Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Jafar cikin yin ajiyan zuciya yace.
"Kai kuma Jafar ka kyauta."
cikin kauda kai Jafar yace.
"Abba ai dole in kare d'an uwana."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Yayi kyau tashi kuje,
gobe ku shirya dan da wuri zamuje Court dan itace shariya ta forko da za'a gudanar."
a tare suka mik'e tare da cewa,
"To Abba Allah ya kaimu."
Amin yace tare da binsu da ido yana jin tausayin Zahra na ratsashi.


Suna fitowa sukayi kicibis da Tatti Maman Aunty Amarya,
Zahra na ganinta ta fad'a jikinta sai kuma ta saki kuka cikin jin tausayin jikar tata tace.
"A a kar kiyi kuka Zahra,
ki dage kici jarrabar da Allah ya jarab ceki,
in sha Allah wata rana zakiyi farin ciki."
sai kuma ta jawo hannunta suka nufi part d'in Mama,
cikin karamci da mutuntaka suka gaisa nan suka had'u Mama da Tatti sukayi ta yiwa Aunty Amarya fad'a da nasiha,
Amman sai kuka takeyi tana cewa ita dai bata son ganin Zahra da cikin ne,
aifa nan Tatti tayi ta mata fad'a sai da taga ran mahaifiyarta ya b'acine tace to,
ba komai.

Kusan a gidan Tatti ta wuni,

Su Goggo Zahra ma duk sun zozzo sunyiwa Hajja Inna nasiha ta dena gorantawa Zahra da bin gidajen mak'ota tana gaya musu,
amman ina kamar zugata sukayi,
domin suna tafiya ta d'aura daga inda ta tsaya,
gida-gida ta rink'a bi tana gaya musu gobe za'a yanke hukunci a kotu suje su gani,
yayinda take jawo wasu har gida wai suzo suga cikin Zahra,
Zahra kuwa rayuwa tayi tsanani tayi kuka har saida fuskarta ta kumbura,
Raihana da Dija chiroma sunzo suma sukayi ta rarrashinta.

Amman Abin mmki Aunty Fadwa da Salimanta basu zoba tunda abin ya faru haka sauran k'awayen Zahra duk sun gujeta sai Dija ce kad'a ke zuwa susha kukansu tare.

Washe gari ta kama ranar za'a shiga court...








*By*
*GARKUWAR FULANI*


jwbl







8:12 Am tanayi mutane suka fara ciccirind'o a harabar court d'in,
kama daga matasa tsoffi mata na nesa dana kusa,
sashin yan jaridu kuwa zancen ya tumb'atsa,
hakan yasa suma sunyi dafifi yayinda suke jiran ace musu kule suce cas.

Kafin zuwa 8:55 Am harabar wurin tayi mak'il da bani adam harma da wasu sashi na halitta,
9:00 Am Al'K'ali Muhammad Usman Girei ya fito daga office nashi cikin shiri,
ya nufi cikin d'akin taron,
nanfa aka fara shiga cikin court d'in kafin kace kobo anyi mak'il duk yawan kujerun dake cikin hall d'in nan sun cika da mutane yan kallo,

Bayan Abba ya zauna sai sauran mutane duk suka zauna aka nitsu kowa ya baza na zokonshi,
yayinda layin gaba duk ahlin da abin ya shafane.
Daddy, Sulaiman, Jafar, Faisal, Ibrahim, sai uncle Gambo da Sani yan uwan Aunty Amarya kenan,
sai su Adda Zulaihat, Hajia Kaka, Raihana,
yau kam abin ya ta'azzara domin harda Mama cikin jerin tawagar masu gani ya kori ji,
wanda Abba ne ya matsa a kan taje a dole.


Bayan shiru ya d'an gibta na yan wasu seconds sai kuwa,
Messenger su ya mik'e cikin nitsuwa ya fara gabatar da k'arar da za'a saurara,
kanshi ya sunkuyar yana mai jin tausayin Abba,
domin ace ana tuhumar d'anka kuma kaine mai yanke hukunci abin da ciwo,
bayan ya gabatar da k'arar ya matso ya mik'awa Abba tarin takardu sannnan ya koma ya zauna,
gyara zama Abban yayi tare da gyara zaman gilashi idonshi hab'ar babbar rigarshi ya tattaro cikin wani irin sautin da Mama bata tab'a jinshi da itaba yace.
"Ina lawyer mai k'ara da wanda ake k'ara?."
da sauri Aryan ya mik'e tare da matsowa gaban court kanshi ya d'an rusunar domin sam kunyar had'a ido da Abba yakeyi,
kuma hakan bazai hanashi ida k'udurinshi ba cikin tsaurin ido ya gabatar da kanshi.
"Sunana barrister Aryan nine lawyer mai shigar da k'ara."
kai Abba ya jinjina alamun gamsuwa,
sannan Affan ya mik'e cikin k'unan rai da jin tsanar Aryan ya matso gaban court murya a raunace yace.
"Sunana Barrister Affan nine lawyer mai kare wanda ake tuhuma."
shima kai Abba ya jinjina mishi,
sannan daga nan aka shiga fafatawa,
Aryan ne ya fara jawabi da rok'o.
"Ya mai girma mai shariya, ina rok'on wannan Court mai adalci datayi duba eh zuwa ga hujjojina,
sannan ina neman alfarma kotu tasa a nemo yarinyar da akayiwa fyad'e domin itace babbar shaidata kuma ta k'arshe."
cikin nitsuwa Abba yace.
"Court zata so sanin k'ananan hujjojin naka kafin gabato da babbar hujjar."
cikin wani irin salon taku mai cike da ma'anoni Aryan ya taka i zuwa tsakiyar wurin cikin d'an d'aga sauti yace.
"Ranar 4 ga watan 1 shekara ta 2015,
ta kasance ranarce Yusuf yayiwa Zahra fyad'e."
cikin d'aga sauti Affan ya mik'e tare da cewa.
"Objection ya mai girma mai shariya,
Barrister Aryan ya gyara kalamanshi,
har yanzu dai zargin Yusuf akeyi,
dan haka baida damar cewa Yusuf ne ya mata fyad'en kai tsaye."
kai Abba ya jinjina tare da cewa.
"Barrister Aryan ka kiyaye."
murmushin mugunta Aryan yayi tare da rusunar da kanshi yace.
"toh ya mai shariya."
shi kuwa Affan rusunar da kanshi yayi tare da cewa.
"Ngd ya maishariya."
cikin k'arfin zuciya Abba yace.
"Menene hujjarka nashi ya aika fyad'en?. "
daga nan sai Aryan yaci gaba da cewa.
"Hujjojina suna da yawa,
na forko dai,
na zargi Yusuf ya dawo gida bayan ya fita,
domin naji haniniyar dawakanshi wad'an da sai in shi suka gani suke irin wannan haniniyar."
dan sauri Affan ya mik'e tare da cewa.
"Objection ya Mai shariya kowa fa yaji da kunnenshi,
barrister Aryan zargi yayi Yusuf ya dawo,
bai tabbatar ba,
inko ya tabbatar to ya sanar mana?."
a nitse Abba yace.
"Barrister Aryan shin kaka Yusuf da idanunka ne ko zargine?."
kai Aryan ya jiya tare da cewa.
"Ban ganshi da ida nuna ba amman na tabbatar shi kad'aine dawakan ke gani suyi haniniya,
sannan koda batun fyad'en ya riskemu naje na binciki k'ofar baya inda dawakanmu suke na samu k'ofar a bud'e,
daga nan zargina ya k'ara tsananta kan Yusuf domin babu wanda yasan da k'ofar sai mu yan gidan."
shi kuwa Abba kanshi ya sunkuyar yana wasu yan rubuce-rubuce,
Affan ne ya kuma mik'ewa tare da cewa.
"Ya Mai s... "
komawa yayi ya zauna sabida dakatar dashi da Abba yayi cikin nuna mishi alamun ya zauna ba'a buk'atar ya magantu,
shi kuwa Aryan cikin izza yace.
"Ya mai shariya meyasa barrister Affan ke saurin katseni yayin bada hujjojina,
ko tsoron asirinsu zai tonu ne?."
kan Abba a sunkuye yace.
"Barrister Affan ka kiyaye."
cikin tsananin tashin hankali Affan ya duk'ar da kanshi tare da cewa.
"Ngd ya maishariya."
shi kuwa Aryan gyaran murya yayi tare da ci gaba da cewa.
"Bayan na samu k'ofar a bud'e sai na kuma dawowa part d'in Yusuf inda anan akayi mata fyad'en,
dan haka ina buk'atar Yusuf a gaban Court zan mishi tambayoyi."
wani irin bugawa zuciyar Abba tayi yayinda tashin hankalinshi ya tsananta,
tsoro mai tsanani ya rufeshi,
yasan Yusuf tun yana k'arami baya son titsen tambaya,
ko b'arna sukayi shida Sulaiman matuk'ar dai aka ritsasu da tamb'aya to Yusuf yakan ce,
eh shi yayi laifin,
ido Abba ya rumtse ganin alamun take-taken Aryan tsare Yusuf yake son yi,
bud'e idonshi yayi jin Aryan na kuma cewa yana buk'atar Yusuf a dandamalin,

Yusuf kuwa wani irin bugawa zuciyarshi keyi tamkar zata faso ta fito,
ida nunshi sun kad'a sunyi jazir tamkar rushi,
jijiyoyin kanshi duk sunyi rud'u-rud'u,
tunawa yakeyi tsawon shekara 8 kenan har an shiga na 9 rabanshi da ganin Abbanshi sai gashi yau k'addara ta had'asu a court,
lips d'inshi ya damk'a da hak'oranshi yana yi musu wani irin tauna tamkar zai hudasu
M. Jabeer ne dake gefenshi ya kalleshi cikin wani yanayi yace.
"Tashi kaje."
ba musu ya mik'e ya nufi tsakiyar wurin, domin yanada begen matsowa kusa da mahaifinshi,
yana jin kewarshi,
taku yakeyi a hankali yayinda sautin takalminshi sau ciki suke bada kab-kab wanda hakan yaja hankalin mutane gaba d'aya aka juyo kanshi akayi mishi caa da idanu,
yayinda yan jarida kuwa keta d'aukarshi hoto,
inda aka tanad'a dan tsayuwa yaje ya tsaya,
cikin izaya Aryan ya matso gareshi,
Affan kuwa zuciyarshi tamkar ta fashe dan takaicin Aryan,
Abba kuwa wani irin rauni da tausayin d'an nashi ne ya rufeshi,
domin shi kanshi baya son abinda zaisa mutuncin Yusuf zubewa,
shi kuwa Aryan ciki izaya yace.
"Kotu na son jin sunanka."
cikin murya mafi rauni da nuna tsantsar tawakkali Yusuf yace.
"Susana Yusuf bin Muhammad Usman Girei."
Mama ce ta rumtse idanunta dan jin wasu azababbun hawaye na tsastsafowa cikin jijiyoyin ida nunta,
Adda Zulaihat da Raihana da kaka kuwa hawaye har habarsu,
shi kuwa Abba ji yakeyi inama mutuwa ta d'aukeshi kafin zuwa wannan ranar,
Zahra kuwa dake rakube da jikin Mama rumtse idanunta tayi ta tsananin k'arfi sannnan tasa hannu ta dafe d'an cikinta dake harbe-harbe,
shiko Aryan cikin kafe Yusuf da ido yace.
"Zamuso musan yadda kayi ka jawo Zahra har part naka har kuma cikin bathroom?."
cikin k'arfin hali Yusuf ya jujjuya kai tare da cewa.
"Ni ban san ya akayi ta shigo side naba kuma bansan meya shigo da itaba."
murmushin shak'iyanci Aryan yayi tare da cewa.
"Ya mai shariya kalli duk da Yusuf ba jahili bane ba kuma bai tab'a shiga kotu bane yayi karatu har jamiwa ya kuma san dokoki,
to amman kalli yazo mana gaban Court da waya da biro a al'jihunshi,
ya karya mana doka,
yadda wannan ke nuna shi karya doka a gunshi ba sabon abu bane."
Affan ne ya mik'e da sauri yazo ya amshi wayar Yusuf da biron yaje ya mik'awa Adda zulaihat dake rusa kuka ganin butulci da ha'incin Aryan a fili."
Abba kuwa sai kanshi daya sunkuyar yana kallon wasu littatafai,
shi kuwa Aryan cikin isa yace.
"Ranar 4 ga watan 1 2015 wanne irin Kalan kaya ka saka?."
"Fari ne ".
Yusuf ya bashi amsa a tak'aice,
murmushin jin dad'i yayi tare da cewa.
"To a lokacin kanada wani ciwone a jikin ka?."
"A a babu ciwo a jikina."
cewar Yusuf kenan,
cikin ganin hak'arsa zata cimma ruwa yace.
"Toh da ka fita kayi fad'a da wanine,
ko anyi wani hatsarine ka kai taimako?."
kai Yusuf ya jujjuya tare da cewa.
"A a babu abinda ya faru cikin biyunnan."
Affan ne ya kalli Abba tare da cewa.
"Objection ya mai shariya barrister Aryan ya kauce layin case d'in da mukeyi bafa tuhumar Yusuf da kisan kai akeyi ba,
meya kawo batun fad'a ko taimakon hatsari?."
da sauri Aryan yace.
"Ya maishariya tambayoyina suna kan tsari."
hannu Abba ya nuna mishi alamar yaci gaba,
cikin izaya ya sake matso Yusuf sannan yace.
"Toh a lokacin da na kiraka na shaida maka abinda ke faruwa da Zahra,
koda ka dawo kaida Jafar naga fararen kayan dake jikinka duk sun b'aci da jini,
mu samman wond'onka,
sannan ya akayi na samu zobenka a cikin bath tub
baya kuma lokacin da ka fita zoben yana yatsarka?."
Affan ne ya k'urawa Yusuf idanu cikin yanayi rauni,
ido Yusuf ya rumtse jin sautin Kukan Mama da Adda Zulaihat a d'aya sashin kuwa yanajin kukan Jafar,
cikin rumtse ido yace.
"Jini kuma a kayana gskya babu wani jini a jikina,
sannan batun zobena dama ban fita dashiba."
kai Aryan ya juya don yaso ace Yusuf ya kasa musa mishi,
shi kuwa Affan cewa yayi a bashi dama yanada mgna.
jin haka Abba yace.
"Barrister Aryan ka gama gabatar da hujjojinka ne?."
kai Aryan ya rusunar tare da cewa.
"Inada hujja da shaida ta k'arshe ,
amman a bashi dama yayi mgna sannan in kawo shaidar."
yana fad'in haka ya koma ya zauna,
Affan kuwa ya sallami Yusuf tare da kiran Raihana bayan tazo ta tsaya cikin kula yace.
"Malama me sunanki?."
cikin zubda k'ollah tace.
"Raihana."
cikin kula Affan yace.
"A shariyar baya kin mana bayanin kinga idris ido da ido a cikin parlour Yusuf inda ya fito da alamun rashin gsky,
sannan kuma baki gaya mana dalilin zuwanki part d'in Yusuf ba."
cikin kuka ta basu lbrin zumar data zube jikin Zahra da kuma rashin ruwa a cikin gidan dama yadda ta kaita part d'in Yusuf ta k'ara da cewa,
"Wannan shine dalilin zuwan Zahra part d'in Yusuf,
kuma da mukaje bamu samu Hamma Yusuf a nanba dan saida na lellek'a ko ina,
ni kuwa ganin idona naga idris ina shiga kuma na samu Zahra a sume."
cikin taushin murya Affan yace ta koma wurin zamanta
sannan ya juyo ya kalli Abba tare da cewa.
"Toh ya mai shariya kaji dalilin zuwan Zahra part d'in Yusuf,
haka nan kuma Raihana ta shaida mana basu samu Yusuf a d'akinba,
ta kuma k'ara da cewa ganin idonta taga idris dan haka ina rok'o kar a sake tambayar Yusuf komai domin kan dalilin zuwansu part nashi dan ba abinda ya sani a kan lamarin."
kai Abba ya jinjjina alamar karbuwar k'orafinshi,
shi kuwa Affan Jafar ya kuma kira bayan ya gabatar da kanshi,
sai Affan yace.
"A bayanin Barrister Aryan ya shaida mana tare da Yusuf kuka dawo lokacin da kukaji lbrin abinda ke faru?."
cikin fidda numfashi Jafar yace.
"ai bama dawowa kawaiba tun bayan la'asar ina tare dashi a gidan mai d'in A S butu."
kai a k'asa Affan yace.
"Toh kaima kaga jininda Barrister Affan ya gani a jikin kayan Yusuf ne?."
Cikin jujjuya kai Jafar yace.
"Ni banga komai a jikinshi ba."
kai Affan ya jinjina tare da cewa Jafar ya koma mazauninshi
sannan ya kira idris yazo ya tsaya cikin taushi yace.
"Kotu zataso sanin sunanka?".
murya cike da rauni idi yace.
"Sunana idris wanda akafi sani da idi mai caji."
cikin kauda kai Affan yace.
"Yanzu Raihana take shaidawa Court ta ganka a gidansu a part d'in Yusuf shin me gskyar lamarin?."
cikin rawan murya idi yace.
"Hakk'un ta ganni na ganta."
a tsanake Affan yace.
"Toh meya kaika gidan har kuma cikin d'aki sannan me kaje yi?."
cikin sunkuyar da kai da zubda hawaye yace.
"Naje ne don naga lokacin da suka shiga da Zahra,
kuma dama da niyar yi mata fyad'e naje."
jin furucin idi yasa gaba d'aya court ta ricabe da yi mishi tofin Allah tsine,
Yusuf kuwa wani irin azabar suya zuciyarshi keyi ji yakeyi kamar ya fad'i ya mutu ko ya huta da bak'in cikin duniyar nan,
Raihana kuwa kai take gyad'awa alamar ga irinta nan ai.
Da sauri Aryan ya mik'e tare da cewa.
"Yana buk'atar Zahra a gaban Court,
jin wannan mgna yasa Zahra sakin kuka mai cin rai,
da ker Mama ta sata taje gaban Court d'in d'aya sashin ta shiga yayinda idi ke d'ayan,
sannan cikin izaya Aryan ya kuma cewa Yusuf ma yaxo,
haka ya taso yazo,
wurinda idi yake ya nuna mishi
cikin takaicin duniya Yusuf ya shiga wurinda idin yake suka tsaya a jere suna fuskantar Jamar dake nan,
cikin k'arfin guiwa Aryan ya kalli Zahra yace.
"Kotu tana son sanin me sunanki?."
cikin zubda k'ollah da rawar murya a disashe tace.
"Zahra."
kai ya jinjina cikin jin tausayin yarinyar,
yayinda mutane da yawa ke zubda k'ollah cikin d'aga sauti Aryan ya kuma cewa.
"Kinji duk abinda ke faru wanda dole kece hujjata ta k'arshe da zan wonki idi wanda nasan bashi ya miki fyad'enba kuma hujjarki da shaidarki itace zatasa a hukunta mai laifi ba tare da an cuci mara laifiba,
shaidarki itace zata nuna mana wayene uban cikin dake jikinki,
dan haka ki fito ki gayawa Court waya miki fyad'e cikin wad'annan mutun biyu dake gabanki Yusuf ne ko idris?."
shiru tayi ba mgna sai sautin kukanta,
ganin haka yasa Aryan sake jero mata tambayar.
"Waya miki fyad'e Yusuf ko idris ne!?."
Cikin rauni da tsananin tashin hankali ta d'an d'ago jajayen idanunta da suke kumb'ure simti-simti ido ta zurawa wani sashi na cikin kotun sai ta kuma juyo da kanta kad'an ta kalli saitin inda Yusuf da idi suke,
ido ta tsura musu tare da bud'e baki cikin fizgo mgnar tace.
"Y.....!







*By*
*GARKUWAR FULANI*

Jgewl


Barka da Jumma'a, ina dai tsammanin duk randa ban samu damar yi muku posting ba zakumin uzuri.
Domin jiki da jini.


"Yasan kanshi!!! duk wanda yayi yasani...! Kowaye shi yasan kanshi.! Amman ni bazan gane fuskarshiba bazan san waye d'aya bane a cikinsu."
Tana fadan hakan bakinta na rawa saboda ilahirin jikinta karkarwa yake.
sai ta kuma kalli inda suke ta gefen ido,
cire idonta tayi daga garesu ganin wani irin razana da Hamma Yusuf d'in yayi lokacin da tace bazata gane waye bane ya mata fyad'e,
shi kuwa Yusuf daga tsakiyar kanshi yaji tsikar jikinshi na tashi,
zufa mai zafi ya fara tsastsafo mishi,
jikinshi ya rink'a b'ari wani irin harbawa zuciyarshi keyi,
ji yake duniyar ta mishi zafi. Inama ba wannan ranan a rayuwar sa inama babushi a duniyar inama ace bacci yake ya farka daga mummunan mafarkin da ba zai taba gangancin kwanciya ba balle har irin hakan takasance dashi. Anya shine .?

Aryan kuwa cikin tsananin bak'in ciki ya kalleta fuska a had'e yace.
"Shaidarki ce kad'ai ta rage a samu damar sanin wayene uban cikin dake jikinki,
sannan a hukuntashi ya kuma wonke wanda baya da laifi,
sai gashi ke kuma kink'i fad'in abinda ya dace."

Cikin rawan murya tace.
"Babu haske a bathroom d'in shiyasa bazan gane waye bane."
ya bud'i baki zaiyi mgna kenan Affan ya mik'e tare da cewa.
"Ya mai girma mai shariya,
Barrister Aryan ya dena kure wacca akayiwa fyad'e da dole sai ta mannawa Yusuf laifi wanda shaidu sun tabbatar da bakinsu lokacin da abin ya faru bayama gidan."
Kai Abba ya d'an d'ago tare da kallonsu a nitse kana yayi gyaran murya tare da cewa.
"k'orafi bai karbu ba."
shi kuwa Abba yayi hakane dan kar Aryan ya zargi ana hanashi gabatar da hujjojinshi ne,
shi kuwa Affan d'an rusunar da kai yayi tare da cewa.
"Ngd ya Mai shariya."
Aryan kuwa murmushi gefen baki yayi tare da cewa.
"Nagode ya mai shariya."
Affan kuwa cikin nitsuwa ya taso yazo gaban Court cikin iya aiki ya tsaya gaban Yusuf da idris,
ido ya tsura musu na d'an wani lokaci,
cikin sanyi yace.
"Idris kanaji dai duk abinda ke faruwa,
shariya tak'i k'arewa,
tunda ni dai bani da shaidu hud'u da shariya take buk'ata wanda zasu bada shaidar sun ganka kaida Zahra a turmi da tab'arya,
ni kare Yusuf nekeyi wanda na tabbatar bai aikata ba,
yayinda shaidu sama da 6 suka tabbatar mana lokacin da abin ya faru Yusuf yana gidan mai,
yayinda kaikuma Shaidu sama da 12 suka tabbatar mana da sun ganka ido-da-ido,
a cikin gidan har a parlour Yusuf wanda alamu suka nuna daga cikin bedroom ka fito,
sannan kaima da bakinka ka jaddada mana cewa tabbas a wannan lokacin kana wurin kuma daga bedroom d'in ka fito lokacin da kaci karo da Raihana,
toh amman kanaji anata jifar Yusuf da kalmar shi yayi mata fyad'e ba kai bane,
ka kuma yi shiru,
kenan hakan yana nufin gskya ne Barrister Aryan ke fad'i Yusuf ne yayi mata fyad'en!!?."
shiru kakeji duk mutanen cikin kotun dama wajen kotun sun nitsu domin son jin amsar idi,
Aryan kuma sai kafe idi yayi da idanu kamar ya karb'i bakinshi yayi mgna,
Safwan kuwa da sauran dandazon zugar yan jarida kama daga maikatan gidajen radio da TV duk suna cike mak'il kowa ya nad'i sautin abin mgnarshi,
Matawalle kuwa ji yake kamar yayi ta kuka domin tausayin Yusuf,
Abba ma shiru yayi yayinda zuciyarshi ke harbawa,
shi kuwa idi rumtse idonshi yayi da k'arfi,
yana tunowa fa shi an tab'a mishi aure,
so kenan haddin kisan kai za'a yanke mishi ta hanyar jifa,
ido ya kuma rumtsewa murya na rawa hawaye na bin fuskarshi yace.
"Yusuf ba mazinaci bane."
sai kuma kawai kuka ya kwabce mishi kuka yakeyi sosai duk jikinshi rawa yakeyi,
shi kuwa Affan cikin jin dad'i yace.
"Toh ya tabbata kaine kayi mata fyad'en kenan?."
ina Idi ya kasa mgna sai kuka,
an maimaita mishi tambayar ya kai sau 3 amman kuka yaci karfinshi,
kuka yakeyi sosai irin kukannan na yin sallama da rayuwar duniya,
Matawalle kuwa tuni ya nad'i mgnar idi inda yace Yusuf ba mazinaci bane a take ya had'e sautin da ma'aikatarsu inda akejin abinda ke faruwa kai tsaye,
Aryan kuwa sunkuyar da kai yayi ida nunshi na zubda k'ollah masu zafi,
yana mai jin kunyar kallon Yusuf dayin dana sani,
ji yake ya juyo gaban yan jaridu yata ihu yana cewa sharri yayiwa Yusuf,
Safwan kuwa ji yakeyi tamkar ya mutu dan takaici shi tabbas yaso zancen Aryan ya tabbata,
jin shirun yayi yawane sai sautin kukan idi da Zahra da Mama yasa Abba yin gyaran murya tare da cewa.
"Za'a d'aga k'ararnan har zuwa biyu ga watan sha'aban,
tare da bawa lawyers d'in damar su tsananta bincike,
sannan kotu ta bada damar a bar Idi da Yusuf suci gaba da harkokinsu,
tunda duk zarginsu akeyi ba'a samu shaidu hud'u da shariya take buk'ataba,
sai in kuma wanda ake zargi ya bada shaida a kan kanshi ne za'a samu damar yanke hukuncin dan haka an d'age shariyar."
lokaci d'aya yan jaridu suka fara kutso kai cikin kotun,
yayinda Abba ya fara tattara takardun gabanshi zai tashi kenan
aje hutu kafin a saurari k'ara na gaba,
daga nesa yan jaridan ke cillowa Yusuf tambayoyi,
Aryan kam zama yayi yana kuka kamar yaro k'arami,
Affan kuwa sai dariya yakeyi yayinda yake gaisawa da sauran lawyers d'in irin ana tashi murna sabida anaga shine yakeda alamun nasara,
Idi kuwa zuwa yanzu kukanshi ya zarta zaton mutun domin kukane mai karya zuciyar mai sauraro,
shi kuwa Yusuf da sauri yasa tafin hannunshi ya rufe bakin idi da fara mgna cikin kuka murya can k'asa yace.
"Eh ni idi ni ne nayiwa Zahra fyad.."
jin haka yasa Yusuf sa tafin hannunshi ya rufe bakin idi tare da jujjuya mishi kai,
Allah sarki Yusuf sai ya gyara tsayuwarshi tare da rumtse idanunshi da azabar k'arfi yana jin wasu zafafan hawaye na tsastsafo mishi ta cikin jijiyoyin idanunshi,
zuciyarshi kuwa tayi wani irin karaya murya na rawa ya bud'i baki a hankali tare da fizgo mgnar da k'arfi cikin disashewar sauti yace.
"Ni ne! Ni ne!."
mgnarshi ta ratsa cikin court d'in.
wani irin zabura Affan da jafar sukayi,
yayinda Mama kuwa ta mik'e tsaye tana kallon fuskarshi,
Abba kuwa har ya yunk'ura zai mik'e jin mgnar Yusuf ya sashi komawa ya zauna yayinda jikinshi ke tsuma,
Affan kuwa durk'ushewa yayi a wurin tare da cewa.
"No...! Yusuf ba kai bane, please kar kayi mana haka."
shiru kakeji court d'in tayi tsit tamkar babu mutane a ciki,
sai idanu da ake zazzarewa anayin kallon-kallo,
Aryan kuwa yana jin haka ya mik'e da sauri tare da tsurawa Yusuf ido yana wani irin gyad'a mishi kai,
Shi kuwa Yusuf cikin d'an d'aga sauti yace.
"Ni ne nayiwa Zahra fyad'en".
wani irin yanayi yan uwa da abokan arzik'i suka shiga,
Uncle Gambo yayan Aunty Amarya kuwa shima kai yaketa jujjuyawa Yusuf yana kuka kamar mace alamar a a kar Yusuf yayi haka,
shi kuwa
Abba cikin sanyi muryarshi na rawa tamkar zaiyi kuka yace.
"Yusuf ka bada shaidar kanka cewa kai kayi laifin baki biyu,
in ka kuma baki na uku dai to Hukuncin ya tabbata a kanka,
shin waye yiwa Zahra fyad'e?."
cikin k'arfin hali ya k'arasa hannunshi ya rufe bakin idi daketa jujjuya kai da yarfa hannu alamar a a zancen Yusuf ba gskya bane,
ido Yusuf ya kuma rumtsewa da k'arfi tare da cewa.
"Ni ne nayiwa Zahra fyad'en."
jin haka yasa gaba d'aya kotun aka d'auki kabbara,
shi kuwa Abba sunkuyar da kanshi yayi tare da bud'e k'ura'anin dake gabanshi,
gilashin idonshi ya cire sabida wasu irin hawaye dake zubawa a idanunshi har yana jik'a gikashin,
Affan, Jafar, idi, Uncle Gambo, Daddy, da Hajia Kaka da Raihana da Mama tare da Adda Zulaihat kuwa kab kuka sukeyi,
cikin sanyin sauti Abba ya d'an buga teburin gabanshi tare da cewa.
"A nitsu aji Hukuncin da Allah yace mu zantar ga masu kaifi zina da fyad'e."
shirun ya gagari wasu sai dai sun rege sautin kukan nasu,
Safwan kuwa ba kunya ya fita woje yana taka rawar jin dadi
saida yaji za'a zantar da hukunci ne sannan ya kuma shigowa.
shikin sanyi Abba yace.
"Duba da shaidar da wanda ake tuhuma da kanshi ya bada a kan kanshi to shariya ta yarda da shaidarsa kamar yadda take yarda da shaidun mutun hud'u da sukayi shaidar gani da ido,
dan haka yanzu mgna ta tabbata kan Yusuf tunda ya bada shaida a kankanshi har baki uhu,
furuci hud'u ya kuma jaddarar da hakan."
Gyara zama yayi tare da bud'e qura'an d'in dake gabanshi,
mutane kuwa tuni an nitsu domin son jin hukuncin da za'ayiwa Yusuf,
Affan kuwa tunda ya durk'usa har yanzu bai tashiba,
Malam Jabeer kuwa wani irin haushin Yusuf yakeji tamkar ya had'iyi zuciya ya mutu kunya mai tsanani ta rufeshi
Aryan kuwa har yanzu hawaye yake zubdawa.

Gyaran murya Abba ya kumayi tare da sharte hawayenshi cikin fidda sautinshi yace.
"A cikin Suratul Nur Surah ta 24 Aya ta 2, Allah (S.W.T) yayi mgna

Please Login or Register in order to submit comment