Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

had'a hannunsa biyu sukayi kara tare da cije lips d'inshi duka biyu.
Cikin kunar zuciya da tsananin bak'in ciki Mama ta mike murya na rawa yayinda ida nunta ke zubda zazzafan hawaye cikin rauni tace.
Dan Allah! ka jik'aina ka tausa ya min ka tuna fa shi kenan k'waya d'aya tal Allah ya bamu dagashi sai Zulaihat da take d'akinta, ka tuna Yusuf d'anmu ne, Yaya kayi hak'uri Yusuf ya dawo garemu, ina Yusuf zai shiga a shekarun shin nan, wa zai zame mai uba bayan kai ka gujeshi, na tuba ka gafarceni, duk hukuncin da zakayiwa Yusuf kayi min shi, dan Allah Yaya ka jik'an tsakanin uwa da d'anta Allah bai rabani da Yusuf ba dan Allah Yaya karka rabu"!.
sai kuma ta zame ta durk'usa bisa guiwowinta tare da rik'o k'afafunshi ta saki kuka mai cike da rauni,
shiru yayi sai jikinsa dake b'ari ranshi na suya akan kuka da rok'on da take mishi, kuma bazai iya mata abinda takeso ba har sai in Hajja inna ce ta tursasashi, zame k'afafunshi yayi tare da juyawa cikin sanyi jiki,
mik'ewa tayi ta rik'o hannunshi cikin kuka da raunin tace.
"Nace maka nagaji Ya Muhammad na gaji da irin wannan rayuwar da nake ciki meyasa duk hak'urin da nakeyi a kan abinda kake min amman ka korar min yaro sannan kace zaka yanke sauran alakar da zata hadani dashi."
juyowa tayi gabanshi tare da had'e nannunta duka biyu cikin neman alfarma ta nuna saitin k'ahon zuciyarta tace.
" Ya Muhammad kasan ciwo da radadin da yake cikin raba uwa da d'anta kuwa!!?".
zabura Abba yayi had'i da daga hannu zai zabga mata mari meya tuna kuma oho saiya fasa,
ido ya zuba mata yana mamakin iya tsawon zamansu yakara kusan 35 Mama bata tab'a tsareshi gaba da gaba ta ambaci sunanshi sai yau.
Cikin kuka da sheshshek'a Mama tace.
"ka koreni ni in bar gidan sai ka dawo min da Yusuf na dan Allah Ya Muhammad".
sai kuma ta fad'a kan gado ta saki kuka mai tab'a zuciyar mai sauraro.
Abba kuwa cikin zafin rai ya juya gidan gaba daya ya fice saboda yayi masa zafi ga tausayin Mama ga tausayin k'anennasa ga ciwo da zafin abin Yusuf yawa Hajja Innansu.



Kwance Mama take akan gado tana kuka shigowar su Gwaggo Zarah mahaifiyar Mama kenan kuma k'anwa ga Mahaifinsu Abba,
wacce itace takwarar Zahra k'arama, amin Daddy yawa k'anwar mahaifinshi ne tokwara, sai su Goggo Aisha da Anty Madina da Goggo Maimuna dake biye da ita a baya,
zama tayi tana fuskantar d'iyar tata cikin tausayawa sai kuma tayi murmushi dan sam bata son shiga maganar dan kar ace ai da ita Yusuf ya daka da su zasu d'au mataki ganin mahaifiyar tata da k'annen mijinta kuma abokan wasanta yayan kawunta Yayan mahaifiyarta kenan ganisu ne ya sakata tashi a gadon had'i da k'ak'alo murmushi tana goge hawayen da yake zubo mata a take wani irin tausayin su ya kamata zama sukayi bayan sun gaisa suke jajanta mata abinda ya faru da kontar mata hankali Gwaggo Aisha tace.
"Yaya Aliyu yana jiranki a parlour k'asayace akwai maganar da zaiyi dake".
tashi tayi ta saka hijab d'inta ta fita,
cikin girgiza kai tace.
"Allah Maman Yusuf akwai hakuri innice tab! wallahi bazan yarda ba".
harara Goggo Fatima ta wullah mata tace.
"Naga randa zaki girma Aisha, ai fushi baya kawo sulhu sai hak'urin, ke da Maman Yusuf irinkice ai da auren nasuma ya mace."
baki ta tunzura gaba gami da cewa.
" wani hak'urin dai yana yawa." ita kam Goggonsu sai dariya takeyi.



Bayan sun gaisa Daddy ya k'ara mata jajen abinda ya faru anan yake sanar mata sak'on Yusuf,
wani irin farin cikine ya mamaye zuciyarta a take ta fara sauke ajiyar zuciya cikin yin hamdala tace.
"Ammm ko zaka kiramin shi a wayarka, in Yayanka bai hanaba?".
wayar shi ya ciro hadi da cewa.
"Karki damu komai zai wuce."
kira number d'in Yusuf yayi bugu biyu ya d'auka ,
dama shima yana zaune ne duk ya damu yanata gwada kiran number d'in Mama taki shiga jin muryar Mama saida yayi ajiyar zuciya bayan sun gaisa nan yake tambayarta meya samu wayarta fada mishi tayi lokacin data d'aga ne ta zame a hannunta ta fad'i garin rawar jiki shine ta fashe, dariya Yusuf yayi yace.
"Kai Mama kamar tsohuwa."
murmushi tayi tace.
"Toh ai tsohuwarce ai".
murmushi yayi sai kuma yayi k'asa da murya cikin sanyi yace.
"Mamah ki goge hawayen."
hannun tasa ta shafa fuskarta sai lokacin tasan ashe har yanzu tana zubda hawaye cikin mamakin ya akayi ya gane tana kuka tace.
"Na goge."
shiru tayi jin ya k'ara yin k'asa da muryarsa kamar maiyin rad'a yace.
"Maama kina min addu'a ko? Mama ki dena zubda min hawaye kinji ko? kiyi ta nema min shiriya a wurin Allah ki kuma yi ta nema min gafarar Abba ya dena fushi dani, amman ki dena damuwa da batun dawowata gida kinji ko Maman Yusuf."
ya k'arishe maganar tare da cije lips d'inshi wanda ya gaji hakanne a gun Abba, zafi da k'unci yakeji a zuciyarsa gashi tun jiya ciwon mararshi ke addabarsa abin ya taru ya mai yawa, amman duk da haka ya daure suketa hira, sai in mararsa ta murd'a sai yayi k'asa da murya yana mai dank'e wirin,
sun dad'e suna hira lokaci d'aya Mama taji duk wani tukuki da bakin ciki da yake damun zuciyarta ya tafi, haka ya rink'a rarrashinta har saida ta sake sosai.



Koda Abba ya dawo da yamma yaga canji tattare da Mama amma saboda babu fuska haka ya hadiye maganar shi, gaba d'aya zaman Abba da Mama ya canja babu wani kula ko tattali irinna mata da miji a tsakanin su babu wani zaman hira Mama tana kokarin sauke duka hakkokin Abban ta bangaren kulawa haka shima Abban amma saisu kwana su wuni basuyi magana ba haka kuma bai saka Abba ya sakko ba, haka rayuwa taci gaba da tafiya gashi Abba ya fito mata da wani sabon salo kwata-kwata baya barinta ta fita haka in fitar ta zama dole ma sai dai ya kaita da kansa ya jira harta gama abinda zatayi su koma gida kwata-kwata baya bata damar dahar zata samu damar hanyar da zata hadu da Yusuf, sosai abin ya damu Mama har wani rama tayi lokaci d'aya ta zabge.


A hankali kwanaki naja i zuwaga makonni, makonnin na juyewa i zuwa ga watanni.

Tafiyar su Yusuf ta k'arato dan saura sati d'aya su tafi kuma a lokacin jamb dinsu ma ya fito Yusuf ya samu 220 Aryan ya samu 215 gashi waec da neco d'insu ta fito kuma Alhamdulillah result yayi kyau cikin jin dad'i Yusuf ya kira Daddy ya sanarmasa sosai ya tayashi murna, sannan daya koma gida ya had'asu da Mama, ta amsar wayar tayi part d'inta sai tsaye beedroom nata ta shige wayar na kare a kunnenta yake shaida mata,
itama tayi farin ciki sosai da addu'ar Allah ya kareshi ya kara daukaka shi tambayarta yayi.
"Mama Yusuf yaushe zakizo kiyi sallama da Yusuf d'inki ne ki samishi albarka a tafiyar da zayi?,".
dariya tayi dan yadda yayi maganar kamar ba shine Yusuf d'inba, dariya sosai ta kumayi jin yace.
"Mama na sai kinga kaina harda furfura yayi dan gashin ya dad'e baiji d'umin tafin hannunki ba da sawar albarkanki."
cikin taushi da sanyin murya Yusuf yayi mata magana saida ta goge hawayen daya zubo mata na tausayin d'an nata ta share tasan yana kewarta kamar yadda itama take kwana ta wuni da tunanin sa cikin sanyin murya tace.
"Yusuf mahaifinka ya canja gaba d'aya baya barina na fita ko ina amma akwai Allah kuma inanan ina kai mishi kukana a sannu zaimin maganin matsalar data kunnomin, kuma duk inda kake addu'ata na tare da kai, kuma dama ka gayawa gashin kan Yusuf na kul kar yayi furfura ya b'ata min kan d'an saurayin yarona mai kyau da tausayi mai kishin Mamarsa da sonta da tausayinta fiye da zaton mutun". sai kuma kuka yaci karfinta ya hanata karasa maganar lallashi da maganganu masu dad'i Yusuf ya dinga fad'a mata har tayi shiru sun d'an taba hira daga haka sukayi sallama.




Yau dai Abba da Mama suna zaune a wuri d'aya amman kowa harkar gabansa yakeyi ita Mama yanke farcenta takeyi, shi kuwa Abba yana konce ne gefenta kad'an ganin shirun yayi mishi yawane gaba d'aya ba jin dad'in irin zaman da sukeyi, shiyasa ya juyo tare da kallonta cikin son sama mata farin ciki dan yana son matarsa, kuma son da yake mata bazai hanashi hukunta d'antaba, hannunta ya jawo har saida ta konto kanshi, cikin sauri ta tsuke fuska tare da yunk'urin matsawa, rik'e hannunta yayi cikin kauda kai daga gareta dan yaga tuni idonta ya cicciko da k'olla, murya a sanyaye yace.
"Ki shirya nanda mako biyu masu zuwa zamu tafi umrah."
sosai taji dad'in tafiyar da yace mata, amman sai tayi kici-kici tace.
"da waye kuma?".
tsuke fuska yayi ya shareta dan ya gane me take nufi, dan tun da Allah ya basu Yusuf tun yana k'arami in dai Umrah zasuje to kullum dashi suke zuwa so ya gane abinda take nufi, shiyasa ya tsuke fuska yace.
"Dagani sai ke dan ina son zamu biya Dubai, so tafiyar tamuce mu biyu".
kai ta tank'warar tare da bud'e baki zatayi magana kenan,
aka kira wayar Abba da sauri ya d'aga dan samun kaucewa maganar Mama dan shi so yake suje daga nan su biya Dubai ya samu ya sabunta soyayyarsa,
yana d'aga wayar Abubakar ke shaida mishi Zulaihat bata da lafiya,
dan sam ya hana Mama rik'e waya tunda ya kamata suna waya da Yusuf ya fasata, cikin girma yace.
"Jikin yayi tsanani ne?".
Mijin Zulaihat yace.
"Eh Abba yanzu hakama ruwa ake k'ara mata dan jiya kwana mukayi bamuyi bacci ba tana amai". Abban yace. "Toh ina dai da shari'ar dazan shiga nanda awa d'aya amma bari na kawo Mamanku d'in taga jikin nata".
cikin girmamawa Abubakar yace.
"Toh Abba Allah ya kawo ku lafiya".
"Ameen". Yace tare da
kallon inda Mama take yayi yace.
"Ki shirya zamuje gidan Zulaihat batajin dadi".
"to" tace tare da tashi ta shiga d'aki ta d'auko mayafi da pace d'in kudinta ta d'auko daga cikin wardrobe dinta ta saka cikin mayafinta.



Lokacin da suka isa gidan Zulaihat sosai takejin jiki saboda laulayi takeyi lokacin dasu Mama sukaje ma bacci takeyi saboda allurar bacci da aka saka mata cikin ruwan da aka kara mata zama sukayi bayan gaishe-gaishe suka samu guri suka zauna har sukayi minti 30 Zulaihat bata farka ba gashi saura minti 30 kenan Abba ya shiga shari'ar da za'a gabatar a kotun sa, kallon Mama yayi cikin kula yace.
"Ko zaki taso mu tafi gida saiku dawo da daddare ku dubata dan nasan Aliyu zai kawo matansa su dubata, sannan in kin koma sai ki turo Amira tazo ita dan kula da yaran da aiyukan ta?" Cikin sanyi Mama tace.
"Da dai na d'an jira inga farkawanta ka dubafa kaga jikin yarinyar nan daga gani kasan tanajin jiki,
in badamuwa kaika tafi mana tunda kanada uziri, nima inta tashi na duba jikin nata sai na tafi ko?".
ta k'arishe maganar cikin neman izini,
wani kallo yayi mata, wanda yasa tayi k'asa da kanta dan tana tsoron su raba hali a gidan surukai suyi abin kunya, shiko sai yaji tausayinta ya rufeshi,
ita dai tunda ta sunkuyar da kai bata kuma cewa komaiba sai kuma taji yace.
"Zan dawo na tafi dake tunda duka-duka shari'ar ba zamufi awa biyu zuwa uku ba".
cikin jin dad'i tace.
"Tom Allah ya dawo dakai lafiya ya bada sa'a".
"Amin Amin."
yace tare da ficewa, har kofar gida Abubakar yayi masa rakiya sannan ya dawo.



Mama kuwa Abba da Abubakar na fita ta d'auki wayar Zulaihat dake gefenta ta kira wayar Yusuf sau biyu tana ringing harta tsinke baya d'agawa wayar ta kuma ci gaba da kira ba k'akk'autawa,
Shi kuwa Yusuf yana jin wayar amman ya gaza d'agata dan azabar ciwo da mararsa keyin, sai murk'ususu yakeyi gaba d'aya ya kik'e da zufa, ya konta rufda ciki yana mammatse cinyoyinshi dan son samun sassauci, wani irin juyawa yayi rigingine tare da yin mik'a da k'arfi saida duk gabb'an jikinshi suk bada sautin k'as,
Aryan da fitowar shi daga d'aki kenan hannunshi rik'e da cup d'in tea da lemun tsami, cikin mamaki da tsorog ganin yadda bnnarsa tayi wani irin cika da mik'ewa tayi cur cikin jallabiyar dake jikinshi ido ya fitar tare da cewa.
"Kai lafiyar ka kuwa? me haka mutun kamar doki? ".
harara ya watsa masa cikin cije lips enshi da yin bushings yace.
"Hauka nakeyi, kuma ba doki bane ni rak'umi ne ni banza kawai".
dariya Aryan yayi yace "maida wukar bada zafi na fada ba, tsoro ne naji kar kayiwa kujerar nan fyad'e, banza jarabebbe sai masifar tsiya, ko baka da lafiya sai kayi masifa, kullum kana cikin yin azumi kamar wanda yayi kisan kai kuma kullum sai k'aruwa fitinarka keyi,".
cup d'in ruwan tea mai lemun tsamin ya mik'a mushi
hararashi yayi tare da tashi zauna.
" Matsa min da wannan banzan ruwan tsamin, dan na lura so kake ka kasheni ka maidani maceccen namiji".

Dariya Aryan yayi sosai harda rik'e ciki yace.
"ohoh haka kace, ai zaka kuma nema in jarabar ta motsa zanyi maganin ka".

"Oh ai bani nayi kaina naba Allah ne ya yini haka kuma shi zai yayemin."

ya k'arishee maganar da alamun abin na damunshi
matsoshi Aryan yayi tare da cewa.
"No karka damu in dai kana azumin in sha Allah zai ragu".
ringing d'in da yaya keyi yasasu yin shirusaura da sauri
Yusuf ya d'aga ganin sunan My blood sister na yawo a screen d'in wayar,
jin muryar Mama ya sashi mik'ewa da sauri , itama Mama cikin sauri tace. "Yusuf maza kazo gidan
Addanka inanan ina jiranka."
ai tuni ya mik'e tare
da sanarwa Aryan.
" Mama tana gidan Adda Zulaihat maza tashi mu tafi. "
cikin happy Aryan yace.
"ah lallai babu zama muyi maza mu tafi".
sauri-sauri Yusuf yayi wonka sarki tare da canza kaya suka fito suka sallami Kaka Aryan nata mashi tsiya,
Aryan ne yayi driving dinsu a lipan dinshi.



Da sauri Yusuf ya sauk'a akan lipan din tun kafin Aryan ya tsaya ya shiga gidan da gudu-gudu sauri-sauri da sallamarsa da shigarsa parlour duk a tare yayisu, Mama na ganin shi itama cikin farin ciki ta mike da sauri ya karasa ya rungumeta sai kuma suka saki kuka a tare lokacin yayi dai-dai da shigowar Aryan ganin halin da suka shiga shiya sakashi tausayin kanshi lokacin daya tuno nashi iyayen dasu rasuwa ma sukayi bazai kara ganin suba kwata-kwata kwallah ce ta zubo mishi a ido ya saka hannu ya goge ya karasa shiga cikin parlourn, kukan sune ya tashi Zulaihat daga bacci nanta bude ido ganin halin da suke ciki itama batasan lokacin data fara nata kukan ba jin shashshekar kukanta shiya ankarar dasu Mama sukayi shiru nan suka zauna Yusuf ya wani shige jikin Mama Allah sarki tsakanin uwa da d''a sai Allah,
ita kuma Mama hannu ta saka tana shafa masa kai sai lokacin Aryan ya gaisheta ta amsa cikin sakin fuska da farin ciki tare da mik'o mishi hanyalamar yazo,
gefenta ya zauna tare da d'ora kanshi bisa cinyarta kamar yadda Yusuf yayi, kansu ta rink'a shafawa tana sa musu albarka tare dayi musu nasiha mai ratsa jiki.
Nan fa suka fara hira tamkar wadanda suka shekara basuga juna ba Zulaihat ma taji karfin jikin nata dan harta tashi tayi wanka.




Tsahon awa d'aya su Yusuf sukayi a gidan sosai Mama tayi musu addu'ar samun nasara da kuma suje lafiya su dawo lafiya 50k ta dauko a Jakarta ta mikawa Aryan tace.
"Ga wannan babu yawa kuyi amfani dashi in kunje". dad'ine ya cika su addu'a suka hau kwararo mata da fatan nisan kwana mai amfani dadine ya ishi Mama badan sunso ba sukayi sallama suka fito zasu tafi saboda gudun kada Abba ya dawo ya samesu dan zai iyayin fushi ma da zulaihat din,
su Mama ne sukayi musu rakiya har kofar gida suna shan kwanar layin ta baya danko gida su Mama basu koma ba suna jiran su k'ule sai ga Motar Abba ta shawo kwanar layin ta gaba,
wata wawiyar ajiyar zuciya Mama taja tare da dafe k'irjinta har a fili saida Zulaihat taji, ita kambakinta ta toshe ta koma cikin gida da gudu tana kuka dan yadda suka ga Abba ya k'araso da gudu yasa kan motarsa yabi bayan.....................!




*BY*
*GARKUWAR FULANI*
[02/01 1:06 PM] My 2nd Mtn: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*HUKUNCIN ALLAH*

Page 1⃣1⃣

*NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*







🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇




*GA masu buk'atar sayan littafin Hukuncin Allah zaku turo katin Mtn na 200 kacal ta layin nan 09097853276 ko kuma ta asusuna 0005388578 Jaiz bank Aisha Aliyu Garkuwa, tabbatar ka/kin turo shaidar biyanki*


*Free page*


Aryan ne ya fito daga gida da niyyar zaije aski ganin mutum a kwance a kofar gidan su kamar bashi da rai shiya saka shi yin baya da sauri,
komawa gida yayi da gudu yana kwalawa Baba mai gadi kira tare da karasa shiga cikin gidan a gigice, Baba mai gadi da fitowar shi daga bandaki kenan shine ya saka shi fitowa a daki shima a tsorace yace.
"Aryan lafiya ka shigo gida a gigice haka meke faruwa?". da hannu yake masa nunin waje yama kasa magana, a hankali cikin sand'a da tsoro Baba mai gadin yake tafiya har ya isa bakin gate d'in sannan ya lek'a da ido d'aya dan Baba isa ba k'aramin matsoraci bane, ganin mutum kwance ya sakashi fitowa da sauri yana. "Subhanallahi ai mutum ne a kwance".
juya shi, ido ya zaro da mamaki ganin Yusuf ne ya fara kwalawa Aryan da yake cikin gida kira.
"Aryan! Aryan!! Aryan..!!! zoka gani ai abokin kane Yusuf".
da gudu Aryan ya fito daga gida ganin Yusuf cikin halin ciwo alamar ya sume shine ya kara rikita Aryan da gudu ya kuma shiga cikin gida.



Kakar su data fito lullube da mayafi tana rike da hannun Rayhana dan zasu fita unguwa,
driver dazai kaisu kuma yana cikin mota yana jiransu da sauri yake kiran Hajiya kakar su yace.
"Hajiya Yusuf a waje ya suma jikin shi duk a farfashe".
da mamakin zancen Aryan Hajiya tace.
"kamar yaya Aryan suma kuma?".
Mai gadi ne ya shigo ya nemi temakon driver dan su d'auko Yusuf sai lokacin Hajiya ta gane abinda Aryan yake nufi cewa tayi.
"kuje ku kamoshi ku saka shi a mota mu kaishi asibitin saimu kira gidansu muji kosun sani?".
Da "toh" suka amsa mata sannan d'aukoshi suka saka shi a motar da Aryan da Kaka da Rayhana suka shiga motar Mai gadi ya wangale musu gate yana addu'ar Allah ya kiyaye hanya.



A gidan Yusuf kuwa Aunty Amarya ce dake rungume da Zarah a cinyar ta tayi bacci saboda kukan da tasha, cikin muryar kuka Anty tace.
"Maman Yusuf ina Zulaihat d'inne naga duk abinnan da ake ban ganta ba?".
Ajiyar zuciya Mama taja had'i da goge ruwan hawayen daya kasa daina zuba daga idanuwan ta cikin kuka tace.
"Kinsan Zulaihat bata son rikici da tashin hankali, duk abinnan daya faru babu wanda ta sani, tana farajin Abbansu yana fada ta tattara kayanta ta koma gidanta nima d'in ban sani ba kirana tayi a waya ta fadamin".
shiru Aunty Amarya tayi tana jaddada hakurin Zulaihat dan tana da hakuri nesa ba kusa ba.



Zarah ce ta dawo da ita daga tunanin data tafi.
"Ancy ina Hamma Yucuf na Abba a kasheshi ko?".
saita kuma fashewa da kuka rarrashin ta Aunty Amarya ta dingayi saboda kukan da Zarah tayi tuni zazzabi ya rufeta ta fara rawar sanyi, cikin tausayawa Ummee tace.
"Kije ki bata paracetamol tasha kafin zazzabin ya kamata da yawa".




A can gunsu Yusuf kuma Kai tsaye F, M,C YOLA su Aryan suka nufa da Yusuf emergency amma firr likitoci sukaki karb'ar shi sukace ai accident ne saida police ana cikin haka Daddy ya dawo dama bai tashi aiki ba kiran da Aunty Amarya tayi masa shine ya saka shi komawa gida.



Aryan daya fito yanata kokarin kiran number d'in Abba tak'i shiga saboda matsalar network danshi shaf yama manta Daddy a asibitin yake aiki,
har ya juya zai koma gun kaka dan shaida mata wayar bata shiga,
sai kuma ya juyo da sauri ganin Daddy da yayi da gudu ya karasa wajen shi nan yake fada mishi da sassarfa Daddy ya shiga da kanshi ya karbi Yusuf shi yayi masa duk wasu taimako daya kamata aka bashi gado,
drip aka saka mishi Bayamon ya farfado daga suman da yayi amma anyi mishi allurar bacci danya samu hutu.



Bini-bini Daddy zaizo ya dubashi har zuwa lokacin da ruwan ya kare yana cikin cire mishi ruwan Yusuf ya farka, a hankali ya fara bude idanuwan sa wani irin sarawa kanshi yake mishi saboda ba karamin ciwo yake masa ba, fess kuwa ya ware idanuwan nashi akan Daddy da tun dazu yake kula da alamun sa ya farka.



Ganin Daddy a gaban shi sai yayi hanzarin maida idon shi ya lumshe hawaye na bin gefen fuskarsa, murmushin gefen baki Daddy yayi hadi da cewa.
"Bud'e idanun ka mana".
jin kunya yasa Yusuf ya kasa bud'e idanuwan shi,shiko Daddy daurewa yake ya gimtse dariyarsa, dan in ya tuna abinda Yusuf yayi dariya ke kamashi ja'irin yaro wato ya ramawa uwarsa abinda ake mata a kan tsohuwarsu, gashi dama yasan Hajja Inna da d'an banzan raki,
murmushi ya kumayi sannan yasa hannun ya tallaboshi ya taimaka mishi ya mike ya jingina shi da pillow amma har zuwa lokacin Yusuf ya kasa hada ido da Daddy dan wani matsanancin kunyar shi yakeji kuma sai yaji danasani ya kamashi.



Daddy ne ya kalli Aryan yace.
"Ka taimaka mishi ya wanke bakin shi ka hada mishi tea yasha ka bashi maganin shi yadda na nuna maka saiya rama sallolin da ake binshi nizan tafi gida dare yayi sai gobe in Allah ya kaimu".
da "toh" Aryan ya amsa saida Yusuf yaji fitar Daddy ya iya d'ago kanshi.



A gida kuwa lokacin da yaran gidan suka dawo Zarah itace ta basu labarin abinda ya faru dan zuwa lokacin zazzabin

Please Login or Register in order to submit comment