Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Mommy ta koma bathroom ta taya Amira gyara jikinta,
ita kuwa Ummi da Rafi'a zama sukayi kan kujerar dake gaban gadon,
Adda Zulaihat kuwa gefen Zahra ta zauna tare da kamo tafin hannunta tana mai ci gaba da kuka,
shi kuwa Dr ya duk'ufa aiki don ya samu ta farfad'o.



A gidan mai kuwa,
Yusuf ne ke tahowa a hankali cikin taune lips d'inshi dan azabar da yakeji har ya dawo inda motarsa take,
cikin rawan jiki ya bud'e motar ya shiga zama yayi tare da kife kanshi jikin siterin motar,
tunda yake a rayuwarsa ta duniya ciwon mararshi bai tab'a sashi kukaba sai yau,
kuka yakeyi tare da taune lips enshi,
yana ji ana bubbuga mishi glasses d'in motar amman ya kasa d'agowa,
yana kuma jin tirelan gabanshi nan taja ta tafi alamun an d'ura mata mai shine a kan layi amman ya gaza d'ago kanshi sabida wani irin azabebben kuka da yakeyi,
ji yakeyi ko in yayi kukan zaiji sauk'i,
bud'e marfin motar da akayi ne ya sashi tsagaita kukanshi tare da jawo rigarshi ya sharte hawayenshi da zufar dake fito mishin,
muryan Jafar yaji yana cewa.
"Hamma Yusuf lfy kuwa,
kainefa a kan layi kaja motar kayi gaba,
nine nake binka a baya in kasha sai nima in sha."
shiru yayi sabida yadda yaga idanun Hamma Yusuf d'in nashi sunyi azabar ja tamkar zasu amayar da wuta,
ga jijiyoyin kanshi da sukayi rud'u-rud'u uwa uba yadda jikinshi yake rawa kamar mazari,
a firgice yace.
"Subahanallahi Hamma Yusuf make damunka."
cikin wata iriyar murya yace.
"Marata Jafar marata."
da sauri Affan ya k'araso wurin sabida tuni sun sha mai,
mutanen dake bayan Yusuf da Jafar kuwa suna bi ta gefen motarshi suna zuwa ana dura musu,
Affan kuwa ganin Yusuf a haka ba k'aramin firgitashi yayiba,
Jafar ne ya mishi bayanin abinda Yusuf d'in yace yana damunshi,
jin haka yasa Affan yacewa Jafar.
"Toh kai Jafar ja motarka kaje kasha mai d'in."
sai ya kuma kalli Yusuf cikin tausayawa yace,
"Sorry Yusuf daure ka koma wancan sit d'in bari Baba sani yazo yaja motar taka."

haka kuwa akayi bayan duk sun sha mai d'in sai suka gangaro inda su Affan suke,
suna isawa Affan ya fito cikin motarshi hannunshi rik'e da takardun da Yusuf zaisa hannu,
ta inda Yusuf yake ya zagayo tare da d'an sunkuyowa yana mai cije lips enshi dan yanayin da yakeji,
takardun ya mik'awa Yusuf d'in,
karb'a yayi tare da bud'esu ya fara sa hannu,
ba tare daya dago ya kalli Affan dake tsaye gefenshi ba,
har saida ya gama sa hannun sannan ya mik'awa Affan d'in takardun tare da cewa.
"Gashi na saka."
sake maimaitawa yayi jin Affan bai tanka mishiba kuma bai karb'a shi yasashi d'an d'ago kanshi,
da sauri ya meda kallonshi inda yaga Affan ya zubawa ido a jikinshi,
fuska ya tsuke tare da jawo rigarshi daya d'age tun d'azu lokacin da zai goge hawayenshi,
rigar ya kuma ja da k'arfi ya rufe saitin kan joystick d'inshi inda yaga nanne Affan ya k'urawa ido
shi kuwa Affan sai lokacin ya dawo daga duniyar kallon da yakeyiwa halittar Yusuf d'in kanshi ya d'an sosa tare da amsar takardun cikin jin kunya kamashi da Yusuf yayi yana kalle mishi tudu da girma da tsawo abinda bai kamata ya kallaba,
juyawa yayi tare da cewa.
"Babba sani kaishi gida."
cikin wani irin yanayi Yusuf yace.
"A a ya bari zan iya tuk'i."
shi kuwa Affan wani irin kallo yayiwa Yusuf na 47 seconds sannan ya juya kanshi tare da cewa.
"OK Baba Sani zomu tafi."
a ranshi kuwa cewa yayi.
"Jarabebben manza sai masifa kana nan kamar doki."
su Affan na tafiya Jafar yazo zai mishi sai anjima,
dai-dai lokacin kuma kiran Aryan ya shigo woyar Yusuf,
sherata yayi tare da kallon Jafar da ya iso bakin marfin motar,
shi kuwa Affan d'an lek'owa yayi tare da kallon fuskar wayar Hamma Yusuf d'in nashi cikin sanyi yace.
"Hamma Yusuf Ya Aryan nefa ka d'aga mana."
tsaki ya d'an ja tare da amsa kiran,
cikin tarin bak'in ciki Aryan ya gaya mishi abinda ke faruwa,
tare daci gaba da cewa.
"Yusuf har yanzu Zahra bata farfad'oba,
please duk inda kake kazo ni ban san tayaya zan gayawa Daddy cewar an anyiwa Zahra wannan ta'asarba."
wani irin zabura Yusuf yayi yayinda yaji k'ahon zuciyarshi tana shirin tarwatsewa, sabida azabar fargaba da tsinkewar zuciyanshi daya ninku sau saba'in akan yadda yakeji d'azun
ida nunshi ya zaro yayinda gaba d'aya jikinshi yake rawa,
sakin woyar yayi tare da komawa mazaunin direba,
ba tare daya saurari Jafar dake gefenshi ba ya fizgi marfin motar da Jafar ke rik'e da ita,
cikin wani irin yanayi ya figi motar tamkar wanda zai tashi sama,
Jafar kuwa da ya koma baya da gudu ganin kamar Yusuf zai takashi,
ido ya zaro ganin irin yadda Yusuf ya karya kwana ya shiga layin gidansu Aryan d'in
ganin haka shima Jafar ya shiga tasa motar yabi bayan Yusuf d'in a guje.

Kusan a tare suka isa kai tsaye part d'in Yusuf suka nufa sabida Aryan ya gayawa Yusuf a side d'inshi suke,
shi kuwa Jafar bayan Yusuf d'in kawai yake bi.

Suna shiga kai tsaye bedroom sukayi tunda sun jiyo alamun a can suke,
dai-dai lokacin da suka shiga yayi dai-dai da lokacin da Zahra ta farfad'o tare da sakin wani gigitaccen k'ara sai ta kuma komawa ta sume.
Dr Rabi'u ne ya sharte zufar dake goshinshi sabida firgici da aikin da yakeyi yasa zufar tsatstsafo mishi,
Aryan kuwa yana isowarsu yayi saurin matsowa inda Yusuf ke tsaye,
a gaban Ummi da take waya da Daddy tana shaida mishi abinda ya faru da kuma halin da suke ciki a yanzu,
sakin wayar tayi ta sulo kan cinyarta ita kuwa tafin hannunta tasa tana share hawayenta da yak'i tsayuwa,
shi kuwa Yusuf komawa yayi ya jingina da jikin gini tare da rumtse idanunshi gaba d'aya k'afafunshi rawa sukeyi kamar mazari hakan yasa bazasu iya d'aukan nauyinshi ba dole tasa ya jingina da ginin,
ya kasa cewa kowa komai,
sai zuciyarshi da yakeji tana wani irin harba da sauri-sauri tana wani irin bugu.

Jafar kuwa tuni sai kuka yakeyi cur-cur da hawaye,
sabida duk k'annenshi yafi d'asawa da Zahra yana sonta har ranshi yama fi jin sonta a kan su Zeenat d'in da suka fito ciki d'aya.

ita kuwa Adda Zulaihat har yanzu kuka takeyi,
Amira kuwa zuwa yanzu murd'awar da cikinta yakeyi ya d'an lafa.


A karo na biyu Zahra ta kuma farfad'owa sai dai yanzu bada ihu ta farfad'oba,
fizge-fizge takeyi yayinda take ta maimaita magiyar da tayi lokacin da ake mata fyad'e.
Adda Zulaihat ce ta matse hannun Zahra dake cikin hannunta cikin muryar kuka tace.
"Zahra bud'e idonki kinji ki bud'e idonki babu wanda zai sake cutar dake gani ga Amira ga Ummi ga ya Aryan."
bata k'arisa jero sunayen nasuba tayi shiru sabida ganin Zahran ta bud'e idon,
d'aya bayan d'aya tayi ta binsu da ido,
yayinda hawaye ke tsiyaya ta gefen ida nunta,
Ummi ta kalla sai ta kuma fara yunk'urin tasowa tare da mik'owa Ummin hannu,
da sauri sukayo kanta,
sai kuma duk sukayi saurin isewo inda take sabida wani ihun da ta kurma sannan ta kuma komawa konce ta sume.

Wannan al'amarifa ya girmama,
gaba d'aya hankalinsu a tashe yake yarinya sai ta farfad'o sai ta kuma sumewa,
cikin kuka Ummi ta juyo ta kalli Yusuf da ya zama tamkar an dasashi,
tace.
"Yusuf ku samin ita a motar Jafar mu wuce gida da ita."
sam Yusuf kam ya gaza motsawa daga inda yake,
shi kuwa Jafar yana jin haka ya sunkuyo ya ciccibi Zahra yayi hanyar fita da ita,
da sauri Adda Zulaihat tabi bayanshi,
Aryan kuwa idonshi na kan Yusuf ya fara mgna,
"Ummi ai da nan da can duk d'aya ne kawai da asibiti zamu wuce da ita zaifi akan a tafi gida da ita."
yana mgnar da Ummi ce amman gaba d'aya hankalinshi da idanunshi kan Yusuf suke wani irin kallo yake yiwa Yusuf kallon da yake k'unshe da ma'anoni da dama,
ita kuwa Ummi kai ta jinjina tare da kallon Aryan tace.
"Ba komai Aryan gwara muje gida Daddynku ya dubata."
tana fad'in haka tabi bayan Jafar,
yayinda Amira da Kakama sukabi bayanta,
Mommy ce tayi k'arfin hallin kallon inda Faisal ke tsaye ruggume da Raihana da taci gaba da kukanta ganin an tafi da Zahra kamar gawa,
itama Mommy hawaye ta share tare da cewa.
"Faisal d'auki matarka ku tafi,
kuje da Rafi'a ta rakaku."
jin haka yasa Faisal jan hannun Raihana suka fita Rafi'a na biye dasu a baya ita kuwa Raihana sai kuka takeyi tana cewa Faisal.
"Honey shike nan ya kasheta,
Honey ka barni inbi su mana inga halin da take ciki,
Honey sanadinmu nefa komai ya sameta bikinmu ne sanadi."
jawo hannunta yayi suka shiga motarshi sannan Rafi'a ta shiga baya jawota yayi ya mannata da kafad'arshi yayinda ya fara tuk'i da hannu d'aya cikin lallashi yace.
"Kiyi shiru my dear insha Allah sai an hukuntashi hukunci na Allah a kan wannan zalumci da ya mata."
haka dai suka fita suka tafi.


Ummi da Hajia Kaka sune a bayan motar Jafar tare da Zahra sai Adda Zulaihat dake gaba Sharifa na kan cinyarta,

Mommy kuwa Amira ta tallabo tare da cewa Aryan,
maza muje.
toh Aryan yace sannan yayi gaba suna binshi a baya,

Safwan ma sauri yayi ya bisu a baya,

Aryan ke jan motar yayinda Safwan yayi uwa makarbiya ya shiga gaba gefen Aryan Mommy da Amira kuwa suka zauna a baya.

Cikin tsananin jimami suka nufi cikin Girei.


A can Girei kuwa kasancewar yau weekend yasa Daddy daga filin d'aurin aure gida ya dawo,
inda ya samu Abba baya nan duk da dama yasan da tafiyar tashi,
tunda ya dawo ya haura sama ya shige bedroom nashi babu abinda ke sauk'o dashi sai zuwa masallaci.

Abba kuwa sai bayan sallan la'asar ya dawo daga Jada
inda shima ya shige side d'inshi domin watsa ruwa sannan ya d'an huta.

Aunty Amarya kuwa bayan ta gama aikinta duk taje tayi wonka ta d'anyi kolliya sama-sama sabida duk ji take jikinta a mace.

Itama Mama saida ta gama aikinta sannan tayi wonka ta shige side d'in Abba don gyara mishi,
tana shiga ta fara gyaran ba jima ta gama,
sannan ta konta a parlour shi ta kontan kenan ya shigo ya dawo daga Jada d'in to tunda yayi wonka ya fito suna zaune a parlour shi suna d'an tab'a hira sama-sama.


Aunty Amarya kuwa cikin sanyin jiki ta haura sama wurin Daddy,
da sallamanta ta shiga sai dai bai amsa mataba,
gefenshi ta zauna sabida taga yana woyane sai dai ko k'ala baya cewa,
sai fuskarshi da taga ya canza sai kuma taji yace.
"Subahallahi Ummin Jafar meke faruwa meya saki kuka."
wata iriyar zabura Aunty Amarya tayi ganin yadda Daddy ya mik'e tsaye lokaci d'aya kuma taga fuskarshi tayi jazir lips enshi sai rawa sukeyi alamun yana sonyi mgna amman ta kasa fita,
matsoshi tayi cikin tsananin tsoro take tambayarshi,
"Dr Lfy kuwa make faruwa."
sakin wayar yayi ta fad'a k'asa,
sai kuma ya fara wani irin tari cikin k'arfi ya fizgo kalmar.
"Innalillahi wa inilaihi raji'un."
ganin yadda yaketa tari sai addu'o'i yakeyi yasa Aunty Amarya ta nufi hanyar sauk'a tare da sassarfa take taka steps d'in yayinda kuma take ta rabkawa Abba da Mama da Hajja inna da Sulaiman kira.
"Yaya! Maman Yusuf! kicewa Yaya yazo Daddynsu Jafar ba Lfy fa,
Sulaiman ina kake ne,
Hajja Inna kizo."
kusan a tare suka fito gaba d'ayansu,
Abba shine a gaba yayinda Sulaiman ke binshi a baya ,
sannan su Maman.

Da sauri Abba ya jawo hannun Daddy ya zaunar dashi kan sofa tare da cewa Sulaiman.
"Kai mik'o ruwa yasha."
To Sulaiman yace tare da mik'o gorar ruwan faro,
da sauri Abba ya amsa tare da bud'ewa ya sawa Daddy a baki,
ba musu ya karb'a tare da shan ruwa kad'an don ko zaiji zafi da d'aci da turiri da zuciyarshi keyi zai ragu,
babu wanda zai san yadda Daddy keji sai uban daya tab'a fuskantar jarrabar wani ya lalata mishi 'yarsa,
gaba d'aya zama sukayi ganin tarin ya lafa sai fuskarsa da tayi jazir alamun tsananin bak'in cikin duniya,
cikin fargaba Hajja Inna tace.
"Kai Aliyu meke faruwa?."
sai lokacin Daddy yaji wani irin d'aci ya sake mamaye mak'ok'oronshi,
sai idonshi da suka k'ara kad'awa sukayi jazir,
Abba ne ya sake ce mishi.
"Kai Aliyu ka gaya mana meke faruwa."
lokaci d'aya Daddy yaji wani irin karaya da tarin bak'in ciki kawai sai yafara mgna cikin rawar murya yace.
"Zahra..!."
cikin kad'uwa da tsoro suka had'a baki wurin cewa.
"Meya faru da Zahran?."
Sulaiman kuwa tuni ganin yadda Daddy ke mgna yasa tausayin mahaifinshi ya sashi zubda hawaye,
cikin fad'a da d'an d'aga murya Abba ya kuma cewa.
"Meya samu Zahran?."
cikin tarin bak'in ciki Daddy yace.
"Zahra Yaya an lalata min rayuwar Zahra anyi mata fyad'e a gidan biki."
Innalillahi,
ai fad'in halin da wannan ahli suka shiga bazai yuwuba,
Aunty Amarya kam zamewa tayi k'asa dirsham ta saki wani irin marayan kuka yayinda numfashinta ke shirin barin jikinta,
Maman Yusuf ce tayi saurin zama kusa da ita yayinda itama kuka takeyi shar-shar da hawaye,
Abba kuwa mik'ewa yayi yayinda gaba d'aya jikinshi ke wani irin rawa da tsuma idanunshi kamar zasuyi aman garwashi gaba d'aya jikinshi rawa yakeyi hatta lip's enshi,
cikin wata iriyar murya mai ban tsoro yace.
"Fyad'e? akayiwa d'iyar d'an uwana waye shi? a ina yake? waye mahaifinshi? lallai yayi kuskure mafi muni a rayuwarsa ta duniya,
tunda yayi gigin tab'a jinin Al'k'ali Muhammad Usman Girei,
ni ko yayan mutanen da ban saniba ina bi musu hakk'insu bare yar d'an uwana,
ko d'iyar mak'otana wani yayi gigin tab'awa to har abada bazai sake gigin tab'a ko katangar gidanba,
Lallai za'ayi shariyar da HUKUNCIN ALLAH COURT zatayi nasarar binciko duk mai sa hannu a cikin wannan ta'asar
ko waye shi tabbas sai na hukuntashi."
gaba d'aya Abba ya birkece fad'a yakeyi tamkar zai bugi babu dan azabar tafasa da zuciyarshi keyi.
Sulaiman kuwa juyawa yayi a guje ya sauk'o k'asa parlour Ummi ya koma key d'in motarshi ya zara tare da ficewa da nufin zai je gidansu Aryan d'in.
Hajja Inna kuwa kai ta jinjina tare tab'e baki tace.
"Shike nan an b'ata min sunan zuriya,
bayan yaro mai dukan kakarshi ga kuma karuwa an samu ai dama wannan yarin rawan kantan nan kam sai dai hakan."
wani irin kuka Aunty Amarya tasa sabida jin furucin surkar tata,
Mama kuwa cikin matuk'ar mmki take bin Hajja Inna da ido ashe mutun zai rink'a yiwa jininsa mugun baki da fata mara kyau,
shi kuwa Abba sabida zafin halin da yake ciki sam baiji furucintaba,
Daddy kuwa sai kanshi yake juyawa alamun a a Zahranshi ba karuwa bace.

Ita dai Hajja Inna fita tayi ko a jikinta.

Shi kuwa Sulaiman yana zuwa harabar gidan ya tsaya sabida ganin motar Jafar da Aryan suna yin parking a farfajiyar gidan.

Wani irin kuka Sulaiman ya farayi lokacin da yaga Jafar ya tallabo Zahra ya fito da ita tamkar matacciya sai rito hannayenta keyi,
Zulaihat kuwa ganin haka sai rauninta ya k'aru ta saki wani irin kuka,
gaba d'aya sai suka rud'e da kuka,
jin gidan ya rud'e yasa Mama lok'owa ta window ganinsu yasa ta juya a guje tayi hanyar fita tare da cewa su Abba.
"Gasu nan sun dawo."
ai gaba d'aya a jere suka sauk'o,
yayinda su kuwa Jafar ke ruggume da Zahra bai tsaya da ita ko inba sai parlour Hajja Inna da yake tsakiyar gidan,
gaba d'ayansu suka shigo parlour,
matan duk sai kuka sukeyi yayinda Sulaiman ke tayasu domin shi yanada raunin zuciya,
Jafar kam tuni hawayenshi ya k'age cikin cushewar sauti yace.
"Daddy zoka duba Zahra a sume takefa."
jin haka yasa Daddy matsowa ya fara dubata,
Abba kuwa tuni sun fita suna babban parlour k'asa shida Aryan,
inda yaketa yiwa Aryan d'in tambayoyi kan al'amarin.


Cikin sa'a Daddy ya samu Zahra ta farfad'o,
yayinda sai ido take binsu dashi d'aya bayan d'aya,
tana ganin Mama a gefenta sai hawayenta ya tsananta,
hannu ta mik'owa Mama ganin haka Maman tayi maza ta ruggumota tare da sakin kuka,
Aunty Amarya kuka kife kanta tayi jikin Hajiya kaka,
kakarsu Aryan kenan,
wani irin kuka takeyi yayinda kaka keta lallashinta,
Mommy kuwa Mama taketa lallashi tana cewa.
"Lallai kam duk wata uwa ta gari babu wani abu da tafi fargaba a rayuwar yarta budurwa kamar wannan kaddara,
toh amman ya zamuyi k'addara ta riga fata,
dan Allah ku dena kuka ai saiku k'ara tayar mata da hankali."
haka dai tayi ta basu hak'uri har suka d'an tsagaita,
Daddy kuwa alluran bacci yayiwa Zahra sannan ya d'aura mata drip,
cikin k'ank'anin lokaci tayi bacci,
ganin tayi baccine yasa duk suka d'an samu nitsuwa,
al'wala sukayi ganin tuni su Abba sun tafi masallaci yin sallan mank'arib,
suma sallan sukayi sannan su Kaka suka bawa Abba labarin da Raihana ta basu.

A gidan Amarya kuwa Mami da Nana su dama sunbi sahun motocin da sukayi tafiyan forko,
so basu san meke faruwaba,
saida Raihana taje ne ta ruggumi Mami tana kuka ta shaida masu abinda ya faru,
ai birkicewa Raihana sukayi dole tasa Faisal ya dawo dasu,
daga nan mgnar fyad'an da akawa Zahra ya bazu a gun yan biki.

A Girei kuma Daddy ne ya kalli Aryan cikin tarin damuwa yace.
"Aryan d'auki su kaka ku koma dere ya fara nisa."
Cikin sanyi Aryan yace toh,
sannan ya d'auki Kaka da Mommy ya koma dasu tare da Safwan,
saida suka komawa Safwan ya d'auki motarshi ya tafi.

Zahra kuwa a parlour Hajja Inna ta kwana sai Mama da ta baro d'akinta tazo ta kwana da ita,
Ummi kuwa dama suna dawowa ta wuce side d'inta
ita da Amira Adda Zulaihat kuma Abubakar yazo ya d'auketa inda ta tafi tanata kuka.

Aunty Amarya kam kwana tayi tana kuka yayinda Daddy kuwa yakeji kamar zai mutu dan bak'in ciki.

Shiko Abba a daren ya rubuta takardar sammaci zuwa ga Idris da nufin gari na wayewa zai bawa maga takarda ya kai mishi takardar gayyata daga kotun Hukuncin Allah.


Yusuf kuwa Al'amarinshi ya girmama,
domin bayan sun firfita dukansu Dr Bashir ma yabi bayansu ya tafi side Aryan,
cikin gida kuma gaba d'aya mutanen biki sun watse da kanun labaran fyad'en da akayiwa Zahra.

Shi ko Yusuf tunda suka fita ya rage shi d'aya a d'akin wani irin,
azabar sarawa kanshi ya fara kuka yakeso yayi kamar d'azu amman abin ya gagagara babu abinda yakeyi sai tattaune lips d'inshi yakeyi wad'anda tuni sun kumbura sunyi jazir sai shek'i sukeyi ida nunshi sun k'ank'ance sunyi jazir gaba d'aya jijiyoyin jikinshi sunyi rud'u-rud'u hatta jijiyar goshinsa ta taso tayi zuwat har zuwa kan hancinsa,
wani irin bak'in cikin duniya yakeji,
ji yakeyi dama ya mutu ya huta kawai.

Tunda suka tafi bai matsa inda yakeba sai zamewa da yayi ya zauna a k'asa dirsham sai rawan sanyi da yakeyi ga wani irin azabebben zazzabi da yakeji tamkar ana sassara mishi k'asusuwanshi,
sanyi yakeji tamkar zai kasheshi amman ya gaza tashi sai karkarwa yakeyi
yana cikin wannan halin Aryan ya shigo bedroom d'in,
tafiya yakeyi cikin wani irin yanayi,
yayinda ya tsurawa Yusuf idanunshi gaba d'aya,
gaban Yusuf yazo ya tsaya cikin rumtse ido ya tsuguna gaban Yusuf d'in yadda zasu kalli fuskar juna da kyau,
ido ya k'urawa Yusuf
yayinda shima d'in Yusuf Aryan d'in yake kallo cikin wani yanayi,
shi kuwa Aryan gyaran murya yayi cikin sauya kala daga Aryan ya koma wani kala wuyar rigarshi ya gyara tare da tsare Yusuf da idanu cikin kausasa murya yace.
" Yusuf!."
ido Yusuf ya zuba mishi ba tare daya amsaba,
shi kuwa Aryan cikin wani kalan fuska da Yusuf bai sanshi da shiba yace.
"Yusuf ina zargi kai ne kayiwa Zahra fyad'e!."
wani irin wawan zabura Yusuf yayi tare da mik'ewa idanunshi kamar zasu zazzago su fad'o k'asa ya rink'a nuna Aryan tare da jujjuya kanshi cikin kad'uwa da alamar,
anya kuwa kasan abinda kake fad'i,
lallaima Aryan ka cika mai mummunan zato,
shi kuwa Aryan cikin cije lips enshi tare da k'ank'ance idanunshi cikin rashin mutunci yace.
"Meyasa zaka yiwa Zahra fyad'e,!? me tayi maka daka wareta cikin dubban yan matan duniya kayi mata fyad'e!?."
zuwa yanzu abin ya zarta tunanin Yusuf domin ganin Aryan yakeyi kamar hoto,
hannu yasa ya rink'a dukan kanshi wai ko zai farka daga wannan mummunan mafarkin da yakeyi domin yasan Aryan d'inshi bazai mishi hakaba,
shi kuwa Aryan juyawa yayi tare da fara tafiya cikin izaya yace.
"Lallai kam gwara ka adana kalamanka domin zasu maka amfani a kotu,
ba mmki ka zakayi zaton zaka iya wonke kanka daga zargin da kotu zata maka."
yana fad'in haka ya fice cikin yin wani mugun murmushi,
shi kuwa Yusuf bathroom ya shiga ya sakarwa kanshi ruwa wai ko zai dawo hayyacinsa,
amman ina abu yaci tura,
wonka yayi,
bayan ya fitone ya shimfid'a sallaya ya fara jera nafilfili,
a cewarsa koma a mafarkine yakega wannan bala'in dake shirin turnik'e rayuwarsa gwara ya fuskanci ubangiji domin shine mai kub'utar dashi,
haka ya kwana kan sallaya koda asuba tayi bai samu yaje masallaciba dan azaban zazzabin da yakeji,
a gida yayi salla sannan yaci gaba da karatun kura'an.

Shi kuwa Aryan yana idar da salla ya d'auki Kaka suka tafi Girei,
bayan ta shiga cikin gidane shi kuwa ya wuce parlour Abba,
bayan sun gaisa ne ya kalli Abba cikin wani yanayi yacewa Abba.
"Abba ka gafarceni,
duk da kasancewata lawyer amman na gaza kare Zahra daga farmakin da nake zargin Yusuf ne ya kai mata."
cikin wani irin yanayi da juyewar kamannin fuska Abba ya kalli Aryan sai kuma yace.
"Wanne Yusuf d'in kake nufi?."
cikin tsaurin ido Aryan yace.
"Yusuf Muhammad Usman Girei,
ina nufin Yusuf d'inka dai,
shiyasa ma tun jiya na shigar da k'ararshi a Criminals court ba mamaki zuwa yanzu takardar sammacin ta isa gareshi,
in yaso ya wonke kanshi a Court."
gaba d'aya Abba kam mutuwar zaune yayi,
saida yaji k'arshen mgnar Aryan sannan ya gyara zamanshi tare da jawo stol d'in gabanshi takardun kan wurin ya dudduba yayinda duk jikinshi rawa yakeyi,
domin zuwa yanzu shida Aryan ba mgna ta tsakanin uba da d'a sukeyiba,
mgnace ta tsakanin lawyer da al'k'aline
mgna d'aya zaiyi kan rashin amincewa da zargin Aryan,
zai sa suyi zaton karewa Yusuf yake sonyi kuma wannan ba k'aramar matsala zai jaza mishiba
cikin sanyi ya jawo wayarshi yayi k'ira,
bayan wasu minutes sai ga wani dottijo ya shigo parlour Abban,
cikin sanyin jiki Abba ya bashi takarda guda d'aya sannan yace.
"Maga takarda ga wannan a kawai adireshin a cikin takardar ka kaiwa Idris na shopping complex."
cikin girmamawa maga takardan ya karb'a ya tafi,
shi kuwa Abba cikin yak'ini da k'arfin zuciya yacewa Aryan.
" Ni kuwa ga sa hannuna matuk'ar court d'inku ta tabbatar da zarginku a kan Yusuf,
ku turoshi k'ark'ashin court d'inmu
duk mai laifi tsakanin shida Idris wanda zamu tuhuma a court d'inmu nayi al'k'awarin zan mishi hukuncin Allah,
zan kuma horashi k'ark'ashin umarnin kotu ta yadda har abadan bazai sake gigin aikata hakaba."
cikin jin dad'i Aryan ya mik'e tare dayin wani irin murmushi sannan ya salami Abba ya fita.

Tunda sanyin safiya Messenger criminals court ya isa gidansu Aryan
domin su tun jiya da dare Aryan ya shigar da k'arar k'ark'ashin hukumar kare hakk'in d'an adam.

Yusuf kuwa yana zaune a inda ya kwana yaji muryar Baba mai gadi yana sallama,
bai iya d'aga murya ya asma sallamarba sabida yanayi halin da yake ciki,
jin shiru yasa Baba mai gadi cewa.
"Yusufa wani ke nemanka yance min shi d'an aikene,
jin haka yasa Yusuf mik'ewa cikin k'arfin hali yake tafiya lokaci guda kuma bugawar zuciyashi ke k'arawu,
tare suka fito da Baba mai gadi
a bakin gate suka tsaya inda messengern criminals court d'in yake tsaye,
gaban Yusuf yazo tare da mik'a mishi hannu suka gaisa,
sannan ya mik'a mishi takardar ya juya yayi tafiyarsa,
cikin tafiya a hankali shima Yusuf ya juya ya koma side d'inshi,
a parlour ya tsaya tare da rumtse idonshi sannan ya zauna kan sofar yana mai bud'e takardar,
cikin wani irin zabura ya mik'e tsaye tare da cewa.
"Aryan......!"




📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



*HUKUNCIN ALLAH*


Page3⃣1⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*



🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




Kasa furta abinda yazo kan harshen shi yayi, sai hannunshi yasa ya dafe k'ahon zuciyarshi dake barazanar fashewa, gaba d'aya jikinshi wani irin tsuma yakeyi hatta lips D'inshi rawa sukeyi, idanunshi ya rumtse da k'arfi tare da kamo lips enshi duka biyu ya taunesu da k'arfin bala'i, komawa yayi ya zube kan sofa d'in sabida rawa da jikinshi keyi k'afafunshi bazasu iya d'aukar nauyin jikinshi ba, wata iriyar zazzafar zufashe ta keto mishi daga tsakiyar kanshi har zuwa babban yatsarshi,
kai ya rink'a jujjuyawa cikin ranshi da zuciyarshi yake k'aryata takardar sam yana zancen zuci.
"No..! Imposible ! Is not my Aryan.. sam Aryan

Please Login or Register in order to submit comment