Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wani abu kuwa?."
da sauri Zahra tace.
"a a."
tsaki ta d'anja kana tace.
"Kawai jiya da dare saiga Safwan wai yazo yana sona,
yace min tunda bai samekiba wai in taimaka mishi ya sameni."
cikin kula Zahra tace.
"Alhamdulillah wlh ni tausayin Safwan naji kinga Allah bai k'addara in zama matarshiba tunda ya koma gareki ki amsheshi wlh yanada mutunci,
Koda Daddy ya kirashi ya gaya mishi cewa ya aurar dani yayi hak'uri ya turo a d'auki kayanshi wlh cewa yayi ya yafe,
wai ya bani a kawo min,
to Aunty dai har tace a kamonin wai sai wannan Hamma Yusuf d'in yace ba dai a gidanshi ba wai a sadakar."
cikin fahimtarta tace.
"To ke waya gaya miki?."
baki Zahra ta d'an tabe kana tace.
"Mama ce ta gaya min da mukayi waya."
tab'e baki Dija tayi kana tace.
"Toh nima d'in yazo a makare domin yayanki ya rigashi, ko dai ink'i Jafar inso Safwan kikeso?."
da sauri tace.
"A a kiso yayana kai Alhamdulillah amman naji dad'in wannan abu."
sai ta kuma yin kalar tausayi tace.
"Ayyah Safwan Allah ya bashi mai sonshi."
Amin Amin Dija tace kana ta jawo wannan ledar ta rink'a firfito da abubuwan ciki tana ajiyewa a gaban Zahra,
yayinda ita kuwa Zahra tuni ta d'auki d'aya daga cikin robobin ta bud'e ganin wani abu kamar mulmule mulmlen fura gashi sai k'amshi yakeyi ai kawai sai ta gutsura jin wani irin dad'inshi yasa ta fara cinshi tare da cewa.
"Ke Dija me wannan mai d'an karen dad'i?."
cikin yi mata dariya Dija tace fara nunnuna mata kayan tare da cewa.
"Kinga wannan duk tsara barkice Aunty kubra ce ta saya mikisu wurin AYSHA ALIYU garkuwa kinga wannan tsumine mai azabar kyau da k'arfi,
kinga galam din ta saya miki, ga kuma garin mad'i, shima babbar ribar ga gumba yar k'asar mali itace kikeci,
ga butar sirri tace dan Allah dan annabi kiyi aiki dashi kayane masu ink'anci."
sai ta kuma bud'e dan wani roba ta ciro d'an wani abu ta mik'awa Zahra cikin nitsuwa tace.
"Wannan sunanshi memory yana had'e mace da tsuketa koda tayi haisuwa ya kai goma,
wallahi kud'i mai yawa ta cire tayi miki sayayyarnan sabida na gaya mata auren bazata akayi miki gashi alamu mijin naki ba sauqi."
tsumin ta d'auka ta fara lasa jin dad'inshi yasa ta d'an sha mai yawa kana cikin sanyi murya na rawa tace.
"Allah sarki Aunty kubra tana so ta gyarani kuma k'addara dai ta rigayi fata budurcina bazai dawoba,
haka fa Adda Zulaihat ma da Adda Amira suka had'o wasu suka kawo min wai na gyarane."
cikin tausaya mata Dija tace.
"Please na rok'eki da Allah da manzonsa kiyi amfani da wannan kayan dukansu wlh zakisha mmki wlh keda kanki zaki bani lbri."
kai ta jinjina kana taci gaba da cin gumbunan duka kala uku cikin jin dad'insu tace.
"Ai ko dan dad'insu zanci kiji tsuminnan in kasha sai harshenka yayi rawa."
cikin hikima dai a ranar Dija ta sata,
tayi amfani da wannan memory,
kana tasata wasu duk ta shanyesu tun a wunin ranar kana ta fara amfani da butar sirri.
hira sukayi tasha sai sallaa ke tadasu,
bayan LA'asar ne Zahra ta kalli Dija cikin zare ido tace.
"Ke Dija wlh sai nasofa nakeyi,
kuma abinga fa ya lik'eni."
dariya Dija tayi mata kana tace.
"Allah dai yasa dama Hamma Yusuf bai rabekiba."
cikin tab'e baki tace.
"Ke mufa ba ruwanmu yana parlour ina bedroom."
dariyar mugunta Dija tayi dan tasan,
duk randafa ta shiga hannun Yusuf zatayi bayani.
nan dai suka wuni sai yamma Jafar yazo ya d'auki Dija ya maidata gida.


Hamma Yusuf kuwa
shine bai dawoba sai bayan sallan isha.

yana shiga daga cikin parlour ya fara rage kayan jikinshi a parlour ya cire sut d'in shi kana ya zame dogon wond'on sannan ya zauna bisa 1 str tare da cilla woyoyinshi kan carpet a tsakiyar parlour,
sunkuyowa yayi tare da sab'ule takalminshi sau ciki,
sannan ya kuma mik'ewa tare da cire sauran rigar dake jikinshi,
ya rage dashi sai boxer,
hannunshi ya cusa cikin sumar kanshi yana yayyamutsa sumar da salon yiwa kan nashi tausa.

Murya can k'asa yayi sallama kana ya kusa kai cikin bedroom d'in,
zaune ya ganta bisa sallaya bisa dukkan alamu shafa'i da wutiri tayi,
baibi ta kantaba ya zarce bathroom dan yau anayin wani irin zafi,
duk mazaunin adamawa yasan irin zafin da suke ji a irin yanayin da damuna takeyin gangami,
yana shiga brush ya farayi daga bisani ya sakarwa kanshi ruwa a k'allah saida yayi mintuna shida ruwa na zubowa bisa tsakiyar kanshi.
kana daga bisani ya fara murje jikinshi da sabulu mai d'an karen k'amshi,
sulle fatarshi yayi fes sannan ya jawo rigar wonkan ya d'an zira tare da d'aure igiyoyinta,
gefen durowar turare ya nufa inda ya murje jikinshi da mai kana ya shafe turare a dukkan sashin jikinshi.
kasan cewar ana d'an zafi-zafi garin yayi dim ba alamar iska ko kad'an shiyasa ya zaro wani tattausan gajeren wondo,
turare ya fesa mishi sannan ya saka,
dagashi bai k'ara komai a jikinshi ba,
ya fito,
inda ya samu tuni ta konta bisa gado.
ba tare da yace mata komaiba ya fita parlour yaje ya rufe ko ina sannan ya dawo bedroom d'in k'ara gudun Ac yayi tare da tattare labulayen ya bar net d'in kawai,
wutan d'akin ya kashe wanda shine yasa Zahra saurin mik'ewa ta sauk'o daga kan gadon cikin sanyi tace.
"Hamma Yusuf ni ina tsoron d'aki da duhu dan Allah barmin wutan a kunne."
kunna wutan ya kumayi kana ya juyo inda take tsaye idanu ya tsura mata,
ita kuwa sunkuyar da kanta tayi dan bazata iya jurewa ganinshi a hakaba yayi mata korjini da yawa,
taku biyu yayi zuwa uku ya isa inda take,
ganin yana k'ara matsota yasa ta fara yin baya-baya,
shi kuwa yana binta fuska a had'e,
tafiya tayi luu alamun zata fad'i sabida tuntub'en da tayi da table d'in dake gaban gadon,
hannunshi yasa ya kamo nata kana ya gyara mata tsayuwarta yayinda ita kuwa taketa sauk'e ajiyan zuciya da yin hamdala.
cikin tsareta da ido yace.
"Ke komai kina tsoro,
kina cutar dani da wannan tsoron naki kina hanani bacci,
kalli yadda kike min jiya kika shak'eni kika hanani ko motsi wai ke kukan kululluka,
ni zaki karni a banza,
shiyasa yau zan konta a nan inji ko nima zanji kulullukan da kike fad'in."
kai kawai take gyad'a mishi ita a niyarta to itan sai ta koma parlour,
shi kuwa hannu yasa ya kamo nata sannan ya mik'e d'aya hannun ya kashe wutan.
da sauri ta matso jikinshi tare da rik'e hannunshi gam.
janta yayi zuwa kan gadon kana ya konta gefe tare da cema.
"konta mana."
cikin sanyi da tsoro ta konta gefenshi ta bayanshi,
yayinda ta ware idanunta wai ko zata ga haske kad'an amman a banza.
dole ta konta tayi tsit da alamun tsoron.

Shima shiru yayi yanajin sanyin numfashinta na sauk'a bisa bayanshi.

Sun dad'e a haka shiru babu wanda yayi koda motsi,

can Zahra ta fara jiyo kukan kule guda d'aya kuma kamar a nesa yake,
hakan yasa tayi juyi d'aya a nabiyu ta mannu da jikinshi,
hannu tasa ta zagaye k'irjinshi,
kana tayi shiru kamar jaren da aka zubawa ruwa.

Shi kuwa Yusuf ajiyan zuciya ya sauk'e jin ta ruggumeshi sanyin tafin hannunta na ratsa k'irjinshi,
gaba d'aya ta fara dama mishi lissafi,
hakan ya sashi yin juyi tare da yi mata rumfa da k'irjinshi,
ido ta rumtse da k'arfi sabida tsoron daya ziyarceta,
sai ta kuma yi maza ta bud'e idanun nata jin ya mirgina gefen hagunta,
hakan yasa suka kwanta suna fuskantar juna,
hannunshi yasa ya jawota jikinshi tare da ruggumeta,
kai ta manna a k'irjinshi sannan ta zura hannunta bisa gadon bayanshi,
daga nan basu kuma motsiba kowa da abinda ke ransa kuma duk dai basuyi baccinba shi yasan batayi bacciba itama kuma tasan baiyi bacciba.
sun kai awa d'aya a haka,
sannan Zahra taji sautin sauk'ar numfashi sa ya sauya shiyasa tayi zaton ko bacci yayi.
hancinta ta manna tsakiyar k'irjinshi ta shak'i k'amshin jikinshi ido ta lumshe kana ta k'ara ruggumeshi,
da sauri ta manna tafin hannunta a tsakiyar bayan nashi dan jin wasu abubuwa a bayan nashi sunyi rud'u-rud'u,
cikin mmki tasa tafin hannunta tana bin zanen abinda take ji d'in,
jinsu birjik a bayanshi har zuwa kafad'unshi ne ya sata k'ara matsoshi,
yatsarta d'aya tasa kan wani layin da taji yafi girma ta fara binshi a hankali wai karya farka.
abinda bata saniba duk abinda takeyi yana jinta,
domin ba baccine ya canza mishi salon fitan numfashin sa,
itace ta jaza mishi sauyin yanayi uwa uba yanzu da yakejin abinda take mishi da yatsarta kamar tafiyan tsutsa take mishi,
gaba d'aya tsikar jikinshi sai yam takeyi duk wani k'ofar gashin jiki yana amsa sak'on yatsarta,
tuni ya bud'e idanunshi da suka cika da wutar fitina.

Ita kuwa Zahra bin shatin zanen tayi da yatsarta har zuwa kan k'irjinshi,
inda taji bakin shatin ya tsaya dai-dai kan nipple inshi na hannun hagu,
cikin al'ajabi ta rink'a bin bakin nipple d'in da saitin abin ya mishi zobe,
wani irin gauron numfashi Hamma Yusuf d'in nata yaja tare da jin dukkan gabban jikinshi sun sake,
ita kuwa bata kulaba dan a zatonta bacci yakeyi,
hakan yasa ta kuma meda hannunta tsakiyar bayan nashi tana bin layi da shatin jikinshi tana mgnar zuciya da bata san ta fito filiba.
"Toh menene wannan a bayanka Hamma Yusuf,
gashi kuma abun har k'irjinka da kafad'unka ji wani kamar tafiyar maciji fa."
ido ya lumshe domin baya son ta gane idonshi biyu ta d'auki tsawon awa d'aya idonta biyu tanata shafa abun inda tabi wani taji yayi k'asa kan mararshi,
jin zata haukatashi ne yasa shi yin saurin juya mata baya kana ya matsa tare da fidda nannauyan numfashi wai dan ta d'auka bacci yakeyi.

Tab ai Hamma Yusuf kam wannan rana bai rumtsa ba kona one minute,
ita kuwa shiru tayi tana sak'e-sak'e har bacci ya saceta.

Shi kam yana jin tayi bacci ya mik'e ya shiga bathroom,
wonka yayi kana yayi al'wala sannan ya fito ya koma parlour yayi ta karatun quraan.


Bayan gari ya waye...!






















By
*GARKUWAR FULANI*
[01/02 5:48 PM] My 2nd Mtn: *HUKUNCIN ALLAH*

*PAGE 21*


NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*








Daga fito warshi masallaci,
mota ya shiga ya bar gidan kai tsaye gidansu ya nufa,
k'arfe bakwai da rabi dai-dai yayi parking a harabar gidan nasu,
yayinda dai-dai lokacin Jafar kuma ke k'ok'arin fita daga gidan,
ganin Hamma Yusuf d'inne ya sashi sauk'e glass d'inshi kana ya lek'o da kanshi cikin girmamawa yace.
"Barka da safiya Hamma."
fitowa yayi cikin motar tashi kana ya meda marfin ya rufe tare juyowa ya fara tafiya kana ya isa inda Jafar yake,
shi kuma Jafar ci gaba yayi da cewa.
"Yauwa Hamma ko in mik'o maka breakfast naku, tunda kazo dama ina sauri kar in makara zuwa office."
kauda kanshi yayi kana yace.
"To da banzo bafa, kuma kasan yaushe zan koma, kawai kayi sauri ka kaimata sai ka wuce."
kai ya jinjina kana ya mushi sallama yaja fita,
shi kuwa Yusuf cikin gidan ya nufa,
yana fatan Allah yasa ya samu Abbanshi domin har yau bai zauna dashi ba wuri d'aya hakama Daddy.

Kai tsaye parlour Mama ya shiga,
bakinshi d'auke da sallama,
jin shiru babu alamun motsin mutunne ya nufi bedroom nanma ba kowa.
hakan ne ya sashi fitowa parlour gefen kitchen ya ratsa ta cikin wani corridor mai girma,
tafiya kad'an yayi sai gashi a bakin k'ofar parlour Abba,
cikin k'arfin hali ya bud'i baki yace.
"Salamu alaikum."
Abba dake zaune a tsakiyar parlour bisa carpet yana karin kumallo,
jin muryar gudan jikinshi ne yasa shi zubawa k'ofar ido tare da cewa.
"Wa alaikassalam."
jin muryar Abba saida yaji zuciyarshi ta tsananta bugawa,
cikin sanyi kanshi a sunkuye ya yaye labulen kana ya kutsa kai,
shiko Abba gyara zama yayi tare zuba mishi ido,
gefenshi yaje ya zauna tare da tonkwoshe k'afa yayi zaman mai sallah kana ya d'an d'ago kanshi cikin sanyi murya a konce yace.
"Abba ina kwana."
gyara zama ya kumayi kana ya fuskanceshi sosai sannan yace.
"Alhamdulillah, ya iyalin naka?."
wani irin sanyine ya ziyarci zuciyar Yusuf har saida yaji tsikar jikinshi na zubawa,
cikin jin dad'i ya kuma d'ago kanshi ya kalli Abban nashi sai ya kuma sunkuyar da kai ganin shima Abba ido ya zuba mishi cikin sanyi yace.
"Tana Lfy."
"Masha Allah."
Abba yace kana ya jawo pillet d'in da yake gabanshi ya sashi a tsakiyarsu, kana ya mik'o mishi kofin da yake rik'e dashi na kunun gyad'a wanda dama can Abba shiya koya Yusuf shan kunun gyad'a,
da sauri ya amshi kofin,
tare da cewa.
"Ngd."
shi kuwa Abba tiren ya jawo kana bud'e yar madaidaiciyar kulan da yake d'auke da zazzafan k'osai,
cika pilet d'in yayi,
kana ya jawa yar k'aramar kulan da ke d'auke da soyayyan kwai wanda aka had'ashi da hanta da murmushwsshen kifi,
kan k'osan ya zuba musu kana ya jawo woni kofin tare da bud'e filas d'in kunun ya d'iba sannan ya kuma kalli Yusuf da yaketa juya spoon a cikin cup d'in,
kana yace.
"Ci abincin tunda zafinshi."
gyara zama yayi yadda ya fuskanci Abba da kyau kana ya d'an had'e gira yace.
"Abba a k'ara min zumar."
murmushi yayi cikin jin dad'in daya dad'e baijiba ya jawo robar zumar kana shi kuma ya mik'o kofin ya tsiyaya mishi zumar sannan ya meda ya rufe,
tare da cewa.
"Wato har yanzu baka rage son zak'in nan bako Yusuf?."
kurban kunun yayi tare da lumshe ido alamar eh.
murmushi Abba ya kumayi kana yace.
"Shima mgna da kai har yanzu baka bari bako?."
kai ya jujjuya alamar wai ya bari kana yace.
"Abba na bari fa."
dariya yayi ganin yadda yayi da kai.
shi kuwa Yusuf cikin jin dad'i ya fara cin k'osan da had'ida kwai d'in shima Abba ya gyara zama suka fara ci a tare yanata yiwa Yusuf irin tambayoyin na yaushe gamo wani ya amsa da baki wani da kai,
wato dama in dai ance maka halittar mutunne haka kawai to rabu dashi a haka,
suna cikin hirar,
Mama da yanzu ta gama wonke bathroom d'in Abba ta fito bedroom jin alamun ana hira harda dariyane yasata fitowa da sauri,
ganin Yusuf ne da Abban shi,
kawai sai ta juya ta fuskanci alk'ibila tayi sujjadar godiya wa Allah domin yau dai Allah ya amsa mata addu'arta.
tasowa tayi da sauri kana ta nufi inda suke tare da cewa.
"Iyeh wato abinma wariyar launi akemin,
ba dumuwa nima Zulaihat na zatazo sai dai kujimu k'us-k'us banda ku."
murmushi sosai Abba yayi domin yau yanajin farinci tamkar randa aka haifa mishi Yusuf,
shi kuwa Yusuf kai ya jinjina tare da cewa.
"Maman Yusuf hirar sirrine fa mukeyi,
wai Abba cewa yake zai sayo reza yamin aski."
sai kuma duk sukayi dariya shi kuwa Yusuf sai ya kuma had'e fuska yace.
"Maman Yusuf waifa Abbana malu zaimin, kato dani amin malu."
dariya tayi kana ta zauna gefenshi tare da cewa.
"aini da wannan aski naka gwara kawai kabar gashin duka ya cika kaid'in amman ka wani yad'e gefe da gefe da k'eya kabar tsakiya zuwa gaban goshi a cike."
harhad'a pillet da kofunan yayi kana yace.
"To ita kuma tace askin nan yana min kyau."
cikin murmushi Mama tace. "Wacce kenan?." murmushi yayi kana yayi k'asa da kai yace.
"Ita mana."
ai gaba d'aya Abba da Mama sai suka zuba mishi ido suna murmushi waishi kunya yakeyi bazai kira sunan Zahra ba,
Abba kuwa gyaran murya yayi tare da cewa.
"Tashi kaje ku gaisa da Daddynku,
ka wuce gida naji kamar hadari ne a garin ka baromin yarinya ita d'aya."
mik'ewa yayi kana ya musu sallama domin shima bacci yakeji.
a tsakiyar gida ya samu Ummi wacce tun d'azu take tsaye tana sauraron dariyarsu tana jin bak'in cikin su yanzu tasu k'addarar tabi jikinsu ta shud'e to itafa da yanzu tata k'addarar ta sauk'o .
cikin girmamawa Yusuf ya gaidata kana yace.
"Ummi Daddy nan kuwa?."
cikin kunya ganin shi har gobe a matsayin uwa ya rik'eta,
cikin yin dariyar baka bata k'aunaba tace.
"Eh bai fitaba ka haura parlour sama."
kai ya gyad'a mata kana ya haura.
Hajja Inna kuwa tana jin haushin yadda Yusuf baya ko kallon inda take,
domin tun randa Aryan ya rasu bata kuma ganinshi da idontaba sai dai taji muryarshi kamar yadda taji,
tana jin ta tsani Ummi sabida itace tayi ta zugata kan karta bari Abba ya yafewa Yusuf bare ya dawo gidan,
tana son jikanta amman makircin Ummu yasa ta farrak'a tsakaninsu.

Shi kuwa Yusuf a parlour Daddy ma kusan tare sukaci abinci sunayi suna hira Aunty Amarya na daga gefensu tana jinsu.
cikin kulawa Daddy ya kalli Yusuf ganin ya ajiye fork d'in da yake cin soyayyan dankalin cikin kula yace.
"Baka son cin abinci ko Yusuf kasa damuwa a ranka kalli duk yadda ka rame,
haka zakuyi ta zama kenan?."
cikin sanyi yace.
"Daddy ina cifa musamman madara da zuma."
murmushi Aunty Amarya tayi kana tace.
"Ikon Allah to madara da zuma abinci ne?."
Cup d'in tea Daddy ya mik'a mishi kana yace.
"Itama k'anwar taka haka take zama babuci sai kuka,
sai ku zauna ku k'untatawa rayuwarku,
ko zakuyi fushi da hukuncin Allah ne?."
da sauri ya jujjuya kanshi alamar a a.
shi kuwa Daddy nasiha ya fara yimishi daga bisani yace.
"Ni banyi zaton haka daga gareka ba Yusuf sabida nasanka da yarda da k'addara lallai nasan rashin Aryan abune mai zama a rai to amman nasan duk zafisa bai kai zafin daka shiga shekaru hud'u zuwa biyar da suka wuceba,
kuma ka jumre kayi imani da k'addararka gashi yanzu tuni ya wuce,
to shima rashin Aryan kuyi hak'uri dashi fatan Allah ya baku wasu masu albarka."
A saman lips enshi ya amsa da.
" Amin Amin ."
haka dai yayi ta mishi nasiha jin an fara yayyaifi ga rugugi gari yayi duhu yasa Yusuf mik'ewa tare da cewa.
"Daddy bari in wuce gida."
Cikin kula Daddy yace.
"A a kayi zamanka ya ruwa na shirin sauk'owa kuma zakace zaka fita kamar wani bak'o."
cikin jin kunya yace.
"Daddy Abba yace maza in tafi wai na baro mishi d'iyarshi ita d'aya."
dariya sukayi baki d'aya kana ya fita ya tafi.

Tuni hadari yayi gagamin domin yau kwana uku kenan ba'ayi ruwan samaba sai zafi da akayi ta tsulawa cewar tsoffi wai ruwan ke tafasa shiyasa ake zafi,
kasancewar ruwan ya fara sauk'a sai shiyasa gaba d'aya kowa ya nemi mafaka kan titin shiru time to time ababen hawa ke gilmawa,
wannan shi ya bawa Yusuf damar tsula gudu son ranshi.
cikin 20 minutes ya isa harabar gidanshi,
tuni lokacin ruwan ya fara k'arfi.

M Jabeer kuwa ganin Affan ya sharesu da team d'insu da iya gaskiyarshi kuma yake jin haushinsu har yau yana k'ulkace dasu kan abinda sukayiwa Yusuf,
to dan cire zargin da Affan yake mishi shida Aryan shiyasa.
Yau ya shirya zuwa gidan Yusuf shida Aryan da Idi kana yace shima Affan yaje shida Jafar su had'u a gidan Yusuf dan su warware abinda ke k'ulle su kuma fito da ainin abu a tsakaninsu asan gskyar lamari da kuma yadda akayi komai ya faru ko sa samu Affan ya dena musu kallon mugaye.
To kuwa haka suka shirya had'uwar so kuma sai ga ruwan sama ya sako shine dalilin da ya hanasu zuwa suka meda zuwan nasu da yamma.


Zahra kuwa tunda aka idar da salla ta kuma yin bacci sai zuwan Ya Jafar d'intane ya tasheta,
sauri-sauri suka gaisa ya tafi ganin lokaci ya k'ure mushi,
ita kuwa yana fita ta koma bacci a parlour,
sai k'arfe tara yunwa ta tasheta,
wonka taje ta sulla kana ta shafa manshi da turarenshi,
ganin yau bai dawoba bare ya bata kayan da zata saka kamar yadda suka saba in tayi wonka ta meda kayan jikinta in ya dawo masallaci sai ya bata kaya,
so ganin yau bai dawoba sai taje ta bud'e duruwar da take ganin yana d'auko mata kaya,
cikin mmki ta rink'a kallon cikin durowar kayane a kimtse a ciki step na sama cike yake dasu atampa las shadda,
sun kai kala bakwai-bakwai sai step na biyu dogayen rigunane masu taushi da azabar kyau wanda sun kai kala goma babu color da babu,
step na uku ta kuma zubawa ido su kuwa takalmane da jakukkuna sai k'ananan kaya a gefe kana sai laffaya masu abar kyau da tsada kusan guda biyar,
sunkuyowa tayi step na hud'u na k'asa kenan,
"Wow masha Allah." tace ganin kayan kolliyane kala daban-daban turarukane iri daban-daban.
cikin k'arfin hali ta zaro wata diguwar riga mai d'an fad'i kalar sararin samaniya sai ratsin fari a ciki,
hakama gyanshi,
kasancewar sam babu bireziya da pan a cikin kayan yasa ta duba gefen k'anan kayan kana ta zaro wani dogon wond'o mai tashi ta saka sannan ta zura rigar, kana ta yafa gyalen a kanta,
wani turare ta ganin Oud ma'aruf ta d'auka ta feffeshe jikinta,
ido ta lumshe jin sanyin k'amshi da turaren keda shi,
bayan ta kimtsa komai yadda ta sameshi sai ta tsaya gaban mirror tana kallon yadda rigar tayi mata kyau,
sai dai kuma wuyan rigar ya mata fad'i motsi kad'an zatayi sai ya zamo,
gashi rigar irin mai taushi da mannewa a jikine,
haka dai ta fito parlour tazo tayi breakfast,
kana ta tatttara komai tsab sannan ta d'auki wayarta ta k'ira Mama suka gaisa sannan ta kira Aunty Amarya da Adda Zulaihat.
ganin iska ya sako duk labulayen sai kad'awa sukeyi suna samane ya sata komawa bedroom tabi lafiyar gado.
ta shiga kenan shima Yusuf ya shigo parlour,
meda k'ofar yayi ya rufe kana ya nufi bedroom,
bakinshi d'auke da sallama ya shiga,
cikin sanyi ta amsa mishi tana mai jin dad'in dawowarshi.
shi kuwa bathroom ya nufa jik'ek'k'en kayan nashi ya cire tare ajesu gefe kana ya matsa ruwan d'umi,
sannan ya shafa mai tare da turare kana yasa wasu riga da wondo masu taushi da tsulb'i wondon iya guiwa rigar kuma mara hannu.

Cikin nitsuwa ya fito daga bathroom d'in,
gefen gado ya zaune can nesa da ita,
cikin sanyi yace.
"Kawo min tea, mai zafi."
a nitse ta mik'e ba tare data amsaba,
parlour ta nufa, cup da tea spoon ta d'auko kana da zama sai filas d'in,
cikin nitsuwa ta shigo a hankali ta diresu bisa table d'in gaban gadon,
kana ta mik'e alamar zata fita parlour,
murya can k'asa taji yace.
"Had'amin da sauri sanyi nakeji."
ba musu ta sunkuyo kana ta fara kiciniyar had'a mishin,
yayinda tuni wuyar rigarta tayi k'asa gaba d'aya rabin k'irjinta yana woje ta yadda duk wanda yake gabanta zai iya k'are mata kallo.

Shi kuwa Yusuf yatsun hannunta kawai yake kallo,
can kuma sai ya d'ago kanshi da nufin kallon fuskantar dan ya lura hannunta rawa yakeyi, gaba d'aya a tsarge take
kafin ya kai idonshi ga fuskantar kuwa sai yayi farin gani,
wani irin yam yaji tsikar jikinshi ta mik'e tsaye,
kana zuciyarshi ta buga dib-dib sau biyar cikin one second,
wata iriyar sassanyar ajiyar zuciya ya sauk'e tare da fesar da zazzafan numfashi,
kana ya lumshe idanunshi,
ita kuwa bata san halinda yake cikiba,
cikin sanyi da rawan jiki ta gama had'a mishi kamar yadda take ganin yanayi,
kana ta d'ago kanta tare da mik'a mishi cup din murya can k'asa tace.
"Gashi."
jin muryarta ne yasashi bud'e idanunshi madadin ya kalli abinda take mik'a mishi a a sai ya zubawa k'injinta ido kana yasa hannu ya ya amshi kofin,
ita kuwa inda idonshi yake tabi da kallo ganin gaba d'aya Brest nata sunyi tirtsi-tirsti a baiyane sai ta kuma yi maza ta jenye wuyan rigar tare da meda idonta ga fuskarshi,
da sauri ta kauda kanta ganin yadda ya tsuke fuska kana ya d'aga mata gira d'aya alamar tambaya ya dai?
ai cikin tarin jin kunya ta juya zata fita sai ta kuma tsaya jin yace.
"Ina zakije?."
murya can k'asa tace.
"Parlour."
"Me zakiyi?."
kamar zatayi kuka tace.
"Konciya."
kurb'ar tea d'in yayi kana yace.
"Dawo nan ki kwanta."
dole ba don tasoba ta dawo ta haura saman gadon taje ta konta inda ya nuna mata,
kana ta zubawa k'eyanshi ido.

Shi kuwa Yusuf shan tea d'in yake a nitse,
saida ya gama sannan ya mik'e ya kashe wutan d'ayakin,
sannan ya hauro saman gadon,
cikin janye blanket d'in ya konta kana ya wareshi ya rufesu gaba d'aya sai k'irjinsu zuwa kansu ne a woje,
ita kuwa Zahra baya ta juya mishi,
shima bai wani kulataba ya lumshe idonshi lokaci d'aya bacci ya fara saceshi.

Ita kuwa Zahra sam ta kasa bacci dan yadda takeji

Please Login or Register in order to submit comment