Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shad'aya na dare Abba yana ta tsumayin Mama amman shiru babu dalilinta,
ya kira a waya kuwa yafi sau 5 bata amsawa,
ganin haka ya mik'e sanin yau babu kowa a sashin nasu babu Zahra bare Aryan da baya duniyarma gaba d'aya,
kai tsaye bedroom nata ya nufa,
bisa sallaya ya sameta don lokacin tayi shara'i da wutiri,
bakin gadon ya zauna tare da zuba mata ido,
ita kuwa mik'ewa tayi tana nink'e abin sallan,
cikin muryar rauni yace.
"Maman Yusuf inata kiranki baki d'aga wayaba kuma gata kusa da ke,
meyasa baki amsaba?."
shiru tayi kamar bata jishiba ganin haka ya mik'e tsaye tare da zuwa gefenta cikin kauda kai yace.
"Kina ji ina mgna kin min kunnen uwar shegu,
mijinki nefa ni."
cikin sanyi tace.
"A da can baya ba."
cikin mmki yace.
"Wai Maman Yusuf lfyarki kuwa."
kai ta gyad'a mishi dan so take ya lashe aman da yayi shekaru goma sha shida da suka wuce,
cikin rikicewa ganin yadda ta canza mishi fuska yace.
"Yau kuwa d'ab'iyar Yusuf d'inki zakimin kenan mgna da kai."
still fuska ta tsuke tare da kama hanyar fita,
da sauri ya kamo hannunta tare da cewa.
"Zo nan ki bud'i baki kimin mgna kinsan bani son body language."
hannunta ta janye tare da cewa.
"Kadafa ka manta ni ba matarka bace."
da sauri yace.
"Inji uban waye?."
kau ta kauda ganin yadda ya zaro ido cikin ko in kula tace.
"Inji uban Yusuf mana."
jawota yayi da kyau tare da cewa.
"A a uban Yusuf kam baifad'i ba."
janye jikinta tayi daga rik'on da ya mata kana tace.
"Ka fad'i kam."
"Yaushe d'in na fad'i?."
ya tambayeta murya a diririce,
juyowa tayi ta d'an kalleshi kana tace.
"Ranar daka korar min d'ana,
kace duk randa k'afarshi ta tako gidannan a bakin aurenmu,
toh yau kuma ya tako gidan kaga kenan ni ba matarka bace ba,
shiyasa naso inbi d'ana da matarshi in huta masifa da dukana da kakeyi."
cikin sanyin jiki da kunya yace.
"Maman Yusuf kimin adalci mana,
yanzu tun randa nayi yunk'urin marinki kika gudu inda tsautsayi yasa kika fad'i kika samu rauni,
d'anki yazo ya dakarmin uwa ciki da woje,
tun daga ranar ni dai nasan ko muntsilinki ban kuma yiba a tsawon zamanmu,
tund'a d'anki ya nuna min zai kashe min uwa,
sannan batun in ya shigo a bakin aurenki,
tun randa aka yanke mishi haddi na janye wannan furucin,
kuma ko bayan nanma d'azu kafin in fita Aryan yaita kuka yana rok'on in yafewa Abeehnshi kuma ni na yafe mishi duniya da lahira,
amman dan ki kunyatani gaban yara zakice zaki bishi,
to wlh insha Allah ni dake matuka raba,
da har zakice zakibi d'anki dani da d'an naki wa kika fara sani,
kadafa ki mance ni d'an uwanki ne ko mutuwa nayi a gidannan zaki zauna,
sannan da kike cewa zakibi d'anki kadafa ki mance ba ke kad'ai kika haifi Yusuf ba,
so kina tafiya gidanshi zanbi bayanki,
kinga abin kunya ya tabbatar mana ko."
cikin sanyi da jin dad'i ta kauda kanta tare da cewa.
"Yoh ai dai dukan ne ka bari amman tsaurin zuciya da fad'an ka barine,
a haka kake ganin laifin Yusuf yaronda duk masifa da fad'a da zuciya kai ya gada,
jininka ne ke yawo a jikinshi."
jawota yayi gareshi kana yace.
"Na yarda kice komaima amman karki gujeni,
musamman a irin wannan ranar da nake buk'atar makusanci,
ko dan sama min nitsuwar da rashin Aryan yasa na rasata."
cikin sanyi tace.
"Toh Abban Yusuf tafi side d'inka ina zuwa."
ba tare daya kulataba ya haura gadonta tare da shigewa blanket.


Haka dai rayuwarsu ta mik'a cikin kwana ukun nan da ake zaman makokin Aryan kullum Aryan Babba da Affan da Idi sai sunzu,
hakama Hajia kaka da Rafi'a da Raihana da Tatti,
duk sunzo sun gaida su Mama amman basuje wurin Zahra ba.


Yusuf kuwa kullum da safe zai shirya yazo gida kusan nan yake wuni,
yayinda Zahra kuwa rayuwa ta mata zafi rashin bacci na neman tab'a mata k'ok'olwa,
da zaran ta rufe ido sai daga Aryan na mata gizo,
ga tsoron da ya addabi rayuwarta ga mutuwar Aryan ta tsaya mata a rai,
gaba d'aya ta rame ta fita haiyacinta.


Yauma kamar kullum kuma yaune sadakan uku,
tun safe Yusuf yazo gida inda kusan a parlour Mama ya wuni dasu Adda Zulaihat da Adda Amira sai Zeenat,
yayinda su Goggo Aysha ma sunzo,
nan suka wuni saida yamma k'annane Abban duk suka shirya Jafar ya kaisu gidan Yusuf sukayiwa Zahra ta'aziya da nasiha,
kana duk ya medasu gidajensu,
shi kuwa Yusuf har yanzu bai zauna da Abba ko Daddy ba dan har lau yana jin kunyarsu.


Bayan anyi sallan ishane ya kuma shigowa gidan,
kai tsaye part d'in Mamanshi ya nufa,
a parlour ya samu Adda Zulaihat da Zieenat sai Amira dake salla a gefensu.

ba tare da ya musu mgnaba ya wuce bedroom d'in Mama,
murya can k'asa yayi sallama,
cikin sanyi da jin dad'i tabbas suna jin ciwon rashin Aryan amman Aryan ya gyara abu da yawa kafin ya rasu,
amsa mishi sallamar cikin sauk'e numfashi.
shi kuwa Yusuf shigowa yayi cikin d'akin gefenta ya zauna tare manna kanshi jikin gado,
ido ta zuba mishi cikin karantar yanayinshi,
kainshi ta shafa tare da cire hular cikin sanyi tace.
"Babana sai yaushene zaka girma kabar irin askin nan kam ne?."
hannunshi ya kai ya shafa k'eyarshi kana ya d'an d'ago kanshi ya kalleta kana ya lumshe ido alamar zai bari.
ita kuwa Mama gyara zama tayi tare da cewa.
"Yusuf! Yusuf!!."
murya can k'asa ya amsa ganin tana kiranshi alamar tanaso ya amsa hakan yasa ya bud'i baki a hankali yace.
"Na'am Maman Yusuf."
murmushi tayi dan ya tuna mata baya.
cikin sanyi tace.
"Yaya zamanku yakene kaida matarka?."
kai ya rusunar dan jin mgnar ta mishi bimborok'wai wai matarshi,
shifa sai yanzu ya tuno Zahra dan wlh shi ya mance komai rasuwar Aryan ce kad'ai ke azalzalar zuciyarshi,
kanshi ya d'an rusunar kana yace.
"Mama nifa kinsan bamu saba da itaba,
na lurama kamar bata son ganina fa,
shiyasa bani zuwa inda take."
ajiyan zuciya Mama ta sauk'e tare da cewa.
"Bata son ganinka ko dai tana tsoron ganinka."
murya can k'asa yace.
"Taji tsoron ganina kamar wani dodo."
kai ta kawar daga kallonshi kana tace.
"Yoh ita tanada wani dodone abin tsoro da ya fika."
da sauri ya kalli Mama tare da cewa.
"To sabida me?."
fuska ta tsuke tare da hararanshi kana ta mishi dak'uwa tare da cewa.
"Hink'o naka ai kafi kowa sanin sabida mene."
da sauri ya sunkuyar da kanshi murya can k'asa yace.
"Astaqfirillah."
ita kuwa Mama kauda mgnar tayi da cewa.
"Tashi muje kaci abincin."
zamewa yayi a wurin kan sallayarta murya can k'asa yace.
"Maman Yusuf bacci nakeji fa."
murmushi tayi ganin kunyace ta rufeshi gashi yadda ya wani konta kamar ya samu d'akinshi,
shigowar Adda Zulaihat ce ta sashi juyowa ita kuwa cikin hararar shak'uwa tace.
"Uhum kalleshi tsoho dashi yazo yayi wani konciya a d'akin Mama."
mik'e yayi zaune tare da kallon Mama cikin kwabe fuska yace.
"Maman Yusuf ki gaya matafa ta dena cemin tsoho."
Murmushi Mama tayi kana ta fita tare da cewa.
"Kunfi kusa."
tana fitowa parlour ta kalli Amira da ta idar da salla cikin kula tace.
"Yauwa Amira sa muku abinci kuje kuci."
to tace kana ta d'auki kulolin abincin da pilet ta nufi cikin bedroom din Mama,
a tsakiyar d'akin suka zauna,
abincin ta zuba musu tare da matsowa inda yake kunsan dama Amira kamar k'arwasu ce shida Sulaiman shiyasa basa ce mata ko Addanma wai ai sun isota tsawo,
Adda Zulaihat kuwa kunsan irin shak'uwar dake tsakaninta da k'annenta,
Zeenat kuwa tunda ta lek'a taga da Hamma Yusuf sukeyin dinner ai da sauri ta juya ta fita.

Shi kuwa Yusuf spoon biyu yayi ana uku ya koma ya jingina da gado tare da cewa ya isheshi,
sai ya jawo filas d'in kunun Abba ya tsiyaya kana yasha kofi d'aya sannan mik'e tare da kama hanyar fita.
Amira ce tayi saurin cewa.
"Ina zaka je?."
"inda kika aikeni." ya bata amsa a gyatsine,
Adda Zulaihat ce tace.
"A a meda wuk'ar, zamuje wurin Zahra ne shiyasa ta tambaya karka tafi ka barmu."
yana mai ci gaba da tafiya yace.
"Toh ni me nawa a ciki ko ance muku gidan a rufe yake,
kuje mana sai kun dawo."
"To ai da kai zamu tafi". Amira ta bashi amsa.
yana daga cikin parlour yace.
"A a kam ku dai nemi mai kaiku ni in na kaiku to wazai maidaku?."
da sauri Zulaihat ta fito tabi bayanshi tare da cewa.
"A a karka damu ni Abban Fa'iq zaije ya d'aukeni tacan itama Amira mijinta zaije ya d'auketa daga can."
Kai ya gyad'a mata alamar to.

Daga nan ita ta wuce d'akin Zahra kana daga baya Amira ma tazo nan suka fara harhad'a mata kayanta.

Shi kuwa Yusuf d'akin Aunty Amarya ya nufa,
inda ya sameta ita da Ibrahim wanda yake k'ok'arin fita zaije ya maida Zeenat gidanta,
gefen gadonta ya zauna kan yar k'aramar durowa wacce kusan nanne asalin wurin zamanshi in ya shigo d'akinta tun yana yaronshi.

Ita kuwa Aunty Amarya dake konce kan gado gyara konciyarta tayi tare da cewa.
"A a Yusuf baka tafi bane?."
Kai ya gyad'a mata alamar,
ita kuwa cikin kula kamar da can baya tace.
"Kaci abinci kuwa."
still kai ya gyad'a mata,
sai bayan 9 seconds ya d'an gyara zama tare da cewa.
"Yanzu dai zan tafi,
to kuma yau ban gaisa da Daddy ba ban gashi bama ko baya gari ne?."
mik'ewa zaune tayi tare da cewa.
"Eh yaje maiduguri zai d'auko Umminku."
Kai ya jinjina tare da cewa.
"Saida safe."
bayanshi tabi tare da cewa.
"Jirani inzo."
to yace tare da wucewa parlour ita kuma kitchen d'inta ta nufa.
wani roba ta d'auko wanda yake cike da zuma
Juyowa taji zuwa parlour ta dawo tare da mik'a mishi robar,
kana tace.
"Gashi inji Daddynku jiya da yamma ya dawo dashi yace in baka,
ya zama madadin sugar in tea zakasha ka sashi a madadin super inma kunune ka sashi,
to ni nama mance sai d'azu ya kira yake tambaya na baka,
to ni mana zata ka koma ne nace sai gobe in kazo in baka."
amsar robar yayi tare da d'an jijjigashi zumace mai kyau sai dai da alamun tanada wasu sinadaran,
cikin sanyi yace.
"Ngd, saida safe."
yana fad'in haka ya fita,
part d'in Mama ya koma inda ya samu su Amira sun firfito da akwatunan Zahra,
baibi ta kansuba ya wuce kitchen inda ya samu Mama ta gama gasawa Abba nama gashin tukunya,
gefenta ya tsaya tare da cewa.
"Mama wai ina zasu kai kayannane?."
sauk'e tukunyar tayi tare da jawo yan ma daidaitan kuloli guda biyu,
ta zuba naman da romonshi kana ta mik'a mishi d'aya tare da cewa.
"Gashi kaje ku tafi dare yayi, kabar min 'ya ita d'aya."
kai ya juya tare da karb'ar Kular ganin bazata amsa mishiba,
a tare suka fito,
kana yayi gaba su Zulaihat na biye dashi a baya,
yayinda suke janye da akwatunan,
bayan motar ya bud'e musu kana yayi shigewarshi ga.
bayan sun shisshigar da kayan ne,
Zukaihat ta shiga baya Amira kuwa tazo gaba inda tayi ta kiciniyar shiga motar da keret ta samu ta shiga,
shi kuwa Yusuf murmushin k'eta ya mata,
ita kuwa sai cewa tayi.
"Wannan mota dai ta rowace garemu gajeru ji saida na tattare siket na har guiwa."
tana fad'in haka tare da jawo kular,
amshe kular yayi tare da cewa.
"Ke matsalarki kenan son bud'e-bud'e,."
sake mishi tayi kana ta jawo robar zumar,
sai tayi maza kuma ta meda ta ajiye dan tana rik'o robar taji tsikar jikinta na tashi,
Adda Zulaihat kuwa sai dariya take musu, a haka dai suka tafi suna d'an tab'a hira har suka isa.



Suna isa gidan ya nuna musu k'ogar inda Zahra take,
Amman sunyi sallama da buk'a k'ofa har sun gaji babu sallama.

Ganin haka sukabi bayanshi,
a parlour suka sameshi yana tsaye gefen dinning table inda ya ajiye naman da zumar,
Adda Zulaihat ce ta matsoshi tare da cewa.
"Yusuf k'ofar a rufe take fa."
juyowa yayi tare da cewa.
"To ni dai bani na rufeba."
cikin had'e fuska Zulaihat tace.
"Babu ruwanmu da wanda ya rufe kawai muje ka bud'e mana k'ofar."
juyawa yayi kana yaje ya bud'e musu k'afar tsakiya,
cikin yin k'asa da kai yace.
" to kubi nan."
rabawa gefenshi sukayi suka wuce,
shi kuwa konawa yayi ya wuce bedroom nashi kai tsaye bathroom ya wuce wonka yayi tare da kimtsawa kana ya fito ya kimtsa cikin riga da wondo yan madaidaita masu taushi wondon iya guiwa sai rigar mai gajeren hannu,
parlour ya dawo kai tsaye kan dinning table ya nufa bayan ya d'auki madara mai sanyi a firij sai ya juyeta a kofi tare da bude robar zumarnan ya d'an tarfa cikin cokali uku,
sannan ya jujjuyashi,
kana ya zauna ya fara cin naman,
yana d'an korawa da had'in madarar da zumar.

Su kuwa su Zulaihat suna shiga parlour ganin ba kowa sai suka wuce bedroom,
bisa gado suka sameta tana zaune ida nunta sunyi simtin-simtin alamun rashin bacci,
gashi dai bacci ne a idiota amman ta gazayi,
ganinsu yasa ta mik'e jiki na rawa suka iso gareta,
kawai sai ta fara zubda hawaye ganin haka Zulaihat tace.
"Toh in dai kuka zakiyi bari kawai mu tafi".
da sauri ta goge hawayenta tare da cewa.
"Na bari bazan k'araba."
cikin jin tausayinta suka zauna bakin gadon,
ita kuwa jiki a mace ta gaidasu,
kana sukayi mata ta'aziya,
bayan sun gaisan ne Amira ta kalleta cikin sanyi tace.
"Zahra baki da lfy ne?."
kai ta sunkuyar dan karsu ga hawayenta murya a sanyaye tace.
"Adda Ami bana iya baccifa, tsoron gidan nakeji, gashi ni kad'ai bana jin motsin kowa kuma gashi ban taho da wayata ba,."
cikin zuba mata ido Zulaihat tace.
"Me yake hanaki baccin?".
kai ta rausayar tare da cewa.
"Wlh Adda in dai na rufe idona sai naga Aryan namin gizo."
Amirace ta katseta cewa.
"Kardai kuruwarshi ce ta kamaki."
Cikin hararar Amira Adda Zukaihat tace.
"Babu wata kurwar Aryan data kamata tsoronta dai ya kamata,
daga ita har Yusuf sunk'i su saki zuk'atansu da jikinsu,
shiyasa suke cikin matsala."
mik'ewa tayi tare da cewa.
"Maza tashi ki shiga kiyi wonka ga kayanki mun kawo miki."
cikin girmawa tace.
"Yanzu nayi wonka kaya ne dai da ban canzaba."
ba tare data kalletaba tace.
"eh na sani kije ki k'arayin wonkan."
haka dai ala dole suka sata tayi wonka kana ta canza kaya inda suka bata doguwar riga mara nauyi sai d'ankwalinta,
Amira da kanta ta feffesa mata turare kana suka shirya mata kayanta a durowar.

Shi kuwa Yusuf maigadi ne yazo ya ce mishi yayi bak'i,
so sai yacewa mai gadin ya shigo dasu saida ya shigo dasune sai yaga ashe Mijin Amirane sai Ya Abubakar da yanzun ya isa gidan.
a parlour Yusuf d'in suka zauna suka gaisa tare da yi mishi ta'aziya,
kana suka d'anyi hira sannan suka fita bayan sun cewa Yusuf ya turo musu su Amiran.

Suna fita shi kuma Yusuf ya kira Adda Zulaihat ya shaida mata ana jiransu,
so haka yasa suka mik'e tare da Zahra.

A parlour Yusuf d'in suka tsaya shi kuwa Yusuf yana rik'e da kofin madarar da ya kuma had'awa yana sha,
cikin kula yace.
"Kuyi sauri kuje mana kun wani ajiyesu kamar direbobinku."
Amirace ta fara fita tare da cewa.
"Bafa sai ka koremu ba."
ita kuwa Adda Zulaihat hannun Zahra ta kamo tare da kawota gabanshi cikin tsuke fuska tace.
"Kuyiwa kanku adalci, ku tausayawa junanku sai ku samu damar cin jarabawar da Allah ya jarabceku,
ni dai ina rok'onka da Allah Yusuf ka rik'e amanar da Daddy ya baka, ke kuma Zahra kiyi biyeyya da zab'inda iyayenmu sukayi miki."
tana fad'in haka ta juya ta fita domin ta kuma ganin kiran Abubakar,
sauri-sauri ta fita inda ta samu tuni su Amira sun tafi,
nan suma suka tafi dan dare ya fara nisa.

A cikin gidan kuwa rumtse ido Yusuf yayi dan yanajin bak'on yanayin da yafi shekara 4 baijiba,
Abinda Yusuf bai saniba zumarnan da yakesha A gun wannan tsohon Daddy ya saya,
inda har zai tafi tsohon yace mishi.
"Alhaji Aliyu in kanada d'a namiji da yayi aure kwanan to ka bashi zumar kada ka shata."
har Daddy zai nemi k'arin bayani kuma sai yaga tsohon har ya juya ya tafi,
kuma dama a gefeb gadar hayin gada ya ganshi,
kafinma ya ankara bai kuma ganin tsohonba,
so shiyasa daya koma ya bawa Aunty Amarya zumar dan ta bawa Yusuf d'in.

Tofa kunji asalin zumar ta dawo da Yusuf ne kamar da d'inshi can tunda yanzu yai aure.

juyowa yayi a hankali inda Zahra take ta gefen ido ya kalleta kana ya sunkuyar da kai tare dayin tattaki zuwa.....!



*HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 19*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*











Step d'in haurawa wurin dinning area ya fara takawa a hankali,
tare da ratsa tsakiyar zirin igiyoyin labulen wurin,
janyo kujera yayi tare da zama a kai,
kana ya kurb'i madarar da zumar,
ido ya lumshe tare da sauk'e numfashi kana ya gyara zamanshi yaci gaba dasha yayinda d'and'anon zumar ke ratsa harshenshi har kwanyarsa na amsawa.

Ita kuwa Zahra da ido ta bishi tana kallon dukkan motsinshi yayinda sam batayi zaton yana kallontaba.
sai da taga ya mik'o mata kofin alamar tazo ta karb'a,
cikin sauri ta sunkuyar da kanta dan ta gane ya gane tana kallonshi.
shi kuwa ido ya lumshe kana ya kuma kurb'a,
ita kuwa idon ta kuma zubawa k'eyarshi tana kallon yadda sumar wurin ke kwance lif-lif sai shak'e yakeyi,
kamar cikin rad'a murya can k'asan mak'oshi taji yace.
"Karki sa in k'ware da wannan kallon,
in zakisha ne toh ki zoki karb'a."
cikin jin kunya ta sunkuyar da kanta kana ta jujjuya kai alamar bazata shaba,
sannan ta juya a hankali ta nufi k'ofar da suka shigo ita dasu Amira,
cikin nitsuwa tasa hannu ta murd'a ma bud'in k'ofar tare da turawa,
amman sai taji k'ofar gam alamun a rufe take,
d'an ramin key d'in ta zubawa ido,
tare shafawa da nufin wai ko da key a jiki,
jin wayam babu Key ne kuma k'ofar tak'i bud'wa sai ta juyo ta kalleshi,
inda ta ganshi zaune inda ta barshi amman yanzu ya juyo yana fuskantar laptop enshi dake kan d'aya kujerar dake gefenshi.
taku d'aya tayi zuwa biyu sannan ta bud'i baki a hankali tace.
"Hamma Yusuf."
ba tare daya d'ago kanshiba ya d'an juya kwayar ida nunshi gefen da take.
ganin alamun bazai amsa bane yasa tayi k'arfin halin cewa.
"Hamma Yusuf k'ofar tak'i bud'uwa."
shiru bai kulataba sai da yayi kusan 4 minutes yana daddana naurar dake gabanshi kana ya mik'e tare da yin mik'ar da saida gabban jikinshi suka bada sautin k'as-k'as,
hannu yasa ya gyara zaman robar wondon jikinshi da ya d'an matsi gugunshi,
laptop d'in ya d'auka tare da wayarshi,
sannan ya juyo a nitse ya fara taka steps d'in zuwa tsakiyar parlour,
ta gefenta ya ratsa zuwa bakin k'ofar,
yana isa yasa hannu ya murd'a hannun k'ofar amman ji yayi k'ofar tayi gim kamar gineta akayi,
kusan 2 minutes yayi yana kiciniya da k'ofar amman sam tak'i ko gezau,
ganin abin kamar abin iska sai ya juya tare da karantar da kanshi alamar ta biyoshi,
kasan cewar idonta na kanshi shiyasa ta gane abinda yake nufi.
bayanshi tabi yayinda shi kuwa ya bud'e k'ofar fita.

Tsakiyar gidan suka fito,
kana ya bud'e k'ofar da zata sadasu da farfajiyar gidan,
ita dai tana biye dashi kamar jela,
k'ofar side d'in da suka bi randa tazo gidan ya nufa,
yayinda shiru babu motsin komai a farfajiyar gidan,
gaba d'aya ba gilmawar d'an adam ko Motsinshi sai su,
sai kukan tsuntsaye da hasken fitulin dake zagaye da gidan in ka gani kace da ranane.

Suna isa bakin k'ofar nanma yayi iya yinshi k'ofa dai tak'i bud'uwa,
ganin bazai iya tsayuwa kiciniyar bud'e k'ofaba ya sashi juyawa ba tare da yace mata k'ala ba.

Da sauri ta juya tabi bayanshi dan wani irin azabebben tsoro da taji ya rufeta gaba d'aya tsikar jikinta sai tashi yake, musamman ma data ga kamar gilmawar kenwa,
yana tafe tana binshi a baya har suka shiga parlourn nashi,
rabawa gefe yayi ya bata hanya ta wuce,
kana ya meda k'ofar ya rufe.

Kan 3 str ya zauna tare da bud'e laptop nashi,
yaci gaba da aikinshi,
time to time yakan d'an kalleta ta wutsiyar idonshi,
ita kuwa Zahra gaba d'aya ta gaji da tsayuwar,
ga baccin da takeji yana fizgarta,
ga makararran yunwa da takeji abu dai ya had'e mata goma da ashirin,
lokaci d'aya tausayin kanta ya rufeta abin duniya ya mata yawa,
rasuwar Aryan ya dawo mata sabuwa,
tasan rasuwarshi ce sanadin aurenta,
hamma taketayi yayinda hawaye ke sintiri a kumatunta kana ta fara yin alamun zata fashe da kuka,
kanshi ya d'ago ya zuba mata ido tare da d'aga mata kai alamar tambaya yaya dai?.
baki ta turo gaba tare dasa tafin hannunta ta goge hawayenta murya na rawa tace.
"Hamma Yusuf zan konta bacci nakeji."
sai ta kuma lumshe idanu tare da yin hamma, a fili ake gane tana tsananin jin bacci.
ajiyar zuciya ya sauk'e tare da cewa.
"Shiga nan ki kwanta."
ya k'arishe mgnar tare da nuna mata hanyar bedroom nashi.
ba musu ta juya ta nufi cikin bedroom d'in.

Shi kuma da idanu ya rakata har saida ta b'acewa ganinshi kana ya sauk'e numfashi tare da lumshe ido,
sai ya kuma zame ya konta rigingine ya d'aura laptop d'in kan ruwan cikinshi.

Ita kuwa Zahra tana shiga cikin bedroom d'in nashi wani irin sassanyar ajiyan zuciya taja tare da lumshe ida nunta kana ta bud'esu a hankali,
sauk'e numfashi ta kumayi jin wani irin daddad'an k'amshi da sanyi na ratsa dukkan sashin jikinta da zuciyarta,
cikin ranta tayi tasbihi da hamdalar ganin wannan d'aki mai tsananin kyau da sanyi da k'amshi mai samar da nishad'i,
ido ta bud'e tare da yin taku uku zuwa hud'u kanta ta sunkuyar tare da kallon yadda yatsun k'afafunta suke nitsewa cikin tattausan carpet d'in dake gaban gadon da take ganin tamkar gadon sarkin birnin sin da ta tab'a gani a mafarkinta,
cikin kasala ta zauna bakin gadon tare da tallabe hab'arta,
tana yiwa labulayen kallon tsab,
kana ta juyo inda tafi zaton window ne mai girma amman an mishi hijabi da labulaye ,
jin kukan tsuntsayen ya yawaita a wurin yasata fahimtar ta gefen wurin lambun gidan yake.
a hankali ta rarrafa tsakiyar gadon kana ta kwanta lub cikin tattausan borgon tare da lumshe idanunta dan wani nannauyan bacci da takeji yana fizgarta.
bayan wasu yan d'ak'ik'une baccin yayi nasarar saceta,
numfashi ta rink'a sauk'ewa a hankali hankali tare gyara konciyarta,
can cikin bacci ta fara ganin wani irin haske mai d'auke ido kana yanata matsowa inda take,
saida hasken yazo gab da ita sai taga ashe Aryan ne yana nad'e cikin likkafani sai fuskarshi ce kad'ai a fili,
cikin tsananin tsoro ta fara ja da baya tana kuka shi kuma sai matsota yakeyi cikin suffar ban tsoro domin hasken da yake tare dashi yayi yawa.
cikin wannan yanayi take baccin tare da tsoro batafi awa d'aya da rabi ba dayin baccin ta farka a razane kana ta tashi zaune bisa tsakiyar gadon,
tare da zazzaro ido,
wayam d'akin ba kowa nan take wani sabon tsoro ya rufeta ga haniniyar dawakai daya karad'e gidan.

Shi kuwa Hamma Yusuf tunda ta wuce d'akin,
ya bita da ido,
kana data k'ule mishi ya lumshe idanunshi,
na tsawon wani lokacin, nazarurrukane iri da dama yakeyi a ransa,
yana cikin wannan yanayin bacci ya saceshi,
bai wani dad'e yana baccinba dan baifi awa biyu ba,
buk'atar shiga bathroom ta tasheshi,
cikin baccin yajishi a matse,
bud'e idanunshi sai ya kuma lumshesu tare da mik'ewa zaune yana ji tamkar fitsarin zai kwabce mishi,
a hankali ya mik'e tsaye tare da juyawa ya nufi bedroom yana d'an tafiya cikin alamun baccin bai isheshiba,
kai tsaye ya kutsa kai cikin d'akin domin sam shi yama mance tana ciki.
Bathroom d'in ya nufa,
sai ya kuma juyowa da sauri jin alamun motsin mutun,
ita kuwa ganinshi yasa ta d'anji tsoron dake tare da ita ya d'an gusa,
shiyasa ta fara kiciniyar gyara zaman takurar da tayi.
ido ya d'an zuba mata na d'an wani lokaci yana nazartar yanayinda take ciki,
sai ya kuma kauda kai jin fitsarin na shirin b'allowa.
d'an gajeren tsaki yaja tsuke fuska kana ya shige bathroom d'in.

7 minutes yayi sannan ya fito bisa dukkan alamu al'wala yayi,
ko inda take bai bai kallaba,
gaban durowa yaje tare da bud'ewa wata

Please Login or Register in order to submit comment