Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da zama kan sofa kana,
ya ajiye yaran kan cinyarshi,
cikin sauri Yusuf k'arami wanda suke kira Yusif ya zama jikinshi tare da cewa.
"Uncle F bari inje in k'ira Daddy na."
kafinma yayi magana tuni ya fita a guje,
itama Asmy zamewar tayi tabi bayan Yusif d'in,
Hajia kaka kuwa,
kitchen ta koma tare da had'o mishi abin tab'awa kana tazo ta dire mishi a tsakiyar parlour,
a kan carpet.
Zama tayi gefenshi tare da cewa.
"Maza sauk'o kaci dahuwata."
kai ya dan jujjuya mata tare da cewa.
"A k'oshe nake."
zamowa tayi tsakiyar carpet d'in tare da bud'e kular d'umamenen miyar taushe mai zafi sai tururi yakeyi ga k'amshin man shanu daya bud'eshi kana ga tanta kwashi,
sai filas da kunun koko mai surkin nonon shanu,
zuba mishi tayi tare da cewa.
"Ai baka isaba dole sai fa kaci."
ganin da gskya takeyi ya sashi sauk'owa kana ya matso tare da turo plet d'in tsakiyarsu cikin shak'uwa yace.
"Toh muci tare."
dariya tayi tare da Jawa yar k'aramar robar data zubo ruwan wonke hannu,
ta mik'a mishi hannunshi ya wonke kana ta wonke nashi a tare suka fara can dumamen sunaci suna hirar yaushe gamo,
dad'in miyar yasa Yusuf ya d'anci mai d'an yawa.
Suna cikin hira Aryan ya shigo tare da sallamarsa,
cikin kula da nuna ba komai Yusuf ya jawo hannunshi tare da cewa.
"Yauwa kaima zaka tura gaya,
inma k'aton ciki zamuyi to muyishi tare."
shi kuwa Aryan cikin jin dad'in yadda Yusuf ke nuna mishi yarda da k'auna har gobe,
sai kuma takaicin kanshi da yakeji,
zama yayi tare da cewa.
"Yoh ai abinma son kaine ni ko tayi dahuwarta bata bani."
hararanshi tayi tare da cewa.
"Yoh kai kace ku yan boko ne bazakuci d'umame ba sai tea da k'wai dasu dankali da kaji,
ni kuwa duk abinda zanci in banci d'umamenanba ba ganewa nakeyi ba."
dariya sukayi ta mata ganin yadda taketa tsotsar k'asusuwan tanta k'washin,
haka dai sukayi ta hira,
har zuwa 11:00 Am kana suka fita tare da Aryan d'in
amman a motar Yusuf d'in,
kai tsaye gidan Goggo Maimuna sukaje,
inda sam tak'i sakewa Aryan fuska,
yayinda Yusuf kuwa sam baiji dad'in hakanba.
Daga nan kuwa gidan Aunty Madina sukaje inda suka samu Goggo Aisha ma tazo duba yaron Aunty Madina yana bak'on daura.
ta gwarama ita Aunty Madina ta d'an sakewa Aryan fuska.
Koda suka fita nan gidansu Ummi sukaje suka gaida kakar Sulaiman kana suka fito,
kai tsaye gidan Adda Zulaihat suka wuce,
sun dad'e suna hira har dai yamma tayi gabanin margin ne Aryan ya kalli Yusuf tare da cewa.
"Darefa yayi ya kama mu tafi."
cikin salon yadda sukeyi da can ya harari Aryan tare da cewa.
"Can da matsalarka bita zai-zai kace dai kana son komawa gida."
dariya Aryan yayi tare da cewa.
"Yoh ai gwara min tunda zan koma in samu madam."
Adda Zulaihat ce ta harari Yusuf d'in kana ta kalli Aryan tare da cewa.
"Gaya mishi dai Aryan, ai shi baisan dad'in zaman gidaba, tunda shi kad'aine gwara ku sashi ya nemi mai tayashi zama."
baki ya tura tare da bin bayanta a k'ofar shiga kitchen ta tsaya tare da cewa.
"Lfy dai kake bina kamar d'an yaye?."
hannunta ya kamo tare longob'ar da kai kana cewa.
"Har yanzu fushi kukeyi da niko?."
cikin kauda kai tace.
"Zamuyi dai in bakayi aureba,
domin ko yaushe sai munji bak'ar mgna a kanka,
sai ayi ta cewa ai bazakayi aureba tunda kana can kanata zinace-zinace,
kullum sai Ummi ta yafawa Mama mgna,
dan haka Mama takeda burin kayi aure."
cikin sanyi da jin zafi yace.
"To zanyi ko dan farin cikin Maman Yusuf."
dariya tayi cikin jin dad'i tace.
"Yauwa d'an k'anina ko kaifa,
yanzu wa kake nema?."
cikin tab'e baki yace,
"Babu sai dai shi wancan ya nemomin."
ya k'arishe mgnar tare da nuna Aryan,
shi kuwa Aryan dariya sosai Adda Zulaihat da Yusuf suke burgeshi,
sam shi yanzu Raihana ko gaisuwarshi sai ta tsune take amsa.
"To Kai Aryan kaji ko yanzu aiki yana gareka."
cewar Adda Zulaihat kenan.
Shi ko Aryan mik'ewa yayi tare da cewa.
"An gama insha Allah nan kusa zamu rabashi da rayuwar gouranci."
shi kuwa Yusuf cikin yin k'asa da kai yace.
"Adda."
ido Zulaihat ta zuba mishi jin yadda ya kirata,
shi kuwa murya can k'asa yace.
"In nayi aure zan karb'e Aryan fa."
ido ta zuba mishi cikin sanyi tace.
"Hmmm."
daga nan bata kuma mgnaba,
shi kuwa Yusuf ci gaba yayi da cewa.
"Adda ki cewa Maman Yusuf,
Yusuf d'inta yana kewarta yana son ganinta,
dan Allah tayi hak'uri tazo nan mu had'u."
cikin tausayawa tace.
"Toh zan gaya mata amman ka fara batun aure kafin nan."
daga nan ta kawo musu zazzafan danderu suka d'anci sannan suka mata sallama suka tafi.

Suna fita kai tsaye gidan Tatti suka nufa,
suna isa dai-dai k'ofar gidanta ana fara kiran salla,
so saida sukayi salla kana suka shiga gidan.

A harabar gidan suka samu Tatti da Zahra,
suna kan babbar taburma bisa dukkan alamu abinci sukeci,
ganin Yusuf yasa Tatti farin ciki sosai ita kuwa Zahra fargabanta ya k'aru yayinda taketa watsa Aryan Babba harara.
cikin happy Tatti taketa jara musu sannu da zuwa.
"Kai maraba lale marhabin da manyan bak'i."
sai ta kuma kalli Aryan cikin tsuke fuska tace.
"Su Aryan manya idonka kenan."
da sauri Yusuf ya katse mata hanzari dan baya son abinda masoyinshi keyiwa Aryan ya kamata a nemi sanin dalilnshi kafin a yanke mishi hukunci shiyasa cikin murmushi yace.
"Baya zuwa ko in bana nan ko Tatti?."
cikin tab'e baki tace.
"Yazo aini ko yazoma bana so,
duk mutumin da zaiji rasuwar Gambo na dai ya kasa zuwa yamin ta'aziya aini bani buk'atarshi."
Cikin sanyi Aryan ya sunkuyar da kai hawaye na tsiyaya sam shi baiji rasuwar Uncle Gambo ba sai d'azu da Yusuf yake gaya mishi,
tabbas da yaji da yazo mata gaisuwa domin baya mance al'khairi da hak'urin da Uncle Gambo yayi da k'uruciyarsu,
ya zama tamkar k'anni ga iyayensu,
murya na rawa yace.
"Wlh banjiba Tatti kema kinsan da naji da zanzo kiyi hak'uri banji bane Allah ya jik'anshi da rahama."
kai ta jinjina hawaye na bin fuskantar,
cikin muryar kuka tace.
"Amin Amin Aryan."
shi kuwa Yusuf tuni yasa hannu ya d'auki Aryan k'arami da yake bacci yayi pillow da cinyar Zahra,
tausayin Tatti na ratsa zuciyarshi,
cikin rawan murya ya gaidata tare da cewa.
"Tatti ki dena yi mishi kuka kiyi ta mishi addu'a."
kai ta jinjina tare da cewa.
"Kasawa nakeyi dai Yusuf am in na tunoshi bana iya tsaida hawayena."
shima Yusuf tuni rauni ya rufeshi ji yake dama zai samu hawaye ya zubo mishi da zaiji sauk'i a ranshi,
haka dai yayi ta bata baki.
saida suka ga ta d'an saki ranta sannan sukayi mata sallama suka mik'e da nufin tafiya,
Zahra da tunda suka zo bata ko motsaba bare tayi musu mgna,
sai kukan da takeyi dan sun tuno mata kawun nata,
sai yanzu da taga Yusuf ya mik'e tare da sab'a Aryan k'arami a kafad'a,
itama mik'ewar tayi tare da gyara hijabin jikinta,
cikin sanyi tace.
"Hamma Yusuf Aryan d'infa?."
bai ko juyoba bare ya kaleta ko ya bata amsa,
ita kuwa Tatti k'asa tayi da murya tare da cewa.
"Ke kiyi kawaici mana."
kai ta jujjuya tare da bin bayansu,
ganin har sun shiga mota ya sata matsowa jikin motar cikin sauri tasa hannu ta rik'e marfin motar tare da cewa.
"Dan Allah Hamma kawoshi wlh yau tun da yamma cikinshi ke ciwo sai kuka yaketayi sai yanzu ya samu ya lafa,
kaga yau ko masallaci bai jeba,
wlh hankali na bazai kontaba in ka tafi dashi."
Ido ya zuba mata ganin duk mgnar da takeyi hawaye na bin fuskantar,
sai ya kuma sunkuyo ya kalli,
Aryan d'in cikin sanyi yace.
"Shiga mu kaishi doctor ya dubashi."
kai ta jujjuya sannan tace.
"Ai ya samu sauk'i."
cikin tsawa d'an d'aga murya yace.
"Toh matsamin daga nan in bazaki jeba."
ganin ya murd'a key d'in motar yasa tayi sauri ta shiga,
bayan motar.

rufe marfin yayi tare da jan motar,
suna shigowa cikin jimeta ganin sunfi kusa da bayan pz sai ya gaggara ya sauk'e Aryan, bayan sunyi sallama Aryan ya shiga cikin gida,
shiru baija motarba bai kuma rufe marfin inda Aryan ya fitaba,
ganin shirun yayi yawane yasa Zahra yin mgna a hankali tace.
"Hamma Yusuf dare na yifa."
kai ya sunkuyar tare da tallabe Aryan cikin murya can k'asa yace.
"Kuma sai aka ce miki ni drivern gidanku ne ko?."
gane abinda yake nufi yasa,
ta fito daga bayan,
sannan ta dawo gaban.
tana rufe motar yaja tare da fita daga layin.
Cikin Mamaki ta kalleshi ganin inda ya nufa,
murya na rawa tace.
"Hamma Yusuf ina zamuje?."
bai kulata ba sai k'ara gudun da yayi,
gaba d'aya sai ta firgita cikin tsoro ta kai hannunta kan.....!




By

*GARKUWAR FULANI*
[25/01 8:49 PM] My 2nd Mtn: [1/23, 10:17 AM



*HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE. 14*





K'irjinta da taji ya tsananta bugawa da sauri-sauri a lamun tsoro ya rufeta,
shi kuwa Yusuf ko inda take bai kayo ya kallaba.

Ajiya zuciya taja a hankali ganin sun isa bak'in wani hospital mai tsananin kyau da girma,
kasan cewar gate d'in a bud'e yake sai kawai ya danna hancin motarshi ciki,
parking yayi tare da kashe motar sannan ya tallabo Aryan da ya fara mutsu-mutsun farkawa,
kan kafad'arshi ya d'aurashi tare da zuro k'afafunshi woje,
sai lokacin ya d'an juyo ya kalleta da alamun ta fito,
ita kuwa kauda kai tayi tare da sauk'e numfashi,
juyawa yayi ya fita tare da gyara rik'on da yayiwa Aryan wanda hasken wurin ya sashi farkawa,
cikin asibitin ya nufa inda ma'aikatan keta gaidashi.
yana shiga cikin asibitin sai yayi gefen dama tafiya kad'an sai gashi ya bulla wani d'an wuri mai kyau ko ta ina haskene kamar rana,
sai fulawi dake jere,
kana sai d'ai-d'aikun mutane dake d'an gilmawa,
wata yar kusrwa yabi wacce takeda d'an fad'i,
yana tafiya kad'an sai gashi a bakin wani office mai matuk'ar girma,
yana sa hannu da nufin bud'ewa sai ya kuma d'an ja baya ganin an bud'e k'ofar,
shi kuwa wanda ya bud'e k'ofar ido ya d'an fitar tare da matsoshi cikin cikin harshen fullanci yace.
"A a Girei da kanka,
Masha Allah."
sai ya kuma d'an matsa tare da cewa.
"Bisimillah shigo."
mirmushi Yusuf ya d'anyi tare da bin bayanshi,
cikin office d'in suka shiga wanda ya wadatu da ababen buk'ata irin nasu na likitoci,
madadin ya koma mazauninshi sai ya zauna kan wata kuje mai d'an girma cikin sakin fuska ya nunawa Yusuf gefenshi tare da cewa.
"Ga wuri."
zama yayi tare da ajiye Aryan kan cinyarshi,
shi kuwa Aryan sai ido ya rumtse da k'arfi gaba d'aya goshinsa zufa ce ke tsastsafowa,
bisa dukkan alamu cikin ne ya murd'a.
ganin haka Dr Mahmoud yasa hannu tare da k'arbarsa cikin kulawa yace.
"Girei yaron nan ba Lfy ko?."
kai ya jinjina mishi Alamar eh.
cikin kad'uwa Dr ya ce.
"A a amsa da baki zaka bani, ba wannan d'abi'a taka ta mgna da gaggan jikiba,
shin inama uwar yaron?."
gyara zama yayi tare da sa tafin hannunshi kan goshin Aryan ya d'an goge mishi zufar cikin tausayin yaro ya juyo ya kalli abokin nashi kana yace.
"Cikin shi ke ciwo?."
gyara zama Dr yayi tare da janye rigar Aryan sama kad'an kana yasa tafin hannunshi kan marar Aryan kana ya d'an kalli Yusuf tare da cewa.
"Kwana nawa yayi da ciwon, yaushe ya fara mishi ciwon?.
Kai ya girgiza alamar bai tsaniba,
"To ya tab'a yin ciwon tun yana jariri ne?."
nanma kai ya girgiza alamar baifa saniba.
ido Mahmoud ya zuba mishi tare da cewa.
"Ba amfanin zuwanka dashi, tunda baka san komai kan ciwonshin ba,
dama kirana kayi nazo gida nasan mamanshi zatayi mana duk bayanin da mukeda buk'ata."
cikin d'an hararar Dr ya ce.
"Tare da ita muka zo ai."
da sauri ya kalleshi tare da cewa.
"Toh tana ina?."
Kai ya d'an juya tare da cewa.
"Tana cikin mota."
cikin mmki yace.
"Toh me amfanin zuwanta?."
Cikin tab'e baki Yusuf ya d'aga mishi kafad'a alamar oho.
to Mahmoud dai yasan Yusuf sarai tunda abokine tun na yarinta kuma suna tare har gobe,
sanin halinshi ya sashi gyara zama tare da cewa.
"To a kirawota."
shiru ya d'anyi na wasu seconds sannan ya zaro wayarshi tare da fara duddubata bayan 8 seconds ya karata a kunne,
jim kad'an aka amsa kiran da yayi d'in,
cikin sanyinshi yace.
"Kai Jafar kira, Zahra kace ta shigo cikin asibitin Dr nason ganinta."
cikin yin wal-wal da ido tare da Kad'a harshe Jafar ya gyara zama tare da danne dariyarshi cikin dakiya yace.
"Hamma Yusuf bana da kud'i a wayar,
yanzuma nake shirin fita in sayo,
sai dai ko in zan turo maka number ta."
wani d'an guntun tsaki yaja tare da cewa.
"Ka kirata da kud'in da zaka turo min number."
da sauri Jafar yace.
"A Hamma Yusuf nera hud'u nefa,
ai daga sallama mtn zasu kwakwashesu,
in dai turoma."
yana fad'in haka ya katse kiran tare da yin sauri ya tura mishi text d'in number,
kana yayi maza ya rufe wayar gaba d'aya,
sannan ya juyo ya kalli Tatti cikin dariya yace.
"Kinga Tatti bari in koma nasan Hamma Yusuf zai maidasu gida."
kai ta gyad'a mishi tare da cewa.
"Toh yanzun suna inane?."
mik'ewa yayi tare da sa takalmishi kana yace.
"Suna asibiti."
itama mik'ewan tayi tana mishi rakiya tare da cewa.
"Eh lallai inaga Aryan suka kai asibitin dan yau wuni yayi da ciwon cikinshin nan."
"Eh to lallai inaga shid'in suka kai,
ai fa gwara a tsayawa ciwon dan kullum k'aruwa yakeyi."
dai-dai lokacin suka iso harabar gidan kana sukayi sallama,
shi ya tafi ita kuma ta koma cikin gida.

A asibiti kuwa Yusuf ya gwada kiran Jafar ya kai sau 3 amman bata shiga haka yasa dole ya bud'e text d'in kana ya d'auki number,
kiranta yayi tare da kara wayar a kunne,
ita kuwa Zahra tana cikin motarshi ta dake sai dube-dube take mishi cikin motar,
can baya ta kayo ganin wasu takardu an musu d'amara da wata yar igiya,
juyowa tayi tare da daukosu konce igiyar tayi kana ta fara duddubasu,
gaba d'aya duk shafin da ta bud'e sunan Aryan take gani,
*Aryan Yusuf Muhammad Girei*
sai kuma shaida da sa hannun Barrister Affan da Jafar sai sa hannun Yusuf d'in kana sai inda Aryan d'in zai sa hannunshi alamun takardun shaidar mallaka mishi wasu abubuwane masu mahimmanci,
ganin suna da yawa yasa ta medasu ta ajiye kana ta dawo mazauninta,
sai ta kumayi shiru tana nazartasu,
yar durowar gaban motar tasa hannu ta danna mad'inshi cikin sa'a kuwa ya bud'u,
nanma wasu takardun ta gani,
shaidar mallakar makarantar Yusrah da wani shopping mall mai suna Yusrah kana sai,
kuma na wannan asibitin da ya kasance sunan Yusrah,
ga sunanshi ga sa hannunshi da komi da komai na lawyer enshi,
medasu tayi ta ajiye kana ta rumtse idanunta cikin ranta tace.
"Toh wacece *Yusrah* da komainshi ya saka sunanta?
ko dai karuwar..".
sai tayi maza ta rufe bakinta tare da jujjuya kai murya can k'asa tace.
"Ba mazinaci bane."
sai ta kuma d'auko turaren da ta gani a gefen takardun,
bud'eshi tayi ta kaishi hancinta,
wani irin lumshe ido tayi tare da cewa.
"Hhhhhyy k'amshi mai dad'i."
sai ta kuma feffesashi a wasu sashi na jikinta.
tana cikin fesawar taji wayarta ta fara suwa,
zabura tayi dan ya firgitata,
cikin zare ido ta amsa kiran tare da mannawa a kunne.
ido ta k'ara zarowa jin muryarshi.
"Ki shigo ciki Dr zai miki tambaya kan ciwon Aryan d'in."
cikin sauri tace.
"Toh."
kana ta katse kiran,
shi kuwa wayar ya zubawa ido tare da taune lips enshi a ranshi yace.
"Nitsuwa dai ta gagareta ji yadda take magana da ihu ta wani katse min kira kamar itace ta kirani."
shi kuwa Dr Mahmoud ido ya zura mishi,
ita kuwa Zahra fitowa tayi tare da meda k'ofar ta rufe kana ta d'an ja saki tare da cewa.
"Ai wannan motar dogayece irinshi,
haka nan ya sani tsalle."
haka dai ta nufi cikin asibitin,
tana shiga harabar cikin sai ta tsaya cas a wurin ta kalli gabas ta kalli yamma ta juya kudu da arewa sai ta rasa ina zata nufa,
gashi wurin yayi shiru sai hasken wuta,
tana tsaye a wurin sai zazzare ido takeyi sabida a take taji tsoro ya rufeta,
haka yasa ta zaro woyarta,
kiranshi tayi domin ya gaya mata ta ina suke,
amman yana jin wayar na ringing ya kuma gani itace ya kuma shareta,
sabida yasan me zata tambaya,
a ranshi yace.
"Hmmm ai gaggawarkin sai ta nuna miki wurin ki nitsu in gaya miki, kika katse min kira ai."
ita kuwa Zahra gaba d'aya tsikar jikinta ke tashi,
haka yasa ta juya da sauri da nufin zata harabar wojen ta koma cikin motar,
wani irin juyowa ta kumayi ganin wani k'aton kule bak'ik'k'in dashi ya zauna tsakiyar hanyar da zatabi d'in ya zura mata ido,
cikin tsananin tsoro tayi cikin asibitin tana,
gudu-gudu sauri-sauri,
tana zuwa inda hanyar ta rabu biyu har ta shiga gefen hagu,
sai ta kuma yi maza ta fito a guje sabida kuliyar ta kuma gani a wurin,
tana fitowa nan kuma taga gana bayantan ai cikin gudu tayi gefen dama wanda tanan Yusuf yake,
gudu takeyi tana juyowa,
ganin kulullukan suna binta a baya yasata nufi k'ofar office d'in turawa ta rink'ayi da k'arfi tare da kuka ganin suna k'ara matsota gashi sun fara irin kukansun nan na jarirai,
bubbuga k'ofar takeyi da k'arfi tare da cewa.
"Wayyo Allah, Hamma Yusuf! Hamma Yusuf!!."
cikin office d'in kuwa cikin taune lips Aryan ya kamo hannun Yusuf tare da cewa.
"Abeeh Ammi na,
Ammi tana kuka Abeeh."
sai ya kuma saki kuka shima yana yarfa hannu,
ita kuwa Zahra gaba d'aya ta gigice sai tsalle da ihu takeyi,
tuni securitys d'in sashin wurin sun nufo ta inda suke jiyo ihun nata,
shi kuwa Yusuf kukan Aryan ya sashi mik'e da sauri ya d'aukeshi tare da yin bakin k'ofar,
yayinda Dr Mahmoud ke biye dashi a baya,
yana zuwa ya bud'e k'ofar,
ai tana ganinshi tayi wuf ta shige cikin office d'in tare da komawa bayan Hamma Yusuf d'in ta rik'e rigarshi gam gaba d'aya jikinta sai bari yakeyi kar-kar
su kuwa kuliyoyin tuni sun bar wurin kamar gilmawar walk'iya,
shi kuwa Dr Mahmoud sallamar securitys d'in yayi kana ya juya cikin office d'in tare da rufe k'ofar,
wucesu yayi saida yaje gaban teburin kana ya kallesu,
sai ya kuma sunkuyar da kai tare da yin dariya ganin yadda ta gwagwume Yusuf ga Aryan dake ruggumeshi dashi sai ya zama sun sashi a tsakiya,
shi kuwa sai shiru yayi a wurin kamar an dasashi,
cikin yin dariya yace.
"Toh mai iyali ka juyo mana."
cikin sauri Zahra ta sakeshi kana ta gyara hijabinta,
sai ta kuma k'araso gaban kujerar ta zauna tare da sauk'e numfashi tace.
"Ya Mahmoud ina wuni?."
cikin d'agawa Yusuf gira d'aya alamar ya dai,
ya cewa Zahra.
"Lfy lau Zahra, ya jikin Aryan?."
Numfashi ta kuma sauk'ewa tare da cewa.
"Alhamdulillah."
shiko Yusuf gefenta yaje ya zauna domin gaba d'aya ji yakeyi k'afafunshi na rawa,
shi ko Dr matsosu yayi tare da fara dudduba Aryan yana kuma yiwa Zahra tambayoyi tana amsamishi.
"Ya dad'e da fara ciwon ne?."

"Eh tun yana jariri."

"Toh lokacin kunje asibiti ne?."

kai ta gyad'a mishi tare da cewa.
"Eh munje aka rubuta mana magunguna to daga nan ya bar'i saida aka yayeshi ya dawo."

zama ya gyara tare da cewa.
"Toh a lokacin kun kuma zuwa asibitin ne?."

cikin sauk'e ajiyan zuciya tace.
"A a bamu jeba sai aka kira wamzami ya dubashi, shine yace ai bayammace."

Tsaki ya d'an ja tare da cewa.
"Kunyi gagganci, babu wata bayamma, hainiya ce ke damunsa,
kinga da kun kuma zuwa asibiti da an tare abun."
sai ya kuma karb'i Aryan d'in daga hannun Yusuf daya zuba musu ido,
kana ya tsaidashi kan table d'in,
wond'onshi ya fara cire mishi hakan yasa Aryan k'ara sautin kukanshi cikin kula yace.
"Sorry bari in shafa maka mgni."
kai ya jinjina tare da share hawayenshi,
shi kuwa k'arisa cire wondon yayi sannan ya juyoshi gabansu yace.
"Ku ga yadda gabanshi ya kumbura."
cikin tsoro Zahra tace.
"Bai tab'a yi mishi haka bafa."
"Eh ai yanzune ya kai matakin hakan,
shiyasa yake yawan ciwon cikin."
cikin kad'uwa Yusuf yace.
"Toh yanzu me mafita?."
yawo wondon yayi ya maida mishi sannan yace.
"Yanzu zamu d'aurashi kan mgnin insha Allah nanda kwana biyar za'ayi mishi aiki."
cikin tsoro Zahra tace.
"Aiki kuma?."
kai ya gyad'a mata cikin basu k'arfin guiwa yace.
"Ai ba wani babban aiki bane, jariraima anayi musu aikin,
dan d'an k'aramine za'ayi a gefen mararshi kuma baya da matsalar komai."
haka dai yayi ta musu bayani,
kana ya rubuta mishi mgnin yaje pharmacynsu da kanshi ya sayo magungunan sannan ya dawo ya basu ya kuma rakasu har bakin motar,
saida suka tafi sannan ya juyo ya dawo.


Su kuwa tun a cikin motar suka bashi magungunan Allah da ikonshi kuma ya samu salama har ya fara zuba surutu,
kai tsaye Girei ya wuce dasu,

A gaban masallaci yayi parking ba tare daya k'arisa k'ofar gidansunba,
ganin sun isa yasa Zahra sa hannu ta tattara bakin ladan magunguna tare da mik'o hannu da nufin karb'ar Aryan d'in ,
shi kuwa Yusuf gyara zama yayi tare da cewa.
"Barshi zan tafi dashi."
ido ta zuba mishi cikin rauni tace.
"Dan Allah kayi hak'uri ka barminshi."
juyowa ya d'anyi tare da tsura mata ido cikin fesa numfashi yace.
"Wai meyasa kikeda gardama ne?".
Rau-rau tayi da ido alamar zata zubda kollah,
sai ta kuma juyo ta kalleshi kana tace.
"Aryan ni zaka bi ko?."
Kai ya juya tare da cewa.
"A a Ammi kizo kema mu tafi gidan Abeeh na."
cikin jin haushin wai yaushe yasan Hamma Yusuf da har yake sonshi haka,
ta ja d'an gajeren tsaki kana ta bud'e marfin motar tare da cewa.
"Bishi Aryan tunda kafi sonshi a kan ni, kuje nima zan d'auko Asina in rik'e ita nasan Ya Affan bazai hanani itaba."
ficewa tayi daga motar kana ta meda marfin ta rufe,
sannan tayi cikin gida.

Shi kuwa Yusuf jan motar yayi tare da mik'e hanya.

Bayan sun isa gida wonka yayiwa Aryan tare da sashi yayi al'wala sannan ya canza mishi kaya,
shima ruwan ya d'an watsa tare da yin al'wala kana ya fito,
shima ya shirya,
konciya sukayi amman alamun Aryan baya jin bacci dole Yusuf ya wartsake daga yanayin da ya fara jin yana dawo mishi.
Parlour suka fito tv ya kunna mishi sannan shi kuma ya fita harabar gidan motarshi ya bud'e tare da d'auko takardun da Zahra ta gama bincikesu d'azun.

A tsakiyar parlour suka zauna,
ganin hankali Aryan ya rabu biyu ya sashi kashe tv sannan ya matso dashi kusa tare da bashi biro cikin kula yace.
"Ka iya rubuta sunanka ai?."
dariya yayi irin tasu ta yara yace.
"Abeeh harda nakama ai na iya."
cikin jin dad'i yace.
"Yauwa to ka rubuta sunanka duk inda na nuna maka a takardun nan."
cikin nitsuwa ya kalli Yusuf tare da cewa.
"Abeeh takardun menene?."
shafa kanshi yayi tare da cewa.
"Takardun gidanka ne da makarantarka da asibitin da mukaje yanzun nan."
cikin rashin fahimta yace.
"Abeeh gidana kuma, to a ina yake?."
gyara zama yayi tare da cewa.
"Wannan gidan da muke ciki naka ne na bakashi halak malak ko nayi aure na haifi wasu yaran to su basu da gado da gidannan."
cikin rashin fahimta dai don Aryan bai kai matsayin gane zantukan Yusuf ba,
shi kuwa Yusuf yana son ginashi kan gskya shiyasa baya canza magana bare ya mishi k'ariya
a hankali yace.
"Abeeh meyasa to ka bani gidannan?."
jawoshi yayi ya d'aurashi kan cinyarshi kana yace.
"Sabida baka da gadona a shariyance,
shiyasa na yanki wani tsagi na dukiyata na mallaka maka ,
domin bani son wata rana k'annenka suyi maka zarra kan dukiyata."
cikin nitsuwa da nazari yace.
"Abeeh to ina yaran naka suke."
murmushi yayi tare da kamo kumatunshi yace.
"Sarkin tambaya to ai basu zo duniyaba tukun."
da sauri yace.
"To sai yaushe zasu zo?."
"Sai nayi aure zasu zo."
ya bashi amsa yana dariya.
shi kuwa Aryan cikin sanyi yace.
"Abeeh ka auri Ammi na mana,
kaga sai mu dawo nan duka,
gashi kullum sai Ummi tace mata wai aure dai ya gagareta,
ko yau da safe da zamu tafi gidan Tatti ce mata tayi,
sai dai tayi ta yawo ba ita ba aure kam."
shiru yayi bai kulashi ba a ranshi yake tunani ya dai yaro kamar aikoshi akeyi,
shi kuwa Aryan cikin sanyi yace.
"Dan Allah Abeeh ka auri Ammi na."
hannu yasa yana d'an bubbuga cinyar Yusuf tare da cewa.
"Abeeh ka auri Ammi na kaji ko Abeeh?."
cikin sanyi Yusuf ya gyad'a mishi alamar eh yaji
shi kuwa Aryan murmushi yayi tare da cewa.
to bani wayarka zan kira Ammina,
kafin yayi wani yunk'uri ma ya nufi bedroom da gudu yana shiga ya haura gado tare da

Please Login or Register in order to submit comment