Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yake tafiya a d'an dai-dai misali tunda shi Daddy cikin salama yake tafiya yayinda kuma ya kira Aryan da Sulaiman ya musu fad'a su rage gudun amman ina sai sunyi kamar sun rage sai su kuma sake fecewa a 360.
suma fadawan kazalika gudu suke ba sassauci ga wasu irin dogayen bulalinsu da suka firfitar ta windows d'in motoci alaman kana yi musu laifi kad'an zaka sha zabga.
sannan ga dawakai da suke masifar binsu da gudu kamar wad'an da suke fagen tsere babu abinda kakeji sai fiw-fiw alamar gilmawar motocin sai kuma kaji kusar-kusar k'aran sautin kofoton dawakan.

Duk mazaunin cikin Adamawa yasan yadda bakin babbar kasuwar Adamawa take wani irin azabebben cika da cunkoso da zaran yamma tayi,
to kuwa a dai-dai irin wannan lokacin su Yusuf da tawagarsa suka ratso wurin dan sun fito daga babban titin daya fito cikin Yola inda kai tsaye zasu wuce bayan P.Z. gidansu Aryan dan can d'in dai Yusuf zai koma kafin a tuntubi Abba da batun dawowar tashi gidansu,
gudun da sukeyi da tarin dawakan yasa
dole gaba d'aya ababen hawa da jama'a suka koma gefen titi,
yayinda wasu suka fidda wayoyinsu suna viewing wasu kuma na daukar hoto,
a dai-dai lokacin ne Zahra da Salima suka fito cikin kasuwar da nufin su hau keke napep ta kaisu mubi round about inda zasu samu taxi d'in zuwa Girei,
dole suma suka tsaya cikin dandazon mutanen,
cikin mmki Salima tace.
"Yau kuma bikin me akeyi a masarauta."
baki Zahra ta tab'e tare da cewa.
"Ina zan sani,
in banda izza da isa da izaya ya za'ayi da yamman nan su biyo bakin kasuwa."
cikin dariya Salima tace.
"Karki wani d'auki zafi uwar tsiwa to in basubi nanba ina kikeso subi?."
cikin fad'a tace.
"GA Bank rouad nan me zai hana subi nan?."
cikin bin tsala-tsalan motocin da kallo Salima tace.
"Toh Hajiya Zahra karfa ki manta sune da garin."
tsaki taja tare da jawo hannun Salima suka fara kutsawa gefen jama'a,
sunzo dai-dai wasu taron matasa wanda a k'alla zasu kai 17 harda manya kad'an a cikinsu,
wani daga cikinsu ne yake cewa.
"A a ba tafiya zasuyiba kunsan Yusuf Muhammad Usman Girei dan wasan polo da yaciyo gasar West Africa shine ya dawo d'azu to inaga yanzu za'a rakashine zuwa gida."
cikin sauri wani daga cikinsu yace.
"OK hakafa lallai naga jikin motoci 3 nan duk a k'asan plet number ansa Braden Adamawa 1 har zuwa 3 d'in."
wani daga cikinsu ne ya kuma cewa.
"Tabbas hakane nifa har Airport d'inma naje d'azu da rana,
kaga sai yanzu na lura da uniform d'insu na Jahan team dake jikin wad'an nan na kan dawakan,
da irinshi Braden ya dawo a jikinshi."
Wani tsoho ne daga cikinsu wanda ya sufa tukub ya jujjuya kai cikin tausayawa ya fita tare da fara tafiya yayinda wani matashi ke bin bayanshi,
da sauri su Zahra suka bishi a baya dan ganin yana samu mutane na kauce mishi yana samun hanya to suma sai suke bin bayanshi,
suna cikin tafiya sun fara fita cikin jama'ar sunzo dai-dai mashigar San Husaini,
sukaji tsohon nan yana mgna cikin wata iriyar murya.
"Wannan yaro Yusufa baki ya mishi yawa,. *Hawu* na bibiyar rayuwarsa gashi yaro matashi mai tsarkakekkiyar zuciya amman yanada mak'iya a kusa dashi,
sannan ga sharrin kambun baka dake bibiyarsa."
cikin yin k'asa da murya matashin yayi mgn wacce su Zahra basuji me yaceba,
sai gani da sukayi tsohon nan ya juyo ya kallesu,
wani irin yarrr Zahra taji dai-dai lokacin da suka had'a ido da tsohon lokaci d'aya jikinta ya fara rawa,
da sauri suka juya suka fara tafiya da sauri,
sunayin gaba kad'an wani mai napep ya tsaya gabansu babu b'ata lokaci suka shiga,
kai tsaye inda zasu shiga taxi d'in girei ya kaisu,
suna zuwa kuma suka samu saura mutun ku,
shiga sukayi sannan suka biya kud'in d'ayan da ba'a samuba suka tafi.


Su Yusuf kuwa kai tsaye anguwar bayan P. Z. suka shiga inda akayiwa Yusuf rakiya har gida,
a baking gate motar fadawar da matasan dake kan dawakan duka suka juya suka tafi,
yayinda sukuwa su Aryan suka kutsa kai cikin gidan ganin mai
gadi ya wank'ale musu gate d'in,
a jere a jere suka shiga cikin gidan Yusuf ne a baya dan haka shine k'arshen shigowa.

A cikin gida kuwa su Adda Zulaihat Raihana, Amira, Mami, Nana, Zeenat, Hajiya Kaka da Rafi'a diyar kawun su Aryan kenan da itama taketa son ganin Yusuf dan yadda takeji sunata hirarshi wunin yau duka,
duk a tare suka fito farfajiyar gidan dan jin hayaniyar jama'u alamun sun iso Sharifa kuwa gefen Jafar da Sadik da Ibrahim taje ta tsaya wanda su dama suna harabar gidan a cikin yan bukkokin da akayi dan zaman.
gaba d'aya ido suka zubawa moticin,
suna jiran su gama yin parking a cikin wurin da aka tanada dan hakan,
suna gama yin parking suka fito a tare.
wani irin tsalle Zulaihat da Raihana da Amira sukayi,
cikin tsananin farin ciki suka nufi inda Yusuf yake tsaye yanata wani irin murmushi,
ganin Amira da d'an k'wajejen cikinta ya sashi,
sake murmushi tare da matsawa inda suke zuwa suna isa Zulaihat ta ruggumeshi ita kuwa Amira ta fad'a jikin Zulaihat d'in yayinda Raihana kuwa ta konto jikin Amira,
wani irin farin cikine mara misaltuwa a zuciyar Yusuf,
Adda Zulaihat kuwa kawai sai ta fashe da kuka tare da kuma marin k'eyar Yusuf d'in sai ta kuma ruggumeshi tana kuka.
shi kuwa Yusuf d'an turesu yayi a jikinshi sannan ya kama kunnenshi alamar neman yafiya,
cikin tonk'oshe wuyanshi kan kafad'unshi yace.
"Ana aspect ya Habibati."
kunnenshi ta d'an ja tare da d'an dungure goshinshi.
ganin yadda tayi ne sai ya kuma marairaice fuska yace.
"Irin tarbar da yakamata kiyi min kenan Adda na."
sai ya kuma kalli Amira tare da tab'e baki yace.
"Mai ciki."
cikin had'e fuska Amira ta kai mishi duka kaucewa yayi tare da jawo hannun Raihana yana dariya tare da cewa.
"K'anwata sai k'amshi amarci fa kikeyi."
tafin hannunta tasa ta rufe fuskarta wai ita kunya,
Adda Zulaihat kuwa k'ara rik'o hannunshi dake cikin nata tayi ta matse da k'arfi tare da cewa.
"Zaka sake tafiya ka barmu?".
tsalle ya d'anyi tare da yin yar k'ara.
"Wayyo Mamana ina kike kinga Addana tana cin zalina ko."
gaba d'aya wurin dariya sukayi dan ganin yadda ya kele fuska,
dengin su Aryan da suka fara taruwa dan bikin Raihana da za'a fara gobe sai murmushi sukeyi suna binsu da kallon sha'awa.
shi kuwa Yusuf hannunshi yasa a kafad'un zulaihat suna tafiya a jere,
murmushi Zulaihat keyi yayinda hawayen farin ciki ke bin fuskarta,
tafiya sukeyi a jere kamar irin abokai d'innan,
Mami Nana da Zeenat ne suka iso gabansu tare da rusunawa suka gaidashi,
amsawa yayi cikin zaro ido ya kalli Sulaiman dake gefenshi yace.
"Kai Sukaiman su Mamine suka zama yan mata haka?."
kai Sulaiman ya gyad'a mishi akamar eh.
shi kuwa Yusuf su Jafar ya ruggume tare da cewa.
"Miss you so much brothers."
Aryan kuwa trollings d'in cikin motocin yake fitarwa tare da bawa Fa'iq yana kaisu part d'in Yusuf.
gaba d'aya sun kacame sunata farin cikin ganin juna,
da sauri suka juyo baki d'ayansu kan Sharifa data daddage ta saki ihu da k'arfinta tare da bubbuga k'afa tana cewa.
"Mommy kin kalli uncle Yusuf ko bai kulani ba."
da sauri Yusuf ya sakesu baki d'ayansu sannan ya duk'o kad'an tare da d'agota ya d'aura a kan wuyanshi yana cewa.
"Oh my sweet baby am so sorry dear i love you,
irin sosai d'innan my Sharifiyar Uncle Yusuf."
dariya ta k'elk'ele dashi tare da yiwa Fa'iq da yazo wuce da akwati na hudu a hannunshi gwala tana mai cewa.
"Yehhh Hamma Fa'iq ganni Uncle Yusuf yana min doki-doki."
dariya akayi baki d'aya,
Fa'iq kuwa zumbura baki yayi,
da sauri Yusuf ya shafo konshi tare da cewa.
"Sorry d'an farina kaifa kasan kai muka fara so."
dariya Fa'iq yayi cikin jin dadi.
dai-dai lokacin kuma Hajiya Kaka ta kamo hannun Yusuf tare da cewa su Raihana.
"Tafi daga nan duk baku iya tarbar bak'oba kun wani tsareshi da shirmenku kun barmin miji da k'ishi da yunwa ko ruwa baku bashi ba."
dariya akayi baki d'aya yayinda ita kuwa taja hannunshi sukayi babban parlour gidan,
shi kuwa binta yakeyi tare da cewa.
"Gskyarki dai uwar gidan Aryan."
cikin wasa irin ta kaka da jika tace.
"Uwar gidan Yusufa d'in dai."
kai ya juya tare da cewa.
"Gskya akai kasuwa ni sai da sabuwar jini."
ido ya d'an rufe wai yaji kunyarsu Goggo Maimuna da Aunty Amarya da Aunty Madina daya samu a parlour.

Kai Yusuf dai yaga soyayyar yan uwanshi a ranar haka sukayi ta hira,
Daddy kuwa tuni ya tafi tare da Aunty Amarya da dama suna fitowa girei Ummi tace ita kam ya sauk'eta a gidansu bazataje ba.

Haka sukayi ta hirar yaushe gamo,
sai gabanin margin Sulaiman ya kwashi Goggo Maimuna Aunty Madina da Amira ya maidasu gidajensu sannan ya dawo ya dauki su Mami ya biya ya d'auki Ummi suka koma,
Aryan kuwa shiya maida Jafar, Sadik, Ibrahim da Zeenat.
Adda Zulaihat kuwa sai bayan sallan isha'i Abubakar yazo d'aukanta da yaransu.





*by*
*GARKUWAR FULANI*

*HUKUNCIN ALLAH*

*Page 2⃣7⃣*

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*


🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇



Assalamu alaikum masoyana masu bibiyar wannan littafi nawa mai Suna Hukuncin Allah,
In nace masoya nafa ina nufin wadanda suka biya kud'insu na sasu a group na,
bada ku nakeba b'ara masu fiddashi ku bawa wasu su watsashi ba,
mosoyana ina baku hak'uri duba ga yanayin azabebben sanyi da muke ciki,
yasa typing fa ya fara gagarata yaseen jinin yatsuna daskarewa yakeyi,
inyi-inyi zanyi typing sai abin ya gagara dan haka ina baku hak'uri da kuma rok'on kuyi min uzuri,
in mun gama part one zanje hutun mak'o d'aya,
Sannan in mun fara fostin part two ba mmki watara ku jini dib,
to in kun jini dib kuyi min uzuri duk da nima na matsu inga na gama rubutashi,
shiyasa nake qoqarin ganin nayi posting kullum,
Wlh yanzu haka ma da kyar nayi wannan dan bayanin,
shiyasa mafi akasarin pages d'in ba editing,
yau kusan sati kena da fara typing d'in part two d'in amman ban kai ga ko 5 page ba.



Yusuf na ruggume da Sharifa Aryan kuwa yana rik'e da hannun Fa'iq yayinda ita kuwa Adda Zulaihat take tsakiyarsu,
Raihana kuwa na gabansu rik'e da hand bag d'in Adda Zulaihat.

A gaban Abubakar dake jingine da motarshi suka tsaya,
cikin sauri Yusuf ya kontar da Sharifa cikin motar gefen da Raihana ta ajiye jakar,
shi kuwa Aryan hannu ya mik'awa Abubakar suka gaisa cikin mutntunta juna,
Yusuf kuwa shima hannu ya mik'awa Abubakar d'in cikin yin murmushi tare da yi mishi irin yar ruggumar gefe d'ayan nan,
hannu Abubakar yasa tare da dan bubbuga kafad'ar Yusuf sannan yace.
"Masha Allah autan Mama fa ya zama balarabe,
Yusuf ka ganka kuwa yadda kake masha Allah."
shiko Yusuf murmushi ya d'anyi tare da shafa k'eyanshi,
sannan ya cusa hannunshi cikin sumar kanshi yace.
"Kai dai Ya Abubakar dama can haka nake."
murmushi Zulaihat tayi cikin kallon k'anin nata tace.
"Toh mu dai zamu tafi karka manta mgnarda mukayi."
Kai ya gyad'a alamar toh,
ita kuwa sai ta kuma kalli Aryan tace.
"Zaku shigo d'inko goben?".
kai ya d'an juya tare cewa.
"Anya kuwa."
Raihana ce ta katsesu da sauri tace.
"Adda Zulaihat kin manta cewa gobema zakizo ne?."
sai ta kuma juyawa gun Abubakar cikin d'an kunya-kunya tace.
"Yaya dan Allah kabar Adda tazo kagafa daga gobe za'a fara bikin,
kuma ba wani dadewa za'ayiba ana shagalin ba gobe Jumma'a za'ayi walima jibi asabar kuma ayi d'aurin aure kuma kasan dole zata zo akai amarya da ita,
shike nan sai jibi lahad'i da yamma ayi fansan ido,
bayan sallan isha'i ayi dinner kuma kaga su Zahra ma duk daga gobe zasuzo sai an gama biki zasu koma ya kamata ace akwai babba cikinmu."
Ido ta rufe tare da juyawa da gudu tayi cikin gida
dan ganin kallon da sukemata na alamun,
"Lallai amaren yanzu ba kunya."
su kuwa dariya sukayi baki d'ayansu,
shi kuwa Yusuf sai tab'e baki yayi yana mmakin yaran wai sun girma har suna rawar kan za'a aura dasu.

haka dai sukayi sallama Abubakar yaja motar suka tafi.

Aryan da Yusuf sukuwa Parlour Yusuf suka koma inda sukayita hirar yaushe gamo,
kusan nan suka kwana sai k'arfe uku Aryan ya mik'e tare da yin hamma sannan ya juya zai fita yana cewa.
"Yau dai munyi kwanan zaune,
bari inje inyi wanka tunda asuba ta k'arato."
hararan sa Yusuf yayi tare da tsuke fuska yace.
"Wai me dalilinka na raba mana wurin kwana,
tunda dai naga dani da kai duk d'aya muke kai tuzuru ni saurayi babu mai mata a cikinmu."
cikin yin mik'a Aryan ya d'an tsaya tare da juyowa kad'an yace.
"Toh yaseen ni dai na kusa aure shiyasa,
gwara ka koma daga gefe."
tsaki Yusuf ya d'an ja tare da cewa.
"Banza kawai fitinenne ai sai ka hak'ura sai kayi auren kafin muraba makwancin."
shiko Aryan dariya yayi tare da juyawa ya fita yana cewa.
"Ikon Allah yanzu kai ne har zaka cewa wani jarabebbe."
shima Yusuf dariya yayi tare da kallon kansa yana murmushi shafa k'ugunshi yayi tare da lumshe ido dan tunowa fa wai allura aka mishi wacce zatayi one week tana mishi aiki amman gashi yau kwananta biyar kacal kuma duk ya fara jin wani irin mahaukacin feelings
jikinshi ya d'an matse tare da mik'ewa ya shiga bedroom yana shiga kai tsaye bathroom ya shige ruwan d'umi ya watsa sannan ya fito yayi shigar larabawa sannan ya shimfid'a sallaya tare da fara nafilfili,
har saida akayi kiran forko sannan ya zauna ya fara karatun k'ura'an,
saida yaji anyi assalatu sannan ya mik'e tare da kawo raka'a biyu,
raka'ainil fajir,
sannan ya fito jin an fara kiraye-kirayen salla,
a bakin gate suka had'u da Aryan sannan suka wuce masallaci,
bayan an idar da salla anan suka d'an zauna sukayi karatu saida gari yayi haske suka koma gida,
a babban parlour suka zauna dukansu inda Raihana ta had'a musu tea and cake ta basu,
nan dai suka d'an tab'a sannan Yusuf ya mik'e tare da cewa.
"Kaka bari inje in d'anyi bacci."
shima Aryan mik'ewa yayi tare da cewa.
"Nima bari inje in rumtsa dan case d'in da nike dashi sai k'arfe biyu ne zamu shiga."
kai Kaka ta jinjina musu tare da cewa.
"Ku dai fito anjima kad'an kuyi break in yaso daga baya kwa koma baccin."
to sukace mata kawai sannan kowa yayi side d'inshi.

Yusuf kam sai juyi yakeyi a kan gado yana jan tsaki dan wannan abu ya fara sashi yana jin haushin kanshi da kanshi.


A Girei kuwa ana idar da salla a masallacin k'ofar gidansu Mama ta fito daga side d'in Abba hannunta rik'e da carbi,
kai tsaye d'akinta ta nufa inda Zahra ke kwance ita d'aya,
ido Mama ta tsurawa Zahran lokacin da ta shigo dan jin wasu surutai da takeyi can k'asan mak'oshinta yayinda takeyi mutsu-mutsu,
ita kuwa Zahra tayi nisa cikin duniyar da Dream Guy d'inta ya kaita,
murmushi tayi tare da matsoshi lokacin da juya mata baya idonshi na zubda hawaye dan ta hanashi *Cabb'ullen* shi,
yayinda a zahiri kuma Mama na ganin murmushin da Zahran takeyi,
ita kuwa Zahra cikin duniya mafarkin nata,
ta bishi a hanlali ta bayanshi tazo ta ruggumeshi tare da manna mishi brest nata a kafad'unshi,
sannan tasa d'an yatsarta manuniya tana shafa soft lip's d'inshi
ido ta lumshe dan jin sanyinsu da taushinsu na ratsa mata d'an yatsa har zuwa cikin mad'igan kanta,
a hankali ya bud'e lips d'inshi tare da lalubo tattausar yatsar tata ya saka cikin bakinshi ya fara mishi wani irin tsotsa,
yayinda yasa hannunshi d'aya kuma ya jawota zuwa kan cinyarshi,
wani irin birkicewa yayi jikinshi sai tsuma yakeyi cikin wani irin salo ya kife tafin hannunshi kan brest d'inta yana wani irin sarrafasu,
sai numfashi take fesarwa tana lumshe ido,
sun fara nisa cikin duniyar da sukeso shiga,
kamar a zahiri taji ya dasa mata cizo mai zafi wanda yasa ta saki k'ara tare da juyowa da sauri kallonshi takeyi cikin mutuwar jiki ganin shima kukan yakeyi kamar ransa zai fita ganin yana cikin wani irin hali sai itama ta fara kukan.

Yayinda a zahirinma kukan takeyi,
cikin mmki Mama ta matsota tare da matsota tana d'an dukan kafad'unta.
"Zahra.! Zahra.!!!."
firgigit ta mik'e zaune yayinda take zubda hawaye,
cikin magagin bacci ta matso jikin Mama tare da cewa.
"Mama anyi salla ko?."
kai ta gyad'a tare da cewa.
"Mafarki kikeyi ne?."
"Eh".
ta bata amsa a tak'aice lokacin da take shigewa bathroom,
tana shiga shower ta sakarwa kanta,
tanayi tana rumtse ido da k'arfi duk sanda ta tuno abinda ya faru a mafarkinta a haka ta fito tazo tayi salla,
ita kuwa Mama sai binta takeyi da ido tana son ta ajiyeta ta tambayeta irin mafarkan da ta lura tana yawan yi a kwanannan,
sai kuma tace bari ta bari sai yau in sunzo konciya zata tambayeta,
kitchen suka shiga tare,
cikin mamaki Zahra ta juyo tare da cewa.
"Mama me zakiyi?."

"Zan tayaki aikin ne kin san ina son mu shiryawa Hammanku breakfast nashi daga nan a kai mishi."
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Kije ki kwanta yanzu zan k'arisa aikin,
ai kinsan tun jiya na gama wasu aiyu kan."
cikin jin dad'i Maman tace Toh tare da juyawa ta fita tana sakawa Zahra al'barka.

Ita kuwa Zahra a kitchen d'in tsaki taja tare da tsuke fuska tana mai fara fere dankali turawa,
tsaki ta kuma ja kamar tana gabanshi tace.
"Ka dai ci al'barkacin Mamata badon itaba yaseen da gishiri zan saka maka cikin kunun a madadin sugar,
in cika yaji a ferfesun ta yadda in ya k'wareka sai ka shid'e,
sannan in soya dankalin sai ya k'one kajinma da nayi maka pepper chicken in zumd'uda attaruhu da gishiri."
hararar gefenta tayi kamar yana tsaye a wurin tace.
"Toh amman kayi sa'a ban iya almobazaranciba dan nasan ba kyau kuma dan in faranta ran Mamata kawai zan ragar maka."
baki ta d'an tura tare da murgud'ashi ta kuma cewa.
"Yauwa ai gwara ka sani ba tsoronka nake jiba ehe!."

Haka dai tayi ta k'unk'uni da masifa tana aiki,
sosai ta shirya mishi breakfast na gani na fad'a,
kuma dama Alhamdulillah kunsan Mama ta hori Zahra da iya girki,
lokaci d'aya gida ya cika da k'amshin soye-soye da defe-defe. da kuma tafashe-tafashe,
Kunun gyad'a da d'anyar shinkafa da kwakwa sai dabino da kanamfari da citta ta dama kunun damu mai kyau,
*gari sakadi kenan* inji fulanin Yola da fad'a sai zumar da ta saka a madadin sugar sai tea mai ganyen na'a-na'a,
sannan pepper chicken dayasha hadi sai couscous da miyar daddageggiyar hanta,
sannan soyayyan dankali da tayi mishi sutura da fefeyayen soyayyan k'wai sai k'osai wanda mahad'in wancan kunun gyad'an nanne mai zuma,
sai zazzafan ferfesub wanda zan mishi inkiya da k'ugiyar yunwa.
bayan ta gama komai ta kimtsashi a manyan kuloli masu tsananin kyau da tsada
sannan ta shiryawa kowa nashi ta kai nasu
Iya shatu da mijinta baba mai gadi,
sannan tazo ta kai na Hajja Inna,
sauri-sauri ta shigo parlour Mama ganin Ya Sulaiman zaune yayinda yake rik'e da k'undun kaza cikin pepper chicken da tayiwa su Yusuf d'in Jafar kuwa yana jidan kulolin yana kaiwa cikin sabuwar motar ya Sulaiman,
kallon Sulaiman tayi tare da kad'a kai ganin yadda yake yagar tsokokin yana taunawa tare da lumshi ido dan yadda yakejin d'and'anon na ratsa mishi jijiyoyin harshensa,
Zeenat ce dake gefenshi rik'e da mayafinta alamun tare zasu tafi,
dariya sukayi mata ganin yadda take had'iyar yawu,
dan Zeenat itama mayyar namace layin su Hamma Yusuf da Sulaiman take sam su basa gajiya da nama a rayuwarsu,
Zahra kuwa sai dai in yunwace taci k'arfinta ta kuma rasa wani abin ci to a nanne take cin nama bisa larura.
Jafar ne yace.
"Ya Sulaiman mu tafi kagafa har 9:38 Am yayi karmu makara mu samu har sun karya."
mik'ewa yayi tare da bawa Zeenat sauran nawan hannunshi,
amsa tayi tare da fara jaga shi kuwa goge bakinshi yayi tare da cewa.
"Toh Mama sai mun dawo."
da sauri Mama tace.
"Yauwa ga zumar nan ka kaimishi kace ya yawaita lasa,
sannan kace gobe zanje gidan Innata,
mu had'u dashi a can."
"Toh." yace tare da
amsar tand'un zumar sannan suka fita.

Ita kuwa Zahra cikin lumshe ido alamar gajiya tace.
"Mama bari inje gidan Aunty Fadwa zan amsowa Aunty Raiha sauran had'inta, sai kuma turarukanta na humrarnan."
cikin gyara konciyarta a kan 3 str tace.
"Toh kiyi sauri ki dawo,
kinsan kece zakije kiyiwa Raihanan lalle,
nama rasa meya hanaki zuwa jiya cikin yan uwanki kinga da kunyi lalle in yaso yau kuyi kitso kafin lokacin walimar."
dariya tayi cikin kawo uzuri dan kar Mama ta gane tak'i zuwane jiyan dan Hamma Yusuf d'in,
"Hmmmm Mama kin manta jiyan naje kasuwa,
kuma Ummi ma ni ta barwa kitchen."
Kai Mama ta jinjina alamar haka ne na tuno.

Ita kuwa gidan Aunty Fadwa taje ta karb'o sauran tsimin Aunty Raiha wanda dama ta karbi' tandu d'aya jiya da dare,
amsa da turarukan wutan ta dawo gida.

Tana shiga parlour Auntynta taje inda ta samu Mami da Nana suna karyawa,
gefen Aunty Amarya ta zauna tare da cewa.
"Auntyna me kika dafa mana ne?."
juyowa tayi ta kalleta tare da cewa.
" Mami ce tayi mana d'anwake."
da sauri tace.
"D'anwake kuma,
toh me aka dafawa Daddy?."
gyara zama Aunty Amaryan tayi tare da cewa.
"Daddy da Abba breakfast d'in da kika had'awa Hamman ku sukaci shiyasa akayi d'anwake kawai."
kai ta jingina jikin kujera tare da cewa.
"Mami kuyi saurifa mu tafi kunga tun d'azu Aunty Raiha keta kirana kar aje wurin walima k'afar amarya ba lalle."
mik'ewa sukayi tare da cewa.
"Gsky kam."
ita kuwa Zahra gyara zama tayi tare da cewa.
"Ke kuma Nana d'an sakomin d'anwaken inci kafun ku shirya na gama."
tab'e baki Nana tayi tare da cewa.
"Eh dole ai in sako miki tunda ke k'anwar uwa tace."
dariya tayi cikin izza tace.
"Yoh wal bani wal baka wal hanani wal k'ememe,
in kukamin abinda nakeso, in muje in muku makeup in kuwa kuka min gardama yaseen kun sanni nafiku iya gardama."
dariya sosai Aunty Amarya tayi tare da cewa.
"Gskyarki Tinana."
Mami kuwa amsar pilet d'in tayi ta zubo mata d'anwake ta kawo mata sannan sukaje suka fara shiri,
ita kuwa saida ta ci sannan taje tayi wonka,
amman duk da sun rigata farawa ta rigasu gamawa sabida ita yadda take da tsiwa hakama aikinta duk a tsiwace take yinshi ta gama.

Bayan sun gama kimtsawa komai da zasu tafi da sune dan in sunje sai an gama bikin zasu dawo,
sukuwa da sauri sukaje suka rok'i Ya Sadik yazo ya kaisu.


Aryan kuwa yana cikin bacci yaji kiran Sulaiman ya shiga wayarsa,
hannu yasa tare da amsawa jin Sulaiman yace mishi,
gasu nanfa a parlour shi ya sashi fitowa da sauri tare da gyara wuyan jallabiyarshi
hannu ya bawa Sulaiman suka gaisa cikin muryar bacci yace.
"Muje parlour Yusuf zamufi sakewa,
nan mutane na yawan shigowa."
binshi a baya sukayi tare da cewa.
"OK."
har sunje bakin k'ofar shiga parlour Yusuf d'in Sulaiman ya d'an juyo ya kalli Jafar cikin bada umarni ya cilla mishi car key yace.
"Kai Jafar koma ka debo kulolin mana."
café key d'in yayi tare da cewa.
"Toh."
sannan ya juya.

Su kuwa cikin sa'a suka samu bai rufe k'ofar da key ba,
shiga sukayi a tare suka sauk'e wani irin ajiyan zuciya dan wani irin sihirtacccen k'amshi da sanyi mai ratsa jiki da zuciya,
lumshe ido Sulaiman yayi tare da zama kan luntsuma-luntsuma sofas dake cike a parlour yayinda yatsun k'afafunsu suke nitsewa cikin tattausan carpet dake malale a tsakiyar kujerun labulayen duk a sassake.
shi kuwa Aryan kai tsaye bakin k'ofar bedroom d'in yaje,
cikin sanyin murya yace.
"Yusuf..! Yusuf.!!!."
yayinda kuma yaketa bubbuga k'ofar da d'an k'arfi,
can cikin baccin daya samu ya saceshi da kyar dududu baifi 25 minutes da fara baccinba,
gashi kwana sukayi basuyi baccinba,
wani irin dogon tsaki yaja lakacin da yaji Aryan na k'ara sautin buga k'ofar,
juyi yayi tare da mik'ewa zaune cikin muryar bacci da fad'a yace.
"Mitseeew wai kai kam wani irin mayene mai d'an banzan nacin tsiya."
murmushi Aryan yayi tare da cewa.
"Banza masifaffe,
toh bani na kar zomonba Mama ce ta turoma sak'o."
tsuke fuska ya kumayi tare da mik'ewa tsaye gyara zaman boxes d'inshi yayi sannan ya

Please Login or Register in order to submit comment