Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*******

Rayuwa taci gaba da tafiya cikin wata d'ayan nan abu da yawa ya faru,
Maman Yusuf tayi kuka har ta godewa Allah,

Aryan kuwa ido kirmishishi yake rayuwa abinshi,
yana yawan zuwa gidansu Yusuf domin a cewarshi Zahrace babbar shaidarshi,
Maman Yusuf kuwa bata nuna mishi komai a fuskarta in yazo sunanan kamar da can baya yanai mata kallon uwa tanayi mishi kallon d'a
Daddy kuwa sam yanzu ko gaisuwar Aryan baya amsawa,
yayinda Abba kuwa ya maida Aryan tamkar d'anshi yana al'fahari dashi.


Yusuf kuwa duk tsawon wannan lokacin babu wanda zaice yaji sautin muryarshi wai a zumar yayi mgna,
yayinda Affan, Jafar, Sulaiman kuwa suka meda gidansu Aryan wurin zuwansu,
sabida suke kula da lamuran Yusuf Kamar matsa mishi ya d'anci abinci ko su jawoshi zuwa farfajiyar gidan,
Hajia Kaka kuwa kulawar da take bawa Yusuf ko Aryan bata bashi wannan kulawar,
hakama Raihana a cewarta ita ta yafewa duniya Ya Aryan d'inta,
ita yanzu ba ita bashi tunda shi maci amana ne,
tana yawan zuwa gun Yusuf tayi ta bashi k'arfin guiwar cewa su zasuyi nasara.


Zahra Kuwa rayuwa ta canza tunda aka shigo da ita gida bata fita ko bakin matsallancin suba,
akwai ranar da k'awarta Dija ciroma tazo mata,
sukayi ta kuka tare,
to da Dijan zata tafi ne Zahara ta rakata bakin gate inda yara ke d'iban ruwa sai taga suna kallonta tare da nunawa jununsu ita sai taga sun fara k'us-k'sun alamun da ita sukeyi,
ranar taci kuka,
toh daga ranar bata kuma fitaba.

Aunty Amarya kuwa Daddy ya tarkata kashinta ya watsar,
tana dai zaune a gidan amman tana ganin tijara da k'uncin rayuwa,
domin wani rashin mutucin Ummi ke zuba mata,
bugu da k'ari ga habaici da zaurancen da take yawan mata,
sai dai a haka take hak'ura,
da abin ya yawauta ta kokawa mahaifiyarta,
inda yayanta Uncle Gambo da Tattin suka zo suka bawa Daddyn hak'uri suka nemi Al'farman ya meda aurenta,
toh Aunty Amarya taci darajar mahaifiyarta da yayanta Daddy ya meda aurensu,
amman fa har yanzu bai huceba.

Adda Zulaihat kuwa ita kam yanzu Affan ne nata yawanci kullum sai sunyi mgna a waya,
takanje wurin Yusuf a kai a kai.

Abba kuwa ya d'aga zaman k'arar idris a Hukuncin Allah court a cewarsa sai yaji me d'aya court d'in suka binci ko.


Malam Jabeer kuwa har yanzu yana Abuja,
kullum sai yayi bincike kan lamarin halin da Yusuf ke ciki,
yana so yayi mgna dashi amman kullum sai ace mai Yusuf bai fara mgna ba,
ya dai tsananta addu'a Allah ya toni asirin mara gskya,
yana son dawowa Adamawa amman babu dama domin shima wani babban al'amarine ya ajiyeshi a can d'in.

Yau ta kama asabar inda ya kasance saura kwana biyu wata d'ayan da kotu ta bada ya cika,
gaba d'aya Affan ya meda hankali kan tattara shaidarsu,
bashi da hutu ko kad'an.

Mama kuwa yau tayi niyar zuwa wurin gudan jininnata,
ta samu tayiwa Abba wayo cewar dubiya zataje asibitoci
so ya barta kai tsaye tunda yasan dama tana zuwa,
gashi yaga ta dena mishi naci kan mgnar Yusuf d'in,
ita kuma Mama Daddy ne ya bata shawarar ta dena yiwa Abba mgnar.

Bayan tayi sallan walaha,
ta idar tayi karatu kusan na awa d'aya,
sannan ta mik'e ta fara shirinta,
yayinda Zahra ke zaune gefenta,
tana yanke farcenta,
a hankali ta kalli inda Zahran take,
a take idanun Mama suka cicciko da hawaye, tausayi Zahra ke bata domin gaba d'aya ta zama abar tausayi yawanci ko me takeyi zakaga hawaye na bin fuskarta,
sai dai tana sa tafin hannunta ta shareware,
toh yanzunma haka ne,
tana sunkuye tana yanke farcen yatsun k'afarta ga kuma hawaye na bin fuskarta har yana d'iga a k'asa,
cikin kula Mama tace.
"Goggon Abba."
shiru bata amsaba,
karo na uku Mama ta kuma cewa,
"Goggon Abba."
nanne ta d'an sha majina tare da amsawa cikin rawan murya tace.
"N... Na... am Mama."
cikin rauni Mama ta ajiye hijabin hannunta gabanta tazo tare da sunkuyowa ta d'agota tsaye suna fuskantar juna,
tafin hannunta tasa tana share hawayen dake bin fuskar Zahra cikin taushi tace.
"Kiyi hak'uri Zahra, dukkan tsanani yana tare da sauk'i,
ki dena kuka kinji ko Goggon Abba?."
kai ta gyad'a alamar to amman still hawaye na zubo mata,
jawota Mama tayi zuwa bakin gado ta zaunar da ita cikin sanyin murya tace.
"Ita rayuwa kowa da irin jarrabawarsa,
domin mumini Allah ke jarabta dan gwada k'arfin imaninshi,
ki ruggumi k'addararki in sha Allah bazaki tab'e ba,
domin ke dai ba zina kikayi ba,
azzalumin daya aikata miki haka kuwa,
shima zaiga sakaiya."
haka dai tayi ta rarrashinta saida taga ta samu nitsuwa,
Aunty Amarya kuwa da tun d'azu ta shigo da nufin zata cewa Maman Yusuf ta fito su tafi sai ta kuma samesu a haka,
so sai ta kuma parlour domin yanzu zasu sata kuka,
toh bayan tayiwa Mama mgnar su tafine itama Zahra ta biyo bayan Mama da Auntyn nata,
da zummar zatayi musu rakiya,
suna gaba tana baya har suka fito tsakiyar gidan inda suka samu hajja Inna da Ummi suna zaune,
Mami na gefen pompo tana wonki,
Nana kuwa tana rik'e da waya da Alana charting takeyi,
suna fitowa Hajja inna dake bayansu ta fara rabka salati tare da cewa.
"Ke Zahra me haka zaki fito mana tsakiyar gida da k'azanta a filin Allah?."
da sauri Zahra ta tsaya yayinda tuni idonta ya ciko da hawaye domin tunda abinnan ya fari wasu lokutan ko abu in ta tab'ashi Hajja Inna bazata ciba wai sai tace Zahra gaba d'ayanta najasace,
toh hakanne yasa tuni idonta suka tara ruwa,
cikin takaici da k'unci Mami ta harari Hajja Inna domin tana jin zafin abinda takewa k'anwarta,
Aunty Amarya kuwa bata tsayaba kawai fita tayi bakin gate dan bata son taji mugayen kalaman surkar tata,
Ummi ce ta tsirtar da yawu tare da cewa.
"Me kuke harararta ai gskya take fad'i ya zaki fito mana tsakiyar gida jiki duk jini."
jin haka yasa Mama saurin juyowa tana kallon jikin Zahran,
itama Zahra kai ta juyo tare da sunkuyawa tare da kallon bayanta,
ido ta zaro tare da kallon Mama,
da sauri Mama ta kamo hannunta suka koma part d'inta,
Hajja inna kuwa sai cewa tayi.
"Ashe kunyi sa'a tunda bai d'irka mata cikiba,
ni nama yi zaton ya tsirta mata ciki ai,
banza me jajayen kunnuwa babu abinda ya iya sai dukan tsoffi da yiwa yaran mutane kaciya,
koda yake ai dama dashi da ita duk yan iska ne."
Cikin takaici Mami ta danne hawayen dake son zubo mata murya na rawa tace.
"In ma Hamma Yusuf da Zahra yan iskane,
dole dai jikokinki ne,
wayama san abinda kika aikata a k'uruciyarki."
Nana ce tayi dari tare da cewa.
"Wlhi kam ba mmki ita suka gado."
habawa ai tsohuwarnan kamar ta cinyesu d'anye,
Ummi kuwa sai ingizata takeyi,
domin ita Ummi har ga Allah taso ace Zahra ta samu ciki a wannan abun,
dan ita tunima ta fara gulmatawa mak'ota cewa Zahra nada cikin shege,
dangi dai babu wanda ta kuma gigin kaiwa gulma,
tunda Goggo Aysha ta solleta.


Mama kuwa cikin sauk'e ajiyan zuciya da jin dad'i tace.
"Alhamdulillah Zahra,
kinga wani ikon Allah ko saida k'addarar fyad'e ta abka miki kafin kika fara al'adarki."
hawayenta ta share,
ita kuwa Mama Mami ta k'ira tace ta in tanada pand ta kawowa Zahra,
to tace sannan taje ta kawo mata,
Mama da kanta ta nuna mata yadda zatayi,
saida ta tabbar ta kimtsa sannan ta fito.

Aunty Amarya kuwa tana tsaye a wurin Jafar ya fito cikin shirin fita,
cikin girmamawa yace.
"Aunty ina zuwa?".
cikin jin dad'in halin Jafar da yadda yake son ta da yaranta babu d'an ubanci ko kad'an a ranshi murmushi tayi tare da cewa.
"Bayan P.Z. zamuje da Maman Yusuf."
mik'a yayi tare da cewa.
"Shike nan kuzo mu tafi nima can zani yanzu Affan yake kirana inje yana jirana a can."
"Toh ba laifi Allah ya kaimu Lfy."
cewar Aunty Amarya,
shi kuwa motarshi ya fitar daga parking lot sannan,
har gaban Aunty Amarya yazo,
yana daga ciki ya bud'e mata ta shiga,
tana shiga Mama na fitowa,
itama ta shiga sannan Jafar yaja motar,
saida suka hau kan titi Aunty Amarya ta juyo ta kalli Mama tare da cewa.
"Zahra nacan na kuka ko?."
da sauri Jafar yace.
Meya sata kukan da safiyar nan."
"Uhum ita da Hajja Inna ce dai."
Aunty ta fad'i cikin kawaici,
Mama kuwa cewa tayi.
"Alhamdulillah, ni yau hankali ya konta,
tunda yanzu dai inada tabbacin Zahra bata da ciki,
kamar yadda Hajja Inna take yawan fad'a."
cikin jin sanyi Aunty tace.
"Da akayi me kika da tabbacin bata da cikin?."
gyara zama Mama tayi tare da cewa.
"Alhamdulillah yau dai Zahra ta fara al'ada kinga dama bata faraba sai yau."
Jafar ma ajiyan zuciya yaja don yaji dad'in hakan,
haka dai sukayi ta tattaunawa har suka isa gidansu Aryan.



Bayan sun gaisa da kaka ita da kanta tayi musu jagora har part d'in Yusuf,
A parlour suka samesu,
Affan, Jafar, Dr Bashir, sai wannan d'an jarida Matawalle, da Sulaiman,
yayinda suka sashi a tsakiya sunata yi mishi magiya dan yayi mgna amman abu yaci tura,
Affan tamkar zaiyi kuka,
shi kuwa Yusuf sai taune lips enshi da yakeyi,
su Mama kuwa suna shiga da sauri suka k'arisa tsakiyar parlour,
gabanshi Mama ta zauna a k'asa kan carpet,
su Affan kuwa kab sai suka koma baya,
suna kallon wani irin k'auna ta tsakanin uwa da d'anta,
Shiko Yusuf tunda yaga Maman,
gaba d'aya sai fuskarsa ta sauya ida nunshi suka cicciko da hawaye masu azabar zafi,
ji yakeyi tamkar yaji aka samishi a idanun,
ita kuwa Mama gyara zama tayi suna fuskantar juna,
cikin danne k'uncin zuciyarta tace.
"Yusuf ya kake tunanin yadda nakeji a raina a kan rashin yin mgnarka,
shin so kake zuciyata ta bugane".
cikin sanyi ya fara jujjuya mata kai a hankali alamar a a.
gaming haka yasa su Affan jin dad'i da tausayinsu kenan Yusuf yana jinsu,
ita kuwa Mama sai ga hawayen da take dannewa sun silalo,
cikin rawan murya taci gaba da cewa.
"Ni dai nasan d'ana ba kurma bane ba kuma bebe bane,
lallai nasan tsananin abinda kakeji a ranka yafi yadda duniya take zato,
nasan d'ana jarumi ne,
toh amman Yusuf ga Dr dayake dubaka ya tabbatarmin lfyarka lau zakaji mgna zaka iya mgna,
toh in dai hakane meya hanaka mgna Yusuf,
ko dai kana son ka samin zargine a zuciyata,
gajifa mutane nata tabbatar da zancen Aryan,
meyasa bazaka bud'i bakiba ka kare kanka."
sai ta kumayi shiru da mgnar tana mai zubda hawaye,
shima Yusuf hawayen yake zubdawa,
cikin kuka ta fara mgna tare da yak'ini tace.
"Ni dai nasan irin tarbiyar da nayiwa Yusuf d'ina ni dai nasan Yusuf d'ina bamazinaci bane,
ni dai nasan wlhi tallahi Yusuf na baya aikata zina."
kanshi ya rink'a gyad'a mata alamar tabbas shi bama zinaci bane,
cikin muryar kuka tace,
"Yusuf wannan d'abi'a taka fa ta body language zata cutar da zuciyata da rayuwata,
kana zaton mgnar da kakeyi da gabban jikinka zai wadatar ne kana tunani a hakane zaka wonke kanka."
madadin ya bud'i baki yayi mgna sai yaci gaba da jujjuya mata kai alamar yasan body language da yakeyi bazai kub'utar da shiba,
wani irin kuka Mama ta saki dan zuwa yanzu ta fara zargin Yusuf baida gskya a d'aya sashin zuciyarta kuwa tana jin Yusuf d'inta bazai aikata hakaba,
Kuka takeyi sosai yayinda ta mik'e tsaye tasa hannunta duka biyu tana marinshi ta ko wanne gefen fuskarshi tana cewa.
"In dai kanada gskya to kayi magana in kuwa so kake zuciyata ta buga kaci gaba da yin body language,
in kasan kai mazinaci ne ka gaya min,
na yarda duniya su zageni a matsayin uwar da bata iya bada tarbiya ba."
kuka takeyi sosai tana maganganu masu tab'a zuciya,
Affan ne ya matso cikin zubda k'olla yake cewa.
"Please Yusuf kayi mgna,
ko dan Mama."
Aunty Amarya kuwa hannun Mama ta rik'o dan tabar dukan Yusuf amman sai fizgewa tayi tana cewa.
"Yusuf ka tabbata mazinaci kenan,
ka gaya min tun kafin zuciyata ta buga in mutu ka huta."
sai kawai ta fara wani irin masifeffen tari,
hannunta d'aya dafe da k'ahon zuciyarta,
Hajia Kaka da Aunty Amarya kam tuni kuka sukeyi Jafarma sai zubda k'ollah yakeyi,
wani irin zabura Yusuf yayi lokacin da yaga idanun Mama sun firfito waje,
sulewa yayi gabanta hannu bibbiyu yasa ya ruggumeshi k'afafunta kanshi ya cusa tsakanin guiwowinta,
cikin wani irin yanayin halin rayuwa ya saki nakasshen kuka,
muryarshi da jikinshi duk rawa sukeyi,
ita kuwa Mama sai tureshi tayi ta koma baya ta zauna kan kujera tana cewa.
"Tambaya ta k'arshe da zanyi maka,
Yusuf kaine kayiwa Zahra fyad'e!!???."
rarrafe ya farayi tare da kuka mai cin rai,
da sauri ya isa gabanta sunkuyar da kanshi yayi,
cikin tsananin kuka murya na rawa ya bud'i baki da k'arfi yace.
"Ni..........!!!!!






D'id'i
*NA*





Ttbl




Masu bibiyata da k'worafin in rufe group in bud'e na comments da ban kuyi hak'uri dan Allah ku bari,
inada dalilin da yasa na barshi a haka.
Masu kirana dan Allah ku bari dan dama tun forko nace muku banda kira, dan ko kin kirani ba d'agawa zanba, karkizo kina kirana ban amsaba kiji haushina.


Gareku masu buk'atar gyara Amare ko uwargidaye ko yanmata masu son gyare fatarsu, k'ofa a bud'e take,
zaku iya bibiyata a shafina na instagram ayshaaliyugarkuwa domin cancad'e haja kan rahusa mai sauk'i.

33

"Ni ba mazinaci bane,
Mama ki yarda dani wallahi ni bamazinaci bane,
Mama ki yarda dani domin ni na yarda da tarbiyar da kika bani."
sai ya kuma kontar da kanshi kan cinyarta ya saki kuka mai ban tausayi,
itama kukan takeyi tare dasa tafin hannunta tana shafa kanshi cikin disashewar murya tace.
"Ni na sani, d'ana bazai aikata fyad'eba,
ko duk duniya zasu yarda da maganar Aryan ni dai bazan yardaba,
dan nasan bazakaci amar tarbiyar da nayi makaba."
Affan kuwa hamdala yayi tare da sharte hawayenshi dan burinshi ya cika Yusuf ya fara mgna,
Dr Bashir kuwa yana ganin yayi magana ya sallamesu ya tafi.
Matawalle kuwa d'an jarida mai mutunci duk hirar Mama da Yusuf ya nad'i har yadda Yusuf ke kuka yana cewa shi bama zinaci bane,
ga hotuna da ya musu kan Yusuf na kan cinyar Mama yayinda tafin hannunta ke tsakiyar kanshi,
Jafar kuwa zama yayi tare da sauk'e numfashi,
Hajia kaka kuwa hamdala tayi tayi,
nan dai suka zauna sukayi ta tattaunawa yadda shariyar zata kasance,
Affan kuwa ya kafa ya tsare ya hana Aryan motsi duk inda yayi zaisa a bishi a baya,
A nan Mama ta wuni da Yusuf d'inta
da yamma Tatti mahaifiyar Aunty Amarya kenan da Uncle Gumbo suma sukazo,
Tatti taita fad'a a gaban Hajia kaka taketa zage Aryan, don yazo gaidasu tana ganinshi sai cewa tayi.
"Wallahi kaji kunya Aryan kayi asara da ka zama azzalumin aboki,
kuma in sha Allah babu kai ba nasara mugun banza."
shi kuwa Aryan ko a jikinshi sai cewa yayi.
"Kurman ya fara mgnane? ko har yanzu yana a bebenshi?."
babu wanda ya kulashi sai ya kuma sunkuyo kan Yusuf yayi mgna k'asa-k'asa shiyasa babu wanda yaji abinda yake fad'awa Yusuf d'in,
shi kuwa Yusuf sai ya rink'a jujjuya kai yana zubda wasu zafafan hawaye,
yayinda yake bin Aryan da wani irin kallo.

Haka dai lamarin ya kasance,
su Mama sai dare suka watse kowa ya koma gida.

Washe gari ranar Sunday,
Abba yake cewa Daddy ya tabbatar Zahra taje court goben,
shiko Daddy ko inda Abba yake bai kallba.


Washe gari Monday ta kama ranar za'a koma court,
12:02 pm,
court d'in cike take maqil da jama'a
baya Aryan ya gabatar da hujjojinsa,
sai aka buk'aci Affan a fili,
in yanada ja ko inkari,
haka kuwa ya fito,
nanfa akayi ta fafatawa tsakanin Affan da Aryan,
ganin kowa ya coge Affan yana k'ok'arin kada Aryan
kuma kotu bata gamsu da hujjojin Affan ba sai aka kuma d'aga k'arar nanda 10 weeks wata biyu da sati biyu kenan.

*************

Abubuwa da yawa sun faru a zaman watannin nan,
duniya ta cika da wannan zance,
hotunan Zahra da Yusuf sun zama abin d'aga kasuwar jarida,
shiyasa ko wacce jarida suke lik'a labarin Yusuf da Zahra a shafukansu na forko,
Zahra kuwa lamuran rayuwa sun juye.

Yusuf kuwa yayi wani rama dan,
yana cike da bak'in cikin zubewar mutuncinsa.

Safwan kuwa burin ranshi na gabda cika,
domin kullum sai ya kira Malam Jabeer yayi ta kai sukan Yusuf,
inda har yace matuk'ar zarginda akewa Yusuf gaskene to ya fiddashi cikin Jahan team ai dama haka Safwan keson ji sai ga jarida ta fito da wannan kanun labaran,
Affan har kuka yayi domin ya fahimci yana tubkane Safwan na warwarewa.

Abba kuwa yanzu Aryan ya zama na hannun damanshi.


Mama kam kullum addu'a takeyi Allah ya baiyyana gskya.

Aunty Amarya da Daddy kuwa yanzu abin da d'an sauk'i.

Komai aka sawa rana zaizo,
10 weeks sunzo kamar yau,
yau laraba kuma yaune za'a koma court,

12:20 pm Al'k'alin ya shigo inda gaba d'aya aka mik'e tsaye saida ya zauna sannan aka zauna,
shiru ya d'an ratsa hall d'in na wasu dak'ik'u,
sannan messenger ya mik'e tare da gabatar da shari'ar da za'ayi yanzu,
gaba d'aya hall d'in cike take mak'il har farfajiyar wojen,
yayinda 'yan jaridu suke jiran ace dasu kule suce cas,
daga cikin kuwa yan kallone da 'yan gulma,
a kujerun gaba kuwa nan Daddy, Jafar, Raihana, Faisal, Adda zulaihat dake zubda hawaye time to time,
sai Hajia Kaka,
can gefen Daddy kuwa Uncle Gumbo ne,
a d'aya sacinma harda Rafi'a
sai limamin masalkacin k'ofar gidansu Zahra da wasu dattijan na unguwa.
Aryan ne ya fara mik'ewa cikin shigarsu ta lauyoyi ya tako zuwa gaban teburin al'k'alin,
ya gabatar da sunanshi da wanda yakeyiwa aiki,
sai ya kuma k'arishe mgnar da cewa.
"Ya mai shariya ina son Zahra tazo gaban Court inda tambayoyin da zan mata."
Cikin nitsuwa AL'K'alin yace.
"Kotu na son ganin Zahra a gabanta."
shiru ya d'an biyo baya, yayinda aketa waige-waigen ta ina Zahra zata fito domin dama da yawa suna son ganinta,
shima mai shariyar ido ya zubawa mutanen ganin babu wanda ya tasone yasashi yin gyaran murya tare da cewa.
"Ko dai yauma Zahra bata zo bane kamar na wancan zaman?".
Daddy ne ya mik'e tare da cewa.
"Zahra bata da lfy bazata samu damar zuwaba."
cikin fad'a al'k'alin yace.
"Kazo gaban kotu kayi bayani ba daga canba."
cikin tarin takaici Daddy ya taso yazo ya shiga d'an wannan wurin da masu laifi ko bada shaida ke tsayuwa,
Aryan ne ya matsoshi tare da k'ara tsuke fuska yace.
"Me dalilin da yasa tunda aka fara sauraron k'ararnan Zahra bata zoba?."
rai a b'ace Daddy yace.
"Sabida bata da lfya ne."
cikin sauri Aryan yace.
"Meke damunta kuma yaushe ta fara ciwon?."
cikin jin haushi Daddy yace.
"Masassarace ke damunta kuma ta jima da ciwon."
murmushi Aryan yayi tare da cewa.
"Kunje asibitine ? in kunje ina shaidar likita?."
cikin inda-inda Daddy yace.
"A a bamuje ba."
Affan ne ya rumtse idonshi sabida shi yaso Daddy yabar Zahra tazo,
kuma yanzu Aryan zai iya juya rashin zuwar tata da wata manufa.
shi kuwa Aryan cikin isa yacewa Daddy.
"Jeka zauna."
rai a b'ace Daddy ya koma mazauninshi,
taku biyu zuwa uku Aryan yayi tare da gyara zamar rigarshi cikin iyawa da k'warewa ya fara koro jawabi kamar haka.
"Ya Mai girma maishariya ina rok'on wannan kotu mai adalci data duba wannan lamarin,
domin babu wani abu dake hana Zahra zuwa kawai shirine irin nasu,
domin yin wasa da hankalin court,
domin batun ciwon Zahra labarin k'anzon kuregene,
dan ko d'azu kafin in shigo Court saida naje gidansu Zahra,
inda na sameta lfyarta lau,
shi dama mahaifin Zahra yace babu ruwan hukumar kare hak'k'in d'an Adam akan abinda akayiwa yarshi,
yayin inkarin cewa Zahra yarsace,
kome Yusuf ya mata ba ruwan wani,
ya kuma k'ara da cewa zaiyi duk abinda yaga zai kare Yusuf."
sai ya kuma zaro wayarshi a al'jihu
cikin second 40 ya lalubo Recording da yayi lacin da ya gayawa Daddy shifa yana zargin Yusuf
to ashe ya nad'i duk mgnganu da masifar da Daddy yayi ta mishi.
bayan ya mik'awa al'k'alin wayar yaji duk abunda Yusuf yace Daddy ya fad'an a cikin wayar,
sai ya gyara zama tare da kallon dukkan mutanen da ke wajen cikin muryarsa me cike da kwarjini Al'k'alin yace.
"Ya zama dole Zahra tazo yau yau d'in nan kafin mudawo daga sallar azahar. Kotu za ta cigaba da sauraron sharia bayan an dawo daga sallah."
Gaban Daddy ne ya fadi da karfi ajiyar zuciya yayi tare da rumtse ido yana mai jin tsanar Aryan aransa fiye da tunani mai tunani. Mikewa akayi kowa jikinsa a sanyaye.

A can gida kuwa Kwance take ta kurawa cillin ido ba abinda take illa tunani da kuma jin k'unci me tsanani daya mamayeta a hankali hawaye ki zirya kan kumatunta lallai duniya tana da ban tsoro ita yau Zahra itace ke jin dacin duniya ? Kuka tafashe dashi Mara sauti.
Tana cikin kuka kamar an jehosa haka taga inuwarsa da sauri ta kallesa idonsa jajir ganin halin data ke cikine yasa ya sassauta muryarshi cikin sanyi Sulaiman yace. "Tashi mutafi."
Ya k'arishe mata mgnar a kagauce batayi musu ba ta mik'e tana goge hawayenta hijab kawai ta zira tabiyo bayansa suka tafi.

Tunda suka shigo Zahra ta rikice hade da razana kuka kawai take mai wuyar fassara. Koda suka shigo dai dai lokacin Al/kali ya shigo ba'a b'ata lokaci ba aka nemi Zahra ta fito a ji daga gareta kasa tashi tayi banda uban kuka ba abinda takeyi,
mik'ar da ita Mama tayi tana zubar da kwalla hade da mata magana k'asa-k'asa. Gyada kanta tayi tayo wajen da ake bukatar ta tsaya tana tafe numfashinta na kokarin tsayawa dalilin cemara birjik data gani ga idanuwan kowa na wajen na kanta juya ce ta kwasheta gab da isarta wajen lumshe idonta tayi tana karkada kanta tana ji aranta inama mutuwa zata zo ta dauketa ta huta.
Daga kanta tayi. Karaf suka hada ido da Idi mai chaji da tunda tazo wajen hankalinsa ya dad'a tashi... Luu juwar ta debeta kafin ta fadi tuni numfashin ta ya tsaya cak hakan yasa bata k'ara sanin meya faru ba ta sume a wurin. Arazana Mama tayo kanta hade da fashewa da matsanancin kuka.
Lokaci d'aya kotun ya kaurewa da hayaniya har sai da Alkali ya buga tabir ya umarci akai ta asibiti mafi kusa a duba lafiyar ta.
Juyowa yayi. yace.
"Uhm Aryan meye hujjar ka ta gaba?"

Juyowa Aryan yayi tare da cewa.
"Shaidata ta gaba dama Zahra ce dan ita zata fad'i waya mata fyad'e to ga abinda ya sameta,
sai kuma hujjojin dana bayar a zamanmu daya gabata."
Affan ne ya mik'e cikin d'an d'aga sauti yace.
"Objection! ya mai shariya sam wad'ancan hujjojin da ya bayar a wancan zaman ba gamsassubane,
domin duk k'irk'irarrune."
da sauri Aryan ya juyo tare da cewa.
"Objection!!! ya mai shariya mesaya Barrister Affan ke dakatar dani yayinda nake kawo hujjojina?."
cikin nitsuwa Maishariyan yace.
"Barrister Affan k'orafinka bai karb'uba,
sannan kabar abokin aikinka ya bada hujjojinsa."
kai Affan ya rusunar tare da cewa.
"Ngd ya mai shariya."
shima Aryan rusunar da kaid'in yayi tare dayin godiya sannan yace.
"Ranar 4 ga watan d'aya shekara ta 2015 da misalin k'arfe 4:27 Pm
lokacin da ya kasance anzo d'aukar auren Raihana,
gidan ya cika da motoci babu masaka tsinke,
ina part na
nida abokaina da yan uwana,
sai naji haniniyar Badsha da gurram dawakan Yusuf ne,
jinsu ya tabbatar min tabbas sunga Yusuf domin muddin sukaga Yusuf to sai sunyi wannan haniniyar,
toh inajin wannan haniniyar na tabbatar Yusuf ya dawo kenan,
domin ya fita bada jimawaba naji haniniyarsu,
sannan koda muka shiga d'akin da abin ya faru,
naga zoben Yusuf a k'asa,
sannan takun k'afafun da suke tsakiyar bathroom d'in wanda shatinsu ya fito da jini,
irin zanen k'afafun Yusuf ne."
sai ya kuma yin shiru tare da juyawa ya kalli mutanen yace.
"in dai Yusuf ya yarda da kanshi meyasa ya zama kurman gangan na tsawon wata d'aya guda?
kuma in ba Daddy ya yasan cewa in Zahra tazo nan zata ce Yusuf ne ya mata fyad'enba tunda ta ganshi ido da ido meyasa Daddy ya nata zuwa?
da wad'annan bayanan nake rok'on Kotun nan mai adalci data hukunta Yusuf bisa laifinshi kar a duba matsayi ko sunanshi."
shiru kotun tayi,
sai sautin mgnar yan kallo
yayinda shesshek'ar kukan Adda Zulaihat dake tashi k'asa-k'asa,
yayinda Raihana ke tayata sabida tana ganin yadda Aryan ke kimtsa sharri yana d'aurawa Yusuf,
Rafi'a ma hawaye takeyi sabida komai a gaban idonsu ya faru har fitowar Idris daga d'akin Yusuf
Tatti kuwa sai tsinewa Idris dake genta takeyi,
Hajia Kaka kuwa sai hawaye
shiru kakeji sai yar shesshek'arsu da sautin masu mgna k'asa-k'asa.
sai da al'kalin ya bawa Affan daman yin mgna,
sannan ya mik'e ya tako zuwa gaban kotun,
cikin iya sarrafa

Please Login or Register in order to submit comment