwan shi murmushi Mama tayi nan suka dinga hira har saida Yusuf yaji kiran sallah yayi sallama da Mama badan yaso ba sai dan ganin lokacin sallah zai k'ure masa.

******

Zarah an zana comment entrance kuma Alhamdulillah tayi nasara taci inda take ta murna ta ishi yan gidansu da iyayi tamkar kanta za'a fara secondary school kuma inda yayi dai-dai bikin Amira saura sati 2 kenan.





Bangaren su Raihana k'anwar Aryan ma yanzu ta zama yan mata dan tana term d'innan da zasu shiga first term zata shiga s.s 1 kenan.


Yusuf ne zaune a Parlour shiru baka jin komai sai sautin A, C dake busawa, yayinda yayi nisa cikin duniyar tunani gaba d'aya ji yake wani irin bacci mai dad'i na fizgarshi lumshe ido yayi tare da gyara kinciyarsa bisa 3 str da yake.
can cikin baccin yaji wani irin abu na diri da ratsa k'ahon zuciyarshi tamkar ana girgizashi cikin zafin nama ya yunk'ura tare da zabura, lokaci d'aya kuma ya koma dirsham kan kujerar dan jin....!






*wasa farin girki, muje zuwa masu karatu. koya budurcin Zahra zai kasance?, ina oga Safwan ne ko menene k'udurinsa akan Yusuf? ya rayuwar Yusuf zata kaya? waima shin wacce kaddararce ke shirin bin rayuwar Yusuf? ko sai yaushe Abba zai Huce? menene zaiyi sanadin dawowar Yusuf gida? gashi nan dai yana dai ta bawa k'annenshi kariya to wai ta ina k'addarar zata shiga gidansu duk da yawan kariyar da yake basu?.*
duk wadan nan amsoshi suna nan tafe



*BY*
*GARKUWAR FULANI*
[31/12/2019 11:55 AM] 👑 QANWAR JIDDAH 👑: *HUKUNCIN ALLAH*


*Assalamu alaikum al'ummar jahar Gombe da kewayenta ina gaidaku tare da fatan al'khairi. Especially ma'aikatan gidan radio R power ina godiya da karamcinku gareni nida k'anina Sadik Namiji one, lallai munga karrama irin ta yan jarudu, fatana Allah yasa Gombawa zasuji daddin tattaunawar da akayi damu, Bikilsu maigado, wacce ke karanta maku littafin Mutumin duniya, tayi muku al'bishirin cewa fa littafi na gaba na Garkuwa za'a karanta muku. Ina kuma k'ara jadda wa ficecciyar yar jaridar nan Zaleeha Baban Gida Hari littafina na gaba nasune domin ko sunan littafin taken program d'inta ne mai taken BABU NAKASASSHE SAI RAGO gaba d'aya sun cika da farin ciki suna kai Masha Allah yau kam gamu ga Garkuwa, Alhamdulillah ni dai kam Garkuwa naga karramawa da karamci a gidajen radio har biyu a Gombe ngd matuka Allah bar zumunci da qauna Gombawa d'iban fari ba'a kwana da kuba a tashi daku Gombe doma hamadar sarki lahirar Sulaimanu 🤝🏻🤝🏻🤝🏻😍 Allah yak'ara daukaka mana gidajen radio nan baki d'ayansu*










~Sadik namiji one Allah ya kiyaye hanya ka gaida mutan Yobe, Maiduguri, Kano, Katsina, da dai sauransu Allah bada sa'an aikin da akaje yi Aunty Nana nayi maka fatan Al'khairi~

2⃣1⃣


Da sauri ya koma ya zauna dan ji wayarshi taken amsa kuwa da diri a aljihun regards zoro woyar yayi da nufin katse kiran sai kuma ya d'an lumshe ido tare amasa kiran dan ganin wacce ke kiran nashi.

gyara zamanshi yayi a kan sofar ya d'aura kafarshi d'aya kan d'aya yana d'an girgiza ta kunnenshi mak'ale da waya yana magana da Amira murmushi ne d'auke a fuskar shi lips d'inshi na k'asa ya taune tare da lumshe ido cikin yanayin jin baccin shiru yayi alamar yana sauraron abin ake cewa daga d'aya b'angaren bayan wasu yan dak'ik'u sannan yace. "Ayyah Amira har yaushe zan zaki dena damun kanki da batun zuwana,
na fad'a miki bazan iya dawowa Nigeria na halarci bikin kiba saboda yanzu karatun da nakeyi me zafi ne kuma ko bayan haka kin manta Abba ya haramta min zuwa gidanshi?".
Ya k'arashe maganar cikin sanyin murya da alamu na karaya banji me Amira tace ba sai naji ya k'ara cewa.
"Kiyi hak'uri Amira ko bayan haka ma bani da wadaceccen kud'in dazan yanki ticket na dawo Nigeria saboda kada ki manta wani bawan Allah ne ya d'auki nauyin karatu na da taimakon Malam Jabir inna ce zanzo gida tamkar zan musu katsalandan ne ko takurasu da k'ara musu wata d'awainiyar".
Ajiyar zuciya yaja had'i da bud'e idanuwan shi ya saka hannu yad'an sosa gashin girar sa sai kuma cikin hanzari yace.
"A'ah a'ah Amira kada muyi haka dake dana halarci bikin ki daban halarta ba babu abinda za'a fasa na daga cikin shagulgulan biki illah na biki da addu'a Allah yasa albarka a auren ki ya baku zaman lfy amma bance ki fad'awa Daddy ba dame zaiji hidimar aurar dake da zaiyi ko kud'in dazai turomin nazo tom in zan dawo wane zai biyamin na dawo?".
K'itt yaji an datse kiran murmushi yayi had'i da d'aura hannun shi kan lallausan gashin kansa ya maidashi baya yace.
"Amira rigima sai dai kiyi hak'uri bazan zo Nigeria ba a yanzu inada dama da kud'in kawai zuwanne ba fa'ida tunda ko nazo Abba bai huceba tukun".
Aryan ne ya shigo d'akin bakin shi d'auke da sallama amsawa Yusuf yayi had'i da cewa.
"Sammakon kenan da kacemin zakazo da wuri?" Fridge Aryan ya wuce ya bud'e ya d'auko ruwa ya zauna saida ya b'alle murfin bottle d'in ruwan ya kwankwad'a tas ya shanye had'i dayin gyatsa yace "Alhamdulillah".



Sannan ya kalli Yusuf cikin harara yace.
"Matsalata da kai wutar ciki kafin ka yiwa mutum tambaya sai kayi masa k'orafi".
pillow kujerar da Yusuf yake kai ya d'auka ya cillawa Aryan had'i da jifan shi da harara yace.
"Tsahon awa nawa na zauna ina jiranka? har bacci na fara".
sai da Aryan yayi balance kan kujerar da yake had'i da tallafe kanshi da hannuwan sa duka biyu yace.
"something d'in assignment na tsaya yi shiyasa ban shigo da wuri ba kaji uzirina sarkin k'orafi".
mik'ewa tsaye Yusuf yayi yace.
"Toh tashi mu tafi nima nan Amira ce ta kirani zata isheni da iyayi wai ya kamata naje bikin ta kamar in babu ni za'a fasa wani abin ne".
wani kallo Aryan ya jefi Yusuf dashi yace lallai guy d'innan baka da tsusayi ko barina na huta ba zakayi ba zakace na taso mu tafi kasan da k'afata fa na hauro ba lifter na hauba".
gaba Yusuf yayi ya fara tafiya yace.
"Eh tunda a k'afa ka taho daga U, C, T har zuwa Jurassic Park polo saika zauna ka huta ai kaga tafiya ta dan muna dawowa yawan da ka sani yi a dole zamu wuce tare zanje, Mowbray golf club akwai wani malami da yazo daga k'asar America zai koyar damu na wuni uku".
tashi Aryan yayi ya bishi yana "Zan rama ne,".



***********


Kwanci tashi asarar mai rai haka lokaci yaci gaba da tafiya Yusuf yana ta practicall class d'inshi kuma yana samun nasara sai dai yana shan wuya sosai, saboda yanayin horar war da ake bashi ba irinna nan Nigeria bane kwararrun malamai masana doki aka samo suke horar dasu da iya basirar su.

Yauma Yusuf ne sanye da kayan polo yana kan wani jibgegen doki brown colour mai kyalli wasu karafuna ne a gabanshi a jejjere kusa da kusa inda cikin gudu akeso ya dinga tsallake ko wanne k'arfe ba tare da kuma dokin nashi ya tab'a

Please Login or Register in order to submit comment