Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

d'an rusunar da kai tare da bashi hannu,
sukayi musabaha kana ya nuna mishi wurin zama tare da cewa.
"Malam bisimillah."
cikin jin dad'i da yarda da tarbiyar Yusuf M Jabeer ya zauna,
kana su Affan, Aryan, Idi Jafar, Matawalle, suma suka zauna.
sannan shima Yusuf ya zauna,
suna cikin gaishe-gaishe sukaji sallamar maigadin,
inda Jafar ya amsa mishi kana yace.
"Baba ya akayi ne?."
cikin hausarshi da bata gama nunaba yace.
"Wani dattijone ke sallama daku."
cikin kauda kai Jafar yace.
"Kaje kace mishi yaje ya dawo gobe."
wannan Dottijon kuwa wanda shine a tsaye a bakin k'ofar yayi muryar mai gadi sai ya gyara tsayuwarshi tare da cewa.
"Yafa ce yana da mgna daku dukane."
cikin jin wani yanayi Yusuf yace.
"Jeka iso dashi."
to yace kana ya juya baya tare da komawa asalin kamannin dasu Yusuf suka sanshi dashi.
cikin dottaku yayi sallama tare da shigowa parlour,
cikin mamaki Yusuf ya mik'e tare da cewa.
"Ayyah Kaka ashe kaine, sannu da zuwa shigo daga ciki ga wurin zama."
cikin tafiya irin tasu ta tsofaffi ya ratso tsakiyarsu kana ya zauna inda Yusuf ya nuna mishi,
Affan ne yayi murmushi tare da cewa.
"Kaka kamar na ganeka fa."
shima tsohon murmushi yayi kana yace.
"Eh lallai kuwa ai mun tab'a had'uwa a Airport ko?."
da sauri Jafar yace.
"Eh tabbas haka akayi."
shima Aryan shiru yayi yana nazari kamar ya sanshi daga bisani yace.
"Kaka ni dai a mafarki na sanka."
murmushi dottijon ya kumayi kana ya juyo ga Yusuf ya mik'a mishi hannu alamar yazo,
ba musu Yusuf ya matso a nan yaga zoben hannunsu iri d'aya sak da sak,
saida ya zaunar da Yusuf kusa dashi kana ya kalli M Jabeer da sam jikinshi bai gamsu da tsohonba,
murmushi yayi mishi kana yace.
"Kada ka wahal da kanka a son sanin gskyar lamarin ni wanene,
zanyi muku bayani,
amman fa sai naji naku bayanan,
dan muma bamasan gaibu bane."
jin haka yasa gaba d'aya suka nitsu kana aka sake sabuwar gaisawa.

M Jabeer ne ya fara yin mgna bayan yayi gyaran murya ya juyo ya fuskanci Yusuf cikin nitsuwarshi yace.
"...!



by
*GARKUWAR FULANI*



*HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 23*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*




"Yusuf ka dad'e kana min tambayar shin wai waye d'auki nauyin karatunka,
har kake cemin kana son ka sanshi kayi mishi godiya ka kuma yi mishi ihsani bisa kyautatawa rayuwarka da yayi.
Duk lokacin da ka gaya min haka ina ce maka babu abinda zaka yi mishi a duniya da lahira sai ka tsare mutuncinka da tarbiyarka."
cikin gamsuwa Yusuf yake gyad'a mishi kai alamar eh,
shi kuwa M Jabeer cikin kamala yace.
"Toh Alhamdulillah yau dai zan gaya maka wanene ya d'auki nauyin karatunka."
cikin zak'uwa Yusuf yace.
"Wanene shi a ina yake meyasa yamin wannan gatan?."
cikin sauk'e numfashi M Jabeer yace.
"Abban kane mahaifinka."
cikin kad'uwa Yusuf, Aryan, Affan Jafar duk suka had'a baki wurin cewa.
"Abba kuma?."
kai ya jinjina musu kana yaci gaba da cewa.
"Abban dai, shine ya d'auki nauyin karatunka,
yace kada in gaya maka shine sabida a lokacin kayi mishi laifi kuma yana son nuna maka illar abinda kayi

[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: yace kada in gaya maka shine sabida a lokacin kayi mishi laifi kuma yana son nuna maka illar abinda kayi ne,
ya gaya min duk abinda ya faru tsakaninku,
ya kuma cemin Maman Yusuf ta shiga tashin hankali kan korar Yusuf da yayi,
shiyasa yayi hikimar turashi k'asar woje,
a cewarshi in taga d'an nata baya k'asarma gaba d'aya zatafi samun konciyar hankali,
zatake ganin kamarma babu komai karatun ya tafi,
yace kuma shima kanshi Yusuf zaifi nitsuwa,
yace min yasan wasan polo burin Yusuf ne dan haka ya biya mishi makudan kud'ad'e yaje Jurassic Park polo,
kana ya k'ara da biya mishi UCT inda ya karanci business administration wanda shine burinshi."
gyara zama yayi tare da ci gaba da cewa.
"Abbanka yanada buri akan in ka dawo zai maka aure,
kafinma kaje buga world polo na 2015 sai ga tsautsayin nan ya rufta da kai tun randa kayi kwana uku da dawowa,
bayan nan kuma sai ga wasu manyan matsalolin sunata bibiyar rayuwarka."
cikin tab'e fuska Affan ya ja d'an gajeren tsaki kana yace.
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: sun tozartashi a idanun duniya sun zubar mishi da mutunci."
sai ya kuma juyo ya kalli Aryan yaci gaba da cewa.
"Wlh kaci amanar abota, koda turmi da tab'arya ka samu Yusuf a kan Zahra wlh kai mai rufa mishi asirine,
bare kaifa zatone domin baka tabbatarba ka kuwa gani a court badan Yusuf mumini bane da wlh baka da nasara."
cikin sanyi Aryan yace.
"Affan ina sonka a raina mutuncinka da darajarka sun k'aru a idanuna sabida nasan ko bayan raina Yusuf yanada amini mai sonshi bisa gskya da amana,
amman ina jin ciwon yadda kake zargina da cin amana,
abinda nayi ya zamarmin dolene,
na forko dai nasan Yusuf ne yayiwa Zahra fyad'en
domin tun lokacin da abin ya faru,
bayan Zahra tayi ta suma tana farfad'owa koda Yusuf yazo na zargi yanayin shi, to rashin tabbaci yasa ban bi ta kanshi ba,
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: lokacin da muka meda Zahra gida,
kai tsaye daga Girei cikin jimata na koma naje wurin sana'ar idi aka kwatanta min gidanshi daga nan na wuce gidan idi,
inda ina shiga gidan na sameshi a tsakar gida halin da nake ciki na tashin hankali yasa banmi shi cikin lumana ba,
kawai sai na fad'a mishi da duka nayi mishi azabebben duka yayinda shi kuwa ko hannu bai d'aga ba don ramawa ko kare kanshi saida naga na galabaitar dashi kana na zauna ina zubda hawaye tare da meda numfashi.
nace idi ka cucemu kaci zarafinmu ka haincemu,
bai cemin komaiba sai kukan da yakeyi tamkar zai had'iyi ranshi,
cikin firgici nace shi kenan ka kasheta hankalin ka ya konta.
Jin haka sai naga idi ya mik'e a firgice cikin tsananin tsoro da fargaba jiki na rawa naga ya shige bedroom ba jimawa naga ya fito da qura'an a hannunshi gabana yazo ya durk'usa cikin kid'ima da azaban kuka ya d'aura qura'an d'in a kanshi tare da cewa.
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: "Wallahi! Wallahi!! Wallahi tallahi!!! na rantse da tsarkin qura'an d'innan na rantse da girman al'arshi wlh banine nayiwa Zahra gyad'eba wlh ban tab'ata wlh ko bathroom d'in da take ciki ban shigaba wlh ban kasheta ba.
sai ya kuma fashe da kuka tare cewa.
Aryan k'addara ce ta ruftawa mumini mummunar k'addara ce ta riski rayuwar Yusuf wlh shine yayiwa k'anwarshi fyad'e yarinyar da ya rayu yana bata kariya,.
nan idi ya bani lbrin yadda abin ya kasance tun daga shigarshi part d'in Yusuf.
sai na had'a da zargin da nake mishi koda na koma gida kuwa na samu k'ofar baya a bud'e take kuma tabbas naji haniniyar dawa kanshi,
abinda ya hanani nasara a court kuwa Idi ne da tausayin Yusuf da k'aunarshi ya sashi yak'i fad'in gskyar da ya fad'in min sannan itama Zahra tazo tak'i fad'in gskya duk suka taru suka rufa mishi gskya,

ni kuwa shine dalilin da ya sani kuka a court in dai har Zahra da yayiwa laifin zata b'oye ashe ni kuwa naji kunyar bayyanawa duk da nima na bayyanane dan kar hak'ik'in kashe idi ya rataya kan Yusuf bana son yaje k'iyama da tarar da tarin zunubai,
nayi kukane a ranar shariyar k'arshe ganin idi da Yusuf bai amfaneshi da komaiba ya yarda zai sadaukar da ranshi kawai dan ya kare mutuci da martab'arshi,
inaga ni da Yusuf yake tamkar abokin tagwaucina inaga nida Yusuf yake ganina tamkar ciki d'aya muka fito. sannan a wani sashin kuma tun randa Yusuf ya dawo ake kirana da min barazar sai an kasheshi,
koda lokacin da kuke gidan maid'in AS butu akwai wata tirela sake gaban Yusuf wlh bibiyarshi sukeyi akan duk inda ya nufa su bishi su take motarshi,
na rasa su wayene to lokacin da muka kai Zahra na d'auko Safwan zamu dawo ne yake cemin,
Aryan bazan b'oye maka ba,
kayi k'ok'ari Yusuf ya bar k'asar nan wlh kasheshi ake son yi ni dai naji Mommy na tana mgna kuma a kan Yusuf ne kuma kasheshi ake son yi, yace min shi
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: yace min shi dai tabbas yana hasada yadda Yusuf ya fishi a harkar polo amman shi dai baya son a kashe Yusuf.
share hawaye Aryan yayi kana yaci gaba da basu lbri yana kuka yace.
Kaina ya d'auki zafi ga abinda Safwan ya gaya min ga abinda idi ya gaya min ga abinda masu min barazana da ran Yusuf suke gaya min,
na rasa ta ina zan kare Yusuf ta ina zan tai maka mishi,
kana in nabi shawarar Safwan Yusuf ya bar k'asar nan tofa za'a kashe Idi domin ko yaya zanyi shaidu sun nuna shine,
ganin abubuwa sun cakud'e ne yasa,
naje na samu Abba na nace zan shigar da karar Yusuf ina zarginshi.
to ganin yadda Abba ya shiga tashin hankali ne shiyasa na gaya mishi gskyar lamari.
anan shi kuwa Abba yake shaida min.
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: "Ba dole matsaloli suyi ta bibiyar rayuwarshi ba, tunda yana tare da mugun aboki maci amana."
jin haka yasa Aryan ya kalli inda Affan ke zaune ido cikin ido yace.
"Uhummm Affan kenan kai wato har yau dai kanaga ba Yusuf bane yayiwa Zahra fyad'e ko?."
cikin tsuke fuska Affan ya d'an zaro mishi ido tare da cewa.
"Aryan kenan to bari kaji in gaya maka ni nan Affan na fika sanin tabbas Yusuf shine yayiwa Zahra fyad'en."
cikin mmki M Jabeer da Aryan suka kalli Affan tare da cewa.
"Kuma kake tuhumarmu da cin amana?."
kauda kai yayi kana ya kalli Dottijon nan cikin takaici yace.
"Dan Allah Kaka abinda Aryan da d'an uwana sukayiwa Yusuf sun kyauta mishi?
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: shiyasa nida Abba da M Jabeer mukafi jin dad'in zaman shi Yusuf d'in a hannun hukuma ko ba komai yana cikin tsaro,
Abba kuwa tausayin Yusuf ne ya sashi kuka a court domin ga nashi magautanma sun dawo kan Yusuf d'in.

Cikin da alhini da mmkin wannan al'amari Jafar yace.
"Ikon Allah wato wannan shine abu a duhu, to kuma meyasa Hamma Jabeer ya fito ya gayawa duniya ya kori Yusuf daga team nashi?."
jin haka yasa M Jabeer gyara zama tare da cewa.
"Tun randa muka dawo Nigeria nida Yusuf na fara amsa kiran wasu mutane kan tabbas in dai nayi kuskuren barin Yusuf ya tafi gasar world polo to a bisa ranshi,
[10/02 9:41 AM] My 2nd Mtn: sun nuna sai dai in saida musu Yusuf domin sunyi imani da maganar matsafansu cewa in dai muka shiga gasar dashi to zamuyi nasara,
su kuwa a matsayinsu na k'asar da duniya takeji dasu basa son ace kamar k'asar Nigeria ta kadasu a duniya."
sai ya kuma kalli Yusuf da ya zama kamar dasashi akayi cikin sanyinshi yace.
"In baka mantaba na bawa Affan wasu takardun ya kaimaka kasa hannu?."
cikin sanyi ya gyad'a mishi kai, alamar eh bai manceba,
shi kuwa M Jabeer Affan ya kalla tare da cewa.
"Toh takardune da k'asar Argentina suka bada akan dole na basu hayarka,
in kuwa ban basu hayarkaba to karmu shiga gasar,
in kuma muka shiga sun cemin sun shirya kasheka har lahira kuma a wurin gasar zasu kasheka,
ina tunanin in kaga takardun zaka k'i sa hannun sai ka tambayeni dalili sai gashi cikin ikon Allah bakama lura da takardun menene bane kawai dai kasa hannu,
idan baku mantaba a ranar na wuce Abuja,

kuma koda naje can Argentina na wuce domin duk shariyar da akayi tayi ai bananan,
sai a shariyarku ta k'arshe na dawo wanda lokacin dudu-dudu wata biyar ya rage ayi gasar,
to ina Argentina naji labarin abinda ya faru da Yusuf tashin forko na binciki Aryan inda ya gaya min gskyar lmarin,
ya kuma k'ara min da cewa Jarsti polo team na Lagos ma sun tasoshi gaba kira babu dare babu rana suna mishi barazar zasu kashe Yusuf domin su burinsu kawai su kasheshi,
a nan adamawa kuwa sunada wanda yake sanar dasu duk motsin Yusuf,
inda saida mukayi bincike muka gane cewa Hajia Yabi ce mahaifiyar Safwan ce take basu dukkan bayanan da sukeso akan Yusuf,
yayinda sam d'anta Safwan baya son abinda take k'ullawa,
ita kuwa tana hakane dan a ganinta Yusuf ya dagushe d'anta a fuskar masarautarmu sannan ga burinta na d'aukan fansa akan shariyar da Abba yayiwa d'anta Lurwan wanda ta haifa a gidan mijinta na forko kafin ya saketa mahaifin Safwan ya aureta.

Ai Hajia Yabi Mommyn Safwan yar sokotoce, to shekaru shida zuwa bakwai da suka wuce an gayyaci Abba yaje yayi wata shariya a sokoto a kan fyad'e inda shi wanda yayi fyad'en d'ane ga ita Hajia yabi wanda ta haifa a gidan mijinta na forko kuma d'an nata yanada mata so shiyasa akayi mishi hukuncin Allah aka jefeshi kamar yadda shariya ta tanadar,
to fa tun rasuwan wannan d'an nata yayan Safwan to daga nan taci alwashin itama sai tasa an kashe Yusuf wai shima Abba yaji abinda taji,
so shinefa ta samu number ta wurin Safwan ta bawa yan daban nata number shine suke kirana suna min barazana da rayuwarshi.
so wannan abu yasa dole na shigar da k'arar Yusuf,
shi kuwa Safwan yayi ta bibiyar gidan Raihana duk lbarin da ya samu sai ya buga a jaridarsu,
da haka ya juya ra'ayin mahaifiyarshi,
yace ta bari ai yanzu shima ya had'u da tasa kaddarar,
randa aka yankewa Yusuf Hukuncin sai yace mata ta bari sai Yusuf ya fito kurkuku da haka dai kuma duk shirinta Safwan zaizo ya gaya min,

So jin haka yasa, nasa Aryan ya binciki gaskiya aka fyad'en da akayiwa Zahra in kuwa Yusuf ne da laifi a hukuntashi.
yayinda duk abinda akeyi ina Argentina sai dai Matawalle yana tura min komai."
cikin mamaki Jafar yace.
"Shima Matawalle yasan komai kenan?."
cikin nitsuwa M jabeer yace.
"Shi Matawalle ai ni na turoshi cikinku domin jin gskya na kuma sanar dashi wani abu so shiyasa duk motsinku na sani.
da wanna damar nayi amfani na hana Argentina samun Yusuf domin na nuna musu yana tsare a hannun hukuma bisa laifin da yayi
shiyasa a wannan shekarar muka shiga gasar amman tun a zagen forko aka kadamu hakane Argentina suma a zageye na biyu aka fiddasu,
inda America ta samu nasarar lashe gasar."
cikin kauda kai Affan yace.
"Nafa san da wannan duka kawai,
abinda na sani ya kamata kuyiwa Yusuf adalci."
cikin sauri Aryan yace.
"Adalcin munsan gskya mu boyeta wa al'k'alan duniya ko,

[10/02 12:07 PM] My 2nd Mtn: ka manta sarkin sarakuna yana ganinmu kana yana jinmu,
Affan so kake in bari a kashe Idi bayan bashi yayi fyad'en ba,
Cikin sanyi Matawalle yace.
"Affan nayi mmki da kace kasan Yusuf ne yayi laifin kuma kake kareshi,
gskyar mgna ni kam a lokacin nayi zaton Idi ne kuma har yau kaina na kullewa in na tuna yadda kuka bada hujjoji a court ta yaya akayi ya zama Yusuf ne yayi laifin?."
cikin sanyi Aryan ya kalli Yusuf tare da cewa.
"Wannan bayani sai Yusuf ne zai manashi,
in ba hakaba babu mai gamsuwa."
[10/02 12:07 PM] My 2nd Mtn: cikin tsananin jin kunya da rauni Yusuf ya d'an harari Aryan tare dayin mgna can k'asan mak'oshi yace.
"Wannan kuma sirrina nida Zahra." jin haka
dottijon nan ya gyara zama tare dayin murmushi yace.
"Bayanin idi ma zai bada haske kan lamarin duk da ni dai nasan sawun b'arawo idi ya taka."
juyowa sukayi baki d'aya suna kallon idi yayinda Matawalle yace.
"Toh amman meyasa idi yaso ya amshi laifinda kuketa cewa ba nashi bane ba?."
Gyara zama idi yayi tare da rumtse idanunshi sai ga wasu zafafan waye suna zuba,
murya na rawa yace.
"Yusuf ba mazinaci bane k'addarace ta rigayi fata."
sai ya kuma sunkuyar da kanshi tare da cewa.
"Aranar da abin ya faru, ina ganin Raihana ta fita nayi maza na shiga parlour,
[10/02 12:07 PM] My 2nd Mtn: ina shiga tsakiyar parlour sai na tsaya sabida, ganin k'ofofin d'akuna guda uku sai na rasa wannene Zahra take ciki,
ganin na tsaya ina b'ata lokacin yin nazari,
sai kawai na kusa kai cikin kofar dake hannun dama,
ina shiga nan sai naga babu kowa a ciki sai nayi zaton ko ta shiga bathroom,
haka yasa na kusa kai cikin bathroom d'in inda ina shiga nanma na samu ba kowa,
ganin ba kowa kuma ga azabar fitina da nasawa kaina ya haddasamin jin fitsari,
sai na tsaya nayi fitsari a nan,
kana na fito,
ina fitowa sai na shiga k'ofar tsakiyar,
nan kuma sai na samu babu komai sai tarin akwatuna bisa dukkan alamu kayan Amarya Raihana ne aka ajiye a wurin,
ban wani b'ata lokaci ba na juyo zan fito daga d'akin amman sai k'ofar ta cije nayi-nayi ta bud'u taki tsoro ya rufeni ganin shi kenan damata zata wuce kuma asirina zai tonu tuni zufa ya ballomin tsoron da nakeji yasa tuni sha'awarma ta guje min,
[10/02 12:07 PM] My 2nd Mtn: haka nayi ta kiciniya nafi minti 6 kafin na samu k'ofar ta bud'u ashe in an murd'a handil sai an d'an d'agashi sama kafin k'ofar ta bud'u,
ina bud'ewa na fito a firgice na nufi d'aya k'ofar inda nakeda tabbacin a nan Zahra take,
na kama hannun k'ofar zan bud'e kenan sai naji sautin murd'a key a cikin labulaye bisa dukkan alamu sun nuna wata k'ofarce a wurin,
cikin rawan jiki da tsananin tsoro na koma bayan kujeru na durk'usa kana raba cikin manyan labulaye da suke zagaye da parlour,
ina gani ta cikin labulayen,
naga an turo k'ofa daga inda nake na jiyo haniniyar dawakai sannan na haggo su sunata mik'a wuya,
sai kuma naga mutun ya shigo,
yana k'arisa shigo tsakiyar parlour sai na gane fuskar da bazan tab'a manceta bane,
ganin Yusuf ne a take na sakejin wani azabebben fitsarin,
gaba d'aya jikina ya fara karkarwa duk k'arfina ya tafi na kasa motsi bare guduwa dan ban mance abinda yamin lokacin yana yaro ma bare daya girma,
ina ganinshi yana tafiya hannunshi dafe da mararshi fuskarshi tayi jazir gaba d'aya zuface ke bin fuskarshi kuma ya kasa mik'ewa tsaye,
k'ofar da nakeda niyar shiga nan naga ya shiga,
yana shiga k'ofar ta dawo ta rufu amman bashi ya rufetaba don ina hangoshi a hankali yake tafiya har gaban gadon d'akin kuma ban hango Zahra ba,
sannan naga k'ofar ita da kanta ta dawo ta rufu,
bayan rufuwar k'ofar da kamar minti 3 sai najiyo muryar Zahra tana cewa,
waye ne kai akwai mutunfa, daga nan kuma sai naji ta kwallah ihu da kururuwa sai na kuma jin shiru na wasu d'ak'ik'u,
can kuma sai naji tanata kuka da magiya yayinda nakeji shima Yusuf yana kuka da myna amman bana gane shi me yake fad'in,
gaba d'aya hankali na ya tashi tsoro ya rufeni naga ishara ido da ido,
inaji Zahra tana ihu har tayi shiru,
jikina tamkar mazari haka na fito cikin labulayen da nake,

gaba d'aya jikina ya fara karkarwa duk k'arfina ya tafi na kasa motsi bare guduwa dan ban mance abinda yamin lokacin yana yaro ma bare daya girma,
ina ganinshi yana tafiya hannunshi dafe da mararshi fuskarshi tayi jazir gaba d'aya zuface ke bin fuskarshi kuma ya kasa mik'ewa tsaye,
k'ofar da nakeda niyar shiga nan naga ya shiga,
yana shiga k'ofar ta dawo ta rufu amman bashi ya rufetaba don ina hangoshi a hankali yake tafiya har gaban gadon d'akin kuma ban hango Zahra ba,
sannan naga k'ofar ita da kanta ta dawo ta rufu,
bayan rufuwar k'ofar da kamar minti 3 sai najiyo muryar Zahra tana cewa,
waye ne kai akwai mutunfa, daga nan kuma sai naji ta kwallah ihu da kururuwa sai na kuma jin shiru na wasu d'ak'ik'u,
can kuma sai naji tanata kuka da magiya yayinda nakeji shima Yusuf yana kuka da myna amman bana gane shi me yake fad'in,
gaba d'aya hankali na ya tashi tsoro ya rufeni naga ishara ido da ido,
inaji Zahra tana ihu har tayi shiru,
jikina tamkar mazari haka na fito cikin labulayen da nake,


[10/02 12:08 PM] My 2nd Mtn: ina fitowa tsakiyar parlour da rarrafe kamar yaro,
nazo tsakiyar parlour kenan saiga Yusuf ya fito daga d'akin rigarshi na bisa kafad'unshi yayinda kuma yake d'aure zariyar wondonshi,
kuma duk jikin wondon ya b'aci da jini.
shi ya ganni ni na ganshi sai dai ina zaton baya cikin haiyacin shi shiyasa yasan na ganshi amman bai bi ta kainaba
domin hankalinshi baya jikinshi domin kuka yakeyi cur-cur tamkar yaro haka kuma jikinshi rawa yakeyi,
ta k'ofar daya shigo ta nan ya fita,
ni kuwa cikin rarrafe na isa bakin k'ofar bedroom d'in lek'awa nayi daga zaune sai na hangi duk inda ya taka shatin kafafunshi sun bata wurin.
ganin jininne ya firgitani ban san lokacin dana mik'e tsayeba na juyo kenan da gudu zan fita ina gudu ina juyowa ina kallon ta inda jinin yake kawai sai naji nayi karo da Raihana.
so daga nan nasan na shiga ban d'aukaba baya fidda b'arawo gashi,
[10/02 12:08 PM] My 2nd Mtn: to shi kuwa daya fahimci haka sai ya rufe min bakina ya fito ya bada shaidar kanshi."



Shiru sukayi gaba d'aya suna alhini Yusuf kuwa sunkuyar da kanshi yayi.



nan Jafar kuma ya musu bayanin ai tsumi aka zuba musu a kun gyad'an da sukasha a wannan ranar,

Amman ya nuna musu rashin sanine yasa Zahra ta zuba musu tsumin inda ya nuna musu wai a zatonta zumace don su gidansu zama itace madadin sugar.



nitsuwa sukayi jin dottijon nan yayi gyaran murya kana yace.

"Ni musulmi ne d'an uwanku kuma ni ba mai cutarwa bane kuma nima bani da ilimin sanin gaibu,

to amman fa akwai abinda Allah ya sanar damu wanda ku bani adam bakwa sani kuma ni ina yawan rayuwa cikin bani adam."

wannan mgna tashi tasasu fahimtar dottijon nan ba mutun bane kamarsu so gaba d'aya sai suka firgita sab'anin Yusuf daya saba dashi M Jabeer kuwa tasbihi yayi ga Allah tare da gyad'a kai alamar gamsuwa,

hakuri dottijon ya basu har saida yaga sun nitsu kana ya basu lbrin randa ya fara ganin Yusuf.
[10/02 12:08 PM] My 2nd Mtn: mugun nufina ya jazamin masifa nayi nadamar halina nayi Allah wadarai da kaina shiyasa nayita kukan nadama, ina tuba da neman shiriya a wurin Allah domin da bani da mugun nufi da ban taka sawun b'arawo ba,
daga nan gidana na kuma inda tausayin Yusuf ya sani nayi ta kuka a tsakar gida nan Aryan yazo ya sameni,
naso in rufawa Yusuf asiri to jin Aryan yace min na kasheta shiyasa na gaya mishi gskya.
Da akaje Court kuwa tausayin Yusuf yasani zubda hawaye kuma duk tambayar da akayiwa Yusuf cewa yake shi bamazinaci bane ba cewa yakeyi bashi bashi ya mata fyad'a ba shifa bai tab'a musawa ba in ance kai ne kayi mata fyad'e sai yace ni bamazinaci bane.
Haka kuma nima in ance min an ganni a gidan dole ince eh tunda naje gidan har cikin parlour,
kuma nima cewa nakeyi Yusuf bamazinaci bane, amman sam hankalin mutane bai dawo kan su fahimci cewafa Yusuf bai musawa kanshiba niko ban d'aurawa kainaba sai dai ina bada tabbacin shifa Yusuf ba mazinaci bane,
sai a shariyar k'arshene naso in karb'e laifin Yusuf da bakina,
[10/02 12:08 PM] My 2nd Mtn: to randa Yusuf ya fito furzin a ranar mum had'u daku Yusuf Jafar Affan da Aryan k'arami a Airport,

cikin sanyi Jafar yace.

"Hakk'un."

Affan ma kai ya gyad'a shi kuma dottijon Yusuf ya zubawa ido tare da cewa.

"Tun daga ranar ban kuma baiyana a gareka ba,

sai lokacin da muka had'u a madina cikin azumin daya wuce,

inda a nan na baka zob'en hannunka."

cikin k'arfin hali da jarumta Yusuf ya jinjina kai,

M Jabeer da Aryan kuwa da Matawalle cike suke da mmki gara Jafar da Affan sun tab'a ganinshi.
[10/02 12:08 PM] My 2nd Mtn: Randa ka dawo daga k'asar Dubai da yamma kun fito daga cikin Yola a lokacin ni kuwa da jikana mun

Please Login or Register in order to submit comment